Hausa novels

Kanwar Maza Page 84 Complete Novel By Ayshercool

Page 84

 

Rumaisa ta ja numfashi, sannan ta fito da wata waya, duk ta sha jiki, screen ɗin ma duk ya tsage, ta ce “Wannan wayar, ita ta fara haɗani da takawa, kafin ƙaddara ta sake haɗa mu a karo na biyu.

Silar haɗuwarmu na farko wannan abu ne da ya shafi rayuwarmu ni da shi, bai shafi abubuwan da suke faruwa a yanzu ba”

 

Ta ɗan yi shiru sannan ta cigaba da cewa, “Kamar yadda wasu suka sani, yayyena maza ne, nice ƙarama da duk wanda ya sanni, aka yi mini shaidar rashin ji.

Wannan wayar na ɗauke da wasu abubuwa da ka iya taimakawa jami’an tsaro, saboda a rashin ji na, bani da tsoro, kuma cikin ikon Allah ranar da mu ka tafi kai ziyara dangin mahaifina, muka haɗa mota da ƴan bindiga. A cikin wayar akwai hotunan wurare da abubuwa da na yi ta ɗauka, ciki har da jakar bullet mai ɗauke da wasu lambobi, da sunan SMOKE.

A rashin ji na, na tattauna da ƴan bindigar, har shugaban su yake ce mini, ƙasa ta san da zaman su, dan kuwa akwai kason su, a kasafin kuɗi da ake duk shekara.

Kasancewar a lokacin bakomai nake ganewa ba, amma na fuskanci wasu abubuwan.

 

Zuwana garin su babana, wanda ƴan bindiga kusan suke mulkar garin, nan ma nayi wata tattaunawar da wani dattijo da aka ƙona rigar su, sai shi kaɗai, wanda shima yana da alaƙa da ƴan ta’adda.

 

Daga nan har zuwa lokacin da aka yi garkuwa da ni, abubuwan dai tamkar a mafarki, duk yadda za a bawa mutum labarin yadda abun yake, sai ya je ya gani. Na sha baƙar wahala saboda ina da taurin kai da rashin jin magana, na daku kamar ba mutum ba, saboda ban daina rashin kunya ba.

 

Kwatsam! Aka kawo matar da silarta abubuwa da dama suka faru, mace da tsohon ciki, ta din ga magiyar a bari ta tafi, ko dan cikin jikinta, aka ce a kula wannan ajiyar wakili ce”.

 

Ɗiff ɗakin yayi, Wambai ya ce “waye wakili, wane waikilin tukuna”.

 

Turaki ya ce “A daina katse ta, mu bari ta kammala tukuna”.

 

Rumaisa ta ɗora da cewa “Lokacin da ta zo ina tsaka da rashin lafiya, halin da take ciki bai dameta ba kamar ni, ta kula da ni sosai da sosai, sai dai wasu lokutan sai tayi ta kuka, idan na bata haƙuri sai ta ce; ba sace ta da aka yi ne dameta ba, mijinta, ba yadda bai yi da ita ta fasa tafiya ba amma taƙi, sai kuma sanya hannun ɗan uwanta a wurin saceta.

 

Ta bani labarin mijinta, iyayensa, yadda suke rayuwarsu, da kuma irin rayuwar da tayi a nasu gidan.

 

Ta gaya mini mahaifinta ya saka sunanta a kadararsa, kuma wasu kuɗinsa na shiga account ɗin ta, saboda ita bai taɓa mallaka mata wata kadara ba, saɓanin ƴan uwanta, da kowa yana da wani muhimmin abu da ya bashi.

 

Ta gaya mini matar mahaifin ta da yayyenta, sun uzzura mata sosai a kan hakan, kuma babu wanda ya san da zuwanta Nigeria, sai yayanta da ta gayawa, ta sanar masa ga ranar da zata je dubiya….

 

“Ƙarya ne, me ki ke nufi, Jamil ne ya sanya aka yi garkuwa da aisha, wallahi ƙarya ki ke yi, ni za a yi wa sharri, a cuci ɗa na a ɓata mana suna”

 

Wambai ya ɗagawa babar su Jamil hannu, ya dubi ruma ya ce “Wani tabbaci zaki bamu a kan haka, ta yaya zamu yarda da ke?”.

 

“Na yi wa anty aisha alƙwarurruka, bayan ta ce mini ta bani amanar mijinta da ɗan ta, duk da ƙarancin shekaruna, na fahimci abubuwa da dama a labarin da ta gaya mini” rumaisa ta basu labarin komai, har kan mutuwar aisha.

