Hausa novels

Halysaah Page 80 By Khaleesat Haydar

HALYSAAH PAGE 80…

Khaleesat ta langwabar da kai tana kallon Ajay a hankali tace “Good evening” Ya kusa 30 seconds tsaye yana kallonsu ya ki cewa komai, Safiyyah ta jawo handbag dinta a hankali ta rataye a kafada tana kallon Khaleesat murya kasa kasa tace “Kar Ya Musty ya fara kirana ni zan tafi gida” A tare suka bi Ajay da kallo ganin ya rufe kofar parlon ya cire makullinsa ya nufi staircase ya wuce sama, Safiyyah ta maida handbag dinta ta ajiye gefe tana washe baki tace “Ba daxu daxun nan na gama ce maki ba shi da matsala ba, wallahi dama nasan bazai ce mana komai ba don kowa yasan PS da shiga rai, ai ba kowa ne fitinanne ba” Plate din abincin da suka ci ta dauka ta kankare sauran shinkafar jiki ta cinye sannan ta ajiye ta dau Controller din da ta ajiye kan kafar Khaleesat zata ci gaba da game din tana cewa “Ai ba abinda zai ce mana wallahi, yana da saukin kai” Khaleesat tayi dariya tace “Kika san me yaje daukowa a sama, ni dai ba ruwana wallahi…” Tana fadin haka ta mike tsaye tana dariya, Safiyyah ta kara jawo handbag dinta da ta ajiye ta makala a hammata ta mike tsaye ita ma tace “Mu je ki bude min kofa ni dai kafin Ya Mustapha ya fara nemana” Khaleesat ta dafa kujera ta dinga dariya ba kakkautawa, Safiyyah ta hade rai tace “Meye haka don Allah, ina makullin gidan yake ni dai ki bude min in wuce” Ganin Khaleesat taki kulata sai dariya take baɓɓakawa, Safiyyah ta fixgo handbag din Khaleesat ta bude ko zata ga makullin gidan a ciki amma bata gani ba, tace “Ni don Allah meye abun dariya, ki bude min kofa in tafi kar yayana ya fara nemana mana” Khaleesat tace “Ki tafi ina? Ai wallahi babu inda zaki je ki bar ni a gidan nan, ba ke kika ce mu zo muyi game ba” Safiyyah tace “Da nace mu zo muyi game tunda kin san baya so ba sai kice min A’a ba, ta yaya ni zan san baya so a taɓa masa kayansa, kin ga kar raina ya baci ki bude min kofa in tafi gida, wannan wani irin iskanci ne ana magana kina dariya” Dariya kawai Khaleesat take yi kamar zata shide, ran Safiyyah yayi mugun baci ta kankance ido tana kallon Khaleesat, lkci lkci take kallon sama kar Ajay ya sauko ya riske su, a fusace tace “Wallahi ban san haka kike ba da bazan biyo ki ba, ina zaman zamana kika ce min akwai Ps5 a gidan nan, in baki gaya min ba ta yaya zan sani, nayi da na sanin biye ki wallahi” Shiru tayi ganin Ajay na saukowa downstairs, Khaleesat ta hadiye dariyar da take tana kallonsa, Safiyyah ta sha kunu bayan ta koma gefen Khaleesat ta tsaya kamar masu jiran hukunci, shi dai ko kallonsu bai yi ba ya nufi kofa ya bude ya fita, da sauri Khaleesat ta tafi tana lekasa ta windon parlor, motarsa taga ya shiga ya tafi, ta dinga kyalkyala dariya tana kallon Safiyyah dake makale jikin windown ita ma tana lekansa, bata ma san sanda ta zo jikin windan ba, Safiyyah ta washe baki tace “Atoh ba nace maki bazai ce mana komai ba amma duk kika bi kika firgice, ai Ajay mutum ne, shi dai kar ka masa rashin kunya kawai” Bata jira cewar Khaleesat ba ta koma gun game din, Khaleesat tace “Ba gida kika ce zaki tafi ba Ya Mustapha na kiran ki” Safiyyah taki tanka ta tana gyara zama ta ci gaba da game dinta, Khaleesat ta dau plate din da suka ci abinci ta kai kitchen, bude baki tayi ganin ashe duka abincin Safiyyah ta juyo masu suka cinye, gashi ya dawo ya tarar suna masa game tasan kuma dole sai yayi mata magana ko ba yau ba, ga kuma an cinye masa abinci, jingina tayi jikin cabinet din kitchen din, ko dai kawai ta dafa masa wani abincin ai ba sani zai yi ba, fara harhada ingredients din da zata yi girkin