Hausa novels

Halysaah Page 98 By Khaleesat Haydar

Sai kusan Magrib Malam Ali ya dawo gida tare da wasu abokansa daga Mariri, bayan anyi magariba Nenne ta sa Aunty Farida ta kai masu abinci compound, Aunty Farida na komawa cikin gidan ta tafi dakin Umma, tana kallon coolern abincin dake dakin da damuwa tace “Wai har yanzu baki ci abincin ba dama Umma? Don Allah me yasa zaki sa ma kanki damuwa haka ne Umma?” Muryar Nenne suka ji tace “Don Allah ki rabu da ita Parida, ta dade bata sa ma ranta damuwa ba, wannan ai sai in iya cewa bakin ciki take ma er cikinta, tun da muka ga har aka daura auren nan to fa dama Allah ya kaddara sai an daura ba wani tsimi balle dubara, to meye bazata bi yarinya da fatan alkhairi ba da kyakkyawan addu’a, tunda dai mijinta da sarki suna son ta ba shikenan ba uwarsa taje can ta karata da mugun halinta, in taga ta haifo mata jikoki masu shiga rai sai a ga ta sakko ta so ta ko don jikokin, nima farko nan ba haka nayi ta fargaban Zahra’u zata raba ni da da na ba da na samu labarin buzuwa ce, har ya aurota ni dai bana sonta don ina tsoron asirin kabilar su haka kawai wataran ta janye min yaro ita da iyayenta, amma tana haifo Khaleesah na saduda saboda yanda yarinyar ta shiga raina da yan unguwa, to ita ma uwargabanta har abinci naga ta ci daxu, sai kece sarauniyar damuwa da kuncin yan Najeriya, to wallahi ki cire auren jikata a ranki, kada Allah ya dubi zuciyarki abinda kike tsoro ya je ya faru mu shiga uku, ai fata na gari lamiri” Nenne na kai wa nan ta fice daga dakin, Dakin Khaleesat Aunty Farida ta shiga ta sameta zaune saman darduma ta idar da sallah, Aunty Farida ta zauna gefen gado tace “kin same su a wayar?” Khaleesat ta girgiza mata kai kawai, Aunty Farida tace “Waya kuma a kashe tun safe, ai Junaid shi naga da wuya a ki samun sa….” Ita dai Khaleesat bata ce komai ba. Karfe takwas da rabi Malam Ali na zaune parlonsa sai su Umma da Aunty Farida da Nenne wanda duk shi yayi kiransu, Nenne na gyara zama tace “Wallahi har ka fara dawowa Alin ka na da, ga hasken ka sai dawowa yake” Malam Ali dai bai ce mata komai ba, babu bata lokaci ya fara sanar masu dalilin da yasa yayi kiransu gaba daya, tun da ya fara magana Nenne ta bude baki tana kallonsa, Umma da Aunty Farida ma sai kallonsa suke kamar ranan suka fara ganinsa, Nenne ta tsuke dankwalinta da kyau, cikin rashin fahimta tana zaro ido tace “Ban gane ba Ali, ba a daura auren ba kenan kake nufi ko me?” Malam Ali ya kwantar da murya yace “Shi ne nake kai ku ai Baaba, ban gama bayanina ba” Nenne ta zauna da kyau cikin kaguwa tace “Gama Ali, Innalillahi wa Inna ilaihi raji’una, muna jin ka Ali, ga jama’a duk mun gayyato mun ce gobe biki ya za mu yi da su ni Dije, amma Allah ya tsine ma wannan yaro Sagir da yace mana an daura aure” Malam Ali ya ci gaba da bayaninsa Nenne bata kara interrupting dinsa ba tana gwale ido har ya kai karshe, Umma ta juya ta kalli Aunty Farida da tsabar mamaki ita ma baki ta bude kamar Nenne tana kallon Malam Ali, Nenne fa bata fasa zare ido ba tana kallon Malam Ali duk da ya gama bayaninsa, can ta kwance dankwalin da ta tsuke tace “Kana nufin kace da wannan dan uwan nasa mara walwala wanda shi ne ainahin dan Sarkin aka daura auren?” Malam Ali yace “Haka maganar take, shi ma ai sunansa kenan Ahmad….” Nenne ta saki wani salati tana tafe hannu sai