Uncategorized

Wace Ce Ita Chapter 38 Complete Novel

WACE CE ITA⁉️ (WHO IS SHE⁉️)

Unique Barakancy

                            THIRTY-EIGHT📍

             “Wani country kikeso mu tafi? I don’t know if you have any in mind?”…..

Zatayi magana kenan taji khaleel ya kwallara ihu, ko kafin ta fahimci abinda ke faruwa khaleel ya sake sakin wani ihun dayafi wanchan saboda yanda yaji kamar anbuga masa guduma akai gashi he wasn’t prepared bare ya kare kansa, daga sama kawai yake jin bugu…. 

Juyowa tayi da sauri daidai lokacin sukayi ido hudu da Deen daketa naushin khaleel ta baki ta hanci ta ko ina, idanuwannan nasa sunyi jawur ga muscles dinsa da suka fito rado rado kana gani kasan ma’abocin karfi ne da cikar halitta…Gashi dai dukan khaleel yake amma idonsa na kanta…..

Sandarewa tayi a tsaye tana kallon Deen da sai jibgar khaleel yake ta kasa yin komai……

Sake kaiwa khaleel da bakinsa ze zubar da jini naushi yayi yana fadin;

        “Ashe dama duka danginku mugayene azzalumai? Na dauka soyayyar tsakani da Allah kake mata ashe kaima wani abun kake nema a gurinta kamar ubanka Ibrahim?! Ubanka be kyaleta ba kai baka kyaleta ba kasheta kuke sonyi ne? Toh kunyi naku kungama a sannu kuma zanyi maganinku gabadaya! Kaje ka gayawa ubanka ni Saifuddeen nasan abinda kuke shiryawa kiris ya rage na tarwatsaku duka, sannan zan baka last warning ka fita harkarta dan ko a mafarki bazaka taba samunta ba, she doesn’t deserve a useless stupid person like you!!”………

Da sauri khaleel ya mike yaci kwalar rigar Deen yana hucin wahalar bugun da yasha yace;

      “Kayi kadan ka rabani da wifey! Kayi kadan! Waye kai? Yaushe kasanta? Get the f**k off out of our life!!”……

Wani zazzafan mari Deen ya daukeshi dashi ya fizge hannun khaleel daga rigar shi yace;

     “A gidan ubanwa ta zama wifey din? Naga kamar baka dakuba tinda kana da bakin gayamin maganar banza!!”….

Deen ze sake kai masa mari kenan kawai khaleel ya zaro bindigar daddy daya fito da ita ya saita akan Deen…….

     “In baka kasheni ba ni yanzu zan kasheka!”…..

Cewar khaleel yana dada saita bindigar daidai kirjin Deen…….

Ganin abun nasu ya fara wuce na hankali tinda har bindiga aka fara zarowa yasa fatima zainab saurin shiga tsakiyarsu, murya na rawa tace;

      “No khal karkayi haka, dan Allah karkayi haka, karka kasheki”…….

    “Akanme zakice karna kasheshi? Ko son shi kike?”…….

     “Wallahi bana sanshi, na fika tsanarshi ma, karka kasheshi because of his family”…….

     “It doesn’t matter! To hell with his family!”…..

Ganin fa dagaske khaleel so yake ya harbi Deen yasata rungumeshi da sauri dan dagaske bata so ya kasheshi kodan Mami da Umm da suke nuna mata kauna sosai, a take jikin khaleel ya mutu jinta a jikinsa, abinda bata tabayi gashi kuma beji irin abinda yaji lokacin daya tabata ba saima wani sanyi da dadi dayaji ya saukar masa lokaci daya……

     “Please ka kyaleshi, muda zamu barmusu kasar? Ka  rabu dashi kawai”…….

    “Okay wifey”….

Ya fada chan kasa jin yanda ta saukar masa da kasala lokaci daya……

      “Give me the gun”…..

