Novel Document

Kazamar Amarya Hausa Novel Document

Kazamar Amarya Hausa Novel Document By Rahma Kabir

 Description/Story:

KazamarAmarya! Hausa Novel Document

Written By Rahma Kabir 

 

Description Of Kazamar Amarya Hausa Novel Document

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Alhaji Hamid.

Yana zaune a cikin mota ya fito daga wani super market da ya yi siyayya, yana ƙoƙarin tayar da motar sai ga kira ya shigo wayarsa, da ya ga sunan daya bayyana akan wayar ai da ya saki lallausar murmushi kafin ya ɗaga yana mai cewa.

Amincin Allah ya tabbata a gareki hasken idaniya, yanzu na fito daga super market domin siyayyarki.

Uhum na ɗauka ka matan da ni ne ai, ɗan naga yinin yau baka kira ni ba.

Ta faɗa a shagwaɓe. Hamid ya yi ɗar dariya.

Aiki ne yasha kaina amma kina raina Madeenar Hamid da fatan kina lafiya.

Ni bana jin daɗi dan zazzaɓi ke damuna na rashin ganinka.

To kisha kuruminki ina tafe bayan sallar magrib In Sha Allah, yanzu haka gida na nufa na kimtsa kafin na zo.

To beb sai na ganka dan ina kewarka sosai ka kula min da kanka.

An gama ranki ya daɗe Madeenar Hamid.

Ya faɗa cikin yalwar farin ciki itama ta saki murmushi mai sauti daga haka suka kashe kiran, Hamid ya sauke gauron numfashi tare da jinsa cikin wani yanayi na shauƙin soyayya, bai taɓa tunanin akwai ɗanɗanon so irin wanda yake ji akan Madeena ba, saboda koda yayi auren farko lokacin yana cikin duhun kai akan sanin daɗin soyayya, duk da ya yi boko dan digree gareshi a fannin kasuwanci amma akwai tarin kuriciya a kansa, musamman matar daya aura Sakina ta kasance kidahuma ba wani ilimi gareta ba, hasalima a gidansu daga primary mace bata ƙara wani karatu ake yi mata aure, na islamiya ma na allo ne shima bata sauke ba, kuma ya aureta cikin ƙuriciya dan tana ‘yar shekara sha huɗu shi kuma yana da shekara ashirin da biyar, shiyasa rayuwar aurensu banda tarin wauta da sakarci ba abinda suka sani, sauƙin ta ma cikin rufin asari suka yi shi domin mahaifinsa Nuhu tsohon soja ne da yayi retire, kuma yana da comfanin sabulu wanda Hamid ke gudanar da shi, Abba shi ne yayi masa aure bai san wani wahala da angwaye kesha ba, har kawo yanzu da aurensu shekara sha biyar suna cikin wadata dan babban gida filat gareshi kusa da na iyayensa ya yi gini, wanda ‘yar ƙaramar ƙofa ya fitar a tsakani dan sauƙaƙa hanyar shiga, da kuɗinsa yayi ginin saboda Hamid mutum ne mai himman da niman na kansa, duk da yana kula da companyn mahaifinsu to sai da ya haɗa da kasuwancin motoci da yake shigo dasu daga ƙasar waje, yaransu huɗu ta farko itace Mufeeda sai Nuhu mai sunan Abbansa sai Yaƙub da autarsu Rauda wacce a yanzu haka Sakina ta yayeta ‘yar shekara biyu da rabi.