 

Ta kalli Abdallah ta ce “Bismillah”

 

Abdallah ya dawo tsakiya, ya zauna da kayan zanensa.

 

Ruma ta ce “Wannan yayana ne, kuma ƙwararre ne wurin iya zana abubuwa, da shi nake koyi, ya sanya nima na iya zane-zane, amma kasancewata ƴar koyo, zan ba shi damar ya zana wani abu, kar ace na yi son zuciya ko sharri nake son yi wa wani, yana daga in da yake zaune, zan siffanta masa abun da zai zana ɗin, Abdallah ba ya nan aka sace ni, nikaɗai aka sace, dan haka you should be good in judgment”

 

Kowa yayi shiru ya zuba musu ido, sannu a hankali take siffanta masa abubuwa yana zanawa, bai ja lokaci ba ya kammala zanen ya miƙa musu takardar da yayi zanen a kan ta.

 

Ta siffanta masa Mutanen da suka je suka ɗauki gawar aisha ne, da motarsu, da yanayin da suka ɗauki gawar.

 

A yadda rumaisa ta suffanta masa ya zana, Jamil ne a gaba cikin kayan ppe, amma yanayin tsayuwar da sashin da aka iya gani na fuskar sa, zai tabbatar maka da shi ne, idan har ka san shi.

 

A lokacin takawa ya tuna a tsukin lokacin yayi ta fama da faɗuwar gaba, da fita hayyaci, kuma Jamil yayi balagro a lokacin.

 

Mahaifiyarsa ta cigaba da bala’i, da iƙirarin wannan shegantakar banza ce ba Jamil ba ne ba.

 

Mahmud ya ce “Allah ya baku yawan rai, muna da shaida ta gaba, ban sani ba kafin ni, ko ta gaya wa wani, amma ta same ni da maganar, kuma da ni da wasu daga cikin ƴan uwanta maza muka yi aikin nan.

Akwai lambar waya da ta bani, lokacin tana magiyar a kai aisha asibiti kan ta rasu, ita ce lambar da aka kira, na bayar an yi tracking ɗin ta, haka zalika ɗan uwanta Yasir yayi tracking ɗin ta, an daina amfani da layin, amma Jamil ne yayi register da layin, Yasir na da tracking result ɗin sa, ni ma ina da nawa da police suka yi”

 

Wani daga cikin ƴan sandan ya ce “Amma wannan ai aikin police ne, mu yakamata ace mun yi shi, ko shi Adam tun da jami’in tsaro ne”.

 

“Ban ji na yarda da kowa ba da zan iya ɗaukar shaidu, masu muhimmanci na bawa ƴan sanda ba, dan a lokacin na ji takaicin ace ƙasata da jami’an tsaro amma aka kasa kuɓutar da ni, daga hannun ƴan bindiga, kuma ƴan bindiga da kansu, suka tabbatar mana da kun san da kune ku ke sauƙaƙa musu aiki, ku jami’an tsaro.

Takawa kuma ban gaya masa komai ba, saboda a wancan lokacin yana cikin damuwa da tashin hankali ne, da kuma fuskantar matsin lamba daga mutane, a yadda yake a zuciye zai iya ɓata komai a wannan lokacin.

 

Maganar ina ƙoƙarin ɓata zumunci ta hanyar haɗa husuma kuma, ina da shaida babu wanda na yi wa sharri, ranka ya daɗe wannan ledar ta gabana, cike take da kayan tsubbu da na sanya baba uwani tsohuwar hadimar ammi tonewa, kuma nayi amfani da wayar ɗaya daga cikin ma’aikatana, na naɗi duk abubuwan da aka saka ta yi mini, suma suna cikin wannan wayar na tura a ciki”.

 

Adam ya tashi jiki a matuƙar sanyaye, ya ɗauki excuse ya fita amsa waya.

 

Tun da suka shiga ake kiran wayar, sai dai da ya duba ya ga private number na.

 

A yadda ruma suka tsara da Mahmud, shi ne zai faɗi abubuwan da suka shafi ɓangaren Mummy, kutungwilar da take shiryawa amma ya kasa.

 

Turaki ya sunkuyar da kai zuciyarsa na yi masa raɗaɗi, saboda abun duniya yana ciki ɗaya da aisha, ubansu ɗaya, ya sanya aka saceta, kuma yake ta ƙoƙarin sanyawa a ɗora zargi a kan Adam, Adam ɗin da ya kasance abokinsa ɗan uwansa da suka tashi tare.