Fatima zainab da har lokacin hankalinta be kwanta ba tana ganin kamar khaleel ze harbi Deen tace ya bata…….

Ba musu kamar wanda ake controlling da remote ya mika mata bindigar…….

Kamar a mafarki Deen yaga ta rungume khaleel, sosai ya shiga shock har saida yaji komai na jikinsa ya tsaya, kamar statue haka ya tsaya yana kallonsu yanajin kamar yayi kuka wai a gabansa zasu rungume juna? Abun da ciwo gaskiya, kamar wanda aka mintsina ya dawo hayyacinsa, fuzgota yayi daga jikin khaleel sannan ya zare bindigar dake hannunta.

Janta ya shigayi kamar akuya yayi hanyar barin wurin da ita, nan khaleel yace masa be isaba, sai aka fara jaye jaye, wannan yajata wanchan yajata kamar dai rago, last last Deen yayi succeeding ya janyeta, sunkutarta yayi da sauri ya nufi inda yayi parking motarsa da ita, yana zuwa ya bude back seat ya wurgata ko tsoron taji ciwo bayayi tsabar yanda ransa yake a bace……..

Ko kafin khaleel ya karaso sun bar gurin, shiga motarsa yayi ya bisu a baya a shima……

Wani irin mugun tuki Deen yake kamar ze tashi sama, kauce masa kawai ake a hanya, tuni ta dade da galabaita tin a jaye jayen da suka dingayi da ita har numfashinta dakyar yake fita, sosai tsanar Deen ta ninku a ranta dan ya zame mata tamkar karfen kafa tinda ya shigo rayuwarta, ada ita ake bi kuma sai abinda tace amma yanzu dole yake mata saita bishi ko tana so ko bata so, yazo yayi kane kane akan lamarin rayuwarta kamar wani ubanta…….

Ikon Allah ne kawai ya kawosu gidan mami dan duk inda sukabi sai andinga Allah yasa karsuyi hatsari da mugun tukinnan da me motar yake……. 

Horn yake babu kakkautawa a bakin gate din gidan mami, sai akayi rashin saa gateman din daya gama jinya ya dawo ya tafi ya dan zagaya, da sauri yazo ya bude kofar bayan ya fito, yana ganin Deen ne ya manna a guje dan be manta illar dayamasa ba last time, a halin yanzu ma hakorinshi guda daya ya tafi…..

Ko daidaita parking Deen beyiba ya fito daga motar, janyota yayi ya fito da ita sannan ya fara janta da karfi har ya kaita parlour mami, wurgata a kasa yayi ya cire belt din jikinsa dan yasan inbe fasa mata jiki yau hankalinsa baze kwanta ba, zuga mata guda daya yayi ta saki wani karar da saida gidan ya amsa, ze kara zubamata kenan Umm ta rike hannunsa tana fizge belt din tace;

     “Ashe baka da hankali saif? Meh tamaka zaka duketa? How can you even think of beating a lady, ashe bakada imani baka da tausayi? Tarbiyyar aka baka kenan?”……..

Tinda Mami da Umm sukaji wannan mugun horn din sukasan Deen ne, da sauri suka sauko saidai anyi rashin saa dan har ya fara zuga mata belt din……

      “Umm dan Allah ki barni in babballa yarinyar nan ko zuciyata zata samu salama, kinsan metayi ne?”……..

      “Koma me tayi be kamata ka tabata ba kodan lafiyarta sannan a responsible man won’t beat a lady kome tayi kuwa”………..

       “Count this stupid girl out, dan Allah ki bani in fasa mata jiki!”……

Ya fada yana fizge belt din a hannun Umm ya daga da nufin cigaba da dukanta mami ta sauke masa wani lafiyayyen mari tana sake kwace belt din…….

     “Wai me yake damun brain dinka ne? Akanka aka fara zafin zuciya ne, kai a wa zakazo kana dukan yarinyar mutane? Meyasa bakada tinani ne? Tana fama da kanta zaka duketa, inka kasheta ai sai kafi kowa shiga damuwa, bismillah cigaba da dukanta”……

Ta fada tana mikashi belt din…..

