Uncategorized

Matar Hariji Page 1-10 Romantic Hausa Novel

 Miqewa tayi da sauri ta daga kanta tana kallon me shigowar ya tafa hannu tare da tuntsirewa da dariya yace “kin dauka wannan raggon mijin nakine ko? Nifa ina mamakin yanda mace kamarki zaki tsaya kina auren wannan sullutun mutumin da baya iya biya miki buqatarki itafa mace tafi kowa yanci kuma tanada zabin daya dace da ita namiji dai har namiji a riga Amma a gado babu fuss sai jinkai da izza a waje, koda yake hakanma ni yayimin ya auromin mata babu ko sisina nayi mata ban ruwa kuma ta cikamin aljihuna da kudi hhhhhhhh!” 

Suka kwashe da dariya ita kuma ta tsuke fuska tace “amma kasan nace maka kada kazo gdannan yau yayanka zai dawo kuma kasan cewa banason ya fahimci akwai alaqa tsakaninmu mu zauna a matsayin abokan gaba haka nakeso shirin ya kasance.

Dara² idanunsa ya sauke akan me tallan furar da ya tsayar ta dago da hardaddiyar hausarta tace “Kado ka hiya niman magana wallah in zaka shiya jaka hudu ka shiya in bakka shiya kuma ka bareshi dama kai ka cika son araha toni komi nawa mi tsadane kajima in hwadi maka”

Yanda take mgnr ne yayi bala’in bawa pillot Lameer dariya yayi murmushi yace “komanki me tsadane nikuwa idan babu damuwa mu buga wani wasa mana ki fadamin komai kikeso zanyi miki zan aureki kawai dan ki rinqa bani dariya ko sau daya kika bari nazo gurinki baki bani dariya ba zan sanya karnukan gdana su cijeki idanfa kin yarda” 

Wani murguda baki Jiddoh tayi tace “hohoho aura kado mi akai akayika da har zan kasa baka dariya yo ko innarka da baffanka ai nabawa dariya kai bura ma kaji wani abu kwanaki da naje burni har wani me qaton ciki nabawa dariya bare kai dan tatsitsi dakai amma fah tsaya kaji ni bani auren kado kado bashi riqon aure saki a jininku shike yawwa kuma jauro Madi ma ya fika kyau gashi dan gayu har agogo fah yake sawa🤣🤣🤣

Sake gyara zaman hularsa yayi ya zuba mata maganadisun idanunsa yana qare mata kallo sama da qasa yace “nononki baiyi tsami ba ko?” Turo baki gaba tayi ta qara tura cokalelen dankwalinta gaba tace “yo nonon shanuwa idan yayi tsami ai saidai akai juji” dariya yayi da ganin bata fahimci me yake cewa ba yace “amma akwai ranar da nonon naki zaiyi tsami fah” wani tsalle tayi tace “ariyyy hege Kaɗo da muguwar alkaba’i kake idan nonona yayi tsami ai goggo kasheni takayi kai barima kaji ranar nan da mukaje dandali ana ajon auren me yar butta da tsalha da nashiga ina rawa kowa saida ya liqamin takarda”

Ɗan ƙaramin bakinta ya zubawa ido yana kallonta yarinyar kyakkyawa sai bambadanci daya dami rayuwarta miqewa yayi tare dayin miqa yace “kisamu leda ki juyemin a ciki zan baki jaka uku da rabi” miƙewa tayi ta zari qwaryarta zata tafi ya riqo hnnunta da sauri yace “tsaya mana Hauwa” sakin ƙwayar tayi jikinta ya dauki rawa ta zube a gurin ta fasa uban ihu ya saki bottle  ɗin hannunsa yayo kanta yayi saurin rufe mata baki yace “ke kinada hsnkali kuwa JIDDAH uwar me nayi miki da zaki zunduma wannan uban ihun salon kisa yan uwanki su bugeni”  

sake rintse idonta tayi ta zunduma ihu tana fadin “shikenan na mutu na lalace jiyannan goggo ta gama hwaɗi mami cewa idan kaɗo ya tabaka mutuwa kakeyi yanzu nima shikenan mutuwata tazo zan tafi inda Allah wayyoh ni goggo wayyoh ni baffa wayyoh ni Madi dan burni kaɗo ya cutamin shikenan walakiri zaya kasheni…”

Sauke Littafin : Dr. Bobby Complete Novel Document


Tsayawa yayi kawai ya zuba mata ido haushi baƙin ciki da takaici kamar su kasheshi baisan sanda ya fincikota ya hadata da jikinsa yace “badai tabaki nayi kike haukannan ba to na rungumeki na tsotsi bakinki ma yarinya sai ki jira mutuwarki kowanne lkc daga yanzu” 

Bai damu da yanda ta bata jikinta da nono ba ya sake mannata da jikin motar ya matseta yanda ko hangenta baayi ya manna mta kiss a goshinta da lebenta ya sauke numfashi ya saketa ta kuwa zube a gurin shikuma ya zaro dubu biyu ya ɗora mata a cinyarta ya shige motarsa yaja yabar gurin itakam jiddah sake neman guri tayi ta kwanta bayan ta soke kudinta tana jiran mutuwarta don tayi imanin a yau kaɗó ya cusheta babu abinda zai hanata mutuwa.

Numfashinta ma ɗaukewa takeyi wai ta mutu idan ta bude idonta saita sunsuna rigar jikinta sai taji ƙamshin jikin kaɗo a jikin rigarta sai ta sake mutuwa taji ko zata dainajin ƙamshin turaren kaɗonta😄😃

Tananan kwance har masu kiwon shanun rugarsu suka fara dawowa idan taji tafiyar mutane sai ta qara kwanciya tayi luf ita a dole ta mutu idan suka wucce sai ta bude idonta tayi ajiyar zuciya tace “hege walakiri ya wucce baiganni ba”🤣

Kai harfa dare ya fara shiga Jiddoh ana kwance jikin ta qaura yayi la’asar qarshe dai ta tashi zaune ta takure a jikin wata bishiya tanata dan kukanta.