Tun lokacin da Allah ya haɗa Hamid da Madeena a bikin wani abokinsa wanda Madeena itama ƙawar amarya ce, a ganin farko da yayi mata Allah ya ɗaura masa mugun sonta da hangen ita ce daidai da sa’ar aurensa, musamman yadda yake jinsa da ɗanyan kuɗi to yana buƙatar matar nunawa sa’a da kece raini dan kuwa Sakina ba tada zubin matan da zai iya fita taro da ita, ga rashin wayewa da rashin ilimi duk da tana da kyanta dan black beauty ce, amma sam Hamid baya ganin kyanta, ko dan sun jima a tare ne da kuma son kasancewa da farar mace yasa yake jin haka ƙila, domin Madina fara ce gata da tsayi dan ba za a sanya ta a jerin gajeru ba kuma tsayin na ta bai yi yawa ba ga shape Masha Allah domin akwai hips da dukiyar fulani, ga kuma manyan idanu da kuma dimple, a takaice itace irin matan nan da ake kira full option, domin ta haɗa komai rashin sumar kai ne kaɗai yayi mata cikas amma bata tsaya hakan ba sai da ta ƙara da na atach, sannan tana da ilimin zamini sosai dan tayi digree a fannin masscom sannan ta kuma yi masters, islamiya ba laifi tana da sani sai dai tafi mayar da hankali wajen boko, wajen shiga kuwa ba a magana dan ta iya ɗaukar wanka da iya kwalliya, sannan ta iya bulbula turare a jikinta dan duk inda ta gibta sai ya ɗauki ƙamshinta, wannan dalilin yasa Hamid ya riƙe mata wuta akan lallai sai ya mallaketa, dan Madina ba irin matar da za a kalla a wuce bane tana buƙatar a killaceta a guri ɗaya, kuma yayi sa’a a gun Madina dan ya samu karɓuwa domin shima ba baya ba wajen iya shiga da kashewa kansa kuɗi, dan fa yana cin guminsa, duk da baƙine shi amma Kana ganinsa kasan hutu ya zauna, yana da kyansa daidai misali kuma yana da tsayi bai da tumbi dan bai yarda cin daɗi ya sauya masa halittarsa ba yana kulawa da hakan sosai, gashi ɗan gaye saboda shigar manyan kaya ko ƙananun kaya babu wanda baya karɓansa, yana da matuƙar tsafta da kuma son mai tsafta, shiyasa yadda yake ganin Madina tsaftsaf kullum shi yake ƙara masa sonta da hangen in ya aureta zata share masa hawayensa, domin Sakina ba tada kula da tsaftar gidansa duk da tana iya nata ƙoƙarin kuma tayi tayi ya ɗaukar mata ‘yar aiki yace shi baya so, ƙazantar ta da yake gani shine ma ya ƙara masa ƙaimin ƙara aure, kuma ga dukkan alamun da yake gani yayi gamdakatar dan Madina yake hange itace mai share masa hawaye da maye gurbin duk abubuwan da Sakina bata yi masa, yanzu ne yake jinsa zai yi rayuwar aure mai daɗi a da can wasan yara ne yayi, duk ya ƙosa wata guda daya rage na aurensu yayi dan a hannu yake kamar bai da mata, domin Madina ce sanyin idaniyarsa.

Haka ya cigaba da tuƙi yana tunaninta har ya isa gida, ya buga hon mai gadi ya buɗe masa gate ya shiga kana ya adana motar, ya fito riƙe da ƙaramin farar leda daya siyawa yaransa kayan ciye ciye dan koda ya siyawa Madina nata bai manta da su ba yana matuƙar son yaransa, ya tsaya a jikin mota ya kwalawa Ibro mai bawa fulawa ruwa da gyaran farfajiya kira, ya tawo da saurinsa yana risinawa tare da gaisheshi ya amsa fuska sake.

Yauwa Ibro ga motata ina so a wanketa amma banda ciki, ba zan jima ba zan fito dan akwai in da zani.

To yallaɓai a fito lafiya.

Ibro yace cikin sauri ya nufi inda kayan aikinsa ya ke domin ya gabatar da aikin Alhaji. Hamid yana tura ƙofar falo da sallama ya hango tsakiyar falon da datti nan take annurin fuskarsa ya ƙaurace ya maye da ɓacin rai, haka ya ƙarasa ciki ya tsaya yana ƙarewa falon kallo, ba kowa a ciki sai hayaniyar yaran da ya ke ji a kitchen, ya kalli carpet ɗin dake tsakiyar falon da yake kalar fari da brown amma har ya fara sauyawa zuwa kalar datti, ga ledan biscut da sweet a kai ga kuma icen alayyahu da aka yi amfani da shi aka barshi, pillon kujerun duk a ƙasa ga plate ɗin abinci da aka ci aka barshi duk an zubar, cikin ƙunan zuciya ya shiga kwalawa Sakina kira kamar tarar aradu.

Sakina! Sakina!! Sakinaaa.

Cikin sauri ta fito daga kitchen tana amsa kiran tare da yi masa sannu da zuwa, Hamid bai amsa ba ya bita da wani irin kallon tsana.

