Uncategorized

Tubali Book 1 Chapter 6 complete hausa novel

NA
AISHA ALIYU GARKUWA

Sautin takun takalminsa dasu Ramadan sukaji ne kuma yasa su maida hankali zuwa gareshi.

Idanunsu gaba daya suka zuba mishi, tare da had’a baki gaba dayansu suka ce.

“Masha Allah! Tsarki ya tabbata ga sarkin daya halicce mu ya kuma halicci Hamman Rayyern dinmu.” 

“Innalillahi kai Hamma Rayyern kayi kyau sosai, wallahi kamar daga Saudiya kazo.”

Cewar Riyyam-nsra daya hangame baki da hanci yana Kallon Rayyern d’in.

Shikuwa Rayyern karasa saukowa cikin falon, yayi ganin Abba da Mamy zaune ne kuma yasashi, d’an rusunawa ahankali yace.

“Mammy a bani Bootle water mai sanyi.”

 Mamy da ita kanta ta yaba da tsananin kyawun da al’kyabban jikin nasa tayi masa ne ta saki murmushi, tare da fadin.

“Masha Allah Rayyern kayi kyau, wannan suturar tayi maka kyau, Lallai kuwa ashe Rayyern din nawa ya kerewa sa’a.” 

Ɗan guntun Murmushin   yayi,  Cikin kuma alaman jin kunyar yabonsa da Mamyn nasa tayi yace. 

“Nagode sosae Mamyna.”

Abba daya kafe Rayyern din da ido kuwa baya ko k’yaftawa, fuskarsa cike da mamaki yace.

“Rayyern wannan shigar fa yaushe ka fara ta? sannan a ina ka samo alkyabba mai tsananin kyau haka?” 

D’an sunkuyar da kansa k’asa yayi, tare da kama y’an yatsun hannunsa ya soma murzawa.

Sam arayuwarsa shi bai iya k’arya ba, impact ma arayuwarsa babu abunda yafi tsana kamar k’arya, bayayin k’arya bakuma yaso ayi masa.

Duk da kuwa yasan Abban nasu bazai so abunba so gskyar da zai fada ba, amma ya zama dole ya gaya masa gaskiya, saboda karya ba d’abi’arsa bace.

“Kayi hakuri Abba Malam Mai-nasara ne ya bani kyautan Alkyabbu guda bakwai.” 

Idanu Abba ya kankance cikin kuma nuna rashin jin dadin hakan ya kawar da kansa gefe. 

Ganin hakanne kuma yasa Rayyern d’in, ya d’an rank’wafar da kansa. 

Kana cikin sigar ban baki yace.

“Kayi hakuri Abba, idan bakason shigartawa sainaje na cire.” 

Ajiyar zuciya Abban ya sauk’e kana ahankali yace.

“A’a ni Bance Banason shigarka ba, kayi kyau Tabbas kuma shigar alkyabba shigace da take da matuk’ar mutumci, gashi kuma ta bayyana tsananin haiba da kwarjininka, saidai amma ka kiyaye nan gaba bafa na son wata alaƙa a tsakaninku.” 

Kai Rayyern din ya jinjina kana cikin girmama zancen Abban nasu yace.

“Nagode Abba kuma Insha Allah zan kiyaye.” 

“Shikenan.” Abban ya fad’a atakaice.

Riyyam-nsra kuwa cikin kasa kosawa da Kallon yanda Hamadan nasu yayi kyau yace.

“Please Hamma Rayyern Ina zakaje.”

“Polo.” 

Ya bawa Riyyam din amsa a taƙaice kuma dai-dai lokacin da yake kokarin fita daga falon. 

Da sauri Riyyam din ya tashi yabi bayansa, yana me fad’in.

“To Hamma Rayyern tsaya muyi video dan Allah.”

Ramadan dake zaune ma mik’ewa tsaye yayi yabi bayansu. 

A compound din gidan suka tsaya, inda Riyyam sarkin tiktok ya saita wayarsa ya soma yi musu video dukansu uku.

Harda sa musu wata y’ar wak’a, shidai Rayyern Kallon Yaron kawai yakeyi, domin a wuni biyu kawai da sukayi da yaron, ya fahimci wani abu, da kuma irin d’abi’a da yaron yayi shura akai. 

Saidai kuma baisan Meyasa ba yakejin yaron acikin zuciyarsa hakan yasa yake kasa yakiceshi. 

Gama k’arasowarsu compound din gidan kuwa, yayi dai-dai da fitowan Baba Maud’o daga cikin d’an madaidacin Part ɗinsa dake gefen gate.

Yana fitowa dinne kuma ya sauk’e idanunsa akan Rayyern, dake sanye cikin al-kyabba.

Wani irin tsayuwa Baba Maud’on yaji zuciyarsa tayi, take kuma wasu irin abubuwa suka shiga dawowa cikin tunaninsa.

Saidai kuma Ina ayanzu kwakwalwarsa bata da wani buk’atar amsar kowani irin sak’o, wannan dalilin yasa zuciyarsa ke cigaba da bugawa da harbawa a hankali.

D’an matsowa kusa dasu Baba Maud’on yayi, tare kuma da sauk’e idanunsa akan Riyyam wanda keta faman bin wak’ar Justin Bieber me suna (Peaches) dake tashi awayarsa. 

Idanu Baba Maud’o ya tsurawa yaron baya ko k’iftawa, Yayinda zuciyarsa ke cike da zallan mamakin, kamannin Rayyern dake kwance akan fuskar yaron. 

“Baba Maud’o barka da yammaci.”

Cewar Rayyern.

Wanda maganan nasa ne kuma yasa Baba Maud’o dawowa cikin tunaninsa. 

Murmushi ne ya bayyana akan fuskarsa, duk da kuwa cewar rabin fuskartasa arufe take, amma hakan bai hana Rayyern din gane cewar Baba Maud’on murmushi yayi ba. 

“Yauwa Barka dai Rayyern, yau kuma inazaka je haka naga kayi shigar da ta bayyana kyau da cikar haibarka.” 

Murmushi Rayyern din yayi, tare da dan matsowa kusa da Baba Maud’on kana yace.

“Wurin wasan polo zanje  Baba Maud’o”.

Kai ya jinjina alamun gamsuwa.

“Shin ko akwai wasu abubuwan buk’ata naka da suka k’are, idan nazo dawowa saina sayo maka.”

Rayyern ya tambayeshi cikin mutunta ma’aikatan gidan nasu.

Again Murmushi Baba Maud’o yayi, cikin kuma Jin dadin kulawan da su Rayyern din sukeyi dashi yace.

“A’a Alhamdulillah ayanzu kam bana buk’atar komai, saidai nace kayi kyau sosai cikin wannan shigar, amma baka daura hiramin naka dai-dai ba, Bari na gyarama irin yanda samarin makka suke saka nasu.”

Murmushi Rayyern din yayi, kana ya matso Baba Maud’o d’in ya gyara masa sakun hiramin.

Riyyam-nsra kuwa da d’an mamaki ya kalli Hamma Rayyern dinnasu, tare da cewa.

“Hamma Rayyern waye wannan mutumin, naga jiya da nazo  banganshi ba.”

“Sunansa Baba Maud’o.”

Ramadam ya bashi amsa.

Saurin jinjina Kai Riyyam yayi, kana ahankali ya matso kusa da Baba Maud’o din.

Fuskarsa dauke da murmushi yace.

“Rawanin da kasa akanka zuwa fuskarka yayi kyau sosai Baba Maud’o, Dan Allah Hamma Rayyern kuzo mu d’auki hoton selfie tare dashi, saboda Idan na koma Ethiopia zan nunawa Mammyna, na kuma bata labarin yanda wasu daga cikin yan Nigeria sukeyin shigarsu.”

Ya fad’i hakan saboda baisan cewa Baba Maud’o’n shigar buzayen Niger 🇳🇪 yayi ba. 

Kamar yanda ya buk’ata kuwa matsowa Rayyern da Ramadan sukayi, inda suka saka Baba Maud’o da Riyyam din atsakiya.

Hakanne kuwa yasa Baba Maud’o da Riyyam din ke iya jiyo sautin bugun zuciyar kowannensu, saboda yanayin yanda sukayi kusan ci sosai da juna, domin Riyyam dan sarkin son jiki, har rungume Baba Maud’on yayi ajikinsa. 

Yayinda Ramadan ya karb’i wayar Riyyam d’in, yayi musu hoton selfie har kala biyu.

