Hausa novels

Zakuna Biyar Page 11 By Princess Teema

Ɗakin da yakasance mallakin ɗaliban aji biyu Madam ta kaita, tin da suka shiga Seraph ke faman kallon ɗakin kamar ta ga wani abin daga wata duniya. Bed guda huɗu ne a cikin ɗakin, uku yara na kwance a kai, ɗaya babu kowa. A nan Madam Rohisha ta kaita, sannan ta kira dikkan ƴan’matan dake kwance a saman gadonsu kan su zo ga bakuwa sun yi. Su ukun dik suka sauƙo, ƴan yara ne da basu wuci Seraph ɗin ba.A wajen gadon suka zazzauna suna kallon Madam cike da kulawa, ita ma cike da kulawa ta ce. “Wannan bakuwa ce, ku kula da ita sosai, Aana kinga kin fi su girma ko? Ki kula da su”…… Wacce aka kira da Aana yarinya ce da zata iya kai 13 years, su kuma kun ga a lokacin 9 to 10 suke, ba’a cika 10 ciff ba.Kama hannun wata kyakkyawar yarinya Madam ta yi, ita ma ba zata wuci 11 years ba, cikin sanyin murya ta ce. “Rimsha, wannan ita ma kamar ke take, she don’t have anyone, bata da Father and Mother, take care of her kin ji? Ki kwarara mata gwiwa”. Da sauri Rimsha ta ɗago kai, dan ta san zafin rashin iyaye, mahaifinta ya rasu, mahaifiyarta babu wanda yasan in da take, a hannun kakanninta take rayuwa sai uncles ɗinta da suka tsani ganinta. Sanadin mahaifiyarta mahaifinta ya rasu, shiyasa dangin mahaifin nata suka tsaneta, kakaninta da suka haifi babanta ne kawai suke kaunarta sai kuma wani Uncle ɗinta ɗaya Ustadz mai zuna Faryan, amma saura dik basu sonta, sun ɗaura laifin mahaifiyarta a kanta, wai in sun ganta mahaifiyarta kawai suke tinawa da ta yi breaking heart na ɗan uwansu har rai ya yi halinsa. Sun tsani ta zo kusa da su, ganin tsanar ta yi yawa ne yasa kakanta ya kawota boarding school dan ta rage zafi, in ta daina ganinsu watakila komai zai warware a zuciyanta.Ta kuwa yi sa’ar shiga hannun Madam Rohisha, malama mai kyan zuciya, ita ta dinga karfafata tana lallashinta har ta mantar da ita bala’in tsanarta da dangin babanta suka yi, gata yarinya kyakkyawa son kowa kin wanda ya rasa, uwarta European ce, kun san turawa idan suka aureka, da zarar baka da kuɗi haɗa kayansu zasu yi su gudu su barka, ko da kana sonsu kamar ka mutu, su dai zasu gudu ne, amma abin mamakin a nan shi ne ita Rimsha mahaifinta nada mahaukatan kuɗi, dan kakanninta yanzu haka haya suke yi a C-P, kun kuma san dik wanda yake haya a Crystal Palace kuma ai kunga kuɗi kuwa ba’a magana, sai dai sun rasa dalilin da yasa mahaifiyarta ta gudu ta bar daddynta, har yau kuma suna nemanta basu ganta ba, abin da ɗaure kai.(Wani rawa kuke tinanin Rimsha zata taka a labarin nan? Kun san bana yabo ko magana a kan wanda bashi da matuƙar muhimmanci a labarin nan, okey mu je zuwa.)Kama hannun Seraph Rimsha ta yi tare da cewa. “Zan kula da ita sosai Madam”. Sosai Madam ta ji daɗi tare da yi masu fatan alkhairi, sannan ta tashi ta fice ta basu waje. Saura yara biyu miƙewa suka yi suka koma wajen beds ɗinsu ba tare da sun yi wa Seraph magana ba, ita kuma Rimsha ta tayata suka shirya kayanta a cikin lokar wajen gadonta, suka shirya komai Rimsha na ɗan janta da hira tana karfafa mata gwiwa. Fuska ɗauke da fara’a Rimsha ta ce. “Your face is shining like a star, can I call you star lady or star girl?”