Hausa novels

Mejo Najeeb Page 17 By Autar Alheri

“Seda yaƙara yin wani wankan tukunnah yafito ɗaureda towel aƙugunshi kanshi na matuƙar sara mishi domin haryanzu bayajin jikinshi Dede, kaitsaye wurin mirror yanufa mayukanshi yaɗauka da tirare yakoma ban ɗakin….shidai doctor ziyad da ido kawai yake binshi haryafito yaƙara ɗaukar kayanshi daze saka yakoma ban ɗakin seda yashige kana doctor ziyad yasaki dariyar dake cinshi hadda daga ƙafa yana mamakin wannan abun wai ashe haryanzu najeeb becanjaba? Yana’nan da muguwar kunyarnan tashi? Lallai akwai aiki kam agaba, yafaɗa Afili yana koma sakin dariyar adede nan kuma mejo ɗin yafito…da kallo yabishi ganin yadda yaketa kwasar dariya kamar wani zararre baki yataɓe dominshi besan abinda yake yiwa dariyaba…shikuma doctor ziyad seda yayi me isarshi kana ya tsagaita yana kallon najeeb cikin shaƙiyanci yace “tab dijam wai mejo nine kake yiwa ɓoyo Hakan dudda man shafawa se a bathroom zaka shafashi? Tab lallai zanso ganin ranarda zakayi sintir agaban mace domin ni irinmu ɗaya namujine kamar kai maima kakasa shafawa agabana balle mace da kasan kowanne acikinku dabanne kuma tsayawa gabanta ahakan doline gashi kuma kai bazaka iyaba Humm zanga wanda ze ajiye tashi kunyar tsakanin kaida koma wacece zata kasance matarka. Yaƙarasa zancen yana koma sakin dariya….tinda yasoma magana mejo yazuba mishi blue eyes ɗinshi masu matuƙar firgita ƴan maza seda yaji yadasa aya ne, yagirgiza kanshi dake mugun sara mishi domin wannan zancenma wani ciwon kan yaƙara haddasa mishi,, batareda yace komai ba yanufi takalmin shi yaɗauko tare da zama bakin gadon zesaka…har doctor ziyad ya fidda ran zeyi magana kana yabuɗe bakinshi ahankali cikin cool voice ɗinshi yace “Humm Ziyad kenan kama dena wannan banzan tinanin naka domin kuwa bayan mahaifiyata ba’ayi wata mace dazataga tsiraicinaba aduniya sabida abune mafi girma da daraja agareni..nisawa yayi ahankali kamin yacigabada faɗar ko mahaifiyar tawa ayanzu bazata iya tantance yanakeba domin maraba data ganni ayadda kake faɗa ita kanta maybe bazata iya tinawaba balle yanzu kakawo zancen wai mace zata ganni Humm. Kuma dakake faɗar dukkanmu ɗaya kaima faɗa kakeyi kawai domin wannan shirmen naka bazeyi tasiri ba sabida kowa aduniya yanada banbanci dawaninsa ba wanda zekasance kala ɗaya koda kuwa jinsi ɗaya ne kamar ni da kai dakake tinanin ɗaya ne to Sam bahaka bane Ina fatar kagane. Yana kaiwanan azancenshi yamiƙe tare da kwasar wayoyinshi yayi gaba abunshi yana faɗar idan katashi kasameni a hospital ɗinku domin nacika alƙawarin dana ɗauka.Ajiyar zuciya doctor ziyad yasauke cikin mamaki yake kallon aminin nashi kamun yamiƙe yabiyo bayanshi yana faɗar”dan renin hankali ƙarya kakeyi wlh kuma wlh Allah duk abinda ka ƙaryata sekayishi inda muna raye sedai idan bakayi aure ba duk wannan miskilanci doline yatsaya iya mu amma mace kam humm nadaiyi shiru, yafaɗa ganin sunfito harabar gidan….shidai mejo komi beƙara cemishiba yashige warshi mota captain Jameel ma yashiga dominshi duk