Bayan ya mikawa Riyyam din wayarsa ne kuma, 

Rayyern ya juya ya shiga motarsa, driver’nsa yaja suka fice daga cikin gidan. 

Ramadan da Riyyam kuwa zama sukayi dab’as Akan wani dan dogon Bencin da Baba Maud’o  ke zama,  haka kuwa suka sa Baba Maud’on agaba sunata hira, musamman Riyyam daya bud’e baki ya dinga shararawa Baba Maud’on labarai kala-kala, wanda duk rabinsu na abun dariya ne. 

                *Arewa 24 TV*

Jannart ne da Salman ke tafe acikin babban corridor din, da zai sadasu da compound din gidan tv’n nasu.

Anutse Jannart take takunta, Yayinda time to time take Kallon fuskar wayarta dake rike ahannunta.

Salman dake biye da ita kuwa, idan hankalinsa yakai dubu to duk akanta yake.

Baisan meyasaba hardai idan Jannart tana waje, baya tab’a iya dauke kansa daga gareta,  koda kuwa yaya baya iya gajiya da Kallon tafiyarta mai kama data hawainiya.

Yayi Imani azuciyarsa cewa Jannart macece ta gasken gaske, ko acikin mata irinta basu da yawa. 

Isowarsu jikin motarsa ne kuma yasa Jannart fakon idanun guard dinta ta shige cikin motar,  kana cikin sauri tace.

“Please Salman kayi sauri mubar nan, Domin idan wayannan kattin suka ganni dakai ina mai tabbatar maka cewar akwai matsala.” 

“Nikuwa nasan da cewar akwai matsala ai Jannart, abu mai sauki ne ma su samin bindiga akaina su harbeni, tsoron da ake baki agidanku ko Gwamna iyakaci.” 

Salman din ya fada adaidai lokacin da yake ta da motar suka bar wajen. 

Suna hawa titi kuwa Jannart ta sauk’e ajiyar zuciya tare da fad’in.

“Allah Yasa dai mudace mu samu ganinsa yau, amma mutum dan ya zama richest man shikenan kuma ganinsa saiya zama wahala.” 

Shidai Salman murmushi kawai yayi kaman zaice wani abu kuma saiya fasa. 

Kaitsaye suka nufi Mai-nasara Hospital.

Tafiyar mintuna kad’anne ya kawosu bakin kofar katafaren asibitin.

Kasancewar kuma ba ashiga can Cikin hospital din da mota, matuk’ar ba emergency bane, yasa Salman parking motar anan babban parking lot na asibitin, wanda shi kansa ya kusan kwatan wata karamar unguwa. 

Bud’e murfin motar Jannart tayi ta fito, tana me k’arewa kyau da had’uwar asibitin kallo.

Lallai privet Hospital ne daya amsa sunansa, saboda daga ginin asibitin ma kasan ba kananan billions aka kashe masa ba. 

“Mai-nasara Hospital! Lallai asibitin ya had’u.”

Jannart din ta fad’a tana me Kallon Salman.

Shima Salman din kallonta yayi, tare da cewa.

“To Kema da bakinki kin fad’a, yanzu kiyi imagine tayaya za ace kinsamu ganin mamallakin wannan wajen acikin sauki? karki manta kuma bawai iya Hospital dinnan ya mallaka ba, yana da companies, bama a iya Nigeria ba, wallahi Jannart wannan mutumin *Richest Man* ne na k’arshe.” 

Kai Jannart d’in ta jinjina, domin ita kanta ayanzu ta yarda da hakan. 

Kaitsaye kuma suka kutsa cikin asibitin. 

Acan b’angaren Rayyern kuwa kaitsaye Wajen buga wasan polo suka nufa.

Koda suka isa wajen da haduwarsa da kuma kyawunsa ya darawa kwatance.

A parking lot driver’nsa yayi parking.

Bayan ya fito daga motar nasa ne kuma kaitsaye ya nufi cikin wajen.

Da kwata-kwata babu mutane acikinsa.

Duk da tsananin girman wajen kuwa, amma bakajin motsin komai saina tarin dawakai da kuma tsirarun masu kula dasu.

Wanda kuma hakan ya faru ne saboda zuwan Dr.Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara, kasancewar idan har zaizo wajen To yakan biya mak’udan kud’ad’e ne, ta yanda ranar baza’a amshi kuɗin wasuba, harsai yayi wasansa ya gama ak’alla na tsawon awa 2, bayan ya tafi ne kuma sauran jama’a zasu dawo su cigaba da harkokinsu bawai kuma yana haka dan isa bane, sai dan sosai hayani kan iya sa mishi ciwon kai, yana kuma jin daɗi wasan polo a jikinsa. 

Shigarsa cikin babban wajen wasan buga Polo dinne kuma yasashi, zare alkyabban dake jikinsa ya ajiye, tare da wayoyinsa harma da y’ar bag din da yasaka bottle water mai sanyi aciki. 

K’arasawa yayi wajen tarin dokunan da akeyin wasan dasu, tare da zab’o wani farin doki, wanda mafi yawanci idan yazo shi yake hawa. 

Batare da wani bata lokaci ba kuma ya dale saman dokin tare da rik’e Sandar buga k’wallon nasa ya soma sukuwa, tare da gabatar da wasan. 

Mai-nasara hospital.

Salman da kuma Jannart dake tsaye abakin k’ofar office d’inne suka tsaya suna Kallon juna. 

Salman ne ya gyara tsayuwarsa tare da cewa.

“Please Jananrt mushiga mana, kinfi kowa sanin irin wahalan da muka sha, kafun mu samu aka nuna mana wannan office din, wannan ita kadaice daman mu ta karshe, kada muyi wasa da ita.”

Kai Jannart ta jinjina kana asanyaye tace.

“To.”

Knocking kofar Salman yayi, inda Dr Sulaiman dake zaune akan wata hamshakiyar kujera ya bada izinin shigowa. 

Hakanne kuwa yasa suka kutsa Kai suka shiga bakinsu d’auke da sallama. 

Amsa musu sallaman Sulaiman yayi, tare da dago kansa ya kallesu.  

D’an Kallon juna suka tsayayi na tsawon sakanni, kafun daga bisani Dr.Sulaiman din yace.

“Bismillah’nku.”

Ya kare maganan yana meyi musu nuni da wasu kujeru guda biyu dake gabansa.

Yayinda kuma acikin mintuna kadan na Kallon daya musu, ya fahimci cewar sudin ba marassa lafiya bane. 

Zama sukayi akan kujerun daya nuna musu d’in, Salman ne ya mik’awa Sulaiman din hannu suka gaisa, Yayinda ita kuma Jannart ta gaidashi da sassanyar muryarta, wanda har hakan yasa shi kasa jurewa saida ya dago ya sake Kallon ta, Yayinda azuciyarsa yake mamakin jin ta gaishe shi da Hausa, domin sam baiyi mata Kallon y’ar Nigeria kuma maijin Hausa ba, kasancewar yanayin kamannin ta da kuma shigarta da tsarinta dabanne, bawai irin normal mata da kowa ya sani bane, ita din akwai abu na musamman atattare da ita, wanda kowanni irin Namiji idan ya kalleta saiya gane hakan.

“Meke tafe daku? Ko kuma patient kuka kawo?.”

Salaiman ya tambaya.

Jin hakan ne yasa Salman d’an gyara zama, tare da fuskarta Sulaiman d’in, kana atausashe yace.

“Sunana Salman Aliyu, wannan kuma abokiyar aikina ce sunanta Jannart Idi Sale Dakata, Mu y’an Jarida ne, ma’aikata Tashar Arewa24.” 

ID Card d’insu suka zaro tare da nunawa Salaiman daya zuba musu ido.

Salman ne ya cigaba da cewa.

“Munzo nanne bisa dogaro da kuma fatan, dacewar samun ganin Dr.Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara, Dan Allah Dr. Idan akwai taimakon da zakayi mana, ka taimaka muganshi, wallahi ganin nasa nada matuk’ar muhimmmanci, musamman ga Jannart.”

Ajiyar zuciya Sulaiman ya sauke, tare da maida hankalinsa ga Jannart, domin kuwa idan har abunda tunaninsa ya basa gaskiya ne, to Lallai ya kamata ace ya taimaka musu.

Domin ya raya aransa cewa aiki aka basu domin su tattauna da Dr.Rayyern d’in. 

Zamansa ya gyara kana anutse yace.