 

Kuka matar turaki take yi, ta ce “Ita haryanzu ba ta yadda da cewa Jamil zai iya aikata mummunan abu irin haka ba sharri ake yi masa”.

 

Bashir ya ce “Hajiya sai dai ki yi haƙuri, domin kuwa jami’anmu sun riga sun kama shi ma”

 

Mahmud kuwa ya dubi Jabir, sannan ya mayar da idonsa kan Hajiya Lubabatu ya ce “In faɗi me Jabir yayi, ko kuma in bari ku faɗa da kanku?”

 

Suka yi tsit babu wanda yayi magana, Mahmud ya ce “Dole ka cigaba da zama a hannun ‘yan sanda su kammala bincike”

 

Wambai ya ce lallai a nemo masa baba uwani duk in da take, gaba ɗaya falon ya hargitse da hayaniya.

 

Rumaisa ta ce “Babban roƙon da zan yi muku shi ne, kar wanda yayi ƙoƙarin yin wani abu a kan wakili, saboda nikaɗai ce shaida a kansa, sai dai in Jamil ne ya yi magana a kan sa, idan ba haka ba”.

 

Bashir ya ce “Haka ne, amma ban taɓa tsammanin wakili zai kai haka ba, saboda tsamar da ke tsakanin sa da Adam ba”

 

 

 

Adam ya ɗaga wayar tare da yin sallama “Na san ko ban yi magana ba, ka san da wanda ka ke magana, Senator mai wakili ne. Ina tayaka da ƴan team ɗin ka murnar gano suwaye SMOKE. Sai dai nikaɗai ka sani a SMOKE, amma ka sani gano smoke ba shi da wani amfani, saboda su kansu wanda ka ke tunanin zasu ɗaukar maka matakin suna cikin SMOKE.

ministan man fetur ke da shiyyar satar mai, Ɓangaren tsaro suna da kamasho a kasafin da ake yi, da wasu manyan mutane a ƙasar nan.

Talakawan da ka ke yi domin su, basu isa su yi maka komai ba, duk wata shaida da kake tunanin kana da ita a kanmu, akwai gaɓar da idan aka kai, kai ne zaka kwana a ciki, dan na san baka isa ka yi jayayya da shugabannin rundunar tsaro ba, ba ka da wata shaida a kan sa.

Dan haka kai zaka kwana a ciki, duk yaranmu da ku ka samu ku ka kama, babu wanda ya san suwaye SMOKE, kai kaɗai ka yi nasarar gano suwaye, ɗan uwanka Jamil yaron Khalifa ne, tare da shi suka yi aiki, sai dai shima bai san mune SMOKE ba, mun yi amfani da sace matarka, wurin ɗauke hankalin ka daga kanmu, kuma cikin ikon Allah ta haihu ta rasa ranta. Abu ɗaya zuwa biyu nake son gaya maka. Ka bar al’amarin nan a iya haka, idan ba haka ba zaka yi ta ranka, ko kuma ran matarka da ɗanka, dan kuwa  ita ce duk sanadin komai, dan kuwa duk motsin ku, da duk abun da take yi, muna samun labari ta ɓangaren Jamil.

Dan haka sai ka zaɓi ɗaya, fito na fito da masu ƙasa, ko kuma ka rasa rayuwarka da na matarka, dan ka san ba abu ne mai wahala ba. Sai dai fa ka yi haƙuri, domin kuwa rayuwar matarka ta salwanta kamar ko wani karabutin ɗan ƙasa, duk da kasancewar ka mai kaki, kuma jinin babbar masarauta, ire-iren yaranmu ne kisan su baya tafiya a banza. Kuma duk wani abu da zai faru Jamil ba zai taɓa furta sunana ko na ɗa na ba. Dan haka gara ka watsar da duk wani yinƙurinka, ka tattala abun da yayi saura a rayuwarka, kan mu gama ɗiaɗaita ku” ya katse wayar.

 

Duk da hatsaniyar da ta kaure a falon, yanayin da takawa ya shigo, ya sanya kowa yin shiru, wani irin gumi yake yi, jikinsa yana tsuma, kuma aka rasa mai tambayarsa meyafaru, kowa ya zuba masa ido.

 

Ruma ce ta miƙe tsaye, ta ce “Papa lafiya kuwa?”

