Hausa novels

Abban Sojoji Takun Karshe Book 3 Chapter 107 Complete Novel

*Father of soldiers*

*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*

Saman Sofa ya zauna,Sehrish ta Æ™araso ta ajiye mashi plate É—in saman table É—in gabanshi,hannu tasa ta cire murfin da ta rufe gurasar dashi,É—an É—agowa tayi tare da satar kallonshi samun shi tayi ya jingina bayanshi a jikin kujerar,idanuwanshi a lumshe suke,gyaran Murya ta É—an yi mashi”Ya rafayet,”slowly ya buÉ—e idanuwanshi akanta,nuna mashi gurasar tayi alamar yaci,

Muryarshi a kasalance yace”who asked u to pick the call?” gabanta ne ya fadi calmly tace”dama naga baka dade da yin bacci ba,don kar kiran ya tashe ka yasa na dauka don in fadi ma mai kiran bacci kake,to kuma sai naji banjin abunda ake cewa shine nai rejecting kiran,amman kayi hkr”ta karasa kanta a kasa,still yayi yana cigaba da kallonta can taji yace”Ni zanci da kaina?” dagowa tayi suka hada ido, saurin kawar da idanuwanta tayi saboda kunyarshi da take ji,musamman inta tuna abunda tayi mashi asaman shimfiÉ—arshi,

DaÆ™yar ta iya buÉ—e baki tace”zan iya baka idan kana so,”

Nuna mata gefenshi yayi ta zagayo ta zauna,ƙamshin turarenshi har cikin kanta,A yangance tasa hannu ta nannaɗo gurasar,tana ƙoƙarin kaiwa bakinshi idanuwansu suka haɗu wuri guda,kasa janye idanuwanshi yayi daga kallonta,wasu abubuwa sun ɗan fara ɗaure mashi kanshi,Ta canza mashi sosai ba kamar daba time ɗin da ko haɗa ido bata iyayi dashi amma yanzu takan ɗan kalleshi harma su haɗa ido,kuma jikinta ya daina wannan rawar da yake yi duk in tazo part ɗinshi,hakan na nufin ta rage jin tsoronshi?ko meyasa?ko dan saboda romancing ɗin da yake yi mata ne?

Download>>> The Governor Wife Book 1 Complete Novel 

Ganin ta kasa tura mashi gurasar abaki yasa ya ruƙo hannunta tare da matso dashi saitin bakinshi ya tura gurasar ya ɗan 6alla yana Ci,yayin da idanuwanshi ke kallon fuskarta,ita kuwa tuni ta kawar da idanuwanta daga kallonshi da take yi,sai dai satar kallon mouth ɗinsa da take yi,yadda yake chewing ɗin gurasar,soft lips ɗinsa na motsi ba ƙaramin fisgarta yake yi ba,sun 6ata mintuna a wurin nan,har sai da ya kammala ci sannan Sehrish ta miƙe ta nufi fridge,Coke ta ɗauko mashi mai sanyi ya kora da shi,bayan ya kammala sha Ya nufi bedroom ɗinshi,bin bayanshi tayi don ta gyara mashi ɗakin,A tsaye ta same shi ya kara waya a kunnanshi yana magana,
Shiga ciki tayi da sallama abakinta,kaitsaye ta fara gyara mashi bed É—inshi,tana jin moving É—inshi lokacin daya kammala yin wayar ya faÉ—a toilet,jim kaÉ—an ya fito yana gyara wrist watch É—in hannunshi”Am leaving”Shi ne abunda taji yace,juyowa ta É—an yi tare da kallonshi”when are u coming back”?daÆ™yar ta samu ta iya tambayarshi,tana Æ™oÆ™arin yin practice É—in abunda Azeema ta koya mata,
Shi kanshi ya jinjina tambayar da tayi mashi,hakanan kawai dai yace”Zan kai 12 na dare,”
GyaÉ—a kai tayi tare da mayar da hankalinta kan Gadon da take gyarawa,tun kafin ma ya fita harta fara Missing É—inshi,ga wani abu da ke yi mata yawo a kanta,Tana so ta sanar dashi about Junaid’s ring da ta gani a cikin drawer É—in Azmee amma ta kasa faÉ—a mashi,saboda bata Æ™arasa investigation É—inta ba,Amma taci alwashin muddin ta gano dasa hannun Azmee dumu dumu saita gaya mashi ne,’

tana cikin wannan zancen zucin unexpected taji yayi hugging É—inta ta baya,gaba É—aya ya saukar mata da kasala,hannayenshi ya zagayo ta saman stomach É—inta,A hankali yake rubbing tsinin Hancinshi asaman fatar wuyanta,lumshe idanuwanshi yayi tamkar maijin bacci,bakomai yake yi mashi yawo acikin kanshi ba,fa ce zancen Marshal Na little Junaid,Still yana deciding din lokacin da ya dace ya aiwatar da hakan duk da yanzu baya cikin kwanciyar hankalinshi,wata irin kasala ce ta kama kowannansu ya jima ahaka kafin ya saketa,da sauri ya fuce daga Bedroom É—in yana jiyo voice É—inta tana yi mashi adawo Lafiya,

Fitarshi ke da wuya,Sehrish ta zauna gefen gadonshi tana tunanin ta yadda zata iya taimaka masu,remain 4 days Yanzu acikin waÉ—annan kwanakin Yakamata Su gano Abu biyu waÉ—anda suka kashe Junaid,ko kuma shi junaid É—in if he’a still alive,Kamar yarda Aunty azeema take hasashe,abubuwa da yawa sun shige mata kanta,akwai buÆ™atar zuwanta É—akin azmee domin Æ™ara yin bincike,Sai dai tana tsoran Azmee ta kamata,

Also Download Hira Da Matattu Page 1 By Jamila Umar Tanko

Miƙewa tayi taci gaba da gyaran ɗakin,bedroom ta fara gyarawa,kafin ta shiga toilet ɗinshi nan ma ta gyara,dawowa palourn tayi tana Aiki tana sambatu kamar wata zautacciya,

