Hausa novels

Abban Sojoji Book 2 Chapter 65 Complete Novel

Abban Sojoji Book 2 Chapter 65

The Father Of Soldier

Written By: Hafsat Bature

Ga duk maison karanta littafin Abban sojoji,zai biya 300 ne,za’a tura mashi tundaga farko har inda muka tsaya,kuma zai cigaba da samun update dinshi akai akai,ga wanda ke buƙata  zai tura mun message ta whatsapp ɗina (08103884440) kada ku bari abaku labari,

“Nima jahad,inaso naga ya rishi ɗinmu ta koma,a qagare nake da naje naganta,Allah yasa gobe ya Omar yazo ya ɗauke mu da wuri  ya kaimu gidansu,”cike da farin ciki tayi maganar,

“Da zarar mun ga rishi shikenan bamu da sauran damuwa,abu ɗaya ya rage mana shi ne ganin Mahaifiyarmu,

Inason sake ganinta bansan a wane hali take ciki ba,”jiki asanyaye Jahad ta ƙarasa maganar,

haka suka zauna tsawon daren nan suna jiran safiya tayi.

Wuraren sallar asuba,gaba daya matasan gidan suka hallara domin zuwa gabatar da sallah,daga ciki hada Uncle ɗinsu Abusufyan,a jere suka jera tare dashi,yadda kasan tsaran su Sgr haka ya koma acikin su,

A 6angaren sehrish kuwa,raɗaɗin ciwon nan ne ya kuma tashinta daga dogon baccin daya ɗauke ta,wata irin zufa ce ta shiga gangaro mata a gefen fuskarta,jikinta na ta faman kerma,daƙyar ta iya yunƙurawa ta miƙe daga zaune tana faman ƙanƙame jikinta tana dan bin dakin da kallo,sam bata lura da jacket ɗin da Rafayet ya zura mata ba,

Jin alamun ana kwankwasa ƙopar dakin yasa ta yin saurin cewa”wanene,”

Muryar azmee taji daga waje tana cewa”Ni ce sehrish,”

Bayan ta bata amsa ta turo ƙopar ta shigo,saboda a buɗe tabar mata ita daren jiya,

“Kin tashi kenan,”ta ambaci hakan yayin da take ƙarasawa daga gefen gadon nata ta zauna tana kallon fuskarta,

Muryarta na kerma tace”Aunty azmee bana jin daɗi,tun jiya nake fama da ciwon ciki sosai,bansan me yasa junaid baizo ya ɗaukeni daga school ba,ina fata dai lafiyarshi qalou ko”?tayi tambayar fuskarta ɗauke da damuwa,

Cike da mamaki Azmee tace”kamarya junaid baije ya ɗauke ki daga school ba!?nifa da kaina na ruƙe hannunki lokacin da kika dawo daga school na kawoki har cikin bedroom ɗinki sannan na shirya maki lunch ɗinki,”

Tunda azmee tasoma kora mata jawabin nan,gaba daya duk tabi ta rikice saboda bata gane inda ta dosa ba,

“Aunty azmee wlh bani bace,nifa bani da lafiya,ina can kwance cikin toilet ɗin makarantar mu,bana acikin hayyacina,har aka tashi daga skul bansani ba,sae bayan da kowa ya watse sannan naji sauƙin cikin nawa,shine har na samu na fito,lokacin da nazo bakin gate ɗin babu kowa acikin makarantar,mai gadi ne ma yace na koma daga waje na jira mai zuwa ɗaukar tawa…………..’gaba ɗaya sehrish ta kwashe duk abunda ya faru ta sanar ma Azmee har zuwa inda taji an ɗauketa an turata cikin mota,tun daga nan ne bata ƙara sanin meya faru ba,

