Fentin Zina Page 15 Hausa Novel
******Adda kiyi tunani sosai kada ki fifita soyayyar wani can daban akan iyayen ki.Kinga fateema, Ameena tace da sanyin murya ni ban fifita Ahmad akan su inna ba amma kuma ina son shi wannan ai rashin adalci ne ma ace za’a tilastamun rabuwa dashi da inna zata san irin zafi da radadin dake zuciyata saboda soyayyar Ahmad data tausaya mun.Tabe baki fateema tayi ta mike tace na lura duk abunda za’a fada miki a yanzu bazaki fahimta ba, tana kaiwa nan tasa kai ta fice daga dakin.Sosai zazzabi ya rufeta kuma inna tana kallonta taki cewa komai don ba karamin bacin rai Ameena ta saka ta ba yau dole malam ya dawo su zauna ayiwa tubkar hanci.Da dare harta kwanta bacci ya soma fisganta ita kadai ce a dakin, fateema ta shigo ta tsaya daga bakin kofa tace adda baba malam yace kije.Ta fita, lallabawa tayi ta tashi zaune ta dau mayafinta ta saka ta mike ta fita.Zaune ta same su duka da baba malam da inna sai fateema data mike zata fita baba malam ya dakatar da ita ta hanyar cewa dawo ki zauna ina kuma zaki je.Ta juyo tace baba dama daki zanje.Dawo sai mun gama magana tukun ki wuce.Babu musu ta dawo ta zauna baba ya dubesu duka yace fateema kiyi mana addu’ah.Addu’ahr tayi kamar yadda ya bukata.Toh innal hamdulillah nahmaduhu wa nasta inuhu wa nastagfiruhu wana uzubillahi min shururi anfusina wamin sayyi ati a’amalina manyahdihillahu fa huwal muhtad wamanyudlil fala hadiyala ash-hadu anlailaha illallah wahadahu la sharikalahu wa ashhadu anna muhammadan abduhu wa rasuluhu anma ba’ad assalamu alaikum.Inna da fateema suka ce wa’alaikassalam.Ya sauke ajiyan zuciya sannan ya cigaba, makasudin dana bukaci ganinku a nan a wannan daren shine in tunatar damu wasu ababe guda biyu zuwa uku, na farko shine kuyi sani cewa Allah yana daurawa maigida hakkin kula da tarbiyyar gidansa daga kan mahaifiyar ku har abubakar zuwa Ameenatu da kuma ke fateema, dukkanku kiwone da Allah ya bani sannan zai tambayeni yadda na gudanar da kiwon shin na tarbiyyantar da iyalina bisa turbar addini ko kuwa banyi ba, wannan karon Ameena yake kallo yace Allah ya gani nayi iya kokarina na tsayu akan tarbiyyar ku na kuma yi kokarin ganin na sauke duk wasu hakkokin da suke naku dake kaina sai abu guda da ban cike ba shine aure wanda nike saka ran nan bada jimawa ba shima zan sauke ya zam babu hakkin daya rage mun a ka.Ameenatu, ta dago a kasalance ta dube shi bata iya magana ba don sosai take jin zazzabin jikin ta.Naji abunda ya faru da kuma ji abunda kika aikata mahaifiyarku ta sanar dani komai ina so kisan wani abu, shifa wannan yaron da yana da tarbiyya da addini da asali mai kyau ni Ibraheem bazan hanaki auren shi ba amma munyi bincike kuma binciken nan namu ya tabbatar mana da sabanin duk wadannan abubuwa dana lissafa wai shin meyasa kike son chanja kyawawan dabi’unki saboda saurayi? Banji dadin abunda kika aikata ba amma wannan karon umurni nike baki kada ki sake kula shi wanna yaron domin muddin ina da rai bazan taba aurar dake wa shi ba ina fatan kina jina.Ga mamakin su duka kuka ta fashe dashi ta matso ta kama kafar malam tana cewa baba dan Allah ka mun rai kada ka rabani da Ahmad wallahi karya ake masa kuma wallahi da gaske yake sona baba bazan iya rayuwa ba tare dashi ba ka taimake ni baba dan Allah kada ka rabani da shi.A kausashe baba malam yace ki bace mun da gani ko in daka ki anan mutumiyar banza kawai shashasha zaki bace ko yaya.Ta mike ta fita da gudu tana kuka, inna tace malam ai wannan yarinyar ta bada mamaki fiye da kima.Jinjina kai yayi tsabar kunar da yake ji a cikin zuciyarsa ya maida kallon shi kan fateema yace ki tabbatar kin samun ido akanta tunda soyayya ta makantar da ita daga gane alkibla, duk intayi yunkurin yin wani abu ki sanar dani kuma yanzu karbo mun wayarta ki kawomun na haramta mata rike waya har sai ranar da ta gane gaskiya koda wasa ban yadda ki ara mata taki ba idan ba haka ba zanyi hukuncin har dake ciko.Insha Allah babu abunda zai faru baba.Allah yasa Allah ya muku albarka, Ameen tace ta fita bata jima ba ta dawo rike da wayar Ameena ta mika mishi kana ta fita.Ya Kali inna yace kada yarinyar nan ta sake zuwa koda kofar gida ne ban amince ba.Insha Allah zan kiyaye hakan.Toh da kyau yace yana kwanciya kan gado.A daki kuwa kuka kawai Ameena keyi fateema ta juya mata baya tana danna wayar ta tunda taga alamar rashin hankali a tare da addar tata tana bukatar a saita ta.Haka ta kwana cikin kunci da damuwa na rashin sanin abun yi.