tayi, sai ga Safiyyah ta shigo kitchen din tace “Don Allah ki zo mu ci gaba mana, tunda bai ce mana komai ba alamar ya bamu permission kenan ai, ke dai kin fiye tsoro” Khaleesat tace “Sophie ashe duka kika juyo abincin, yanxu idan ya kara dawowa yaga babu wani abincin fa?” Safiyyah tace “Ba sai kice masa Housemate ne ya zo ya ci ba, ai bazai san mu muka ci ba” Khaleesat ta wani kalleta, can tace “Kawai sai in ma Housemate dina sharri, ni dai wani zan dafa masa kawai” Safiyyah tace “To ki dafa har mu don ban koshi ba dama, kuma yayi dadi irin nasa don Allah” Daga haka ta koma parlor ta saka game din ita kadai tana yi, har kusan karfe biyar na yamma Safiyyah na bakin PS a zaune tana ta yi, Khaleesat tuni ta gama girkin da take har da grilling masa chicken lap biyu yanda dai yayi sannan ta kira Safiyyah tana tambayarta yanda ta ga abincin a kitchen, Safiyyah ta jera masa yanda taga ya bar kayansa sannan suka koma suka ci gaba da game…. Wajen karfe shidda game din ya dauke ya shiga wani waje daban, kokarin gyarawa Safiyya ta dinga yi amma yaki, Khaleesat tace “Dama sai da nace mu bar game din haka kika ki ji” Safiyyah taki tanka Khaleesat sai kokarin gyarawa take, garin gyara kawai ya dauke gaba daya, Khaleesat ta bude baki tana kallonta, Safiyyah ta ajiye controller din hannunta ta jawo handbag dinta ta makala a kafada tace “Kilan ma Ya Musty na ta kirana wayar na silent” Kokarin mikewa tsaye take Khaleesat ta rikota tace “Ban gane Ya Mustapha na ta kiran ki ba, waye zai gyara masa kina ganin abu ya dauke gaba daya?” Safiyyah tace “To ni bakanikin PS5 ce, ki kashe socket din kawai ki wuce sama ni kuma in tafi gida, ai mu ma bamu san me ya samu abun ba ya dauke, kilan ya dau zafi ne” Zaro ido Khaleesat tayi jin ƙaran mota a garage, Safiyyah ma ta gwale ido tana kallonta, mikewa Khaleesat tayi ta tafi window da sauri tana leka garage, ganin motar Ajay ta dawo da sauri tace “Wallahi shi ne ya dawo, gashi kin lalata masa abu…” Safiyyah ta zaro ido tace “Ban gane na lalata ba? Ni kadai nake game din? Me yasa bakya tsoron Allah Khaleesat” Cikin few seconds Khaleesat ta kashe komai ta mayar masa da controller dinsa inda yake ajiyewa, ta mayar da throw pillows dake ƙasan carpet zuwa kan kujera, tana juyawa taga Safiyyan har ta haura sama, ta bi bayanta da sauri suka shige dakinta, Khaleesat ta dinga kyalkyala dariya har da rike ciki, Safiyyah ta hade rai tace “To wai meye abun dariya? Ke abinda ya kamata ayi dariya ba shi kike ma dariya ba sai wanda ba na dariya ba, yanxu meye abun dariya don Allah a nan, ni ban ma san yamma tayi haka ba ai da tuntuni na tafi gidanmu….” Khaleesat dai bata fasa dariyar da take ba, suka ji ya bude kofar daya daga dakunan dake sama, Safiyyah na jin haka ta bude kofar dakin Khaleesat a hankali ta fice, kafin Khaleesat ta fito har Safiyyah ta bar apartment din gaba daya ta mike can karshen layi tana yi tana hadawa da gudu, Khaleesat ta kasa dena dariya ta dawo cikin apartment din ta kulle kofar ta wuce sama ta shige dakinta don kar ma ta hadu da shi. Karfe tara saura Khaleesat ta bude kofar dakinta a hankali ta fito corridor tana leka downstairs don yunwa take ji, zaune ta gansa a parlor yana online game, ta sauko downstairs ganin ya gyara game din da suka rikitar, plate din abincin da ya ci ta kalla, saura kadan tayi dariyar da bata yi niyya ba, ga dai shi ya ci abincin da ta girka yau, kitchen ta nufa tana kallonsa, shi dai ko kallonta bai yi ba game dinsa kawai yake, ta duba sauran abincin da ya rage a kitchen din sai kuma ta fito tana kallonsa tace “Zan iya daukan sauran