……. Seraph dake ta ƙoƙarin tura kayanta cikin drawer ne ta amsa da. “Why not? Also your face is shining like mine, if you call me Star lady, I will call you star baby”…… “Most of people here are calling me beauty, but now when I saw you I realized that I didn’t deserve that name”……. “Why?”. Seraph ta tambaya. “Because you’re the really definition of beauty”……. Siririn one side smelling Seraph ta saki, bata sake cewa komai ba, suka cigaba da aiki a tare.A haka suka kasance, cikin ƙanƙanin lokaci suka yi mugun sabo da juna, Seraph ta fara sakin jiki da Rimsha, sauran dake ɗakinsu basa shiga harkarsu, kuma basa takura masu, kowa yana harkar gabansa ne, su je class tare su kuma dawo a tare, sun zama tamkar ƴan uwan juna, Madam Rohisha ta zama tamkar mahaifiyarsu. Dik karshen wata Champion yana kawowa Seraph ziyara haɗe da kayan cima na kwalam, sai dai bai taɓa haɗuwa da ita ba, office na director kawai yake zuwa ya basa ya fita.Idan an yi hutu yana turawa ne a ɗauketa a kaita wani gida, ita kaɗai kamar mayya haka take rayuwa a cikin wannan gida na tsawon hutu, da an buɗe school ya sanya a dawo da ita…… Yau ta kama Monday, kuma farkon sabon watan da suka shiga. Shirye suke cikin uniform ɗinsu. Mini sket ne zuwa gwiwa baki, da riga fari zuwa waist ɗinsu mai dogon hannu, kayan ya yi mugun yi masu kyau, sun fito sosai, a dokar makarantar ana ɗaure gashin kai ne gida biyu, jelar gashin a ɗaure da bakar rebon kalar sket ɗin uniform, sai kuma a zuba jelar a gefen shoulders ɗinsu, haka kuwa suke yi, yana ƙara fito da kyansu, sai santin ash hair ɗin Seraph kowa yake yi!.Suna rike da hannun juna ita da Rimsha, sun fito daga hostel zasu wuce class. Lokaci guda Seraph ta tsaya cak tamkar mai tinanin wani abu.Taɓata Rimsha ta yi tana faɗin. “Star lady meyasa kika tsaya a nan? Mu je mana!”…… Da sauri Seraph ta juyo da jikinta gabaɗaya ta kalli bayanta. Wani irin firgici ne ya bayyana a kan fuskanta, muryanta na rawa ta ce. “Uncle meyasa ka zo nan?”. Champion dake tsaye a bayanta ya zura hannaye a cikin aljuhun jacket ɗin jikinsa yana kallonta ne ya ɗan ɗauke kansa daga kallon nata. Mugun tsoronsa Seraph take ji. Da sauri Rimsha ta juyar da kallonta a kansa ita ma. Yana dai sanye da face mask a face ɗinsa, kuma da alama ba ainahin fuskansa bane wannan. Baya-baya Seraph ta fara ja tana son gudu ta bar wajen, dan zamanta a school ɗin nan har ta fara mancewa da su a rayuwarta kawai ya dawo, bata buƙata. Idanunsa a kanta ko kyaftawa babu, yana ganin yadda take ta ja da baya. Sai da ya bari ta ɗan yi nisa, tana ƙoƙarin juyawa da gudu ta bar wajen ya yi taku ɗaya ya damƙota ta ciki-ciki, dama yana ankare da motsinta. Ihu ta fara ƙoƙarin kurma mashi ya dakatar da ita ta hanye toshe mata baki, sannan ya ɗagata sama ya wuce da ita. Da gudu Rimsha ta nufi office na Madam Rohisha dan ta sanar mata da cewa wani ya ɗauke mata star ladynta.Shi kuwa bai direta a ko’ina ba sai a cikin motarsa, a gidan gaba ya sanyata tare da shiga driving side. Tana kokarin fita ya rufe motar tare da cewa ta natsu, ya yi maganar ne a natse sosai. Tsoronsa yasa dole ta natsu tsit. Zuba mata ido ya yi na ƴan mintoci, sai sharan kwallah take yi, violet eyes ɗin nan nata sun kara cizawa saboda kukan, pink lips ɗinta sai kerma suke yi alamar tsoro.”Me alaƙarki da hoton wannan dattijon da kika taɓa a ɗakin aikinmu before in kawoki nan?”