Durkushewa yayi a kasa yanajin kamar yasa kuka, tabbas da ze iya kuka da yau yayishi saidai duk girman abu taurin zuciyarsa bata bari yayi kuka, ko mami da dad da suka haifeshi basu taba ganin kukansa ba, haka Umm ma data renesa…….

     “Kunsan me suke shirin aikatawa ne? Guduwa fa zasuyi itada yaron mugunchan da bamusan dame yake nemanta ba, amma saboda karamar kwakwalwarta take cemishi zata bishi su gudu suyi aure gasu tantabaru, har fa I love you tace mishi mami, wai har wannan yarinyar tasan soyayya Umm?”……

     “Au yanzu kuma tayi yarinya ta fara soyayya? Ina cewa kayi zaka mata aure dama? Tinda ga wanda takeso sai ka aura matashi”….

     “Wallahi bazata aureshi ba Umm, yes she’s too young for love kamata yayi ta maida hankalinta kan karatunta! Ko auren zan mata bazan aura mata shashasha irinta ba bare na fasa mata auren, karatu nakeso tayi”…….

Yana fadin haka ya fice daga parlourn….

     “Wai meke damun brain din yaronnan ne Umm?”……

    “Hmmm mu tayashi da addu’a kawai, I’m speechless”…..

Lallashin fatima zainab data fara kuka bayan fitarsa suka hau yi, birkice musu tayi ita saita bar gidan bazata zauna da wannan mugun a gida daya ba dan dagaske fushinsa ya tsoratata, hakurin duniya sun bata taki hakura sai kuka take musu ita bazata zauna ba, Umm ce ta kalli mami tace;

      “Innalillahi yanzu ya zamuyi? Kinga abinda ya janyo ko”….. 

     “Huh meye abunyi banda mukirasa yazo ya san nayi tinda shi ya jawo komai!”……

    “Bari in kirasa”…..

Fita Umm tayi ta tafi part dinsa da beda wani tazara dana mami, samunshi tayi yanata safa da marwa kamar wanda aka yiwa wahayin masifa, harararshi tayi tace;

     “Tace bazata zauna a gidannan ba, sai kazo kasan yanda zakayi da ita!”…..

Ta fada tana ficewa daga parlourn……

Da sauri yabi bayanta dukda har lokacin be wuce ba, so yayi yaki zuwa ya nuna musu yayi zuciya da ita taje duk inda taga damar zuwa sai zuciyarsa taki bada hadin kai kawai yabi bayan Umm…… 

Kukanta ne ya fara masa iso tin kafin ya karasa parlourn, sosai yaji zuciyarsa ta karaya akan yanda yaga tana kuka, shida ko wani ne yasata kuka sai inda karfinsa ya kare sai gashi shine ya sata kuka da kansa? A kuma lokacin ya fara nadamar yunkurin dukanta dayayi har yakai ga zuba mata belt sau daya, meya aikeshi meya kaishi? Yanzu da badan an kwace belt dinba me zai faru?…. Girgiza kai yayi ya tsuguna daidai inda take, su mami na ganin haka suka haura sama suka barsu su karata……

 Hannunsa yasa ya goge mata hawayenta sannan cikin kwantar da murya kamar bashi ya gama masifa dazu ba yace;

      “Stop crying baby girl! Banaso kan ki yayi ciwo”…..

Bige hannunsa tayi tace;

     “Bazan dena kukan ba kuma bazan zauna a gidannan ba!”…..

Pecking hannunta yayi ya dauko belt din yasa matashi a hannu yace;

      “I know I did you wrong, gashi ki rama ko guda nawa kikeso, amma dan Allah karki kara cewa bazaki zauna a gidannan ba”…..

     “Wallahi bazan zaunaba, kai mugune”…..

