Hausa novels

Asanadin Makwabtaka Book 2 Page 64 Complete Novel

*ASM Bk2064*

 

_Destiny may be delayed but cannot be changed…._

 

 

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

 

 

 

……….tana shiga tace mata ya tafi ta d’aga mata kai kafin tace eh a hankali , a inda ta tashi ta koma ta zauna Hajiya ta fara magana “irin nuna kulawa haka yana k’ara dank’on k’auna tsakanin ma’aurata, yanzu kinga kece abu na k’arshe da ya gani kafin ya fita to zaki ga kin tsaya mashi a ran shi yana tafiya yana tunanin ki har ma kiga yana d’an murmushi kaman ta6a66e, ba kamar yadda kika ci gayun nan” Dariya Fatuu ta saki ba kaman da tace kaman ta6a66e ta bata dariya sai Maganar ta tuno mata da Maganar Aunty Mareeya, itama hajiyar Dariyar take taci gaba “naji dad’i dana gan ki haka tsaf kin sha gayu wannan ma zai taimaka wurin siye zuciyar shi don shi mutum ne mai tsananin son tsafta nasan kin san da hakan, ga son k’amshi don haka ki dage da tsafta, amman fa kuma kar tay yawan da zaki janye man hankalin shi gaba d’aya” ta d’an ta6e baki, sosae Fatuu ta saka dariya, cigaba tay bayan ta d’an murmusa,

 

“Komai nashi Sak kakan shi wllh, yana tuna man dashi a koda yaushe shiyasa bazan 6oye ba a duk jikokina nafi jin shi a raina kowa ma ya sani, hatta y’ay’an cikina ban jin su kaman yadda nake jin shi, Duk irin halayen shi na kakan shi ne, koda ake ganin Sojoji kaman basu da kirki basu da tausayi ba haka bane kowa da irin halin shi kaman dae a sauran mutane…..” D’an dakatawa tay tana kallon hoton Gen. Adamu Zakee dake a jikin bango cikin shiga ta Alfarma, da gani akwae k’auna mai k’arfi a tsakanin su kuma rashin shi ba k’aramin ta6a mata zuciya yay ba,

 

“Shima haka yake da son K’amshi, ko 6ata mashi rai kikai in dae zaki je bashi hak’uri ya kasance kina sakin k’amshi to Magana ta k’are tuni zai yafe maki, koda ma ba ke kika 6ata ran ba in dae zaki rarrashe shi kina k’amshi yanzu ya saukko” idonta akan hoton take Maganar, tausayin ta ne ya kama Fatuu itama ta kai idon ta kan hoton ta d’an girgiza kai, bayan d’an wani lokaci Hajiya ta sauke idon ta tare da ajiyar zuciya, kallon ta Fatuu tay da d’an murmushi tace “Allah ubangiji ya jik’an shi da rahama yasa ya huta, Allah ya h….had’a ku a Aljanna” tana murmushi ta amsa da Amin sai kuma tace “muci gaba da soyewa acan ko?” Dariya Fatuu tay suka d’an yi shiru, can ta kalle ta tace bari taje wurin Aunty Saude ta taya ta aiki,

 

“to ke waya fad’a maki Amarya na wani aiki, ki zaman ki ki huta, ki k’yale ta tayi aikin ta lokacin yin aikin zai zo sai kita yi” shiru tay ta maida kanta k’asa, “in kina son zuwa kije k’yama k’ara koyon wasu abubuwan tunda Saude ba daga baya ba wurin iya girki tasan hannun ta, sai ki dage ki k’ara koya duk da ma Mijin naki ba gwanin cin Abinci bane, amman k’ilan ya rink’a cin na Matan shi” tana d’an murmushi ta mik’e zata tafi, har ta juya Hajiya ta dakatar da ita, “Yauwa na tuna, Maganar gyaran part d’in naku Tukur ne ke yi, to tun kafin ki tare yayi man magana kan zai cigaba ne ko a’a nace ya bari ki zo duk da dai shi Namiji ne ina ganin baida Matsala, amman ke ya kike so” d’an jimm Fatun tay ta rasa mi zata ce Hajiyan tace ta bud’e baki tay magana, a sanyaye tace duk yadda ta yanke yayi,

 

