Hausa novels

Asanadin Makwabtaka Book 2 Page 65 Complete Novel

ASM Bk2065*

 

_Destiny may be delayed but cannot be changed…._

 

 

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

 

 

……….. Kissing d’in ta ya shiga yi deeply a nutse hannun shi duka biyun talla6e da kanta da ba kallabi gashinta dake fake yayi k’asa, Fatuu kam tuni ta k’ame ta kasa ko d’aga hannunta don abun yazo mata unexpected sai numfashin ta da ke fita rapidly kirjinta na hawa da sauka da sauri da sauri, sun d’auki lokaci a haka kafin slowly ya kwantar da ita akan kujeran tayi Flat still idanunta na a rufe, had’e fuskokin su yayi ta yadda tsinin hancin shi ya had’e da nata inhaling each other’s breathe wanda gaba d’aya yake fita da k’arfi, sun d’an d’auki lokaci a haka kafin slowly ya janye fuskar ya fara Moving dinta around her neck yana inhaling scent d’in jikinta, a wannan lokacin a wata irin duniya ta daban Fatuu take jinta the world around her faded away, sai faman sakin nishi take ta kai har saida ta d’an bud’e bakinta don ji take numfashin ta na neman katsewa, wani irin salo yake mata mai rikita kwakwalwa a nutse cike da gwanancewa, suna cikin haka ya kai hannu ta k’asa a hankali ya fara tattare rigar ta, Fatuu na jin haka bugun zuciyar ta ya k’aru, dakatawa yay da shak’ar K’amshin wuyan ta da yake ya fara jawo fuskar k’asa har ta sauka kan flat tummy d’in ta daya bayyana sakamakon dama iya rigar baccin ce ta rufe shi, har saida Fatuu ta d’an gantsare lokacin da taji ya kai nan jikinta ya fara d’an rawa ta fara mommotsa k’afafun ta, bin cikin nata ya fara yi yana cigaba da shak’ar Scent d’in da jikinta ke saki giving her soft kisses at the same time, she’s savoring every touch and every kiss ji take tamkar zata suk’e, cigaba da moving face d’in shi yay yana yi mata abunda yake mata, a haka har ya rage da ya k’ara janye rigar boobs d’in ta zasu bayyana a lokacin numfashin Fatuu kusan d’aukewa yay, yana k’ok’arin k’ara janye rigar hannun shi ya gogi boob d’in ta, dakatawa yay da abunda yake matan tamkar an latsa mashi pause yay d’an jimm can kuma sai ya d’ago daga jikin nata, dakatawar da yay yasa da k’yar ta d’an bud’e idanun ta da sukai mata wani irin nauyi ta hango shi zaune daga gefe kan shi a k’asa yasa hannu guda ya dafe gefen fuskar tashi, k’arasa bud’e idanun ta da tuni sun canza daga ainihin kalar su da yanayin su tayi ta bi shi da kallo har lokacin numfashin ta da d’an k’arfi yake fita, sun d’an d’auki lokaci a haka can wata zuciyar ta raya mata zaman me take ta tashi ta tafi d’aki, da k’yar ta yunk’ura ta tashi zaune ta saukko da k’afafawun ta k’asa kafin ta mik’e, ko ta kan littafin ta da laptop d’in bata bi ba ta nufi hanyar corridor tana tafiya a harhard’e gaba d’aya jikinta jin shi take kaman ba nata ba sai kace na wadda ta tashi daga ciwo sam ba k’arfi a jikin nata kwata kwata, Slowly ya d’aga idon shi da suka sauya daga yanayin su yana kallon ta har ta shige d’aki sannan ya maida kan nashi k’asa yasa dukkan hannuwan shi ya talla6e shi, tana shiga ta nufi bakin gado ta zauna dabas ta kankame jikinta da har lokacin yana d’an yin rawa, gaba d’aya ji take kamar har lokacin yana cigaba da yi mata abubuwan da suka wakana tsakanin su, gaba d’aya ya tado mata da urge d’in ta dama kuma a tsume take a yadda take ji ma sai tayi wanka, ta d’an d’auki lokaci a haka can ta kai kwance k’afafunta na a k’asa tay tsuru tana ta imagination hakan ya k’ara kashe mata jiki sosae, zuciyar ta ce ta fara raya mata anya Ya Haisam na son ta kuwa, inda yana son ta bata tunanin yadda suka kai wani mataki haka zai k’yale ta, wata zuciyar ta k’ara raya mata da bai son ta zai yi mata abubuwan da yayi mata ne sai kuma ta sake raya ai k’ilan bada niyya bane kaman yadda ya faru a G.r.a dalili ne ya sa komai ya faru to k’ilan yanzu ma haka ne tunda ita ta fad’a mashi, idanunta ne suka ciko da k’walla ita kad’ai tasan abunda take ji a jikinta can ta runtse idanun ta suka fara gangaro mata, ta d’an d’auki lokaci a haka saida taji ta d’an samu sassaucin abunda take ji a jikinta sannan ta yunk’ura ta tashi zaune sai kuma ta mik’e tana tafiya a hankali ta nufi wurin kayanta ta d’aukko hula tasa, gaban dressing mirror ta tsaya tana kallon kanta kwalla na ci gaba da zubo mata daga baya ta sa hannu ta goge ta juya ta nufi hanyar laundry, d’aure da towel ta fito ta koma wurin kayanta ta curo doguwar riga ta zumbula daga haka ta nufo gado ta kwanta ta ja duvet ta lullube har kanta. Tun bayan da ta shige yake zaune a yadda yake tsawon lokaci sai daga baya ya mik’e ya nufi hanyar fita daga cikin parlon walking slowly, not too long da fitar shi ya dawo hannun shi ruk’e da wani abu har ya zauna sai kuma ya mik’e bayan ya aje abunda ya d’aukko a kan kujerar ya nufi hanyar Dining, bottle water ya d’aukko daga cikin freezer ya dawo, zaunawa yayi ya shiga bud’e ruwan bayan ya bud’e ya aje shi akan c-table ya kai hannu gefen shi ya d’aukko abunda ya aje wanda d’an kwali ne kamar na magani ya bud’e, ciro abunda ke ciki yay ya 6allo guda d’aya ya saka cikin bakin shi ya kai hannu ya d’aukko robar ruwan, bayan ya shanye ya rufe robar ya aje ya maida abun cikin kwalin wanda kaman magani ne, bayan ya rufe kwalin ya sake mikewa ya nufi hanyar fita, bada jimawa ba ya dawo ya nufi wurin Switch ya kashe hasken Parlon ya bar na wasu k’ananun fitilu kaman yadda yake yi ya koma wurin Kujerar, Zaune yay idon shi akan Corridor kaman mai tunanin wani abu, ya d’an d’auki lokaci a haka kafin ya kwanta yau ko pillow d’in babu saidae ya tada kan shi da hannun kujera yasa tafin hannun shi d’aya ya rufe fuskar shi, ta dad’e bacci bai d’auke ta ba sai tunane tunane take tana juye juye har dare ya yi sosae tana a haka, har Addu’a tay a cikin ranta kan Allah yasa tayi baccin, sai bayan wani lokaci sannan baccin ya d’auketa cike da mafarkan abunda ya faru.