“Babu damuwa tunda dai harkunzo nan Insha Allah zaku gansa, duk da cewar ayanzu baya cikin hospital d’in, amma Ina da tabbacin inda zaku sameshi, saidai kuma ganin nasa ba shine ba, dan Ina da tabbacin ba lallaine Dr. Rayyern ya amince kuyi hira dashi ba, saboda aduk k’asarnan babu wani gidan Jarida daya tab’a amincewa sukayi hira dashi.” 

Idanu Jannart ta d’an lumshe ahankali, Yayinda ajikinta takejin Wannan shine last chance dinta, akasin haka kuwa zata iya rasa aikinta, wanda kuma shine ke sata acikin farinciki. 

D’an cije labb’an bakinta tayi, kana cikin siririyar muryarta tace.

“Please Dr. I need your help please!! Banason nayi losing job d’ina!!!”

Takai k’arshen maganan muryarta araunane. 

Wanda hakan yasa Dr.Sulaiman Jin tausayin yarinyar, saidai kuma har acikin zuciyarsa yayi mamakin, Jin tace bataso ta rasa aikinta.

Domin yasan kamarta dinnan ba ace daga gidan talakawa ta fito ba, Sam Kwata-kwata ma batayi kama da hakan ba bare kuma waye bai san sunan mahaifintaba Alhaji idi Saleh Dakata.

Sake gyara zamansa yayi, tare da cewa.

“Badamuwa zan taimaka muku Insha Allah, yau Wednessday kuma duk ranan wednessday at this time Dr. Rayyern yakan je wajen wasan Polo, ba kuma ya barin wajen sai 5 na yamma, saboda haka zan baku Andreas din wajen, zakuma ku iya zuwa kusa meshi. 

Wani irin sanyi Jannart taji acikin zuciyarta, Yayinda Salman kuwa yayiwa Dr.Sulaiman din Godiya.

Shikuwa Dr. Sulaiman a paper ya rubuta musu adress din wajen, tare kuma da yi musu fatan nasara. 

Godiya sosai sukayi masa kafun sukayi masa sallama, cikin hanzari suka fito daga cikin asibitin.

Direct wajen da motar Salman din ke fake suka nufa.

Suna shiga kuwa ya tada motar suka nufi wajen buga wasan Polo’n kaitsaye. 

Tafiyar da bata wuce ta 20mn sukayi ba, sai gasu abakin kofar babban mashigar wajen wasan Polo’n da yake duka a unguwa ɗaya ce.

Bayan kuma Salman yayi parking motar ne suka fito, direct mashigan wajen suka nufa.

Amma sai guard din dake tsaron wajen suka dakatar dasu, had’e da cewa bazasu shiga ba, anyi clossing wajen na two hours, suje anjima su dawo.

Rau-rau Jannart  tayi da ido, Yayinda Salman kuwa ya zaro ID card d’insa ya nuna musu, cikin sanin makamar aikinsa kuma yace.

“Mu y’an Jarida ne, ankuma tabbatar mana da cewar mutumin da muke nema yana cikin wajen nan, please dan Allah kubari mugansa, abune na gaggawa.” 

Dan Kallon juna guard din sukayi, kaman zasu hanasu kuma sai suka matsa musu alaman su shige. 

Aikuwa wani irin sanyi Jannart taji zuciyarta tayi,  cikin sauri kuwa suka sakai suka wuce cikin wajen.

Y’an tsirarun mutanen dake wajen suka soma wuce wa, ganin kuma kamar babu alaman yalwan mutane awajenne yasa sukayi tsaya, saboda su kansu basu San ta Ina zasu fara nemansa ba. 

Jannart dinne ta kalli Salman kana zuciyarta akarye tace. 

“Anya kuwa Salman kana ga zamu sameshi anan wajen?” 

Shiru Salman din yayi, alamun nazari dai-dai lokacin kuwa wani ma’aikacin wajen yazo gilmawa ta gabansu.

Salman dinne ya tare mutumin, tare da cewa.

“Dan Allah Malam muna tambaya ne,”.

“Allah yasa na sani.”

Ya basu amsa yana kallon Jannart.

Numfashin gajiya Salman ya sauƙe tare da cewa.

“Please Dr. Rayyern Basheer Mainasara muke nema.” 

Idanu sauran ma’aikatan wajen da sukaji abunda Salman din ya fada suka zuba musu.

Shikuwa wanda Salman din ya tambaya, kansa ya girgiza cike da mamaki kuma yace.

“Dr. Rayyern Bashir Mai-nasara kuma anan wajen? gaskiya bana tunanin hakan, saboda muma bamu sanshi ba, sunansa kawai dai mukeji, amma dama yana zuwa nan dinne.” 

Baki Jannart ta cije tare da sanya hannayenta ta kama waist dinta.

Cike da takaici tace.

“Again na sake rasa damata.” 

“Calm down Jannart, mu k’arasa can cikin wajen mu duba ko zamu dace.” 

Salman ya ce mata.

Fuskarta ta kwab’e saboda zuwa yanzu ta fara gajiya da gantalin neman mutumin tunda shi ba kuɗi bane. 

Amma da yake ta San wannan din shine last hope dinta, hakan yasa tabi bayan Salman suka shige cikin inda ake gudanar da asalin wasan Polo din. 

A dai-dai lokacin kuwa Rayyern yayi nisa acikin wasan nasa, sai sukuwa yakeyi akan doki cike da k’warewa da jin daɗin yanayin wurin shiru ba hayani ba mai takura mishi. 

Yayinda kuma ya kasance shi kad’ai ne awajen yake sashi karsashi. 

D’an shigowa su Jannart da Salman sukayi Cikin wajen, Saidai kuma ganin da sukayi babu kowa awajenne yasa Jannart jingina bayanta da jikin wani k’arfe.

Akasalance tace.

“Salman zuwa yanzu Tabbas inaji ajikina cewar na kusa rasa aikina, wannan ɗan is ɗin  mutumin ba saukin ganine dashi ba, kalli wajen nan fa babu kowa sai wancan mutumin daya bamu baya yana ta sukuwa akan doki shima ɗaya kamar mara aikin yi.”

Takai karshen maganan nata tana me Kallon bayan Dr Rayyern, da yake nesa dasu sosai.

Dan kallonta Salman yayi cikin kuma son k’arfafa mata guiwa yace.

“Karki damu Jannart Insha Allah zamu hadu dashi, Yanzu dai mukarasa wajen wancan mutumin sai mu tambayeshi koya San wani abu dangane da wanda muke nema.” 

Still fuskarta ta kwab’e tare da cewa.

 “shikenan muje.”

Hakan kuwa akayi inda suka k’arasa shiga can cikin wajen wasan dake malale da koriyar ciyawa mai cike da damshi.

 

Suna kara kusantan cikin wurin wasanne kuwa Rayyern din ya juyo da akalar dokinsa.

Sai-dai kuma Sam baisauke idanunsa akansu ba. 

Idanu gaba dayansu suka zazzaro, Yayinda Jannart kuwa cike da mamaki tadan matsa bayan Salman.

Tana fadin 

“Laaa Salman wannan mutumin nefa da na fasawa waya a airport, wayyo Allah Salman nikam kazo mu gudu, tun kafun ma ya ganmu.”

Kai Salman din ya girgiza tare da cewa.

“Mu gudu kuma Jannart? saikace marasa gskiya muje dai ki bashi hakuri dama ai aranar baki bashi hakuri ba, daga ganinsa ma Babban mutum ne watakila ma zai iya taimaka mana muga Dr. Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara din.”

Fiki-fiki tayi da idanunta, kana adan tsorace tace.

“Shikenan muje.” 

Nanfa suka nufi wajen Rayyern d’in. 

Dai-dai lokacin kuwa Rayyern dayake matuk’ar gudu akan doki, batare daya d’ago ko waiwaye ba ya taho aguje. 

Kaitsaye kuma direct inda su Jannart d’in ke tsaye ya nufa. 

Gadan gadan.

Su Jannart din kuwa kansu basu ankar ba, saida dokin ya kusan zuwa gab dasu.

Wani irin k’ara mai cike da tsoro da firgici Jannart ta saka da karfi, tare kuma da daura hannayenta akanta ta rumtse Idanunta k’am, domin ta gama sadak’arwa akan cewar dokin ya nuk’urk’usheta ma angama lokaci ɗaya numfashin ta ya fara fizgan firgici. 

Domin hatta Salman dake gefenta shima yayi surrender.