“Shi d’in ne ya nuna yana so, tun farko ma ni ba shi naso yayi aikin ba bayan Haisam d’in ya dawo sawa nayi ya nemo wani amman ya matsa, kwanaki har zaunar dashi nayi nai mashi Magana kan hakan tunda ko ni bai bari akai kayana wurin wanki ga Karatu lokacin amman sai cewa yay wai baida abunda zai saka mana sai dai hakan kawai, nace to mu duk abunda ya ga an yi masa ai don Allah ne ba wai don ya saka mana ba, dama can Allah ya k’addaro akwae rabon shi a tare da mu” ta k’arasa tana murmushi itama Fatun shi take yi, “Yanzu tunda naga ya nuna yana so ke ki rink’a gyara Bedroom da Kitchen ala bashshi shi sai ya rink’a gyara maki parlon tunda dama yana da girma ko in kin tafi Makaranta sai ya shiga ya gyara, Wankin k’ananun kayan mijin naki kuma kyaci gaba in zai mashi na manyan kaya sai yazo nan yay amfani da injin d’in nan, koma kawae bari na mashi magana tunda ga naki sun k’aru ya bari a rink’a kaiwa dry cleaning kawai”, kallon Fatun tay “lafiya lou zaki rink’a gyara Bedroom d’in da Kitchen d’in ba takura tunda naga karatu kike?” Da sauri tace mata eh, a ranta ta raya ita da ke yin fin wannan aikin a gida wannan ai ba wani aiki bane, ce mata tay taje tayi mata godiya ta juya ta fita, Kitchen ta nufa a ciki ta iske Saude na shirye shiryen d’aura girkin rana, da yar sallama ta shiga ta juyo tana murmushi ta amsa mata ta nufi gefenta gaban drawer ta jingina fuskar ta da murmushi tace “Sannu da aiki Aunty Saude”,

 

“Yauwa Amaryar mu kun shigo” kai ta d’aga mata suka d’an yi shiru,

 

“Aunty Saude aiki na zo taya ki” d’an waro ido tay “aiki kuma Fateema keda kike Amarya, ki rufa man Asiri kar nayi laifi” tana murmushi tace “kai Aunty Saude daga taya aiki sai yin laifi ai na fad’i ma Hajiya zan zo in taya kin” tace “to amman ai ina iya yin laifi wurin Angon naki yaga duka daga kawo mashi Amaryar shi jiya yanzu na saka ta aiki” d’an tura mata baki tay tana murmushi “Kai Aunty Saude shi ina ruwan shi kuma ma ai ya fita bai gidan”

 

“Ya kamata dai kije ki huta don kina buk’atar shi ansha hidima” still tura bakin ta k’ara tana kallon ta itama Sauden kallon ta tay tana yar dariya, Fatuu tace “ni dae na huta har na gaji ma” kafewa tay kan sai ta taya ta aikin girkin tace ai ta k’ara koya ma Sauden tace shikenan tunda ta kafe,

 

“Mi kike so a dafa tunda ban kaiga d’aura komai ba sai ayi gaba d’aya kawai” d’an bud’a ido tay alamar mamaki tace “Aunty Saude ni zan fad’i mi za’a dafa” yar dariya tayi “Eh mana ki fad’i abunda kike so a dafa maku keda Angon naki” d’an jim tay ta maida idon ta k’asa alamar kunya, ganin ta tsaya tana kallon ta alamar amsa take jira yasa ta d’ago tana d’an far far da ido tace “Aunty Saude kiyi abunda kikai niyya kawai” tace “to ko shi ki fad’i abunda yake so sai ayi” d’an jimm ta k’ara yi sai kuma tace “to ai kin fi ni sanin abunda yake so ni dai kawai nasan bai son tuwo da miyan yauk’i”

 

“Eh bai cin tuwon masara ko dawa da miyar yauk’i sai na shinkafa da yake yana son Abinci irin haka su sakwara har teba ma yana ci” Fatuu dake kallon ta tace “to ko ayi ebar?” Dariya tay “haba Fateema ya za’a had’a ango da teba kuma” itama Fatun dariyar tay bata ma san ya akai ta furta hakan ba, “ina ganin ko ayi sakwara don gaskiya yana son ta” Saude ta fad’a, da d’an sauri ta d’aga kai tace to ayi, amsar gyalenta tayi ta kai mata d’akinta bayan ta dawo suka fara aikin Pounded Yam d’in ba 6ata lokaci, Fatuu na tsaye tana yanka su alaiyyahu da Albasa harda ganyen ugu tace “Aunty Saude wai sai yaushe zaki tare?” tana juya miya tay yar dariya “ai na riga na tare Fateema” da alamun mamaki “kin tare, amman kuma yanzu ba d’akin ki na cikin nan kika kai man gyale na ba?”

 

