Hausa novels

Gargadar So Chapter 55 By M Shakur

Ranan gabaki daya Hawwa jitayi batajin dadin komi, har Ramla saida taga Hawwa was not in good mood sabida yanda tai shiru batama iya magana da kyau, sai lissafi take how zata fita daga this mess? Idan yanuna video ko pictures yacema Baba tayi kokarin mai fyade duk zasu yarda ta ina kunya zai barta ta kallesu dagashi har Ammi that means everything Ni’ima said is true about her.Washe gari tsaf ta shirya ta tafi aiki around 12 DIG yakirata tashigo office nashi murmushi yamata yace “okay Ogana gabaki daya yakirani yace nabaki leave sabida kiyi planning wedding naki da kyau an baki 60 days” zaro idanu Hawwa tayi tace “Innalillahi 60 days that’s 2month, mezanyi da all this time Sir”? Dan murmushi DIG yamata yace “Hawwa have you seen abinda nafada miki jiya? Imagine danaje wajen Babanki to, wannan da Ogana ne yakira yace abaki 2months wedding leave abinda 3weeks ake bayarwa but naki is different, so zaki iya tafiya, we will see you on the wedding day in sha Allah idan kinyi inviting namu, Hawwa May Allah bless your home, Allah miki albarka, nasanki da ibada da yawan azumi Allah shine maganin komi so call on to him shine yasan wats best for you” kuka taji yana zuwan mata amman tahadiye ta gyadamai kai ta tashi ahankali tafito tana tafiya zuwa office nata wani officer yace “Miss Hawwa kinada bakuwa bamu barta tashigo nan ba tana chan” yamata pointing waiting room nasu, da mamaki tadinga tunanin waye ko wacece zatazo wajenta, dudda Ammi na hanya dan yau zata dawo amman ai baici ta iso ba tace mata by 11 zatabar gida, why is she even thinking of Ammi? Ammi bazata taba zuwa wajen aikinta ba, hanyar waiting tayi ganin Ni’ima taci gayu cikin atampa mai kyau ta yafa dan gyale ta rike handbag a hannunta yasa ta tsaya turus Ni’ima tamata murmushi kawai ta taso da gudu tazo batai wata wata ba ta rungumeta tace “Best suprise” chak Hawwa ta tsaya without hugging her back harsaida Ni’ima tadago ta kalleta tace “are you not happy to see me?” Dan girgizamata kai Hawwa tayi tace “no is not like that” dasauri Niima tace “muje office naki anata kallonmu anan” kawai takama hannun Hawwa, ahankali Hawwa tabita har zuwa office nata suka shiga idanunta ne suka sauka akan iPhone 15 pro max na Hawwa dake kan table last she check Hawwa was using Samsung S10 harya chanza mata wayane? Lallai gayen nan, abu taji ya tsaya mata arai dasauri tasaki hannun Hawwa tai wajen wayan tadauka tace “wow kin chanza waya Hawwa? Kin koma iPhone? Ni fa banson iPhone ance basu rike charge duk application saika saya? Baka iya downloading movies anyhow, komi kudi, Ke kika siya ko mijinki ya saya miki”? Karasowa Hawwa tayi ciki tazauna ahankali tace “shi ne” wani irin murmushi Ni’ima tana danne bakin ciki da zafi datakeji aranta tayi tace “awwwn lovebirds, ohh my my, Hawwa I’m happy for you Allah yaga how patient you are yabaki mai sonki, wai yaushe kuka hadu ne baki taba bani labarinsa ba, eh yaushe kuka hadu?” Baki Hawwa tabude zatai magana akai knocking kofan da sauri dukansu suka kalli kofan Abraham ne ganin Ni’ima yasa ya tsaya yace “can I see you Miss Hawwa”? Gyadamai kai tayi tace “sure” ta mike suka fice tarufe kofan dawani irin sauri Ni’ima ta danna screen din wayan ganin babu password yasa tashiga cikin wayan dasauri tace “calls” call log tashiga d only number datai magana dashi for long batai saving ba saina Ammi datai saving da Ammi hakan yasa tashiga kwashe number da she’s sure Khaleel ne dan ya kikkirata bata dagawa daidai tana gama kwasa tanaji ana taba kofan da sauri tafita tarufe wayan ta ijiye kan table Hawwa ta shigo rike da Maltina ta ijiye gaban Niima, Ni’ima tace “thank you Best” Hawwa ta zauna Ni’ima tace “gist me Best ya shirye shirye? Kayan daki kayan kitchen? Na kaiki wajen wanda yamin na dakina?” Ahankali Hawwa tace “Baba da Ammi are in charge of everything bansan