Uncategorized

Macizai ne Page 1-10 Hausa Novel

 

“Subhanallahi! Wannan bala’i ya yi yawa, a ce a kwana uku an kashe mutane goma? Masu kama macizai mutum takwas, wannan wani irin masifa ce ta macizai da ya fara addabar mu haka a gari? abu sai tsamari yake yi, tun ana samun sara kaɗan-kaɗan, ga shi saran macizai din bakinsu da girma! Me yake shirin faruwa ne haka a cikin wannan alƙarya na da mutanen yanki na?” cewar mai garin yankin kauyen kwana dake jihar yola da yake can cikin dajin fulani wanda ya cika da albarkatun korayen shuke-shuke, a wannan sassanin fulani ne suke rayuwa a wannan yanki, kuma su na da yawa dan sun hayayyafa, basu fita cikin gari kuma ba a shigo musu.

Jama’ar da suke tsaye a wajen ne cike da jimami da fargaba su na alhini, wani dattijon tsoho cikin harshen fullanci ya ce

“Gaskiya muna cikin hatsari a wannan alƙarya, ga shi yanzu an fara samu kisan macizai da yawa, ya kamata mu san abun yi” sai tattaunawa suke yi ta yadda zasu shawo kan wannan babbar matsalar da suke ciki, wata kyakkyawar budurwa ce a tsaye a can gefe fara sol, tana da idanun mage, sanye take da kayan fulani ta naɗa farin mayafi a saman kanta, ta rufe gefen fuskarta da shi, rabin gashinta ya sauko ya rufe mata rabin fuska wanda ya sake hana asalin kyawun nata fitowa sosai a gani,kafarta babu takalmi, a hankali ta bi mai kama macizai wanda aka kashe da kallo, ranta a b’ace ta juya a hankali tana tafiya dukkan sassan jikinta yana lankwasawa, a yadda take taka kasa da ka ganta kasan bata yi maka kama da cikakkiyar mutum ba, daji ta yanka ta shiga cikin korayen bishiyoyi inda zata samu yar uwarta kawai take hari, can kusa da wani rafi mai sanyi da dadin kallo ruwan fari k’al da shi abun sha’awa taja ta tsaya, bata ankara ba taji saukan wani zureriyar wutsiyar maciji🐍, ko kaɗan hakan bai tsoratata ba, tunda ita ma macijiyar ce, d’aga idonta ta yi saman bishiyar da wutsiyar macijin ya sauko mata, ta kalli yar uwarta wanda dukkanta macijiya ce,a hasale ta ce

” *AZIMA!!?* me yasa kika son kashe mutane kwanan nan ne kam?” macijiyar da aka kira da Azima a hankali ta sulalo daga saman bishiya ta kanannaɗe yar uwarta tana lasarta da harshe, hannu dayar tasa ta ture kanta a macijiyar, sannan ta ce

“Azima tambayarki fa nake yi?” gefe ta koma ya yinda ta saki wani huci ta girgije nan ta zama rabi mutum rabi macijiya, daga ƙugunta abun da ya yi sama mutum ce, daga kugunta abun da ya yi ƙasa macijiya ce.

Dariya ta sheƙe da shi cikin wata murya mai amo da rashin dadin sauraro, sai jijjiga take yi tana naɗe jelar macijinta ta ce

” *AZIZA!* bana mantuwa kuma bana yafiya!! Duk wanda ya shiga gonata sai na hallaka shi, sai na ga bayansa ko ma waye! Duk wanda nake kashewa sun tab’oni ne! Dan haka bana bukata ki din ga tuhumata akan abun da kike da masaniya a kai”

“Amma Azima kisan ya yi yawa! Da an miki laifi kaɗan sai kisa? So kike yi sai an gano mu ba mutane bane macizai ne mu a kore mu a gari?” 

Rintse blue eyes dinta Azima ta yi sannan ta buɗe tana zaro harshenta suffan na macizai sak ta ce

“Ina so na bar wannan alk’aryan, ina so na shiga cikin gari wanda yake da al’umma da yawa ta yadda zan tarwatsa su!” girgiza kai Aziza ta yi ta ce

“Ke nan za ki iya tafiya ki bar su Baffa da Hajja?”

“Me zai hana Aziza!? Ina da burin shiga cikin jama’a masu yawa duk da na san ni din ba mutum ba ce!”

“Shigarki jama’a ba alkhairi bane Azima, dan haka ki bar wannan maganar ki zo mu tafi gida kar mu koma mu samu Baffa ya dawo ya titsiye mu da tambaya daga ina muke, amma dan Allah ki koma mutum tun daga nan” Aziza ta faɗa tana yin gaba, dariya Azima ta yi a madadin ta zama mutum kamar yadda aka ce mata sai ta rikiɗe ta zama katuwar macijiya mai sheƙi da ban tsoro,   ko da Aziza ta juya ta ganta a haka girgiza kai ta yi, ba tare da ta ce mata uffan ba.