Baffanta ne yazo wuccewa yaci karo da qwarya yayi saurin ja da baya tare da ciro touch light dinsa ya fara haske haske can ya hangota a takure ya matsa da sanda gabanta yana ware Mata kallo Saida ya tabbatar itace sannan ya matsa kusa da ita ya hasketa tayi saurin dagowa tare da qanqame jikinta tana karkarwa tace “na tuba azara’ilu mazarin rai alqur’an   bansan ya taba hannuna ba kuma ma har rungumeni yayi sumbaceni nidai yau mutuwa kala uku zanyi wayyohh Baffa zan tafi nabar ko harda Madi dan burni aradun Allah kado ka cuceni…” 

Naushin da taji taji an sakar Mata a bakinta shine ya dawo da ita hayyacinta ta bude idonta ta saukeshi akan baffanta aisai ta zabura ta miqe da sabuwar rawar jiki tace “kaima Baffa ka mutu ne ashe zanci gaba da ganinka a lahira amma baffa ance a lahira baa zalumci meye yasa ka bugemin baki” fincikarta yayi yace “dama Yadammu ta hwadi mani cewa akwai wani kado da yake zuwa yake siye nononki kullum har yana qara miki kudi yanzu har takai ya hwara rungumarki yana sumbarki to alqur’an baki jamin abin hwadi a duniya ba a rinqa nunani da lebe muje wuro nijiyya ubanda yace ki rinqa hutta kina neman maza mazanma asararru irin kadawa su shusheki su tai su barki”

Figarta yakeyi da dukkan qarfinsu suna shiga ya watsata tsakar gdan fadi yake “Laure Ladi ku fito kuji abunda almurar diyar nan take aikatawa nan fa duk gida aka fito akayi cirko² ita kuma ta qara bajewa a dole itafa mutuwa take jira.

Gyaran murya Baffa wuro yayi yace “wato Laure kene kika lalata yarki da kanki yanzu gatanan ta hwadi miki abinda suke aikatawa da kado” salati aka hau yi ana tafa hannuwa fadi suke sun banu sun lalace wani uwar maqura da goggo tayi Mata ne yasata sake shiga hayyacinta tace “qur’anin ubangiji bani nace yayimin shine yayimin kuma nima har mutuwa nayi walakiri yaqi zuwa ya tafi dani da tuni na huta” 

Buge bakinta goggo tayi tace zakici uwariyonki yar qaniya” Baffa ne ya daga murya yace “Tani kaje kace da Jauro mudi anjima inason ganeshi aradun Allah aure zanyi miki tunda ke bakyajin magana yau ki tsokano masunta gone ki tsokano manoma yanzu kin fara biyewa shiriritar kado to gara kowa ma da kado donni ko gaisuwa banso ta hadani da kado shashashan kawai” 

___________Qarfe tara na dare ya shiga cikin garin Kano saboda tsakanin Kano da qauyen Alqalawa da nisa sosai don’t qallah yakai kilometer 94.

Gdan iyayensa dake cikin unguwar Tarauni ya fara zuwa yayi parking ya fito ya qwanqwasa bayan yan mintina yaji ana zare saqatar gdan suka gaisa da maigadin yace “Alh kuwa yananan?” Shafa kansa yayi yace “Sai Hajiya dama tace idan kazo ince tanason ganinka” 

Saida gabansa ya fadi don yasan Kiran mahaifiyar tasu ba alkhairi bane, hakanan yasa aka budensa get din ya shiga da motarsa yayi parking ya fita ya dauki ledojin da yasa aka yanko masa zabbi manya guda ashirin ya raba biyu zaikai gidansa daya daya kuma ya taho dashi gdan iyayen nasa ya shiga.

Da sallama aka amsa masa ya miqawa me aikin da take yankan apple ledojin guda biyu days zabbi daya qwansu ta tafi shikuma ya zauna tare da rusunawa yace “hajiya barka da hutawa”……….

Karanta Littafin : Macijine Shi Complete Hausa Novel

Wani mugun kallo ta watsa masa tare da yatsina fuska ta qara cokalo dankwalinta gaba tacr “wato kai Lameer bakajin mgn ko ban isa dakai ba jiya jiyannan mukayi muku sulhu da wannan yarinyar arziqin Mubaraka amma yau ma dake kai dan tsiyane Saida ka qara towai meye matsalarka ne kullum ku kenan a sulhu kamar qananun yara?” 

Tattare girar sama data qasa yayi yace “yanzu dai qarata ta kawo miki kenan towai ita yaushe zata fahimceni ne yanzu ace matarka ta sunna ta kasa gane matsalarka to waye zai gane kuwa” daquwa ta watsa masa ta gyara zaman mazaunanta tace “qaniyarka dan kusun uwa taya zata gane baka yi Mata ban ruwa yanda ya dace har cemin tayi fah sai kayi wata baka nemeta ba idan kuma ka nemeta din saidai kabarta da ciwon mara dakayi kuruf kuruf na minti biyar ka gama oni Kandala qanwar maza anya wannan da ba mace zaayi ba kuwa aka manta akayima abin maza kai komai naka a sanyaye”

Wata uwar kunyace ta kama Lameer kamar qasa ta tsage ya shige shikam ya shiga uku da barbada a dangi tun yana boyewa iyayensa matsalarsa yau gashi Mubaraka ta tona masa asiri ta yaye masa zani a kasuwa shiwai wacce irin mace yake aure mara sirri bata riqe nata bama bare ta riqe na wani to waima yaushe ma sukayi auren ne duka duka har yanzu basu rufa shekara uku ba da yarsu daya amma duk ta tallatashi a dangi bayan shima bashi yayi kansa a hakaba hakanan ya tashi yaganshi bashida qarfin sha’awa.