Wuraren ƙarfe 4 na yamma,Amrish na kwance tana bacci saman katafaren gadonta,daga ita sai gajeran wando black colour,sai half vest wadda bata rufe cibinta ba,juyi ta soma yi alamun zata farka daga baccin,lokaci guda ta ware manyan idanuwanta tana kallon ceiling,ranta yayi matuƙar 6aci lokacin da ta tuna dalilin yin baccin nata,sam batasan ya ɗauketa ba,kuma tana zargin cewa maganin bacci aka bata,dama kwanakin nan duk in Mommynta zatayi baki saita ɗura mata ƙwayar da zata sata bacci,Yawanci acikin abunsha take sanya mata,miƙewa tayi daƙyar saboda kasalar da take ji,Saukowa tayi daga saman gadon tana miƙa tare da yin Hamma,toilet ta nufa zata shiga sai kuma ta fasa,Fitowa tayi daga cikin ɗakinsu ta nufi bedroom ɗin Mommynta,hannu tasa zata ruƙo handle ɗin ƙopar ɗakin don ta buɗe,Surutun da tajiyo daga cikin ɗakin yasa ta dakata,tare da kasa kunnanta tana sauraranta,
“Wlh bazan ta6a Æ™yalesu ba,Zasu yi galaba akanmu ne,ai kawai ku kashe shi,ku kashe shi kawai,ko ku cire mashi idanuwanshi,Uban kowa ya rasa,idan har ba zaku iya É—aukar mataki ba,to ni zan É—auka dakai na,”da alama waya take yi,yadda kasan yar daba,
Hankali amatuƙar tashe,ta toshe bakinta da hannunta,gudun kada ta saki ihu,jikinta sai kerma yake yi,lalla6awa Amrish tayi cikin sanɗa ta koma bedroom ɗinta,agefen gado ta zauna,Yayin da zuciyarta ke ta bugawa,Dama ta jima tana zargin Momynta,
“Amma mommy bata da Imani,sai cewa takeyi akashe akashe,kamar wata zararra,wlh nima bazan Æ™yaleki ba mommy ki yi kisan kai ina gani,Zan cigaba da samaki ido ne batare da kinsani ba,kuma Allah muddin nagano cewa kashe Æ´a’Æ´an mutane kikeyi da kaina zan kaiki Æ™ara wurin hukuma su garÆ™ameki,”tana magana tana cizon le6enta,

Turo ƙopar ɗakin nata akayi,da sauri ta baje saman gadon tana baccin ƙarya hada minshari,mommy ce ta shigo hannunta ruƙe da wayarta,

Zuba ma Amrish ido tayi tana kallonta,kafin ta Kanga wayar a kunnanta
“Har yanzu Bata farka daga baccin ba,Ni na bata maganin bacci,Wlh ta cika sa ido,ga bin Æ™waƙƙwafin tsiya,Har sa’insa take yi dani shiyasa nake bata maganin bacci”dakatawa ta É—an yi da yin maganar tana sauraron wanda suke yin wayar dashi,

“Ae ni na kwace wayar hannunta,Shiyasa ko ka kira bazaka same ta ba,idan ba haka ba zata iya zame mun matsala,”
Kasa kunne Amrish tayi tana sauraronta,Aranta tace”Asirinki ya tonu mommy,yau naji da kunne na,wato ke kike bani maganin bacci ina sha,ko wa take faÉ—ama cewa ina bacci hmmmm,ta Æ™arasa zancen zucin tare da jan dogon numfashi irin na wanda yayi nisa a baccin nan,
“Okey,Bazan barta da yunwa ba,Yanzu zan tashe ta taci abinci,Ae bazan Æ™ara wasa da lafiyarta ba,duk da bata da hankali,”
Sallama sukayi da mutumin da take yin wayar dashi,zama tayi daga gefen gadon,a tsanake ta soma kiran sunanta
“Amrish!Amrish!”kusan sau biyar tana ambaton sunanta,hada bubbuga Æ™afarta,A hankali Amrish ta É—an buÉ—e idanuwanta,muryarta a kasalance ta furta”Mommy,lafiya kike Æ™wala mun kira”?
“Tun É—azu kike bacci,Ko sallah bakiyi ba halan?Ga la’asar ma na Æ™oÆ™arin yi,ki tashi ga Abincinki can a dining kije ki ci,”
miƙewa tayi daga zaune,tana yin hamma kafin ta wuce cikin toilet,koda zata rufo ƙopar saida ta ƙara leƙen Mommynta,kafin ta datse ƙopar,

*AMANI*

Zaune suke acikin falon gidan,Hayaam Da Abra na zaune saman 3 seater,Yayin da Amani ke zaune saman 2 seater,hayaam ce ta soma magana”Aunty Amani,mun yanke shawarar zamu koma gida gobe,bai kamata mu cigaba da zama anan ba muna É—aura maku nauyinmu,kinyi mana abunda bazamu ta6a mantawa ba,”ta Æ™arasa maganar yayin da idanuwanta ke acike tab da kwalla,
Ajiyar zuciya amani ta sauke tare da cewa”Shikenan,gaskiya yakamata ku koma kam kodan Saboda Mammy da Abra ta baro kwance tana jinya,Bamusan a wani hali take ciki ba ayanzu,’
“Aunty laila fa’?Abra ce tayi tambayar,
Hayaam tace”Ina ruwanmu da ita?tana raye kota mutu matsalarta ce,bata da amfani acikin rayuwarmu,”
“Kada ki ce haka hayaam,itafa Æ´ar uwarkuce,duk da bata kyauta maku ba amma bai kamata kuyi watsi da ita ba,Yanzu dae bamu san awani hali take ciki ba,Amma mujira mu gani,indai Laila ce nasan zata dawo ne,sannan ina Æ™ara gargaÉ—inku akan irin rayuwar da kuka É—aurawa kanku,musamman ke Abra,kinga dai irin abunda ya faru da hayaam kema kuma in baki kiyaye ba,zaki jefa rayuwarki cikin hatsari ne,mazan da kuke mu’amala dasu É—aya daga cikinsu bazai iya aurenku ba,Idan ma ya aureku to bazai darajaku ba,sannan kullum zaku kasance cikin zargin juna,so wannan rayuwar ba mai 6ullewa bace,kuma ku mika dukkan al’amuranku wurin Allah,duk abunda yake rabonka ne kana zaune zai same ka,in ku ka ga baku samu abunda kuke so ba,to Allah bai kaddaro rabon ku bane….”sosai Amani tashiga yi masu nasiha jikinsu duk yayi sanyi,hada kuka,

