Job

Kamfanin MTN Sun Bude Shafin Bayar Da Tallafi Da Kuma Horo

Assalamu alaikum barkanmu da wannan lokaci fatan kowa yana cikin koshin lafiya.

Gidauniyar MTN Nigeria ta sake kaddamar da shiri mai taken Y’ellopreneur Initiative a shekarar 2022. A mataki na daya, ‘yan kasuwa mata 4,711 ne suka sami horo kan “ginin harkokin kasuwanci da ci gaba”. A wannan shekarar gidauniyarta fadadashi zuwa mata Mata 1000 inda mace 250 zasu samu tallafın Naira miliyan uku – uku.

Shirin MTN Y’ellopreneur Initiative shiri ne dake ba da gudummawa da rage mata marasa aikin yi da ci gaban mata a cikin ‘Kasuwanci’ ta hanyar habakasu, basu tallafı, basu bashi na lamuni, da koyarda su kyauta, basu shawarwari don dorewar kasuwancinsu.

■ Mataki na 1: Mata 1000 ‘yan kasuwa ne zasu samu damar shiga wannan shirin

■ Mataki na 2: Horo kan shirin Kasuwanci

■ Mataki na 3: Tallafin rancen kayan aiki na kusan Naira miliyan 3 ga kowace mace ‘yar kasuwa 250

■ Mataki na 4: Bayarda shawarwari akan kasuwancin zamani

■ Mataki na 5: Hanyoyin biyan lamuni bayan kammala shirin

Yadda Ake cikawa

Domin cikawa danna Apply Now dake kasa

APPLY NOW

Back to top button