Mijin Marigayiya Page 20 Hausa Novel
Sai da tayi da gaske sannan ta hana kanta kiran Mustapha a wannan daren; ta yiwa kanta alkawarin daga yanzu ba zata sake kiranshi ba har zuwa bayan sallah. Idan ya zo su koma, idan kuma bai zo ba ita dai to ba zata nemeshi ba.Haka ta kwana tana matse kwalla……….Duk yanda ya so ya daure zuciyarsa daga sharewar da Khadeeja tayi masa zuwa yanzu ya gaza; ya riga ya saba tana kiransa tana lallabashi da bashi hakuri amma shiru. Yana kallon kiranta ranar asabar yaki dauka don ya san zata ce ya zo gidansu ne; shi kuma ba zai je ba in dai ba daukanta zai je yi ba. Don haka yaki daukan kiran yana sa ran idan dare yayi ma zata sake kira, a lokacin sai ya bata uzurin dare yayi.Sai dai har ya kai yaran gidan Mama ya huto gida ya gama duk abinda zai yi bata sake kira ba; lokacin da ya tashi sahur ma wayar ya fara dubawa yaga ko ta kirawo yana bacci amma ga mamakinsa babu kiranta ko daya. Haka yayi sahur ya gama ibadarsa ya kwanta.Sai da gari ya waye zuwa azahar sanna ya tuna akwai messages dinta na whatsapp da ta turo bai bude ba don haka ya je ya lalubo sakonnin ya bude. Ya bisu daya bayan daya ya tura mata amsa, wanda tambayarsa take yi ko zai zo sannan tana gaya masa kayan da zai dauko mata a dakinta ya taho mata dasu.Har zuwa la’asar bata amsa sakonninsa ba sai dai sun nuna alamar sunshiga; ya buda whatsapp sau babu iyaka amma har zuwa loakcin bata karabta sakonninsa. Bata taba shareshi haka ba; to ko dai bata da lafiya ne? kada fa yaje wani abune ya sameta don idan dai Khadeeja ce ya san zata nemeshi. Zuciyarsa tana gaya masa wulakanci ne kawai take so tayi masa don haka ya rabu da ita duk da yanda ya kasa cire tunaninta daga ransa.Haka suka zauna basa waya kumaga sakonninsa nan ta gani amma taki ta abshi amsa.Ranar jajiberin sallah ya kasa jurewa shiru din don haka ya kirawota; wayar tana dab da tsinkewa sannan ta amsa.Murya kasa-kasa cikin halin ko in kula tace ‘Bana kusa da wayar ne.’‘Kwana biyu na jiki shiru ne, kuna lafiya?’‘Lafiya Alhamdulillahi. Ya yarana?’‘Suna nan kalau, suna gidan Mama.’“Allah sarki, don Allah in kaje kace ina gaida su maman.’Suka yi shiru na dan lokaci, jimawa kadan yace ‘Kin yi zamanki a gida gaba daya kin manta da ni ko?’Tayi ‘yar dariya tace ‘Ka dai manta da ni.’‘Ko kayan sallarki ma baki tambaya ba.’‘Uhm, akwai wasu ma a nan da Mommy ta dinka min.’‘To ya kike? Lafiya dai kike ko?’‘Lafiya kalau.’Suka dan taba hirar haka wadda duk gaba daya kusan shine yake ta daddagewa don itama ta ji haushin abinda yayi mata, daga baya yace ‘Gobe fa Sallah, yaushe zan zo mu taho gida?’‘Umm, in dai ka cire jibi duk lokacin da ka shirya zaka iya zuwa mu tafi, tunda an riga an samo min mai aiki gata har ta koyi duk wani aiki da nake so.’‘Uhm, dole dai sai kin sani cin tuwon sallah a gidan hajia ko?’