Also Download>>> Mijin Malama Page 1 By Nimcy Sarauta

Suna cikin tattaunawar nan,Amal ta faÉ—o cikin falon,hannunta ruÆ™e da wayar Amani,Æ™arasowa tayi wurin da amanin take a zaune ta miÆ™a mata wayar”Yaya Abbas ne ya kira,”
Harararta Amani tayi”Dama wayata tana a hannunki,”?sunnar dakai Æ™asa tayi tana dariya,
“tare da Amal zamu tafi gobe’?acewar abra,tayi maganar tana kallon Amal É—in
Wani irin kallo Amal tayi mata,hada cizon la66a,dariya Amani tayi tare da cewa”Ba zaki bisu ba,kinga yanzu komai ya dai daita,ki amince kawai ki koma cikin Æ´an uwanki da zama,
A shagwa6e Amal ta bubbuga Æ™afarta tare da ruqe qugunta”Nifa wlh bazan bisu ba,idan kin gaji da zamana ne a gidanki,nan bada jimawa ba,Yaya Jahan zai É—auke ni,”
Gaba daya suka zuba mata ido suna kallonta cike da mamaki a fuskokinsu,banda Amani dama ita tasan tsakaninta da Jahan,
Murmushi Amani ta saki tare da cewa”Nima wasa nake maki,Ae Amal ta gama zaman maiduguri in ba dai zuwa kai ziyara ba,daga Abuja sai Æ™asar waje ko ba haka ba?’cike da zolaya tayi mata maganar,
Murmushi Amal tasaki,tare da juyawa da gudu tabar falon tana dariya
Tashin sense,jikinsu Abra ba ƙaramim sanyi yayi ba,duk irin burin da suke dashi na zama surukan Alexandra ya tashi abanza,Sai gashi Yarinyar da suka raina,Suke wulaƙantawa ita ke da rabon auran jinin Alexandra,Abun ba ƙaramin ta6a masu zuciya yayi ba,sunyi danasanin rayuwarsu,zuba masu ido Amani tayi tana kallonsu ganin yadda kowa tasha jinin jikinta,

*General Ishaq*

Fitowarshi kenan daga cikin toilet,Jikinshi sanye da jallabiya,tun yana acikin toilet yaji ringing É—in wayarshi,Æ™arasawa yayi tare da kai hannu ya É—auki wayar,New number ce aka kirashi da ita,Bin kiran yayi kiran na shiga aka É—aga wayar”Assalama Aleekum”muryar wani inyamurin mutunce,
“Wa’alaikum salam,ko zan iya sanin dawa nake magana”?
On the other hand mutumin yace”Yalla6ai dama wani bawan Allah ne keson magana dakai,Shine yace in taimaka in kira mashi layinka,”
“To bashi wayar,”tsayawa yayi yana jiran jin muryar mutumin da akace yana son magana dashi,
Abun mamaki sai yaji kukan Laila Acikin wayar,ya cika kunnanshi,cikin shessheÆ™ar kuka ta wanda ya galabaita ya jigata sosai ta soma magana”Abban hafsat ni ce laila,dan Allah akawo mun É—auki,ina cikin mawuyacin hali,”
Murmush Ishaq ya É—anyi tare da cewa”Bangane wake magana ba?kodai wrong number ne aka kira”?

Also Download Banana Island Book 1 Hot Romantic Hausa Novel Complete Document

Jin haka yasa ta Æ™ara sautin kukan nata”Ishaq kada kayi mun haka,Wlh ina cikin masifa,gani nan a Enugu yashe gefen bishiya,sai an bani sadaqa sannan nake samun abunda nake sawa acikina,Wlh Ishaq na tuba nabi Allah,Akawo mun agaji Æ™afata ta lalace ta ru6e….”tana magana tana kuka,
Handsfree ya sanya don yaji daÉ—in sauraronta,Sai da takai Æ™arshen maganarta sannan yace”the number you’re trying to call is switch off,pls try again Later”yana kai Æ™arshen maganar,yayi rejecting kiran yana dariya,ko kaÉ—an baiji tausayin kukanta ba,Don tafita aranshi kwata kwata,Yayi mamakin jin wai tana a Enugu ko ubanme yakaita enugu?ta6e le6enshi yayi tare da faÉ—in”I don’t care Allah ya raka taki gona,nasamu na rabu da jangwamgwam,”
Ƙarar shigowar message yaji,da sauri ya duba screen din wayar ya soma karanta saƙon
_Ishaq ka taimaka ka ceci rayuwata,wlh ina cikin masifa,naga tashin hankalin da banta6a gani ba Ishaq,wayar ma aronta nayi a hannun wani inyamuri,kayi taimakon musulunci ishaq karka duba halina,dan Allah zakayi,ataimaka a dauko ni daga Enugu ko maiduguri ne a mayar dani in mutu acan_
Guntun tsoki ishaq yaja,tare da yin deleting É—in saÆ™on,a karshe ma blacklist ya tura number,yadda ko an kira baza a same shi,”
Murmushi ya saki lokacin daya tuna da hajjaju,macen da yake burin aure,duk da taƙi amince mashi amma kullum saita kirashi ta tambayi lafiyarshi,Wannan ya tabbatar mashi da cewar tana sonshi,tunda ta damu dashi,sannu a hankali Zai samu yayi Wuff da ita ya kawota Cikin gidan shi,

*Boss Bature*

Yinin Ranar Sehrish da Ciwon kai Tayi shi saboda tsabar tunane tunanen da take yi,ta kasa tsaye ta kasa zaune,Har magani tasha amma kan yaƙi lafawa kamar ana kunna wuta acikin ƙoƙan kan nata,abun ya ɗaure mata kai yadda Azmee ta share zancen bata Labarinta,Har lokaci suka samu amma bata tada zancen ba,kuma ko tayi yunƙurin zata tuna mata sai tayi saurin Canza zancen,hakan ne yasa Sehrish ta fara accusing ɗinta,Ta sanya mata ido sosai duk wani motsinta akan idanuwan sehrish take yinsu,