Ruwa yaji Hajiya ta watso masa tace “soko sakarai tashi ka bacemin a guri nikam na haihi Ladidi da hula har mace take kawo qararta dubi jikinka duk wani farin abu ya bushe kamar wani Fadwah yar cikinka ma tahika natsuwa” 

Kallon jikinsa yayi da sauri yana tunanin to meye a jikin nasa tunawa yayi da yanda suka rabu da Hauwa yar fillo dutse a hannun riga baisan sanda yayi murmushi ba tare da shafa kansa yace “nono naje siyo mana rugar Sambajo a garin Alqalawa wlh wata sokuwar yarinya Hauwa tayimin barinsa a jikina wai kawai saboda by mistake na taba hannunta a shirmenta wai goggonta tace idan kado ya tabata mutuwa zatayi” 

Dariya sosai Hajiya takeyi tace “dada fillo bazai waye ba batasan kaima hakan take ba” fara’ar fuskarsa ce ta dauke ya tsuke fuska idanunsa ya kada yayi jajir yace “zan daina zuwa gidan nan Hajiya tunda nayi aure bantaba zuwa gdannan na tafi da farin ciki ba kullum sai kin fadamin kalma mara dadi akan lalurata Hajiya idan ban samu tausayi dajin qai a gurinki ba a gurin wa zan samu?” 

Binsa tayi da kallo cike da sanyin jiki kuma fa mgnr dan nata haka take kamata yayi take kwantar masa da hankali tabe baki tayi tace “hotiho kawai” 

__________Horn yaketa dokawa a gidan nasa kafin maigadin yazo ya bude masa ya shiga yayi parking ya dauki kayan dayazo dasu ya bude qofar parlourn ya shiga TV tanata aiki ga yarsa nan Fadwah tanata baccinta a saman kujera ita kuma uwar bata parlourn.

Iska ya furzar ya nufi qofar dakin ya kama jarmlock din amma sai yajishi a kulle yayi Knocking ya juya ya shiga kitchen ya nade hannun rigarsa ya fara jera naman da yazo dashi a ciki ya koma kan kayan miyan Suma yaji an bude qofar parlourn an mayar an rufe, to be kawo komai a ransa ba saboda zuciyarsa ta tafi tunanin Hauwa wanda ya addabi zuciyarsa cikin kwanakin nan ko kwanciya yayi itace da sakarcinta sukeyi masa yawo a kwanya saidai yayita zuba murmushi shi kadai gashi gobe zaiyi tafiya zuwa sounth Africa zaiyi missing dinta sosai.

Baiji shigowarta ba sai ji yayi ta bugeshi ta baya ta wucce ya dago manyan maganansa ya kalleta ta daga masa hannu tace “oh sorry mistake ashe ka dawo” murmushin kawai yayi ya matsa gabanta yace “naji saqonki na gode waike Mubaraka yaushe zakiyi hankali ne ki riqe mana sirrinmu kinsani fah nafi kowa son naga na zama jarumin namiji wanda bakeba zan iya gamsar da wasu matan ma amma ban samu wannan damar ba ya kikeso nayi don Allah kina gani kullum cikin neman magani nake kuma kin sani ko banyi sex ba Ina iyakar qoqarina naga na cire miki kewa amma komai nayi miki bakya gani saboda kawai wannan matsalar  Mubaraka mata da yawa irin damarki suke nema sun rasa kinga ke ba rashin ci ba ba rashin sutura ba duk abinda kikace shine nakeyi miki Toni meye ya hana ki karbeni a yanda nake bayan kin sani abubuwa da yawa naki bayimin sukayi ba Amma saboda kada tawayar tayi yawa nake qyaleki yanzu idan baki rufa asirinmu ba a duniya waye zai rufa?”

Tabe baki tayi ta juye indomie dinta a flat sai yanzu ma ya lura da yanda gashinta yake a hargitse shi dama ba kirki ba, kafin yayi mgn tace “dallah malam kauce na wucce” matsawa yayi ta wucce har takai bakin qofar yace “yinin yau banci abinci ba Ina abinci na?” Ko kallon arziqi bai samu ba tayi ficewarta.

Ajiyar numfashi yayi ya dauki yourghut da cake ya fita ya nufi dakinsa dake sama abin takaici da mamaki dakin kaca²  gadon harda danshi alamun baa dade da tashi akai ba ya ajiye yourghut din ya fara gyara dakin ya gama ya shimfida sallaya yaci abinda zaici ya miqe yayi wanka ya dawo ya dauki laptop dinsa ya fara aikace²nsa sai wajen daya sannan ya kwanta saime?

Zuciyarsa taqi hutawa da tunanin Hauwa da zarar ya rintse idonsa kallonta yakeyi matse jikin mota ya hade jikinsa da nata yana sauke mata kiss a kuncinta jikinta na rawa tunaninsa gabadaya ya karkata ya koma Rugar Sambajo qauyen su Jiddoh yasan dai bai barta da matsala ba tunda ya biyata kudin nononta da wautarta tasa ya zubar da haka ya kwana ko cikin baccinsa itace wai tana shafa gemunsa tana cemasa “I LOVE U My Lameer” shikadai yaketa zuba murmushi yana qara qanqame pillow.

Hodijam Jiddoh baiwar Allah wannan dare ta daku gurin goggonta har saida ta kumbura mata jiki saboda duka da muburgi fadi takeyi “ni zaki kunyata ki jawa abin hwadi a gari dan ubanki ki rasa wa zakike kulawa kuna shiga duhun dawa dashi yana lalubeki sai kado ashe da gaskene da Madi dan burni yashe yana ganinki kina kaiwa wani dan yankon kayi nono yanayi miki juyensa ya baki kudi da yawa, to daɗa Allah ya nunamin kuɗi har jaka goma a jikinki ɓingel wato kuɗi yake baki yake ƙwaƙuleki ko?”

