Hausa novels

Gargadar So Chapter 74 By M Shakur

Da asuba Ammi ta tada Hawwa dan ta hada important kayanta datake bukata su Hafsat suka tayata akwati daya tahada na kayan datakeso uniform nata da credentials dinta, Umma ta karba sannan su Ammi da manyan maza suka shiga kai kayan Hawwa zuwa trailer da Khaleel ya aiko musu aka fitar da komi waje, zuwa around 10 mata suka shiga jeep da yazo daukan su, Aminu ma yabisu as namiji aka tafi dasu jere gidan Hawwa.Kowa saida yayi salati dasukaga gidan Hawwa gate harsun gaji da kirgawa ga yan sanda da sojoji tako’ina, Mommy na tsaye wajen window office nata su Umma suka sauko daga mota tsaki tayi tace “bunch of local people look at them” tawuce ciki Excellency na falo tareda Khaleel daya kwanta yasa kansa akan cinyansa yana chatting abinsa cikeda masifa tace “wai Khaleely akanme zakaje kayi aure from this local family kuma harda biki maisa ba’ayi descreet marraige damuka sabayi ba? Wlh kunyan gayyatan mutanena reception na yau nake sabida kalan yar gidansu wayanda ka auro, batare da Khaleel ya dagoba yace “Pops talk to Mommm oooooo” Dasauri Excellency yadan rufe Mommy da fada yace “wai me haka Madam? How many time will you go forth and back on this matter eh? Kibar yaro yayi abinda yakeso idanma destination wedding yakeso let it be, meruwan mu da family su ko status nasu badai ya auri abinda yakeso ba fakat!”Tashi zaune Khaleel yayi yakalli Mom cikeda rashin mutunci yace “ko kallon banza kikama family matana you will see the other side of me Mom” yana maganan yawuce hanyan side nashi yace “ask the workers akaimu su abinci da drinks” kaman Mommy zatai kuka cikin masifa tace “PA” zuwa yarinyar tayi da gudu Momy tace “attend to Khaleely Inlaws” ran Mommy abace tawuce fuuu tayi ciki Excellency yabita da kallo yana kadakai kafin ya cigaba da waya abinshi yau da gobe da jibi yadauki off sabida bikin dansa.Mutane cike gidansu Hawwa kaman zasu zauna akatanga sabida yanda jama’a suka cika ko’ina, Hawwa na daki tayi wanka tasaka atampa mai bala’in kyau dinkin yamata sai addu’a ake ana mata Allah sanya alheri.Wuraren 5 stylist nata da makeup artist nata suka fara shiryata in white gown around 7:30 aka gama shiryata lokacin duk an tafi da yan gida hall, salla tayi sannan aka mata daurin kai, wani diamond sarka aka samata Hawwa was screaming money ya Allah ita kanta data kalli madubi sai kawai ta tsaya dan she can’t believe itace, bata taba sanın she’s this beautiful ba, she looks like all this instagram brides da ake gani online, dagata sukayi Hafsy dake rike da wayanta tace “mijinki sai kira yake Hawwa” kin magana tayi dan batajin dadin komi fita waje sukayi wani red roll Royce ke pake akofar gidansu da akai arranging da flowers ga motocin security gaba da baya bude mata akayi ta shiga ahankali batare data kalli Khaleel dake zaune yana kallonta ba aka rufe akaja motan hannunshi yakai zai taba bata tadauke dasauri shi kawai kallonta yake gobe tana dakinshi around this time dan tun 5 zai turo atafi da ita tahowa yayi yadaura fuskanshi akan shoulder nata yakawo wayanshi yayi snapping nasu yana murmushi yace “I have the most beautiful girl as my wife” mtswww Hawwa taja gajeren tsaki gaban hall din akai parking aka bude musu suka fito suka tsaya Moh yazo yana sanye da suit yace “you are late” Hawwa ya nuna da kanta ke kasa yace “matana tarikeni” “Welldone Mrs Lee” Sam yafadi yajuya yakoma ciki dan bride da grooom shigowansu su kadaine bayason hayaniyan mutane na binsu, daganan waje sukaji muryan MC yana ladies and gentlemen the moment is here, Momy and addy Uncle and sister the bride and groom gasunan abasu standing ovation DJ DJ” DJ yasaka wakan like my father by Jax wanda Khaleel yace asamai idan zasu shigo sabida Baba yabashi labarin Mahaifiyar Hawwa and he wants to communicate to Hawwa da wakan ya gayamata cewa he will loves her the way Baba loves her Mom,Shiga Hall din Khaleel yayi da ita ya Allah Hawwa da Khaleel sunyi kyau watttttt Tana sanye da white gown nata gawani net da aka dauramata akan gashinta da aka gyara yayi kyau kaman tasaka attachment, Khaleel na sanye da suit black yarike musu hannu, yanda ake kallonsu sai Hawwa taji kuka, wakan dake tashi that is so cool na ratsata kallonta Khaleel yayi cikeda so yanuna mata Baba dake sanye cikin kaya exactly irin na Excellency yana tareda excellency yana kallonsu yana murmushi sosai, kawo kanshi yayi saitin kunnenta suna tafiya yace “I will love you Hawwa just like the way Baba keson Maman ki har yau dudda she’s late, I will love you a million times more!” wani irin kallon Khaleel tayi tayi cus she felt his words har cikin heart nata cikeda so ya gyadamata kai yana kallonta.Mommy datai shiga na alfarma tasha zinare sarkan jikinta har cıbiya ta tsaya tana kallon Khaleel da yanda taga yana kallon Hawwa daidai sun shigo tsakiyan hall din aka saki wannan hayakin soyayyan wanda duk aikin Juzzyfabevent ne dan ita tayi handling entire wedding decor din aka samusu wakan soyayya na Christina Perri A thousands years, Khaleel yasaki hannun Hawwa yanuna ta yana waka yana rawa Hawwa na kallonshi Excellency da Mom suka saki baki suna kallon Khaleel tunda suka haifeshi basu taba ganin Khaleel this happy ba ko ranan da aka haifi Noor but look at him, today is the happiest day of his life ahankali Excellency yace “Khaleely this is not fun, you’re inlove” rawan yagama kawai yazo ya rungume Hawwa very tight akahau ihu Hawwa ta boye kanta ajikinshi sabida kunya dan har su DIG tagani dasu Abraham da Hayatu kowa ya gayyacesu oho, DJ yace “our shy shy bride”.

Back to top button