abinda akeyi besaniba sam besan cewar ciwon mejo yatashiba…Shima doctor ziyad tashi motar yashiga suka nufi hospital ɗinshi….bayan sunje duk wani gwaji dayadace ayiwa mejo najeeb anyi mishi kamar yadda aka saba amma sam bawani ciwo ataredashi dama duk akayimai gwaji ba’aganin komai…ajiyar zuciya doctor ziyad yasauke bayan ya gama duba gwajin cikin jimami yace “wlh baka ɗauke da kowacce irin cuta ninarasa minene matsalar ka mejo..”okay badamuwa Dama nasan ba’abunda kedamuna Allah yasa mudace cewar mejo najeeb ɗin yafaɗa cikin ko in kula tareda miƙewa kawai yafice daga office ɗin…da kallon tausayi doctor ziyad yabishi yana mushi fatan samun lafiya me ɗorewa.Bayan mako biyu( 2 week ago)Awannan mako biyun da’akayi sam mejo najeeb bekoma gidanda yakai Isseta ba hasalima yamantada yazoda wata yarinya gaba ɗaya sha’anin gabanshi kawai yakeyi na hidimar aikinshi gabaki ɗaya yazama busy…Itama agunta hakanne gabaki ɗaya tamanta dashi dudda cewar daga farko taɗanji tsoron zama gidan Ita kaɗai amma data fahimci akwai masu tsaro aciki se hankalinta yakwanta takeyin komai nata hankali kwance babu wani takura kodamuwa. Acikin mako biyun nan kuwa tayi wani irin kyau taƙara ƙiba da haske sakamakon tanacin me kyau tasha me kyau kuma ga kwanciyar hankali………..afanni kawar Ummi juwaira kuwa tuni tazo gidansu Ummi tun ranarda ciyon mejo najeeb yatashi inda tasamu karɓuwa sosai agun mutanen gidan sedai itada mansura ne kawai ake taƙon saƙa,,kuma har ila yau datayi mako biyu agidan basu haɗu da mejo baGombe StateYau jimu’a bayan fitowa masallaci zaune suke dukkansu atsakar gidan kowa na abinda yadameshi yayinda mama bintu ke zaune jigum tana jiran tsammani domin tinda abunnan yafaru tadena samun sukuni arayuwarta….da sallama yashigo gidan amma kallo ɗaya zakamishi kasan cewar abirkice yake, yaran gidanne suka taso suna mishi sannu da dawowa amma kota kansu bebiba, yafaɗa ɗakin mama bintu yana ƙawala mata kira…tashi tayi tana salati tabi bayanshi domin tinda abunnan yafaru take tsoron Kiran abban nasu sabida fargaba….da kallo matan gidan suka bisu kamin sushiga aikin nasu wato gulma.Tana shiga taganshi tsakiyar ɗakin Se Safa da narwa yakeyi, jiki asanyaye taƙarasa wurinshi tana faɗar mlm lafiya? Miyafaru kuma? Jin tambayar da takemishine yasakashi jiyowa gareta cikin tashin hankali yake faɗar “shikenan bintu asirinmu yakusa tonuwa wlh mutanen dasuka karɓi auren Maryama ne sukazo kinsan yau ne alƙawarin damukayi dasu yanzunnan naga wucewarsu faɗar megari, yaƙarasa zancen yana yashare guminda yawanke mishi fuska… “innalillahi wa’inna ilaihiraji’un yanzu yazamiyi kenan mlm? Kasan dai bazamuce maryama ta ɓataba kuma bamusan wazamu bada amadadintaba domin wlh da zaka yadda wata daga cikin yaranka zaka bada seka gaya musu Maryama tana makaranta kayi tunanin fidda tane da akayi auren amma hukumar makarantar bata amincebe sabida haka gawata daga cikin ƴaƴanka aɗaura da ita iyaso daga baya mijin yasaki maryama…shiru malam Musa yayi yana tinanin maganar mama bintu wata