Sai da suka kusan isowa gida kafin ta girgije ta zama mutum, yadda yar uwarta Aziza ke tafiya haka ita ma take tafiya, mayafinta da ta ajiye ne kusa da gida ta dauka ta yi irin lullub’in da yar uwarta ta yi, su na yin wannan lullub’i ne saboda idanunsu da yake abun tsoro barin ma kwayar idon Azima blue, ita kuma Aziza idon mage mai fari-fari, ko kaɗan basu da baƙin ido,shi yasa Hajja mahaifiyarsu ta basu su din ga lullubi, shi yasa idan sun yi lullubin suke saukowa da dogon gashinsu ta gefe ya rufe musu gefen fuska, ga shi dai alk’aryan duk fulani ne kuma kyawawa, amma duk fadin yankin kwana babu mace ko namijin da ya kai su *AZIMA DA AZIZA* kyau.

Ko sallama basu yi ba suka shiga gidan suka iske mahaifiyarsu Hajja a jikin murhu tana aikin hura kara, Aziza ta ce

“Sannu da aiki Hajja” dagowa ta yi ta kalli kyawawan yan biyun nata ta ce

“Yauwa sannu Aziza, daga ina ku ke haka? Tun safe fa ku ka fice a gidan nan”

“Amm Hajja muna rafin jimulo” murmushi Hajja ta yi ta kalli Azima wanda idonta yake kan garin Mahaifiyarta, haka kawai take ji ta watsawa garin dafi, Aziza ta ce

“Hajja karan ya ƙi kamawa ne?” 

“Eh Aziza ya ƙi kamawa wallahi ga idona ya yi ja yana min zafi”

“Ayya sannu Hajja bari na hura miki!”

“Yauwa yar albarka hura min, Azima lafiya kuwa kika ƙurawa garin da zamu yi tuwo ido?” murmushi ta yi ta ce

“Lafiya lau Hajja” girgiza kai Hajja ta yi ta duƙa ta shige bukka, ita kuma Aziza Hajja na shiga bukka ta rufe idonta ta rintse nan idon ya dawo ja, bakinta ta buɗe ta fiddo da turirin ta hura a murhu nan kuwa ya kama da wuta, Azima kuwa wajan garin ta je ta bude bakin tana shirin zuba dafi sai ga sallamar Baffa, da sauri ta mai da harshenta, amsa sallamar Baffan suka yi tare yi masa sannu da dawowa ya amsa, fitowa Hajja ta yi,ita ma ta ma sa sannu da dawowa tare da shinfiɗa masa tabarman kaba, ya zauna, Aziza ta ɗiba masa ruwa ta kawo masa, sannan suka zauna dukkansu.

Sai da Baffa ya sha ruwan sannan ya saki ajiyar zuciya, cikin fulatanci Hajja ta ce

“Baffan Azima da Aziza lafiya kuwa?”

“Ina kuwa lafiya, wannan alk’arya ya kafu tsawon shekaru sama da hamsin, anyi gwagwarmaya da aljanu da mayu, amma a yanzu bala’in da yake tunkaro wannan alk’arya ya yi yawa, ina wannan shahararren mai kama macizai din nan, Ilu Mai Macizai?” Hajja ta ce

“Eh na ganesa,waye bai san Ilu mai Macizai ba”

“To shi ma an kashesa yau” salati Hajja ta sa tana tafa hannu ta ce

“Hande in bone ni Jamila, yanzu shi ma Ilu mai macizai an kashesa?”

“Eh har ma anyi masa jana’iza an binnesa, ga shi duk macizan da ake kamawa babu wanda bakinsa ya yi dai-dai da saran da ake samu, ga shi yanzu har zargi ya fara shiga tsakanin mutane da mutane, yanzu haka mai gari ya yiwa Jarman Macizai aike da wasiƙa,kin ganesa?”

Hajja ta riƙe hab’a alaman tunani ta ce

“Jarman Macizai ba wannan na yankin al’karyan jimo ba?”

