Zamantakewar Aure

Abubuwan Dake Haddasa Matsalar Saurin Kawowa, Raunin Gaba Da Kuma Ƙanƙancewar Gaba Masu Wahalar Magani.

ABUBUWAN DAKE HADDASA MATSALAR SAURIN KAWOWA DA RAUNIN GABA DA KANKANCEWAR GABA,MASU WAHALAR MAGANI.

 

1=-BASUR hakika cutar basur idan dan adam ya bari har yakai da yayi masa tsiro,ko fitar baya yana kankantar da gaban namiji da dauke masa da sha’awa, sannan kuma yana saka masa yawan kasala da zafin jiki,da mutuwar jiki dayawan kasala da kuma shan wahala wajen bayan gida.

 

Matsi Ga Sabbin Amare Kafin Kije Gidan Miji

 

2=- SANYI Sanyi wanda kusan shine yafi yiwa aksarin jama’a illa wanda wasu ma basa sanin suna dauke dashi,wasu kuma sun sani amma basu dauke da da muhimmanci ba,wani zai kasan ce yana ganin farin ruwa ko kaikayin gaba ko zafin fitsari,amma sai kawai ya dauka bayan kwana biyu wai zai dena jinsa.

 

Hakika zaka iya dena jinsa a cikin kwana 2 amma matsalar bawai tafiya yayi ba,yana nan tare dakai,idan kuma ya tashi dawowa zai dawo ne da wasu sabbin matsalolin wanda suka sha banban dana baya.

 

Acikin matsalolin sanyi akwai zafin fitsari kaikayin gana, daukewar sha’awa, kaikayin jiki rabuwar fitsari 2,yawan fita fitsari a dare ba tare da kasha ruwa ba,zafin jiki hana samun rabu(haihuwa)fitar da kuraje a gaban namiji ko mace,kumbura gaban mace da saka mata kaikayi kamar ta shafa barkono da tsaga gaban mace da jin zafi wajen saduwa.

 

TSARABA GA AMARE DA MASU NIYYAR AURE FITA TA 1

 

3=- ISTIM’NA’I A gaba daya matsalolin da muka lissafa wannan shine yafi illa kuma yafi hatsari kuma yafi wuyar shaani da wuyar jin magani.

 

Da yawa wasu suna afkawa cikin Matsala aikata istim’na’i,wai don kaucewa zina,wanda kuma shima istim’na’i zina ce,sai dai laifin aikata shi baikai kafin zina ba,hanyar kaucewa afkawa jina ko masu fama da yawan sha’awa shine yin azumi,mutum ya tika yawaita azumi Wannan shi e hanya ingantacciya.

 

Amma yin istim’na’i yana da illoli masu yarin yawa wanda duk sanin mutum saidai ya fada maka wasu amma wasu kam baa gane su.

 

Maganin Rage Radadi Da Wahalar Nakuda

 

Akwai wadan da ke aikata wannan kuskure amma sai suce sunyi aunyi amma sun kasa denawa, wallahi wallahi Wallahi.mutum koda mutuwa yaji zaiyi idan be aikata ba yafi masa Alkhairi akan ya aikata shi.

 

Matsalolin da istim’na’i ke haifarwa suna da yawa amma ga wasu daga ciki.

 

Akwai zafin fitsari ciwon mara ciwon kai mai tsanani fitar farin ruwa daukewar sha’awa, mutuwar kwayoyin halitta, jin zafi a kwarkwaron azzakari yawan ciwon jiki zafin jiki kasala tamushe fatar mutum,bayyanar da tsufa cikin sauri,toshe ƙwaƙwalwa haddasa yawan mantuwa,da yawan kokonto,daidai sauran su wanda lokaci bazai bari mu kawo su baki daya ba.

 

Wadan nan dai sune kusan manyan abubuwan dake haddasa matsalolin da muka ambata a sama,bayan su akwai wasu matsalolin amma insha Allahu anan gaba zamuyi bayanin su.

 

Back to top button