“Eh ai ban bar d’akin ba har yanzu matsayin nawa yake inna shigo ina aiki kinga ba sai nata zarya zuwa baya ba, kuma ma in ya tafi garin su wurin d’ayar matar shi a nan zan cigaba da kwana” kai Fatun ta d’aga alamar gamsuwa sai kuma tace “Amman Aunty Saude tarewa ba sanarwa balle ai mana d’an shagali” tana yar dariya ta k’arasa, itama dariyar tayi “Kai Fateema har kin bani dariya wane shagali kuma tsofe tsofe dani wannan ai sai ku, kema kawai nasan don ga yadda Al’amarin ya kasance ne da ba k’aramin shagali za’ai ba duk da haka kina iya ganin anyi daga baya” murmushi kawai Fatun tay tana fad’in ba wani tsufan da tayi wllh ai da ko yar Walima an yi masu, Sauden tace Hajiya ma taso tayi itace ta nuna bata so, cigaba da aikin sukai har Sauden na tambayar Fatuu turaren da ta shafa k’amshin yayi mata dad’i in ba tsada zata siya irin shi tace mata ai Humra ce duk da ta shafa turaren kad’an amman dai k’amshin na Humra ne, ta fad’i mata wadda ta siyo mata tace aikuwa tana so gaskiya zata bada a siyo mata Fatun tace ta bari zata d’ibo mata, nan fa suka hau yin yar jayayya Saude na fad’in a’a karta kwashe abunta ta bari a siyo mata kawai tace to ai kafin a siyo mata sai ta fara amfani da wadda zata batan tunda akwai da yawa, basu d’au wani lokaci mai tsawo ba suka gama had’a komai saura k’arashe, bayan an kwashe Fatuu tace bari ta nik’a cikin Food processor Sauden tace ta bari ta daka a turmi tafi dad’i Hajiya ma tafi son a daka, bayan ta fiddo turmin ta wanke ta fara d’akan sakwara Fatuu ta kafe kan sai itama ta daka farko Sauden ta k’i bata k’arshe da ta matsa ta bata tana faman fad’in tabi a Hankali don Allah kada tsautsayin Amarci ya gifta Fatun sai dariya take, kan kace mi daddad’an k’amshi ya karad’e Kitchen d’in har cikin Parlor, bayan an kammala hada miyan egusi da ta sha ganye ga ganda da kuma nama tayi wani irin kitif bata ko juya jikinta sai an juya ta, a tare suka nannad’a sakwarar a farar leda, bayan sun gama a wasu jigunannun luxury Warmers aka zuba tasu Fatun,

 

“Ban taho da Warmers d’in jiya da kuma kayan breakfast d’in da aka kai yau ba da yake duk akwae sauran Abinci na saka a fridge, sai dai inna koma sai in kawo ko Almajirai in suna zuwa sai a basu kada ya lalace” Fatuu tayi Maganar tana kallon Saude, tace “ai Almajiran ma sun zo tun d’azu da safe na tattara masu wanda za’a basu, amman Abincin nada yawa ne?” d’an jimm Fatuu tay alamar tunani “Eh gaskiya da d’an yawa don na jiyan bamu ci sosae ba sai breakfast d’in yau shima bread d’in da saura sosae sai itama kazar wurin rabi ce don shi cinya kawae yaci ma sai chips d’in shima ba sosae ba” Jinjina kai Saude tay sai kuma tace “amman mi zai hana ki aika dasu gida kawae kinga itama gwaggo ta huta da yin girki tunda daga ita sai Amadu” d’an waro ido Fatuu tay “Aunty Saude in aika dasu gida kuma, in aka gani fa zai zama kaman fa nayi rashin gaskiya ne”, yar dariya tay ganin yanayin fuskar fatun tace “to miye abun rashin gaskiya fita da Abinci gidan nan ai ba wani abu bane, kullum cikin fita ake dashi ba wanda zai maida kai ya ga kinyi wani rashin gaskiya” shiru tay kaman tana nazarin Maganar tata can ta kalleta “amman Aunty Saude ba ance ba kyau ka d’auki abinci bada izini ba ka bayar” Saude ta fahimci abunda take nufi wato bada izinin miji ba tace “Wannan ai ana nufin d’anyen Abinci Fateema, amman dafaffe ba laifi in ka bada gudun kada ya lalace ya zama anyi Almubazzaranci kuma kai laifi” d’an gyad’a kai tay alamar ta fahimta, saida suka had’a kunun Aya mai shegen dad’i kafin a tare suka kai wanda za a kai dining table, bayan sun gama Fatuu cikin d’an jin kunya tace mata bari taje tana son tayi wanka Saude na dariya tace ai haka yakamata, da kanta taje d’akinta ta d’aukko gyalenta bayan ta fito ta shiga Bedroom d’in Hajiya don yi mata sallama, bayan ta shiga ta iske ta kwance akan gado tana bacci hakan yasa ta juya zata tafi sai kuma taji muryarta ta kira sunanta ta juyo ta ga ta d’ago da kanta tana kallonta, nufar gadon tay tana niyyar duk’awa kan Carpet da hannu tay mata alamun ta zauna a bakin gadon, cikin Muryar wanda ya tashi daga bacci tace “Bacci ne ya d’auke ni halan Azahar ma tayi tuni?” tace “A’a an dai fara kiran sallar” ta fad’a tana d’an kallon gefe, jinjina kai tay suka d’an yi shiru sai kuma ta sake cewa”har an gama aikin girkin ne” kai ta d’aga “Eh mun gama zan koma can ne” kanta a k’asa tay Maganar, “Ok, sai ki tafin maku da naku ma” amsawa tay da to tana k’ok’arin mik’ewa Hajiya ta dakatar da ita da fad’in “kinga na manta jiya nace zan sa a kirawo balaraba tay maki kitso ko a bari sai yamma kawai” shiru Fatun tay kanta a sadde tana d’an wasa da yatsun hannunta, ganin bata ce komai ba yasa Hajiya tambayar ko bata son kitson ne ta d’ago ta d’an kalleta fuskar ta da d’an murmushi ta d’aga mata kai alamar eh, yar harara Hajiya ta wurga mata “ashe har yanzu halin ki na rashin son kitso na nan Fateema?” Shiru bata ce komai ba Hajiya tace “yanzu in baki yin kitson zaki takura ne, in gayun Amarci kike son kiyi na k’yale ki aita gayu lafiya, amman dole ki rink’a yin kitso, amsa mata tayi da to a kunya ce tace mata taje ta mik’e tay mata sallama.

