Hausa novels

Asanadin Makwabtaka Book 2 Page 3 Complete Novel

*ASM2003*

 

 

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

 

 

 

 

 

“……..KIYI HAKURI FATUU….” Fuzge hannunta tayi kaman wadda

Shock yaja tunkan haulat d’in ta rufe baki tana fitar da numafashi da sauri sauri tace”Hakuri! ya zaki ce in yi hakuri bacin na gaya maki ina sonshi,ni dai bazan iya hakuri ba Haulat ki taimaka ki gaya man yadda zanyi in ba haka ba na gaya maki zuciyata bugawa zatayi” nan da nan idanun Haulat suka ciko tabb da kwalla ganin wai Fatuu ce a wannan halin ita da sam so bai gabanta bata da burin daya wuce tayi Karatu amman lokaci guda komae ya canja so yayi mata mugun kamu, duk gani take laifinta ne hakan, kamo hannun Fatun tayi cikin karewar murya tace “da inada shawarar da tafi wannan da na baki k’awata don nima banson ganinki cikin irin wannan mawuyacin halin to amman ya zamuyi dole saidae fa hakurin tunda dai kinga har ansa masu biki”,

cikin muryar kuka tace “to ko in fad’i mashi ina sonshi don Allah ya Aure ni nima?” D’an girgiza kai Haulat tayi jin wata Magana ta Fatuu wadda daga ji bata yi tunani wurin fad’inta ba,

Gyara zama Haulat tayi tace “duk da bansan ya kike ji acikin zuciyarki ba amman zan iya fahimta daga yanayinki tabbas nasan kina cikin mawuyacin hali, amman fa kisani in kika ce zaki hakan to fa ba k’aramin kuskure zaki yi ba kizo ki k’ara jefa kanki wani halin don karshe nasan ba samun biyan buk’ata zaki ba, ke da kanki kince yayi farincikin zuwanta sosae kinga alamar yana sonta kenan sannan yanzu a gabanki ta fad’i cewa an gaya mata ni aminiyarki ce wa kike tunanin ya fad’i mata hakan in ba Ya Haisam d’in ba, kinga kenan duk wani abu game damu yana sanar mata ko daga kanki ma ai zaki gane yadda ta sanki sosae tun kafin ta ganki a zahiri to baki tunanin in kin gaya mashi zai iya sanar da ita kuma in tasan hakan mi kike tunanin zai faru? Duk fa yadda kike ganin kaman tana da kirki wllh tasan da wannan Maganar za’a samu matsalane babba don ba yarda za’ai ace bata kishin Ya Haisam baima yuwuwa wllh kuma tana iya sanar da Hajiya k’arshe in Maganar ta dawo kunnan gwaggo mi kike tunanin zai faru? kiyi tunani Fatuu kowa na iya yi maki kallon mara hankali ma ”

 

“Amman ai ba lalle in yaji irin wannan Maganar ba ya sanar da itan” k’ara girgiza kai Haulat tayi don ta fahimci Fatuu bata cikin hayyacinta shiyasa bata ganin hakan a wani abu tace “to kina tunanin in kin fad’i mashin Auren naki zaiyi, ni na tabbatar hakuri zai baki Ya nuna maki yana da wadda zai Aura kiyi tunani bafa zai ta6a aurenku ba ku biyu, ai ko danginsu ma bazasu ta6a yarda ba kar fa ki manta yar’uwarshi ce waye zai goyi bayan ayi mata kishiya a cikinsu bafa mai son kishiya Fatuu sai dole, duk da halin da kike ciki kar ki bari tunaninki ya gushe kizo kuma ki abunda zaki danasani ki daure ki cije ki yak’i zuciyarki ta fitar da Ya Haisam daga cikinta shine abunda yafi Alkhairi” bin ta da ido kawae Fatun keyi yayin da cikin ranta take juya Maganar Haulat d’in lokaci guda ta tuno da Farha da Abubuwan data rink’a yi mata lokacin data fara ganinta da kuma wani zuwa da suka k’ara yi yanzune ta gano dalilin da yasa hakanan ta d’auki karan tsana ta d’aura mata ashe kishi take taya yar’uwarta, ganin tayi shiru yasa Haulat cigaba da tausarta tana k’ara nuna mata had’arin dake tattare da abunda take tunanin yi na sanar mashi,