kuma ta dafe kanta, can tace “Ikon Allah yafi gaban haka Ali, dama shi bama shi da uwa a gidan ta mutu balle mu ji fargaban zata zo ta walakanta mu, yanxu dai kana nufin Yarima ne mijin Khaleesah, shi ainahin dan sarkin?” Umma ta rasa me yasa taji wani nutsuwa ya zo mata bayan bayanin mai gidanta, Aunty Farida tsabar yanda lamarin ya girgizata ta ma kasa cewa komai don ganin abun ta dinga yi kamar al’mara, Junaid kuma, Nenne ta sauke ajiyar zuciya tace “Lallai sarki ya cika mutum, wato da uwar Ahamad ta nuna masa ba shi ya haifi Ahamad din ba sai ya nuna mata me yayi zafi shima ai ya haifa, ikon Allah, to amma yanxu wannan kwamacalar ta ina za a fara Ali, shi dai wannan kamilin yaro da ko magana sai ya ga dama yake yi ma mutane bai ce fa yana son Khaleesah ba ita ma haka, to ta ina za a fara wannan lamari, sannan shi Ahamad wani hali ake son ya shiga yanda yake bala’in son yarinyar nan ace kuma yaga dan uwansa da ita a matsayin matar aure, anya Sarki bai bar baya da kura ba kuwa, kamar fa yan biyu zaka ga yaran daya me fara’a da faram faram da mutane, daya kuma dunkum, to a gaskiya uwar Ahamad er iskar mace ce mara tsoron Allah, hatsaniya kawai take son jawo masu a masarautar ta raba kan yaran nan biyu, anya Sarki yayi shawara kuwa kan ya zartar da wannan hukunci, ni dai jikata ma nake jiye ma kar ace ta raba kan yan uwa” Kuka Nenne ta fashe da shi tace “Amma Wallahi matar nan ta cuci dan ta, yaro mai biyayya zata yi ma irin wannan cutarwa ta hanasa abinda ransa ke so don son ranta, to ni dai shawarar da zan bayar a nan duk mu bar wannan bayanin a cikin ranmu, kada wannan yarinya Khaleesah ta daga mana hankali mu kanmu muji bama son auren gwara ayi mata shiru kawai tukunna….” Aunty Farida ta kalli Nenne tace “Avi mata shiru kuma Nenne? Ai wannan ba maqanar da za avi shiru bane qwara tasan abinda ke faruwadaga mana hankali da bakin dake gidan nan? to wallahi duk wanda yace ma zai gaya mata ya tada mata hankali Allah ya isa tsakanina da shi, gwara a bar mu muyi shagalinmu cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, ga yan unguwan nan duk an gayyacesu gobe za mu yi taron biki me aji, yan Mariri ma duk za su zo, to a gaya mata ga abinda ake ciki ta watsar mana da taron tunda ba hankali gareta ba ku ke nufi ko me?” Duk aka yi shiru ana kallon Nenne, Nenne tace “Ai abinda yayi shi wannan miskilin shi yayi Ahamad din ma, kuma duk ta saba da su, naga ma ta fi tsokanar shi miskilin shi ne baya ma shiga sabgar ta, Ahamad din ne kawai abun tausayi don shi aka cuta, har raina kuma ban ji dadin wannan cutarwan da uwarsa tayi masa ba, don za mu fi jin dadinsa a matsayin surki tunda shi faram faram yake akan wannan miskilin” Nenne na kai wa nan ta mike ta bar masu parlon tana kara nanata Allah ya isa in aka gaya ma Khaleesat an canza mata miji ta tarwatsa masu taro, Umma ta kalli Malam Ali tace “Sai aki sanar mata abinda ke faruwa kenan Malam? Ai yana da kyau ta san matsayarta tun wuri, wannan ba abun da za a boye mata bane gaskiya, ai ba karamin magana bace wannan” Malam Ali ya sauke ajiyar zuciya yace “To kin dai ji abinda Baaba tace, amma ni kam wannan sauyin bai dameni ba Zahra’u, don dukkaninsu mutanen kirki ne masu girmama dan Adam duk yanda yake, kuma wannan privilege ne babba Sarki yayi mana, ya mutunta mu matuka, na kuma ji dadin irin