Kannywood

Abba hikima yayi martani akan murabus din Sheikh Daurawa

Fitaccen lauya nan barista abba hikima yayi martani akan saukar mukamin da sheikh Aminu Ibrahim daurawa Kano yayi a yau din nan safiyar juma’a inda abba hikima yake cewa.

Ina roƙon gwamnan Kano da ya ƙi karɓar murabus ɗin Mal. Daurawa kuma a zauna a ɗinke wannan ɓaraka. Don Allah.

Lokacin da AKY ya ci zaɓe, aka kafa transition kwamiti, an saka ni cikin kwamitin shariah wanda a karkashin wannan kwamiti mai ma’aikatu kusan 9, Hisbah ta faɗo. Muna cikin aikin wannan kwamiti sai aka rarrabawa ma’aikatun karkashin yan kwamiti, sai hukumar Hisbah ta faɗo karkashina.

Wannan ya bani damar yin zuzzurfan binkice akan Hisbah, ayyukanta, matsalolinta da sauran su. Sannan ya bani damar fahimtar irin sakacin da shugabancin Hisbah na wancan lokaci yayi wanda hakan ne yasa ayyukan Hisbah da ƙimarta suka dakushe.

Amma da zuwan Daurawa, wannan ya chanja. Duk da gaskiyane akwai buƙatar gyara a wasu daga ayyukan Hisbah, amma lallai Mal Daurawa yana kan nuna nagarta da sanin makamar aikin. Kuma daf yake da cin gagarumar nasara.

Maganganun gwamnan Kano a bainan nasi kuma a dai-dai wannan lokaci da ake ta kai ruwa rana mutane masu bayyana baɗala ba dai-dai bane. Kuma don Allah ya janye su. Domin bai wuce yin kuskure ya kuma gyara ba. Amma shima Mallam don Allah, ya fahimci aikin Allah ya gaji jarrabawa. Idan an samu damar kuma ya zama babu zubewar mutunci ko ƙima, ayi haƙuri

Allah ya basu ikon baiwa shaiɗan kunya domin ci gaban Kano. Amin.

Back to top button