Zafafa 2023

Cuta Ta Dau Cuta Chapter 36 By Billyn Abdull Complete Novel

*_Typing📲_*

   *_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_

_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_

_Shafi na talatin da shida_

Follow this link to join my WhatsApp community: https://chat.whatsapp.com/F7aIYP99bGn9mIqLhjUWKR MUNA SAYAR D KAYAN KITCHEN D FURNITURES N TURKEY D ABAYA AKAN FARASHIN SARI DA CAPSULES MASU KYAU D INGANCI.

_________

*_ASHE SUN DAWO😱???!!_*

_Su waye🤔?_

*_ZAFAFA BIYAR MANA_*

*_🤥AMMA NAKE ZAUNE NAN WANGALAU DA BAKI😨 KAMAR ƘOFAR RIJIYA. KAI AMMA DAI GASKIYA TAWAJENA BAKI ƘYAUTABA. MU ZAFAFA BIYAR NA FARA HARKA AI ZAMA YA ƘARE MANA, CIN DATA A BANZA DA GANTALI BABU WAJEN ZUWA A MEDIA KUMA YAZO ƘARSHE. BARI DAI KIGA DA SURUTUN NAN NIMA NAJE NA YANKO NAWA TIKITIN SHIGA A DAMA DAMU. KIN SAN IN ANA ZAFAFA BAKAI BABU DAMUWA, NISHAƊI ZALLA A LITTAFAN SU, KAI HARMA DA GIDAN COMMENTS._*

*_WANNAN GASKIYA NE, INA KUKE MA’ABOTA KARANCE-KARANCEN LITATTAFAN HAUSA. KU GARZAYO MAZA GA WATA SABUWAR DAMA TA SAKE SAMUWA FA. DOMIN KUWA ZAFAFA BIYAR ƊIN NAN DA KUKE TA JIN LABARI SUN SAKE DAWO MUKU DA WASU DABBIN SALO NA SABUWAR SHEKA MASU ƘAYATARWA_*

*_ILMANTARWA!!_*
*_NISHAƊI!!_*
*_SOYAYYA_*
*_BARKWANCI_*
*_ƘAYATARWA_*

*_ƳAR UWA KE MI KIKE JIRA ANATA YANKAR TIKITIN SHIGA JIRGIN ZAFAFA BIYAR AMMA KE KINA A NIGERIA GASHI KUMA YANA GAB DA TASHI. KIN YARDA DUK WANCAN ABUBUWAN NA SAMA SU WUCEKI? KENAN?_*

*_HABA TAWAJENA MAZA GARZAYO A DAMA DAKE KEMA A WANNAN TAFIYAR. NASAN ZAKIJI DAƊINTA ZA KUMA KIYI ALFAHARI DA ITA. DOMIN MASU IYA MAGANA KANCE SAYEN NAGARI MAIDA KUƊI GIDA. TO SAYEN ZAFAFA HAR RIBA MA ZAKI MAIDA INSHA ALLAHU._*

*_Ƙayatattun littafan naku sune kamar haka👇🏻_*

*_GUDUN ƘADDARA🏃‍♀️_*
_(Na SAFIYYA HUGUMA. kai daga jin sunan kasan za’a ɗauki darasi tare da ilimi harma da soyayya mai ƙayatarwa. Dan kun san HUGUMA bata kawo muku labaran banza. Za’a warwasa matuƙa da nishaɗi mai gamsarwa🥰🫡)_.

*_KWANKWASON JIMINA…🦃_*
_(HAFSAT MISS XOXO. Masu iya magana kance kwankwason jimina mai wuyar shafawa. Daga ji babu tambaya wannan littafi na ɗauke da darasi, ilimi na musamman, tare da gagarumar cakwakiya, ilimi harma da nishaɗi. Kun san dai Miss xoxo a fagen ƙayatar daku, ga soyayya mai tsayawa a zuciya kaji kamar ana zanata ne a cikin kanka.😍🫡)_

*_AMEENATU🧕🏻_*
_(NA MAMU GEE. Kun dai san Mamun taku a fagen iya tsara labari, ta kasheku da sinƙi-sinƙin ƙauna ziryan mara gaurayen algus. Daga jin sunan littafin ma kasan za’a kwashi romon ƙauna da ilimin ƙulle mai gida a haɓar zane kai soyayya fa tayi. Kun san dai Mamu gee bata kawo muku labaran banza😘🫡)_.