. Ya faɗa babu alamar wasa a tattare da shi!. Cak ta dakatar da kukan nata, slowly ta ɗago da kallonta ta saci kallonsa, dan tsoron haɗa ido da shi take yi ma. “I don’t know him, kawai naga mammyna tana da irin hoton ne, ta sanya cikin frame tare da rubuta love of my life a jiki”…….. A takaice ya ce. “Are you Dr Hushaima’s daughter?”. Ya yi maganar da alamar mamaki a kan fuskansa, kuma da alama a ƙage yake da son jin amsa…….. Kai ta jinjina mashi alamar e. Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, lokaci guda ya ɗan ɗauke wuta, har wani irin huci mai zafin gaske ya furzar daga bakinsa, hannu yasa ya ɗan dafe gaban goshinsa, kamar ya shiga damuwa. Zuba mashi ido na ɗan lokaci ta yi, ganin bashi da alamar sake motsawa yasa ta ce. “Uncle should I go?”.Siririn ajiyar zuciya ya sauke, a sanyaye ya ce. “Just call me daddy”…… Tsare shi da ido ta yi, tamkar tana son karantarsa ne. Hakika ya shiga damuwa, yau ya shiga ɗakin aikin nasu ne yana binciken tsoffin hotuna sai ya kalli alamar an ja hoton an kusa ciresa, yasan kuma ita kaɗai ta shiga ɗakin shiyasa ya zo tambayarta, dan a dik hotunan dake ɗakin wannan kawai ta so cirewa, idan bata da alaƙa da hoton ba zata taɓa ba a cewansa. Dik yadda aka yi suna da alaƙa da ita, wannan hoto dai nasan kun fahimci daddyn Seraph ne a jiki, in kuwa haka ne kunga alama ta nuna su suka kashesa, ya ratso ta cikin aikinsu ne suka gama da shi, in kuma basu kashesa ba to dole ɗaya daga cikinsu ne shi, kila shima gangster ne.Kada ku manta ba’a san ainahin face ɗinsu ba, kila ma Champion ɗin nan ne shi, dan haka kawai ba zai ce ta kirasa daddy ba, in ma bashi bane to da wuya idan ba Lion bane daddyn nata, akwai dai matsala, ku duba yadda ya ɗauke wuta a take daga jin yar wacece ita!.”Daddy should I go?”. Ta faɗa cikin shessheƙa. Wani irin yawu ya haɗiye mai sauti tare da sauke ajiyar zuciya jin ta kirasa da daddy, har cikin ransa ya ji sanyi. Hannayenta ya riko tare da cewa. “Kina karatu sosai ko?”……. Ta yi mamakin sauyawarsa lokaci guda! Amma sai ta basar da cewa yeah tana yi. Jawota jikinsa gabaɗaya ya yi ya rungume, kanta ya fara shafawa a natse, cikin sanyin murya ya ce. “For give me”……. “Why are you asking me to forgive you, daddy?”….. Kai ya ɗan girgiza mata alamar babu komai tare da raba jikinsu, idanunsa da alamar ruwa a kwance a ciki ya saketa tare da cewa. “You can go! At anytime zan sake dawowa, ki natsu ki yi karatu sosai, don’t let anyone to know daga in da kike ko wani labari a kanmu kin ji ko?”