Wuraren ƙarfe 9;30 na dare,gidan yayi tsit da alama wasu daga cikinsu sunyi bacci,Oummansu kaɗai ta rage a ɗakinsu,Zaune saman sallaya tana tasbihi,Yayin da su sehrish ke kwance saman gadon,hosana da jahad sunyi Bacci banda Sehrish wadda idonta biyu,ta kasa runtsawa,jira take yi Oummansu ta kammala Sallar ta dawo saman gadon ita kuma ta koma ɗakin Azmee,

Also Download Dr Eeshatt Romantic Hausa Novel Complete Document

Tana cikin Jan cazbahar nan wani abu ya faÉ—o mata aranta,abunda ta jima tana Æ™oÆ™arin tunanawa,a hanzarce ta miÆ™e jiki na rawa ta tunkari gefen da sehrish take kwance saman gadon,Hannu tasa tana É—an bubbuga kafaÉ—arta”Rishi!rishi!ko kinyi bacci ne,”yatsina fuskarta ta É—an yi daÆ™yar ta iya huÉ—e idanuwanta,
“Tambayar da kika yi mun game da wannan Auntyn taku Azmee,Na tuna inda nasanta..”tunkan takai Æ™arshen Maganar,jiki na rawa Sehrish ta tashi daga zaune tana kallonta”Oumma a ina kika Santa?
“Zan faÉ—a maki Sehrish amma fa karki kuskura ki sanar da ita cewa nasanta,tunda bansan da wata manufa take zaune acikin gidan nan ba,”
“Bazam faÉ—amata ba Oumma”
Jinjina kai abu ta É—anyi”Wannan matar da kike gani,Lokacin da na haifeku babu wanda yazo yi mun wankan jego,Sai daga baya Ya sayyadi yazo da ita amatsayin Æ´ar uwarshi da zata yi mun wankan jego….”
Jin wannan maganar yasa hankalin Sehrish yayi mugun tashi,Saboda tsabar kiÉ—ima gaba É—aya idanuwanta suka firfito waje,Hannu tasa ta daki Æ™irjinta”Ƴar uwar Ya sayyadi!”ta ambaci hakan a tsorace
Abu ta lura da Yanayin da Sehrish ta shiga,bata dakata da yin maganar ba taci gaba da cewa”Wlh Sehrish matarcan da kike gani,Ba Æ™aramar shu’uma bace!abun tsoroce ita,Dalilin dayasa nace maki haka,Lokacin da sayyadi yazo mun da ita don tayi mun wankan jego,Kamar kurma haka ta koma,duk in naso na bugi cikinta don ta sanar dani wani abu game da danginsu,Sae taÆ™i tanka mun,Nasan dai ta bani kyakkyawar kulawa a lokacin amma gaskiya ba abun yarda bace,saboda nayi mamaki dana ganta acikin gidan nan,Kuma sai surutu take yi kamar ba ita ba,Sa6anin a yadda nasanta lokacin da tazo gidanmu ko uffan bata cewa,daga um sai um um shine abunda ke fitowa daga bakinta,”
Hannu sehrish tasa tare da dafe kanta dake jujjuya mata,a hankali tashiga furta”Innalillahi’wa’inna ilaihirraji’un!Amma Azmee ta gama damu!indai abunda nake zargi ya tabbata to tabbas Azmee Itace Ƴar leÆ™en asirinsu dake fitar da surrukan gidan nan……”
Cike da mamaki abu ke sauraron kalamanta sae da takai Æ™arshen maganarta Sannan tace”Meyasa kika ce haka?Dama kina zarginta ne?Amma naga kamar kuna zaman lafiya da ita,’
Hawaye na kwaranyowa akan furkarta ta shiga faÉ—in”Oumma,muna cikin tashin hankali in har ya kasance AZMEE itace take shirya maÆ™arÆ™ashiya acikin gidan nan….”dafa kafadarta abu tayi”ki sanar dani abunda yasa kike zarginta inaso inji,ko Zan iya taimaka maku”
Duk da tana cikin mawuyacin hali na firgici,haka ta zauna ta kwashe dukkan abunda ke wakana acikin gidan ta sanarwa Oummansu,abun mamaki tana kai ƙarshen maganar sai taga Abu na murmushi gami da girgiza kanta,
“Oumma ko kin gano wani abu akanta ne?naga kina murmushi,”

Also Download Wace ce ita (Who was she) Hausa Novel Complete Document

“Akwai wani abu da nakeso na sanar dake sehrish!Shi É—an adam ba abun yadda bane,Bakomai zaisa kiyi kokwanto akan azmee ba fa ce Yardar da kukayi da ita,Ta ko’ina azmee ta gama daku,Ta siye zuciyoyinku ta hanyar kyautatawar da take yi maku,Shi mutun maison É—aukar fansa,Zai iya yin 6adda kama ya shiga jikin maÆ™iyansa har na tsawon shekaru Yana yi masu bauta batare da gajiyawa ba,yayin da yake shirya masu maÆ™arkashiya batare da sun ankare ba,Har sai ranar da ya tarwatsa su gaba daya tukunna zai bayyana kanshi,Yanzu kinga gaba É—aya ta gama sanin surrukanku……”dakatawa abu tayi da yin maganar,Ta jinjinawa azmee sosai,ta iya shirya tuggu
“Gaskiya sehrish dole kiyi taka tsantsan,don wlh in har ya kasance zargin da muke yi ya zama gaskiya,To fa Azmee ba Æ™aramar shu’uma bace,Kuma zata iya kashe duk wanda yayi gigin tona mata asiri,a yadda ta faro shirinta tsawon lokaci yanzu bazata bari wani Ya fallasa ta ba,”
“Amma Oumma,nibansan ya zanyi ba,abubuwa sunyi mun yawa akaina,”tayi maganar damuwa Æ™arara a kan fuskarta,
Dafa kafaÉ—arta abu tayi”Ni dai shawarar da zan baki shi ne,Ki samu wani babba ki sanar dashi komai dangane da ita…..”
A ruÉ—e sehrish tace”Wazai yarda dani Oumma!idan har na faÉ—i cewa Azmee Æ´ar uwar sayyadi ce,kuma ina zarginta da mutuwar Junaid”
“Tabbas kuwa babu wanda zai yarda dake a halin yanzu,a Æ™arshe ma reshe zai iya juyewa da mujiya,Zata iya É—aura maki laifin kinsan fa shi mugun mutun hatsari ne shi,balle su da suke da tsafi,duk da dai mu mun dogara da Allah ne,babu ja da baya Allah shi zai bamu kariya,”
“Yanzu ya zanyi!inaso naci gaba da bincike akanta,Saboda inaso na tambayeta dangane da zoben Junaid dake a wurinta me yakai shi cikin kayanta,”
“Nace maki karki kuskura ki ce zaki nuna cewa kinsan wani abu game da ita,in ba haka ba zatayi maki mummunar illane,Nidai shawarar da zan baki A yanzu ki damÆ™a binciken nan a hannun É—aya daga cikin mutanen gidan nan,Zaifi ma ki sanar da Daddynku,Zan ma yi mashi magana,nasan zai yarda dani sosai’
Shikenan Oumma,Yanzu zan iya zuwa É—akinta in kwanta”?
“Me zai hana amma dai ina Æ™ara jan kunnanki akanta,karki kuskura ki tsananta bincike akanta,Don zata ganoki ne,”gyaÉ—a kai Sehrish tayi tare da saukowa daga saman gadon ta nufi hanyar fita daga É—akin,ruÆ™o handle É—in Æ™opar tayi,bayan ta fita taja Æ™opar ta rufe,gyara kwanciya Oummansu tayi saman gadon,ita kanta abun ya razanar da ita,Ta yadda akai har Æ´ar uwar sayyadi ke aiki acikin gidan,daÆ™yar bacci yayi awon gaba da ita,