*_TSUTSAR NAMA….🥩_*
_(NA BILYN ABDULL. Tofa cakwakiya. Lallai akwai tsallen tsalli watsanga kenan a wannan littafi. Kun san dai Bilyn taku wajen kawo muku darasin rayuwa, ilimi, nishaɗi, cakwakiya, kai harma da soyayya mai sa kaji kamar dan kai akeyi. Ƴan uwa akwaifa ƙura hummmm🫶🫡)_

    _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

🔥🔥🔥🔥🔥🔥💥💥💥💥

_________

…….“Sunana Alhaji mai-kuɗi. Ni ne mamallakin gidan nan a yanzu. Nazo ne nai magana da masu hayar gidan. Dan haka ina mijinki?”.
Wani shegen kallo na amma ka haukace Kainaat taima dattijon mutumin. Kafin cikin rainin wayo ta ce, “Dama yanzu shaye-shaye ya wuce kan matasa har dattijai ma ɗorawa suke yi. To idan hankalin naka baya a tare da kai bari na dawo maka da shi jikinka. Sunana Kainaat, wannan gidan kuma mallakina ne. Idan ma wani sakaran ɗan damfarar ne ya siyar maka kai maza kafin ya ɓace ma ka karɓa kuɗinka.”
Sheƙeƙe Alhaji mai-kuɗi yay dariya, shima dai kallon ke wawuya ce ya jefeta da shi, kafin cikin gadara da ƙyaɓe fuska ya dubi yaransa a umarce ya ce, “Wannan naga ƴar hau ce. Tunda bata buƙatar masalaha ku gaya mata na bata nan da kwanaki uku in ma ita kaɗai ce, in ma da mijinta suke tare su tattara su barmin gidana dan ina da buƙatarsa. Ku nuna mata shaida maybe ta farka a mafarkinta”. Yana gama faɗa ya fice yana wani takun faɗi kamar bajimin san da girma yayma yawa…
Wani kalar ihun rashin mutunci Kainaat ta musu lokacin da suke ɗaga mata takardun, kafin ta koma ciki fuuu. Kai tsaye ɗakin Dafeeq ta nufa. Jin ƙofar gam-gam ta shiga masa bugun hauka. A fusace ya buɗe ƙofar, daka kallesa kaga wanda ya tashi abarci. Ranta ɓace ta ce, “Kazo nan kana barcin asara na rashin aikin yi. To sai ka fito ga wasu ƙadangarun bariki nan sunzo wai gidan nan nasu ne. Harda bamu notes na kwana uku”.
“Kamar ya Notes?”.
Ya faɗa cikin mamaki. Bata amsa masa ba ta juya a fusace. Da kallo ya bita, sai kuma ya saki wani lalataccen murmushi yana komawa ɗakin bayan ya sakama ƙofar key. Tsalle ya dirga saman gado yana wani ƙaramin ihu. Sai kuma gimtse bakinsa yana waro idanu. Wayarsa ya ɗauka ya shiga dannawa, kafin yay dailing wata no da aka sakama Dr G. Tana fara shiga ya wani yi baya a saman gadon ya kwanta ƙafa ɗaya kan ɗaya like saraki ɗin nan dai. Yay filo da hannunsa ɗaya ɗayan na riƙe da wayar. Harta tsinke ba’a ɗaga ba, bai kawo komai a ransa ba ya ƙara kira. Nan ma dai ba’a ɗaga ba har sai da yay kira kusan huɗu sannan aka ɗaga ana ƙarshe tana gab da tsinkewa. Ajiyar zuciya ya sauke kafin yay sallama a gadarance.
Daga ɓangaren Doctor Giɗaɗo ya amsa murya a sauƙaƙe tamkar yanama murmushi ko yanayin nishaɗi. “Aboki kana kira ina cikin aiki ne. Ykk?”.
“Normal”. Dafeeq ya amsa a gadarance. Kafin cikin yamutsa fuska kamar yana gaban doctor ɗin ya cigaba da faɗin, “Naga mutanenka sun zo. Harya bada kuɗinne?”.
Wata ƴar dariya doctor ya saki, sai kuma ya bashi amsa da, “Yes ai harma na damƙa masa takardun. Suma kuma yanzu haka duk sun iso hannuna.”
Karan farko Dafeeq ya saki murmushi, sai kuma a ɗan zumuɗe ya furta, “Okay good. Yanzu mu haɗu da kai a inda muka saba haɗuwa. Amma kafin nan ka bama yaron nan nasu 1mil..”.