. Da kallo cike da mamaki ta bisa, ganin bashi da niyar sake yi mata magana ne yasa ta fita da sauri bayan ya buɗe mata kofa. Slowly ya ɗago idanu ya bi bayanta da kallo har ta kurewa ganinsa, ajiyar zuciya ya sauke tare da tada motarsa, ya ja ya nufi gida. Yana parking a parking lot ɗinsu ya fito da sauri ya nufi elevator. Sama ya haura. Kai tsaye ya faɗa ɗakin aikinsu. A nan ya isko Lion and Scorpion suna aiki. A tsakiyar room ɗin ya tsaya tare da cewa. “Lion kun samu saƙo?”. Dikkansu suna kan aikinsu suka gyaɗa mashi kai, dan bala’i irin nasu a ɗakinma fuskoki a rufe tsabar rashin gaskiya da tantiranci. Karisowa ciki ya yi, a kusa da Lion ya zauna tare da fara pressing nasa computer…….. “Ya batun wancan aikin?. Hope everything is going well?”. Champion ya faɗa ba tare da ya kalli in da suke ba.Dik ɗakin shiru ya yi babu wanda ya amsa, sai can wayoyinsu ya yi ƙara ban da na Lion, a natse suka fito da wayoyin, sms aka yi masu. Buɗewa suka yi, a tare suka ɗago suka kalli Lion dake tsakiyansu yana pressing nasa computer…….. Mai da kallonsu a kan sms ɗin suka yi, hoton wani dattijo ne mai zubin kamala da dattaku, fari tas da shi mai ɗan tsawo, shi ne Lion ya tura masu saƙon a wayansu. Cikin wata iriyar muryan da ba zaka taɓa iya shaida voice ɗinsa ba Lion ya ce. “He will arrive in the Us tonight, he will check in at the Star hotel, and have dinner by the waterfront, by the end of the night, his fate will be sealed, he will not see the next day!”…… Kallon juna Champion and Scorpion suka yi. “Guru kai ne a kan wannan aiki”. Champion ya faɗa yana kallon Scorpion da suka fi kira da sunan guru, abin da yasa suke ce mashi Scorpion ma shi ne, kamar kunama yake, in dai ya kalli mutum sai gabaɗaya gangar jikinsa ya amsa kamar yadda in kunama ta harbeka sai gabaɗaya gangar jikinka ta amsa. Abin da yasa suke ce mashi guru kuma shi ne namijin gaske ne wanda gabaɗaya baya tsoron mutuwa, rungumar mutuwa yake yi a lokacin aiki, suka ce mutuwa da kanta shakkar ɗaukar guru take yi!. “Tare zamu buga”. Lion ya faɗa a sanyaye. Mamaki ne ya kamasu, dan sun san basu cika aikata aiki a tare ba, meyasa yau zasu yi a tare? Kaifin kwakwalwarsu da kaifinsu yasa mutum ɗaya a cikinsu yana iya jagorantar aiki dik girmanta, yau ace su uku dikka a aiki ɗaya? Lallai koma wanenen wannan babban kai ne!.Shigar da hotonsa computer ɗinsa Champion ya yi domin ya duba waye shi? Yaki faɗa masu ya je wajen Seraph, ya bar abin a ransa dan yana jin kamar shi ne ke da kusanci da ita ba su ba ko in ce ya fisu kusanci da ita, dan haka a ransa ya kudurta niyar bata kulawa koda basu sani ba!……. Dik yadda aka yi shi ya kashe mata daddy ko kuma shi ne ma daddyn nata ɗan banza!.Kammala bincikensa a kan hoton Champion, bayanai suka fito mashi kamar haka. Taimur Abbas Ali, dattijo mai shekaru 55 a duniya, preministar ƙasar India, dattijo mai mulki cikin gaskiya da amana, ya tsaya tsayin daka wajen ganin ya dakatar da kisan kiyashin da ake yi wa musulman indiyawa, bashi da nuna banbanci ko kyara ga wasu addinan, akwai addinai dayawa a ƙasar, amma bai takura masu ba, ya bari suna yi kayansu, ɗan gwagwarmayar ne sosai, amma a yau so ake yi ya faɗi saboda gwagwarmayarsa kan ganin lallai sai