 

Gabanta ya ƙarasa, jiki a matuƙar sanyaye ya zube a kan gwiwoyinsa ya furta “Na gaza, dama kin gaya mini, na gaza rumaisa ba laifina bane, na yi iya yina, abun ya fi ƙarfin yadda nake tunani, na barwa Allah, tun da a cikin gidanmu ma aka kware mini baya, ba ni da saurin ƙwarin gwiwa. Da izzar da tawa da sarautar tawa da komai na zube su a kan gwiwoyina, na gode rumaisa, na gode. Ke alkhairi ce ga rayuwata da ahalina, wataƙila ba dan ke ba, ba zan gane bara gurbin da suke rayuwata ba” Hawaye yake zubarwa kamar ƙaramin yaro, cike da ƙunar zuciya. Lallai faɗa da aljani ba daɗi, shiya san bai isa cigaba da fito na fito da wannan mutanen ba, in dai a Nigeria ne, mutane sun san ta’addancin Smoke, sai dai basu san suwaye ba, kuma wani abun shaidar rumaisa kawai ba zata wadatar ba, hakazalika da rayuwar rumaisa ta salwanta gara ko menene ya haƙura da shi, yarinyar tayi sacrificing alot”.

 

Rumaisa ta durƙusa ta ce “Papa dan Allah ka tashi, ka sakani a duhu, ni ban gane me ka ke nufi ba, ka tashi dan Allah, a gaban mutane ne fa”

 

Mahmud ne ya tashi ya kama Adam, ya miƙar da shi tsaye, ya ja hannunsa ya cewa rumaisa su tafi.

 

Ƴan sanda suka tattara duk wasu bayanai da suka kamata, wanda rumaisa ta bayar, da zanen Abdallah da aikin da Yasir yayi, Bashir ya karɓe ya ce sai sun kammala na su binciken tukuna, zasu gani idan da yiwuwar ba wa ƴan sanda.

 

Wambai kansa ya girgiza da jin lamarin, tausayin ɗan uwansa turaki ya kama shi.

 

Sosai babar Jamil ke kuka, tana cewa turaki ya saka baki, ya ƙaryata abun da suka faɗa, ya sanya a saki Jamil.

 

Wambai yayi mata tsawa, ya ce su tashi su tafi sai ya sake nemansu.

 

Mummy godiya ta yi wa Allah, da ba a faɗi komai a kanta ba, Hajiya Lubabatu ta zube tana yi wa wambai magiya ita ma a kan a taimaka a sanya baki, a saki Jabir.

 

Mummy ta ce “Wallahi ba ta isa ba, ba zai lalata mata ƴa ya ci bulus ba” jin abubuwa babu Allah a ciki, dagulewar lamuran yayi yawa, ya sanya wambai cewa su tafi su je su ƙarata a wurin ƴan sanda.

 

Sai da ya rage daga shi sai turaki, sannan turaki ya samu zubar da hawaye, ya daɗe matar nan tana citar da shi da Aisha, amma ba ya iya ɗaukar mataki, dama tun a farko rumaisa ta gaya masa komai, sai dai bai tabattar ba sai a yanzu.

Wambai ya dafa kafaɗarsa ya ce “Ina neman afuwarka ɗan uwana, na rashin tsayawa in fuskance ka a abubuwa da dama. Dama na san biyayya ce ta sanya ka auri Sa’adatu, sai dai wannan abu ba kai kaɗai ya shafa ba, zan yi iya ƙoƙarin ganin cewa maganar nan ba ta fita ba”

 

“Kar ka yi haka, ko kayi hakan, ko ba kayi hakan ba, dole sai maganar ta fita, Allah ya jiƙan fulani da mahaifiyarta, rumaisa kuma Allah ya yi mata kyakykyawan tukuici da ita da iyayenta.

 

 

Mahmud kai tsaye har gida ya kai Adam da rumaisa.

 

Adam na kwance a jikin rumaisa kamar uwa da ɗa, sai aikin rarrashin sa take yi, tana bashi haƙuri.

 

“Rumaisa, ni wakili yake gayawa sai in dai in yi haƙuri, ran matata ya salwanta a banza, saboda wautata da rashin hankali, kuma wai ba wani abu da zan iya yi a kai”

 

“Ban gaya maka ba? Na ce zaka iya bincike ne kawai, amma in dai a ƙasar nan ne, kar ka yi tsammanin samun adalci, mu bar wa Allah papa, you try your best, Allah shaida ne”

 

Mahmud ya ce “Takawa dan Allah ka daina kukan nan haka, kar ka tayar mata da hankali, ga ciki tana fama da shi”.