Hankalin Azmee fa ya tashi,abun ya ɗaure mata kai,musamman da taga Uniform ajikin sehrish wannan ya ƙara tabbatar mata da cewa daga school ɗin take,tunani ta shiga yi,shin wacece kuma Yarinyar da junaid ya ɗauko daga makaranta a maimakon ita sehrish din!kodae Aljana ce ya ɗauko!tabbas zai iya yiyuwa aljannar ce in ba haka ba,kamanninsu yayi yawa komai na fuskarsu iri ɗaya,

jin sehrish na sakin nishi yasa azmee dawowa daga duniyar tunanin data tafi,cikin sauri ta ruƙo hannunta tare da cewa”Tashi mu shiga toilet na taimaka maki kiyi wanka da ruwan zafi,kafin mu fito nasan cewa sun dawo daga masallacin,zanyi ma wani daga cikinsu magana yayi ma babban yayansu magana akan ya baki maganin da zaki sha ki samu sauki,

a hankali tasamu ta sauko daga saman gadon tabi azmee suka shige cikin toilet din,daga baya azmee ta fito ta barta acikin toilet din tana ƙarasa wankan,

Zagaye ɗakin nata Azmee ta shiga yi,yayin da take cigaba da tunanin Wacece wannan yarinyar da tazo gidan ɗazu mai irin fuskar sehrish komai da komai,tabbas mutunce ba aljana ba,abun yayi confusing dinta,

amma me yasa ta tambayeni ya Omar na nan amaimakon Sgr!

Azmee ce ta jefa ma kanta wannan tambayar,lokaci guda ta tuna da twins ɗin da Omar yace zai kawo gidan Abusufyan ɗinsu,tabbas ba shakka yarinyar tasan Marshal Omar shiyasa har ta tambayeta shi,

cike da mamaki azmee ta ɗan tsaya daga zagayen da take yi na wani lokaci ta ɗanyi shiru tana nazarin wani abu kafin daga bisani tace”in har dagaske ne abunda nake hasashe,wannan yaran da Omar yake Ruƙo a wurinshi,ƴan uwan sehrish ne!dama ta ta6a sanar dani cewa su ƴan ukune,kuma kamanninsu ɗaya sak!ina tunanin cewa Yaran suma a makarantarsu sehrish suke,wannan dalilin ne yasa junaid yayi kuskuren ɗauko yarinyar amaimakon sehrish !”

Bata da tabbacin abunda take hasashe ko gaskiya ne,amma ranta na bata cewa tabbas haka ne!

fitowar sehrish daga cikin toilet,yasa azmee juyawa tana kallonta,daƙyar take iya ɗaga kafarta,jikinta na sanye da inners farare,half vest da kuma white short wanda bai kai guiwarta ba,

Ganin yadda take tafiya tana dafe saitin mararta yasa azmee,ƙarasawa wurinta da sauri ta janyo ta ajikinta,ta taimaka mata harta haye saman gadon,abu kamar wasa sehrish ta soma yarfa hannu tana ambaton sunan Allah abakinta,daga bisani kuma tashiga bubbuga ƙafafunta asaman gadon tana matse cikin nata,

Cikin fita hayyaci take cewa”Aunty zan mutu!cikina zafi yake mun,kamar ana ƙona ƴan hanjin cikina,ko’ina raɗaɗi yakeyi mun,”

Jin wannan maganar ta sehrish ba ƙaramin tayar mata da hankali yayi ba,

juyawa tayi da sauri ta fuce daga cikin ɗakin,kai tsaye ta nufi main palour din tana jiran ƙarasowar su,saboda taji dirar motocinsu alamar sun shigo cikin gidan,

Marshal Omar ne tare da Sgr suka fara shigowa cikin babban falon,yayin da Uncle abusufyan ke abayansu shi da Abbansu sae Junaid dake ruƙe da hannun Uncle din nasu acikin nashi,

ganin azmee atsaye cikin damuwa yasa Omar cewa”meya faru ne naganki atsaye nan?

tsayawa da tafiyar suka yi gaba daya suna jiran jin amsarta,

hankali amatuƙar tashe azmee tace”Sehrish ce bata jin daɗi sosai,tana acan ɗaki na barota tana ta kuka tana cewa zata mutu..dan Allah a taimaka mata,”

Omar yace”subhanallahi!meya ke damunta ne?