Tafiya sehrish takeyi kamar wadda aka zarewa lakar jikinta,komai ya tsaya mata Cak,don abun ya girmi tunaninta,a Æ™opar É—akin Azmee ta tsaya gabanta na faÉ—uwa a hankali ta furta”La’ila ha illa anta subhaka inni kuntu minazzalimin,tana kai Æ™arshen addu’ar ta tura Æ™opar ta shiga daga ciki,abun mamaki bata samu kowa ba acikin É—akin,Ranta ne ya bata cewar kodai ta shiga toilet ne,
A wauta irin na Sehrish,maimakon tabi abunda Oummansu ta sanar da ita,Sai ta soma tunanin Yin bincike acikin É—akin don a qagare take da ta gano gaskiyar wacece AZMEE,

Also Download Nurul Kalb Hausa Novel Complete Document

Agaban bedside drawer ɗinta ta zuƙunna jikinta na kerma,ta shiga bubbuɗe drawer chest ɗin,Yawanci duk tarkace ne na magunguna sai ƴan ƙulle ƙulle kamar na maganin Zafi,gida na ƙarshe ta bincika anan ne taga abun daya ɗaure mata kai,Ƙura ido tayi tana kallon Galleliyar wayar dake ajiye a wurin,Ƙirar i phone 13pro

Batasan lokacin da ta furta”Ya Allah!dama Aunty Azmee tana da waya?Amma meyasa ban ta6a ganin wayarta a hannunta ba,”ta Æ™arasa maganar tare da zura hannunta ta É—auki wayar,ta kunna power É—inta,Nan take haske ya kawo,Gabanta ne ya faÉ—i Ganin Hoton dake ajikin Wallpaper É—inta,bakowa bane face Fuskar HAROON,da Æ´ar Æ™uruciyarshi,nan fa tashiga ruÉ—anin abun al’ajabin da take gani,Menene AlaÆ™arta da haroon da har ta É—aura hotonshi a fuskar wayarta?dama ta jima tana zargin haroon ba mutumin kirki bane,kodai hadashi atare suke shirya maÆ™arÆ™ashiyarsune?

Tana cikin wannan wasi wasin,kira ya shigo cikin wayar da baÆ™uwar lamba,kwata kwata babu sautin ringing an sanya wayar silent,Yadda ko an kira baza’aji Æ™ararta ba,

Sehrish da karanbani sai ta É—aga kiran tare da kara wayar a kunnanta,
Shiru tayi tana jiran jin wanene zaiyi Magana,
Cikin harshen fulatanci taji ana magana,gashi ita bata iya yaren ba,Tunani ta shiga yi dama azmee bafullatana ce?dama ta ta6a ganin Zanen kalangu a gefen fuskarta,

Tana cikin wannan zancen zucin tajiyo takun tafiyar mutun yana tunkaro É—akin,Ba shakka Azmee ce,A tsananin tsorace Sehrish ta katse kiran,gashi wayar akwai password,babu yarda za’ae ta goge kiran da akayin,dole idan aka shiga Call log agane cewa An É—aga kiran da akayi,
A matukar firgice Sehrish ta tura wayar acikin drawer ɗin,Duk tabi ta ruɗe ta rasa inda zata dosa,A ƙarshe ta faɗa toilet ta rufe,tana faman sauke ajiyar zuciya,jijiyoyin wuyanta duk sun fito saboda tsabar tsoro,Tayi danasanin ɗaga kiran wayar Azmee da tayi,

A hankali Azmee ta turo ƙopar ɗakin ta shigo,Jikinta sanye da baƙaƙen kaya,Jallabiya ce tare da mayafinta,kamar wadda taje anguwa,zama tayi daga gefen gadon,tare da kai Hannu jikin drawer ɗin ta ɗauko wayarta,dannata ta shiga yi,kafin ta danna call,

Sehrish dake la6e acikin toilet É—in da alama mutumin da ya kira Sehrish ta É—aga shi Azmee ta kira,Addu’a sehrish tashiga yi hannunta na kerma ido ya raina fata,tuni zufa ta wanke mata fuskarta,Ga fitsari daya matse,ta kasa tsugunnawa tayi futsarin gudun kada azmee taji Æ™arar fitarshi,
Ba ƙaramin haushi Sehrish taji ba lokacin da Azmee ta soma Magana Cikin harshen fulatanci,taso ace da yaren hausa tayi maganar don ta samu taji abunda zata ce,yanzu ta ƙara ƙarfafa zarginta akan Azmee,