 

K’arshe dai saidae fasa zuwa islamiyyar Haulat tayi sai gab da Magrib ta bar gidan duk jikinta yay sanyi lakwas, Tun bayan da Haulat d’in ta tafi tay zaune saman gado ta had’e kafafunta ta d’aura ha6arta idonta akan bangon d’akin tana ta nazarin Maganganun Haulat tabbas tasan in har Gwaggo taji wannan Maganar kashinta ya bushe k’arshe ma tana iya cewa zata maida ita ruga, tsorone ya kama wani 6angare na zuciyarta yayinda wani 6angaren keta k’ara azalzala mata son Haisam tana a hakan aka kira sallar Magrib amman ta kasa tashi taje tayi sai can bayan an gama ta daure ta saukko daga gadon ta fita don yo alwala, bayan ta gama sallar jin jikinta sam bai mata dad’i ne yasa ta mik’e ta cire rigar jikinta ta d’aura towel ta yafa gyale saman kanta ta nufi toilet don yin wanka, bayan ta fito tana cikin shiryawa ta jiyo sallamar Fanan dam kirjinta yay irin bugun da yakeyi duk in taji sallamar tata, a bakin kopar d’akin ta k’ara yin sallama a hankali Fatun ta amsa ta d’aga labulen ganinta tsaye yasa ta washe baki tana mata dariya ta nufeta tana Fad’in”am so happy seeing u’r recovering Sis Zarah” tayi Maganar hannunta guda kan shoulder d’in Fatuu, d’an guntun Murmushi ta daure tayi mata ta tambayeta wanka tayi ne Fatun ta d’aga mata kai, kama hannunta tayi suka nufi gefen gado ta aje ledojin dake a d’ayan hannunta tace gashi taci tasan bata jin dad’in bakinta, ita dae fatun shiru tayi hakan yasa Fanan ta bud’e leda d’aya ta fiddo shawarma bayan ta warware ta kai bakin Fatuu tana Murmushi tace “ki daure kici kinji, ina son inga kin samu lafiya kin koma normal condition naki cos am not happy seeing u like dis” d’an d’aga ido Fatuu tayi ta kalleta ta jinjina mata kai alamar tabbatar mata da abunda ta fad’a, alamar ta bud’e bakin tayi mata da nata bakin kaman bazata bud’e ba sai kuma ta d’an bude kad’an tasa mata ta gatsi yar kad’an, ganin tana kokarin k’ara bata yasa ta kai hannu zata amsa amman sai ta girgiza mata kai tace “in na baki bazaki ci sosae ba” ba yarda Fatuu ta iya haka ta rink’a bata tana ci har ce mata tayi ta k’oshi amman tak’i k’yaleta har saida Fatuu ta ruk’e hannunta tana yamutsa fuska sannan ta k’yaleta ta bud’e d’ayar ledar ta fiddo ice cream shima ta fara bata a bakin d’an kad’an tasha ta kauda kai tana Fad’in ruwa take son sha, tambayarta tayi inda ruwan yake Fatun ta mik’e tace zata je tasha, a tare suka fito ta shiga Falo ta d’aukko ruwan ita kawae so take Fanan d’in ta tafi amman saida ta rakota har Parlorn tayi mata tsaye saida tasha ruwan, bayan sun fito tace mata tazo Ya Haisam na waje yaganta ya damu da ciwon da take sosae, bata ce komae ba ta bita dama akwae gyale asaman kanta, lokacin da suka fita yana saman bike zaune yana latsa wayarsa tunda suka tunkareshi gabanta ke bugawa da sauri da sauri suna zuwa gabanshi cike da farinciki Fanan tace mashi ga Zarah ta fara samun sauk’i, idonshi akanta yana d’an Murmushi yace mata ya karfin jikin tace da sauki yace Allah ya bata lpy ta amsa da Amin, ce mashi tayi saida Safe yace Ok ta juya zata tafi Fanan tay saurin kama hannunta suka tafi tare saida ta kaita cikin gidan tace mata saida safe ta juya, da hanzari ta nufi d’akinta tana shiga ta fad’a saman gado tasa wani irin marayan kuka mai cin rai ganin Haisam din ya k’ara dagula mata lissafi, k’afartace ta ta6a ledar da Fanan ta kawo mata aikuwa ta mik’e ta d’auki ledojin tai wurgi dasu k’asa har ice cream d’in data bata ya zubo hakan bai isa ba ta rarumi filo shima ta wurgoshi k’asa, ita yanzu shikenan ta rasa Ya Handsome, duk Rayuwar da take hango ma kanta zata yi dashi watace zata yi hakan, a zuciyarta take ta raya hakan, sosae tasa kuka mai sauti tana cikin wannan halin gwaggo ta dawo don bata bari sai lokacin tashi ba saboda Fatun na ranta, tana shigowa gidan d’akin Fatun ta nufa tun kafin ta k’arasa ta jiyo kukanta aikuwa da sauri har tana tuntu6e baiwar Allah ta fad’a dakin, ganin halin da take ciki ba k’aramin tashi hankalinta yay ba nufarta tayi tana tambayar mike damunta ta d’agota tana kallon fuskarta da tayi jage jage da hawaye nan da nan itama idonta ya ciko da kwalla don ganin halin da take ciki yasa ta tabbatar ma kanta da zargin da take yi game da ciwon Fatun, hannunta ta kamo ta d’aura kan kirjinta tana Fad’in “Gwaggo k’irjina zafi, zai 6are ki taimaka man” nan da nan kwallan suka fara zubo mata ta hau yi mata Addu’oi tana tofa mata, A hankali ta fara jin sauk’in k’irjin don a halin da take ciki ganin Mutum a kusa da ita wani sauk’i ne, lamo tayi a jikin gwaggo tana maida numfashi gwaggon na cigaba da tofa mata Addu’oin tana shafa kanta, ganin ta natsu tay shiru yasa ta d’an leka fuskarta cikin harshen fulatanci ta tambayeta da sauk’i ta daga mata kai alamar eh sannu tayi mata taci gaba da shafa kanta tana adduoin can ta d’ago kanta tace bari in zubo maki Abinci da sauri ta girgiza mata kai alamar a’a tace “to ayi ciwo ba cin abinci Fatuu ki daure ki d’an ci ko ba yawa” Murya a disashe tace “naci shawarma” da d’an mamaki ta tambayeta inda ta samu shawarmar ta d’aga yatsa ta nuna mata ledojin dake yashe a k’asa tace “Aunty Fanan ta kawo” jinjina kai tayi tace “to amman kin ci d’in da gaske?”