Baffa ya ce

“Eh shi dai, ya ma amsa da gobe zai zo, zai taho da ruwan wani magani wanda za a ba wa kowa ya sha wanda hakan ne zai bayyana waye ba mutum ba a cikin al’umman yankin kwana, kin san titsiyeni aka yi a kan su Azima da Aziza, wai yarana basu abu irin na mutane, shi ne za ayi wannan gwajin” wani firgita Azima har ma da Azizan suka yi, suka kalli juna, ba tare da iyayensu sun san halin da suke ciki ba,tuni idon Azima ya kara komawa blue sosai, nan ta kalli fatar jikinta ta ga ta fara zama blue da sauri ta miƙe ta shige bukka, ita ma Azizan tashi ta yi, Hajja ta ce

“Dan kawai yara basu mu’amala da kowa, sannan idonsu ba baƙi ba shikenan sai a saka mun yara a gaba?” Baffa ya ce

“Amma kin san dai har da maganar aurar dasu, bisa al’ada ta wannan yanki namu yara da sun shekara 11 ake aurar dasu, yanzu kuma su Azima da Aziza su na da shekara 15 kin ga kuwa dole a saka musu ido mun ƙi aurar dasu, ga shi kullum Arɗo sai ya min magana” tabe baki Hajja ta yi ta ce

“Allah ya kyauta amma ai aure lokaci ne” ta miƙe taje duba ruwan tuwonta.

A bukka kuwa sadda Azima ta shiga nan kasanta ya koma macijiya har sai da ta cika bukka din, kalar fatarta ta koma blue, Aziza ce ta biyo bayanta ta ce

“Azima ki koma dai-dai kar Hajja ta shigo ta ganki haka fa?”

A hautsine Azima ta ce

“Dole na kashe Jarman Macizai! Nayi alkawari sai na ga bayan wanda yake shirin ya san su waye mu na asali!.”

“Ba ki da hankali ne Azima? Jarman macizai za ki kuma kashewa? To bari kiji! Kin ga wannan kashe-kashen shi zai sa a gane su waye mu, dan Allah Azima karki kashesa, bana son kisan da kikeyin nan” Aziza ta faɗa tana bin Azima da kallo, cikin huci Azima ta ce

“To tsammaninki me zai faru? Idan har jarman macizai ya kawo maganin gwaji dan a tabbatar da su waye ba mutane ba? Ke a tunaninki mutanen yankinmu zasu barmu a raye ne? Ina kashemu zasu yi, dan haka kafin hakan ta kasance ni nan zan kashe Jarman Macizai kuma ba ki isa ki hanani ba” Azima ta fada tana komawa mutum tare da ficewa a bukkan, tana fitowa hanyar waje ta nufa Hajja ta ce

“Azima ina kuma zaki je bayan baku jima da shigowa gidan ba?” kafin Azima ta yi magana Baffa ya fito daga kewaye yana fadin

“Ban hanaku fita sakakan ba Azima? Ina za kije?” cikin in-ina da kame-kame ta ce

“Zan duba abu na ne a nan waje” Baffa ya ce

“Ba za ki duba ba koma ciki” haɗe rai sosai Azima ta yi tare da yiwa Baffa wani irin kallo ta koma fuuu, da kallo Baffa da Hajja suka bi Azima, jiki a sanyaye Baffa ya koma ya zauna, tunanin abunda ya faru shekara ashirin shike dawo masa kwakwalwa, kar dai ace fansar da *Banju ya ce zai dawo ya daukar wa kanwarsa Bahula da kansa shine ya dawo dauka kan yaransa!?* Haqiqa shima zuciyarsa ta fara yi masa saqe-saqe a kan yaransa ba cikakkun mutane bane amma baya so zarginsa ya tabbata, rintse ido ya yi yana karanto kalmar “Innalillahi wa inna ilayhirrajiun!” kallonsa Hajja ta yi ta ce

“Lafiya kuwa Baffan Azima da Aziza?”

    “Haqiqa Jumala ina jin tsoro!” 

“Tsoron me fa Baffan yan biyu?”

“Inajin tsoron furucin Banju lokacin da zan kashesa maganarsa ta karshe, ko kin manta da kalman da ya ce….” Baffa bai karasa ba Hajja ta dakatar da shi

“A’a Baffan Azima da Aziza! Karka yiwa yarana baki! Taya wa inda suka mutu shekara ashiri a ce sun dawo? Azima da Aziza dai ni na haifi yarana! Kuma ni mutane na haifa, kwata-kwata wannan maganar bai kamata ace ya fito daga bakinka ba, kai da kanka ka fara zargin yaranka to ba dole jama’ar gari ma su fara zarginsu!” Hajja ta faɗa cikin sosuwar rai, girgiza kai Baffa ya yi ya ce

“Ba haka bane Jumala, amma dai jikina ya yi sanyi! Allah ya kaimu gobe jarman macizai zai zo ya warware komai” ita dai Hajja ba ta sake cewa kala ba, illa aikinta da ta ci gaba da yi, Azima kuwa tana saman bukka a macijiya tana jin maganganun Baffa, a ranta take ayyana yadda zata kawar da Baffa!.