“Ciwon ciki ne,”ta bashi amsa,matsowa Abbansu yayi kusa dasu Omar yace”Tasha magani ne”?

“Bata sha komai ba,”azmee ta amsa mashi,

Mayar da idanunshi yayi kan Sgr dake tsaye ya goya hannayenshi asaman ƙirjinshi,

Yace”Ko zaka iya taimakawa ka duba mana ita ne?in yaso ko allura ce sae ayi mata,zata fi samun relief ɗin ciwon nata”

Download>>> Dr Bobby Hausa Novel Document

sakin hannayenshi yayi daga saman chest dinshi,sannan ya kalli azmee tare da cewa”muje ɗakin nata”

murmushi Abbansu ya ɗan saki ba ƙaramin daɗi yaji ba,daya amince zai duba ta,shi fa yanzu abbansu kallon mata da miji yake yi masu,tun ranar daya fara kamasu manne da juna,tun daga ranar ya daina yi masu kallon wai saurayi da budurwa,fatihar ce kawai ba’a kaiga shafawa ba,

“Yaya hussein wai wacece bata da lafiya ne”?Abusufyan ne yayi mashi tambayar a lokacin da suke wucewa daga cikin,

Fuskar abba ɗauke da murmushi yace”Yarinyar dake taya azmee aiki ce,itace ɗazu junaid yake magana akan ba’a ganta ba,hankalinmu duk ya tashi da 6atanta,cikin ikon Allah sae gata an samu rafayet ya dawo da ita cikin gidan nan,”

Abusufyan yace”Allah ya bata lafiya,”

Abba ya amsa mashi da ameen,

Daganan suka raba hanya dashi,kowa ya wuce bedroom ɗinshi,

 

Acan kuwa,bayan Azmee tayi ma sgr jagora har izuwa ɗakin sehrish,ita tafara shiga sannan ya bi bayanta har izuwa wurin gadonta,karo na farko kenan da Sgr yafara shiga ɗakin Sehrish,lokacin ne yama san inda dakin yake,tsayawa yayi daga tsaye yana kallonta,sae faman juyi takeyi atsakiyar gadon gaba ɗaya tagama fita hayyacinta saboda raɗaɗin ciwon cikinta,

Hannu azmee tasa tare da janyo bargo ta lullu6e mata jikinta,ganin yarda surar jikinta ta fito sosai,

“Wane kalar ciwon ciki ne takeyi”?yayi maganar ba tare daya kalli azmee ba,yana da tabbacin cewa menstruation ne,amma yafiso yaji daga bakinta,

“Na al’ada ne,”azmee ta bashi amsa,

“Okey,”ya ambaci hakan tare da juyawa ya fuce daga ɗakin,

Komawa azmee tayi tare da zama daga gefen sehrish tana kallonta gwanin ban tausayi,Ba ƙaramar wahala tasha ba,ta jigata sosai,ta wani 6angaren kuma taji daɗi da Sgr ne zai dubata,don tasan cewa zata samu kyakkyawar kulawa awurinshi,zaiyi mata abunda ya dace ne,”

Karanta>>> Fassarar Mafarkin Ruwan Sama

15mins da fitar shi,sae gashi ya dawo cikin ɗakin hannunshi ɗauke da Allura har ya ɗura ruwan allurar acikin sirinjin,

Ganin shi yasa azmee mikewa daga zaunen da take gefen gadon ta bashi wuri don ya samu damar yi mata allurar,

Zama yayi daga gefen gadon tare da ruƙo hannun sehrish da ta fito dashi daga cikin bargon da azmee ta rufa mata ajikinta sae faman hargowa take tana ambaton cikinta,