“Eh itama ta bani a baki” d’an Murmushi gwaggon tayi tace “Allah sarki, wllh ban ta6a ganin mace irinta ba Allah ya bata komae amman sam bata da girman kai bata d’auki duniya da zafi ba gashi nan tun yanzu ta fara cin ribar hakan Allah ya bata Abokin rayuwa Nagari, gaba d’aya naji masu dad’i Allah ubangiji ya albarkace su da zuria ta gari kaman yadda suke” k’asa k’asa Fatun tace Amin idanunta sun ciko da kwalla amman bata bari sun zubo ba, mik’ewa gwaggo tayi ta d’aukko ledar ta dawo ta zauna tace “to tashi ki d’an k’ara” tayi Maganar tana fiddo sauran abubuwan dake ciki wanda duk snacks ne da sauri ta girgiza mata kai don ita ko k’amshinsu ma bata son ji ganin tak’i ci ne yasa gwaggo ta fita taje ta d’ebo mata Abinci ta tasata gaba saida taci ba wani mai yawa ba, bayan ta gama tace mata tayi sallar isha tunda an fara kira sai ta kwanta inta yi bacci zata k’ara samun sauki ta amsa mata da to, tana gama sallar akan abun sallar ta kwanta tayi lamo tana ta tunane tunane itama gwaggo sallar taje tayi tana son tayi wanka amman kuma tana son taje wani wuri hakan yasa ta bari in ta dawo tayi don kar dare yayi sosae saida ta leka d’akin Fatun ta ganta a kwance duk a tunaninta bacci take ta juya ta nufi kopar gida lokacin Amadu ya dawo daga Masallaci yana kokarin bud’e shago ganin gwaggon ya nufeta yace “wani wuri zaki ne?” da yar damuwa tace “eh zanje wurin Malam tanimu ne inason gaya mashi game da halin da Fatuu take ciki ko zai yi mata Addu’a” yace “jikin har yanzu kenan, d’azun na dubata sau biyu duk a kwance nike isketa inna tambayeta ya jikin sai tace man da sauki”