Wannan wani iri hauka ne zan zo naga falo kamar filin dambe, yanzu da ace da baƙo na shigo haka zaki saka na ji kunya, a matsayina na Alhaji Hamid ya dace aga falon gidana haka kaca kaca, wlh tallahi na gaji da wannan ƙazantar taki, ayi mace sai ka ce tunkiya uwar tamɓele, taya ma bazan ƙara aure ba kina irin wannan jakancin, madadin na shigo naji falo ya ɗauki ƙamshin turaren wuta, ina can waje ina hura hanci da fankama mutane na ga Alai Hamid ina yaƙe baki dajin ni wani shege ne, amma matata ba abun ke ba ilimin ba kuma tsafta, in je taro dake ana zuba ruwan turanci kina zare ido kamar kyanwar data ci barkono kina baje hanci kamar kinji warin jaɓa, to Wlh da sake Sakina aure ba fashi nan da wata guda Madina zata zo ta wanke min baƙin cikin da kike ƙunsa mini.

Abban Mufeeda ina iya kokarina kuma ka ce baka so ka dawo ka tadda ban gama girkin dare ba, kuma ina ta sauri ne na gama da kitchen kafin na fito falo na gyara kan ka shigo fa.

Ta ƙare maganar hawaye yana cika mata ido dan sosai maganganunsa suka ƙona mata zuciya, duk da yaci ace ta saba da irin cin zarafin da yake yi mata wani sa’ilin ma a gaban yaransu, Hamid ya ja guntun tsaki.

Amma ai na fada miki ki riƙa fara yin komai da wuri kafin lokaci ya ƙure miki, idan kin ɗaura girkin ai sai ki zo ki gyara nan ɗin…

Hamid ya kake so nayi ne, kuma kace Waina kake so nayi maka yau, ga ƙullun bai tashi mini da wuri ba dan ban daɗe da gama suyar ba, yanzu ne na samu damar ɗaura miya ina wanke ganye ne ka shigo, kuma saurin da nake yi na gama na zo na gyara nan. Kasan halin yaran nan in sun dawo makaranta ɓata guri suke yi ga Mufeeda Hajiya ta aiko kiranta tana can gidan bata dawo ba dama…

Dama me? ai kin iya jero magana kamar wacce ta haɗiyi Radio, wlh rashin ilimi ba ƙaramin cutar dake yake yi ba Sakina, dole zan zo na fara shirya yadda zaki koma makaranta koda yaƙi da jahilci ne ki samu wataƙila zaki san yadda kan duniya take ciki, shiyasa ko taron makarantar yaran nan ban yarda kije ba dan karki bani kunya. Ki kuma gyara gidan nan kafin na fito daga ɗakina na ji yana ƙamshi, shashasha sai anyi magana ki riƙa fuskar tausayi kina sunsun da kai uwa mumina.

Ya ƙare maganar yana danƙara mata harara kana yayi gaba ya wuce ɗakinsa, Sakina da ido ta bishi wanda hawaye cike fal da idonta kamar zasu zubo mata, sauke numfashi tayi tana girgiza kai ta juya dan ta koma kitchen sai taga yaran sun tsaya suna kallonta, wato komai ya faru a kan idonsu, baba ƙarami ɗan shekara sha ɗaya shi ne yace.

Mama kiyi haƙuri ba zamu ƙara ɓata falon ba tunda faɗa Abba yake yi miki.

Baba ƙarami bana son surutu maza kaje ka kwashe jakar makarantarku ka kai ɗaki.

To yace kana ya nufi inda jakarsu na makaranta yake ya ɗauka ya nufi ɗaki, ita kuma tsintsiya ta ɗauka ta fara gyaran falon, ba jimawa ta gyara falon ta saka turaren wuta a burner sai ta wuce kitchen dan duba sanwar miyanta, sai dai zuciyarta kunshe yake da tsananin damuwar abin da Hamid yake yi mata tun da ƙuruciyarta har kawo yanzu, babu abinda yafi kona mata rai sama da yadda yake zaginta da jahila, ga komai tayi bata taɓa burgeshi, tunda ya haɗu da Madina ya rushe sauran ɓarɓashin son da yake yi mata, ga tarin wulaƙanci daya ƙara, ita tun tana jin zafin kishin auren da zai yi har ta haƙura tana burin wannan amarya tazo gidan ko zata huta da cin kashin da Hamid ke yi mata…

Kazamar Amarya Hausa Novel Document txt

 

File Name   Kazamar Amarya… Hausa Novel Doc.
Title   Kazamar Amarya Hausa Novel Complete
Author    Rahma Kabir
Group    Ai  Hausa Novels
Genre    Fiction Story
Published Date    17/07/2024
File Size    800KB
Format Size    TXT
Book Price    Free
Phone No   09034940106
Download Kazamar Amarya Hausa Novel Document By Rahma Kabir 

Click the below green button to read the novel online

 READ THE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

 

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button