Girgiza kai takeyi kamar zata tsinkeshi tana kuka jikinta na rawa goggo ta sake nufota tana cewa “kina yimun bayani ko sai nasha aradu ani gaton uwarki”

Jiddoh bata iya qaryaba cikin kuka ta zayyane musu komai suka rinqa sallalami da tafa hannaye suna hwadin “aradun Allah Jiddoh kin riqa qugunki ya isa daukan bindira tunda har kado ya hwara hwadi maki batun aure to kuwa ai dole baffanki yayi miki aure da Madi dan burni tunda ke shegiyar ya ce” 

Wata wawura goggonta ta kumayi mata ta zauneta ta bare qafafunta tana kuka tana ihu ta dauki danyan tasshi ta murza Mata ta dagata tace “gobema ki qara bari Kado ya tabaki har ya dambusheki dau uwariyonki aurakiya kawai almura me idon agwagwa”

Habawa me Jiddoh zatayi banda kuka tumami da ihun azaba danyan barkono a gatonta sai tsuku yakeyi Mata ita kuma tanata dara tana tumami tana ihu da kuka me ban tausayi.

A haka goggonta ta cillo Mata bokatin qarfe tace “tashi dan ubanki kije rafi ki daukomin ruwa kizo kiyi wanka kiyimin wankin daudata ki sukole wadannan kayan naki bazan kwanta dake bukka dai ba babu tsarki yau sai kin qarar da ruwa buta goma” 

Hakanan tana tafe tana talewa tana kuka taje rafin ta zauna a bakin rafi tanata rera kukanta taji an warce bokitin nata ta dago da sauri zatayi bala’i sai taga Madi a tsaye sai washe baki yakeyi yana turo harshe gaba yace “hegiya Jiddoh yau nayi miki burni ai ya nine nazo nace naganki da Kado a cikin duhun dawa kuna cicin tsuli kuma aradun Allah gobema na ganki kin qara kai mushi nono sai nayi miki sharri da yahi haka tunda ke bakyaji kuma kin rainani aradun Allah bindira ta tahi ta Kado qarhi kuma kizo muje bayan rafi a gwada ki gan….”

Qumm yaji an buga masa Abu a goshinsa jini ya balle ita kuma taja da baya da sauri tace “alqur’anin Allah kai tsinanne ne Innan qotai tayi asarar aihuwa shege dan durun uwa danma ka samu nace da Kado ka iya sa agogo to tunda kai Dan iskane na daina sonka ma na tsaneka na tsaneka hege bindirar ka din uwarka an hwadi muka di diyat iskace”

Damqota yakai hannu zaiyi ta qara jifansa da bokatin ta kwasa da gudu ta shige cikin duhun dawa tanata bubbuda qafa saboda zafin tasshin da takeji a qasanta har yanzu ta jima a gurin sannan taga yabar gurin ta fito da sanda ta kandami ruwanta ta dora akanta ta nufi cikin rugarsu takai tayi wanka ta wanke gidan dadin sosai Amma har lkcn zafi yakeyi Mata ta shafa versilin a gurin ta rinqa fifitawa har Allah yasa taji relief ta koma daki tayi sallah ta kwanta  tanata juyi qasan zuciyarta cike da tunanin Kado tare dajin haushinsa na jamata dukan da yayi a fili tayi tsaki tace “Kado hege ne harda wani hmwah yayimin qaton kawai saikace Bandirawo Iro”…………

Karanta Littafin : Abban Sojoji Hausa Novel

Washegari tun asuba ya tashi ya fara shirya kayansa cikin trouble bag dinsa kasancewar yasan Koda ya tashi Mubaraka ba lallai ta tashi ba zatace yayi wuri da yawa to shima baiyi yunqurin tashin nataba ya gama shirinsa tsaf ya hada tea dinsa yasha ya kira drivern office dinsa ya daukeshi zuwa airport kasancewar tafiyar bashi daya bane da sauran abokan aikinsa zasuje training din.

Yana zuwa babu bata lkc suka daga zuwa South Africa zuciyarsa cike da kewar parents dinsa da yar fulaninsa Hauwa da kewarta take neman zame masa jiki a wannan lkcn haka ya wanzu cikin wata irin rayuwa daya kasa gane wacce iri ce kullum zasuyi waya sau biyu da Mubaraka ya tambayeta lfyrta data yarsa Fadwah amma ya kasa daina kewar qasarsa ta gado musamman Rugar Sambajo.

____________Kwananta uku bata dauki tallan nono ba ko dandali ta daina fita duk a qoqarinta na karsu hadu da Madi dan burni yace zai sanya mata bindara tunda taji Indo qawarta da akayi Mata aure tana cewa bindira lubebiyace idan ta shiga bata iya fita saidai ta yayyaga mutum kuma idan ta tashi dane yake tunkudota waje.

Shiyasa take masifar tsoron bindira ita har kuka takeyi da tumami idan akace zaa kaita asa mata bindira, tana tafi tana yan waqoqinta taci uwar dammara abinka tayi kwalliya ta rambada kanta kile harda digon india a goshinta da kumatunta tasa kayansu na fulani shudaye tana tafe tana waqar  “lula lulaye aluliya zani bikin andi aluliya” batasan binta akeyi ba saida tazo jikin wata bishiya kawai taji an dumbular mata nono an kwasa da gudu.