      🍃🍃🍃🍃🍃

Washe gari tun kafin garin Allah ya waye Azima ta sulale ta fice, hanyar yankin Jimo dai-dai kan layin shigowa yankin kwana a kan wata babbar bishiya ta kwanta ta nannaɗe idonta sun kara komawa blue, tana jiran isowar jarman macizai, awanta kusan uku kafin ta hangosa, wani murmushi ta yi mai tattare da zallar mugunta kafin ta sauko ta koma mutum, tsayuwa ta yi bayan ya gama shigowa yankin kwana.

     Yana kan tafiya akan dokinsa a hankali ya hangi budurwa tsaye a hanyarsa,magana ya hau mata amma shuru, tana tsaye da lullubi, saukowa ya yi a kan dokin ya tunkaro inda take tsaye, sai da ya zo kusa da ita kafin ya ce

” *MUTUM KO ALJAN!?”* 

     Murmushi ta yi tana lankwasa harshe ta ce

” *RUWA BIYU!”* sannan ta juyo ta yaye mayafin da ta lullube jikinta ta jefar, jarman macizai na ganin idonta ya yi saurin ja da baya, dariya Azima ta sheqe da shi ta ce

“Na ga bai kamata ace kasha wahala ba wajan zuwa gwajin wanene wanda ba mutum ba a wannan yankin! Gani na zo da kaina dan dakatar da kai! Ba zaka shige ba sannan ba zaka koma ba!” da sauri jarman macizai ya yi baya dan dauko kayan aikinsa tsalle daya Azima ta yi ta zama macijiya ta cakume jarman macizai nan suka hau kokawa, duk yadda yaso kwace kansa daga hannun Azima ya kasa, daga karshe ta rufesa da sara, sosai ta yi masa jina-jina sai da ta ga ya daina mutsu-mutsu sannan ta sakesa ta sulale ta yi hanyar rafin jimulo, tana isa rafin ta hau kyalkyala dariya nan ta zube kusa da rafin.

       🍃🍃🍃🍃🍃

      A cikin unguwa kuwa ana nan ana jiran isowar jarman macizai, tun ana sa ran ganinsa takwas har goma, inda a karshen mai unguwa ya ce aje a duba ko lafiya a binciki hanya aka tura mutum uku.

    Ai kuwa can suka gano gawar jarman macizai a yashe cikin jini, cikin tashin hankali suka juya da mugun gudu suka koma suka sanar da jama’ar gari an kashe jarman macizai.

    Fadin tashin hankalin da mai unguwa da jama’ar gari suka shiga b’ata lokaci ne.

🍃🍃🍃🍃

Fitowa Aziza ta yi daga bukka dan tun sadda taji motsin yar uwarta jikin dare kafin garin Allah ya waye  jikinta ya bata ta tafi kashe jarman macizai, abunda yasa bata yi yunkurin bin bayanta ta dakatar da ita ba sabida tasan dole Hajja da Baffa su leƙo duba lafiyarsu, tana fitowa dauke da murmushi a fuskarta Hajja ta ce

“Aziza ke kin tashi? Azima ta farka ta yi sallah kuwa?” tsilli-tsilli da ido Aziza ta fara kafin ta ce

“Eh Hajja ta tashi ta yi har ma ta fita wai ta je rafin jimulo” Aziza ta karasa maganar da in-ina sabida da asuba da Hajja ta shigo tada su kara Aziza ta jera kusa da ita ta yadda zata ga kamar Azima ce ke bacci, dan lokacin da Azima ta fita Aziza ta ji motsinta tsoron kar su fita duka a gane yasa Aziza hakura ta kwanta, dan Baffa kunnuwansa akwai saurin jiyo abu.

Kallon Aziza da kyau Hajja ta yi kafin ta ce

“Me ku ke zuwa yi kullum ne a rafin jimulo?”

   “Ba komai Hajja kawai rafin akwai dadi ne, ga iska mai dadi, Hajja kin manta sadda kike kai mu muyi wasa?” murmushi Hajja ta yi ta ce 

“Eh na tuna, yanzu dai je ki kirawo Azima ku zo kuci abinci” 

“To Hajja, Baffa ya fita ne?” Aziza ta tambayi Hajja kamar bata san Baffan ya fita ba, Hajja ta ce

“Eh ya fita kin san ai jiya yace yau Jarman macizai zai zo, yace min idan yazo zai zo ya kiramu muje gabadaya ayi gwaji” Aziza ta jinjina kai tana fadin “to Hajja bari naje na kira Azima kafin Baffa ya dawo” 

“To a dawo lafiya,ki tabbatar kinyi lullube da kyau fa” 

“To Hajja” Aziza ta fada tana ficewa jiki a sanyaye, tana fita da gudu ta yanki rafi inda tasan Azima ba zata wuce can ba.