 

Bayan ta fito Kitchen ta nufa don ta d’aukko Basket d’in Abincin su ta taras da Saude na gyara Kitchen d’in, bayan ta d’aukka tay mata sallama ta fito, tana isa part d’in nasu bayan ta shiga parlon ta nufi Dining Area, a saman table ta d’aura Basket d’in ta shiga fiddo da warmers d’in tana jerawa, bayan ta gama d’aukar Basket d’in tay ta wuce Kitchen don ta aje, tsaye tay a gaban drawer bayan ta aje ta shiga tunanin Maganar Aunty Saude tana wasi wasin ta aikata yadda tace ko a’a, can ta yanke yin yadda tace d’in ta bud’e fridge ta fiddo sauran Kazar da Abincin jiya ta fara k’ok’arin dumama su a cikin Oven, bayan ta gama ta d’aukko kwalin Warmers masu kyau ta bud’e, mai d’an girma a ciki ta d’auka bayan ta wanke ta juye Abincin, sake d’aukko wata tayi itama bayan ta wanke ta juye Kazar, shiru ta d’an yi tana tunanin yakamata ta samu leda ta saka su ba ta aika dasu haka ba can ta tuno da ledar kayan baccin da Aunty Mareeya ta bata tana da girma Warmers d’in zasu shiga ciki, da sauri ta juya ta fita ta nufi Bedroom, bada jimawa ba ta dawo ruk’e da ledar ta fara saka Warmers d’in ciki hannun ta har d’an rawa yake, gaba d’aya sun shiga harda sauran wuri ma nan ta tuno dasu Snacks da ice cream d’in dake a Fridge d’in parlor ta juya da sauri ta fita daga cikin Kitchen d’in, d’ebo su tay ta saka harda robobin yoghurt da ice cream guda guda, bayan ta had’a komai tay tunanin kiran kawu Amadu don ya turo mata yaro da sauri ta juya ta fito ta shiga Bedroom, Wayar ta ta d’aukka ta kira shi yana d’agawa tunkan tayi magana yace mata miye kuma, yar dariya tay tace ba komai don Allah yaro take son in akwae wanda yazo siyayya ya turo mata shi yace to, aje wayar tayi ta juya ta fita tay tsaye bakin corridor tana dakon isowar wanda za’a turon, bada Jimawa ba akai knocking da sauri ta nufi kopar ta bud’e, wani yaro ne d’an unguwar ya turo tana ganin shi tace mashi tana zuwa ta juyo, ledar ta d’aukko harda dublan ta d’ebo mashi bayan ta kawo tace gwaggo zai kai mawa ta bashi ta dublan d’in tace gashinan ya ci yana washe baki yay mata godiya da Allah yasa Alkhairi ta amsa, juyawa tay da sauri ta koma Bedroom ta nufi gaban mirror bayan ta cire su sark’a da yankunnan ta ta cire kayan jikinta ta d’aura towel ta nufi laundry room, after some minutes ta fito jikinta sanye da bathrobe da ta gan su cikin cabinet d’in laudary ta d’auka, bayan ta fito doguwar riga tasa da hijab ta shimfid’a abun salla ta kabbara sallar Azahar da har angama ta a Masallacin gidan, bayan ta gama ta cire kayan ta linke da abun sallan ta maida kowanne wurin shi ta d’auki towel ta d’aura sannan ta nufi gaban mirror ta fara shafa, tana cikin yi wayarta ta fara ringing ta nufi gefen gado ta d’auka har saida gabanta ya fad’i ganin gwaggo ce mai kiran, bayan tayi picking ta gaidata nan tace mata mi ta aikata haka da sauri ta tari numfashin ta ba kamar yadda taji tayi Maganar cikin yar rawar murya ta fad’i mata duk yadda sukai da Saude, yar ajiyar zuciya ta sauke tace mata duk da haka yayi wuri da yawa ta fara hakan tace to zata kiyaye daga baya sukai sallama, bayan ta gama shafe shafen da goge gogen ta nufi wurin jakunkunan kayanta ta duk’a, tunanin kayan da yakamata tasa ta shiga yi, tana son saka k’ananun kaya don ko a gida tafi saka su ba kamar in ba inda zata je saidae tana gudun yay wani tunanin na daban, d’aya daga cikin Akwatunan kayan ta na gida ta bud’e ta fara ruwan ido can dae ta fiddo wata fitted gown d’in lace yellow da touches d’in dark ash bayan ta rufe akwatin ta bud’e na Undies ta d’auki wanda zatai amfani dasu, bakin gado ta nufa ta fara k’ok’arin sakawa bayan ta gama ta koma gaban mirror tana k’ara gyara kwalliyar da tayi yar light, sosae rigar ta amshe ta dama ita duk kayanta suna amsar jikinta Saboda irin d’inkin da ake yi mata dake fiddo dirin ta sosae, irin d’aurin kallabin d’azun tayi ta k’ara zubo da gashin gaba can kuma sai ta raba gashin na 6arin hagu ta maida shi baya na 6arin dama ta barshi a gaba, sosae hakan da tayi ya k’ara mata kyau sai kace wadda zata gasar kyau, bayan ta feshe jikinta da turare ta gyara komai ta maida bathrobe d’in, a gefen gado ta zauna ta fara tunanin ko akwae abunda yakamata tayi can ta mik’e ta nufi dressing mirror ta d’aukki robar Air Freshener ta shiga feshe Bedroom d’in Bayan ta gama ta juya ta nufi kopar fita, parlor tazo nan ma ta shiga feshe ko ina tana haka taji an turo kopar parlon ta kai idanun ta da sauri, Haisam ne ya shigo shima da alama wanka yayi don ya canza kaya zuwa farin jeans sai yellow polo shirt daga jikin tsayayyar collar d’in akwae ratsin fari haka a k’asan hannuwan ma sannan daga gaba 6angaren dama akwae farin tambarin polo d’in, yadda yasa Yellow d’in riga abun kaman had’in baki da itama tasa kaya Yellow, Cikin parlon ya shigo ya nufi inda ya saba zama ya zauna, slowly ta nufi inda yake hannunta ruk’e da robar freshener d’in, daga d’an gefe ta tsaya tayi mashi sannu da zuwa ya jinjina mata kai tay tsaye suka bi juna da ido tana d’an motsa baki, “Ya gida?” taji ya tambaya har saida taji mamakin tambayar ganin ya kafe ta da ido fuska a sake yasa ta yin d’an murmushi tace mashi lafiya lau ya d’aga kai,

