Halysaah Page 51 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 51…Khaleesat na fitowa parlor suka hada ido da Ummu dake kokarin kiran Alhaji Musa da wayarta cikin bacin rai, sunkuyar da kai Khaleesat tayi tana goge hawayen dake ta zuba idonta, Ummu tace “Zo ki zauna tukunna diyata” Khaleesat tayi shiru bata ce mata komai ba don har cikin ranta bata ji zata iya zama a parlon ba kamar yanda Ummu ta umarceta, amma kar tayi disrespecting matar duba da tsaya mata da tayi sanda Abdul ke ci mata mutunci yasa kawai ta duka kasan carpet kanta a kasa, Sau uku Ummu na kiran wayar Dad din Abdul, daga karshe ya daga kiran, cikin fushi ta fara koro masa abubuwan da ta zo gidan Abdul ta tarar da kuma abinda Abdul ya aikata daga karshe, Alhaji Musa dake ta sauraronta ya jira har ta gama, sannan yayi gyaran murya yace “Ai ina ganin Muhusina wannan ba issue bane da zaki shigar da kanki farat daya, ke da ba ma a kasar kike ba zuwa kawai kika yi, i don’t think it’s proper kiyi involving kanki sama ta ka, it’s not done that way, alright? kuma tunda kika ga ya saketa definitely yana ganin hakan shi ne dai dai so meye zaki damu kanki, ko mu iyayensa we are not in the rightful place to question his act, okay? decision dinsa ne, so just stay out of what u know nothing about Muhusina, ba naji kin ce flight din karfe biyu gare ki ba? Ko kin daga tafiyar taki ne?” Kasa cewa komai Ummu tayi tsabar mamaki, kana ganinta kasan she is speechless, ita dai Khaleesat kanta na kasa don ba handsfree Ummu ta saka wayar ba balle ta san abinda Dad din Abdul ke cewa, a hankali Ummu tayi ending call din ta ajiye wayar a gefen kujera don ba ma ta da amsan da zata ba ɗan uwan nata, sosai jikinta yayi sanyi, yanxu dama Family din Alhaji Musa basu canza ba daga yanda ta san su tun tale tale, don ita sai tayi shekara aru aru ba a ganta a Nigeria ba in ba muhimmin abu bane ya kawo ta, Momy ce ta bude kofar parlon fuskarta a murtuke, ashe all this while tana kofar gida tana jiran ganin Khaleesat ta fito ta bar gidan amma shiru shiru bata ga ta fito ba, Momy na kallon Khaleesat tace “In dai ba gidan ubanki bane ko na uwarki nan din tunda har ya furta ya sake ki ai kya fito ki kama gabanki, ko zaman ubanki kike yi har yanxu? Da wani abinda kika zo gidan da shi ne kika yi waya a zo da mota a kwashe maki ko yaya?” Ummu ta kalli Momy tana girgiza kai cike da takaici tace “Ki ji tsoron Allah Hajiya, ki ji tsoron haduwar ki da Allah, ke ma fa kina da yaran nan mata….” A mugun fusace Momy ta karaso cikin parlon ta dakatar da ita tana nunata da ɗan yatsa tace “Kin ga wannan family issue ne ki cire bakin ki a abinda bai shafeki ba Muhusina don ke bare ce a wannan ɓangaren, kuma ba ke kika haifar min Abdul din ba da kike neman cusa kai abinda ya shafi rayuwarsa, who are you to even interfere? Ko Musa kin zata ya isa ya hana Abdul abinda yayi niyyar zai yi ne? To wallahi ki cire bakin ki da idonki akan abinda ya shafi zuri’ata, ‘ya ya mata kuma dama ko wani shege ya haifa ai, meye a ciki” Momy na kai wa nan ta kalli Khaleesat cikin daga murya tace “Baza ki tashi ki san inda dare yayi maki ba ko sai na kira su Meemah sun fitar min da ke daga gidan nan??” Mikewa Khaleesat tayi bata bari sun hada ido da Momy ba ta nufi kofa tana tafiya a hankali, Ummu ta kasa cewa komai tana kallon Momy tana girgiza kai, sai da Khaleesat ta fita daga compound din gidan