“Eh ai kasan irin wannan ciwon dama haka yake yanzu da sauki anjima ba sauki, yanzu fa dana dawo baka ga halin dana isketa ba da alama sun rik’e mata k’irji ne tana ta cewa zafi take ji kaman zai 6are” girgiza kai yay yace “Allah ubangiji ya bata Lafiya mai d’orewa, muje to in raka ki”

Tace “A barta ita kadae kuwa, ko ka shiga gidan in je in dawo sai ka bud’e shagon” amsa mata yay da to ya wuce itama ta tafi, bata k’arasa gidan bama ta had’e dashi a hanya ya dawo daga Masallaci suka tsaya suka gaisa kafin tayi mashi bayanin halin da Fatun take ciki,sosae ya jajanta mata yace zuwa gobe da safe a zo a amsar mata ruwan Addu’a yace da za’a samu zam zam ma da yafi tace bari taje zata sa Amadu yaje ya siyo sai a aiko dashi ya amsa da to ta tambayi abunda za’a bada na sadaqa yace ba sai ta bada wani abu Allah ya bata Lafiya, tayi mashi godiya sosae da Addu’a kafin ta tafi. Tana komawa gidan ta iske Amadun a d’akin Fatuu yana zaune k’asa kusa da ita Addua ya gama yi mata yana d’an yi mata fira sama sama take tanka mashi, sak’on yaje ya siyo zam zam d’in ta bashi tace in ya dawo ya wuce ya kaima Malam Tanimun, wannan shi ake kira da cuta daban Magani daban don ma dai Maganin ta wani bangaren zai taimaka don ba abunda yafi karfin Addu’a.

 

Bayan sun isa gida saida ya raka Fanan har d’akin Hajiya lokacin tana zaune kan Sallaya ta gama sallar Magrib tana jiran isha suna shigowa cike da tsokana tace “Luv birds an dawo” nufarta Fanan tayi tana dariya ta zauna kusa da ita ta kwantar da kanta kan kafad’arta, gaisawa yay da Hajiya yace zaije yay wanka Hajiya tace ya bari yay sallar isha sai yayi yanzu ana iya kiran salla yana wanka ya amsa mata da Ok ya nufi bakin gado ya zauna,

“Wai nikam ya jikin Fateema ne?” Hajiya ta tambaya Fanan tace “tana samun sauk’i sosae sunje yanzu” jinjina kai Hajiya tayi kafin tace “Allah ya k’ara sauki” amsawa sukae da Amin harda Haisam d’in, bada jimawa ba kuma aka fara kiran isha ya mik’e yace zaije Masallaci Fanan ta d’aga hannu cike da kauna tana mashi bye bye har ya kama kopa zai bud’e tace “Babe kai man Addu’a in baka twins nine Months after we get married” hannu Hajiya ta kai zata bugi bakinta ta fad’a jikinta tana dariya shima dariyar yay ya fice, bayan angama sallar part d’inshi ya nufa yayi wanka ya shirya kafin ya dawo part d’in Hajiyar lokacin itama Fanan din tayi wanka ta shirya cikin kayan bacci riga da wando milk masu santsi kanta tasa hula itama milk ta saki brown gashinta, atare gaba d’ayansu suka nufi Dining don cin dinner, kaman sauran lokutta suka rink’a ciyar da junansu har Hajiya nama Haisam tsiyar yadda yake cin abinci yanzu don yaga Fanan ita daya raina sai taita fama dashi yak’i ci sosae sai ya gadama, dariya Fanan d’in tayi tace baison 6acin ranta ne hajiya tace sai nata yake so ko, bayan sun gama falon suka koma suna kallo Fanan dai na manne dashi lokacin da Hajiya ta mik’e tace ita dae bacci take ji shima tashi yay ya mik’ar da Fanan d’in ya rakata har cikin dakin, saida yaga ta kwanta ya manna mata kiss a gefen fuskarta yay masu saida Safe ya nufi hanyar fita idon Fanan akanshi yana kama handle d’in kopar ta d’aga murya tace “I luv u nd I can’t do without u Babe” juyowa yay ya sakar mata k’ayataccen murmushi kafin ya fice Hajiya dake zaune gefen gadon ta ta6e baki tana girgiza kai Fanan taja duvet ta rufe fuskarta tana dariya.