   Tana zuwa ta sameta kwance a kusa da rafi.

Hannnu tasa ta janyota ta ce

“Kin kashesa ko Azima? Na ce kin kashesa ko!?” dariya ta kyalkyala cikin amo marar dadin sauraro ta ce

“Ai na gaya miki Aziza sai na kashesa!” 

Rike kai Aziza ta yi ta ce

“Me kika so ki zama ne kam Azima?”

“Bana son ganin zaman lafiya a wannan yankin! Na fi so ayi ta b’arin jini! Ina so na haɗa maƙotan yankunan nan faɗa, duk wani mai kama macizai wanda za a yi masa aike ya zo yankin nan sai na kashesa! Kin ga daga nan za a fara yaƙi tsakanin yankuna da yankuna, sannan dama akwai y’ar tsama tsakanin yankin kwana da yankin tudu da kuma yankin Ja’i nasan kuma dole mai unguwa zai bukaci taimakonsu, duk wanda aka turo ni kuma zan kashesa! Na tabbata daga lokacin zaman lafiya ya kare, Baffa shine jarumi na farko a wannan yankin wanda da shi aka yi gwagwarmaya kinga kuwa ba mamaki a wajan yaƙin a kashesa!”

      🍃🍃🍃🍃

Zaro ido Aziza ta yi tana kallon Azima kafin ta ce

“Na rasa dalilinki na son ganin bayan Baffa! A yadda na fahimceki, ke ba ki ƙi kowa ya mutu ke ki rayu ba, idan kika samu dama na tabbata za ki kashe Baffa”  dariya Azima ta kyalkyale da shi tana kewaye wajan kafin ta koma ta haɗe rai sosai ta ce

” *AI BA YAU BANE KAWAI NA SHA GWADA HAKAN!*  ko a yanzu na samu sarari sai na kashe Baffa! Ko kin manta na sha yunkurin kashesa!? Lokuta da yawa ke ce kika katse min burikana! Ga shi ke ban san ya zanyi dake ba! Ke ta biyu na ce! Ba zan iya kasheki ba! Sabida duk muguntar gubana naki yafi nawa! Kuma ina sonki yar uwata! Da ace nike da karfin dafin da kike da shi da na jima da shafe wannan yankin kakaf dinta!” Azima ta fada tana daga hannuwanta sama.

    Aziza ta girgiza kai ta zauna a kasa tare da fashewa da kuka ta ce

“Azima ba zan taba bari ki cutar da Baffa ba,ko da kuwa zaki iya,ni dai a gaskiya inaji a jikina kamar ni da mutum ce! Ban san a garin yaya muka zama macizai ba, miye dalilinki na son kashe Baffa Azima!?” Aziza ta faɗa tana haɗa kai da guiwa tana ci gaba da kuka,duk sadda ta kalli jikinta ta ganta a macijiya tana jin zafi a zuciyarta, ta yi nisa sosai a kuka ta ji wani irin murya na namiji wanda yake abun tsoro an bata amsar maganarta.

     ” *ZUNUBIN DA BAFFANKU YA AIKATA NE YAKE BIBIYARKU!, TARE DA GOYA MASA BAYAN DA JAMA’AR YANKIN NAN SUKA YI!*” da sauri a matukar firgice Aziza ta dago tana waige ta ga daga ina ne maganar ya fito? Amma bata ga kowa ba illa Azima dake wasa a cikin rafi kana ganinta zaka san tana cikin nishaɗi, ta zama macijiya ta koma ta zama mutum.

Sauri tashi tsaye Aziza ta yi tana waige a fili ta kara furta kalman da ta ji “Zunubin da Baffanmu ya aikata? Me Baffanmu ya yi kuma?” tambayoyi ne maqil a ranta amma babu mai bata amsa, ko dai zata je ta tambayi Baffa ne? Kai amma kuma idan ta yi haka za a gane su ɗin ba mutane bane, riƙe wuyanta ta yi jin kamar zuciyarta yana shirin fitowa bakinta, kallon Azima ta yi ta ce

“Azima ki zo muje gida”

“Tare muka zo dake ne?” 

“Idan ma ba tare muka zo ba Hajja ta ce mu dawo tare yanzu, kar Baffa ya dawo….” Aziza ba ta karasa ba Azima ta fito tana fadin

“Ke komai ki ce Baffa?” 

“To idan ban kira sunan Baffana ba sunanki zan kira?” murmushi Azima ta yi ta ce

“Yau bana jin yin faɗa dake, dan yau ina cikin farin ciki, nasan idan sako ta iske sarkin yankin jimo an kashe masa Jarman Macizai me kike tunani zai faru Aziza?”