zuciyar tace ya amince wata zuciyar tace Hakan baze yubaNisawa yayi kana yace “anya kuwa bintu Hakan zeyu domin kuwa wannan abun akwai ɗaure kai acikinshi tayaya za’aɗaurawa mace biyu aure da muji ɗaya bayan kowa namusu kallon ubansu ɗaya? Yatambayeta cikin damuwa. “To mlm babu wata mafitarce kawai gayawa megari gaskiyar lamarin zakayi kozamu samu mafita domin kanada tabbacin wannan auren na maryama babu inda zekai muddin ma mallakanta sukasan dashi? “Ajiyar zuciya mlm Musa yasauke kana yace “Hakane bintu badamuwa bara muyi yadda kikace muga. To mlm yanzu yoshe zaka gaya mishi? Cewar mama bintu..baki mlm Musa yabuɗe zeyi magana kenan iyya hassi tafaɗo ɗakin kamar anjefota sabida tsabar gulma…dukkansu da kallo suka bita bawanda yace komai…ganin Hakan yasa Tasha jinin jikinta cikin dabircewa tafara kame’kame tana faɗar “dama uhm dama sallama ce akeyi aƙofar gida shine nace barana kiraka, tafaɗa akunyace.. shidai mlm Musa bece mata komaiba yafice daga ɗakin hakama mama bintu batakobi takantaba tashiga naɗiyar kayanta dake zube akan godo…ganin ba wanda yakulata yasa tafice daga ɗakin akunyace.Mlm Musa nafita ƙofar gidan yaga saƙo daga fadar megari ne Hakan yasa ko gida bekomaba yabibayan ɗan Aiken.*Audio book na Autar alheri dama sauran littafan Hausa nasaurare zaku iya samunsu a YouTube channel ɗinmu me suna s Zaria Hausa tv in sha Allah game ƙatar ƙarin bayani kuwa ze iya tuntuɓar wannan nomber👉07037092176 Audio book zallsh 💃💃*Koda yaje fada kuwa kowa ya hallara ana jiran isowarshi..wuri yasamu yazauna kana akashiga gaishe gaishe wanda duk abinda akeyi jikin mlm Musa asanyaye yake, seda kowa yanutsu tukunnah megari yayi gyaran mura kana yace “mlm Musa gasu Alhaji Abubakar nan kamar yadda sukayi alkawari sun dawo ɗaukar amarya. Seda megari yakai ƙarshe azancenshi kana mlm Musa yace “wlh ranka yadaɗe akwai matsala, Yafaɗa kanshi aƙasa… “Subahanallah matsalar me kuma mlm Musa?? Yatambayeshi cike da fargaba karya kunyatasu….nisawa mlm Musa yayi kana Yagaya musu duk abinda suka tsara shida mama bintu seda yakai ƙarshe sa’annan yaɗora da faɗin sabida Hakan nake neman alfarma idan bazaku damuba zanbashi yar uwar maryama wato hawwa Se aɗaura da ita sabida ita tagama karatun.”Tofa iKon Allah tayaya duk Hakan zefaru mlm Musa? Ina kataɓa ganin namuji ɗaya ya auri mace biyu kuma ubansu ɗaya? Aikasan Hakan badede bane sedai idan sakin ɗayar yayi tukunnah mukeda damar aura mishi ɗayar ko idan ɗayar mutuwa tayi amma babu ko ɗaya acikin wannan kuma kace a ɗaura aure haba kaima kasan bazeyuba, cewar sarkin faɗa yafaɗa cikin mamakin furucin mlm Musa sekace wadda bashida ilimin addini…liman yace gaskiya kam bazeyuba sedai idan sakin tafarkon yaron zeyi iyyaso aɗaura da wannan ɗin… shikenan ma zance yaƙare sedai ayi Hakan sarkin fada yakoma faɗa cikin ƙwarin gyuiwa.Duk wannan zancen da’akeyi waƴannan alhazawan basuce komaiba Seyanzu Alhaji Abubakar yayi magana cikin dattako yake faɗar “sam Hakan bazeyuba bedace ayi wasa da igiyoyin aureba sabida Hakan