     “Naji ni mugu ne but I’m a changed person now, I promise bazan kara miki masifa ba kuma bazan kara dukanki ba amma ki rama naki yanzu sai ki dena jin haushi”…….

Batace komai ba ta shiga shauda masa belt din da karfi a jikinsa, daga baya dataga kamar dukan baya shigansa tace ya mikohannunsa, mika mata hannun yayi ta shiga jibgarsa kamar mallama dalibinta…..

Dariya ta bashi sosai har saida ya kasa rikewa, betaba tinanin yarinyarta takai haka ba sai yau, wannan aka mata aure yanzu ai akwai matsala, harda ce mishi karya janye hannunsa sai tace ya janye, toh kawai yace mata ya cigaba da kallon ikon Allah dan an zuba mishi belt yafi so talatin a hannu and he didn’t complain kamar yanda yace…….

Sake sakkowa su Umm sukayi jin karar duka su a tinaninsu Deen ne yake sake dukanta, sai dai me? Gani sukayi  Deen ya mika hannu tana zuba masa bulala yana murmushi kamar wanda ake yiwa abu me dadi, tabe baki mami tayi tace ‘sunfi kusa’, suka juya suka koma sama……

Saida tayi me isarta lokacin hannunsa yayi ja kasancewarsa farin mutum sannan ta dakata dan itama ta gaji…….

     “Ya kika tsaya, ya isheki haka ne?”……

    “A’a sai anjima zan cigaba”……

    “Ba matsala yanzu kin dena fushi dani baby girl?”….

    “I’ll decide later”……

A ranta ko cewa take kome zakayi saina bar gidannan kuma bazan taba dena fushi dakai ba…..

   “Allah ya kaimu, zo muje muyi girki kinga bakici abinci ba muka fita”……

    “I’m not hungry and I can’t cook”….

    “I know, muje in koya miki”…..

     “Banaso!”…….

    “Ki daure muje in koya miki karki auri foodie yace ze miki kishiya saboda baki iya girki ba, dama irina zaki aura baki da case dan babu abinda ban iya ba”…..

      “Khaleel knows that I can cook and he loves me like that”…..

Nan da nan fuskarsa ta chanza, belt din data gama dukansa dashi ya dauka, a tsawace yace;

    “Idan muna magana kina sakomin maganar wani namiji saina fasa miki baki”………

Tashi tayi ta shige daya daga cikin bedroom din dake kasa dan bazata tsaya ya hallakata a banza ba gashi ya dauki belt, in yace ze rama dukan data mishi ai suma zatayi yanda bata da kwarin jikinnan……

       “Da kin tsaya ai, mara kunya fisararriya kawai!”…..

Zama yayi a parlourn ya kunna tv yana gadinta dan tsoro yake karta gudu dukda yaga kamar ta hakura amma ita ba abin yarda bace dan ya kula tanada wayo sosai, murmushi ne ya kwace masa daya tina abinda ya faru last night, wai yar yarinya da ita harta san tayi seducing mutum ya mata abu?, sai kuma ya hade rai tuno yanda ta rungume khaleel harya mika mata bindiga kamar wawa, yanzu duka khaleel yaji komai na jikinta, tudun kirjinta da komai?, kodai haka take yiwa maza idan tanaso su mata abu tinda rannan ce masa tayi tasan abinda zatayi a bata codeine kyauta, glass cup din dake center table ya dauka ya fasa shi ko zeji sanyi a ransa, chan kuma sai ya tashi ya fara bubbuga kofar dakin da take cikin daga murya yace;

     “Ki zo ki bude kofarnan kona ballata! Yau sai kin gayamin wa da wa kika taba runguma a rayuwarki,Ki bude nace!”…….

Banza ta mishi kamar bata jishi ba, haka ya karaci bugunsa bata bude ba, karshe barin part din yayi gabadaya ya tafi yayiwa kansa allurar bacci ko zai samu saukin abinda yakeji, nan take bacci me nauyi ya daukesa………

           “Hmmm lamarin Saif da yarinyarnan na damuna wallahi”……

Umm ta fada bayan sun koma sama……

      “Nima haka wallahi”….