Yana ƙokarin tsira mata allurar,ta ware idanunta sosai kai tsaye suka sauka akan Syringe ɗin dake hannunshi,duk da bata acikin hayyacinta amma ta gane cewa Allura ce fa za’ayi mata,

a firgice sehrish ta fusge hannunta tare da yin wurgi da bargon da azmee ta yafa mata,gefe guda ta jefar dashi,matse kanta tayi ajikin headboard na gadon tana faman shesshekar kuka tana cewa”banaso!dan Allah ku kyaleni kada kuyi mun allura,”gaba daya duk tabi ta firgice dama ta tsani allura arayuwarta mugun tsoranta take ji,

sanin cewa Sgr yana da bad temper bazai iya jure koke-koken da sehrish keyi mashi ba,muddin taƙi tsayawa zai iya kwashe ta da mari,don ta dawo dai dai,

Cikin sauri azmee tace”Zan iya ruƙe maka ita?

“E” ya bata amsa ataƙaice,

Wucewa saman gadon azmee tayi tare da rurruke sehrish,aikuwa a gigice sehrish ta shiga kokawar kwace kwanta hada gartsa mata cizo a hannunta,

Cire hannunta tayi daga ruƙon da tayi ma sehrish,saboda taji zafin cizon da tayi mata,

Ganin haka yasa sgr bata Umarnin ta fita daga ɗakin,

Saukowa azmee tayi daga saman gadon,tare da kama hanya ta fuce daga cikin dakin,

A waje ta samu junaid atsaye sae faman zagaye yake yi a wurin ɗakunan nasu,bawan Allah duk ya rasa natsuwarshi tunda yaji cewar Sehrish bata da lafiya,

“Junaid,” jin an ambaci sunanshi yasa shi yin firgit ya juya yana kallon azmee dake tsaye a kopar dakin,

Ƙarasawa yayi wurinta fuskarshi ɗauke da damuwa yace”Aunty azmee wai meya faru da sehrish ne?ina taje ne?duk nabi na ruɗe wlh,bansan ta yadda akai ta sanya ƙafa tabar gidan nan ba,nifa dakaina na ɗaukota daga school na kawota gida,”

Karanta>>> Amfanin Hulba A Jikin Mace Yana Da Kyau Yan Mata Su Karanta

ruƙo hannunshi azmee tayi taja shi daga dan gefe suna fuskantar juna tace”Junaid ka kwantar da hankalinka,ba abunda ya faru da sehrish,stomach pain ne kawai kuma insha Allah zata ji sauƙi ne,sannan maganar fitar sehrish daga cikin gidan nan,kada kayi confusing kanka,ka manta da wannan kawai,komai ya wuce,”

ajiyar zuciya ya shiga saukewa,har cikin ranshi yaji daɗin bayanin da azmee tayi mashi,

“Yanzu kaje ka kwanta mana,zuwa da safe in yaso sae kazo ka dubata ko”?

cike da shagwa6a yace”Aunty azmee kona koma ɗaki bazan iya bacci ba,in har ban sanyata acikin idanuna ba,’

Murmushi azmee tayi tace”ummm romeo kenan shugaban ƴan soyayya,dama tunda na ganka nan tsaye nasan cewa abunne ya motsa,”

Sunnar da kai ƙasa junaid yayi yana faman sakin murmushi,

A nan suka tsaya suna cigaba da yin fira atsakaninsu,janye mashi hankali azmee ta dinga yi saboda ta lura da yadda yake firgita duk in yaji sautin kukan sehrish,daƙyar tasamu junaid ya wuce bedroom dinshi itama ta wuce nata ɗakin,

suna barin wurin hayaam ta fito daga ɗakinta,cikin sanɗa take tafiya harta ƙaraso wurin kopar ɗakin sehrish,anan ta tsaya tare da jingina kanta ajikin ƙopar ta kasa kunnanta tana sauraran kukan da sehrish keyi,duk atunaninta ita kaɗaice acikin ɗakin take kuka,hakan yasa taji daɗi acikin ranta har tana cewa”Shegiyar Allah yasa ta mutu kowa ya huta,wlh bazan shiga in taimaketa ba,koda ciwon zai kashe ta,