 

Sai da gari ya fara wayewa sannan ta farka lokacin har anyi sallar Asuba tuni, bayan tayo Alwala tazo ta kabbara salla, zaune tay da ta gama cikin ranta tana ayyana Ya Haisam bai shigo bane yin Alwala da bai tashe ta ba, haka tay ta zancen zuci ita kad’ai sai bayan wani lokaci sannan ta mik’e ta cire Hijab d’in data yi sallar ta ninke ta d’auke prayer mat duk ta maida su wurin da suke, komawa tay gado ta kwanta ta kudundune taci gaba da yin sak’e sak’e a ranta, tsawon lokaci tana a hakan bacci yak’i d’aukar ta har taji ta gaji da kwanciyar ta mik’e don ta gyara d’akin, bayan ta gama gyaran d’akin tasa turaren wuta toilet ta wuce tayo wanka, bata canza kaya ba doguwar rigar jikinta ta bari haka jikinta ma iya mai kawai ta shafa sai turare data fesa ta koma bakin gado ta zauna, hakanan rashin shigowar Haisam d’in ta tsaya mata ta raya k’ilan don abunda ya faru ne k’ilan kuma ya shigo tana bacci, gaba d’aya ta rasa mike mata dad’i har wayarta ta daukka don tayi ko chatting ne amman k’arshe sai dai ta aje ta ta haye gado tay shiru, tana kwancen taji anyi knocking kopar d’akin ta tashi zaune da alamun mamaki, jin an k’ara kwankwasawa yasa ta mik’e ta nufi kopar, tana bud’ewa taga Saude ce tayi mata murmushi itama ta d’an yi mata ta gaishe da ita, bayan ta amsa tace mata dama Breakfast ne ta kawo to bata iske kowa a parlon ba kar ta aje ta tafi kuma ba’a san ta kawo ba yasa tace bari tayi mata magana, Fatuu ta d’an yi mamakin jin tace ba kowa a parlon kenan ma baya nan godiya tay mata har Sauden zata juya ta tafi sai kuma ta dakata idon ta akan Fatun tace “amman ko baki lafiya ne?” d’an fad’uwa gaban ta yay tayi d’an murmushi tace mata a’a lafiyar ta lau, Sauden tace “amman Fateema naga idanunki sun canza kaman ma kuka kikai ko?” da sauri ta girgiza mata kai “a’a Aunty Saude” tana kai Maganar ta sunkuyar da kanta k’asa don sai taji idanunta na tara k’walla, hakan da tayi yasa Saude zargin da wani abu ta kai hannu ta dafa Shoulder d’inta tace “in wani abu ke damun ki Fateema ki fad’a man in da taimakon da zan maki, barin damuwa ba abunda yake ma mutum sai haddasa mashi ciwo” da k’yar ta maida k’wallan ta kalle ta da d’an murmushin yak’e ta girgiza mata kai tace “ba abunda ke damuna Aunty Saude kawai na tashi da ciwon kai ne” kai Sauden ta jinjina ta yarda da abunda tace ta tambayi to tasha magani tace mata eh tun jiya da daddare,