Musulman kasar sun samu ƴanci suna rayuwa kamar kowanu Musulmi a duniya, shiyasa aka yi ca a kansa, har poisoning ɗinsa an so yi, amma ALLAH ya ketarar da shi, musulman indiyawa suna ji da shi, amma gwamnati ta basu kwangilar kashesa, kun ji kuma abin da Lion ya ce. Jinjina kai Champion ya yi bayan gama karanta bayanai a kan dattijon, watau wanna babban aiki ne shiyasa Lion ya ce tare zasu yi, saboda akwai tsananin tsaro sosai, dole su mayar da hankali.”Me plan ɗin?”. Guru ya tambaya yana share bayanan da ya shi ma ya duba kan dattijon. Take computers dake gabansu ya yi ƙara alamar saƙo. Buɗewa suka yi a natse cike da kware, saƙo ne daga computer Lion, dik wani plan da ya shirya dan kashe mutumin ne ya basu jawabi. Natsuwa suka yi suna karantawa, plan A and B ne, basu taɓa tsara plan ya yi felling ba, amma dik da haka kullum sai sun tsara A and B saboda tsaro. Natsuwa suka yi suka karanta komai daki-daki kafin su goge saƙon, dan basu barin irin wannan shirin nasu gudun ɓacin rana. Daga nan suka shiga gudanar da aiki. Gabaɗaya Champion ya manta da Seraph again, ya kama aikin ƙoƙarin ganin komai ya tafi daidai. A tinaninku wani irin plan Lion ya shirya dan kashe wannan mutumi? Za su yi nasara ko a’a? Me kuke tinani a wannan ɓangare? Uhm da aiki babba a gabanmu, kwata-kwata ban taɓo dalilin kirkiran wannan labari da na yi bama, amma mun kusa isa wajen, zan so kowa ya karanta wannan ɓangare dan abu ne da zai shafi kowa da kowa musamman mata, ALLAH dai ya yi mana mai kyau!. —————————-🔥AZURE. Bayan sun ci sun ƙoshi V ta ce su je wajensu Arya. Cike da farinciki suka miƙe zasu haura sama kenan suka jiyo tsayuwar motocin GAT a harabar gidan. Ai mantawa da su V ta yi, da gudu ta nufi door tana faɗin. “Aunty I’m coming”….. Su dai kome ta yi burgesu take yi, dan haka suka bita da kallo.Daidai lokacin su Arya suka sauko da gudu, suna sanye da sleeping dress, silky short trouser and vest daga ta sama. Ai a mikiyan su Lisa suka bisu da kallo, ai sai suka rikice, a take a wajen suka rasa wacece V a cikinsu. Ba dan V kayan jikinta daban da nasu yake ba da wlh ba zasu gane ta ba, dan hankalinsu ba zai basu cewa V bata kai su tsawo ba.GAT na shigowa parlo suka rungumesa da karfi suna mashi oyoyo, ai gyara tsayuwa su Lisa suka yi suna kallonsu, gwanin burgewa. Rirrikosu GAT ya yi yana yi masu oyoyo ɗin shi ma, a haka suka kariso tsakiyar parlon. Sai a lokacin ya lura da su Lisa a tsaye, ɗan sake su V ya yi, idanunsa a kan Aunty Lisa ya ce. “Welcome”. Fuskokinsu a ɗauke da murmushi suka amsa da. “Thank you daddy!”….. “Where’s your dad?”. Ya tambaya yana kamo V dake ƙoƙarin zamewa, so take ta gudu ɗaki dan ta ga call ɗin Noor ya shigo wayar Angelie dake hannunta. “Daddy yana cikin room”. Suka bashi amsa kusan bakinsu a haɗe.Yana satar kallon suran jikin Aunty Lisa ya ce. “I hope you’re enjoying this moment and hope you take your dinner?”