“Okay an gama abokina, amma baka tunanin bama yaron kuɗi zai sa su Nadwan su fahimci abinda ya aikata. Ya kamata mu bari har sai ka bar garin, koma ka tafi da shi mana Please”.
“No no, ai ni bana aiki da mutum sau biyu, na tafi da shi nima wataran zai iya cin amanata. Batun su Nadwa kuma ai bashi kaɗai yay aikin ba da taimakonka ne. Tunda da bata yarda ta sanar maka ina suke ba ai bazaka sani ba?”.
“Yes kuma hakane. Amma inada shawara, bai kamata mu haɗu yau ba, mu ɗan bada ƙafa 3days okay”.
Ɗan jimm Dafeeq yay kamar zancen bai shigesa ba. Sai kuma zuwa can ya furta, “Hakan bazai yiwu ba, nasan yau gidan nan akwai ƙura, anjima kaɗan zan nemeka kazo saika saman anan kawai”.
Doctor ya amsa masa da “To babu damuwa”. Daga haka suka yanke kiran. Sai da yasha dariyarsa sannan ya saka jallabiya ya sauka ƙasa. Ya samu Kainaat zaune a falon da waya a hannu, da alama wani take nema amma ta gagara samunsa. Cikin wani irin sauri ya ƙaraso gareta. “Am sorry Baby. Na ɗan zagaya toilet. Please yimin bayani yanda zan gane ɗazun kin barni a duhu nikam”.
Kamar bazata ce komai ba, sai kuma ta shiga masa bayani a zafafe. Ta ƙare da faɗin, “Dafeeq narasa miyyasa hankalina ya gagara kwanciya. Yanzu haka kuma kiran wayar Nadwa da Mom nake amma babu wacce ta shiga.”
“A’a miya haɗa wannan maganar kuma da su Nadwa?”.
Cikin rasa control ɗin ta ta ce, “Takardun gidan nan fa dama duka documents ɗina suna hannunsu. Ina son jin ko an samu kuskurene da ga wajen su da har mutumin nan ke jin ƙarfin gwiwa, dan wlhy na hango tarin rashin mutunci a idon mutumin nan fa”.
Wani kalar gyara tsaiwa yay cike da salon karyar da murya ya furta. “Oh yanzu Baby tsana da rashin yarda har takai haka a tsakaninmu. Ki ɗauki komai naki ki fita da su a gidan nan saboda ni?….”
Da sauri ta shiga girgiza kai, sai dai ta gagara cewa komai. Shima bai sake cemata koman ba ya koma gefe ya zauna shi adole yayi fushi. Duk da taji wani iri sai dai batashi take ba. Ta cigaba da kai-kawo da neman layin Mom da Nadwa. Sai dai samun ya gagara. Da ga ƙarshe dole ta yanke shawarar fita. Ko kaɗan baiyi yinƙurin binta ba. Itama batako masa tayin hakan ba ta figi key ɗin mota ta fita. Mintuna kaɗan suka kawota ƙofar gidan su Nadwa, sai dai ta samu gida garƙame da kwaɗo. Mamaki ya kamata, tana tsaye tana ƙullawa da kwancewa maigadin maƙwaftansu ya leƙo. Da sauri ta nufesa tana tambayarsa ko ina masu gidan? Cikin rashin damuwa da kuma sanin da yay mata ya bata amsa da, “Ai sun tashi anan, sun kuma saida ma gidan jiyan nan. Ga wannan ma sukace a baki dan da alama dama sunyi tunanin zuwanki ma ashe”. Ya ƙare maganar yana miƙa mata brown envelope. Hannunta har rawa yake wajen amsa. Harta kama zata buɗe suka ji an tada mota. Da sauri suka waiga a tare, sai me har an birka motar a guje. Ihu ta shiga kurmawa tana tsalle da kiran ɓarawo-ɓarawo. Nan fa masu gadin gidajen layin suka shiga firfitowa a guje. Sai dai kamar asiri basu ko kama hanyar cimma ɓarawon ba. Hasalima ya ɓace ma ganinsu ɓat kamar abin rufa ido……