gaba daya sannan ta fara share hawayen dake sauka idonta, tunanin yanda zata koma gida bata da ko sisi ta fara yi, tafiya me nisa tayi har ta iso titin da zata samu abun hawa, daga karshe bayan jiran kusan minti sha biyar ta samu wani adaidaita sahun da zai kai ta Mariri a dubu biyu da dari biyar, in taje gida sai ta basa kudinsa, har Khaleesat ta isa gida hawaye ya ki tsaya mata a ido, ita kanta bata san yanda take ji a ranta ba game da abinda Abdul yayi mata, farin ciki take ko akasin haka har sannan ta kasa ganewa a zuciyarta, but she was deeply hurt and pained, daurewa kawai take kar ta fashe da kuka a adaidaita sahun, bayan ya tsaya dai dai kofar gidansu ta sauka tace “Za a kawo maka kudin yanxu, nagode” Daga haka ta shiga cikin gidansu, a tsakar gida ta tarar da kishiyoyin Ummanta sun gama abincin siyarwansu na yamma yara za su fita da shi talla, ta gaishesu ba tare da ta bari sun hada ido da su ba direct ta nufi dakin Ummanta, duk suka bi ta da kallo, Aunty Farida da fitowar ta daga bandaki kenan zata yi alwala don lokacin sallan La’asar yayi ta ajiye butan hannunta ta bi Khaleesat da kallo ita ma duk da Khaleesat bata ganta ba, Khaleesat na shiga dakin Ummanta ta fada jikinta ta fashe da kuka a hankali, Kasa cewa komai Umma tayi tana kallonta da mamaki, sai ga Aunty Farida ta shigo dakin ita ma, sosai gabanta ya fadi ta tsaya nan bakin kofa tana kallon Khaleesat, da kyar Umma ta dago kanta cike da karfin hali tace “Me ya faru?” Khaleesat ta kasa cewa komai tana kuka sosai, Umma da nan da nan ita ma hawaye ya cika idonta ta rungumeta bata sake ce mata komai ba ta bar ta tayi kukan me isarta, cikin sanyin jiki Aunty Farida ta karasa cikin dakin ta zauna gefen katifa tayi shiru, Umma ta goge idonta tana patting Khaleesat a baya a hankali trying to calm her amma bata hanata kukan da take ba, sun fi minti biyar a haka sai ga Mama Zubaida ta dage labulen dakin tace “To ɗan sahu dai na ta jira a mika masa kudinsa a kofar gida” Magana take amma idonta na kan Khaleesat da Umma, tsabar gulma yaron makota me adaidaita sahun ya aiko cikin gidan amma tayi karaf ta mike bayan yaron ya sanar masu ta nufo dakin Umma taki barin yaron ya karasa, don tun shigowar Khaleesat suka baza kunnuwa ko za su ji wata magana amma shiruu basu ji ko tari ba a dakin Umma, Aunty Farida ta dau handbag dinta ta fita daga dakin ta sake labulen daga hannun Mama Zubaida dake rike da shi, sannan ta fita zuwa gun mai adaidaita sahun, sai a sannan Umma ta iya daga kan Khaleesat, suna hada ido Khaleesat ta sauke jajayen idanuwanta, Umma tayi karfin halin cewa “Me ya faru Jiddah?” Khaleesat ta sauke idonta wasu hawayen na zuba idonta tace “Yace ya sakeni” Hawayen dake makale idon Umma ya zubo tana kallon Khaleesat babu ko kiftawa, Khaleesat ta rufe fuskarta jikin Umma ta fara wani sabon kukan, Umma ta rungumeta sosai, cikin rawan murya tace “Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhairi a gare ki, kiyi hakuri kin ji?” Kai kawai Khaleesat ke gyada mata tana shesshekan kuka, a haka Aunty Farida ta dawo dakin ta same su, Aunty Farida ta zauna gefen Umma tana kallonsu, Da kyar Umma ta kalleta tace “Wai sakin ta yayi” Ƙasa cewa komai Aunty Farida tayi tsabar yanda ta girgiza, ta dinga kallon Umma babu ko kiftawa, nan da nan ita ma hawaye ya cika idonta, after a while ta goge hawayen dake zuba idonta ta fita ta dau buta tayi