 

“Sit” ganin tana ta tsayuwa yasa shi ce mata haka, zama tay a bangaren inda take shiru ta biyo baya da d’an murmushi take kallon shi tana yi tana maida idanun k’asa, “Kin yi kyau” kaman daga sama taji Maganar ta kalle shi had’i da d’an waro ido mamaki kwance akan fuskar tata, ya fahimci hakan sai kawai yay d’an guntun murmushin gefe idon shi a Kanta ya maida bayan shi ya jingina da jikin kujerar, Maganar sai ta tuno mashi da Fanan ita ta koya mashi cewa hakan duk in tayi kwalliya bai yaba ba sai tay ta k’orafi daga nan ya fahimci mata basu son suyi kwalliya a k’i yabawa, da k’yar ta furta mashi ta gode bai ce mata komae ba sai ma ya maida idanun shi kan wayar shi dake a hannun shi ya fara latsa ta, “k..Kai ma kayi kyau” da k’yar ta tattaro kalmomin muryar ta na d’an rawa ta furta mashi, shiru kaman ba zai ce komai ba can taga yay mata kallon k’asan ido fuskar shi a sake ya furta thanks kafin ya maida idon kan Screen, bin shi da ido tay ta ayyana sam baka ta6a gane mashi, tana cikin kallon shi ya d’ago suka had’a ido, d’age mata gira yay ya tambayi da wani abu da sauri ta girgiza mashi kai sai kuma tace ga Abinci can kan table ya jinjina kai, saida ya d’an k’ara lallatsa wayar kafin ya aje ta a gefe ya mik’e ganin haka yasa itama ta mik’e ta bi bayan shi, Kitchen ta wuce anan ta aje Freshener d’in ta wanke hannuwan ta sannan ta d’auki duk abunda zata buk’ata na cin Abinci ta fita, bayan ta iso dining d’in ta fara zuba mashi tana sa sakwara guda d’aya ya d’aga mata hannu alamar ta isa kawai sai gani yay ta k’ara d’aukko guda ya d’ago ya kalleta ta d’an tura baki ta fara k’unk’uni a shagwa6e tace “ya za’ai abu d’aya ya ishe ka” wani kalan kallo ya ke bin ta da shi ya d’an d’age gira,

 

