Uncategorized

Hira Da Matattu Part 4 (True Life Story) By Jamila Umar Tanko

 HIRA DA MATATTU…..4

     Abinka da qaton gida irin na attajiran da, mu ka wuce baranda sannan mu ka shiga wajen zaman jira kafin a yi maka iso zuwa falo wato (reception). Mu ka isa bakin falo sai ta tunkuda ni ciki, kafin in waiwayo babu ita ta bace. 

Tsarki ya tabbata ga Ubangijin da ya samar da ni Ya samar da Sharifah, babu alamar bil’a dam na zaune a gidan nan saboda yana da ko ina a lullube yake da qura.  kansu kujerun falon baqaqe an rurrufe su da fararen gyallaye dan kada su yi kura, hakan ya nuna babu rayuwa a cikin gidan nan da dadewa. 

Na qara fadawa tsoro mai tsanani yayin da na shiga barbaza idanuwa ko zan ga ‘yan uwana bil’adama su Nanah Ahmad da na jawo musu, na dauko su na kawo su gidan halaka. 

Abin tambaya anan shine shin ina Hamidah da na ga ta shigo dazu? Ina Bello da ya shigo tare da su Nanah? ina Su Nanah kansu suke?

Wannan karon Allah Ya bani ikon yin kalmar Shahada bayan na baje na kwanta a cikin qura ina birgima. Gara komai ya iske ni ina daga kwance ba a tsaye ba. 

Bala’i ya kai bala’i. Na Shiga tunano laifin da na yiwa wannan baiwar Allah da ta addabe ni bayan ta mutu. Ban yi mata komai ba kawai dai na rasa lambarta dadewa.

Kenan su Bello ma gaba daya ba mutane ba ne su Hamida, su yaran da na gani a hanya masu kamar Sharifah.

Sallama na ke ji da wasu lunguna na gidan domin katon gida ne mai dauke da dakuna ba adadi. 

A iya sanina babansu ya rasu ya bar mata hudu da yara sama da ashirin kuma dukka anan gidan suka zauna sama da qasa. Toh duk su na ina yanzu? 

Na runtse ido yayin da karkarwar da jikina ke yi ta jawo har kujerun da suke kusa da ni su na girgiza. 

Cimak na ji an daga ni an tashe ni zaune, na kwalla qara mai firgitarwa na ce “na rantse da wanda raina yake hannunSa ba zan bude idanuwana ba. Kazantar da baka gani ba taafta ce. Ga dai gangar jikina nan ku yanki in da yayi muku.”

“Samha Mahmud lafiya? Ki bude idanuwanki, ki taso mu tafi, banga alamar gidan nan akwai mutane ba. Mun leqa ko ina babu kowa da alama ma an dade baa rayuwa a gidan nan.” Muryar Nanah Ahmad ce.

Ramatu Alqali ta ce “ni fa tsoron gidan nan nake ji ina ta ganin giftawar yara amma sai in ga wayam.”

Na tabbatar qawayena ne sai na miqe tsaye da sauri na ce da su “gidan MATATTU  ne fa, ku zo mu fita. Sharifah ta rasu amma ni ina ganinta ita ce ma ta shigo da ni falon sannan ta bace. Ku fadawa iyayena da mijina su yafe min. Sharifah so take ta tafi da ni. Ni kadai nake ganinta.”

Su ka gwale idanuwa yayin da suka fara waiwayen sama da qasa a tsorace, tabbas sun fara gasgata maganata. 

Maryam Auwal ta ce ” shin ina qanin nan na ta da muka shigo tare da shi har muka yi masa gaisuwa a qofar gida?”

Na zabura na ce “ciki ya shigo amma ba a ganshi ba, ku zo mu fita daga gidan nan.”

Jikina babu kwari haka suka rirriqe ni muka fito farfajiyar gidan, abin mamaki qofar get a datse. Idan Shariah mutum ce data tunkudo ni falo ta fita ai da an ga get a bude dan haka bata fita ba, tana cikin gidan ko kuma koda yake ina uwan fatalwa ma da kofa?”

Anan su ka tsinto min takalma da mayafina suka bani na qi karba na ce su bar ni. Me gawa zata yi da takalma kuma.

Nanah tayi-tayi ta zare sakata ta kasa. Wata karamar qofa na hango wacce a baya ban santa ba. An huda katangar. Ban yi wata-wata ba na afka, dan na ga alamar zata iya kai mu waje, sai su ma suka  biyo ni.