 

“Mahmud baka san me nake a zuciyata ba, ba zaka gane ba”

 

“Na sani mana, saboda sauƙaƙa maka raɗaɗin da ni da rumaisa muka yi aiki tare dan sauƙaƙa maka aiki. Ina mai baku haƙurin rashin exposing Mummy, amma ita ma very soon in sha Allah, ka yi haƙuri dan Allah”

 

Cikin kuka ya sake cewa “Jamil fa mahmud, a ɗakin Ammi muka yi wasa tare muka faɗi muka tashi, amma ni Jamil zai din ga yi wa wannan cin dunduniyar? Me nayi masa? An kashe mini mata kuma ya cigaba da bibiyata da ƙoƙarin ɗora mini sharri? Me nayi masa ne?”

 

“Baka yi masa komai ba Papa, hassadar ka fi shi komai ne kawai da kwaɗayin abun duniya ya sanya shi haɗa kai da maƙiyanka, gashi wanda ka ke yi wa kallon maƙiyin, shi ne ya taimake ka, duk lalacewar ɗan uwa naka ne papa”.

 

“Na gode mimi na gode sosai”

 

“Dan Allah ka daina yi mini wannan godiyar, ni ba abun da na yi ”

 

Mahmud ya miƙe ya ce “Daughter, ki kula mini da shi sosai dan Allah, zan je gida wurin ammi, na san tana cikin damuwa ita ma”

 

Ruma ta ce “Wait, wai ba daga gadon asibiti ka taso ba?”

 

“Rabu da ni na warware ”

 

“Amma ka yadda maman jabir tayi maka wani abu?”

 

Ya ce “Na yarda, Kamar yadda muka saka Yasir bibiyar wayar Mummy, ya kunna mini wayar da Mummy tayi da Hajiya Lubabatu. Na karɓi duk wata shaida ta hannunsa, jibi in Allah ya kaimu zai tafi wurin Anty laila, kar ma a samu wata matsala saboda aikin da ya yi mana”

 

Ruma ta ce “When are you exposing her?”

 

“Soon in sha Allah”

 

“Idan ba zaka yi ba, allow me to do it”

 

“I will in sha Allah” ya juya ya fita.

 

Haka ruma tayi ta aikin rarrashin Adam, dan abun ya dake shi sosai da sosai, duk iya tunaninsa bai ga ta ina zai iya jayayya da SMOKE ba.

 

Kuma dolensa ya haƙura da cigaba da duk wani yinƙuri a kan garkuwa da aisha, saboda rayuwar rumaisa.

 

***

Kwanaki uku kenan, gidajen sarautar suka shiga ɗimbin tashin hankali, komai ya damalmale, ba kama hannun yaro, aka gaza samo bakin zaren abubuwan da suka riga suka dagule, Kodayake ba komai ne zai gyaru ba, kasancewar wata ɓarakar ta samo asali ne tun shekarun da suka gabata, ba tare da an mayar da hankali an gyara su ba.

Kodaye rumaisa ta kawo gagarumin cigaba da kuma gyara wasu abubuwan.

 

Ba tare da wani cikakken shiri ba, Mahmud ya ce lallai sai Yasir ya tafi canada, Yasir ya so ayi bikin yaya Abubakar yana nan, amma ba dama, aikuwa sai da yayi kuka saboda rabuwa da mama da ƴan uwansa. Mahmud kuma ya ƙarfafa yin hakan ne, kar wani abu ya samu Yasir, saboda aikin da yayi musu, dan a wata fuskar laifi ne abun da ya aikata ɗin, kutse da satar bayanan mutane ba tare da izinin su ba.

Haka ya tsallaka ya tafi ya bar Nigeria.

 

Abdallah kuwa Bashir ya ce sai sun tafi da shi Abuja, mama ta tashi hankalinta ganin kamar ana yi wa yaranta ɗauki ɗaya-ɗaya, amma ya bata tabbacin babu wata damuwa, a kan Jamil ne ita ma rumaisa Adam ne zai wakilce ta, saboda tsohon cikinta.

 

Ranar da zasu tafi Abuja, takawa yayi ta rarrashin ruma, tare da bata tabbacin, Abdallah zai dawo lafiya, tun da har da shi zasu tafi.

 

Rumaisa suna ta shirin fara Waec, sai dai fa nauyin ciki ya hanata sukuni sosai, tun da ta dawo daga makaranta, mararta take yi mata ciwo da ƙafafuwanta, kuma takawa ya riga ya tafi, dama ya ce mata idan ba zata iya zaman gidan ba, ta tafi gida wurin mama ko ammi.

 

Jin ciwo yaƙi ƙarewa, ta kira Usman a waya, ta ce ya zo zata mutu.