    “Me kike ganin ya kamata muyi?”…..

    “Gani nake gwara mu mata aure tinda tanada wanda takeso, har suna batun guduwa kinji”……

     “Bazaiyiwu a mata aure yanzu mami, kinga fa bata iya komai na mata ba, shi kuma namiji bashi da tabbas gajiya zeyi da ita da sunyi kwana biyu, gwara a fara koya mata komai tayi aurenta a cikakkiyar mace”……….

      “Hakane kuma gsky”….

    “Toh kingani, ni wai da in tafi da ita UK tinda na kusa komawa, in bata duk wata tarbiyyar data dace da duk wani abu daya kamata ta iya”……

      “This is a nice idea, kinga zata nitsu musamman in taga me takura mata bayanan”…..

      “That’s the point!”…..

     “Amma bakya ganin ze iya cewa ze biku? Naga kamar ya hakura da aikinsa yanzu”……

    “Ah haba shi ya isa ya bimu, sai in tafi da ita a boye toh”…..

      “Hhhhh har kin ban dariya, zamu san yanda zamuyi Insha Allah”…..

      “Allah ya yadda”…….

      Tsaki taja ta dan yaye bargon data rufe jikinta dashi tana tsinema wanda ke kiranta a waya by this time da take jin dadin baccinta, saka wayar a kunne tayi cikin magagin bacci tace;

     “Waye!”…..

   “It’s me hamida ta”….

    “Ok, amma mom ya zakina kirana bayan kinsan bacci nake by this time”……

     “Haba hamida ko mu anan Nigeria gurin 12 ne fah yanzu fah, inagaku?”……

Bata rai tayi kamar mom na ganinta tace;

      “Shikena bazanyi bacci ba kuma?”….

    “Bance karkiyi bacci ba yar lelena, albishir na kira in miki”…….

Gyara zama tayi tana murza ido tace; 

      “Ina jinki mom, meya faru?”……

    “Yau za’a daura aurenki da yayanki Deen!”…..

Ta fada with a devilish smile……..

      “Aurena kuma? Bangane ba?”……

     “Eh mana aurenku, your dream will finally come through shiyasa naketa cemiki ki kwantar da hankalinki baki da miji sai Deen”……..

    “This is not the agreement we made, ya zaayi a daura mana aure kamar a kauye, ba event ba komai sai daurin aure?”…….

    “No my dear, auren zaa fara daurawa sai ayi bikin afterwards sannan ku tare”……

    “Gaskiya ni bazan yarda ba mom, so kike friends dina sumin dariya? Kinsan yanda nagama tsara bikina kuwa? Nida nakeso ayi bikin da baa tabayi a Nigeria ba, atleast muyi weeks ana events sai kice a fara daura aure bayan kinsan yaya Deen baze yarda ayi wani event ba muddin aka daura auren!”……

      “Ni na miki alkawarin ba zaki tare ba sai anyi komai daya dace, ina sane da dream wedding dinki and I’ll fulfill that, so nake kawai a daura auren hankalin kowa zefi kwanciya”…….

      “Ni gaskiya bazan yarda ba wallahi, abinda in one month time zan dawo, basai a jira na dawo sai ayi gabadaya ba”……

Sai kuma ta fashe da kuka dan babu abinda mom zata gayamata ta yarda Deen ze bari ayi event bayan daurin aure, halinshi ne babu wanda bata sani ba…..

      “Ya isa, ya isa, ba zaa daura auren ba sai kin dawo”……

Mom da zuciyarta ta karye akan kukan da hamida takeyi dan ba karamin sonta take ba ta fada…..