*Boss Bature*

Around 10pm

Jami’an da Sgr ya sanya su tsare grave É—in Junaid,sunyi 6adda kama yadda kasan ba Sojoji ba,kowannansu na sanye da Kaya namu na hausawa,riga da wando na yadi,É—aya daga cikinsu yana zaune saman dogon benci yayin da É—ayan ke zuÆ™unne agaban bencin gefenshi kayan Shoe shiner ne,Yana goge ma na saman bencin Takalminshi,dayake akwai hasken street light,Bakomai suke jira ba fa ce wannan mai zuwa yana yin zarya a Æ™abarin nasa,bisa Command É—in da Sgr ya basu nasu sanya ido akanshi idan ya Æ™araso,Su sanar dashi yana so yaga ko wanene,Suna zaman jiran zuwanshi,Aikuwa cikin sa’a Æ™arfe goma na bugawa,kamar yadda ya saba zuwa,Sai motar nan Æ™irar Venza ta shararo da gudu izuwa titin,tunkan ya Æ™araso É—aya daga cikin sojojin wanda ke zaune saman Bencin yace”Gashi nan!yakamata mu sanar da Sgr,tun kafin ya kufce mana”
Wanda ke goge mashi takalmin yace”sai munyi taka tsantsan if not zai gudu ne,”

Koda ya ƙaraso wurin ƙabarin slowly yayi parking ɗin Motar a gefen titin batare daya fito ba,

Download>>> Bintu Diyar Bayi Ce Book 1 Complete Document

A hankali Sergeant ɗinnan dake zaune saman bencin ya ɗauko wayarshi tamkar yana dannata,message ya turawa Sgr,bayan ya kammala tura saƙon Ya mayar da wayar cikin trouser ɗinshi,

Buɗe murfin motar yayi tare da saukowa daga cikinta,kamar yadda ya saba zuwa haka yau ma yazo,Ya sanya face mask a fuskarshi yayin da idanuwanshi ke sanye da glass baƙi,Jikinshi na sanye da Crazy jeans tare da T-Shirt purple,tafiya ya soma yi har izuwa gefen bishiyar nan inda aka kewaye ƙabarin Junaid,tsayawa yayi kamar mai neman wani abu,hada ruƙe qugu,kusan minti 5 kafin ya soma zagaye bishiyar yana jinjina kanshi,

Miƙewa ɗaya daga cikin Sojojin nan yayi,A hankali ya nufe shi batare daya ankara ba,koda matashin nan Ya lura da cewa wani na tunkaroshi,Aikuwa da gudun gaske yabar wurin bishiyar,Sojojin nan suka bishi a guje,duk yabi ya rude ko motarshi bai tsaya ɗauka ba,a rikice ya faɗa saman titin yana gudun ceton rai kamar zai tashi sama,da gudu suma suka bi bayanshi don karya kufce masu,yana gudu yana waiwayen bayanshi,Unfortunately Yana ƙoƙarin karya kwana,Adai dai Lokacin Motarsu Sgr ta shawo kwanar,Kwatsam ya faɗama motarsu ta bugeshi sosai,ya saki wata irin razananniyar ƙara tare da zamewa ya faɗi wanwar ƙasa,Ƙarasowa Sojojin suka yi suna faman sauke ajiyar zuciya,Ta kwana gidan sauƙi,

Fitowa Sgr yayi daga cikin motar,Armstrong ma ya fito,Atare sojojin suka sara mashi,Kafin É—aya daga cikinsu ya nuna saurayin dake a kwance Æ™asa yana bullayi”Sir,Wannan shi ne wannan matashin dake zarya a Æ™abarin Æ™aninka,rashin gaskiya yasa yana ganinmu ya zabura zai gudu”,

Zuba mashi ido Sgr yayi yana bin shi da kallon ƙurulla,tun kafin ma Ya cire mashi face mask ɗin fuskarshi,Ya shaida shi,zuƙunnawa yayi saman guiwarshi ɗaya,tare da kai hannu Ya zame face mask ɗin saurayin tare da cire glass ɗin fuskarshi Yayi throwing dinshi saman titin,runtse idanuwanshi yayi jikinshi sae kerma yake yi,

A hankali Ya furta sunanshi”HAROON” kamar bashi ba,Ya rame,yayi baÆ™i,jin muryar Sgr yasa haroon ware manyan idanuwanshi masu kama dana mujiya,koda yayi tozali Da Sgr a hargitse Ya tashi daga zaune yana kallonshi yayin da yake faman zazzare ido,wata irin zufa ce ta soma tsastsafo mashi agefen fuskarshi,.
“Dama kaine”?cike da mamaki Sgr yayi tambayar,
Shiru Haroon yayi bai tanka mashi ba,
“Me kake yi a wurin grave É—in Junaid”
DaÆ™yar ya iya furta”Æ™abarin junaid kuma?yayi maganar tamkar baisan akan me suke magana ba,
É—agowa Sgr yayi tare da kallon sojojin dake tsaye suna ta faman haki”Zaku iya komawa bakin aikinku,”juyawa su kayi da sauri suka bar wurin,
“U will explain it don ubanka,I have been suspecting you for a while,Zuba maka ido nayi kawai inga Æ™arshen gudun ruwanka,abunda ka aikata ne yasa ka gaza samun natsuwa acikin ranka That’s why kazo kana zarya akan Æ™abarinsa”?

Waro ido haroon yayi amatuƙar tsorace Yayi yunƙurin miƙewa ya gudu,damƙar ƙafarshi Sgr yayi hakan yasa ya gaza motsawa,
“Amstrong,É—aukarmun shi ka sanyamun shi acikin mota,”

Karanta>>> Idan Ba Ke Complete Novel Document

Gadan gadan Amstrong ya tunkareshi,Yadda kasan ƙaramin Yaro haka ya ca6eshi asaman kafaɗarshi,Ya turashi cikin motar Sgr,Front seat suka shiga,Sgr da Amstrong Tada Motar yayi da gudun gaske ya fisgeta,
“Wai ina zaku kaini ne?Motata fa?kun barta a wurin”shiru su kayi mashi babu wanda ya tanka mashi,
“Wlh kada kuce zaku ta6ani,Rafayet ku sauke ni in kama gabana!Ni bansan akan me kuke magana ba”Sai faman sambatu yake yi,zufa duk ta wanke jikinshi”
Har Lokacin basu tanka mashi ba,Æ™oÆ™arin buÉ—e motar yayi donya buÉ—e,amma yaji Æ™opar adatse ta ko’ina babu hanyar da zai gudu,