 

Allah sarki gwaggo tsakar dare har tashi tayi tayi salla tayi ma Fatuu Addu’ar Allah ya yaye mata lalurar da take fama da ita sosae tayi mata Addu’oi,Washe gari da Asuba ta tada Fatun tayi salla bayan ta gama ta koma ta kwanta itama gwaggon komawa tayi saida gari ya waye ta tashi don ta had’a masu breakfast lokacin da Amadun yazo amsar nashi tace mashi in ya gama yaje wurin Malam tanimu ya amso mata sak’on yace to, a d’akin nata ta kai kayan breakfast d’in ta tashi Fatuu tace ta lalla6a taje ta wanko baki, bayan ta dawo ta had’a mata tea mai kauri tace ta daure ta sha zata ji dadin jikinta, ba laifi taci abun breakfast d’in sosae don ta danji dad’in jikinta ba kaman jiya ba, suna cikin yin karin kumallon Amadu ya kawo ruwan addu’ar ya fad’i mata yace a bata tasha safe da dare sai kuma a shafe mata fuskarta da kirjin nata daya rik’e, sosae gwaggo taji dad’i bayan ya tafi ta bud’e marfin gorar ta mik’a ma Fatuu tace “kiyi bismilla kisha” zuru tayi tana yi mata kallon rashin Fahimtar abunda take batan ganin hakan yasa tace “ruwan Addu’a ne ganin halin da kike ciki jiya da daddare naje na fad’a mashi shine yace zai maki Addu’a yau da safe aje a amsa” kasa Magana tayi tana dai ta kallonta ita kuma gwaggon ganin kallon da take matan yasa ta yin tunanin suna iya hanata sha hakan yasa ta matsa tana niyyar kwafa mata robar a baki Fatun tasa hannu ta amsa ta kai bakinta bayan tasha ta mik’a mata ta zuba a hannunta ta shafa mata kaman yadda aka ce,

“Yauwa in sha Allahu zaki ji kinsamu sauki ki koma ki kwanta” gwaggo ta fad’a da d’an Murmushi don taji dadin yadda Fatuu tasha ruwan Addu’ar, mik’ewa tayi ta hau gadon tay lamo ta shiga duniyar tunani zuciyarta na raya mata Ya Handsome na can suna shan soyayyarsu da Fanan ita tana nan tana ta fama, runtse idonta tayi yar siririyar kwalla ta zubo mata tasa hannu ta goge batare data bud’e idon ba. Misalin karfe sha biyu saura gwaggo na cikin Kitchen Fatuu ta fito ta tsaya a bakin Kitchen d’in tana ganinta ta nufota tace “Sannu kin tashi” kai ta d’aga mata tace “to ya jikin?”

“Da sauki sosae” ta bata amsa a sanyaye,

“Alhamdulillah, Allah ya k’aro sauki, halan kin gaji da kwanciyar?” kai ta sake d’aga mata tace “to ki shiga Falo ki zauna ko ki kunna kallo”,

“Ki kawo in yi wanke wanke in baki yi ba” ta fad’a idonta akan gwaggon duk bata jin dad’in yadda ta saka ta damuwa,