“Ba zai isheka ka k’oshi ba sai dae ko biyu” tana gama Maganar ta k’ara mashi d’ayar tana yi tana kallon shi, yanayin fuskar shi ne ya sauya taga kaman ya d’aureta ta fara d’an kikkafta idanu a marairaice tace “har yanzu fa in baka cin Abinci sosae Ulcer zai iya kama ka” still yay yana bin ta da ido without saying anything, jikinta ne yay sanyi ta kai hannu da niyyar ta cire wadda ta k’aran taji yace “in ya kama ni I have got married now” da sauri ta kalle shi taga ya d’an d’age mata gira kuma ya saki fuskar lokaci guda ta saki murmushi jin bai manta da Maganar data ta6a yi mashi ba, bayan ta gama serving nashi itama ta zuba ta fara ci tana yi tana satar kallon shi yana cin nashi a nutse, sunyi nisa da farawa ta dakata idon ta a kan shi tana d’an murmushi slowly ya d’aga ido ya kalleta don yaji kallon shi take, “ya yi dad’i Abincin?” ta tambaya, bai bata amsa ba ya maida idon shi kan Abincin, saida ya k’ara ci sannan taji yace miye na tambaya tunda ba ita tayi ba, a hak’ik’an ce tace ai tare fa suka yi kuma ko ita kad’ai zata iya yin shi, d’an guntun murmushi kawae yay yaci gaba da ci, sai ga shi ya take duka sakwarar cikin wasa ta tambayi ta k’ara mashi ya d’an wurga mata harara, bayan ya sha kunun ayar ya yago tissue ya goge mouth d’in sa sannan ya mik’e zai bar wurin idon Fatuu a kan shi, dakatawa yay ya kalleta suka had’a ido Slowly taji ya furta “the empty plate is ur answer for d question u asked” daga haka ya juya yana tafiyar shi ya nufi cikin parlon tabi bayan shi da kallo tana Murmushi shi komai nashi na daban ne, saida taci ta k’oshi don ita kanta Abincin yayi mata dad’i sosae, bayan ta gama ta fara kwashe kayan da sukai amfani ta kai Kitchen, saida ta gyara Dining table d’in sannan ta koma Kitchen ta wanke komae da suka 6ata ta maida shi a wurin shi, bayan ta gama har zata fita idanunta suka sauka akan bokitan su cin cin a ranta ta raya tunda aka yi su bata ci ba wata zuciyar ta ayyana shi k’ilan ma baya cin su, tunanin ta d’iba ta kai mashi taga in yana ci tay ta d’aukko plate mai kyau ta bud’e ta d’ebo kowanne bada yawa ba harda alkaki, bayan ta zuba ta nufi hanyar fita yana kishingid’e kan kujera idon shi akan Tv yana kallon American film ta nufo shi tana tafiya a nutse sai kace mai yin yanga, tunda ta tunkaro cikin parlon ya maida idanun shi kanta har ta k’araso ta d’aura plate d’in kan c-table ta k’ara matsar dashi kusa dashi ta d’ago tana murmushi suka had’a ido tace mashi gashi nan ya ci, maida idon yay kan abunda take maganan kafin ya d’ago ya kalleta tana tsaye still Murmushin take tana d’an wasa da yatsun hannunta da ta had’e, ji tay yace a ina zai saka wannan d’in da sigar shagwa6a tace ai su ba Abinci bane,

 

