Hausa novels

Mijin Marigayiya Page 45 Hausa Novel

Haka dole Khadeeja ta hakura ta cigaba da hidimar gida da ta yara.Shima Mustapha da ya gama zagaye-zagayen haka ya sameta a dakinta yana nuna mata jin dadinsa ganin yanda take kula da yaran sai dai baya jin dadin yanda idan ta jera abinci take komawa daki ta barsu shi da ‘yayansa.Duk yanda ya so ta bashi hadin kai su tattauna maganar ta ki, da ya dameta da zance ma sai tace ‘Don Allah ka bari! Kai dai ba so kake na cigaba da hidimar gidanka da yaranka ba amaryarka tana hutawa? To ai ina yi ko? Ina ga duk a inda na zauna naci abinci ma wannan bai kamata ya zama damuwa ba tunda dai ku kun ci naku.’Kafin ya bata amsa ta fice ta bar masa dakin. Dole ya hakura ya zuba mata ido tunda dai tana yin abinda yake so kuma duk ranar da ya kai mata kwananta bata hanashi bukatarsa.000000Da fari lokacin da Mustapha ya kara aure Khadeeja taga ‘yan uwansa basa wani damunta tayi zaton tunda an mata kishiya sun fita harkarta. Sai dai tunda suka ji labarin Naja tana da ciki sai suka kama zarya gidan; babu yanda za ayi Yaya Jidda tayi sati bata zo gidan ba. Haka zata taho da girki a flask wai Hajia ce tace a kawowa Naja saboda kwadayin mai ciki. Gashi idan ta zo a wajen Najan zata sauka, sai dai idan Khadeejan tana nan ta shiga su gaisa sai ta koma wajen Najan. Sai kuma tayi ta aiko yara; a bata abinci. Idan ta cinye kuma tace a bata wani dan abun tabawa. Ranar da bata zo ba kuma sai a turo yaranta da abincin; haka zasu zo ta wuni surutu da hidima da su bata taba jin wani yace Hajia tana gaishwta ba. Kuma shima Mustaphan kuma yana kallo ana yi amma bai taba cewa komai ba; sai dai yawan godiya da zata ji shi yana yiwa mutan gidan nasu.Haka ta kawar da kai ta cigaba da duk wannan hidimar tana ganin rawar kai kala-kala.Haka ta cigaba da dagewa har Allah ya sauki Naja lafiya, aka sami yarinya mace wadda tun ranar da aka haihu Mustapha yayi mata huduba da suna Rukayya.Basu tsara zata tafi gida ba don haka sai aka kawo kanwar mahaifiyarta Alawiyya waddad suke kira da Anti Wiyya ta zo yi mata zaman dabaro.Tun Khadeeja tana saka ran zata ji Mustapha yace zai hade mata kwanan saboda Naja tana jego har dai ta fitar da rai.Ranar da aka kwana takwas da haihuwa ranar ta kama kwanan khadeeja ne sai dai a daren ranar zata fita daga girki.Da yake a dakinta suka kwana a nan yake shirin fita office; musamman tunda bandakin dakinsa ya kwana biyu rabon da a wanke saboda Naja ba zata iya wankewa ba kuma Khadeeja ta ki ma shiga dakin; gashi kuma yana kyashin ya saka Afaf ta wanke tunda baya son damuwarta.Yana zaune a gaban mudubinta yana shafa mai ta fito daga wanka, ta dauki kayan shafawarta ta koma gefen gado, suna yi suna taba hira.Jimawa kadan tace ‘Yauwa, tazarce zamu yi ko? Sai na hade kwanakin tunda Naja tana jego har zuwa tayi arba’in ko?’Ya dan yi dum, alamar maganar ta shammaceshi; tun ranar da Naja ta haihu ta gaya masa ba zata bayar da kwanata ba saboda ko ba zata iya biya masa bukatarsa ba tana so ya kwana da su ita da Baby, in ya so kwana biyu sai su hakura. Ya riga ya amsa mata hakan domin shi ma hakan yayi masa; duk da dai shi ba mutum ne mai son jarirai ba domin ko daukan yaro baya son yi har sai yaro ya iya zama sosai. To amma dai tunda ta nuna tana so shima sai ya ji hakan yayi masa ko hira ce sa yi, musamman da yake bai taba tsammanin Khadeeja zata nemi wani karin kwana ba duk da ita ta bada nata kwanan an bawa Najan.‘Um, no ina ga ba haka za ayi ba. Na riga nayi magana da ita amma bata bada kwanan nata ba, tunda kin ga kema tambayarki nayi kika bayar ba tare da nayi miki dole ba. To ita bata bayar ba, don haka sai a cigaba da kwana bibbiyun kawai.’ Ya fada cikin in-ina yana satar kallon Khadeejan ta cikin mudubi.Sai da tayi da gaske sannan ta hadiya malolon da ya tokare mata makogoro; duk da dama hakan ta sa rai zai fada amma sai da abun yayi mata ciwo. Ita bata ma yarda Naja ce ba zata bada kwananta ba, ta fi yarda shine di ba zai iya bata kwana arba’in ba ba tare da ya ji dumin rabin ransa ba. Ta daure tayi murmushin yake sannan tace ‘Allah sarki hakane kam, to babu damuwa Allah ya raya mana Rukayya ita kuma mai jego Allah ya kara mata lafiya. Shikenan ai tunda ta haihu lafiya idan ta karbi kwana yau to ta hada da sauran hidimar gida da yara da nakeyi nima na samu na huta.’Yayi shiru da bakinsa a bude yana kallon Khadeejan ta cikin mudubi; to a gaban Antin tata zai sakar mata aikin gida da na yara bayan ga danyen jego sannan kuma ga Khadeejan tana kallo? Kuma ace ita ce zata tashi ta shirya masa yara, duk da dai kusan sun iya shirya kansu amma dai idan ba a tsaya a kansu ba haka zasuyi ta shiririta har su makara. Gashi Afaf ta shiga SS 3 yanzu tun 7:15 am ake tare su makara. Ya san idan dai ba a tsaya a kansu ba to kullum sai dai ya dawo da Afaf. Ya rasa ma me zai ce mata, domin ya san kusan ko me yace tana da amsar bashi kuma ya tabbatar fitnar da bata yi bace a lokacin da Baffanta yace ta dinga taya Naja aiki take shirin biyan bashinta yanzu.Ta mike ta kwashi mayukanta da ta gama shafawa ta karasa gaban mudubin ta ajiye. Ta dan tsaya daga gefensa tana kallonshi fuskarta cike da walwala kamar ba yanzu ta hadiye bacin rai ba, tace ‘Kuma ni na yafe nawa kwanan ka hada mata, idan kuka yi arba’in sai mu cigaba da rabon. Ka ga ita da Baby suna bukatar lokacinka da kulawarka sosai a wadannan kwanakin.’Ta wuce ta nufi gaban wardrobe domin saka kaya.Yana nan zaune a gaban mudubin ta shirya ta fice ta barshi a dakin; nan da nan ta hada masa breakfast ta jera a kan table sannan ta dawo dakin ta sameshi ya riga ya gama saka kaya. Tana tsaye daga bakin kofa tace ‘Na yi serving breakfast.’‘Ok.’ Ya amsa.Ta juya ta fice ya biyo bayanta.Suka zauna tare suna cin abincin. Har suka ci kusan rabin abincin babu wanda yace wani abu; kowa da abinda yake ransa. Ya ajiye kofin shayinsa bayan da ya kurba sannan ya dauki fork dinsa ya tsikari dankalin baturen da yake gabansa, ya dan ajiye fork din ya kirawo sunanta a hankali kamar ma baya so ta ji kiran. Ta daga kanta daga kallon kwanon abincinta ta amsa tana kallonsa. Yayi gyaran murya sannan yace ‘Um, da-Allah kiyi hakuri ki cigaba da girki akalla har zuwa lokacin da Antin Naja zata gama yi mata wanka ta tafi, tunda kinga ga Hafsa nan tana taimaka miki kuma na san Afaf din ma yanzu duk abinda kika gwada mata zata iya tayaki da shi.’Saura kadan dariya ta kwace mata; wato yanzu Afaf ta kai ta taimaka wajen girki kenan tunda ya auro matar so? Ashe ma ya san kunya tunda ga shi baya so yaji kunyar iyayen Naja. Ta ajiye cokalinta ta kurbi shayinta sannan tace ‘Don Allah Abban Afaf mu bar wannan maganar, hidimar gidannan ta wata takwas na karbar mata. Ai nayi ko? Yanzu sai ta cigaba daga inda ta tsaya. Kwanan kuma da nace na bata da gaske nake, kuje kuyi jegonku na masoya kwana arba’in; watakila dai a kwankin da suka kama nawane na yi aikin gidan idan ina nan in ya so ita sai ta kwana da angonta.’Cike da jin zafin abinda ta fada yace ‘Khadeeja ni kike gayawa wannan maganar?’A cikin abinda ta fada bata san menene ya bata masa rai haka ba tunda ita dai a iya saninta ba rashin kunya tayi masa ba, amma ta ga ya fusata yana faman yi mata muzurai. Ita da ya kamata ace itace ranta ya baci haka saboda nauye-nauyen da yake nema ya dora mata wadanda karara suke nuna rashin adalci.Ta kalleshi ta kawar da kai tace ‘Allah ya baka hakuri.’Ta kurbe ragowar shayinta ta mike da kofin da kwanonta ta wuce kitchen…

Back to top button