 

Ya je ya tarar da ita duk a firgice, ta bashi mukullin ɗaya daga motocin takawa, ta ce ya kaita asibiti.

 

Suna tafe a hanya ya ce “Ko dai haihuwa zaki yi?”

 

“Edd ɗin bai cika ba fa”

 

Ya ce “Ikon Allah, muna zaune yarinyar da muka goya, muka yi wa wanka za ta haihu, haryanzu muna gararamba, bakomai akwai lokaci”

 

Bakin rumaisa bai mutu ba, sai da aka ce mata haihuwa ce a asibiti, ita dai ta san lokacin haihuwa da saura, aka ce usman ya je ya kwaso kayanta.

Maimakon ya kira mama a waya, ko ammi, kawai sai ya kira Aliyu da Huzaifa, sannan ya ƙarasa gidanta, ya ɗaukko akwatin da ta kwatanta masa, dan tuni takawa ya gama sayen komai na jariri.

 

Mamaki ya kama nurses ɗin, suka ce babu wata mace wadda za ta zauna da ita duk sai maza.

Huzaifa ya ce “Hajiya gidanmu ita kaɗai ce mace, babarmu kuma tsohuwa ce ba ta da cikakkiyar lafiya, duk abun da mata zasu yi, mu ma zamu yi”

 

Nurse ɗin ta ce “A dai duba dangi a samo wata”

 

Usman ya ce “Hajjaju, wallahi zamu iya komai, ki ƙyalemu kawai”.

 

“To ina mijinta?”

 

Aliyu ya ce “Tafiya ce ta kama shi ɗazu”

 

Ta jinjina kai ta ce “Lallai ƘANWAR MAZA”

 

Rumaisa ta sare da al’amarin, saboda tun da mama ta haifeta ba ta taɓa jin masifaffen ciwo kamar wannan ba.

 

Mai sunan baba kuwa, ganin hankalin Adam yayi wani wurin, mahmud kuma ya warware, ya sanya ya yi wa mahmud zancen, mahmud ya din ga murna, ya ce dole su je Lagos tare, dan tabattar da wannan lamari, dan haka ya ce zai yi musu booking Flight su je, su yi abun da za su yi, saboda su koma bakin aiki.

 

Mai sunan baba ya kira Huzaifa a waya, yana masa faɗan duk suna ina, gida ba kowa sai mama itakaɗai a gidan.

 

Mama ta ce “To yarinya ce ni, da lallai sai sun zauna a gida?”.

 

Huzaifa ya gaya masa in suka tafi, ba tare da ya gaya wa mama abun da ake ciki ba, ya tafi asibitin.

 

Ƙarshe sai da suka cika asibitin, Abdallah da Yasir ne kawai babu.

 

Gaba ɗaya suka zama abun kallo a asibitin, wai sun kawo ƙanwarsu haihuwa a asibiti.

 

Ruma ba ta haihu ba sai bayan magariba, babyn pre term ne, watanni bakwai da sati biyu.

 

Nurse ta fito ta ce “Kun ga ga mahaifa, ga kayan jini, dan girman Allah ku nemo mace”

 

“Sai kuma ki yi, karɓar haihuwar ma da kin matsa sai mu karɓa, ko abun da ya fi kayan jini ne zamu gyara, babarmu tsohuwa ce, bamu da ƴar uwa mace, dangi ba kowa ke son ka katse masa hidimomin sa ba, dan haka ba jini ba, ko menene zamu iya”

 

Mai sunan baba ya ce “Ina jaririn?”.

 

“Nursery zamu kai shi, sa an saka shi a kwalba”

 

Sai da suka jira aka basu damar shiga su ga ruma, tana kwance kai da ganin idonta ka san an sha gwagwarmaya.

 

Nurses suka ce a kawo mata abinci, sai a lokacin mai sunan baba ya tafi gida, ya gaya wa Iman, ruma ce ta haihu.

 

Mamaki ne ya kamata, dan washegarin taron nan sun haɗu a gidan ammi, ta ce mata haihuwarta da saura.

 

Nan da nan ta yi girki, jiki na rawa tare da mamakin haihuwar ruma, ta kira ammi ta sanar mata.

 

Ammi ta ce “Ba dai rumaisa ba, takawa ya ce da saura ai”

 

“Wallahi ammi da gaske nake, yanzu yaya umar ya shigo ya gaya mini”.

 

Nan da nan aka cika asibitin, ƴan barka, sai dai ba ganin jariri, rumaisa kuma ba baki, duk wanda yayi mata sannu, sai dai ta jinjina kai kawai, amma ta san halin tashin hankalin da ta shiga a haihuwar.