 

“to yanzu ai yakamata ki k’ara sha tunda ga Abinci nan na kawo ki zo ki ci sai ki sha maganin in kuma kinji bai daina ba gara kiyi magana akai ki Asibiti, kinsan yanzu haka malaria ke sa mutane suyi ta ciwon kai mai tsanani” kai ta d’aga mata tace ta zo tayi breakfast d’in, ba musu ta fito suka shigo parlon tare Sauden tace suje tay serving nata da sauri tana murmushi tace mata lafiya lau zata yi ai ba wani ciwo yake mata sosae ba tay mata godiya ita kuma tay mata Allah ya sawak’e ta tafi, zaune tay a dining d’in ta kasa yin Breakfast sai tunanin inda Haisam d’in ya tafi take wata zuciyar ta raya mata k’ilan ma ba gidan ya kwana ba k’arshe ta yanke watak’il yana G.r.a, ta d’auki lokaci a haka kafin ta fara yin Breakfast din, bata wani ci da yawa ba ta mik’e ta koma d’aki, ji tay duk zaman bai mata dad’i ta yanke tafiya part d’in Hajiya bayan ta d’aukko gyale ta yafa ta fita, tana kaiwa bakin k’opar parlon zata bud’e taga an turo ta kalli mai shigowar da sauri, Haisam ne ya shigo jikin shi sanye da k’ananun kaya da gani wanka yayi sai sakin uban k’amshi yake, suna had’a ido ta sadda kanta k’asa da sauri, k’arasa shigowa yay idon shi a kanta ya tsaya daga gefe, kirjinta ne ya fara bugu da sauri sauri da k’yar ta bud’e baki ta gaishe dashi ba tare data kalle shi ba ya amsa, shiru ba wanda ya k’ara tanka wa balle ya motsa still idon ta na k’asa shi kuma ya kafeta da nashi idon wata irin kunyar shi taji ta rufe ta, jin bai k’ara cewa komae ba kuma yayi tsaye yasa ta d’an d’ago ta kalle shi suka k’ara had’a ido da sauri ta juyar da face d’in ta gefe ta fara motsa baki murya na d’an rawa ta fad’i mashi zata part d’in Hajiya ne, shiru bai ce komae ba hakan yasa ta d’an juyo still kallon ta yake sai kace mai nazarin wani abu, tambayar ta yay bata lafiya ne ta d’aga ido ta kalle shi sai kuma ta girgiza mashi kai had’i da maida idon k’asa, ji tay ya k’ara cewa in bata lafiya ne su je Hospital ba tare da ta kalle shi ba a sanyaye tace mashi lafiyar ta lau k’asa k’asa ya furta Ok ya fara k’ok’arin wucewa ciki, har zata fita sai kuma ta tuna da breakfast d’in da aka kawo ta juya ta koma ciki daga gefe ta tsaya ta d’an kalle shi yana zaune kan kujera tace mashi ga breakfast can an kawo ya jinjina kai yana kallonta, ganin tayi tsaye yace taje in da zata tace zatay serving nashi ne yace no problem zai yi da kan shi ta je, kallon shi ta sake yi idon su ya k’ara had’uwa da sauri ta juya ta nufi kopa ta fita, Tana tafe tana zancen zuci gaba d’aya ta kasa gane ma wannan auren nasu, tasan ana aure ne in ana son juna to su ita ce ke sonshi shi ba son ta yake ba kawae ya aure ta ne don ya taimaka mata ba don suyi rayuwar Aure ba abun kuma turns out this way, yanzu haka zasu cigaba da yin tasu rayuwar auren? Ta jefa ma kan ta tambaya, ta so ace shima yana jin son ta ya kuma nuna mata tasan da ba k’aramar rayuwar Aure mai dad’i zasu yi ba, idanun ta ne suka ciko da k’walla daga baya suka fara zubowa, saida ta iso bakin part d’in sannan tasa gefen gyalenta ta goge Fuskar sosae sannan ta shiga, ganin ba kowa a parlon yasa ta wuce Bedroom d’in Hajiya nan ta iske ta tana bacci ta fito ta nufi Kitchen ba kowa a ciki ta juyo ta nufi d’akin Saude, ciki ta isketa tana