Karamin yaro ne a tsugunne a gabanmu yana wasa, sanye yake da farin wando gajere boxers da farar shima. 

Na daka tsalle na ja baya dan da ya waiwayo fuskar Sharifah ce, ba ni kadai ba sauran ma sun razana.

Mu ka daka tsalle muka rungume juna. Farfajiyar tsakar gidan a cike take da datti, ganyen bishiyoyi da suka fado suka bushe in abin a kwashe ne zasu kai cikin mota tirela, in da za ka tabbatar an dade baa yi shara ba, kura kuwa ma baa magana.

Ba mu tambaye shi ba ya ce “mamana ta ce in kun fito ku bi ta wannan get din.”

Ya nuna mana wani get na daban.

Ramatu ta zabura ta tambaya ta ce “wacece mamarka, tana ina?”

Na toshe bakinta na wawuri hannunta na ce “ina ke ina tambayar mamarsa bayan amsar a bayyane take. Ku zo mu yi ta kanmu.”

Yaro ya bi lungu da gudu ba mu sake hango shi ba. Yayin da mu ka ware injin qafafuwanmu muka fita da gudu ta cikin wannan get din da ya nuna mana. Sai gamu a gaban motocinmu. Motar Bello bata nan, Babu maganar tsayawa bayani ban san ma motar wacce na shiga ba a cikinsu.Kowa ma salati yake yana neman yadda zai ceto rayuwarsa.

Daidai kan kwanar layin na yi ido hudu da su, ga Sharifah, ga Hamidah, ga yara ‘yan makaranta nan guda biyar sanye da kayan makarantar islamiyya har da Sharifah. 

Su ka bi mu da kallo kuwa har muka shude. Ni da Ramatu ne a motar duk da hankalinta na kan tuqi amma ta kalle su . Ba na so in fara yin magana dan ko na yi ba ta masu hankali ba ce. Na fi son ta fada da bakinta. 

Ramatu ta zazzare ido ta ce “kai ga wata mata mai shigen kama da Sharifah ta na kallonmu.”

Na zabura na ce “Alhamdulullah na gode Allah da ke ma kika fara ganinsu. Sharifah ce fa fatalwa take yi min.”

” Fatalwa kamar yaya? Daman akwai fatalwa? Haba Samha kamar wacce ba ki je makaranta ba? May be yayarta ce, kin san su na da yawa a gidan kuma kusan kamarsu daya su dukka.”

Bello muka gani a bakin titi yana sanye da fararen kaya ba kayan dazu ba ne a zaune a kan motarsa shi kadai. Sai yau kamanninsa da Sharifah ya sake bayyana, shima ya tsura min ido yana kallona ina kallonsa. Daga dukkan  alamu Ramatu bata gan shi ba hankalinta yayi titi wajen tsallakowa.

Ni na san ba Bello ba ne Sharifah ce take canja launi.

Kaina babu dankwali qawayena sunyi-sunyi in daura na kasa. Na dora hannu aka ina salati ina kuka. Yayin da Rsmatu ta kasa gane wannan lamari domin a ganinta damuwar ta yi yawa.

Ta ce da ni ” wai ke samha menene damuwarki? Sharifah bata mutu ba tunda ga gidan babu kowa ma.”

Na zabura na ce “babu kowa kamar yaya? Fatalwar da suke ciki fa? Na ga Sharifah da idanuwana har ta fisgo ni ta danna ni a cikin falo sannan ta bace. 

Yaron da muka gani ma fatalwa ce, Bello ma fatalwa ne, ga Hamidah da sauran yaran. Ke ma da idanuwanki kin ga Sharifah yanzu “

Ramatu ta girgiza kai ta ce “ban ga Sharifah ba na ga dai mai shigenta. Sharifah fara ‘yar gayu, wannan ai ko a mai aikinta ba zata dauke taba. Sai dai ko yayarta ko cousin su na kama dai.”

Shikenan abinda nake gudu ya faru, babu me yarda da ni, basa ganin abinda nake gani. Hauka ta tabbata a kaina. 

Na fara tunanin asibitin mahaukatan da zan zabawa kaina na private amma dan kada a kai ni asibitin dawanau. In hadu da masu yin ta gasken su lahanta ni. Abin sai ya yi min yawa ai kuma.

Hira Da Matattu Part 3 (True Life Story)  By Jamila Umar Tanko


Also Download: Hira Da Matattu 1 to 10 complete

Back to top button