zamujira waccan tagama karatun kawai inaga zefi.. da mamaki megari ke kallon Alhaji Abubakar ɗin kafin yace “miyasa kace Hakan Alhaji? Bayan lalurace tasaka za’ayiwa yaron wannan auren kawai de a ɗaura da ita ɗin iyyaso idan waccan tadawo seshi yaron yasaketa kawai tinda dukkansu ba wanda yasanda wannan auren koba hakaba?? “Shikenan ranka yadaɗe badamuwa ayi Hakan amma aranarda aka kai wannan ɗin se a gayawa yaron yadda abin yakasance kunga seya saki waccan kafin yatare da amaryarsa ko ya kuka gani? Alhaji Abubakar Yafaɗa yana kallon ƴan uwansa…Hakane bamatsala Alhaji. Wani Alhaji mustapha Yafaɗa yana gyara zamanshi…ajiyar zuciya megari yasauke bayan duk yagama jin bayanansu kana yace “tunda kunyanke wannan hukuncin ba’abunda zance sedai Allah yazaɓa mana abinda yafi alkhairi sabida Hakan a ɗaura da hawwa. Daga Hakan aka sake ɗaura auren wannan yaron da aka ɗaurawa Isseta aure dashi da anty hawwa akan sadaki dubu ɗari semuce Allah ya kyauta……seda aka gama ɗaurin Auren kana mlm Musa yashiga sauke tagwayen ajiyar zuciya ganin yatsallakewa tarkon Auren Maryama yanzu saurana ɓatanta( nikuwa nace anya mlm Musa ka tsallake kuwa ? Kamar yadda kake tinani🤨)Bayan anshafa fateeha ne su Alhaji Abubakar suka buƙaci mlm Musa da sarkin fada haddama wasu dattawa biyu acikin dattijawan faɗa akan suzo sutafi domin suga inda za’akai yarsu…sosai wannan zancen yayiwa megari daɗi dudda cewar sunsan mahaifin Alhaji Abubakar amma yanada kyau Susan inane za’akai amaryar kafin Kaita..anan kowa ya amince da zancen Alhaji Abubakar Hakan yasa waƴanda za’ayi tafiyar dasu suka koma gida domin sanar da iyalansu tafiyar dazasuyi…abbba kam yana komawa gida kaya kawai ya canja kana yasanarwa da matan gidan zeyi tafiya kuma yanasaran gobe zedawo, batareda yasanar musu dalilin tafiyar ba. dahakan yayi musu sallama yatafi suka rakashi da addu’ar sauka lafiya…yana zuwa faɗa Babu ɓata lokaci suka ɗauki hanya kasan cewar dukkan wanda zasu tafi sunfito shine kawai ake jira…LagosZaune yake acikin tangamemen office dinshi Yana sarrafa na’urar dake gabanshi cikin ƙwarewa da bajinta domin computer ma se anyi mata miskilanci (ohh ni ɗiyar babanmu🙄 matar miskili tashiga ukku🤭) turo ƙofar office ɗin kawai akayi akashigo ciki,,sarai yaji amma yayi kamar bejiba domin yasan kowaye ze iya yimishi Hakan..wuri general aliyu yasamu yazauna Yana kallon aminin nashi kafin yayi gyaran murya cikin kulawa yake faɗar ” afternoon my man how your work?? Mejo Najeeb bece komaiba yamiƙawa general aliyu hannu kawai sukayi musabaha kana yashiga haɗa kayanshi domin lokacin tafiyarshi yayi kasan cewar bayajin daɗin jikinshi tun lokacinda ciwonshi yatashi…da kallo general aliyu yabishi harya gama haɗa kayan sa’annan ya kalleshi dakulawa yace “Se ina yanzu mejo? amma dai ba gida zakajeba gidanka zakaje gun sister ko? Yatambayeshi yana kafeshi da golden eyes ɗinshi……shikuwa Mejo Najeeb wani irin faɗuwa gabanshi yayi Allah yasani sam yamanta da wata yarinya daya ajiye agidanshi dudda cewar bata cikin lissafinshi