“Who told u ba Abinci bane, yanzu kaci wannan kasha ruwa bazaka k’oshi ba?” Ya tambaya had’i da d’age gira, d’an tura baki tay “Ya za’ai su kosar da Mutum, saidae in da yawa aka ci kuma ai kai kad’an ne na kawo maka ko” tana Maganar ya kafe bakinta da kallo, sigh yay ya d’an shaking kan shi “bansan ina zan sa shi ba as am stuffed, I couldn’t eat another bite” bin juna sukai da kallo na d’an wani lokaci can ta kai hannu a sanyaye ta d’auki plate tana shirin juyawa taji yace zai ci wani lokacin ta juyo suka had’a ido ya d’an bud’a mata ido alamar taji abunda yace ta d’aga mashi kai daga haka ta wuce ya bita da kallo, bayan ta maida su ta fito ta wuce Bedroom, bada jimawa ba ta fito hannunta ruk’e da laptop d’inta da babban hardcover ta nufo cikin parlon ya maido idon shi kanta, a gefen shi ta tsaya a d’an marairaice tace “please, could you help me with this Assignment, ta email malamin yace mu tura mashi gashi harda drawing nayi k’ok’arin in d’aukko in saka na kasa” shiru yay just staring at her har saida tasha jinin jikinta ta d’an juyar da fuskar ta, tana haka taji cool voice d’in shi yace ta kawo ya gani ta matsa, akan c-table ta d’aura ta shiga nuna mashi yadda Assignment d’in yake bayan ta gama ta d’ago ya kai hannu ya fara latsa Computer din, can bayan d’an wani lokaci ya d’ago suka had’a ido yace mata sai ya d’aukko abu a G.r.a za’a iya tura mashi zuwa dare zai nuna mata, murmushi ta shiga yi tayi mashi godiya bai ce mata komai ba ya koma ya jingina bayan shi jikin kujerar, hannu ta kai zata d’auki laptop d’in slowly taji yace an hana ta zama a parlor ne, kallon shi ta d’an yi still da murmushi ta fasa d’aukar laptop da littafin ta koma d’ayan side d’in kujeran ta zauna, remote ya d’auka ya canza daga channel d’in da yake kallo zuwa Arewa 24 lokacin suna cikin yin maimaicin shirin dad’in kowa da yake k’arfe ukku yayi, d’an juyawa tay ta kalle shi ta d’an yamutsa baki nan take ya gane mi hakan ke nufi ya k’ara canza channel zuwa tauraruwa ganin suna yin wak’ok’i yasa ta d’an yi murmushi, voice d’in shi taji yana tambayar yayi mata ta juya ta d’aga mashi kai ya aje remote d’in dama ta dalilin ta ya san channels d’in hausa, tana kallon wakokin tana d’an bi wani lokacin har d’an juya kai take akwae wata da ya lura tana mata dad’i don sosae take bin wak’ar tana juya kai, still yay yana ta kallon ta kai kace ita ta raira wak’ar saidae kuma kunnan shi na akan wak’ar yana sauraro can kaman taji kallon ta yake ta juya suka had’a ido yar dariya tayi mashi shi kuma ya d’an yi mata guntun murmushi, ana yin wakokin kaman guda biyar suka datse suka sako tallar magunguna, juyowa tay tace mashi ya maida channel d’in da yake kallo sun gama fuskar shi a sake kaman zai murmushi ya kalle ta, tambayar ta yay ba wani da ake irin shi, ta gane wakokin yake nufi tace mashi ko an canza ba lalle ana yi ba dama nan an fi sa su, shiru yay can ya kai hannu ya d’auki remote d’in ya canza channel d’in da yake kallo farko suka cigaba da kallon American film d’in tare, gaba d’aya Fatuu ta takura don sai yin abubuwan sa kunya suke, suna cikin kallon aka nuno jarumin Film d’in da budurwar shi suna romancing juna ji Fatuu tay kaman ta nutse a wurin don abun bana Arziki bane, can abun ya kai ga an sa6ule rigar budurwar har boobs d’inta sun bayyana Fatuu na ganin hakan ta mik’e zumbur ta nufi hanyar corridor without even looking at him ya bi bayanta da kallo shi sai ma ta so bashi dariya yadda tayi, tana shiga Bedroom d’in ta nufi gado ta zauna a baki ta d’an waro ido tay shiru kaman mai tunanin wani abu, a hankali ta kwanta ta takure a guri guda tana cigaba da tunanin da take yi, bata dad’e da kwanciyar ba aka kira sallar la’asar, har tayo Alwala ta zo ta kabbara sallar bai shigo ba, bayan ta gama zaune tay kan abun sallar ta jingina da gado tana haka taji wayar ta na ringing ta mik’e ta nufi bedside drawer inda wayar take ajiye, d’an jimm tay ganin shine ke kiran kafin ta d’auka a hankali tayi sallama amsa mata yay yace mata ya je ya dawo ta yi mashi adawo lpy, tambayar ta yay akwae abunda take so tace mashi a’a daga haka yay cutting kiran, bin wayar tay da kallo bayan ta cire ta daga kunnan ta a ranta ta shiga raya shi d’in ba dai kula ba duk zai fita sai ya tambayi ko tana son wani abu, d’an murmushi tay tana jin k’aunar shi na k’ara ninkuwa a cikin ranta, tunanin tafiya part d’in Hajiya tay ta taya Saude girkin dare tunda ko ta zauna ba abunda zata yi ta mik’e, bayan ta d’aukko gyale da takalma ta k’ara gyara fuskar ta a gaban mirror sannan ta tafi, saida ta tsaya Kitchen ta d’aukko wasu daga cikin kayan da aka kawo masu Abinci don ta maida sannan ta tafi, tare sukai aikin Abincin daren kaman da rana a nan tayi sallar Magrib da isha’i sannan ta baro part d’in tare da Abincin su ta dawo part d’in su har lokacin Haisam d’in bai dawo ba, bayan ta aje kayan Abincin kan table ta wuce Bedroom, har ta zauna bakin gado zata fara latsa wayar ta Zuciyar ta ta ayyana mata yakamata tayi wanka ta mik’e bayan ta aje wayar ta nufi gaban dressing mirror ta