ganinta ta washe mata baki tana fad’in har ta samu sauk’i da ta fito, a gefen Katifarta ta zauna tana murmushi tace mata ai fa dama ba sosae yake mata ciwon ba yanzu ma ta samu sauk’i ta zo ta taya ta aikin Abinci Sauden tace a’a yau dae ta huta ko ta k’ara samun sauk’i Sosae tay murmushi kawae, kwanciya tay akan Katifar Sauden don tak’i yarda ta taya ta aikin bada jimawa ba kuma bacci yay awon gaba da ita, saida akai sallar Azahar Saude tazo ta tashe ta don tayi salla, bayan ta gama sallar ta nufi Bedroom d’in Hajiya ta isketa zaune akan prayer mat tun bayan da ta gama salla bata tashi ba ta nufi gefen ta ta zauna tana gaishe da ita da murmushi ta amsa tana tambayar ina Angonta ta sanar da ita ai tun d’azun tazo ta iske tana bacci shine ta wuce d’akin Aunty Saude nan bacci ya kwashe ta, tana zaune a d’akin Hajiyar sai ga Haisam ya shigo tunda suka had’a ido ta maida kanta k’asa ya zauna a bakin gado bayan ya gaida Hajiyar suka shiga d’an yin fira jefi jefi daga baya Saude ta shigo ta sanar da ita an shirya table tace ai sai su tashi suje suci gaba d’aya tunda suna nan, Fatuu ce tay Serving d’in su bayan itama ta zuba nata ta zauna saidai kasa sakin jiki tay taci sosae sai faman Jujjuya cokali take har Hajiya ta gane ta tambaye ta ko bata son Abincin ne da sauri tace mata a’a tace to taga tak’i sakin jiki taci sosae in bata son shi tayi Magana sai a samar mata wani abun tace a’a tana so dole ta daure ta rink’a turawa, bayan sun gama Haisam ya tafi dama shi ya fara tashi su kuma suka koma Parlor suna kallo, sai bayan la’asar sannan Fatuu ta koma part d’in su tana zuwa ta wuce toilet don tayi wanka, bayan ta fito ta shirya cikin doguwar rigar Atamfa A shape ta d’an shafa powder da lip glow ta fesa turarurruka, wayarta ta d’auka ta haye gado ta fara yin Azkar bayan ta gama tay tunanin kiran Haulat don tun ranar tarewar ta rabon ta da ita, ta dai san da ita aka kawo ta amman bata san lokacin data tafi ba, sai bayan isha Haisam ya dawo yau ma harda ledar su ice cream ya kawo mata tayi mashi godiya daga baya suka wuce dining area don cin Abinci, bayan Fatuu ta gama duk abunda zata yi na shirin kwanciya ta d’aukko Al’qur’ani ta zauna a saman gado tana karantawa lokacin Haisam ya shigo shima tuni yayi shirin kwanciya, dakatawa tay da karatun ta kalle shi ba laifi ta rage jin kunyar tashi Fuskar shi a sake ya nufo gadon ya d’auki pillow yace mata “Gud night” kai ta d’aga mashi ya juya ta bishi da ido har ya fita sannan taci gaba da karatun, Washe gari ana kiran sallar Asuba ta farka, tana gama yin sallar ta wuce toilet tayo wanka, bayan ta fito ta fara shirin zuwa Makaranta, Yana kwance kan kujera idanun shi a rufe ta fito sanye da Uniform ta nufo cikin parlon, daga gefen shi ta tsaya tana kallon fuskar shi ta fara tunanin ko bacci yake yi, slowly taga ya fara bud’e idon suka sauka a kanta, gaishe da shi tayi ya jinjina mata kai cikin yar inda inda tace mashi dama Makaranta take son zuwa, kafeta yay da ido ba tare da yace komai ba hakan yasa ta maida nata k’asa, tana haka taji yace tayi breakfast ne ta girgiza mashi kai alamar a’a, shiru yay ta d’ago ta kalle shi yace to zata tafi School d’in ne ba tare da tayi breakfast d’in ba tace mashi eh,