“Ban sani ba!” Aziza ta faɗa a ƙufule ta yi gaba, ita ma Azima a macijiya ta hau bin bayan Aziza, yau tsananin takaici ya hana Aziza ta cewa Azima ta koma mutum, Azima kuwa da gangan take wani abun dan Aziza ta mata magana.

A macijiya ta shiga gidan Allah ya so Hajja na bandaki, zama Aziza ta yi ta buga tagumi, Azima kuwa bukka ta shige, bayan Hajja ta fito ta ga Aziza da tagumi ta ce

“Ah Aziza kun dawo?” shuru Hajja taji dan Aziza ta yi nisa cikin tunani, sai da Hajja ta tabota tukunna ta dawo hayyacinta ta ce

“Na’am Hajja magana kike yi ne?”

“Tunanin me kike yi haka Aziza?” murmushi Aziza ta k’wak’ulo ta ce

“Abunda yake faruwa a mahaifana shine yake tayar min da hankali Hajja”

     “Karki ce zaki saka hakan a ranki,addua ita ce mafita,duk abunda ya yi tsanani maganinsa Allah” kuka Aziza ta fashe da shi ta rungume Hajja ta ce

“Dole ne na saka a raina Hajja! Idan mun san abunda ya faru yau ba bamu san me zai faru gobe ba Hajja!” sosai Aziza ke kuka yayinda hankalin Hajja ya tashi, Azima ce ta fito daga bukka dauke da abinci a hannunta zama ta yi ba tare da ta kalli Hajja ko Aziza da ke kuka ba,abincinta ta hau ci hankalinta kwance, Hajja ta kalli Azima wacce ta jima da gane ita damuwar wani bai dameta ba, ta ce

“Azima meke faruwa da yar uwarki!?” 

Cikin halin ko in kula ta ce

“Oho mata! Tana son ɗorawa kanta damuwar da bata da mafita a kansa, ta ga zata iya ne, Hajja ki daina damun kanki a kanta!” Hajja zata yi magana sai ga Baffa a fujajan ya shigo ko sallama babu, da sauri hankalin Hajja da Aziza ya koma kan Baffa akasin Azima da ta yi kamar bata san da shigowarsa.

    “Baffan yan biyu lafiya kuwa na ganka a cikin wannan yanayin?”

       Sharce zufa Baffa ya yi ya ce

“Jumala ina kuwa lafiya! Ku zo muje gaban gari ana neman dukka mutanen yanki, kin san an kashe Jarman Macizai kuwa?” hannu Hajja ta zuba a kirji tare da fadin

“Ma’asabumin Musibati qalu Innalillahi wa inna ilaihirrajiun! An kashe jarman macizai to waye kashesa!?” 

     ” *MACIJI! SARAN MACIJI NE A JIKIN JARMAN MACIZAI!*” Baffa ya faɗa yana sauke idonsa a kan Azima wanda hankalinta sam baya kansu, Hajja ta ce

“Ba ri na dauko mayafina mu tafi gaban gari din” Hajja ta karasa maganar tana shigewa bukka, Aziza kuma tana gyara mayafin kanta hankalinta a tashe! Baffa ya ce

“Ke Azima? Ana gaya miki mahaifarki babu lafiya amma kina zaune hankalinki kwance ba tare da kin nuna damuwarki ko a fuska ba kina cin abinci! Za ki tashi ne ko sai na saka sanda na roɗe miki shingen kafafunki nan masu kama da fuffuken sauro!” Baffa ya faɗa yana yin kan Azima da sauri ta tashi tana huci tare da juya baya, hanyar randar kasan dake tsakiyar gidan taje ta ɗibo ruwa a kwarya tare da fakan idon Aziza ta watsa dafi a ciki, sannan ta juyo tana kallon Baffa a ranta take fadin

“Ba zan taba samun salama ba idan har ban kasheka ba!”  tunkaro Baffa ta yi har ta zo gabansa tana tura baki ta ce

“Baffa na ga alama kan ka ya dau zafi kaɗan sha ruwa zuciyarka ta huce! Baffa ita fa damuwar duniya bata karewa barin ma idan mutum yasa hannu ko nace mutane suka sa hannu suka jawo bala’i wa kansu, sannan dole akwai abunda ku ka aikata ma wasu yake bibiyarku! Dan haka Baffa a koma a yi tunani da kyau, ga ruwan ka sha” ta mika masa tana sunkuyar da kai kasa sai kace wata ta Allah, shuru Baffa ya yi yana son yayi tunani a kan maganar da ta fada amma tashin hankalin da suke ciki ya ƙi basa damar haka, hannu yasa ya karbi ruwan caraf idon Aziza ya sauka a kan ruwa ta hangi dafi, cikin azama ta ce 