yanda ya daukeni da kuma yanda ya kirani da kansa yayi min bayanin sauyin da za a samu kafin ma ranan daurin auren, ya kuma bukaci sai da amincewata ma za ayi hakan, naji dadin wannan abu matuka, Ahamad din ne kawai abun dubawa duk da bamu san ko da yardar sa Sarki yayi hakan ba tunda shi mahaifiyarsa bata so, bana tunanin Sarki zai yi haka ba tare da sanin shi Ahmad din ba, zai iya yiwuwa shi ne ma ya bar ma Junaid din auren Khaleesah” Umma ta sauke ajiyar zuciya tace “Ni kuma kawai sai naji hankalina yafi kwanciya da daurin auren da Junaid Malam, duk da ba wai bana son Ahmad bane don yaron kirki ne shi ma amma mahaifiyarsa ce abar tsoro, nayi mugun girgiza da abinda ta zo gidan nan ta mana, tun da garin Allah ya wave vau nake fargaban kar ta sake zuwa mana in taii an daura auren” Aunty Farida dai banda hamdala babu abinda take yi hanasa yin magana me tsayi da ita, sai dai deep down tana tausayin Jawwad sosai cause bai yi deserving haka ba, ya kuma yi masu abinda baza su taba mancewa ba a sanda suke cikin bala’in Abdul da iyayensa….Ajay ya dago kansa da kyar bayan duk ya gama sauraron kalaman Mai martaba, wanda tun safe sai yanxu ya samu suka zauna da mahaifin nasa, duk da Ac’s dake parlon banda zufa babu abinda yake yi, he have never been this confuse all his life, sai goge zufan goshinsa yake da karamin towel din hannunsa, after some seconds yayi karfin halin kallon Mai martaba, murya can kasa yace “Abba i am sorry, i am so sorry, ka gafarce ni, kasan bana taba questioning dinka akan duk decision din da ka yanke kaina, ko bai min ba haka nake accepting with no complain, but why me plss? Why me Abba?? Kasan Jawwad fa….” Sai kuma ya kasa ci gaba don gaba daya he is confuse, Calmly Mai Martaba yace “You because… You are My son, ba kuma wanda ya isa yayi setting min boundary da kai ko ya nuna min ban isa ba, na kuma san baka ja da duk abinda na yanke a kanka, shi yasa ban yi shawara da kai ba, Jawwad ya nuna min kallon kanin Mahaifinsa yake min ba Mahaifinsa ba, banda haka bazai fifita maganar mahaifiyarsa sama da nawa ba ya nemi ya maida ni karamin mutum a idon mahaifin yarinya bayan rashin mutuncin da uwarsa taje har gidansu yarinyar tayi, daga karshe sai Aseeyah tayi amfani da zuwan da yayi wajena sau uku ban basa listening ears ba ta nuna dan ta yace bai son auren yanzu amma saboda ni bana nufinsa da alkhairi shi yasa nace sai anyi auren…” Murmushi Mai martaba yayi kalaman Mami na sake dawo masa, wanda tsakaninsa da ita ne wannan ba sai ya tsaya yana furta ma Junaid ba, Ajay ya girgiza masa kai cikin karfin hali yace “Junaid ba, Ajay ya girgiza masa kai cikin karfin hali yace “Amma Abba considering our bond with Jawwad, why not Waleed? I think Waleed would have been better not me” Mai martaba Vace “Saboda totally speechless, ya dafe kansa dake masa wani irin ciwo tun dazu, har a sannan kuma ganin abun yake kamar a mafarki ya kasa aminta, babu kalan tunanin da bai zo ransa ba a wannan moment din, Mai martaba yace “In kai ma ban isa da kai bane let me know Ahmad” Ajay ya daga kai ya kallesa da sauri yana girgiza kai yace “Allah ya huci zuciyar ka ranka shi dade, Who am I to question ur act? Allah ya baka hakuri, bani da ja da duk hukuncin da ka zartar” Mai martaba yace “Zaka iya tafiya, ina bukatar zan huta, inda wani shirye shiryen da kake