abincin?” Ba tare da ya kalleta ba yace “Da can tambayata kike kafin ki dauka, so you can steal it as usual ai kin saba” Juyawa tayi ta koma kitchen din ta juyo sauran abincin sannan ta fito, zaunawa tayi a bakin stairs tana cin abincin tana kallon game din da yake yi, bayan ta gama cin abincin ta bar plate din a wajen ta koma cikin parlon ta zauna kan carpet ɗan nesa da shi kamar munafuka tana satan kallonsa, sai kuma ta jawo controller daya ta langwabe kai tace “Zan yi nima pls” Ya daga ido ya kalleta, sai kuma ya hade rai yace “Duk wanda kika yi yau bai isheki ba” Bata san sanda tayi dariya ba tace “Ba mu sake yi ba fa bayan da ka dawo daxu da rana” Yace “Karya kike, daga yau ku ka sake taɓa min PS ke da loud friend dinki Allah sai kun siyo sabo kun ajiye min, an gaya maku na public ne PS din, in game za ku yi ku je kuyi da na Jay, shima yana da shi ae” Ita dai Khaleesat bata ce komai ba tana jiran ya gama fadan su yi game din tare, juyawa tayi ta kalli wayarsa dake vibrate, ya dau wayar ganin Mai martaba ke kiransa ya mike ya nufi kofa ya fita waje, kafin ya dawo har ta saita game din yanda za su yi su biyu tana jiransa, yana shigowa parlon ta kallesa tace “Sau daya zan yi kawai pls” Bude baki yayi yana kallonta ganin ta cire game din da yake yi, ta langwabe kai ita ma tana kallonsa, ya hade rai yace “Yaushe na fara wasa dake zaki canza min game?” Tace “Idan kayi defeating dina sai in tashi in bar maka, idan kuma nayi defeating dinka zan ta yi har sai sanda na fadi” Bata jira me zai kara cewa ba ta fara game din, after some seconds ya dau controller dinsa, ko minti daya ba ayi ba yayi defeating dinta, ya juya ya kalleta, dariya tayi tana girgiza kai tace “Wallahi ban yarda ba this is foul play, don Allah last chance….” Sau biyu suna haka duk yana defeating dinta, a na uku ya juya ya kalleta yace “Tashi ki bar parlon nan” Marairaice masa tayi tace “Ni wallahi mugunta kake yi, ai ba haka ake game din ba, just this last time plss…” Ya gyada kai yace “Last time kika ce ko” Ta wani kallesa, suka fara game din, tana ganin alamar zai yi defeating dinta ta mike da sauri ta nufesa zata amshe controller din hannunsa yaki bata, tace “Wallahi ban yarda ba, mugunta kake yi a game din” a haka ta samu ta kwace Dual sense controller din hannunsa tana dariya, Lokaci daya duk suka juya jin an bude kofar parlon, zamewa Khaleesat tayi ba tare da tasan tayi hakan ba ta zauna kan carpet ganin Housemate dinta, Ajay ya kwace Controller din hannunta ya ci gaba da game dinsa har sai da yayi defeating dinta, Jay ya karaso cikin parlon yana kallonsu ya zauna yace “PlayStation ku ke yi” Sai a sannan Khaleesat ta daga kai ta kallesa, haka kawai taji gabanta na faduwa, a hankali tace “Ina yini?” Jay ya ɗan yi murmushi yace “Lafiya lau, continue with ur game” Ta ɗan kalli Ajay tace “Foul Play yake yi ai…” Mikewa tayi ta nufi Jay ta mika masa controller din hannunta tace “Ka taya ni let defeat him” Jay ya kalli Ajay, sannan ya amshi Controller din, Ajay ya ɗan kallesa sai kuma ya canza zuwa game that is more complicated suka fara, Khaleesat sai addu’a take Allah sa Housemate dinta yayi defeating dinsa, ai ko bayan wani lokaci Housemate yayi defeating Ajay, wani shegen dariya ta kyalkyale da a parlon, dariyarta ne ma yasa Jay yayi dariyar da bai yi niyya ba, har ranta taji dadi kada Ajay da Jay yayi, Ajay ya ɗan yi murmushi suka ci gaba da game din, Jay ya sake defeating dinsa, sai da suka yi haka sau uku ana kada Ajay, Khaleesat abun nema ya samu dariya kamar ana mata cakulkuli, Ajay ya hade rai yana kallonta, gwalo tayi