Aikuwa ta dora hannunta akan nononta tana ihu tana burgima tana hwadin “shikenan na mitu na lalashe dan innini na sun tabamin wayyoh Goggo wayyohhhh Baffa wlh bazan yarda ba saina taba nonon uwarsa nima” wasu yanmata ne guda uku sukazo wuccewa suka ganta a kwance duk tayi birgima tayi tumu² suka tsaya suna kallonta tare da tafa hannu sukace “Hamdi imboni Jiddoh meye hakadin?” 

Miqewa tayi zaune tana karkade qasar data shiga cikin dogo baqin gashinta da ya mulku da manshanu tace “Qur’ani saina mulmulawa uwar Wanda ya dumbularmin Inninina Fura a gatonta”🤣🤣

Dariya suka kwashe da ita Lantana ta kalli Jummai tace “kiji doluwa to yau aka fara dumbular inninin naki naga cewa akayi har Kado kike bawa yakesha shiyasa sukayi girma sukayi ruguza ruguza haka” 

Zabura tayi tace “kutmar dumadu naci hagu naci dama naci tattabatsinin kantalin baqoramar inyaniyar marurun tsohon gwailon uban wanda ya hwadi haka” kafin suyi wani aune ta hade kansu guri guda ta kama jibgarsu hagu da dama tana wani tsalle tana naushi ta ko Ina.

Suna ganin haka kowa yaci na kare ta kuwa rufa musu baya a guje fadi take.

 Yau har bayan tsoho da tsohuwa suna doki doki sai nabi ƴa naci uwar galken ubanta Kaɗon dako mgn bata dameshi ba ina ya iya wannan iskancin shi banda sumba da qaquba babu abinda ya iya kuma qur’ani saina hwaɗí muhi bashi kawo lantarki gidanku”

Yanda suka rinqa gudun a daji abin abin dariya kuma sai qara rungume qirjinta takeyi wai kada a qara dumbular mata nono😁

Jitayi an riƙeta ta baya taja ta tsaya tana huci tare da waiwayowa zatayi bala’i sai tayi ƙasa luuuu saboda ganin yayanta lawan tasan ta kaɗe har rassanta rirriƙeshi tayi tana kuka tana cewa.

“Alqur’an bani na tsokalesu ba sune kawai ina kukana da burgimar tuba sukazo suka tambayeni meye yasani kuka nace adumbili akayimin shine sukace wai ai dama ance ina bawa Kaɗo nono na wannan na jikina bana shanuwa ba yanasha kuma aradun Allah ƙarya sukeyi barima na fito maka dashi ka gani”

Hannu ya dora aka yace “honi lawwali ni zaki nunawa dan qaniyarki yar  ja’ira tashi muje wuro kiyi bayani” yanayin gaba ta miqe da sauri ta nade zanenta ta kuma kwasa da gudu ta nufi gdan yana kiranta yana komai amma bata tsayaba saida ta isa gdan ta shige dakin kishiyar Goggonta tana mazari Inna Jummah ta miqe da sauri tace.

“Wanne niya meye hakadin ubanwa kika taokano” sake qanqameta tayi tana kuka tana girgiza kai yana zuwa ya cake yace “zakici qaniyarki yar kusun uwa”

Yana fita ta zube a tsakar dakin tana mayar da numfashi tace “wlh sai nayi qulla ciki akan wanda yayimin adumbuli” tafa hannu jummah tayi tace “gide shiyasa nice da baffanki yayi miki aure” 

Saurin rufe Mata baki tayi tace qur’ani baniso ance idan akayi wai…Wai….” Saurin daga mata hannu tayi tace “aradu ya isa kuma dole baffanki ya aurar dake shekara sha hudu qawayenki harda yayansu ke kinanan kina bambadanci a gari” 

Miqewa tayi tace “ai saiki aurar dani din yo aradun Allah guduwa zanyi kamar yanda Ladin Moddibo ta gudu nima na rinqa shigowa daga maraya Ina taunar danqo Ina tafiya qwasqwas.

Binta tayi da kallo har ta fice daga dakin ta nufi dakinsu ta kwanta tare dajan mayani ta lullube jikinta dashi yau goggonta da kanta ta fita tallan nono, zuciyarta ce ta tafi tunanin Lameer ta dallawa kanta mari tare da jan tsaki tace “aikin banza ma ko meye gamina dashi.

Karanta Littafin : Matar Makaho Complete Hausa Novel

___________Lkc yanata tafiyarwa Lameer ya kasa sukuni kullum da tunanin Hauwah yake kwana yake tashi idan ya kwanta bashida mafarki sai nata wannan mafarki shine yake dauke masa kewar abubuwa da yawa saboda idan yayishi yakan yini cikin walwala da farin ciki.

Watansu biyu suka gama abinda sukaje yi suka fara haramar tahowa gida shidai farin ciki gurinsa baa cewa komai ya rasa meye yakeji game da Hauwah amma yafi alaqanta abin da soyayya to kuma shi wanne irin so yakeyi mata ya zaiyi ma ya tunkari iyayenta yace yana son yarsu?

Ya fahimci sudin irin fulanin nan ne masu tsauri sosai a dan shiga cikinsu din da yakeyi ya fahimci sun tsani Bahaushe musamman ta fanni auratayya zaiyi walaha kaji mutanen rugar Sambajo sun aurar a waje ko sun auro.

“To wai nima da nake wannan lissafin ta Yaya zan auri mace sama da daya bayan dayar ma bana iya sauke nauyinta dake kaina dari bisa dari?” 

Ya tambayi kansa yana shafa qasumbarsa tare da lumshe idonsa ya hadiye wani yawu me ciwo shikam yanason Hauwah matsayin Mata to amma ya zaiyi ya riqeta ya sauke mata dukkan haqqoqinta sannan ya zaiyi da Hajiyarsa data tsani ko mgnr kishiya taji wani yayi balleshi da dama kamar ta tsaneshi cikin yayanta ya lura har tafison Mubaraka akansa saboda indai abi ya shafi Mubaraka to yanzu zata rufe ido taci mutuncin sa, “Ni wai ya zanyi ne?” ya fada yana dafe qirjinsa da yakeyi masa zafi saboda ba yau ya fara wannan tunanin ba.