Rayyern kuwa Sam bai Ankara ba saida ihun Jannart din ya shiga dodon kunnensa, wanda hakan yasa cikin sauri ya dago kansa.

Ganin yana gab da bi ta kansu ne, yasashi saurin.

Damƙe igiyar linzamin  dokin da ƙarfi ya tsayar dashi cak. 

Saboda ganin macen da yayi agabansa ne kuma ya sashi dirowa daga saman dokin.

Bayan ya juyashi.

Wani irin dogon tsaki yaja.

Tare da Kallon Salman wanda keta sauk’e ajiyar zuciya, kana ya watsawa Jannart din dake gabansa wani kallon da yasa cikinta ya murda ya haɗe da numfashin dake sauya salon fita da shiga.

Cikin tsuke fuska yace.

“Bakwa ganine, yanzu idan da nabi takanku fa?” 

“Kayi hakuri dan Allah!” Salman ya fad’a asanyaye. 

Itakuwa Jannart sai ayanzu ta bud’e idanunta, Yayinda gaba daya jikinta ke kakkarwa. 

Hannu tasa ta dafe ƙirjinta.

Rayyern kuwa y’ar gajerar tsaki yaja, batare kuma daya sake ce musu komai ba ya juya ya nufi inda kayayyakinsa suke. 

Yana zuwa kuwa ya zauna akan wata kujerar silver mai daukar mutun uku,

Sunkuyowa yayi tare da bud’e jakan daya shigo da ita ya zaro bottle water, b’alle murfin goran yayi, kana ya soma zubawa akan tarin sumar dake kansa wanda yake jin zufa na tsastsafo mishi. 

Jin da yayi baisamu gamsuwa bane kuma yasashi karkad’a gashin kannasa dan yadda ruwan zai taɓa fatar kansa, wanda hakan yasa har ruwan dake kan nasa ya watsu akan fuskar Jannart.  

Salman dake tsaye kuwa dan matsowa yayi, tare da gaishe da Rayyern d’in. 

Batare kuma daya dago ba ya amsawa Salman d’in atakaice. 

Idanu Salman yayiwa Rayyern dake tsaye, alaman ta gaishe shi.

D’an k’aramin bakinta ta turo gaba tare dasa hannunta ta goge ruwan daya watsa mata, kana asanyaye tace.

“Ina wuni.”

Shiru yayi bai amsa taba, tare dayin kamar ma baijita ba.

“Ina wuni.”

Jannart d’in ta sake fad’a akaro na biyu.

still shiru yasakeyi kamar baijita ba.

“Kibashi hakuri.”

Salman dake tsaye ya fada kasa-kasa.

Karamin bakinta ta sake turowa, cikin kuma wata irin murya mai kama da shagwab’a, sakalci, sanyi da kuma tsoro tace.

“Kayi hakuri please, ranan nayi maka b’arna amma bada sanina nayi hakan ba, Dan Allah da Manzonsa kayi hakuri.” 

Idanunsa yadan lumshe saboda jin ta had’asa da sunan Allah da Manzonsa ne kuma, yasashi gyaɗa mata kai alaman yayi. 

“Nagode.” Ta fad’a asanyaye. 

Shikuwa Salman ganin hakanne ya sashi dan matsowa, cikin neman alfarma yace.

“Dan Allah ranka ya dad’e tambaya mukeyi.”

D’ago Kai Rayyern din yayi ya kalli Salman din afakaice. 

Batare kuma dayace komai ba ya maida kansa k’asa tare da ɗaukan ɗan karamin towel ɗin dake gefe ya fara goge suman kanshi zuwa wuyanshi da fuskarshi da sajenshi da ruwan ya jiƙa. 

Salman kuwa ganin hakanne yasashi Kallon Jannart, wanda gaba d’aya mood dinta ya sanja,tun lokaci da  taga kamar dokin zai takesu ta soma sakin wani irin numfashi sama-sama a hankali. 

Wanda da dukkan alama kuma tsoritan da tayi dazunne yakeson tayar mata da ciwon ta. 

Sanin yanda ciwon keyi mata idan ya tashi ne kuma yasa, Salman din cewa.

“Subahanallah Jannart ciwonki ko?.”

Kai ta gyaɗa mishi cikin jawo ajiyan zuciya da take son yi.

Cikin kula ya nuna mata gefen Rayyern dan babu wata kujerar a nan kusa dasu.

“Maza ga waje ki zauna.”

Ya kare maganan yana meyi mata

Nuni da d’an gefen Rayyern, wanda kuma dama wajen zaman daya rage din bai wuce na zaman mutum daya ba sabida ya ajiye tarkacensa a wajan zaman mutun ɗaya gashi kuma a ɗaya wojen.

Jannart kuwa kasancewar dama ta gaji da tsayuwa kuma ga numfashin ta dake fizga ne yasa, batare da ta musa ba ta zauna awajen sanin in ta zauna zai iya dai-dai-ta. 

Shikuwa Salman ƙara matsosu yayi.

Tare da sake maimaita maganarsa ta dazu.

“Dan Allah ranka ya dad’e tambaya mukeyi.” 

“Inaji.”

 Rayyern din ya fada agajarce, nan ma saboda yaji Salman din ya hadashi da Allah ne.

“Dan Allah wani mutum muke nema”.

Uhum ya kuma cewa a taƙaice.

Gyara tsayuwa Salman yayi tare da cewa.

” Sunan shi Dr. Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara.

Shi  muke nema, munje Hospital d’insa ne aka tabbatar mana da cewa Lallai-Lallai yana nan, shine muke tambaya dan Allah koka sanshi?”

Ad’an fakaice Rayyern din ya kalli Salman, saidai kuma cikin halin nuna ko inkula yace.

“Meyasa kuke nemanshi me zai muku? Wa yace muku yana nan?.”

Jannart dake dan haki ne taja ajiyan zuciya ta fizogishi da ɗan ƙarfi kana tace.

“Mitssss mutun sai rashin gsky, gaba ɗaya ya wahal damu.”

Ta wutsiyar idonshi ya ɗan kalleta a fizge.

Ita kuwa ci ga da cewa tayi.

“Nemansa kawai mukeyi, wallahi daga yanzu kuma ni nagaji, 

Dan bazan zauna inyi ta neman wani can ƙato baƙi mummuna mai ƙaton tumbi ba dan yayi kuɗi yana jin kansa waya masan TUBALI kuɗin nashi ko na haram ne shiyasa yake tsoron yin ido huɗu damu ƴan jaridu.

Kada ya gaza amsa mana tambayoyinmu.”

Numfashin ta fesar a hankali jin ya dai-dai ta.

Salman nata jujjuya mata kai ina bata ganiba bare tasawa bakinta linzamin.

Tsaki ta ɗan ja tare da ci gaba da cewa.

“Mutumin nan ya wahalar damu sosai, na farko dai shiba kudi ba, amma na lura kudi yafi saukin samu akanshi.” 

Alama Salman ya mata akan tayi shiru, da yin gyaran murya.

hakanne kuwa yasa tayi shirun.  

Shikuwa Rayyern tunda ta fara maganan yake kallonta ta wutsiyar idanunsa baki cai-cai.

Salman kuwa gyara tsayuwarsa yayi, tare da fadin.

“Mu yan jarida ne kuma ma’aikatan tashar Arewa24, munzo nanne domin samun daman yin hira dashi, Lallai kuma muna da buk’atar ganinsa.

Domin rashin samun tattaunawa dashi ɗin, dai-dai yake da rasa aikin mu.” 

Fuska Rayyern din yadan tab’e tare da cewa.

“Uhummm.” Atakaice. 

 Jin hakanne kuma yasa jikin Salman yin sanyi,  still cikin yanayin dake bayyana damuwarsa yace.

“Dan Allah In dai kasan hanyar da zanbi wajen ganinsa ka taimaka min, Banason rasa aikina, inason aikina sosai, Dan Allah Idan ka sanshi, ko kuma kasan inda zan sameshi ka fad’amin, domin da wannan aikin kad’ai na dogara, dashi ne kuma nake ciyar da iyalaina da iyayena, dan Allah ka taimaka kada in rasa aikina.”

Tabbas Salman ya karyo lagonsa tunda ya hadashi da Allah da kuma nuna masa aikin shine mafogararsa, Idanunsa yadan lumshe ahankali, batare kuma daya kalli daya daga cikinsu ba yace.

“Naji badamuwa amma dai yanzu kam bayanan, Zan gaya masa idan ya amince shikenan, zan kawoshi har cikin tashan Arewa24 din kuyi mishi duk tambayar da kukeso.” 