ganin za ayi ka sanar min” Ajay ya kasa cewa komai ya mike yana kallon Abbansa, lokaci daya idanuwansa suka kada sosai, ya juya yana jan kafa ya nufi kofa ya fita daga parlon with Jay in his mind. Mami na kallon Aunty da mugun mamaki kamar me counting words dinta tace “Junaid? Kina nufin da Junaid aka daura auren? Junaid dai Fulani?” Aunty da bakin ciki ke kwance fuskarta karara tace “Zan maki karya ne Fulani, bakina da na Mai martaba ya sanar min haka wallahi don da naji jita jitar ban yarda ba da farko, kan Junaid ya mayar da auren bazawarar, shi kuma Jawwad aka daura aurensa da Hadiyah” Mami ta mike tsaye tana kallon Aunty babu ko kiftawa tace “Shi Mai martaban yayi ma Jawwad haka? Ita buduwar tasa ya aura ma dan sa don ya kuntata mana ni da shi?” Sai kuma ta fashe da kuka ta koma ta zauna, Aunty ina ma ta samu abun cewa tsabar bakin ciki da takaici, just like that ace Junaid yayi aure bayan planning dinta a kansa, aure fa, cikin kuka Mami tace “Ban yi mamakin hakan da yayi ba, yayi hakan ne don ya nuna mana iyakar mu ni da da na a gidan nan, in da kara ya kamata ya aura ma dan sa budurwar Jawwad? Wannan wani irin damuwa yake son jefa min da na ciki? Jawwad yayi deserving haka daga sarki?? Duk yanda aka yi ya samu wannan labarin shi ma don ni tun daxu nake kiransa ban samu wavarsa ba kuma baya gidan nan” Wani kukan hakin ciki ne ya sake kwace mata, daga can ta fara magana cikin bakin ciki ya kashe min da kenan shi yasa ya yanke wannan danyen hukunci? Ko tsakaninsu da bond dinsu bai duba ba yayi wannan aika aikan? Ta yaya yake son Jawwad ya rayu yana ganin warce yake so a matsayin matar Junaid? Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un, Lallai sarki ya nuna mana iyakar mu a gidan nan, kuma sai yayi da ya sanin wannan abun da yayi” Aunty ta mike ta fita zuwa bangaren Sarki, a Bedroom dinsa ta samesa ta zauna tana kallonsa cikin nutsuwa tace “Amma ranka shi dade ko dai ka sha’afa da tsarin masarautar nan ne da har ka dau bazawara ka aura ma Yarima da bai taba aure ba? Kasan irin maganganun da ake ta yi a masarautar nan yanxu haka kuwa, kuma kan kace me zance sai karade gari, tsarin dake nan tun iyaye da kakanni saboda kayi pleasing wasu can ka take wannan tsarin Mai muhimmanci ranka shi dade?” Mai martaba yace “Na soke tsarin nan daga yau a masarautar nan Fulani, shi yasa nayi using dan cikina as example wajen soke tsarin, kuma ban soke wannan tsari ba sai da na zauna da amintattu na, so ko Walid ya kawo min bazawara yau yace yana so zan aura masa, sarki na gaba zai iya maida tsarin idan ya so….” Aunty was speechless, ta dinga kallon sarki babu ko kiftawa tana jin wani mugun tsanar Khaleesah a ranta, wannan fa shi ne anyi ba ayi ba, da ta sani ai bazata taba biye Mami a fasa auren da Jawwad ba, yanxu gashi aure ya koma kan wanda bata fatan ace yau gashi da mace a matsayin matarsa a nan duniya, shikenan ana nufin shirin da take ta yi ya wargaje kenan saboda biye Mami da tayi, Mai martaba yace “Kina da sauran magana ne Fulani?” Ta sauke ajiyar zuciya tace “Duk abinda ka tsara ai ya zauna ranka shi dade, no one is in the position to question you, Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhairi” Yace “Ameen” Bayan kusan minti biyar ta mike ta fice daga dakin cikin tsananin bacin rai ta koma bangaren Mami…

Back to top button