__________★

          Tunda ya koma aiki kamar yanda ya saba ƙarfe biyar yake dawowa gidan. Yau ma hakane. Sashen mahaifiyarsa ya fara shiga suka gaisa kafin ya nufo nasu sashen. Tun kafin ya shiga wani ƙamshin turare mai ratsa zuciya ya gama cika masa ƙofifin hanci. Lokacin da ya gama shiga tsakkiyar falon sai yaji kamar ya shiɗe dan daɗin ƙamshin turaren wutar. Kamar mai jin zazzaɓi-zazzaɓi a hankali ya furta, “Baɗɗo am”.
Murmushi Khadijah dake laɓe bayan labule ta saki, kafin ta yaye labulen a hankali jin ya sake kiran sunan nata. Wani kalar luuuu yay da idanunsa kamar mai shirin suman tsaye sai kuma ya buɗesu a slowly. Tabbacin ita ɗin ce dai ya saka shi jin numfashinsa na wani fita guda-guda. A hankali Khadijah da ke kallonsa ta sake sakin murmushi, sai kuma tai ɗan yi juyi a hankali.
“Habba Baɗɗo am kasheni zakiyi? Maza zo gareni karna sume, Baɗɗo am Hammanki mai rauni ne akan ki common zo zo”. Yay maganar yana yafito ta cike da nutsuwarsa. Nufosa ta shigayi a ƙasaitance. Yayinda shi kuma ya buɗe mata hannayensa alamar ta shige jikinsa. Sai da tazo gab da shi ta wani saki murmushi da sakar masa gwalo da sauri ta koma ta bayansa ta ɗane tare da zagayo hannayenta duka biyu a saman cikinsa ta kwantar da kanta a bayan nasa ta lumshe idanunta tana murmushi da rungumesa ƙam-ƙam. Ajiyar zuciya mai ƙarfi suka saki a tare. Musamman ma shi da kwalliyar tata tai masifar hargitsa lissafinsa. Da ɗan tsumar jiki ya kama hannayenta da ke saman cikinsa ya zagayo da ita gabansa. Idanunta ta rufe gam tana murmushi. Shiko ya tsareta da kallo tun daga ƙafafunta har zuwa kan bomshot ɗin data saka na jeans blue da akaima adon stones masu ƙyalli, zuwa kan ƙaramar farar shirt data saka ta ɗaureta a saman ciki har kana iya ganin cikinta dake buɗe a yanayin gayu, zuwa ɗaurarren gashinta data raba biyu kowanne ta ɗaure kamar wata matashiyar budurwar turawa. Sai dai ita dan kawai baƙa ce. Sake kamota yay ya rungume tsamm a jikinsa, cikin raɗa a kunnenta tamkar mai tsoron a jisu ya furta, “ALLAH yay miki albarka Baɗɗo am. Yanda kike sanyani farin ciki, ALLAH ya faranta miki da sakamakon gidan aljanna ke da iyayenki da ahalinki baki ɗaya. I love you Baddo am”.
“Amin ya rabbi Hamman Baɗɗo. Tare da kai da zuri’arka baki ɗaya. I love you too”. Ta faɗa itama tana manna masa sumba a dai-dai maƙoshinsa dan iya inda tsahon nata ke zuwa kenan. Fuskarta da take ƙoƙarin janyewa ya damƙe da tafukan hannunsa duka. Kallon juna sukayi cikin ido, a wani irin salo ya kashe mata ido ɗaya da sakar mata murmushi kafin ya kai lips ɗinsa kan nata. Ajiyar zuciya suka saki a tare, sai kuma suka lumshe idanu a taren nan ma. Sun jima a haka kafin su rungume juna na wasu mintuna. Sai da suka gama dai-daita kafin ta bar jikinsa, hannunsa ta kama suka koma cikin falon, ruwan data ajiye a Centre table domin shi ta zuba masa, sosai yasha yana saka mata albarka, kafin ya miƙe muryarsa acan ƙasa, “Baddo saura wanka.”