Da gudun gaske motarsu ta shigo cikin gidan A lokacin Sehrish na la6e cikin toilet ɗin Azmee,Har cikin kunnanta tajiyo sautin Shigowar Motar Sgr,kamar ta fasa ihu haka take ji ga Azmee taƙi yin bacci bare ta lalla6a ta gudu,Sae dannar wayarta take yi,Yadda kasan tasan da zaman wani acikin ɗakin,

Window ta hango acikin toilet ɗin,Da gudu ta nufe ta,so take ta leƙa window ɗin don taga idan shi ne ya dawo dagaske,net ne ajikin tagar,kuma tagar tayi nesa,Tsawon sehrish bazai kai ta leƙa tagar ba,Lalla6awa tayi cikin sanɗa ta ɗauko bokiti,Ta kifa shi ajikin bangon,Sannan ta daddage ta haye saman bokitin cike da tsoran karya fashe bokitin,

Ƙura idanuwanta tayi tana leÆ™an wajen gidan daÆ™yar take hangen wurin da motar Sgr take,fitowa yayi daga cikin motar tare da zagayawa ya ShaÆ™o wuyan rigar haroon ya wurgo shi waje,gaba É—aya ya kife Æ™asa a susuce,Gabanta ne ya faÉ—i rass!lokacin da taga Ya damÆ™o rigar haroon,Tabbas ranta na bata cewar Sun kamoshi ne a matsayin me laifi!tsoranta kada Sgr yayi kuskuren raunata shi,wata’Æ™il Sunji kalamanshi ne dayake cewa zai kashe Farin cikin mutanen gidan Shiyasa suke tuhumarshi,kamar ta bur6a tagar ta fito haka take ji,

ÆŠaukarshi Sgr yayi asaman kafadarshi Ya wuce dashi cikin gidan Amstrong na biye da bayanshi,É—akin horon nan nasu Ya shiga tare dashi,É—akinda idan aka rufe Æ™oparshi ko ihun mutun ba’aji,

Sauke shi yayi yana tangal tangal Zai faÉ—i Æ™asa,Nuna mashi É—aya daga cikin kujeru biyu dake kallon juna yace”Ave a seat,magana nakeso nayi dakai,”
“Nifa bansan komai ba!meyasa ka shigo dani wurin nan”?
Wani irin kallo da Sgr ya wurga mashi yasa shi lalla6awa ya zauna,jikinshi nata kerma,kai cike da iskanci ga shegen tsoro

Zama Sgr yayi suna fuskantar juna yayin da Amstrong ke atsaye yana kallonsu,

Sai faman mazurai haroon keyi,irin na marasa gaskiyar nan,
“Meyasa ka aikata hakan”?girgixa kai ya shiga”Ni wlh ban aikata komai ba,Nifa bansan komai ba,bansan akan me kake magana ba”
Tsabar takaici ne yasa sgr ware yatsunshi Biyar ya kwasa mashi mari asaman fuskarshi,nan take le6enshi ya fashe,hannu yasa ya dafe kuncinshi saboda zafin daya ji,

“Ka faÉ—amun meyasa ka kashe junaid”?
“Rafayet ba zaka ta6a jin komai ba,a abakina”Duk da halin da yake ciki hakan baihana shi gaya magana ba,
..rai amatuÆ™ar 6ace,Sgr Ya damÆ™i kwalar rigashi da iya Æ™arfinshi na Æ™arshe ya daddaÉ—ao da haroon a zafafe ya tunkari faskeken Madubin dake a aÉ—akin,Gaba É—aya ya rotsa kanshi acikin glass É—in,Wata irin gigitacciyar Æ™ara Haroon ya fasa yana fadin”Nashiga uku!Rafayet ka kashe ni!Na bani Na Lalace!!!..”kafin Haroon yayi wani yunÆ™urin kwace kanshi tuni Sgr ya Æ™ara Tarwatsa kanshi Acikin glass É—in madubin,Nan take jini Ya soma tsastsafowa Asaman kanshi,Ya hada mashi Jini da Majina,Fitsari ya saki a wando ya shiga zubowa Zirrrrr yana kawarara Yaji bala’e,
Naushin cikinshi sgr ya shiga yi gaba É—aya,Duk In ya naushe shi sai Jini ya fito ta bakinshi,Ganin yana Æ™oÆ™arin kashe shi yasa Amstrong Yin saurin dakatar dashi Ta hanyar ruÆ™o damtsen hannunshi”Allah ya huci zuci zuciyarka,Bai kamata ya mutu a yanzu ba,Still bamu samu bayanan da muke son samu a wurinshi ba,”

Download>>> Dr Bobby Hausa Novel Document

Ranshi amatuÆ™ar 6ace yake magana”Kabarni in kashe wannan mugun mutumin Mara imani da tausayi!In har ban kashe shi ba,bazan samu kwanciyar hankali ba,Bazan cigaba da jure ganinshi yana yawo araye ba,
Haroon dai tuni ya fita hayyacinshi sai faman ambaton Innallahi wa’inna ilaihirraji’un yake yi acikin bakinsa kamar wani musulmin Æ™warai,Jini duk ya wanke mashi fuskarsh,
Daƙyar Amstrong ya samu ya shawo kanshi,Ya haƙura da zancen kashe haroon,Zuƙunnawa yayi agabanshi Yana kallonshi,Idanuwanshi tuni sun jima da juyewa,Yayi bleeding sosai,
“Sir!ya rasa jini sosai,Yakamata Abashi Emergency treatment,don ya dawo cikin Hayyacinshi,idan yaso sai mu tuhu me shi daga Baya,
Hannu Sgr yasa tare da kinkimar haroon ya wuce dashi medical Room É—insu,Ba don yaso ba haka ya shiga duba shi,Uban bandage ne akan goshinshi,duk ya cire mashi pieces na gilashin daya Sossoke shi,biji biji yake kallonsu