cire jewellery d’in jikinta ta maida komai ma’ajiyar shi sannan ta wuce laundry room, after some minutes ta fito sanye da bathrobe kanta ba kallabi sai short towel tana goge fuskar ta da gefen gashin ta, gaban dressing mirror ta tsaya ta shafa mai da su humra bayan ta gama ta wuce wurin kayanta a ranta ta ayyana yakamata ta jera kayan a cikin closet ta yanke gobe tunda ba Makaranta zata je ba tayi hakan, ruwan idon kayan da zata sa ta shiga yi daga k’arshe ta yanke ta saka sleeping dress kawai tunda dare ne kwanciya zatayi ta bud’e jakar da suke ta fiddo wasu riga da wando silk cikin wanda aka kai mata rigar gajeran hannu gare ta ta d’an saukko zata kai cinyoyin ta, gefen gado ta koma ta fara saka su ba tare da ta d’aukko undies ba tunda dare ne, gaban mirror ta koma ta k’ara gyara parking d’in gashinta, bayan ta gama ta maida su bathrobe d’in ta d’aukko phone d’inta ta haye gado ta fara latsa ta, bata dad’e da hawa ba taji an turo kopar da sauri ta kai idonta suka had’a ido dashi ya shigo da yar sallama tana d’an murmushi ta amsa mashi, a gaban gadon ya tsaya tayi mashi sannu da zuwa ya d’aga mata kai, mik’a mata ledar daya shigo da ita yay ta matso ta amsa tana kallon shi kafin ta maida kallon kan ledar shi kuma ya nufi gaban mirror ya fara cire Wrist watch d’in shi, bud’e ledar tay ta lek’a sai kuma ta kai hannu ta fara fiddo abubuwan dake ciki nan taga Pop corn ne da tuwan Madara harda gullisuwa sai Chocolates manya manya with surprise written on her face ta d’ago tana kallon shi don bata tsammaci ganin su ba tunda bata ce mashi tana so ba, hanyar laudary room ya nufa ba tare da ya kalle ta ba da d’an d’aga murya tace “Thank u so much, Allah ya k’ara bud’i na Alkhairi” d’an juyowa yay ya kalleta fuskar shi a sake ba tare da ya ce komae ba ya juya yaci gaba da tafiya har ya shige, tana ta sakin murmushi da alama taji dad’in kawo mata su da yay ta bud’e ledar tuwon madara ta fara sha nan take wani dad’i ya ratsa ta harda lumshe ido lokaci guda zuciyar ta ta tariyo mata can baya irin su ne kyauta ta farko da ya fara mata da hannun shi ta dingi zuba mashi santi harda bashi labarin irin Pop corn d’in da ake kawo masu a Makaranta duk tsakuwowi da gishiri don an raina masu wayau, tunowa da lokacin yasa tay ta dariya can tay tunanin yakamata ta bashi wuri tasan wanka yake in ya fito ya shirya ta saukko daga kan gadon ruk’e da ledar ta nufi hanyar fita, tana zaune a parlor tana cigaba da cin abubuwan ta tana yi tana kallon sabon shirin dad’in kowa ya fito shima ya shirya cikin sleeping dress riga da wando tun kafin ya k’arasa shigowa k’amshin shi ya karad’e parlon, tana ganin shi ta mik’e da hannu tay mashi alama da Dining area ya nufi can ta bi bayan shi, ba wani Abinci sosae yaci ba ya dawo cikin parlon, bayan ta gama ta gyare wurin ta had’o mashi Fruit salad, a kan c-table ta d’aura mashi tace gashi nan ya sha ya furta mata thanks tay d’an murmushi ta koma inda ta taso ta zauna taci gaba da kallon ta, bayan an gama ta juyo suka had’a ido lokacin har ya gama sha tay mashi d’an murmushi taji yace zasu iya yin Assignment d’in yanzu tace eh, bud’e Computer d’in yay dama tana nan ba’a d’auke ba ya fara operating nata tana ta kallon shi can taga yay mata alamar tazo da hannun shi ba tare daya d’ago ba ta mik’e ta nufe shi, a gefen shi ta ja ta tsaya ya k’ara mata alamar ta zauna a kusa da shi still bai kalleta ba, a d’arare kaman mai jin tsoro ta raku6a gefen nashi ta zauna ya shiga nuna mata yadda zatai, tun dai bata saki jiki ba har ta washe suka cigaba da yi har ta kai ya kama hannunta yana koya mata yadda zata d’aukko zanen, tuni jikin su ya had’e da na juna gaba d’aya sun cika juna da fitinannan k’amshi, ba’a d’au wani dogon lokaci ba suka gama har an tura ma malamin tana ta murmushin jin dad’i ta hau yi mashi godiya, d’an murmushi kawae yake ba tare daya ce komai ba ta mik’e ta kai hannu ta d’auki book d’in tana shirin juyawa ta tafi kwatsam tay tuntu6e da kafar shi ta tafi gaba d’aya zata kifa aikuwa cikin zafin nama ya jawo ta tayo baya ta fad’o jikin shi gaba d’aya, tsit kake ji Wutar Fatuu ta d’auke don ba k’aramar razana tayi ba gaba d’aya ta runtse idanunta gam jikinta sai d’an rawa yake tana fitar da numfashi da sauri da sauri, still yay yana bin fuskar ta da kallo ya kasa cewa wani abu idanunta sai rawa suke, bayan wani lokaci natsuwar ta ta daidai ta a hankali ta fara bud’e idanun ta, bayan ta ware su gaba d’aya suka sauka akan face d’in shi dake gab da ta ta, sam kowa ya kasa yin kwakkwaran motsi sunyi tsit gazing in to each other’s eye and inhaling each other’s sweet scent, Fatuu ce tay k’arfin halin ce mashi ta gode da taimaka da yay ta fara k’ok’arin d’agowa sai dae ta kasa don ya ruk’e ta tightly, slowly ya d’ago da fuskar ta ta yadda saura kad’an su had’e Fatuu na ganin haka da sauri ta runtse idonta breathing d’in su ya fara had’uwa zuciyarta ta fara beating da sauri da sauri, numfashin ta ne ya nemi tsayawa jin ya had’e bakunan su………

Asanadin Makwabtaka Book 2 Complete Novel Txt

Back to top button