…… Da sauri suka amsa da. “Yes daddy, we really love this house, especially da yakasance our beautiful princess tana ciki”. Lisa ta faɗa tana nuna mashi V da hannu. Da yake yasan a yaran nasa V da Angelie ne masu saukin kai sai ya yi zaton ko V ta saki jiki da su ya kyautata masu ne yasa suke yabonta, and yasan ta fi sauran saurin shiga rai, ko kusa ko alama bai gane dalilinsu na kiranta beautiful princess ba. “Let me see your dad Ina zuwa”. Ya faɗa tare da dawo da kallonsa a kan V da gabaɗaya ta gama ƙosawa daddy ya saketa ta gudu ɗaki, ta yi picking call na Noor, dik da tasan batun waya zai yi mata, amma ta matsu ta ji voice ɗinsa.”My baby naga kina sauri ki gudu sama hope lafiya?”. GAT ya tambayeta….. A ɗan shagwaɓe ta ce. “I want to go to toilet daddy”….. Da sauri ya saketa yana faɗin. “Run my baby”…… Kashe mata ido Angelie ta yi, dan ya ga call ɗin ita ma, da gu V ta nufi sama tana maidawa Angelie martani da ɗaga mata gera guda.Harara Arya ta bisu da shi dan dik abin da suke yi ta gansu. Sama GAT ya nufa yana faɗin bari ya duba daddy Noor yana zuwa. Wucewa Arya da Manassa suka yi izuwa room na daddyn nasu ba tare da sun kalli in da su Lisa suke ba. Angelie ce ta ce. “Aunty Lisa ku zo mu je room ɗinku ko?”. Da okey suka amsa, ta wuce gaba suk rufa mata baya. Yanzu Angelie ta gane suna da alaƙa da mutumin da V take so watau Noor, shiyasa ta matsu ta koma room ta ji bayani daga bakin V, ita kuwa V sai addu’a take yi kada su Aunty Lisa su sanar da Noor ga in da ta fito. Tana hayewa sama ta faɗa balcony, zama ta yi saman chair dake wajen ta fara ƙoƙarin kiran numbersa kenan kiransa ta sake shigowa. Sai da ta saita natsuwarta kafin ta yi picking.”Hello”. Ta faɗa a shagwaɓe. Nisawa ya ɗan yi tare da satar kallon Leo dake kokarin sanya botiran sleeping dress ɗin jikinsa. “Barka da dare”. Ya faɗa tamkar mai raɗa dan kada Leo ya jiyosa…. “Barka dai, fatan ka koma lafiya?”. “Lafiya”. Ya amsa tare da ɗan yin shiru, sai kuma ya ce. “Kin manta baki karɓi wayarki ba! Ga shi gobe da sassafe zan bar barrack ɗin nan, sai ya kenan?”… Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce. “Ba kai ka sanyani na manta komai ba”…. “Like how?”. Ya tambaya…… “Like the way you did mana, ka sanya na manta kaina ni wacece, na mance a wata duniya nike, ai ka yi freshing brain ɗina my heartbeat”. Ɗan waro eyes ɗinsa ya yi, shagwaɓar nan tata ta tsuma zuciyansa, ta yi melting heart ɗin nasa, in a cool way ya ce. “Me na yi maki wai?”……. “Uhm baka san a lokacin da ka matso kusa dani ka yi freshing komai ɗina ba ko?”….. Shiru yayi, lallai yarinyar nan tana son wuce dik lissafinsa, tana faman goge mashi hadda. Satar kallon Leo ya yi kafin ya ce. “Kina da zola, yanzu dai faɗa mun ya za’ayi da wayar nan?”. Turo baki ta yi tamkar tanaa gabansa, a ranta ta kuduri niyyar sanya shi sakin jiki ya yi hira da ita dolensa ko yaki ko ya so. Dan haka sai ta ce. “Da sassafe mu haɗu ka bani wayar kawai”….. Jinjina kai ya yi tare da cewa. “Okey goodnight”………. “Uhm komai naka daban ne, to mu haɗu a Whatsapp”. Bata jira amsar shi ba ta katse kiran. Mamakin yarinyar ne ya rufesa, a ransa ya ce ƴar karama da ita sai karfin hali. A fili kuma ajiye wayar tasa ya yi irin zai shareta ɗin nan. Amma sai ya