masa ta kwace Controller din hannun Jay ta ajiye tace “Kace baka yi kuma, dama tun daxu sai ojoro yake ta min kar ya fara maka haka kai ma” Bata yarda su ci gaba da game din ba don kar ma Ajay yayi defeating Jay yayi masu dariya, Jay dai kallonta kawai yake yi, mikewa Ajay yayi ya ajiye controller din hannunsa kan kujera ya wuce sama, Khaleesat ta kalli Housemate dinta tana dariya tace “Kilan haushi yaji ko? Daxu fa he didn’t give me a breathing space sai kasheni kawai yake ta yi” Ganin Jay kallonta kawai yake bai ce komai ba ta sunkuyar da kanta tana murmushi, Calmly Jay yace “A sama kika bar wayarki kika sakko downstairs kuna game kenan” Khaleesat ta kallesa tace “Did you call me?” Kai ya gyada mata, tace “Wayar na sama, kasan me? Safiyyah ce ta zo daxu muna ta game din da ita shi ne ya dawo ya kama mu, yace kar mu sake taɓa masa, idan game za mu yi wai kai ma kana da shi, ni da ita muna son game din sosai fa… Sanda muna level 2 Former Housemate dita saurayinta ya kawo apartment dinmu, kullum sai mun yi” Jay yace “Baku yi karatu ba dai kenan yau?” Khaleesat ta ɗan kallesa, sai kuma tace “All works and no play….” Murmushi yayi yace “I see” Tana murmushin ita ma tace “Kayi dinner?” Yace “Wa zai bani?” Mikewa tayi tace “Ohk let me make you noodles” Yace “A’a kar ki ba kanki wahala” Tace “Ni dai sai nayi” Bata jira cewarsa ba ta wuce kitchen da sauri, ya bi ta da kallo, Ajay ne ya sauko downstairs ya dau dual controller da Khaleesat ta ajiye ya jefa ma Jay sannan ya dau nasa ya zauna, irin bai yarda din nan ba, dariya kawai Jay yayi suka fara game din. Har wajen karfe sha daya suna abu daya, Khaleesat har ta gaji da kallon game din ta kwantar da kanta saman kujera ta fara bacci, Jay ya tasheta ta tafi daki ta kwanta, tana murza ido ta mike ta bar parlon zuwa dakinta, wajen karfe daya da rabi ruwan sama da ake ya farkar da Khaleesat, mikewa zaune tayi bayan ɗan lokaci ta tashi ta fita daga dakin, leka downstairs tayi tana ganin mutum kwance a parlor ta san Housemate dinta ne don Ajay tunda ya dawo gidan bai fiye kwana a parlorn ba, sauka tayi ta kunna wutan parlon me haske to be sure is her Housemate, taga Housemate din nata ne ke bacci a parlon, ta kashe wutan sannan ta koma sama ta dauko masa duvet, tana rufa masa ya bude ido, ta ɗan masa murmushi a hankali tace “The weather is cold, I don’t want you to catch cold” Bata jira me zai ce ba ta wuce sama da sauri, a corridor din dakunan taga Ajay a tsaye ashe ba bacci yake ba, ya bi ta da wani irin kallo yace “Munafuka” Ta wani kallesa, sai kuma ta tura baki ta shige dakinta ta kulle. The Spring semester exams was so smooth for Khaleesat, da yake bata da damuwar komai a ranta unlike last exam da tayi sa cikin tension da tashin hankalin Abdul, a satin farko na Exams din nasu kullum sai Safiyyah ta biyota gida don su yi playing Ps5 ko karatun kirki Safiyyah ta dena yi saboda game, Allah Allah take su yi exam su kamo hanyar apartment din Khaleesat ayi game, ita Khaleesat dama cikin dare take karatun ta sai ta biyeta su yi ta game, ranan alhamis suna dawowa gidan da rana suka ga an kwashe PS5 din, Safiyyah ta kalli Khaleesat cikin bacin rai tace “Dama me hali bazai taɓa canza halinsa ba, bai san lada yake samu ɗan nishadin da muke yi da game din ba, da ace na Housemate ne nasan bazai taɓa kwashewa ba sai dai yace mu rage buga game din saboda Exam” Ko minti daya Safiyyah bata kara a gidan ba ta kara gaba rai a bace, nan ko bata san Housemate bane ya kwashe PS5 din.

Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah

07087865788

Back to top button