alwalanta ta dawo ta tada sallah, Umma ta dago Khaleesat da tayi shiru a jikinta, sai taga bacci take, Khaleesat ta bude ido a hankali, Umma tace “Kin yi sallah ne?” Girgiza mata kai Khaleesat tayi, Umma tace “Ki je kiyi alwala kiyi sallah” Khaleesat ta mike tana tafiya a hankali ta fita daga dakin. Khaleesat na idar da sallah Aunty Farida na kallonta tace “A zubo maki abinci?” Khaleesat ta girgiza mata kai cikin sanyin murya tace “Na koshi” Daga haka ta mike ta hau saman gadon Ummanta ta kwanta, nan da nan bacci me nauyi ya dauketa, daga Umma har Aunty Farida babu wanda ya iya cewa komai a dakin, suna ta zaune har kusan karfe shidda, ita dai Aunty Farida tana rike da Al-qur’ani tana karatu silently a ranta, su Islam suka dawo hadda wanda suke zuwa har ranan friday, Umma ta sa su je su hura gawayi su dora girki, muryar Nenne suka ji a tsakar gida tana cewa “To Zubaida sai ki dau na annabawa don kin tafka asara lafiyayye yau, almajirai na mugun wasa suka hamɓare Suwaiba tallan da kika dora mata ya kife a kasa, su kuma suka tsere, sanin azaban da zaki mata ta taho ta sameni tana kuka kamar ranta zai fita, yanzu haka tana can gidana nace tayi zamanta, ga robobin tallan da faranti nasa an kwaso maki kayanki, ko roba daya bata siyar ba suka hambare farantin” Mama Shatu ta saki salati tana kallon Mama Zubaida da ta nemi waje ta zauna jin abinda Nenne ke cewa, Nenne ta kwashe da dariya har da kyakyatawa tace “Yaran layi kuwa duk suka wawushe abincin da ya zube a kasa suka loda ma cikin su” Daga haka ta nufi dakin Umma ta dage labulen tace “Zahra’u kina da er kuka ko kubewa ki tsam inje in ƙada miya” Umma bata yarda sun hada ido da Nenne ba tace “To bari in duba maki, Ina wuni” Nenne tayi mitsi mitsi da ido tace “Wacece wancan kuma a kwance kan katifarki?” Umma dai bata ce komai ba ta tashi zata dauko ma Nenne kubewa busasshe, Aunty Farida ta gaida Nenne ba tare da ta kalleta ba, Nenne na kallon Khaleesat tace “Wai wa nake gani kamar Khaleesah a kwance?” Aunty Farida ta ajiye Qur’anin hannunta still bata kalli Nenne ba tace “Ita ce” Nenne ta shigo dakin tace “Wato ni dai shikenan kun nuna mata banda matsayi da har zata shigo unguwan nan ta karasa gidana ta gaisheni ko? In ma bata je ta gaisheni don Allah ba ai sai tayi don ubanta Ali tunda ni na haifesa har ya haifeta” Daga Umma har Aunty Farida babu wanda yace ma Nenne komai, Nenne tace “Mijin ne ya kawota? Shi ma ai shegen ne tunda ba karasawa yake yi gidana ya gaisheni ba, banda kaddara a ina za mu san sa har mu aura masa Khaleesat mutumin da baya ganin mutuncin mu, kana masa magana yana amsa maka cikin gadara da yanga wai shi ɗan Alhaji Musa, waye bai san satan da ubansa ya zabga a gwamnati ba kafin ya koma kasuwanci, ko don muna kauda kai?” A takaice Aunty Farida tace “To sakin ta yayi…” Nenne ta juya ta kalli Aunty Farida na en sakwanni, can tace “Ban ji me kika ce ba Parida?” Aunty Farida da har hawaye ya kawo idonta tace “Sakinta Abdul din yayi” Nenne ta kasa motsi a inda take tsaye, a hankali tace “Sakin aure ko sakin me?” Aunty Farida dai bata tanka ta ba, ita dai Khaleesat na kwance tayi backing din Nenne bayan surutunta ya tasheta daga baccin da take, Nenne ta saki wani salati muryarta na rawa tace “Wato dai ɗan nawa ne ba a son a ga ya zauna lafiya a gidan duniya kamar yanda kowa yake zaune” Fita tayi ta koma tsakar gida ta rushe da kuka sosai tace “Allah ya isa tsakanina da Zahra’u da er ta, babban burin su a duniya su ga Ali ya tagayyara, babban burinsu su ga Ali cikin mawuyacin hali cikin tashin hankali, banda haka ko dukanta da zaginta Awdul ke yi a gidan bazata hakura ta zauna ba albarkacin ubanta? Shi ne har zata amshi sakin da yayi mata hannu bibbiyu ta dawo mana gidan nan domin shari’arsu da Ali ya dawo sabo?” Mama Zubaida da Mama Shatu tuni suka mike tsaye jin abinda Nenne ke cewa, cikin kuka Nenne tace “Ban taɓa ganin er da burinta taga ubanta a walakance ba, kun ga ai ta dawo taga yanda za ayi da uban nata ko furson din za a mayar da shi ko hukuncin rataya za a yanke masa, ni dai na shiga uku na lalace, Allah ya hada Ali da mata da ‘ya yan da basa tausayinsa kuma su za su yi ajalinsa, yanxu in Khaleesat er arziki ce da yace ya saketa ba sai tace babu inda zata je ba tunda bautar Allah take??” Malam Ali ne ya shigo gidan da er taliyar Hausa da ya siyo cikin Bacco bag, Nenne na ganinsa ta rushe da sabon kuka tace “Wallahi ta kashe auren ta dawo taga yanda za su yi da kai Ali” Malam Ali ya tsaya yana kallon Nenne, Nenne na fyace majina tace “Ga ta can dakin uwar a kwance tana jiran taga da wace motar za a zo a kwashe ka, dama wallahi tun da muka je gidan da parida nasan za a samu babban matsala don babu alkhairi a ran Parida, kuma in bata yi hankali ba daga ita har Zahra’un sai dai su koma kasar su, duk wanda baya son kwanciyar hankalin ɗa na to kwanciyar hankalina ne baya so wallahi” Malam Ali dai ya nemi tabarma ya zauna ya kasa cewa komai, Mama Zubaida tace “Ikon Allah, kuma abinda ya faru kenan ni Zubaida? Aure wata daya da yan kwanaki amma har an yi saki? Yanxu zawarawa har biyu garemu a gidan nan kenan?” A fusace Nenne tace “Ta zauna tayi ma uban wa zawarci a gida? Ai ko taki ko ta so sai naje na ba Awdul hakuri ya maidata dakinta don kaf zuri’armu babu wanda ya taɓa zawarci sai in mutuwa mijin yayi, to ko bakin halinta bai isa ya sa ya korota ba bai shirya ba, Khaleesah ce duk wani mummunan bakar maganar da ya zo bakinta take yaɓa ma mutum, ko kuma in ka gaya mata abinda bai gamsheta ba tayi maka wani kallon walakanci da kaskanci da tula tulan idanuwanta, wani lkcn kana mata magana tayi maka banza wannan duk mun san halinta ne ba wai sharri ba, ga nukurci kamar er sarkin kutare, to ai ba ko wani namiji bane zai dau wannan, don haka zan je in basa hakuri ya dubi girman Allah ya maidata dakinta…” Mama Shatu tace “Toh ko samun sa kika yi ai sai yayi niyya zai maidata Nenne, in zai iya ai bazai fara sakin ta ba” Wani zagi Nenne ta kundumo mata a fusace, dai dai nan aka rafka sallama a kofar gida, Malam Ali ya mike tsaye yana kallon hanyar fita gidan, Nenne tayi tsit zufa na keto mata, can ta fara kuka a hankali tace “Innalillahi wa inna ilaihi raji’una, Zahra’u dai bata zo mana pamily da alkhairi ba, kun ga har an zo tafiya da shi” Mama Zubaida ce ta yafa gyale ta nufi hanyar fita daga compound din, wani mota taga anyi parking a kofar gidan, mutumin dake tsaye kusa da motan ya nufota yana kallonta, Mama Zubaida ta gaishesa har da risinawarta, ya amsa yace “Mai gidan na ciki kuwa?” Mama Zubaida tace “To Allah ya sa dai lafiya Malam” Mutumin yace “Eh to, ni Dreban Alhaji Musa ne, an bani sako ne in kawo ma mai gidan” Mama Zubaida tace “To ni mai dakinsa ce, ni ce uwar gidansa, ko zan iya karba in mika masa, don baya jin dadi ne” Mutumin