Karanta>>> Maganin Olsa Sahihi Da Izinin Allah

acan cikin ɗakin kuwa duk yadda sgr yaso sehrish ta tsaya yayi mata allurar abun ya faskara,taƙi bashi haɗin kai,sae faman yawo take mashi da hankali,wannan ne yasa shi fusata har ya daka mata tsawa,wannan tsawar da sgr ya daka ma sehrish yasa ta dawo cikin hayyacinta sosai,waro ido waje tayi hankalinta a matuƙar tashe take kallon sgr,abun kamar a mafarki take kallonshi,wai dama shine!taya akai ya shigo ɗakinta?

a tsananin tsorace take binshi da kallo,jallabiya ce fara ajikinshi mai gajeran hannu,hakan ya bayyana damtsen hannun nan nashi,

zazzare ido tashiga yi tana kallon kyakkyawar fuskarshi,

Matsawa sgr yayi kusa da ita,suna facing din juna face to face,a hankali yake bin fuskarta da kallo yayin da itama take ƙare ma tashi kallo,har lokacin kokwanto takeyi anya shine da kanshi ya shigo ɗakinta,Sgr sukutum da guda yau a bedroom ɗinta zaune gefen gadonta,a kusa da ita?

Hmmmmm ina labarin Hayaam dake la6e ajikin ƙopar ɗakin tana sauraron kukan Sehrish,ae tun lokacin da taji muryar sgr ya daka ma sehrish tsawa,jinjina kai ta shiga yi tana faman sakin huci kamar wata zakanya saboda tsabar 6acin rai da takaici,acikin ranta tashiga cewa”lallaima yarinyar nan,wato harta samu matsayin da sgr zai dinga takawa da ƙafafunshi yana shiga ɗakinta,’

ɗagowa tayi tare da aza hannunta asaman kanta tana cewa”nashiga uku ni yau hayaam bansan ya zanyi da yarinyar can ba,tana shigar min gonata!tabbas dole nayi wani abu akanta,bazan ƙyaleta ba tayi nasara akaina ba,

Tana cikin wannan zancen zucin nata ta jiyo muryar sgr yana magana daga cikin ɗakin,cikin sauri ta kasa kunne tana sauraron me yake ce ma sehrish ɗin,

“Bana son wannan koke koken da kikeyi mun,kamar zan rabaki da ranki ne,”!.

tsit Sehrish tayi tana sauraranshi,yayin da take bin pink lips ɗinshi da kallo,

Cigaba da magana yayi anatse yace”idan kika natsu,ba da zafi zan maki ba,a hankali zanyi maki,batare da kowa ya ji mu ba,”

tashin hankali tunda hayaam taji wannan zancen da Sgr yakeyi ma sehrish nan take taji gabanta ya faɗi rass,zullumi ta shiga yi gabanta na faduwa,duk atunaninta wani mummunan abunne sgr da sehrish ke aikatawa,gaba daya ta rasa natsuwarta,kamar ta fada cikin ɗakin  taga me suke aikatawa haka take ji aranta,zuciyarta sae faman azalzalarta takeyi tana tunzurata akan ta shiga taga me sukeyi,

Yanayin yarda sgr keyi mata magana cikin sanyin murya,yasa taji wani irin yanayi atare da ita,da kanta ta miƙa mashi hannunta don yayi mata allurar,

Hannunshi yasa tare da ruƙo wrist din hannunta,sannu a hankali ya zura allurar a cikin jijiyar hannun nata,lokacin da tsinin allurar ya ratsa cikin jijiyar,a ɗan razane sehrish ta saki ƴar ƙara tare da runtse idanunta tana faman cizon la66anta,

a hankali sgr ya ɗago da blue eyes ɗinshi yana kallon fuskar sehrish,zuba mata ido yayi yana kallon eye lashes ɗin idanunta masu tsayin gaske,kafin ya mayar da idanun nashi akan la66anta dake ta faman kerma,tana ɗan cizon gefensu da Teeth ɗinta,