 

“Dama kina yin haka?” taji ya tambaya, ta gane yana nufin dama tana zuwa Makarantar ba tare da tayi breakfast d’in ba, a hankali tace “a’a, amman in na tsaya jira zan iya makara, nasan bata san da zanje Makarantar bane yasa bata yi da wuri ba” tana Maganar ya kafeta da ido, sigh yay taji yace sai tayi breakfast zata je ta kalle shi yanayin fuskar ta ya sauya, tunawa tay da ice cream d’in daya kawo mata ko roba d’aya bata sha ba tace mashi bari tasha ice cream da cin cin to, wani kallo yay mata ya d’an yamutsa fuska yace ya zata sha abu mai sanyi da safe ta yamutsa fuska a shagwa6e tace to ai lafiya lau in ta tsaya jira sai an kawo zata makara ne fa, shiru yay kaman bazai ce komai ba can yay mata alamar ta zauna da hannu, bayan ta zauna ya yunk’ura ya mik’e tana ta kallon shi ya nufi kopa ya fita, bayan fitar shi tana zaunen idanunta suka sauka akan pillow tay tunanin ta d’auke tunda tasan shi zai kai ta School d’in kuma daga can ba lalle ya dawo nan ba, mik’ewa tay ta nufi kujerar ta kai hannu ta d’aukko filon, wani abu ta ji ya fad’o akan k’afarta ta kai idanunta k’asa don taga minene, duk’awa tay ta kai hannu ta d’aukko abun, k’aramin kwali ne wanda ya d’aukko jiya ta bishi da kallo, daga yanayin sunan dake jiki da hotunan jiki ya nuna magani ne saidae ta kasa gane maganin ko na miye daga sunan shi amman daga yanayin hoton jiki ya nuna kaman na ciwon ciki ne don wani mutum ne a jiki ya daddafe cikin shi ya d’an duk’e sai kuma daga gaba gashi nan bayan yasha maganin a kwance yanata bacci harda d’an murmushi akan fuskar shi, jujjuya kwalin ta shiga yi a ranta tana raya Ya Haisam bai lafiya ne amman bata ga alama ba wane irin ciwon ciki yake yi, ranta ne ya bata ta bud’e k’ilan akwae leaflet a ciki sai ta duba k’ilan ta gane na ko wane irin ciwon ciki ne, har zata bud’en sai kuma wata zuciyar tace mata bafa kyau yin bincike hakan yasa ta fasa sai ma ta maida pillow d’in kawae ta tura maganin a karkashi don tana tunanin anan yake ya fad’o, bata dad’e sosae ba da komawa ta zauna sai gashi ya shigo hannun shi ruk’e da d’an babban tray ta bi shi da ido har yazo ya aje akan c-table, matsar mata yay da table d’in yace gashi nan ta kalli tray d’in sai kuma ta kalle shi ya koma ya zauna, hannu ta kai ta bud’e plate d’in da aka rufe wani plate nan take k’amshi ya bugi hancin ta taga indomie ce tasha vegetables harda soyayyun cinyoyin kaza guda biyu tayi gwanin kyau a ido daga gefe kuma Cup d’in tea ne an had’a shima an rufo shi, da alamun mamaki ta d’aga ido ta kalle shi ya jingina bayan shi yana kallon ta mamaki ta shiga yi a cikin ranta na badai shi ya dafa ta ba, hannu ta kai ta d’auki fork ta fara ci sosae tay mata dad’i, kasa jurewa tay tana cikin ci ta dakata ta kalle shi yana ta latsa wayar shi,

 