amma koba komai ita ɗin amanar maahh ce bedace yawo fatarda itaba, blue eyes ɗinshi yawaro tunowada Ita kaɗai cefa agidan kaddai wani abun yasameta besaniba, inko Hakan tafaru meze gayawa maah “innalillahi wa’inna ilaihiraji’un yafaɗa daɗan ƙarfi kafin yayi waje asukwane batareda yabawa general aliyu amsar tambayar shi ba secewa dayayi “please bro follow me now…..ganin Hakan yasa general aliyu mara mishi baya kawai Shima batareda yaƙara cewa komaiba domin ya san koyayi maganar ba amsawa zeyiba…koda general aliyu yafito harabar wurin harya shiga mota captain Jameel yaja suna ɗauki hanya, Hakan yasa Shima yashiga tashi motar captain Ameer yaja sukabi bayanshi.IssetaZaune take a general parlor gidan domin yanzu nanne wurin zamanta tinda tagano bakowa agidan, fruit salad ne agabanta tanasha gaya tayi wankan wasu mayun riga da wando wanda tagani acikin kayanda yasiya mata tinda dukkansu ƙananun kayane, wandon roba ne red color bakin guywarta yayi masifar ɗame mata ajiki inda dukkanin ilahirin halittar mazaunanta suka bayyana acikinshi kamar bata saka komaiba aciki,, sekuma rigar data kasance kamar bubu roba domin bata kamata ba hasalima setayi mata kamar ɗinkin unburela kuma batada dogon hannu iya kacinshi hannun bra, gabaki ɗaya ta bayyana asalin Nashanunta kuma tasauka ƙasa har mazaunanta sedai kuma kamar ƙara temaka musu tayi wurin bayyana.. sa’annan kuma ta gyara gidan ko ina yaɗauki ƙamshi sekace jihar barno😅…zaune take hankali kwance tana kallo a YouTube channel na s Zaria Hausa tv inda take kallon wani lbr mesuna SIRRI tana kallo tana saurara domin sosai lbr yaɗauki hankalinta dubada yadda ƴan ukkun cikin labarin ke masifar kama dajuna, Sam bataji tsayuwar motaba balle tasanda akwai wanda yashigo gidan…ahakan harya buɗe ƙofar perlor yashigo asukwane wanda rufe ƙofar dayayine yadawo da ita duniyar data tafi taɗago arazane tana kallon wanda yashigo mata bako sallama domin a iya tinaninta bakowa agidan bancin masu gadi sukuma iya kacinsu waje basu basu taɓa shigowa wurintaba…ido huɗu tayi dashi wanda harta fara manta kaman ninsa segaya yau yazo mata kamar daga sama aka jefoshi.Shiko tinda idonshi yasauka akanta yakasa koda kiftasu sakamakon wani mugun kyau dayaga taƙara taƙara ƙiba da haske harwani sheƙi fatarta keyi a idonshi…itako ganin bece komaiba se kallon ƙurillar dayake binta dashi yasa tabi jikinta da kallo Taga miyake kallo aiko tawaro ido waje ganin kayanda ke jikinta domin Allah yasani sam batayi tunanin zezo gidanba Dama bazata sakasuba inkuwa taska to zata nemi hajab tasaka, ai a 360 tamiƙe dagudu tanufi Saman benen…Shima ɗin sake waro Blue eyes ɗinshi yayi cikin mugun mamakin ganin yadda kayan alatun jikinta ketafasa kamar ana dafa ruwan zafi, domin duk ilahirin halittar jikinta juyawa takeyi tana kaɗawa kamar zasubar jikinta sufaɗo….cikin giɗima yadafe setin mejo ɗinshi yana sauke numfashinda besan dalilin yinshiba acewarshi akuma Dede wannan lokacinne general aliyu yabuɗe ƙofar perlor yashigo…!

Back to top button