Ya jima yana saqawa da warwarewa domin samun mafita amma ya kasa jin Hauwah yakeyi a duk wata kusurwa ta jikinsa.  

Ji yakeyi dama ace zai sameta batare da yasha wahala ba shikam koma meye zai faru saidai ya faru Hauwah itace muradinsa a yanzu baya fatan ya rasata a rayuwarsa jima yakeyi kamar idan ya rasa Jiddah bazai rayu ba.

____________Abubuwa da dama sun faru a cikin watanni biyun ciki harda tsayar da ranar  aurenta da Madi wannan abu ba qaramin dagula lissafin Jiddoh yayi ba ta tashi hankalin kowa akan cewa itafa bazata aure Madi ba dan iskane har cewa yayi suzo su zagaya duhun dawa ya gwada mata bindira.

Duk yanda tayi tunanin abin zaizo Mata da sauqi ta kasa samun wannan gatan hakan yasa kullum cikin kuka take da damuwa ko zaman gidan ta daina duk da sun hanata fita amma suna fita tallan nono zata haure dangar karar da suka kewaye gidansu da ita ta shiga cikin duhun daji.

Sau tari sai baffanta yaje gindin magwaron data mayar gurin zamanta ya korota sannan take tafiya hatta abinci ta dainaci saidai idan taji yunwa Tasha madarar shanu ta kwanta sukam iyayen ko a jikinsu hidimarsu kawai sukeyi.

Ana haka ta fara rashin lfy sosai kamar bazatayi ba nanfa hankalin baffanta ya tashi sosai ya shiga damuwa dan baiyi tunanin qiyayyar da takewa dakai har ta kwanta jinya ba.

Yaso ya canza raayi amma yayarsa Yadammu tazo har gida ta rinqa sababin bala’i wai ai iskokine da Jiddoh dama haukanta ba irin na masu hankali bane wauta tsokana da rashin kunya duk ta tattara kuma a gurin uwarta ta kwashe komai.

Shiga gdan yayi yana fadin “Hari! Hari!! Ke Hari dake nake wannan ja’irar yar taki bazata jamin abin fadaba maza fito Yadammu tace yau Boka bawa yake hawa bori fito da Jiddoh muje yau duk uban aljanin dake kanta saiya sauka kuma aure tsakaninta da Madile babu fashi saidai idan bana raye”

Dukkan matan gdan fitowa sukayi suka fara sallalami suna fadin “oya maigida Moddibo Dalha ma yana maganin iskoki basai kaje gurin Boka Bawa ba” 

Daquwa ya watsa musu yace “kunfini ko kunfi Yadammu sanin abinda ya dashe ne to aradun Allah duk Wanda shi qara buda baki sai ta koma gdan tsohonta almuran banza almuran wofi ai dama nasan kune kuke daurewa Jiddoh gindi takeyin abinda taga dama nan har gda akazo aka yimin gorin nabarta ta gandame ta zama uwar mata a gda tunda rugannan take babu yar data tabayin shakara sha hudu a gdan iyayenta sai ita kunsani yarinya tun tanada shekara tara ake dauranta aure a rugannan amma ita saboda bakin jininta da mugun halinta gatanan daqyar ta samu Madilen ma ya tsaya yo banda sharrin iskoki inane zatashe batasonshi har tani jinya yo kwarankwatsa saidai tayi bunga”

Shiga daki goggonta tayi tana tashinta amma fir taqi tashi saida sukakai ruwa rana sannan da taga Baffa ya dauko kokara zai sabeta yasata tashi ta fice da gudu tayi bayan gdan gudu takeyi sosai bata tsayaba saida tayi nisa da rugarsu ta shiga wata fadama ta samu gindin bishiyar kashu ta zauna tana haki dafe da qirjinta saida tayi me isarta sannan ta hade kanta da gwiwa taci gaba da rera kukanta zuciyarta na tuno mata da Kado tana tuna rana ta farko da suka fara haduwa dashi.

WAWAYE

_________Goggonta ta dora Mata tallan nono su Idin Tasha suka shanye Mata harda sanyata ta siyo musu sukari ta zuba musu suka tashi zasu tafi tace su bata kudinta suka kama zaginta harda dungure mata kai Mati ya zare Wuqa yace zai yankata idan bata tafiba babu arziqi ta tashi ta dauki qorenta ta nufi hanyar rugarsu tana tafi tana waiwaye batayi auneba kawai taji ta bugi mutum tayi baya da sauri jikinta na rawa ta dago ta kalleshi kyakkyawan Saurayi me cikar zati dago kakkaura wankan tarwada sanye da kayan turawa injita da fada.

Shima kallonta yakeyi cikin hasala yace “ke wacce irin yarinya ce kina tafe kamar makauniya kalla yanda kika batamin jiki da nono….”

Daga hannunta tayi tana ajiyar zuciya da niyyar bashi haƙuri bata iya buɗe bakinta ba saboda kukan da yaci ƙarfinta kawai sai ta kama ƙafarsa ta fashe da kuka.

Jikinsa ne yayi sanyi tunaninsa mgnr daya fada mata ce tasata kuka shima durƙushewa yayi ya sanya hannunsa ya ɗago fuskarta ya zuba mata kyawawan manyan idanunsa ƙirjinsa na bugawa da sauri da sauri  yace “meye dalilin kukan?”