“Amman kai ka dafa ta ne?” da k’yar ta tattaro kalmomin ta tambaye shi, shiru kaman bai ji tambayar da tayi ba har ta fidda ran zai amsa taga ya d’ago ido ya kalle ta taji yace ta tambayi Abincin mana, d’an tura mashi baki tay ta maida idon ta kan Abincin, tana cikin ci taji yace shi ya dafa akwai matsala ne, har saida ta maimaita Maganar tsabar mamaki ba wai don ya dafa matan ba sai don bata ta6a tunanin ya iya girki ba koda dafa tea ne, saida ta cinye ta duka farko ta rage yace mata wa zata bar mawa tana d’an murmushi tace shi d’an murmushi yay kawai ya gane wasa take mashi tunowa da can baya, naman ne ta rage ta kwashe kayan ta kai Kitchen, saida ta wanke komae ta d’ebi su dublan don ta kai ma su Fauzy harda ice cream ta d’aukar mata sannan ta koma Bedroom ta d’aukko jakar ta da takalma dama ta saka safa tun da tasa uniform.

 

Bayan sun isa ya fiddo kud’i ya bata ba tay mashi musu ba don tasan ba maidawa zai ba tayi mashi godiya ta bud’e Motar ta fita, tun kan ta shiga aji wasu da suka ganta sukai shelar zuwanta, tana zuwa bakin Class d’in su Zainab suka fito da gudu suna mata oyoyo Amaryar su suka rungume ta tana ta masu dariya, bayan sun saketa ta tambaye su Fauzy suka ce bata kai ga zuwa ba suka nufi cikin ajin suna ta tsokanar ta wai k’amshin Amarci take gashi tayi Fresh ita dai sai murmushi take kawai, bata dad’e da zuwa ba Fauzy tazo tun daga bakin Class ta hango ta ta shigo da gudu tana fad’in k’awarta Amarya tana zuwa seat d’in ta rungume ta Fatun nata dariya, zama tay sai kallon Fatun take tana sakin murmushi tace “ai banyi tunanin zaki zo yau d’in ba, nayi zaton zaki k’ara kwana biyu kaman yadda na baki shawara” d’an girgiza mata kai tay alamar a’a, “wai badai duk Amarcin bane yasa baki magana” Fauzy ta fad’a baki bud’e Fatun ta sa dariya tace mata a’a,

 

“Amarci dad’i, Wai kinga yadda kikai Fresh duka kwana ukku, gaskiya nima na fara jin son aure wllh” ta k’arasa tana dariya itama Fatuu dariyar take suna haka malamin su ya shigo, bayan anyi break sun fito ne Fauzy ke tambayar Fatuu wai ko wani abun na damunta ta lura da suna class kaman tana yawan yin tunani a sanyaye tace mata ba komai saidae Fauzyn bata yarda ba tace in wani abu ke damunta ta fad’i mata in na shawara ne sai ta bata barin damuwa ba zai mata magani ba har da ce mata ko bata yarda da ita bane tace mata a’a, ganin yadda duk ta damu da son jin ko wani abu na damunta yasa a sanyaye tace “ba wani abu ke damuna ba Allah Fauzy, kawai dai….na rasa gane kan Ya Haisam, gani nike bai so na kaman yadda ake hasashe kawai ya yarda yaci gaba da zama dani ne ba wai don yana sona ba” idanun ta ne suka ciko da k’walla da sauri ta fara k’ok’arin maida su, ajiyar zuciya Fauzy ta sauke duk da bata san dalilin da ya sa tace haka ba ranta ya bata wani abu, tambayar ta tay dalilin daya sa tace haka tay d’an murmushi tace mata ba komai kawae dai yak’i sake mata ne, hak’uri Fauzyn ta bata tace ita tana ganin a k’ara bashi lokaci k’ilan da dalilin hakan amman tana kokonton ace bai sonta kuma ya za6i cigaba da zama da ita to miye ribar hakan, ai indae dama ya aure ta tun farko don ya taimaka mata ne to ba dalilin da zai cigaba da zama da ita Fatun tace bata ganin ko don abunda ya faru yaga bai kyauta mata ba in ya rabu da ita yasa, Fauzy ta girgiza kai tace gaskiya bata tunanin hakan koda da hakan to akwae wani dalilin wanda kuma tana ganin so ne Fatun tay shiru kawai, Fauzy na son ta yi mata Maganar magunguna amman dalilin wannan Maganar yasa ta fasa, ana tashi Haisam yazo d’aukar ta saida Fauzy ta rakata har bakin Mota ta gaisa da shi sannan ta wuce Hostel su kuma suka tafi……..

Asanadin Makwabtaka Book 2 Complete Novel Txt

Back to top button