“Baffa wani ruwa kuma zaka sha? Ka manta Azima ita bata damuwa da damuwar wani? Kawo ruwan nan Baffa” Aziza ta karba, wani kallo ne Azima ta bi Aziza da shi jikinta har na tafasa tsananin takaicin abunda Aziza ta yi, Aziza na karban ruwan da gangan ta yi tuntube ruwan ya b’are kwaryar kuma ta riɗata da dutse ta fashe, cije baki Azima ta yi, idonta ya kara rinewa tana shirin tunkaro Aziza wacce itama ke kallonta ko gizau bata yi ba, Hajja ce ta kara katse mata hanzari ta fito tana fadin

“Yi hakuri Baffan yan biyu! Na zubar da wake ne na tsaya kwashewa shiyasa ban fito da wuri ba,muje” gaba Baffa ya yi Aziza ta bisa a baya, Azima ta zo fita Hajja ta ce

“Ina mayafinki?”

“Ba zan saka ba! bana jin saka wa Hajja! Raina a b’ace yake karki min maganar wani mayafi!” daskarewa Hajja ta yi jin amsar da Azima ta bata,ita ma Azima bata san lokacin da ta faɗi ba  dan bata taba yiwa Hajja magana haka ba,ganin Hajja ta tsaya tana kallonta ne yasa ta cewa “yi hakuri Hajja bara naje na dauko,kuyi gaba zan zo a baya” Hajja dai bata iya cewa komai ba illa bayan su Baffa da Aziza da ta bi wanda sun yi gaba abunsu.

    Su na kan tafiya Aziza ta ce

“Baffa?”

“Na’am Aziza yaya ne?”

“Baffa baka taba bani labarin kafuwar mahaifata ba, kullum kana cewa an sha gwagwarmaya da aljanu da mayu, amma baka taba bani labarin kalar gwagwarmayen da ku ka sha dasu ba”

“Yo to banda abunki Aziza ana cikin wannan tashin hankali kina maganar labari? Abunda ya kafu sama da shekaru hamsin? Ki bari Allah ya bamu ikon dakatar da wannan ambaliyar wutar masifan dake tunkaro wannan yankin” shuru Aziza ta yi ba tare da ta sake magana ba, da haka har suka karasa gaban gari inda cincirindon fulani suke tsaye kowa ka gari hankalinsa a tashe, har anyiwa jarman macizai jana’iza an binnesa.

    Ana ta shawaran yadda za a rubutawa sarkin fulanin yankin jimo sakon cewa an kashe jarman macizai wanda yankuna sun san shi jarumi ne, idan ka cire yankin ja’i da yankin tudu za a iya cewa babu wani jarumi wanda ya shahara a kama macizai sama da jarman macizai, amma a yankin Ja’i akwai wanda har aljanun macizai yana kamawa tsananin shahararsa wanda har laƙabi ake masa da INNU MACIJI, daga shi kuma sai na yankin tudu wanda shike takawa Innu Maciji baya wato IRO MAGANIN MACIZAI daga shi sai wanda aka kashe na yankin jimo wato JARMAN MACIZAI, lokacin da aka raba kambun girma na wa inda suka shahara a kama macizai aka ba wa INNU MACIJI lamba daya, aka ba wa IRO MAGANIN MACIZAI lamba ta biyu sai kuma JARMAN MACIZAI lamba ta uku, har ta Ilu mai Macizai da Azima ta kashe na yankin kwana shine aka ba wa lamba ta shidda, sannan aka rabawa na ƙasa dasu, tashin hankalin da yankin kwana ke ciki shine rashin jituwar da basu da shi da yankin tudu da yankin ja’i, barin ma yankin ja’i tsatstsauran gaba ce daɗaɗɗiya, dan kuwa an sha gasan kisa a tsakani, yankin tudu kuwa dan sarkin yankin ne ya zo yankin kwana ya yiwa yar yankin fyaɗe bai kyaleta ba har sai da ya kasheta! Hakan ce tasa ARƊO ya bada umarnin a kashesa shi ma,aka gille masa kai aka turawa mahaifinsa da shi daga nan gabar ta soma, yanzu taya zasu fara neman taimakon Yankin Tudu ko kuma yankin ja’i? Yanzu dai ba shi bane tashin hankalin, tashin hankalinn shine yadda zasu fara tunkaran yankin jimo da sakon an kashe jarman macizai.

@@@@@@@

Su Baffa sun iso ana kan shawara ba a tsaida mafita ba, sai da Baffa ya karaso aka sake yin shawara a kan a rubuta sako a tura mutum huɗu da suje yiwa yankin jimo ta’aziyya tare da rigan Jarman Macizai wanda yake jina-jina da jini, sannan ayi musu bayanin abunda ya faru bai kai ga yin aikin da yazo yi ba aka iske gawarsa, tare da sakon ban hakuri iri da kala daga wajan mai unguwan yankin kwana da kuma sarkin fulanin yanki kwana tare da Arɗo, hakan ce ta kasance aka tura mutum huɗu izuwa yankin jimo, tare da kayan Jarman Macizai da kuma dokinsa da takwabinsa.