Babu musu ta ɗan masa kallon shagwaɓa, sai kuma ta noƙe kafaɗa da faɗin, “Uhm-uhm ni hannuna ke ciwo da ƙafafu na”.
“Please Baɗɗo am, nifa jikinne duka ke min ciwo, baki tausayina daga office fa nake nema muku na tuwo”. Ya faɗa shima cikin marairaicewa.
“To sai in ka yarda zaka goya ni”.
“Abu mai sauƙi” ya faɗa yana duƙawa. Ƴar dariya ta saki tare da hayewa bayansa tana ɗora fuskarta a wuyansa tare da hannayenta tana ƙanƙamesa. Murmushi yayi kawai shima yana ɗan lumshe idanu. Dan siririyar dariya tata ta shiga har ƙasan ɓargon jikinsa, ga ƙamshinta dake ratsashi. A haka ya nufi sashensa da ita, duk da tana da ɗan nauyi bai damu ba. Shi dai fatansa tai farin ciki kamar yanda shima take sakashi akoda yaushe. Shi kaɗai yasan yanda yake jin sati biyun nan da suka kasance a tare a cikin ransa. Dan sun zo da ɗunbin tarihi da bazai taɓa iya goguwa a ransa ba. Ko aurensa na farko baya jin ya shiga irin wannan nishaɗin. Kodan ita ɗin wannan ƙaramar yarinya ce yanda yake so haka yake juyata ta kuma masa biyayya babu gardama, saɓanin waccan da take sa’arshi idanunta kuma a buɗe oho shi bai sani ba.
Har bedroom ɗinsa ya kaita, da taimakonta ya cire kayansa, sai dai duk yanda yaso kauda kai a kanta ya gagara hakan. Bai ma san sanda labarin ya canja ba sai tsuntar kansa da yay a wata duniya da fassarata badai baki ba. Yana jin farin cikin yanda sam bata masa musu. Ko yanzu tai kwalliya ya ɗakko hanyar ɓatata ko a fuska bazai taɓa ganin ɓacin ranta ba. Idan zai zo mata sama da babu adadi bata musa masa ko nuna gazawa koda kuwa ta cancanci ta gaza ɗin. Da ga ƙarshe tare sukai wankan, ya shirya itama ta saka rigarsa t-shirt data sakko mata sosai. Fita yay sallar magrib, itama ta koma sashenta tayi tata. Har isha’i sannan ya dawo, kamar yanda suka saba suka nufi sashen mamy dan can ne dandalin cin abinci da hirar dare.
Duk da anan ma ta kusan raba yininta tare da Mamyn a yanzuma cikin zumuɗi ta tarbesu. Gaskiya Mamy nada daɗin zama sosai. Mace ce kamila mai tarin dattako. Dan halayen Abaan da yawa ya gajesu daga gareta ne. Abinda zai birgeka duk wannan soyayyar dake tsakanin Abaan da Khadijah da zaran sun je gaban Mamy sai kaga kowa ya kama kansa, yanda suke share juna bazaka ɗauka ma sunada wata alaƙa ba. Komai cikin dattako da girmamawa yake kasancewa. Bayan sunci sun ƙoshi aka buɗe babin hira. Tara da rabi nayi Mamy ta korosu sashensu. Cikin nuna ba haka suka so ba suka fito, Noor ko na musu dariyar tsokana. Suna fitowa Khadijah ta dogare tana tura baki gaba. Kallonta yay sai kuma ya saki dariya. Gwalo ya mata da faɗin, “Ai Mamyn ce ma maganin ki”. Baki ta sake turawa tana kai masa mintsini. Kaucewa yay, ta sake kai masa ya kauce. Sai kuma ya fara ɗan gudu tana binsa……..✍️