“Har kin samu sauk’in da zaki iya yin aiki kije ki zauna zanyi, so nike in gama amfani da abubuwan da suka 6aci sai in had’a in wanke gaba d’aya” tace “ki kawo zan iya” gwaggon tace to don dama tafi son taga ta dawo kamar da, tana cikin yin wanke wanken Fanan tayi sallama ta shigo jikinta sanye da Maroon skirt babba mai tattara a sama sai rigar brown da ratsin maroon kanta ta yafa Maroon d’in veil kafafunta sanye da flat shoe brown ta matukar yin kyau, suna had’a ido da Fatuu data d’aga kai ta kalli kopan shigowan tana ganinta ta saki Murmushi ta nufeta tana Fad’in “am so Happy sis Zarah kinsamu lpy ko” kai ta d’aga mata kafin a hankali tace mata ina wuni ta amsa still da fara’a, gwaggo ce ta fito daga cikin Kitchen tana fadin”Muryar wa nike ji kaman y’ata Fan…fanna ko haka sunan yake ni shige man yake wllh” tana dariya ta gyara mata sunan tace yauwa bazata kara mantawa ba,

 

“Naga Sis Zarah ta samu lpy nayi farinciki” da jin dad’in Maganarta gwaggo tace “aikuwa Alhamdulillah sauki ya fara samuwa, ki shigo falo” ta kai maganar tana nuna mata kopar falon,

“No let me help her” tayi Maganar tana tattare hannun rigarta alamar zata taya Fatuu wanke wanken da sauri gwaggo tace “Don Allah ki kyaleta ta idasa ita tace zata yi bama ni na bata tayi ba” tace “ba wani abu zamu gama tare, inata so mu had’u da ita muyi fira sosae and nazo kuma bata lafiya” d’an girgiza kai gwaggo tayi aranta tana Fad’in wace irin yarinyace wannan,ganin tana niyyar duk’awa yasa da sauri tace bari in kawo maki kujera to tunda kin matsa sai kinyi, bayan ta kawo mata kujerar tace ta curo agogon hannunta kar ruwa ya shiga ya lalace ta cire ta mik’a mata harda wayarta, bayan ta zauna d’auraya ta shiga yi mata tana kifewa a cikin kwando tana d’an yi mata firar india akai akai take d’agowa ta kalleta da Murmushi a fuskarta itama fatun sai ta d’an yi mata a haka har suka gama Fatuu tace mata ta shiga falo tace to, bayan ta kai kayan kicin ta dawo ta wanke wurin itama ta nufi Parlon tana niyyar zama kan kujera Fanan dake zaune kan 3 seater tace tazo ta zauna kusa da ita batare data ce komae ba taje ta zauna, gallery d’in wayarta ta shiga ta d’an kwanto gefen Fatun tana nuna mata videos d’insu ita da friends dinta da suke karatu tare acan india, tun dai Fatun na dar dar harta saki jiki abunda ya bata dariya ta d’anyi wani kuma tayi Murmushi suna haka gwaggo ta shigo zama tayi kan 1 seater fuskarta da Murmushi don taji dad’in ganin yadda Fatuu ta d’an saki jiki, d’agowa Fanan tayi tace ma gwaggon “sannu granny kinata aiki ko inzo in tayaki?” d’an bud’a ido tay tace “ai ba wani aiki bane Abinci ne nike yi kuma ban tunanin ma kin ta6a cin abunda nike dafawa balle har ki iya tayani” da d’an mamaki kan fuskarta ta tambayeta miye take dafawa tace mata dambu, a hak’ik’ance tace “I know dambi mana….” tun kan ta k’arasa gwaggo tasa dariya fatuu ma saida ta d’anyi,

“To ai y’ata Fanan tun wurin fad’in sunan nashi ma kinga ya nuna baki sanshi ba” da sauri tace “Serious granny na ta6a cin dambin ba shine kaman cous cous ba?” kai gwaggo ta daga”tabbas shine amman ba dambi sunanshi ba dambu ake cewa Fanan d’in tace yauwa shi to take nufi,

