Uncategorized

Da Dumi-Dumi: Wasu daga cikin kananan hukumomi 10 cikin 17 a Katsina sun samu yanci.

 Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya aike da rubutacciyar takarda ga hukumar sadarwa ta Najeriya NCC, inda ya bukaci ta dawo da aiyukan sadarwa a kananan hukumomi goma daga cikin 17 da dokar hana datse layukan sadarwa ta shafa, wadda aka datse kimanin watanni hudu da suka gabata.

 Babban Daraktan yada labarai na Gwamnan Jihar Abdu Labaran Malumfashi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya aike wa DAILY POST da sanyin safiyar yau Juma’a.

 Labaran ya bayyana kananan hukumomi goma da aka dage haramcin da suka hadar da: Kurfi, Dutsinma, Matazu, Musawa, Malumfashi, Dandume, Bakori, Funtua, Kafur da Danja.

 Sai dai ya ce har yanzu akwai ƙananan hukumomin da haramcin amfani da layukan sadarwar ya shafa, guda Bakwai da suka haɗar da: Faskari, Sabuwa, Batsari, Safana, Kankara, Danmusa da Jibia.

 A cewar Labaran, gwamnatin jihar ta yanke shawarar dakatar da dokar ne a kananan hukumomi goma sakamakon komawar al’amura yadda su ke, duk da cewa an ci gaba da kokarin ganin an samu zaman lafiya a kowane bangare na jihar”

 Kwanan nan, kwamishinan ‘yan sanda kuma shugaban kwamitin aiwatarwa da tabbatarwa kan kalubalen tsaro a jihar, CP.  Sanusi Buba, a wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Sufeto Gambo Isah ya rabawa manema labarai, ya ce gwamnati ta sassauta dokar hana siyar da kananan dabbobi irin su awaki da tumaki a kasuwanni a fadin jihar.

 Daidai, a ranar 31 ga watan Agusta, 2021, Gwamna Masari, bisa la’akari da yadda matsalar tsaro ke kara ta’azzara a jihar, ya sanya hannu kan dokar ‘Security Challenge Containment Order’ don magance matsalar.

Back to top button