 

Mama ta kalli rumaisa ta ce “In ce dai ta bakin ki ka haifo ɗan naki, yau mata sun ga ta in da ake haihuwa” ruma tayi murmushi kawai.

 

Da ƙyar ta iya cin abincin ma, ta fara cewa ita a kawo mata ɗan ta fa, saboda lokacin da ta haife shi, tana gani ana ta fama, ya ƙi yin kuka yadda yakamata.

 

 

Abdallah ya sha tambaya a babbar headquarter Dss ta Abuja, dan sai da aka karɓi zanen aka sa shi sake yin wani, suka yi iya binciken da zasu yi, babu ko shakka Jamil ne, Wanda dama already yana hannunsu, takawa yayi kamar ya gaya musu da sanya hannun wakili, amma tayaya meye hujjarsa? Rumaisa ce kawai ta ji sun ambaci wakili, idan da wanda zai faɗi da sanya hannun wakili, to Jamil ne yakamata ya faɗa.

Duk wani report na bincike lokacin ɓatan aisha da suka yi, sai da suka gabatar da shi a wurin hukumar, laifin Jamil ya zama biyu, da na tuhumar fitar da sirrin hukumar, da kuma haɗa baki tare da yin garkuwa da ƙanwarsa, ga kuma ɓatawa Adam suna da yayi.

 

Ko da ana nunawa Jamil zanen nan, da Abdallah yayi, sai da ya zabura, saboda tabbas ya san shi ne.

 

Adam ya ce “Jamil ka tabattar wannan kai ne? Jamil me muka yi maka ni da Aisha? Idan ma wani abun na yi maka, meyasa zai shafi aisha? Ka haɗa kai da wakili ka cutar da ni?”

 

“Adam jin dalilin hakan ba shi da wani amfani a gareka, tun an riga an kama ni, sai ka je ka cigaba da rayuwarka, ka ƙyaleni. A kan me mahaifinmu zai fifita aisha a kanmu? Kuma duk wani abu na cigaba, ko na masarauta sai dai ya sanya ka a ciki alhalin gani. Wallahi da na san yarinyar nan ta gane ni, da ban barta ta rayu ba”

 

Adam yayi murmushi mai ciwo ya ce “Na gode sosai Jamil, sai dai ka sani, duk da ciwon hauka da nake fama, na tsaya ga Allah, shiyasa nake cigaba, kuma na barka da Allah Jamil, Jabir ma har shi da duk wanda ku ka cutar da ni, kamar yadda rumaisa ta faɗa, ta ce in bar ku da Allah, zan ga yadda zai yi da ku, na bar ku da Allah”

 

 

Takawa suka koma masauki shi da Abdallah, tare da Bashir.

Sosai suke bawa Adam baki, tare da bashi ƙwarin gwiwa.

A lokacin yake sanar da su abubuwan da wakili ya kira shi ya sanar da shi.

Sun girgiza sosai da sosai, Bashir ya ce “A gaskiya na girgiza, dama biri yayi kama da mutum, yadda aka kasa magance wannan Smoke ɗin. Amma ina ga kamar yadda madam ta faɗa, ka yi ƙoƙarin gano wanda suka yi maka maƙarƙashiya, amma hukunta su sai Allah”.

 

Ammi ce ta kira Adam a waya, ta sanar da shi rumaisa ta haihu, sai dai yaron an saka shi a kwalba.

 

Adam kansa abun ya ɗaure masa kai, wace irin haihuwa ana zaune ƙalau, ba tare da cikakken lokaci yayi ba.

 

Gashi bai bai gama da abuja ba, amma ya ce dole ya koma kano. Zai bar Abdallah da Bashir ko za a buƙaci wani abun, idan komai ya lafa sai su taho, shi kansa Abdallah abun ya bashi mamaki, a kan ya aka yi rumaisa ta haihu a wannan lokacin.

 

 

Sai dai cikin ƙudura ta Ubangiji mai kyauta da ƙari, yaron da mimi ta haifa ya koma ga mahaliccinsa cikin dare, dama ana ta fama, yaƙi kuka amma d girmansa ba ka ce bai kai lokacin haihuwa ba.

 

Aka yi shiru ba a gayawa mimin ba sai washegari da safe, aikuwa rumaisa ta dira rigima, ta din ga kuka, tun mama na rarrashinta, sai da ta ƙular da ita, ta fara zaginta.

 

Mama ta ce “Ba zaki rufe mini baki ba?”