Zama daga gefen gadon Sgr yayi,yana kallonshi cike da jin tsanarshi acikin zuciyarshi,
“Najima Ina samaka ido haroon,ban ta6a É—aukar mataki akanka ba,saboda ina zargin cewa Ba yin kanka bane,Akwai wanda ke take maka baya kana aikata hakan!
“Nazo nigeria ne saboda in Æ™arfafa bincikena akanka,kafin na yanke maka hukunci,Na sanya maka ido sosai duk wani motsinka acikin garin nan ko ince acikin Æ™asar nan a idona kake yinshi!!”
Haroon dai sai binshi da idanuwayake yi,sunyi jawur dasu ga raɗaɗin ciwon da yake ji,ga wani nishi da yake saki don ba ƙaramin jiki yaji ba,
“Tun lokacin da ka sanyawa yarinyar can ido,Ka takura mata akan cewa ta amince ka kusanceta ko kuma Ka tona mata Asiri,Anyi haka ko ba’ayi ba”
Waro ido waje haroon yayi Yana kallonshi,hankalinshi a matuƙar tashe,
Cigaba da magana Sgr yayi”A kwai ranar dana sanya ta kawo mun injection inyiwa kaina,Saboda bata iya karanta hand writting É—ina,Sai kayi mata wayau da nufin zaka taimaketa,Shi ne ka bata allurar Maye ta kawomun,bisa rashin sani har nayiwa kaina”!
Wani irin wahalallan Yawu haroon ya haÉ—iya,abun yayi mugu mugun É—auke Mashi kai!Taya akai duk yasan da wannan?mutun sai kace Aljani
Cigaba da magana sgr yayi”Bayan wannan,Kayi masu Twins barazana akan su baka 80million ko ka fallasa porn video wanda ka É—auka a hotel room É—insu yayin da suke aikata Homo!Anyi haka ko ba’ayi ba’?
Tashin Hankali,kasa buÉ—e baki Haroon yayi sai faman wurga idanuwa yake yi,
“Kullum kalamanka sune zaka kashe farin cikin gidan na,kayi niyar kashe junaid sai kuma ka fasa saboda Æ™aunar da yake nuna maka,Har so kayi ka shiga Jikinshi donka cutar dashi Amma ka gaza yin hakan saboda sonshi da kakeyi,Daga baya kuma Sai wani abu ya faru tsakaninka da Marshal Omar sakamakon marin da kayiwa Reesh,Shi da Uncle suka kwasa maka mari a lokaci É—aya,bayan haka kuma Omar yayi maka bugun tsiya,wannan yasa ka dawo da wannan mummunan Æ™udirin naka na son kashe Junaid…..”tunkan yakai Æ™arshen maganar Haroon daya gama razana yace”Duk ya akai kasan da wannan?kuma meyasa tun lokacin baka hukuntani ba?bayan kasancewa Ni maÆ™iyinku,Na tsaneku bana son farin cikinku,banda burin daya wuce inga na tarwatsa farin Cikinku,Kuma nayi nasara akanku tunda har na Kashe junaid,Ko yau nafaÉ—i na mutu na gama daku,

A fusace Amstrong ya zabura zai É—auke shi daga saman gadon don ya rugurguzashi dasauri Sgr ya dakatar dashi”Ka barni dashi,Na ishe shi,”
“Bansan wanene yake tunzuraka ba haroon,Amma inaji araina cewa Sanyaka akeyi kana yi,Laifin me muka aikata maka?da har muka cancanci hakan a wurinka?me junaid ya aikata maka da har kayi silar mutuwarshi?duk irin halarcin da akayi maka acikin gidan karasa dame zaka saka mana sai wannan?Da wani ido kake tunanin Abbanmu zai kalleka?Ya ta6a banbantamu dakai ne”?

Also Download Banana Island Book 1 Hot Romantic Hausa Novel Complete Document

“Banbanci kuma na yaushe?babu mai sona acikin gidan nan,ba ku damu dani ba,bakusan halin da nake ciki ba,kowa kuna nuna mashi so da Æ™auna acikin gidan nan,Ni kaÉ—aine kuka ware kamar wani bare,”yana magana yana kuka
“Nikaina bada son raina nayi silar mutuwar junaid ba,É—acin raÉ—aÉ—in Æ™uncin da kuke cusa munne yasa har nasa aka bi takanshi da mota,Yanzu bana jin tsoran kowa yaji cewa Na kashe junaid,Saboda nima so nake na mutu,tun ranar dana kashe Junaid na gaza samun kwanciyar hankali,duk wani mugun abu da nake aikatawa na daina duk don saboda shi,haƙƙinshi kaÉ—ai ma bazai barni inyi rayuwa cikin salama ba,Duk ni najawa kaina wannan masifar da nake ciki……..”sosai ya fashe da matsanancin kuka,gaba daya basu yarda da kalamanshi ba,Yana yin magana tamkar wanda yayi danasani,
“Ka fadamun wanene yake baka Command kana aikata hakan?idan har ka faÉ—amun zan Æ™yaleka kayi tafiyarka,”
Girgiza kai Haroon ya shiga yi yayin da hawaye ke kwaranyowa daga cikin idanuwanshi”Wlh bazan iya faÉ—a maka ba!bazan iyaba,da ace zan iya dana fada maka,Amma bazan iya ba,”
Jinjina kai Sgr yayi tare da miÆ™ewa tsaye yana kallonshi”its okey,tunda baza ka faÉ—amun ba,Amstrong É—aukarshi ka mayar dashi É—akin horon nan,”.
Fashewa haroon yayi da matsanancin kukan Yana ƙoƙarin dakatar da Amstrong akan karya ɗaukeshi,abun ba ƙaramin ɗaure masu kai Yayi ba,
“Leave him,”Ya ambaci hakan tare da dakatar da amstrong daga É—aukarshi,”
Allura Sgr ya É—auko,Aikuwa a firgice haroon ya shiga girgiza mashi Kai yana fadin”kada ka kashe ni dan Allah,kabarni da raina,inason Na nemi yafiya a wurin Abba kafin nabar duniya….”
“Kasan daÉ—in ranka meyasa shi junaid ka kashe shi baka bari ya gana da iyayenshi ba?Haroon Rayuwarka bata da amfani”Turmushe shi Amstrong yayi,Sgr ya Caka mashi allurar a wuyanshi,lokaci guda jikinshi ya saki gaba É—aya,Lokaci guda idanuwanshi suka kakkafe,daga bisani ya sanÆ™are babu numfashi,

Tashin Hankali!Haroon Zai rayu Koya mutu?Ya sehrish ƙare acikin toilet ɗin Azmee ga futsari ya matse ta,Junaid Yana raye Koya Mutu?Am confused.

Back to top button