Mijin Marigayiya Page 19 Hausa Novel
‘Ai Baito sai da rana take zuwa, kuma safiya tana yi Hajia take cewa mu tafi gidan Anti Jidda muyi wanka a can muci abinci a can. Kuma idan mun je sai Anti Jiddan tace babu abinci sai dai kawi wata ran ta bamu bakin shayi da ragowar kosai ko doya. Idan kuma mutum ya dameta sai ta yi masa fada, itama Shukra da Nasreen ragowar kunu ne kawai ko kuma idan an yi sa a an rage abincin shan ruwa shine ake basu.’Mamakinsa ya karu, yace ‘A’a, ai na turowa Anti Jidda kudi a sayi indomie da cornflakes harda madara, ba a siya ba ko me ya faru da su.’Ya dan zaro ido ‘Tab, tunda muka zo bamu taba cin indomie ba ko cornfalkes. In an sha ruwa dai da yake muna gidan hjia shine aka hada mana shayi da madara harda kwai ma ake soya mana da kaza, amma dai da rana babu wanda yake bamu abinci. A wajen Hajia ma muke shan ruwa tare da ita da Alhaji.’Yayi matukar mamaki kuma ya ji tausayin Habib; amma kuma yana matukar mamakin yanda za ayi ace Yaya Jidda ta bar masa yara da yunwa. Ranar da ya kawosu bayan ya tafi ta kirawoshi tana tambayarsa kudi a sayi kayan shayi da indomie, kua a take ya tura mata naira dubu goma don a siyo da wuri. To me ya faru da kudin da ake hora masa yara da yunwa?Tare suka jero da Habib din suka nufi cikin gidan, suna daf da shiga suka ci karo da Afaf tare da Shukra da Nasreen kowacce sanye da hijabinta, nan da nan suka fada jikinsa suna murna ‘Abba, Abba.’Bayan ya amsa gaisuwarsu yace ‘Ina zaku je?’Afaf tace ‘Gidan Anti Jidda zamu je suyi breakfast.’‘Ke kina azumin ne?’‘Eh ina yi.’‘To ku zo mu wuce ciki kuyi breakfast din a nan.’Nasreen tayi dariya tace ‘Tab ai babu abincin, da an gama shan ruwa Baito take juye duk wani ragowar abinci ta tafi da shi. Kuma Hajia cewa take muje gidan Anti Jidda a dafa mana indomie amma idan mun je ba a dafa bana, bakin shayi ake bamu da ragowar kosai ko kunu.’Ya dauki shukra ya ja hannun Nasreen yana cewa ‘ku zo muje.’Bayan sun gaisa da Hajia tace ‘To ka barsu suje gidan Jidda ta dafa musu indomie din su karya sai su dawo ko? Yunwa suke ji gasu nan.’Nan suka yiwa Hajia bayanin abinda ake basu idan suka je gidan yaya jidda; itama tayi mamaki sosai. Tace ‘To me yasa baku taba fada ba?’Nasreen ta zumburo baki tace ‘Yaya Meena ce tace duk wanda ya fada sai taci ubansa ta karta masa rashin mutunci don ta san mu da tsinin baki.’Daga Hajiyan har Mustaphan mamaki ne ya kamasu, Meena itace babbar ‘yar Yaya Jidda. To amma me zai sa tayi haka bayan Jiddan da kanta ta gayawa Hajia ya turo kudin indomie da kayan karin kumallon yaran?Tace ‘Lallai daga Aminan har Jiddan zasu zo su sameni.’Saboda tsabar takaici Mustapha kasa magana yayi. A nan ya sake bada kudi Habib ya fita kanti ya siyo musu indomie, yana kawowa Afaf ta dafa musu da kwai tunda dama da akwai kwai a gidan. Haka ya saka su a gaba duka saida suka karya azumin suka ci suka koshi.Nan ya zauna suka cigaba da hira wajen Hajia tunda shima Alhaji ya fice; sai dai har la’asar ta kawo jiki Yaya Jidda bata zo gidan ba saboda yaronta Abdallah ya shigo gidan lokacin suna cin indomie shima ya zauna