*****Kwanaki nata shudewa a yayinda hukuncin baba malam ke cigaba da guda akan Ameena sai dai a sace take daukar wayar fateema taje bayi ta mai flashing ya kira suyi ta hira na tsawon lokaci kafin su kashe sai ta goge lambar akan sashen kira ta yadda bazata gane ba, kullum haka takeyi.Yauma ta lallaba ta dauki wayar bayan fateema ta dade dayin bacci ta fita cikin sanda ta dauki buta ta nufi bayi tayi flashing ya kira ta dauka.Ajiyar zuciya ya sake yace yau kinyi lattin zuwa.Tace kasa-kasa batayi bacci da wuri bane shiyasa.Ok na fahimta, ya maganar mu ta jiya ina muka kwana a zancen?Kada ka damu zamu hadu amma ina jin tsoro ne don inna saita kusan kasheni da duka idan ta gane gaskiya.Haba sweetheart common nayi kewar ki sosai kusan kadan ya rage in zauce ki taimakeni ko mituna biyar bazaki wuce ba zaki koma gida.Haka ne nima nayi kewar kagoben zanyi kokarin fitowa zan same ka a inda kace din.Ina sonki sweetheart, nan suka ci gaba da hirar su cikin manta irin yanayin da suke ciki.Fitsari ne ya tada fateema ta laluba wayarta bata jita ba sai ta haska torchlight taga babu Addan ta tayi jira bata ga ta shigo ba sai ta mike ta fita a kusa da bayin ta tsaya nan ta soma jin magana kasa-kasa ta kara matsawa da kyau hta kasa kunne tana sauraren hirar su daidai inda sukayiwa juna sai da safe, fateema bata tashi a gunba don so take tasan ta ganta, Ameena da ta fito daga ban dakin taga fateema a tsaye ta dan tsorata amma sai ta waske tayi shigewarta daki, ita kuma fateema ta shiga tayi uzurinta ta fito ta shiga dakin.Ameena har ta kwanta fateema ta dauki wayarta tace yaushe kika fara daukar mun waya kina magana da wani cikin dare?Tashi zaune Ameena tayi tace ji nayi ina son jin muryar shi shiyasa yau dai nace barin kirashi ina fatan zaki rufa mun asiri wurin su baba malam? Ta fada tana kallon fateema.Itama fateeman ita take kallo tace kada ki manta kefa ‘yar uwatace idan da wanda ya dace da ya rufa miki asiri toh nice amma kinsan girman laifin da kike kokarin aikatawa kuwa? Baba malam bazai miki da dadi ba bare inna kinsan halinta, sannan ni banga abun nacewa ga Ahmad dinnan ba dahar iyayen mu suka cancanci rashin biyayyar ki a garesu.Ke fateema kada kiga don ina kwantar da kaina sai ki nemi takani kina manta cewar ni yayar kice zan saba miki wallahi.Ko kadan ban raina kiba adda amma zan tambaye ki, bata jira cewar Ameenan ba ta cigaba, ki duba yadda kika hayayyako mun saboda kina tunanin na raina ki na fada miki magana marar dadi meyasa bazaki kwatanta hakan da rashin jin maganar iyayenmu da ke kike kokarin nunawa kowa amma kiyi hakuri idan na bata miki rai.Kwafa Ameena taja ta kwanta ta juya baya tana jan bargo don rufe jikinta, kasa-kasa fateema tace Allah yasa ki gane abunda kike yi ba daidai bane.Sarai Ameena ta jiya amma ta shareta.Washe gari bayan an kammala dukka ayyukan gida kowa ya koma ya kwanta Ameena tayi sadaf sadaf ta fice daga gidan ba tare da ta bar kowa ya sani ba dake suna baccine dukkan su , unguwar daya kwatanta mata nan tace mai adaidaitan ya kaita, har bakin gate din gidan ya sauke ta ta hango shi yana tafe.Sun a hadewa ya rungumeta a jikinshi yana sinsinar ta, ta ture shi tana cewa meye haka ne baka san haramun bane dan Allah ka daina.Jan hannunta yayi suka shiga ya rude gate din kafin ya juyo ya kalleta yace dama nasan duk soyayyar da kikace kina mun ta karya ce baza ki iya sadaukar da komai saboda son da kike mun ba, idan kina ganin da matsala gara tun yanzu mu rabu kada mu wahal da juna.EESHERT ADAMUMATAR MAJEEDADI✍️