mesuke ba” gyadamata kai Ni’ima tayi saikuma tace “wai har yanzu kin rikeni azuciye ne? Best I’m really sorry wlh ina sonki you mean the world word to me kinji” dan lumshe idanu Hawwa tayi saita gyadamata kai tareda bude idon, Ni’ima tace “anko fa? Nafitar miki da anko?” Shiru Hawwa tayi saikuma ta gyada mata kai, murmushi Ni’ima tayi tace “thank you, can you call Baban Yaseer for me yanzu da wayan naki”? Shiru Hawwa tayi all maganganun Ammi nadawo mata ahankali tace “Ni’ima banso nakara shiga lamarinki da Baban Yaseer I promise kaina that, for licence naki nayi magana za’a samu nasara in sha Allah” murmushin karfin hali Ni’ima tayi tana danne abinda takeji azuciyanta tace “shikenan hakan ma I’m grateful after kalan abinda namiki not everyone will even help me that much, kinada zuciya mai kyau Hawwa, thank you” gyadamata kai Hawwa tayi, daidai nan wayan Hawwa yahau ringing Ni’ima ta saci kallon screen din ganin number data kwashe ne kaman Hawwa bazata dauka ba, but ganin Ni’ima and tanaso tanunama Ni’ima she’s cool with Khaleel kodan tacire tunanin Baban Yaseer da ita aranta yasa gently tadauka takai kunnenta, murya chan kasa Khaleel yace “I sent a delivery guy what’s your office number”? Shiru tayi chan tace “baza’abarshi ya shigoba” dan murmushi yayi yace “no one can stop my delivery, office number Kulu” murya chan kasa tace “0040” katse wayan yayi almost 1min saiga knocking anatse Hawwa tace “come in” bude kofan akayi wani delivery guy ne rike da flowers na red roses da akai wrapping katon gaske, saikuma platter na yan gayu na different intercontinental dishes da note ajikin both of them delivery guy din yace “I’m looking for Mrs Hawwa Alhassan Ibrahim Khaleel” Ni’ima jitayi yawun bakinta yayi daci da kyar tahadiye, ahankali Hawwa ta mike ta nunamai table din zuwa yayi yafara mika mata flowers din dake kamshi sosai like Khaleel plus kamshin roses again, office din yacika da kamshi, karba tayi ta ijiye sannan yabata platter na abincin shima ta ijiye yabata note nashi tai signing sannan ya tafi, kafin Hawwa ta zauna har Ni’ima tasa hannu tadauki card dayayi note ajiki tace “love bird bari muga meya rubuta miki” dasauri kafin Hawwa tace wani abu, tace “_I know you haven’t had breakfast banson matana looking skinny you are too light for my liking, eat and get chubby, cheers to starting your leave today! Sowie about yesterday with love Mijin Kulu_”Murmushin dole Ni’ima tayi ta ijiye card din, taja platter box na abincin tana budewa tace “eat mana” wow tafadi ahankali lafiyayen abinci ne aciki dat are very hot, mash potatoes da chicken wings, samosas, Pasta sai Mandi rice, ga salad ga fruits juice very cold ga sweet da cingum na mentos, kallon abincin itama Hawwa take, deep down she feels happy but then she don’t wanna feel d happiness ahankali tace “ke kici idan zakici” dasauri Niima ta girgiza kai tace “a’a inacin abinci nafito” gyadamata kai Hawwa tayi saita rufe platter ta matsar gefe idanunta suka sake saika akan rose din kawai ta tsaresu da idanu Niima duk na kallonta, aranta tace “munafukar mugun son mijinta take amman tana bobboyewa, hala ma sun riga sun sadu” wayan Hawwa ya shiga ringing dasauri ta waigo ganin Khaleel ne yasa ahankali tadauki wayan takai kunne murya chan kasa Khaleel yace “have you eaten? Is the food good? Kona chanza mana Chef? Shizai dinga mana girki bayan auren mu, abincin yayi”? Shiru Hawwa tayi murya ciki ciki tace “mesa baka dafa da kanka ba”? Dan zaro idanu Khaleel yayi yace “Momy bata barina in kitchen I don’t know me akayi a kitchen” murya chan kasa Hawwa tace “uhnn Moms boy” murmushi kadan Khaleel yayi yace “do you like the rose?” Kin magana Hawwa tayi, ahankali Khaleel yace “but I said sowie about yesterday” murya chan kasa Hawwa tace “sowie is not sorry” dan dariya kadan Khaleel yayi ahankali yace “wa akace tana tareda ke a office?”

Back to top button