yace “To ba damuwa” Hannu yasa a aljihu ya ciro Envelope ya mika mata, ta amsa yayi mata sallama ya koma zai shiga mota, Mama Zubaida ta koma gidan tana juya takardan ita kanta sai da gabanta ya fadi don irin wannan in an kawo ai sammaci yake nufi, Nenne na ganin Envelope din hannun Mama Zubaida ta rushe da matsanancin kuka tace “Innalillahi wa inna ilaihi raji’una, shi kenan Ali a haka zai kare kenan ni Zainabu? wani takardan kotun aka sake kawo masa kenan?” Malam Ali ya amshi Envelope din hannun Mama Zubaida ya yage ya ciro takardan ciki ya warware, “Ni Abdallah Musa, na saki er ku Hauwa saki daya, biyu, uku” content din dake jikin takardan kenan, Shatu ta amshi takardan hannunsa tun da tayi karatun primary, tana duba takardan ta karanto abinda ke jiki amma fa da kyar tana in ina, Nenne ta tsaida kukan da take bayan taji Shatu ta karanto rubutun jikin takardan tace “Ji tsinanne la’ananne matsiyaci? saki har uku kamar warce ta kashe ubansa ko uwarsa? To Allah Ubangiji ya tsine masa albarka, dama banda kaddara uban me Khaleesat zata ci da ɗan barawon Gwamnati? ubansa barawon gwamnati shi kuma ɗan daba, Ai mu wannan sakin abun farin ciki ne a gare mu gaba daya tunda ba na’am muka yi da auren ba, kuma ko yau Khaleesat ta fita sai ta samu mijin nuna ma tsara da ya fi sa komai wallahi, bakin cikinmu daya zawara da ya maida ta, dama kullum da fargaban aurenta da shegen nake don har raina bana son sa babu yanda na iya ne kawai, banda jarabawa wasu iyayen kwarai ne za su dau er su su ba tsinanne irin Awdul? Khaleesah sai dai kawai tayi hakuri don cuta kam Ali ya cuceta, ya cuci Rayuwarta, don duk shi ya ja mata wannan masifa, da suka ce maka er ka suke so bayan an fito da kai furson in kai uba na gari ne sai ka cije kace sam baka yarda ba sai dai a maida ka furson din ka mutu a can, amma saboda tsoron azaban duniya ba na lahira ba ka zabi ka sadaukar da erka don samu encin kanka, to gashi nan bayan ya rabata da budurcinta ya sako mana ita, dama auren sha’awa kawai yayi da ita, Allah ya isa bamu yafe masa ba wallahi” Nenne na kai wa nan ta fashe da kuka ta jawo kujera er tsugunno ta zauna tana rera kuka sai kuma tace “To yanxu ko zuwa za muyi mu basu hakuri ya dubi girman Allah ya maidata tunda malamai sun ce saki uku a madadin daya yake” Wajen karfe goma na dare Aunty Farida ta zauna gefen Khaleesat dake zaune da cup din kunun da Umma ta dama mata tunda ta kasa cin abinci, Aunty Farida tace “Baki shanye kunun bane?” Khaleesat ta dau cup din ta ci gaba da shan kunun a hankali, Aunty Farida tayi shiru bata sake cewa komai ba tana kallon buhun abubuwan da ita da Umma suka hada zata kai ma Khaleesat gobe, don da gobe zata je wajenta, tun daga dakakken yaji, kubewa busasshe, kuka, kanwa, su citta da kanumfari, gyadar miyar, har da garin danwake da sauran abubuwa da yawa duk su ne a cikin buhun, ga turaren wuta da suka siya mata masu kyau, Aunty Farida ta sauke boyayyen ajiyar zuciya ta kalli Khaleesat da ta kasa shanye kunun hannunta, a hankali ta jawota jikinta, soothingly tace “Kiyi hakuri Daughter, Allah yasa hakan shi ne mafi alkhairi gare mu baki daya, kar ki saka komai a ranki kin ji?” Khaleesat ta gyada mata kai, Aunty Farida bata sake ce mata komai ba don ita bata ma son ta tambayi abinda ya hadasu don mayar da maganar bacin rai kawai zai kara masu, Ita dai Umma na zaune kan darduma Islam na bacci a jikinta, Maman Salame ce tayi sallama ta shigo dakin tana kallon Umma tace “Wani labari ne wannan nake ji a garin nan Zahra’u?” Umma dai tayi shiru tana kallonta, Maman Salame ta zauna kan tabarma tana kallon Aunty Farida da Khaleesat dake gefenta tace “Farida” Aunty Farida ta ɗan yi murmushi tace “Ina yini Maman Salame” Maman Salame tace “Wai da gaske ne? Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” Aunty Farida tace “A ina kika ji Maman Salame?” Maman Salame tace “Ga labari nan ya baza Mariri? Dawowata daga Wudul kenan kusan mutane biyar suke gaya min haka a hanya tun ban karasa gida ba, wallahi buhun hannuna kawai na ajiye bayan na shiga gida na yo nan” Aunty Farida tace “To Allah ya sa mu dace” Maman Salame tana kallon Khaleesat cike da tausayinta tace “Garin yaya haka Khaleesah?” Khaleesat ta sauke idanuwanta bata ce komai ba, Maman Salame tace “To Allah Ubangiji ya sa hakan shi ne mafi alkhairi gare mu baki daya, in kuma auren bai kare ba Allah ya kaddara za ki koma sai ki ga an koma” Aunty Farida ta sauke ajiyar zuciya tace “Ai saki uku ne Maman Salame” Maman Salame ta kasa cewa komai tana kallon Aunty Farida, kana ganinta kasan sosai jikinta yayi sanyi, ita dai Umma babu abinda tace a dakin, bayan kusan minti goma Maman Salame ta mike a sanyaye tace “Toh Allah ya sa mu dace, Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhairi gare mu duka, sai na shigo da safe in sha Allah” Umma tayi mata sallama, Maman Salame ta fita daga dakin rai babu dadi, sarai Umma tasan kishiyoyinta ne suka baza labarin a garin, don ko Nenne bazata gaya ma kowa wannan labarin ba ita da ta tsani tonan asiri, Aunty Farida ta sauke ajiyar zuciya don exactly tunanin da Umma take yi ita ma shi ne a ranta, Khaleesat ta kalli Aunty Farida a hankali tace “Aunty kina da number Safiyyah?” Aunty Farida tace “Ina da shi” Khaleesat tace “Ina son zan kirata ne” Aunty Farida tace “Babu kati a wayar, kuma yanxu dare yayi, ki bari gobe da safe sai kiyi magana da ita” Khaleesat ta gyada mata kai sannan ta mike tayi kwanciyarta saman gadon Umma, yaron Mama Shatu ne yayi sallama bakin kofar dakin Umma ya daga labulan yace “Wai Babanmu yace Khaleesat ta je” Umma da Aunty Farida dai sai kallon yaron suke, ya juya ya bar bakin kofar, Khaleesat ta mike zaune bayan taji abinda step brother dinta yace, tun dawowarta gidan ita ko haduwa da baban nata bata yi ba, ta sauka daga saman gadon tana gyara hulan kanta ta fita daga dakin Umma ta bi ta da kallo taji hawaye na taruwa idonta, Khaleesat na tafiya a hankali ta karasa har bakin kofar Babanta don yana zaune kan tabarma shi kadai a bakin kofar nasa, dukawa tayi daga gefen tabarman ta sunkuyar da kanta cikin sanyin murya ta gaishesa, maimakon ya amsa sai taji a hankali yace “Kiyi hakuri Jiddah, i failed you as a father, i caused you all this, but everything happened because I am a nobody, everything happened because….” Shirun da taji yayi ya sa ta daga kai ta kallesa taga hawaye a idonsa, bata san sanda ta fashe da kuka ba, yace “I am sorry for failing you daughter, albarkacin biyayyan da kika min baza ki taɓe ba in sha Allah, my wish for you since u were born was to give you the best of everything i could amma Allah bai nufa hakan ba kaddara ta fada min….”*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788 👈🏻, it’s better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*