aka ci da shi kuma yana gamawa ya koma gida ya gayawa uwarsu Abban Afaf ya zo harma ya saan dafa musu indomie da kwai. Don haka tana sanetaki zuwa saboda rashin gaskiya.Haka ya wuni a gidan ransa a bace yana tunanin mafita; tabbas duk Khadeeja ce ta janyo masa wannan wulakancin. Tunda da ta dawo babu wanda zai yi wa yaransa wannan wulakancin, Kuma shi ya tabbatar ta sami lafiya ko daga ganinta ma ai an San kalau takeTo yanzu ya zai yi da yaran? Idan ya tafi dasu ba zasu barshi ya zauna a nutse ba, kuma ma ya san Hajia ba zata yarda ya tafi dasu gida su zauna tare da shi ba. Sai dai kamar yanda ta riga ta fada yaje ya siyo abubuwan da suke bukata ya kawo ita sai ta dinga dafa musu kafin Baito ta zo; domin itama Baito din mijinta ne bashi da lafiya take jinyarsa shi yasa ba zata iya zuwa da safe ba.La’asar tana matsowa ranshi ya sake baci, kuma har loakcin Yaya Jidda bata iso ba. Bayan ya idar da sallar la’asar yana zaune a kan dadduma yana tunanin mafita Habib ya shigo ya sameshi. Bai dade da zama ba yace ‘Abba da ma ka kaimu gidan Mama, ka ga dama mun dade bamu je ba tunda muka koma gida.’‘Um, to ai da sallah zaku je ko? Ko ba kwa son zama a nan din ne? ai ka ga yanzu Hajia da kanta zata dinga baku breakfast din ko?’‘Um, nan din ma muna son zama amma can din ma muna so, in ya so idan Anti Khadeeja ta dawo sai mu dawo.’Nan sauran yaran suka shigo suka saka shi a gaba a kan su gidan Mama suke so suje; shi din ma yana so ya kaisu don ya san ba za a barsu da yunwa a can ba tunda ko babu mai aiki akwai ‘yan mata. To amma yanzu hakan yana nufin kenan ba za a iya rike masa yaransa a gidansu ba ko me? Ita kuma Yaya Jidda me take nufi? Gashi taki zuwa, shi kuma ba zai je gidanta ba don ya fi so tazo suyi a gaban Hajia. Haka dai yaran nan suka saka shi a gaba dole ya amsa zai wuce da su. Itama Hajia da ya gaya mata zai kaisu sai da ta nuna bacin ranta don gani take kamar fushi yayi da yanda ya sami yaran, sai da Alhaji ya sa baki kuma suka ga nasreen tana nema ta saka musu kuka sannan suka bari ya kwashi yaran suka wuce gidan Maman su Ma’u.Duk da bai ce mata zai zo yau din ba amma dai haka kawai zuciyarta take gaya mata zai zo tunda an bude gari kuma tun wancan lokacin da aka bude gari basu hadu ba. Ta san dai yana jin haushinta daga yanda yake amsa wayarta amma ta nutsu a zuciyarta cewa zai zo din. Tun wuri ta tashi tayi wanka ta shirya don ya sameta a shirye; sai dai ga mamakinta har azahar tana zaune a parlor tana ta faman duba waya, duk wanda ya buga gate da hanzari take tashi ta bude tana saka rai Mustapha ne amma har la’asar bai zo ba.Dab da la’asar tana zaune a parlor tana ta faman latsa waya tana duba whatsapp ko ya bude sakon da ta tura masa amma ga mamakinta har zuwa lokacin bai bude ba. Mommy ce ta fito daga dakinta; har ta kama hanyar kitchen sai kuma ta kula da Khadeeja a zaune a parlor din. Ta dawo ta tsaya tace ‘Ya na ganki a nan, ina Nabila PA din taki?’Tayi dariya tace ‘Tana can tana abinda ta saba wato bacci.’Ta wuce kitchen ta barta a nan, jimawa kadan ta fito ta dawo parlor din ta zauna a kan three seater daga bangareb da yafi kusa da single seater din ta Khadeeja take zaune. Ta dan yi gyaran murya tace ‘Uhm, ai na zata Mustapha zai zo yau din, ko sai da yamma zai zo?’Ta dan gyara zama tace ‘Umm! Ina jin dai sai da yamman, watakila gidansu ya wuce tunda shi da yara ne.’