Share hawayen munafurcinta tayi tace;

      “Thank you mom! This is why I love you”……

    “Anything for you my baby, yanzu bari na kira alhaji na fadamasa a fasa daura auren dama sai one zaa daura……

Tana katse wayar ta kira dad, bata sha wahala ba gurin hana auren kasancewarta mutum me siyasa da iya magana, haka ta gilla masa karya shi kuma ya hau ya zauna nan taron daurin aure ya watse…….

Hamida ko tinda mom ta kashe wayar ta fara tinanin wanda yace a daura auren, bata kawo mom bace saboda tasan mom bazatayi wannan shirin batareda ta sani ba, ‘Yaya Deen’ zuciyarta ta bata akan shi yace a daura auren tinda dole saiya amince kafin ayi, toh ko ya fara sonta ne? Kai amma da taji dadi, dialing numbershi tayi taji a kashe, haka tayita trying duka nambobinsa da take dashi har Allah yasa daya ya fara ringing amma be dauka ba, bata hakura ba ta cigaba da kira still aka ki dauka, wata zuciyar ce tace mata kila kunyar daukan wayarta yake tinda yayi abun kunya yace a daura musu aure, wanka ta tashi tayi da niyar taje gidan wata kawarta ta kirashi da number kawarta maybe nata ne bayaso ya daga……

Luckily tana kiranshi da number friend dinta ya daga means ita yake ignoring, a daidai lokacin kiran waya ya ishe Deen dake nannauyen bacci ya dauka kawai yasa a speaker……

      “Yaya Deen”…..

    “Waye!”…..

Ya tambaya murya chan kasa…..

     “Yanzu harka manta muryata bayan kagama ignoring calls dina”……

      “Who the hell are you or I cut the call!”……

       “Hamida ce”….

Ta fada murya na rawa jin yanda ya daka mata tsawa…….

      “Why’re you calling?”…..

    “Magana nakeso muyi!”….

     “Ina jinki!”……

    “Ashe haka ka matsu ayi aurenmu shine harda cewa a daura aure baayi biki ba, ashe dai kana sona hhhh, toh wallahi bazan yarda a wani daura aure ba biki ba kuma……”

      “Shut up you fool!”….

Deen ya katseta da wani mugun tsawa kamar ze fasa wayar……

     “Wake up from your never happening dream, ni zaki yiwa rashin kunya dan ubanki! Toh bari kiji wallahi ko a kafa aka dauramin ke saina kunce na yar, kuma ko mata sun kare a duniyarnan ba abinda zanyi dake dan ban taba kallonki a matsayin mace ba, kije ki gayawa uwarki nace kullin datayi be dauru ba, idan sun shirya mai dake kamar bazawara su daura aurennan, idan kika kara kiran wayata I won’t hesitate to come over, in babballaki sannan na dawo idiot!”…….

Wani kuka me ciwo Hamida ta saki bayan ya kashe wayarsa, sosai maganganunsa suka mata zafi harda ce mata kullin da uwarta tayi be dauru ba, toh me yake nufi, tana kuka ta sake dialing number mom ta fadamata yanda sukayi da Deen……

Shiko Deen baccinsa ya cigaba dayi cikin kwanciyar hankali……. 

      

       Around 5pm fatima zainab ta bude kofa ta fito parlour, tsit kakeji kamar ba kowa a gidan, akan wayar Umm dake kan kujera idonta ya sauka, wayar da Umm batasan ta bari ba saboda rikicin da suka shiga, har zata share sai wani tinani ya fado mata kan ta dauka ta kira khaleel tinda ta haddace numbersa, dauka tayi tana duba wayar taga ba password, sai kuma wata zuciyar tace gwara ta samu ta fita daga gidan sannan ta kirashi, kamar wacce aka fadawa ta shiga laluben key a drawers din dake parlourn, aiko ta samo su dayawa, fita tayi da sauri hannunta rike da wayar Umm ta nufi gate din baya…..

 Tafi 10mins tana trying keys din data kwaso be budeba, hartayi losing hope tana zira dayan daya saura a hannunta kofa ta bude!!!!!!

Back to top button