Farinciki da tsananin jindadi ne ya lullub’e cikin zuciyar Jannart da Salman.

Cikin bayyana zallan jin dadi Salman yace.

“Mungode sosai ranka ya dad’e, mungode kwarai, saidai amma dama ka sanshi ne?” 

Kansa ya jinjina tare da cewa.

“Eh nasanshi uban gidanane zan gaya masa Insha Allah kuma zaizo zan roƙeshi in gaya masa uzurinka bisa tausayawarsa kan kada ka rasa aikinka da kake kula da ilanka zaizo in Sha Allah.” 

Murmushi Jannart dake gefe tayi, tare da lumshe idanunta saboda wani irin sanyi da taji acikin zuciyarta sai kuma ta ɗan gyara zamanta. 

Shikuwa Salman cikin tsananin jin daɗi  yace.

“Sir! Nagode! Nagode!! sosai!!! Dan Allah kayi mishi magana, ni kuma zan tsumayeka har zuwa nan da y’an wasu kwanaki, wallahi Banason rasa aikina yau kuma saura kwana takwas za’ayi hirar dashi ranar Alhamis na sama.” 

Kai Rayyern din ya jinjina, tare da sake cewa.

“Insha Allah zaizo.”

“Ka tabbatar zaizo?”

Jannart da nutsuwa ya dan fara sauka azuciyarta ta fad’a.

Dan juyawa yayi ya watsa mata harara, cikin zuciyarsa kuwa cewa yayi.

“Oho bansani ba shegen baki.”

Salman da farinciki ya cika zuciyarsa kuwa, cewa yayi.

“Mungode sosai amma dan Allah in ba matsala ka bamu numbern ka saboda idan zaizo din musani.”

Kansa yadan girgiza, cikin kuma rashin sabonsa da yawan magana yace.

“No kai dai ka bani taka numbern.” 

To Salman yace Cikin gaggawa kuma ya bashi numbernsa.

Mikewa tsaye yayi fuskarsa cike da farinciki yace.

“Alhamdulillah Jannart taso mutafi Insha Allah yanzu kam na samu full confidence.”

Yayi maganar yana me soma tafiya, saboda tsananin farincikin da yake ciki kuwa bai majira Jananrt dinba. 

Jannart kuwa ganin Salman din ya soma tafiya ne yasa ta mik’ewa tsaye itama.

Tashin nata kuwa yayi dai-dai da juyowan Rayyern inda ya sauke idanunsa Akan bayanta.

Da sauri ya rumtse idanunshi da ƙarfi tare da kame jikinsa sabida yadda yaji tsikar jikinshi na mimmiƙewa yana tashi tsaye.

Sabida a bunda ya gani ajikinta.

Yadda yaji tsikar jikinshi na tashi ne ya kuma sashi buɗe idanunsa.

Damatsan hannunsa ya kalla gaba ɗaya tattausan gargasar jikinsa ta miƙe tsaye.

Ita kuwa Jannart taku ta farayi da nufin bin bayan Salman wanda haka yasa ta ƙara matsowa gabanshi tana takun dake juya kyawawan mazaunanta.

 Fuskarshi ya kuma yamutsawa.

 Tare da saurin kawar da kansa gefe.

“Meye haka?”

Ya fad’a azuciyarsa yana mai jin kamar ana tsikarinsa

Jannart kuwa da batasan komai ba, ahankali ta soma dan takawa.

“Ta yaya mace zata kasa sanin ranakun al’adar ta? Ko ta kasa kimtsa kanta har ya fito ya ɓata mata sutura?”.

Yayiwa kansa tambayoyin a jere.

“Miteeeew”. Ya kuma jan gajeren tsaki.

“Daga nan zuwa parking lot mutun nawa zata sa suga jininta, maza nawa zasu ganta a haka, yanzu ita in an barta wai mai hankali ce ko? Waɗanne irin iyayene gareta da zasu barta kara zube da irin wannan shigar, na tabbatar da suturarmu ta hausa fulani tasa baza’a gane lalacewar kayan jikinta da wuriba kamar wannan tsukekken farin wondon pallozo ɗin ko ya ɓata mata jiki hijabinta zai kareta.”

Yayi kalaman a saman harshensa.

A hankali ya ɗan juyo ya kalleta tana mai ci gaba da tafiya.

“Ko ba komai musulmace yana da kyau   ta suturce kanta”.

Ya faɗa yana kallon yadda take jujjuyawa tamkar Wahainiya.

 Sai-dai bai wuce taku goma tayi ba zuwa sha biyu. 

Taji muryarsa ta ratsa dodon kunnenta.

Inda yace “Stop.” Cikin wata irin kakkauran murya.

Aikuwa cak ta tsaya saidai kuma Sam ta kasa juyawa ta kalleshi.

Shikuwa Rayyern fuskarsa ya sake had’ewa, tare da yamutsaawa dan ji yake tamkar zaiyi amai kana ahankali ya juyo ya kalli alkyabbar shi dayake gefenshi.

A hankali yasa hannunshin ya d’auki alkyabban.

Ya  tashi tsaye kana ya fara taku a nitse.

Har lau bata juyoba kuma bataci gaba da tafiya ba.

Salman kuwa juyowa yayi ya zuba musu ido.

Kauda kansa gefe yayi lokacin daya  kara taku ɗaya ya iso kusa da Jannart ɗin.

Ƙara matsowa yayi kusa da ita yana mai ware alkyabbar.

Kanshi ya ɗan ronkofar cikin yamutsa fuska yace.

“Duk wata Macen da tasan ciwon kanta, bata yawo a haka kamar yanda ke  kike yi, sannan mata da yawa suna sirranta kansu, amma ke kina bayyana kazantarki in kika sani nayi amai  bazan yafeba.”

Cike da mamaki ta ɗan juyo yana kallonshi.

Hakan ya zama kamar irin hirar masoyane irin ana kallon juna nan.

Wani saurayi ne dake can ta bayane yana kallonsu ta cikin raga,

Ya zaro wayarsa da sauri ya fara ɗaukar su hoto, domin ya gano ƙanwar Junaidu ce.

Shi kuwa Dr  Rayyern Mai-nasara harara ya watsa mata tare da cewa.

“Mitssssss Ni ki dena kallona ko in tsokale idanun”.

Ya fad’i maganar yana me zagayeta tare da dago alkyabban ya d’aura mata akan K…!

 Kafad’anta wanda ya sauk’o ya rufe bayanta. 

Batare kuma daya sake cewa komai ba, ya juya fuskarsar nan amurtuk’e.

Bottle water da kuma phone d’insa ya d’auka, kana ya zo ya wuce ta gefenta. 

Itakuwa Jannart Idanunta ta rumtse da k’arfi, tare dasa hakwaranta ahankali ta cije lips d’inta. 

“Duk wata macen da tasan ciwon kanta, bata yawo ahaka kamar yanda ke kikeyi, sannan mata da yawa suna sirrranta kansu, amma ke kina bayyana k’azantarki.” 

Ta maimaita maganar daya fad’a mata d’in, wanda yasa tajin zafi har acikin zuciyarta, cikin kuma k’unan rai da b’acin ran kalaman nasa da wata iriyar fitinenneyar kunya mai masifar kashe ido da jiki tace.

“Waye shi da har yake fad’amin irin way’annan bak’ak’en maganganun,  meya gani ajikina haka? Sannan akan me zai rufamin wannan abunnasa me shegen mayataccen k’amshi?.” 

Ta fad’i maganar tana me d’an zame alkyabba’n ajikinta, dare da juya bayanta ta kalli jikinta, saboda tanason sanin mai ya gani ajikinta da har zai fada mata irin wannan maganan. 

Karab kuwa Idanunta suka sauka akan jinin, dake jikin farin wandon ta, wanda da alama kuma daga jikinta jinin ya fito.

Idanunta tad’an zazzaro waje cike da mamaki da wata sabuwar kunya tace. 

“What period dina kuma? Innalillahi Wa’inna Ilaihirraju’un Period at this time, Oh My God!!”

Ta fad’a da d’an k’arfi, cikin kuma muryar dake bayyana tsananin takaicinta, saboda Sam bata tab’a tunanin period din nata zaizo a irin lokacin ba, kasancewar tasan da sauran lokacin daya rage masa, har na tsawon kwana  uku kafun yazo.

“But amma why yazo yanzu? Meyasa Meyasa?”