‘Um to bari mu gani. Amma dai kuna waya ko?’‘Eh, jiya da daddare ma munyi magana.’‘Ai shikenan bari mu gani.’Suka yi shiru na dan lokaci; jimawa kadan tace ‘Mommy kina neman Mustaphan ne da naga kamar jiransa kike yi?Ta jijjiga kai tana murmushi ‘A’a me zai yi min; kawai dai na san ya kamata ace ya zo ya duba ki ko, ai ko gaisawa ne a yi duk da dai da an sallace zaki koma.’Itama dariyar tayi sannan tace ‘Zai zo Mommy in sha Allahu.’Abu kamar wasa har aka sha ruwa babu Mustapha babu labarinsa’ haka dai ta lallaba ta ci abincin ba tare da tana jin dadinsa ba. Tana kula da yanda Mommy ta saka mata ido sosai tana kula da duk wani motsinta tu dazu da suka yi magana.Sai da aka tafi sallar isha’i lokacin ‘yan gidan duk sun tafi masallaci sannan Mommy ta kirawota; ta riga ta san kiran don haka cikin sanyi ta tashi ta wuce dakin Mommy din. A zaune a kan dadduma ta sameta don haka ta zauna daga gefenta a kan kafet. Sai da Mommy ta dauki lokaci tana allon fuskarta kamar mai karanta littafi sannan tace ‘Wai ya aka yi Mustaphan bai zo ba? Gashi kin san ba za a sake bude gari ba sai satin sallah. Ko wani abu ne ya tare shi?’‘Umm! Kin san sai sun je office da zarar an bude gari. Sai da aka fara kiran magariba sannan ya kirawoni yake gaya min a lokacin yake barin office gashi yana so ya isa gida kafin a fara tare hanya.’ Ta sharo karya.Ta sake kakkafeta da ido na dan loakci sannan tace ‘Umm! Ko dai fushi yake don an ce ba zaki koma sai bayan sallah? Naga fa bai sake zuwa ba tun wancan lokacin da ya zo daukanki baki bi shi ba.’Ta sunkuyar da kai atana ‘yar dariya tace ‘Umm, ya ma gama fushin ai. Da farko ne ya fara fushin ya zata zan fasa zama har bayan sallar amma daga baya da yaga ba zai sami yanda yake so ba ya hakura.’‘Umm! To ko shi yasa bai zo ba?’‘A’a fa Umma, na gaya miki ya je aiki ne shi yasa ya makara bai zo ba. Idan aka sake bude gari ko kuma ranar sallah zai zo.’‘To Allah ya kai mu. Idan dai da akwai wata matsala gara ki fada tun kafin ki koma a san matakin da za a dauka don na kula kamar akwai abinda kike boyewa.’Ta dan yi murmushi sannan tace ‘Babu wani abu fa Mommy, aiki ne kawai da raino; kin san harkar yara. Bana samun lokacin kaina kullum cikin hidimarsu nake. Shi yasa tunda Biba ta tafi ban sami natsuwa ba. Kinga yanzu kin ce kafin sallah za a samo min yarinya sai mu koma tare, daga wannan babu wata matsalar.’Ta kalleta da alamomin tambayoyi domin jikinta yana bata kamar akwai abinda Khadeejan take boye mata, amma babu wani abu da zata iya yi a kai tunda bata ma san menene matsalar ba. Tace ‘To kuma shi Mustaphan baya baki wata matsala?’Tayi dariya ‘Mommy kema dai kin san da da matsala da tuni na gaya miki fa, babu komai.’Dole Mommy ta hakura ta kyaleta da tambayoyin nan ba don ta gamsu da amsoshin da ta bayar ba.………