Cikin in…ina tace “su… su Idi da Mati suka shanyemin nono har sukashe ni siyo masu sukari da ciniki na kuma suka hanani kuɗin kuma sukashe idan nace sune sai sun kasheni kullum sai sunsa Goggona ta bugeni idan kuma na hanasu su shunamin karnukansu suyita yimin haushi kwanaki wani har cizona yayi” ta zauna sosai ta bude masa gurin saman santala santalan sangalalin qafarta farare tas da suka cika da suma kwantacciya lufluf dashi ya sauke idonsa a gurin da karen ya cijeta gurin har yayi rami sai ruwa yake zubarwa………..

Rintse idonsa yayi da sauri yace “subhanallahi meye yasa bakije an wanke miki gurin ba?” Shiru tayi tana sharar hawaye kafin ya miqe yace “zo na wanke miki nasa miki magani” batayi jayayya dashi ba ta miqe tabishi yasa ta zauna a gefen motarsa shikuma ya dauko hydrogen da corton ya fara wanke Mata tana kuka tana ciccije leɓe yanayi Mata sannu lkc zuwa lkc yana ɗagowa yana kallon kyakkyawar fuskarta data jiqe sharƙaf da hawaye yanajin wani tausayinta yana kwarara a sassan jikinsa.

Koda ya gama yayi mata plasting ɗin zama yayi ya zuba mata ido yana kallon kyakkyawar halittar bafulanar yanajin wani shauqi na taso masa, a hankali cikin dashewar murya yace

 “Ya sunanki?” haɗiye kukanta tayi tace “Jiddoh Arɗo Jibir” iska ya furzar ya miƙe yace “ok gobe kizonan idan kin ɗauko nonon ki kawo min zan siya zan taho da likita yayi miki allura kinsan cizo kare dafine dashi ƙafarki zata iya ruɓewa idan baayi miki allura ba, na nawane nonon dasu Idin suka shanye miki”

Shiru tayi kamar bazatayi mgn ba ta fara haɗe kayanta bayan ta gama ta miƙe zata tafi ya riƙe hijjab dinta fuskarsa murtuk ya zaro dubu biyu ya bata yace “ki ajiyemin canji na gobe zan karba kada Goggo ta dakarmin ke” ƙememe taƙi karɓar kudin wai dukanta zaayi nononta na jaka huɗu da rabi ne.

Kama gefen kallabinta yayi ya ɗaure mata dubu daya ya bata ɗaya a hannunta yace “kice da goggo wani ne ya siyi nono babu canji shine yace gobe kibashi na rabin jakar”

Dariya tayi tace “aradun Allah kaɗo kanada wayo sosai zaka tai dani burni na ƙaro wayo?”

dariya ta bashi ya shiga motarsa ya kunna tana tsaye har yayi kwana zai tafi ta bude baki tace “Kaɗo” juyowa yayi ya tsaya wai kaɗo sai kuma yayi murmushi ya daga mata hannu itama ta daga masa hannu ta juya ta tafi, yabi bayanta da kallo yana ajiyar zuciya a hankali yace “Hauwa’u kulu Maijiddah.

Figar motar yayi a guje ya fice daga lungun tundaga wannan lkc ya kasance kullum shine yake siye nononta idan ta dauko idan kuma zaiyi tafiya bazaizo ba to yakan bawa manajan gdan gonarsa kudin ya rinƙa bata kullum hakanne ya wanzar da shaƙuwa me ƙarfi tsakaninsu.

ASALIN LABARIN

___________Tananan zaune a wannan guri har duhun magaruba ya fara sawo kai ta miƙe a hankali ta fara fita daga saƙaƙiyar har ta fito titi sosai ta fara tafiya cikin rashin kuzari har ta isa rugarsu takuwa yi saa Allah bai haɗata da ƴan dumbule ba don ta lura nononta da Allah ya wadatata dasu suna mugun jan hankalin maza duk da cewa kullum cikin taresu takeyi da hannunta kasancewar ba bra suke sanyawa ba haka suke yawo da abunsu a tsaye cako cako wannan dalilin yasa kullum take taresu saboda kunya takeji taga sunyi cokal cokal dinnan.

Isarta gda kenan taga gilmawar wata baqar LAND GRUSSER ta bayan bukkokinsu a guje hakanan taji gabanta ya fadi tanason ganin waye a ciki amma babu dama da alamun na cikin ma a fusace yake.

Ƙwafa tayi ta shiga gdan nasu taja tayi turus ganin ƴan gidan nasu gabaɗaya tun daga kan baffansu har zuwa kakansu mahaifin baffansu kowa yayi cirko cirko suntada gemu da alamun wani abune mara daɗi ya hwaru batasan hawa ba balle sauka taji an fincikota tsakiyar filin da mutane sama da talatin sukayiwa da’ira wanda ko gutsuttsurata akayi ƙila wani bazai samu ba anyi cilli da ita an hau bugunta ta ko’ina suna haki kamar waɗanda aka sanyasu dole.

Itakuwa baiwar Allah Jiddoh sai ihu takeyi tana roƙonsu su bar dukanta zata mutu amma babu wanda yaji tausayinta ya ƙyaleta ita kuwa goggo tashi tayi tabar gurin saboda tanayin mgn kanta zaa dawo ace tayi rashin kunya.

Basu bar jibgar Jiddoh ba saida sukaga ta daina numfashi sannan kowa ya koma gefe yayi duru duru suna kallon kallo wannan yana faɗin kaine ka daketa a makasa wannsn yana faɗin aa kaine, baffane ya ƙuta yace “yo ba gwara a kashetan ba a huta da wannan abin kunyar da ta janyo mamu, wai ni Arɗo Jibo nine Kaɗo ya iya tarar cikin idona yace yanason irin mutum daga gareni wannan wanne irin tozarci ne Jiddoh tajamin a duniya”……………

Kuka sosai Baffa yakeyi yana kwaso kwashewar albarkar duniya yana jibgawa Jiddoh dake kwance a qasa magashiyan rai a hannun Allah.