“Ai da har ina tunanin in sama maki wani abun kici bansan kin iya cin shi ba” girgiza mata kai tayi tace “zanci sosae na dad’e banci shi ba Mom na mana” mik’ewa gwaggo tayi tana Fad’in to bari taje tayi sauri ta gama ko don d’iyarta taci, Fanan d’in na Dariya jin Maganar gwaggon, kiran sallar Azahar aka fara suka tashi ita da Fatun suka je d’akinta su kai salla bayan sun gama suka dawo falon lokacin gwaggo ta kawo masu dambun na Masara ne yaji zogale sai kamshi ke tashi, tare ta zubo masu a babban plate don tasan ko ta zubo masu kowa da nashi karshe Fanan din sai tace a had’a masu, sosae taji dad’in dambun duk yadda Fatuu taso k’in ci da yawa ta hanata tace in bata cin abinci sosae koda ta samu lafiya karfin jikinta bazai dawo ba, ba yadda ta iya haka ta rink’a turawa ba don tana wani jin dadinshi ba, koda suka cinye gwaggo tace a k’aro masu cewa Fanan tayi eh sam bata nuna bak’unta kai kace yar ‘uwarsu ce ma, k’in ci Fatuu tayi bayan an k’aro tace ita ta koshi dole ta kyaleta taci gaba da ci ita kadae, tana cikin ci Hajiya tayi sallama gwaggo dake zaune itama tana cin dambun ta mik’e da sauri ta fita tana Fad’in “Maraba da Hajiya” ta amsa mata da yauwa tana nufota Saude na bayanta itama gwaggo tayi mata sannu da zuwa ta gaisheta da fara’a ta amsa mata tace su shigo, suna shiga idon Hajiya ya sauka kan Fanan da ta tura dambu a baki tana mata dariya Hajiya ta ruk’e ha6a tace “Oh su shanshani kafan yawo ana nan ana kwalama ashe, to Allah ya jikanka dambu ki dai bi a hankali in ba haka ba ya shaqe ki” tayi Maganar tana kokarin zama kan kujera gwaggo dake Dariya tace “Mutum da gidansu ai ba kwalama take ba” Fanan d’in ta gyad’a kai alamar atoh,nuna ma Saude kujera gwaggo tayi tace ta zauna tayi tsaye ta nufi wurin ta zauna, gaisawa suka shiga yi suka yi mata ya mai jiki tace da sauki kallon fatuu dake zaune kan carpet gefen Fanan tayi shiru tace “Oh sannu Fateema kinji, Allah ubangiji ya yaye maki wannan lalura baki d’aya ki huta wannan zuwa Dam bai yi dad’i ba sam” gwaggo dake d’an Murmushi tace “to ya za’ai haka Allah ya kaddara” hajiya tace “hakane amman dae da sauki sosae ko?”

“Eh jiyane dana dawo dae na iske abun yayi tsanani har tana kirjinta zai 6are to sai nayi mata Addu’oi na kuma je wurin Malam tanimu na fad’a mashi halin da ake ciki shine ya bukaci ruwan zam zam yayi mata Addu’oi yau da safe aka amso tasha na shafa mata kaman yadda yace Allah cikin ikonsa ta samu sauki sosae wllh” gaba d’ayansu duk suka girgiza kai alamar tausayawa ita dae Fatuu zuru tayi tana binsu da ido don ta fahimci ciwon da suke tunanin yana damunta, mik’ewa gwaggo tayi tace bari a zubo masu dambu Hajiya ta tambayeta na miye tace na Masara ne tace to a zubo masu kad’an don ta kwana biyu bata ci shiba, wuri daban daban ta zubo masu ita da Saude Hajiya na ganin haka tace maimakon ta zubo masu wuri guda sai sun cinye masu abinci dama ga wata acicin nan sai turawa take Fanan na jin haka tasa dariya suma duk dariyar suke, bayan sun gama Hajiya ta tambayi gwaggo bazata aiki bane yau tace tana son zuwa amman tana tunanin yanayin jikin Fatuu don jiya yadda ta dawo ta sameta hankalinta ba k’aramin tashi yay ba, Fanan na jin haka tace taje aikinta zasu zauna tare Hajiya tace “to ku taho can gida mana in ta dawo ba sai ta dawo ba” girgiza kai Fanan tayi tace “ban komawa fushi nake da Babe” Dariya Hajiya tayi tace “Saboda yau yak’i zuwa dake aikin kika yi fushi dashi” kai ta d’aga alamar eh, tace “hum dama dae zaki iya duk cika baki ne” gwaggo dake dariya tace “ai y’ata kishinki yake shiyasa bai je dake ba” bayan sun gama gaba d’aya suka nufi gidan Hajiya………..

.

Asanadin Makwabtaka Book 2 Complete Novel Txt

Back to top button