 

“Mama baki san me nake ji ba ne”

 

Mama ta ce “Dan ubanki ƴaƴa biyu na binne, da zaki ce ban san me ki ke ji ba”.

 

Ammi ta ce “Maman rumaisa ki yi haƙuri, yarinya ce kuma dole za ta ji babu daɗi”

 

Aka naɗo jaririn, aka kawo wa rumaisa, kamarsa ɗaya sak da Adam.

 

Sabir da yake zaune a kusa da rumaisa ya kalleta ya ce “Mimi, baby ya buɗe ido” yayi maganar cikin yarinta.

 

“Boy babynmu ya mutu”

 

Ammi ce ta karɓi jaririn, ana jiran shigowar adam, ayi masa sutura.

 

 

Ƙarfe tara na dare Adam ya dira, ko gida bai je ba, kai tsaye asibiti ya taho, ammi tuni ta sanar masa da rasuwar yaran, dan haka hankali a tashe ya ƙarasa asibitin jikinsa duk a sanyaye.

 

Ya tarar tuni Ammi na can ita da nusaiba, mama tana wurin rumaisa.

 

Ya durƙusa suka gaisa, ammi ta tambaye shi ya ake ciki, ina Abdallah?.

 

Ya ce mata yana lafiya, yana tare da Bashir, akwai abun da zasu ƙarasa.

 

Ammi ta miƙa masa jaririn, ya karɓe shi ya buɗe zanin, kamar mai bacci, kamar sa ɗaya sak da shi duk da jikinsa yayi fari, amma da gani ka san yaron fari ne.

 

Ya miƙawa ammi shi, ya ce “Allah ya sa mai ceto ne” suka amsa da amin.

 

Mama tuni ta tashi ta bar ɗakin, ya ƙarasa gaban gadon mimi, ya zauna a kusa da ita ya riƙo hannunta.

 

Kawai ta fashe da kuka ta ce “Papa babyna ya mutu, kuma ina son shi”

 

Ya rungumota jikinsa ya ce “Am sorry mimi, ni kaina na ji ba daɗi, amma Allah ya fi mu sanin me ya dace da mu, kiyi haƙuri ki daina kuka”

 

Yayi maganar yana shafa bayanta, shi kansa ya ji mutuwar yaron, sun sanya rai da yaron sosai da sosai.

 

“Ko dai abubuwan da suka faru ne, ya sanya ki ka tashi hankalinki ki ka fara labor?”

 

Ta girgiza masa kai alamar a’a.

 

“To shikenan, Allah ya bamu mai amfani, ya sanya wannan mai ceto ne, na sanya masa sunan mahaifina Muhammad, Allah ya bamu wani” rarrashinta ya din ga yi tana jinjina masa kai.

 

Iman ta shigo ita da Usman, Usman sai da ya sunkuyar da kai, kunya ce ta kama shi, ganin yadda takawa ke zaune ya rungume mimi yana rarrashinta, ga ammi a zaune.

 

Abun da bai sani ba shi ne, har abun da ya fi haka yi suke, ita ba abun da ya dameta bane ba, domin ita kanta bata manta lokacin da aka yi mata aure, ba shirmen da ba sa yi ita da marigayi galadima, dan haka duk taɓrar da ruma take ba ta damunta.

 

Usman suka gaisa da Ammi, ammi ta ce wa Iman “Ina mai sunan baban?”

 

“Ƙarfe takwas suka tafi Lagos shi da yaya mahmud, wai wani abu za su je su yi”

 

Ammi ta ce “To, ni yanzu Mahmud tsoro nake ji, kar ya sake ɓallo mana ruwa, ba a gama da wannan tarzomar ba, kodayake tare suke da mai sunan baba, ba zai bari yayi wani rashin jin ba.

 

Aka sallami ruma daga asibiti, tare da jaddada mata yadda za ta kula da kanta, saboda ɗinkin da aka yi mata.

 

Mutane suka din ga zuwa barka, Adam yayi mursisi ya ce ruma ba zata tafi gida ba, gidanta za ta koma, a ɗaukko mai kula da ita.

Ya kafa hujja da mama ba cikakkiyar lafiya ce da ita ba.

Gashi ya samu labarin su Huzaifa ne suka kawota asibiti.

 

 

 

Mai sunan baba kuwa lokacin da suka isa lagos, suka je gidan Alhaji Aminu, suka tarar yayi tafiya, Ade kuma ta koma Gombe!.

 

READ ƘANWAR MAZA PAGE 85 END HERE


Proceed with your download by clicking the below button

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button