Click Here To Read Cuta Ta Dau Cuta Chapter 35 By Billyn Abdull Complete Novel

*_ASHE SUN DAWO😱???!!_*

_Su waye🤔?_

*_ZAFAFA BIYAR MANA_*

*_🤥AMMA NAKE ZAUNE NAN WANGALAU DA BAKI😨 KAMAR ƘOFAR RIJIYA. KAI AMMA DAI GASKIYA TAWAJENA BAKI ƘYAUTABA. MU ZAFAFA BIYAR NA FARA HARKA AI ZAMA YA ƘARE MANA, CIN DATA A BANZA DA GANTALI BABU WAJEN ZUWA A MEDIA KUMA YAZO ƘARSHE. BARI DAI KIGA DA SURUTUN NAN NIMA NAJE NA YANKO NAWA TIKITIN SHIGA A DAMA DAMU. KIN SAN IN ANA ZAFAFA BAKAI BABU DAMUWA, NISHAƊI ZALLA A LITTAFAN SU, KAI HARMA DA GIDAN COMMENTS._*

*_WANNAN GASKIYA NE, INA KUKE MA’ABOTA KARANCE-KARANCEN LITATTAFAN HAUSA. KU GARZAYO MAZA GA WATA SABUWAR DAMA TA SAKE SAMUWA FA. DOMIN KUWA ZAFAFA BIYAR ƊIN NAN DA KUKE TA JIN LABARI SUN SAKE DAWO MUKU DA WASU DABBIN SALO NA SABUWAR SHEKA MASU ƘAYATARWA_*

*_ILMANTARWA!!_*
*_NISHAƊI!!_*
*_SOYAYYA_*
*_BARKWANCI_*
*_ƘAYATARWA_*

*_ƳAR UWA KE MI KIKE JIRA ANATA YANKAR TIKITIN SHIGA JIRGIN ZAFAFA BIYAR AMMA KE KINA A NIGERIA GASHI KUMA YANA GAB DA TASHI. KIN YARDA DUK WANCAN ABUBUWAN NA SAMA SU WUCEKI? KENAN?_*

*_HABA TAWAJENA MAZA GARZAYO A DAMA DAKE KEMA A WANNAN TAFIYAR. NASAN ZAKIJI DAƊINTA ZA KUMA KIYI ALFAHARI DA ITA. DOMIN MASU IYA MAGANA KANCE SAYEN NAGARI MAIDA KUƊI GIDA. TO SAYEN ZAFAFA HAR RIBA MA ZAKI MAIDA INSHA ALLAHU._*

*_Ƙayatattun littafan naku sune kamar haka👇🏻_*

*_GUDUN ƘADDARA🏃‍♀️_*
_(Na SAFIYYA HUGUMA. kai daga jin sunan kasan za’a ɗauki darasi tare da ilimi harma da soyayya mai ƙayatarwa. Dan kun san HUGUMA bata kawo muku labaran banza. Za’a warwasa matuƙa da nishaɗi mai gamsarwa🥰🫡)_.

*_KWANKWASON JIMINA…🦃_*
_(HAFSAT MISS XOXO. Masu iya magana kance kwankwason jimina mai wuyar shafawa. Daga ji babu tambaya wannan littafi na ɗauke da darasi, ilimi na musamman, tare da gagarumar cakwakiya, ilimi harma da nishaɗi. Kun san dai Miss xoxo a fagen ƙayatar daku, ga soyayya mai tsayawa a zuciya kaji kamar ana zanata ne a cikin kanka.😍🫡)_

*_AMEENATU🧕🏻_*
_(NA MAMU GEE. Kun dai san Mamun taku a fagen iya tsara labari, ta kasheku da sinƙi-sinƙin ƙauna ziryan mara gaurayen algus. Daga jin sunan littafin ma kasan za’a kwashi romon ƙauna da ilimin ƙulle mai gida a haɓar zane kai soyayya fa tayi. Kun san dai Mamu gee bata kawo muku labaran banza😘🫡)_.

*_TSUTSAR NAMA….🥩_*
_(NA BILYN ABDULL. Tofa cakwakiya. Lallai akwai tsallen tsalli watsanga kenan a wannan littafi. Kun san dai Bilyn taku wajen kawo muku darasin rayuwa, ilimi, nishaɗi, cakwakiya, kai harma da soyayya mai sa kaji kamar dan kai akeyi. Ƴan uwa akwaifa ƙura hummmm🫶🫡)_

    _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

🔥🔥🔥🔥🔥🔥💥💥💥💥

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

Back to top button