     Aziza na tsaye a gefe da lullubi hawaye ne cike a idonta,ba dan komai ba illa su na zuwa wajan aka fara darewa ana matsawa babu wanda ya tsaya kusa da ita.

   Azima kuwa za ta zo yau ne gobe ne shuru, har aka gama tattaunawar da za ayi Azima bata zo ba.

     Bayan an fara watsewa Arɗo ya kira Baffa gefe ya ce

“Magaji? A gaskiya ba zan boye maka ba, ka binciki yaranka! Barin ma wannan yarinyar taka Azima,jiya an kawo min wani magana a kanta, bana son na tsawaita zargi dan babu kyau, sannan jikokinane kasan dai ba zan so abunda zai cutar dasu ba, amma ya kamata mu san abunyi,kasa ido sosai a kansu, bana so na kirawo Jumala dan duk abinda za a gaya mata ba yarda zatayi ba, sannan bayan sallar isha’i za a zauna ayi tattauna a faɗar mai unguwa, zamu je neman alfarma a yankin tudu” da sauri Baffa ya ce

“Arɗo yankin tudu kuma?”

“E Magaji, yankin tudu bamu da wani mafita wanda ya wuce hakan”

“To amma Arɗo kana ganin anya Sarkin Tudu zai sauraremu? Ko ka manta abunda ya shiga tsakanin yankinmu da nasu ne? Ɗansa yazo ya yi laifi a yankin nan an masa hukunci hakan ne ta haifar da gaba mai tsauri a tsakani, bana tunanin Sarkin yankin tudu zai yarda Iro Mai maganin macizai zai zo taimakonmu, kana gani duk wasu masu kama macizai da muke dasu a yankin nan sun mutu, a gaskiya inajin tsoron abunda zaije ya dawo, kar bamu gama da wani yaƙin ba mu sake kunna wani, a gaskiya bana so duk shawaran da za ayi ace za a bukaci taimakon yankin tudu da yankin ja’i” 

    Nauyayyiyar ajiyar zuciya Arɗo ya sauke ya ce

“To Magaji mai zai hana kai ka maida hannun agogo baya?”

“Bangane ba Arɗo?”

“Ina nufin ka dawo yadda kake a da dan mu taimaki yankinmu, Kayan aikinka da kaje ka binne kaje ka hakosu saboda……” girgiza kai Baffa ya hau yi yana ja da baya, ya ce

“A’a Arɗo na riga da nayi alkawari ba zan sake ba, har kwanan gobe ban manta da kuskuren da na aikata bisa tsautsayi a baya ba, abun shekara ashiri amma a yanzu gani nake yi yanzu abun ya faru, Arɗo ba a son raina na kashe *BANJU* ba, na kashesa ne sabida shafe mutanen yankin nan da ya fara, sannan idan baka manta ba yace zai dawo daukar fansa a kaina da mutanen yankin nan! tunda na kashe Banju nayi alkawari na dai na! duk wani abu wanda na gada daga gareka da kakanni! Dan Allah Arɗo a bar wannan maganar”

   🍃🍃🍃🍃🍃

WLH IDAN NAYI POSTING A GRP BAN CIKA BI TA CIKIN GRP DIN BA, AKWAI WASU GRP DIN MA BANA BUDEWA INDAI BA GOGE SAKONNI ZANYI BA, IDAN KINA SON BIYAN KUDIN BOOK DIN NAN KI TUNTUBENI TA LAMBAR WAYATA TA SAMA, IDAN TA ACCT NE KO KATI.

AND PLS&PLS 4 ALLAH’S SAKE, IDAN KIN SAN BA BIYA ZAKIYI BA KARKI KIRANI KI GAYA MIN MAGANAR DA BA HAKA BA, A BOOK DIN NAN DAI BAN CE DARI BIYAR  KO DARI UKU BA,HAR TA DARI BIYU MA BANCE BA, DARI NE NACE DAN MASOYANA,BAN SAKA TA INDA BA ZAKI IYA BIYA BA, SO PLSS A DINGA FAHIMTA,DAN WATA MAGANA JIYA BAI MIN DADI BA SAM.👏🏻

    

MASU KIRA NA DAN KARA MIN ƘWARIN GUIWA NA GODE,NA SAN ZAKU GANI DIK DA BAN SANKU BA AMMA KUNA RAINA🌹🤝🏻

COMMENTS AN SHARE

BY MOMYN AHLAN

Back to top button