gaba daya ya gaza control ɗin kanshi,har ya gaza janye idanunshi daga kallon la66anta da yake yi,ba ƙaramin yanayi ta jefa shi ba,cos she looks so sexy a wannan lokacin komai tayi bashi sha’awa yake yi,

siraran hawaye ne suka shiga gangarowa daga cikin idanunta,batare da saninshi ba yakai hannu zai share mata hawayen,buɗe idanuwan da tayi ne yasa shi dakatawa tare da janye hannunshi,

ya kawar da kanshi gefe guda a lokacin ya kammala yi mata allurar,

tayi danasanin buɗe idanuwanta da tayi,taso ace ya sanya hannayen shi ya share mata hawayen,ko ba komai zata ajiye wannan ranar a matsayin ɗaya daga cikin ranakun da suka kafa tarihi a rayuwarta,

Ganin ya miƙe tsaye tare da kama hanyar fita daga cikin bedroom ɗin nata yasa tayi saurin cewa”ngd da taimakon da kayi mun,”

Batare da ya juyo ya kalleta ba yace”get well soon”

Yana ƙarasa maganar tashi yasa hannu ya ruƙe handle ɗin ƙopar zai buɗe door ɗin ɗakin,jin motsin shi yasa jiki na rawa hayaam ta watsa da gudu izuwa cikin bedroom ɗinta,

Upstairs ya nufa ya wuce part ɗinshi a wani irin yanayi ya faɗa saman katafaren gadonshi,yayin da idanunshi ke kallon saman ceiling ɗin ɗakin nashi,

Download>>> Bintu Ɗiyar Bayi Ce Complete Document

Wani abu ne ya faɗo mashi aranshi,lokacin suna da shekaru goma sha wani abu a duniya,a katafaren gidansu dake a los angeles California,su shida suke rayuwa acikin gidan bayan masu aikin dake kula dasu,Uncle donald tare da matar shi wadda suke kira da Mommy,sae Ƴa’ƴansu mata guda biyu Eva da jessy,Sae shi tare da Omar,wata irin rayuwar farin ciki sukeyi acikin gidan,saboda tarairayar da suke samu a wurin matar uncle ɗinsu kamar ita ta haifesu,Allah ya jarabceta da son su,ko ƴa’ƴan data haifa batayi masu irin son da takeyi ma Sgr da Omar,A wannan lokacin Uncle Abusufyan ya ta6a yi masu zuwan bazata,sunyi murna kamar kamar me,suka manne mashi suna tambayarshi ina tsarabar da yazo masu da ita,

Hannu yasa tare da ciro wasu hotuna biyu daga cikin aljihunshi,ya aza hotunan asaman table ɗin gabanshi,ya kifa hotunan yarda bazasu iya tantance hotunan menene ba,

yana daga zaune saman 3 seater,su kuma suna atsaye ruƙe da qugu suna jiran ganin wannan tsarabar da yazo masu da ita,maimakon suga chocolate suga iyayen shan zaƙi sae suka ga Hotuna guda biyu,nan take suka ɗaure fuskokinsu,atare suka haɗa baki wurin tambayar shi menene wannan yake 6oye masu acikin hotunan

Abusufyan yace”so nake kowanne daga cikinku ya za6i ɗaya daga cikin hotunan,kuma duk abunda mutun ya za6a dole ya rungume shi hannu bibbiyu,kun amince da hakan”?

“Yeah,”suka amsa mashi,,

“Waye zai fara canka acikin ku”?