Goggo dake bayan danga tana hangen halin da ƴqr tata take ciki ta share hawaye ta koma ta zauna tana tunanin ko meye yasa baffa yake tsangwamar ɗiyar tata tilo wadda duk cikin ƴaƴansa babu meyi masa biyayya kamarta.

Allah ya sani har ranta itama bataji zata iya bawa kaɗo auren ɗaya ɗayar ɗiyar tata ba amma wannan dukan yayi yawa dole ne tasan abinyi saboda ta lura rayuwar Jiddoh ake nema a rugar tasu, da wanne zataji da auren dolen da ake shirin yi mata da ɗan shaye shaye ko kuwa da mangarin da akeyi mata ko kuwa da mugayen alkaba’ain da akeyi mata?

Bata koma cikin gdanba saida kowa ya fashe sannan ta shiga ta tarar da jummai akan Jiddoh tanayi mata surkullensu na fulani tana shafa mata ruwa a fuskarta.

Miƙa tayi tare da jan zuciya suka miƙar da ita zaune ta zauna tana bude idonta daya kumbura saboda bugu tana kallonsu gwaggo da Inna Jumme tana matsar kwallah ta buɗe bakinta daqyar tace.

“Meye nayiwa Su Moddibo da Arɗo suke buguna wlh bansan komai da nayi musu ba wayyoh bayana Gwaggo wayyoh ƙuguna zani mutu wayyoh kaico….” tana mgnr ne cikin zubar hawaye kamata sukayi suka shiga da ita bukkarsu Inna Jumme ta ɗora sanwar ruwan zafi ta dawo ta zauna kusa da ita tace.

“Kema Jiddoh bakyaji kinsani cewa a wannan rugar tamu bamu bawa kaɗo aure meye yakaiki soyayya da kaɗo kaɗon ma maƙiyi irin jinin sarkin noma Mudansir na alƙalawa kinsan har abada babu jituwa tsakaninmu da irin sarkin noma nikam saidai hande jiddoh wai har kika turoshi shikuma ya ɗauko tsayi kamar daren mutuwa yazo wai yana neman izinin aurenki”

Kallonsu takeyi da rashin fahimta tace “ni bani bace ɓatan burtali yayi ya shigo jejinmu amma ni ban saneshi ba aradun Allah…”

Buge mata baki tayi tace “kusun uwarki ya kawoshi bakece kika faɗi mashi sunanki Hauwa ba yar gidar Arɗo jibo ko kuwa ƙarya yayi miki to nidai shawari zan baki in kinƙi kisha wahala garama ki nemai inda kuke haɗuwa ki hwaɗi masa yabi tsawanyarsa daban kibi taki saboda mudai ko mazan rugarmu sun qare bamu daukan subarjo kamarki mu bawa kaɗo kaɗon ma jinin Sarkin noma”

Miƙewa Inna jumme tayi taje ta juye ruwan zafin ta surka tazo ta kamata ta kaita makewayi ta rinƙa gasa mata jiki ita kuma tana kuka tana ciccijewa tana rufe ƙirjinta a cewarta da tsirarar  nono gara ta gindi.🙈

__________Shigar dare Lameer yayi cikin garin saboda yana tafiya yana hutawa kasantuwar irin suyar da zuciyarsa takeyi masa tunda yake a rayuwarsa bai taba ganin wulaƙanci irin wanda yau ya fuskanta a rugar sambajo ba.

Ikon Allah ne kawai ya kawoshi gdan yana shiga baibi takan komai ba ya haye samansa ya cire kayansa ya faɗa bathroom  ya sakarwa kansa ruwan sanyi duk da sanyin damunar da yake garin badon komai ba saidon ya samu sauqin abinda yake masa tuƙuƙi a ƙalbinsa amma ina kamar turi ma haka yaji.

Fitowa yayi ya zauna a saman resting chair din ya dafe kansa yana furzar da iska me zafi cikin ƙunar zuciya, zabura yayi ya miƙe ya fara safa da marwa yana tunanin mataki na gaba maganganun Arɗo Jibo suna dawo masa inda  yake cewa “kai kaɗo dubeni nan ni ba ɗan iska bane mu ba asararru bane ba rakiya mukayowa bayin Allah duniya ba idanma kana tunanin haɗa zuri’a dani to ka daina aradun Allah dana baka auren ɗiyata Jiddoh ƙwamma ni tsireta na cinye namanta”

 wannan Kalami sun daki zuciyar Lameer fiye da dukan dorina sosai suke zaga masa a kwanyarsa kuma suka sashi cikin tunani da son sanin meye dalilin da yasa Arɗo Jibo yayi wannan furucin tare da ƙara ɗaura ɗambar neman auren Jiddoh.

“Kuma munyiwa Jiddoh miji dama mun daɗe da samun lbrn kaine kake hure mata kunne har kanayi mata juyen nono kana janta ku shiga duhun dawa kasata ta fito innininta ta baka kasha…” “meye innini ya tambayi kansa tare da miƙewa ya buɗe ƙofar ya shiga kitchen ɗin dake saman ya dafa tea ya dawo parlourn nasa ya zauna ya tusa kofin a gaba ya kasa shan ko kurɓa daya saboda Hauwah kawai yake gani a idonsa dukan kansa yayi tare da tambayar kansa wai yaushe ya shiga wannan cakwakiyar rayuwar ne wacce ƙaddara ta kaishi Alƙalawa har ya ƙarasa Rugar Sambajo ya haɗu da Jiddoh ya fara yimata wannan son na mutuwa da rayuwa…………….

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels

Copyright 

If you are the right owner of this novel and you want us to remove it from our site please mail Us at aihausanovels@gmail.com

Back to top button