‘To ina laifi, idan ka ci nima kayi min take away.’Haka suka cigaba da hirararsu a hankali suna sakewa, daga baya suka yi sallama a kan ranar sallah zai zo yaci tuwo kafin ya wuce gidan Hajia.Ranar Sallah yana tashi ruwan shayi kawai ya sha ya shirya ya fice; bayan an idar da sallar idi kai tsaye gidan Mama ya wuce wajen yaransa. Yana gamawa da su ya wuce gidan Mommy wajen Khadeej; ko da dai ya ji haushin yanda tayi zamanta a gidansu ta ki dawowa amma ya san yayi kewarta. Duk wani haushi nata da yake ji ya riga ya huce, abu daya yake so a yanzu shine ta dawo gida ya samu ya daina fama yawo shi da yaransa sai kace wasu wadanda basu da gata. Ya kalli kayan sallarta wadanda ya taho dasu ya kai mata ko zata kara, ya kauda kai ya cigaba da tukinsa. Shi ya ga ma kamar bata damu da kayan sallar ba tunda da ita aka kai dinkin amma da yake ta so tayi sallah a gida ko bi ta kansu bata yi ba sai ma ce masa da tayi Baffa yayi mata kayan sallah.Haka dai yayi ta tunani kala-kala har ya karasa gidansu Khadeeja. Lafiya kalau suka gaisa cikin mutunci kamar babu wanda yake jin haushin wani a tsakaninsu; ya shiga ya gaida Mommy sannan ya gaida Baffa. Suka dawo ita da shi suka zauna a parlor din baki inda ba tare da bata lokaci ba ta kawo masa tuwon sallah da lafiyayyen zobo mai sanyi. Suka zauna yana ci tana yi masa hira. Bayan ya gama ya huta yayiwa Baffa sallama inda Baffan ya sanar da shi jibi ya zo ya dauki matarsa. Suka fito tare da Khadeejan ta rakoshi bakin mota. Tana tsaye rike da murfin kofar motar yayinda shi kuma yake zaune a kujerar direba ya juya kujerar baya ya dauko ledar da take ajiye a kan kujerar ya mika mata yana cewa ‘Ga kayan sallarki duk da na ga baki damu da su ba.’Tayi ‘yar dariya tana tura masa ledar tace ‘Ka koma da su ka ajiye min a dakina tunda jibi zan dawo.’ Shima dariyar yayi yana mayar da kayan yana cewa ‘Ko dubawa ma fa baki yi ba.’‘Haba kayan da na riga na sansu, idan na dawo zan duba sannan nayi kwalliyar sallah ta.’Cike da farin ciki da walwala suka yi sallama sannan ya wuce gidan Hajia.Yana shiga gidan ya tara da Hajia a parlor dinta suna hira ita da Yaya Jidda, yaranta kuma suna ta kaiwa da kawowa a tsakar gidan.Bayan ya gaida Hajia yayi mata barka da sallah ya juya suka gaisa da Yaya Jidda wadda take ta faman shan kun tana basarwa saboda kar yayi mata wata magana. Bayan sun gaisa sun dana taba hira da hajia ya dubi Yaya Jiddan yace ‘Yaya bari na baki account number ki turo min 10k din da na tura miki ta tiwa yara sayayyar kayan shayi; tunda sun ce min ba a saya ba ko?’Ta sake hade girar sama da kasa ta kalli hajia sanna ta kalleshi tace ‘Ban gane ba a siya ba, an saiya mana. Kawai dai ba rabar da ka bayar ba don kafin ka turo kudin masu kantunan sun rufe. Shi yasa ba a samu an saya ba har sai ranar da aka sake bude gari, ranar da ka zo kenan ka kwashesu. Da safen da ka tafi da su ai da sun zo zasu tara da kayan komai an saya don har ciko ma nayi.’Hajia tace ‘Ai kuwa ka ga babu maganar dawo da kudi tunda an sayi kaya.’Takaici ya kama shi don ko daya bai yarda da wannan zancen nata ba, ya kawar da kai sannan ya sake dubanta yace ‘Hakane, to shi kenan, sai a dauko min ragowar na tafi da su tunda jibi yaran zasu dawo har Khadeejan kuma ko suga babu a gidan sai na sake siya. Ki aika a dauko min su tunda kusan ma ba ayi amfani da su ba kenan tunda ranar da aka siyo ranar suka tafi.’Kafin tayi magana Hajia tace ‘To su sauran yaran gidan ba ‘yayanka bane da ba za a basu ba, kayan shayin kawai ba wani abu.’ Ta dubi Jiddan tace ‘Ko da yake bari na barku watakila suna nan ki bashi ya kai gidan nasa.’Ta sake kicin kicin sannan tace ‘Hajia kema dai kin san yaran nan ba zasu bari ga kayan shayin harda Indomie su bari na ajiye ba tare da na basu ba. Sai dai kawai idan biyansa zan yi na yiwa babansu waya ya biya abinda ‘yayansa suka ci tunda yana kallo suna ci kuma ya san ba shi ya siyo ba.’Hajia tace ‘A’a ba za ayi haka ba, sai kace a garin matsiyata ake.’ Ta dubi Mustaphan tace ‘Kai Mustapha kayi hakuri, bana son wannan rigimar taka. Wannan ma ai ba wani abu bane da za a daga tunda daga yaranta har nakan duk ‘yayanka ne.’Muryarsa a makogoro yace ‘Shikenan Hajiya.’ Ya mike tsaye yana cewa ‘Bari naje wajen Alhaji mu ci tuwon tare, ko da yake ma a koshe nake me sanyin kawai zan shaYana shigewa Jidd a ta kalli Hajia tace ‘Kin gani ko Hajia, a kan kayan shiya zai yaga min rigar mutunci, wallahi yaron nan har yanzu bai yi hankali ba.’Tace ‘Ya fi ki gaskiya, ya zaki karbi kudinsa kuma ki dinga bar masa yara da yunwa?..’‘Hajia wallahi na gaya miki karya yaran nan suke yi, kawai don sun san za a biye musu ne suke abinda suka ga dama. Idan banda haka ya za ayi na hanasu abinci na bawa su Nawwara tunda ai duk tare suke wuni suna wasansu; kawai dai suna so su nuna su ubansu mai kudi ne.’‘Ki dai bi shi a hankali kin ji na gaya miki. Bari ma ya fito naji sai yaushe zai kawo min yaran yawon Sallah ko kuma nima laifin naki ne ya shafe ni ya kai yaran wajen waddad da baya son ya bar mata su?’…….. Haka yana ji yana gani ya hakura ya kyale Yaya Jidda; daman ya riga ya san Hajia ba zata taba bari a ga laifinta ba.Kamar yanda aka yi alkawari ranar uku ga sallah tun wajen karfe tara na safe ya tafi daukan Khadeeja; da yake sun riga sun yi waya a shirye ya sameta don haka ba tare da wani bata lokaci ba ya daukota ita da mai aikinta Rashida suka kama hanya. Sai da suka tsaya a gidan Mama suka kwashi yara sannan suka wuce gidan Hajia. Nan suka zauna a parlor ana ta hira yayinda yara suke ta kaiwa da kawowarsu. Jimawa kadan Yaya Jidda ta dubi Khadeeja tana nuna Rashida tace ‘Wannan yarinyar taki kuwa zata iya wani aikin kirki? Kada fu kuje a kama ku da child abuse?’Tayi dariya duk da yanda maganar ta bata mata rai tace ‘Ah haba dai, shekarunta fa sha biyar yaya don dai kawai bata da girma ne. Aiki kam ta iya sosai ko a gida ma Mommy ta koya mata.’ ‘To amma idan Habi ta dawo sai a mayar da ita ko? Tunda na ji Habi din tace baku da wata matsala da ita kuma tana nan itama tana shirin dawowa.’‘Uhm, sai a hada biyu ma tunda kin ga ga hidimar gida ga ta yara, kuma ina zuwa makaranta.’‘Haba wace hidima ce sai an hada ‘yan aiki har biyu a wannan gidan? Hidimar har nawa take?’Kafin ta bata amsa Mustapha ya shigo yana cewa ‘Ku tashi mu tafi ko, don na san kuna da aiki a gidan nan don duk yayi kura.’Suka fara shirin mikewa yayinda ita kuma Yaya Jidda ta kalli Mustaphan tace ‘Na ga kun samo ‘yar aiki, Baba Habi ma fa tana nan tana shirin dawowa.’Yace ‘Ah ai kawai sai kice mata tayi zamanta tunda dai gaskiya bamu da inda zamu ajiye ‘yan aiki har biyu.’‘Da nace ta mayar da wannan din idan Baba Habi ta dawo?’‘To gata nan kuyi magana idan ta fi son Baba Habi din sai a mayar da wannan din.’Ba tare da bata lokaci ba Khadeeja tace ‘Uhm ai gara a bar wannan din, in ya so in da wata matsala sai nayi magana a nan din a kawo wata.’Haka dai dole Yaya Jidda ta barsu suka tafi ba tare da ta iya gamsar da su cewa Baba Habi zata dawo ba.……….