Shiru rafayet yayi tare da maƙe kafaɗarshi alamar bazai fara ɗauka ba,Kallon Omar Abusufyan yayi yana jiran jin shi mai zaice ko zai fara ɗauka ne,

da yake shi mai sauƙin kaine,baiyi gardama ba,ya sanya hannu tare da ɗaukar ɗaya daga cikin hotunan,juyo da hoton yayi ta gaba yana kallon shi,

Kyakkyawar yarinyace,ƴar ƙarama bazata wuce 5 years ba,tana tsaye akayi mata hoton,’

Murmushi Omar ya shiga saki yana kallon hoton,

“Saura kai Mr arrogant,pick d other one,”yayi maganar cike da zolaya yana kallon Sgr,

tsuke baki yayi tare da miƙa hannunshi ya ɗauki ɗayan hoton daya rage asaman table ɗin,ɗago dashi yayi tare da juyo da gaban hoton yana kallonshi,

Koda yayi arba da hoton yarinyar daya dauka nan take ya ɗaure fuskarshi ya haɗe girar idanunshi alamar ranshi ya 6aci,

Muryarshi tamkar zaiyi kuka yace uncle I don’t like her, she’s ugly, she doesn’t have even shoes on her feet,ko gashin kanta ma bata iya gyarawa,ƙazama ce”

Fashewa da dariya Omar yayi hada dafe cikin shi,hakan ya ƙara fusata sgr,

Abusufyan kuwa,ruƙo hannunshi yayi cikin sanyin murya yace”Look rafayet,itama ba laifinta bane kuma bada son ranta ta kasance haka ba,kai kana da gata ne shiyasa kake ganin cewa ita da son ranta ta kasance hakan,Bata da wanda zai gyara mata gashin kan nata ne,babu wanda zai janyota ajikinshi yayi mata wanka ne,kuma kaga ƙarama ce bata da hankalin da zata iya gyara jikinta da kanta,dole sai an nuna mata ga yadda zatayi sannan tayi…..’

Shiru Sgr yayi yana faman hura hanci shi an haɗa shi da mahaukaciya,ɗago da hoton yayi yana ƙare mashi kallo kafin ya kuma kallon uncle ɗin nasu yace”Ita bata da Mommy ne?ina daddyn ta yake ne?ko basu raye ne”?ya jera mashi tambayoyin yana jiran amsar su,

Abusufyan yace”bata dasu, marainiya ce,amma yanzu ta samu,in har ka amince zaka aureta,kaga shi kenan zaka ruƙe ta amana,kuma zaka dinga gyara mata gashin kanta,kana sanya mata takalma,har ma wanka sai kayi mata….’tun kafin abusufyan ya ƙarasa maganar Sgr ya bubbuga ƙafafunshi rae a6ace yake cewa”Uncle I can’t marry her,but since I hv a lot of money i will give her to buy whatever she wants”

Murmushi Abusufyan yayi yana kallon shi,wato shi bazai aureta ba,amman tunda yana da kudi da yawa zai bata kuɗi ta sayi duk wani abu da take so,yaji daɗin jin maganarshi,koba komai yaron yana da tausayi ta wani 6angaren,dama ya jarabasu ne don yaga reaction ɗin kowannansu,kuma ya samu abunda yake so,

Har kawo yanzu,wannan hoton da uncle abusufyan ya basu,yana nan a wurinsu kowannansu ya adana hoton kamar yarda uncle ɗin nasu ya roƙesu akan su ajiye hotunan a wurinsu,karsu yadda su,’

“Har yau uncle abusufyan,bai faɗamun wace yarinya ce ajikin photon nan ba,inason nasan kowacece ita,saboda in taimaketa,kamar yarda nayi niyyar taimakonta,” Sgr ya fadi hakan.

Lumshe idanunshi yayi tare da gyara kwanciyarshi,nan take bacci ya ɗauke shi,

*su wanene acikin hotunan da Uncle abusufyan ya basu*!

 

 

_Ayi mun uziri,in bansamu damar yin posting gobe ba,abubuwa sunyi mun yawa sosai,bansan ya zanyi ba,amma koda ace banyi a gobe ba zan yi ƙoƙarin biyan bashin wanda banyi ba,tunda ina ƙoƙarin ganin na Kammala littafinn ne insha Allah Zan yi kokarin sanya maku long pages,sannan kuma Labarinsu sehrish da nake tacewa za’ayi za’ayi lokacin shi yazo dama akwai abunda nake jira ne_

Domin Sauke Littafin book 3 Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

 

Back to top button