gagara, dan kuwa tin da ta ambata mu haɗu a Whatsapp gabaɗaya ya ji hankalinsa ya tattara ya koma kan Whatsapp ɗin nasa, hannunsa sai kaikaiyi yake yi, burinsa ya kunna data. Siririn tsaki ya ja tare da jawo wayar tasa again. Wunna light ɗinta ya yi tare da kunna data. Aikuwa yana kunnawa sai ga saƙonta ya shigo, haka kawai ya tsinci kansa da saurin buɗewa. “Baka son yin magana dani ko my heartbeat? Laifin me na yi maka? Ko baka son mace irina ce? Baka son yin abota dani? Me na gaza da shi a cikin abubuwan da kake fatan abokiyarka ta mallaka?”. Shi sakon da ta fara turowa. A ƙasan kuma sai ta sake cewa. “Ɗan hakinka da baya son buɗewa ya yi maganar nan kada ka bari in kama shi, dan ba zai maka kyau ba!”.One side smiling ya ɗan saki tare da fara typing reply kamar haka. “Gaskiya bana son mace irinki!”. A gajarce ya rubuta ya tura mata. Ai tin bai gama cire yatsarta a wajen ba ta fara yi mashi ruwan emoji na hawaye kala-kala. Ya fi emoji 100 ta tura mashi. Da sauri ya hau typing. “Oh sorry, lafa haka nan, da wasa nike”. Yana tura mata ta turo mashi emojin shagwaɓa tana turo baki. Sake sakin one side smiling ya yi kafin ya hau serious typing na amsarta kamar haka. “Kina dikkan abin da kowa zai ji yana son alaƙa dake, kawai ban sanki bane yasa, kin ki faɗa mun wacece ke? Daga ina kike? A ina kika sanni? Idan kika bani amsa zan saki jiki mu yi hira, kuma zaki zama ƙawata”. Lokacin da ya tura mata daɗi yasa ta miƙe ta ɗan daka tsalle tare da komawa ta zauna, sannan ta fara typing.”Promise me that in na faɗa maka wacece ni ba zaka fasa abotarmu ba?”….. Kai ya jinjina tamkar yana a gabanta kafin ya hau typing na ya ɗauki alkawari………. “Vanisha by name, daughter of GAT, na sanka ne since ban wuci 9 years ba a jinin robar man shafawarmu, kullum da tinaninka nike kwana kuma nike tashi, na ji a raina kamar kai ba a zahiri kake ba shiyasa da na ganka na rikice, please kada ka yi breaking promise da ka ɗauka mun, na zaɓi in faɗa maka gaskiya ne kawai dan nasan dik alaƙar da aka kulla a kan ƙarya bata ƙargo, nasan zaka fahimceni kuma ka mun uzuri”. Tana gama rubutawa ta tura mashi kirjinta na dukan uku-uku, cike take da fargabar amsar da zai biyo baya, kada ya ce ya karya alkawari, ina zata sanya ranta in hakan ta faru? Safe kirjinta ta yi tana jiran amsa daga garesa, har ƴar gumi ta haɗa. Shi kuwa a lokacin da saƙonta ya shigo mashi, natsuwa ya yi ya karanta da kyau. Ai yana zuwa in da ta ce ƴar GAT take bai san time ɗin da ya miƙe zaune ba. Wani irin waro idanunsa a kan wayar ya yi, sai yake ganin kamar bai karanta daidai ba, hakan yasa ya faro karantawa daga farko. Tabbas abin da ya karanta a farko shi ne. Ɗan ɗauke wuta ya yi, ya gagara yi mata reply, a can kuma tana can cike da zulumi da fargabar jiran amsa daga garesa, shi kuwa ya rasa a wani point ma yake tukun nan. Me kuke tinanin zai faru? Zai bata amsa ko yaya? Zai cika alkawarin da ya ɗauka? Zai take zokar AZURE ne ko dai zai bi doka ya gogeta daga babin rayuwansa?.STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥

Back to top button