Tayiwa kanta tambayar tana me b’ata fuska, domin sam bataji dadin abunba, cikin sauri kuma taja alkyabban daya rufa mata din ta sake rufe jikinta.

Lokaci d’aya kuma taji wani irin matsanancin kunya, da takaicin kanta na taso mata, duk da kuwa tasan cewar ba laifinta bane, period dinne ya sanja time wanda ko wacce mace kan iya fuskantar hakan musamman in tashin hankali da tsinkewar zuciya ya riski mutum, amma tayi matuk’ar takaicin ganin jinin period dinta da wani  da bata sani ba yayi.

Tabbas taji kunya yanzu da wani idon zata sake kallonshi? kuma shi dinma ayanzu wani irin kallo zainayi mata karo na forko a rayuwarta da taji haushin irin shigar da takeyi.

“Wata macen da batasan ciwon kanta ba, bata iya ankilta kantaba.”

Zuciyarta ta bata amsa atake.

Idanunta ta rumtse cike da takaici.

Dai-dai lokacin kuwa Salman Ya ware idanunshi a kansu tare da dawo da kallonsa gareta.

Fuskarsa dauke da d’an mamaki yace.

“Ha’a Jannart lafiya kuwa kizo mutafi mana..”

 Sauran maganar tasance ta mak’ale, alokaci da yaga jikin Jannart din lullub’e da Al’kyabban, da dazu ya ganta agefen mutumin da har yanzu baisan sunanshi ba. 

Jannart kuwa fuska  tad’an marairaice, kana cikin sanyin jiki ta soma takowa zuwa inda Salman din ke tsaye. 

“Jannart wannan Al’kyabban fa? Kin sanshi ne?”.

Salman din ya tambaya, saboda yayi mamakin  ganin ya sawa Jannart din da al’kyabban k’warai.

“Shi ne ya bani.”

Jannart din ta fad’a kaitsaye, bisa kuma sanin rashin dacewar Salman din yasan gaskiya abinda yasa yasa mata, shi yasa ta fad’a masa hakan, batare kuma da ta bada wata kofar da Salman din, zaiyi mata wata tambayar ba ta soma tafiya. 

Salman kuwa idanunsa ya zuba mata, yana mai Kallon yanda al’kyabban tayi mata matuk’ar kyau duk da tayi mata yawa, saidai kuma Jin tace wancan mutumin ne ya bata, yasa shi jin babu dadi  acikin zuciyarsa.  

Saidai kuma bashi da ikon bayyana hakan. 

Ab’angaren Dr. Rayyern kuwa Koda ya fito daga wajen wasan, kaitsaye Inda motarsa ke fake ya nufa. 

 idanun y’an tsirarun mutanen dake wajen ke kansa,  duk da cewar kuwa basusan shi din asalin waye bane, amma kallo daya zakayi mishi kafahimci cewa   mutum ne mai zarra.

Baya ga haka kuma ga tarin baiwar kyau da Allah Yayi mishi. 

Tun kafun ya karasa isowa Parking lot din wajen kuwa, Hadi driver’nsa ya fito tare da bud’e masa k’ofar motar.

Yana shiga kuwa driver’n ya rufe k’ofar, tare da zagayawa cikin sauri ya tada motar. 

Suna ficewa daga Parking lot din kuwa, su Jannart na isowa. 

Nanfa kallo kuma ya dawo kan Jannart, domin al’kyabban dake jikin nata ya k’ara bayyana asalin kyau da kuma kawata shigar dake jikinta da jawo hankalin mutanen dake wurin kanta. 

Murfin motar Salman din ta bud’e, tare da zagayawa gidan baya ta zauna, wanda tayi hakanne kuma, saboda idan sunzo shiga cikin gidan tv’n nasu, kada masu  tsaronta su ganta, ko kuma wani wanda yasanta . 

Salman ma shiga cikin motar yayi, tare da yiwa motar keyi suka fice daga cikin wajen wasan gaba d’aya.

Jin sun hau titi ne kuma yasa ta lumshe Idanunta, tare da sauke wata irin ajiyar zuciya mai karfi. 

Lallai ayau din tana cikin tarin damuwa tsananin kunya da kuma takaicin kanta da kanta.

Yayinda acikin zuciyarta kuwa take fatan Allah Yasa.

 Dr Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara din yazo, kamar yanda wancan yayi musu alkawari, kan. 

Numfashin ta fesar a hankali tare dayin mgnar zuci.

“Allah yasa kada in sake haɗuwa dashi har abadan, wannan kayan kunyar ina zan kaishi.”

Tayi mgnar cike da kunya.

“Idan shi  Dr Rayyern Mai-nasara kuma baizo bafa, shikenan na rasa aikina?”

Tayiwa kanta tambayar, dayasa duk taji zuciyarta ta Karye. 

Salman dake driving, wanda kuma tun dazu yake satan kallonta ta cikin madubi ne yace.

“Munsamu full confidence din samun daman yin hira da Dr. Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara, amma kuma sai naga kamar bakya cikin farinciki, kamar akwai wani abu dake damunki, please ki fad’amin wacce irin damuwa ce haka ke damunki?”. 

Idanunta dake alumshe ta bud’e, tare kuma da k’ak’alo murmushi ta daura akan fuskar ta. 

“Ina farinciki mana Salman, Ina cikin farinciki Tabbas, saidai bansan me yasa ba zuciyata keson sanyamin wasu/wasi, Ina fargaban kada ace wancan mutumin raina mana hankali kawai yayi.”

Ta fad’i hakan tana me gyara zaman al’kyabban jikinta. 

Salman kuwa jin hakanne yasashi yin Murmushi, cikin son karfafa mata guiwa yace.

“Karki damu Jannart Insha Allah zakiyi hira da Dr Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara, domin na tabbata wancan mutumin da muka hadu dashi awajen wasan polo bazaiyi mana karya ba, Lallai nagamsu akan cewar yasan shi, ki duba da kyau shima ai daga ganinsa ba karamin mutum bane, duk da kasancewarsa matashi amma yayi ruwan mutane masu kamala da dattaku” 

 Maida idanunta tayi ta lumshe, batare kuma da ta sake cewa Salman din  komai ba, ta shiga fesar da numfashi ahankali. 

Domin zuwa yanzu zuciyarta tatafi wani waje na daban.

Lumshe idanun nata da tayi kuwa, yayi dai-dai da lumshe idanun Dr Rayyern Mai-nasara, dake zaune acikin motarsa.

 Gaba d’aya ya yamutsa fuskarsa, saboda yanda yakejin zuciyarsa na d’an tashi kad’an kad’an.

Tabbas jinin da yagani ajikin yarinyar ya b’ata masa rai, Yayinda kuma yasa shi jin wani irin takaici had’i da tashin zuciya.

Kwata-kwata arayuwarsa bayason ganin wani abu daya shafi jinin sirrin mace shiyasa ya wadata asibitin sa da likitoci mata da zasu iya lura da ɓangaren haihuwa Allah ya sani bai son ganin jini.

Ayanzu kuwa idan akwai abunda ke  bashi matuk’ar takaici, To bai wuce yanda yarinyar ta jawo ya shiga harkarta.

D’abi’arsa ce baya  shiga harkar kowa, more especially ma mata, sometimes bayan Uwa mahaifiya yakanji babu wata alaka da zai iya kullawa da wata Mace awaje ta daban, sai gashi bisa dole wata can ta shigo harkarsa.

Wanda kuma yayi imani cewa badon sanin rashin dacewar barinta ta tafi a haka da jini ajikinta ba, To da bazai tab’a bata al’kyabbarsa mai matuk’ar daraja da kyau ta sanyawa jikinta dake abude ba, domin ai bashine yace tana yawo haka babu hijab ba.

Shidai kam Sauda yawan  lokuta yana mamakin, yanda wasu matan ke yawo haka sakaka, babu wata kulawar kirki da suke bawa kansu ina iyayensu?.

Yar gajeriyar tsuka yaja, tare da bud’e idanunsa.

Dai-dai lokacin kuwa suka iso cikin farfajiyar katafaren asibitin nasa. 

Anan cikin babban parking lot, Hadi driver yayi parking motar.

Yana  gama dai-dai-ta  parking din motar, kuwa Dr Rayyern ya bud’e murfin motar ya fito, fuskarnan tasa kuwa babu alaman murmushi akanta.

Dan Kallon Hadi driver din yayi, kana cikin yanayin dake  bayyana, rashin iya tsawaita maganarsa yace. 

“Kaje gida ka huta idan na tashi zanyi driving din da kaina .”

Kai Hadi ya jinjina, kana cikin girmamawa  yace.

“To Ranka ya dad’e nagode.” 

Karb’an makullin motar yayi, batare kuma daya sake cewa Hadin komai ba, ya kutsa kansa cikin asibitin.

Saboda mood din daya samu kansa aciki ne kuma yasa, ko iya amsawa tarin ma’aikatan dake gaishesa baiyi ba,  kaitsaye ya wuce office d’insa. 

Yana shiga cikin office dinnasa kuwa, ya murzawa kofar key.

Saboda ayanda yakejin kansa kwata kwata bayason damuwa.

Karasawa gaban dan madaidaicin fridgen dake cikin office din yayi, tare da zaro bottle water mai sanyi ya kafa abakinsa.

Bai dauke goran daga kan bakinsa ba kuwa har saida yasha  fiye da Rabin ruwan dake cikin goran. 

Take kuwa ya soma sauk’e ajiyar zuciya, Yayinda yakejin sanyin ruwan na mamaye kirjinsa.

Wanda hakan yasa acikin kaso 10 na b’acin ransa, kaso 6 yayi kaura.

K’arasawa yayi ya zauna akan wata had’add’iyar leather sit dake cikin office din.

Cikin kuma son rage tarin ayyukan dake gabansa, ya jawo laptop d’insa dake kan desktop.

Atsanake ya soma shigar da wasu bayanai akan Campany’shi da aketa aikinshi yanzu, wanda yafi duk sauran na jahohin girma.

Still kuma time to time yake sauke ajiyar zuciya.

Acan b’angaren su Jannart kuwa, daga wajen buga wasan Polo’n, basu wani dau lokaci mai tsawo suna tafiya ba, cikin mintuna kalilan suka iso gidan television din nasu, na  Arewa24. 

Kamar yanda suka fita asace kuwa haka yanzun ma suka dawo asace.

Inda Salman yayi parking motar tasa acan baya, inda babu wanda zai gansu.

Hakanne kuwa yasa cikin sauri Jannart ta fito daga motar, tare da sanya hannayenta duka biyu ta gyara zaman al’kyabban dake jikinta. 

Ahankali ta soma tafiya sai-dai kuma taku  daya zuwa biyar kawai tayi  ta tsaya cak, tare da juyowa ta kalli Salman wanda ya zuba mata idanu baya ko kyaftawa. 

Murmushin daya kara bayyana kyawun fuskarta tayi, batare kuma da ta fahimci ma’anan irin Kallon da Salman din keyi mata ba tace.

“Nagode sosai Salman, nagode da taimakonka, tabbas ka taimakeni awannan  tafiyar, saboda nasan cewar badon kaiba dana rasa wannan babbar daman dana samu ayau.” 

Idanu Salman din ya lumshe, cikin kuma nuna mata girman matsayinta awajenshi yace.

“Akoda yaushe bana buk’atar godiyarki Jannart, domin Ina tabbatar miki da cewar kin wuce haka awajena, kamar kuma yanda kikeson aikinki, haka muma mukeson aiki dake, bamason rasaki Jannart, saboda haka duk wani abu daya shafeki ya shafeni.” 

Ya fadi hakan yana mai bayyana iya gaskiyar abunda ke kwance acikin zuciyarsa. 

“Bazan iya daina gode maka ba Salman, saboda akoda yaushe kana iya kokarinka wajen bani kwarin guiwa, thanks alot ni zan wuce gida sai munyi waya.”

Ta kai karshen maganan nata tana me juyawa, kaitsaye ta nufi wajen da guard dinta suke.

Shikuwa Salman da idanu ya rakata, har saida ta  b’acewa ganinsa, kafun ya juya ya nufi cikin office d’insu.

Yayinda itakuwa tana isa bakin motarta, gaba daya guard dinnata suka mimmik’e,   Shashashai duk acikinsu kuwa babu wanda yasan cewar ta fita. 

Bud’e murfin motar tayi, bayan ta shiga ta zauna ne kuma driver’nta yaja sukayi gaba, Yayinda sauran guard dinnata suka rufa mata baya. 

Kwata kwata kuwa Tafiyar 40 minute ne ta kawosu katafaren gidansu Jannart din. 

Inda suna shigowa compound din gidan motar Junaid ma na shigowa.

 Ganin motar yah Junaid dinne kuma yasa zuciyar Jannart bugawa da wani irin karfi, lokaci daya kuma taji duk fargaba da tsoro ya lullub’eta.

Tabbas ita kanta tasan cewar tana matuk’ar tsoron Yah Junaid, wanda kuma hakan ya samo asali ne saboda yawan takurawan da yakeyi mata. 

Al’kyabban da yake jikinta ta kalla, sanin da tayi kuma cewar idan Yah Junaid din ya gani, zai iya fassarata da wata manufa tasa ta daban, yasa cikin sauri ta zare al’kyabban daga jikinta, tare da sauko da ita ta daura akan waist dinta. 

Cikin yanayin tsoro da kuma fargaban dake kwance acikin ranta, ta bud’e murfin motar ta fito.

Hannunta rike da jakanta ta soma tafiya ahankali.

Dai-dai lokacin kuwa Junaid ya fito daga Cikin motarsa, hannunsa rike da karan sigari yana zuk’a tare da tankadi alamun a bige yake yayi tatil da barasa, dishi-dishi yake ganin komai hakan ke sashi tangadin

Idanunsa ya dan kurawa Jannart din, Yayinda yakejin kamar ya rufeta da duka, dan tsananin takaicin rashin samun Galaba akanta da bayayi.

“Daga Uwar Ina kike?”

Ya tambaya cikin kakkausar murya tare da son gano meke daure a kugunta kuma ya kasa.

Jannart kuwa da sautin fitar muryar tasa, yasa hanjin cikinta kad’awa Idanunta ta rumtse, kana cikin muryarta dake bayyana zallan tsoronsa tace.

“Daga wajen aiki nake.”

“Wajen aiki? Munafuka makaryaciya sai yanzune ake tashi daga wajen aikin karfe shida saura? 

Makaryaciyar yarinya wato kinje kin gama rabawa kattin banza jikinki kin more sun more, shine sai yanzu zaki dawo ko, tafi daga nan wajen kona tattakaki nayi kasa-kasa dake.”

Ya fad’i maganar amatukar tsawace da maye.

Hakanne kuwa yasa Jannart d’in, Cikin yanayin sassarfa ta nufi cikin gidan kaitsaye, domin tasan ba karamin aikinsa bane yayi kasa kasa da itadin kamar yanda ya fad’a. 

Sam tasan baya mutumta duk wani abu nata.

Yayinda akullum take sake ganin wutar mugunta acikin idanunsa.

Duk da kasancewarsa  dan Uwanta amma yana muzantata, kwata-kwata babu ruwanshi da cewar ita k’anwarsa ce.

Komai yazo bakinsa furta mata yake.

Harsai yaushe ne zata tsallake rashin mutumcinsa? Harsai yaushe ne Yah Junaid din zai mutum tata amatsayinta na kanwarsa?

Yaushe zai daina gwada mata kiyayya da kuma tozarci?

Wasu siraran hawaye masu zafi ne suka silalo daga cikin idanunta, adai-dai lokacin da ta karasa bakin kofar da zai shigar da ita babban falonsu.

Hannu tasa ta share hawayen nata, kana ahankali ta murda handle din kofar ta shiga. 

Rashin ganin kowa acikin falonne kuma yasa ta sauk’e ajiyar zuciya, batare kuma da ta.

Nemi Mamy ko Abdull ba, kaitsaye ta wuce bedroom dinta. 

Tana shiga bedroom din kuwa ta soma rage kayan jikinta, tare da shigewa cikin toilet ta kimtsa kanta.

Koda ta fito kwanciya tayi lub akan gado, tana me tunanin yanda halin rayuwa keyi da ita. 

Sam babu wani farinciki da take  samu acikin gidan nasu.

Kullum Cikin fargaba da tsoro take,  awaje daya kawai takejin dadi, shine wajen aikinta, ananne take yin farinciki batare da wani ya tsangwameta ko ya harareta ba. 

Idanunta dake dauke da danshin hawaye ta  lumshe.

Kana cikin sanyin murya tace.

“Allah Kazama gatana akoda yaushe.”

*Dr Rayyern Mai-nasara.*

Ajiyar zuciya ya sauke tare kuma da mikewa tsaye, ahankali ya soma tattare tarin takardun dake gabansa. 

Bayan ya kammala had’a takardun ne kuma ya d’auki waya da makullin motarsa dake aje akan desktop.

Kaitsaye ya fice daga Cikin Office  din. 

Koda ya fito compound din asibitin, bai wani tarar da yalwan mutane ba, kasancewar lokacin magriba ta fara yi.

Direct wajen da motarsa ke fake ya nufa. 

Bayan ya shiga ya zauna ne kuma yayiwa motar key, tare da cillata kan shumfud’add’iyar Titin dake cikin asibitin har zuwa waje.

Tuk’i yakeyi cike da nutsuwa, Yayinda ahankali kuma yake bin karatun Alminshawy dake tashi acikin motar. 

Da fitansa acikin Hospital din kuwa, yanzu ak’alla yakai 18minute, inda kai tsaye ya nufi masallacin Al’furƙan dake Cikin unguwarsu ta Nassarawa G.R.A.

Dab da zai shiga cikin layin masallacin kuwa, ahankali ya d’ago kansa ya kalli madubin dake Cikin motar, kasancewar kuma aikin madubin shine bayyana maka wanda ke bayanka, hakan yasa idanunsa suka gane masa wata bakar mota mai tint dake biye dashi. 

Kawar da kansa gefe yayi tare da ci gaba da tukinsa, isowarsa Cikin layin dinne kuma yasa shi shiga wata kwana.

Aikuwa d’aga kan da zaiyi sai yaga wannan motar dake bayansa itama ta shigo kwanan.

Idanu ya d’an tsurawa motar, fuskarsa dauke da mamaki, saboda zuwa yanzu ya tabbatar da cewa motar shi take bi.

“Bibiyata akeyi.”

Ya fad’a fuskarsa d’auke da dan murmushi, ba tare kuma da tsoro ko fargaba ba ya cigaba da tafiyarsa, inda tuni ya d’auki numbern motar dake bayansa din ya rike akansa.

Isowarsa gaban babban masallacin Al’furƙan dinne kuma ya sashi parking motar,  tare da bud’e murfin motar ya fito, domin zuwa lokacin an soma kiraye kirayen sallan magriba. 

Fitowarsa daga cikin motar ne kuma yasa, motar dake biye dashi din, yin reverse cikin sauri matukin motar da ba a iya ganin fuskarsa, ya Karkata akalan motar zuwa wani waje daban. 

Dr Rayyern kuwa ganin wanda yake bibiyannashi ya juya ne, yasa shi sakin Murmushin dake dauke da ma’anoni daban daban.

Wayarsa ya maida cikin motar, bayan kuma yayi alwala da bottle water’n da ya d’auko acikin motar ne, kaitsaye ya wuce cikin masallacin.

Koda aka idar da salla’n bai fito daga cikin masallacin ba saida ya kammala addu’o’insa kana akayi sallan isha’i sannan ya fito.

Daga masallacin Al’furƙan din kuwa kaitsaye gidansu ya nufa.

Yayinda acan gidannasu kuwa Abba da Baba Maud’o ne zaune acikin compound din gidan, inda suke hira cike da girmama juna da Kekkyawar mu’amala.

Dai-dai lokacinnne kuma Rayyern din ya iso bakin tankamemen gate din gidan.

Horn din motar tasa ya danna.

Wanda hakan yasa Baba Maudo tashi da dan sassarfa.

 saurin dakatar da Baba Maudon Abba yayi kana cikin girmamawa  sanin tabbas Baba Mauɗo ya girmeshi yace.

“A’a Baba Maud’o zauna ka huta, yau bari in taya ni zan bud’e gate din.”

Cike da mamaki Baba Maud’o ya koma ya zauna, ganin da yayi kuma har Abban ya karasa jikin gate dinne yasa shi komawa ya Zauna tare da zuba mishi idanu.

Kana a hankali ya lumshe su tare da sauke nannauyan numfashin.

Abba kuwa bud’e katon gate din yayi, Inda Rayyern ya tura hancin motar tasa cikin gidan, saidai kuma ganin da yayi cewa Abban nasa da kansa ya bud’e gate din gidanne yasa, batare daya kutsa can ciki ba yayi parking motar.

Tare da bud’e murfin motar ya fito.

Cikin dan girmamawa hade dayin kasa dakai yace.

“Abba Baba Maud’o barkanku da dare, amma Abba da ka bari ai na fito da kaina ma zan iya bud’e gate din.” 

Kai Abban ya girgiza tare da cewa.

“A’a ai hakanma baiwuce motsa jini bane, Baba Maud’o ma da kansa yace zai bud’e amma nace masa ya bari, sannunka da dawowa ya hospital din?” 

Abba Yayi masa tambayar cikin kulawa.

“Alhamdulillah Abba,”.

Kana ya kalli Baba Mauɗo cikin kulawa yace.

“Baba Mauɗo gsky ni na gaya maka bana son kana aikin nan naka, zamu Ari ya rinƙayi aikin gadin, wlh bana jin daɗi inga kana buɗe mana gate.”

Murmushi Baba Mauɗo yayi tare da cewa.

“Rayyanu kenan to me a ciki ai motsa jiki ne kawai”.

Kanshi ya jujjuya kana ya kalli Abba tare da cewa.

 “Ramadan yana ciki ko.”

Kai Abban ya jinjina masa, tare da cewa.

“Eh shima Ramadan din yanzu ya dawo ya maida wancan bakon yaron masaukinsa.” 

Dan jinjina kai yayi kana kaitsaye ya wuce cikin gidan.

Ahankali ya tura kofar falon ya shiga bakinsa dauke da sallama.

Ramadan da kuma Mamy dake zaune acikin falonne suka amsa masa.

Cike kuma da farincikin ganinsa Mamy tace.

“Masha Allah Rayyern ka dawo.”

Kansa ya jinjina tare da cewa 

“Eh.” 

“Barka, ya hospital din.”

“Alhamdulillah.”ya fada yana me karasowa cikin falon.

“Hamma Rayyern sannu da dawowa, tun dazu Riyyam ke jiran dawowanka, amma ganin baka dawo da wuri ba, yasa na maidashi masaukinsa dan yaƙi ya tsaya yaci abinci ma, sai zuba mishi Mamy tayi ya tafi dashi.”

Cewar Ramadan Wanda yake Kallon Hamman nasa.

Gajiyayyun Idanunsa ya d’an lumshe, tare kuma da gyad’a kanshi ahankali, cikin yanayin kasalan daya saukar masa ya nufi stairs din dazai haurar dashi sama zuwa d’akinsa. 

Da kallo Mamy da Ramadan suka bishi har saida ya b’acewa ganinsu, kana Mamy taja  dogon numfashi tare da  sauk’e ajiyar zuciya…!

*GARKUWAR taku ce dai MA’AURATA, da masu shirin aure, da masu jego, da yan gayu masu son k’amshi kece raini, da gyaran da zaike  maimaita muku dararen forkon kuruciya*

Ko kunsan Jikinmu na da sinadaran hormones da suke taimakawa dan’adam akan komai musamman lokacin da mace take mu’amalar aure da mijinta. Mafi akasari wannan hormones din ne ke samun matsala ko su yi sanyi koma su daina aiki kwata-kwata shi ne dalilin da zai sa mace tace bata jin sha’awa ko bata san dadin aure ba. Albishirinku ina da kayan da ke taimakawa wannan sinadaran du dawo aiki tukuru don karkato miki da kimarki wajan mai gida sannan su taimakawa wannan sinadaran hormones dinki su dinka secreting din ni’ima wadatacciya da zata taimaka miki ki gamsu mijinki ya gamsu fiye da tunaninki. Note: Kayana ba sa tsinka ruwan ni’ima suna dai taimakawa hormones dinki ne su tsattsafo da ni’imar musamman wacca cutar sanyi ko dattin mahaifa ya dankarar da su ya hana su yin aikinsu yanda ya kamata. Haka zalika idan kina da kyau ki kara da wanka. Zaki iya amfani da magani na na gargajiya wanda zai gyara miki sex hormones din kullum ki kasance cikin humidify wato cikin damshi mai albarka kamar yanda ake son mace. Yana gyara miki mara. 

Sai kamshi. Hajiyata daure ki fara amfani da turarena ki ji irin salon kamshin sa salo ne da zai daidaita ki da mijinki ya kankaro miki da kimarki a wajansa. Siyan na gari mayar da kudi gida.

Back to top button