Hausa novels

Asanadin Makwabtaka Book 2 Page 58 Complete Novel

*ASM Bk2058*

 

_Destiny may be delayed but cannot be changed…._

 

 

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

 

 

………Tunda suka taho take ta faman zullumin abunda zai biyo baya in ta iske shi, wannan karon bata wani sha Wahalar gano gidan ba da suka iso don ta rik’e sunan Road d’in, a bakin tangamemen gate d’in tace ma mai Napep d’in ya tsaya bayan ta fito tace zai jirata ne su koma yace to ba matsala ta juya ta nufi k’aramar kopar a d’arare, Officer dake zaune shi kadae yana ganin ta ya hau washe baki harda mik’ewa yana mata sannu da zuwa abun har saida ya bata mamaki a hankali ta amsa mashi ta tambaye shi ko Ya Haisam na ciki da sauri ya d’aga mata kai yace eh yana nan tace zata gan shi ne yace mata ba Komai ta fito lafiya ta wuce, tunda ta shiga harabar gidan gabanta ke ta fad’uwa tana tafiya tana yan waige waige har ta isa bakin mai entrance na gidan ta turo kopar ta shige, ba kowa a cikin parlon farko ta wuce Corridor d’in da zata kaita d’akin nashi cike da fargaba har ta iso bakin dakakkar kopar dake a rufe, tsaye tay ta kasa kwankwasawa sai faman wasi wasi take a cikin ranta ta had’e hannawun ta tana cakud’a su, can dae ta kai hannu yana d’an rawa ta fara knocking a hankali, kusan sau biyar ta kwankwasa amman shiru bata ji an yi magana ba, dakatawa tay da knocking d’in tay jimm tana tunanin ko dae bai nan wata zuciyar ta ayyana mata amman ai Officer yace yana nan kuma da ya fita bazai ce mata haka ba ta raya to ko bacci yake yin Wannan tunanin yasa ta yanke ko dae ta tafi, har zata juya sai kuma ta dakata tay tunanin k’ara d’an kwankwasawa k’ilan tay sa’a yay Magana, can cikin bacci yaji knocking d’in sama sama har dai yaji shi sosae ya fara motsa idanuwan shi kafin slowly ya bud’e su dai dai lokacin ya k’ara jin anyi knocking d’in cikin disasshiyar murya irin ta wanda ya tashi daga bacci ya tambayi wanene shiru ba’a amsa ba saima k’ara yin knocking d’in da akai ya k’ara tambaya nan ma shiru, tunani yay k’ilan Officer ne ko ya kira landline bai ji ba hakan yasa ya yaye lallausan duvet d’in daya rufe rabin jikin shi da shi ya saukko da k’afafun shi kafin ya idasa mik’ewa daga shi sai farar singlet fara kal sai short da iyakar shi rabin cinyoyin shi, saida ya zura takalman da ke a bakin gadon sannan ya nufi kopar, ganin ta k’ara kwankwasa har sau ukku ba’a bud’e ba yasa ta hak’ura tana shirin juyawa ya bud’e kopar da sauri ta kai idon ta kan shi suka had’a ido, wani irin bugu kirjinta yay ta d’an zaro ido tana kallon shi shima irin kallon baka tsammaci ganin mutum ba ya bita dashi, gaba d’aya ta kame kanta ba kamar a yadda ta ganshi hannuwan ta da ta had’e sai d’an rawa suke, sakin kopar yay ya juya ba tare da ya ce mata komae ba, d’an jimm tay kaman bazata shiga ba sai kuma ta shiga ta maido kopar wani irin ni’imtaccen sanyin Ac had’i da daddad’an k’amshi mai ratsa zuciya suka tarbeta har saida ta d’an lumshe ido taja numfashi, in da kujeru suke ya nufa ya zauna kan 2 seater ta nufi can walking slowly gaba d’aya a d’arare take, a gefen wurin ta tsaya tana kallon shi ya sa duka tafukan hannayen shi ya dafe goshi alamar baccin bai ishe shi ba aka katse mashi, saida ya d’an d’auki lokaci sannan ya cire ba tare daya kalleta ba da hannu yay mata nuni da kujera alamar ta zauna jiki a sa6ule ta nufi cikin wurin ta zauna akan one seater tana facing d’in shi, gaba d’aya ta tsorata da yadda ta ganshi don bata ta6a ganin shi haka ba duk ilahirin jikin shi inda gashi ke fitowa suma ce a kwance liya liya ga farin shi gaba d’aya ya tafi bai d’aya skin d’in shi sumul da ita ba ko d’an ta6o ko bambancin kala harta gwuiwar shi ba bak’i ko tabo kamar bai yi rarrafe ba da yana yaro kawae dae skin d’in wurin jan ta ya d’an fi cizawa ga suffar k’arfin shi ta bayyana muraran gaba d’aya a murde yake, tana cikin k’are mashi kallon ya kai idon shi kanta suka had’a ido ta fara motsa baki da k’yar ta k’ak’alo Kalmar ina kwana tace mashi kaman ba zai amsa ba sai kuma ya amsa can k’asan makoshi ganin yana mata kallon da take ganin na fushi ne yasa ta sunkuyar da kanta yaci gaba da kallon ta,

 

“Why are u here not in School?” Bayan wasu sakanni taji cool voice d’in shi ya fad’i hakan, d’ago kanta tay ta kalle shi ta fara motsa baki tama rasa ta ina zata fara mi zata ce mashi duk ta dabarbarce ba kaman da ya kafeta da kaifafan idanuwan shi masu k’ara mashi kwarjini gathering much courage ta fara magana cikin yar rawar murya “d…dama zuwa nayi in baka hak’uri kan abunda ya faru….nasan nayi maka laifi amman ni bansan komai bane shiyasa na aikata wannan kuskuren….don Allah Ya Haisam kayi Hakuri” da k’yar ta k’arasa Saboda idon shi dake a kanta tana yi tana maida kan ta k’asa tana d’agowa, bin ta kawae yake da ido kaman ma bashi da niyyar tanka mata duk tasha jinin jikinta sai yan kame kame take,

 

“Ba zan yi hakurin ba!” Kaman saukar aradu haka taji Maganar da sauri ta tsaida idanunta akan shi ta zaro su don bata ta6a tunanin zata ji ya fad’i haka ba, d’agowa yay daga jinginar da yayi da kujeran a kausashe yace “da baki san komae ba banyi k’ok’arin sa ki sani ba? Tell me how many times did I call u to explain everything amman Saboda taurin kai kika k’i picking all my calls har message na tura maki warning u not to do anything amman Saboda abu ya faru bani da sauran girma da mutunci a wurin ki shiyasa bazaki bi umarni na ba, ni da kika zo nan I gave u chance kin fad’i duk abunda kike so u even shouted at me kin kira ni Azzalumi, macuci, maci Amana which I never expect to heard from u and dat’s d worst thing that ever happened to me…..” Dakatawa yay yana d’an girgiza kai fuskar shi d’auke da tsantsar 6acin rai ya d’an cije baki Fatuu ko tunda ya fara magana ta kid’ime don bata ta6a ganin irin yanayin da yake Maganar ba tunda suke da shi sai zare ido take tana sakin numfashi da k’arfi ta had’e hannuwan ta akan k’irji tama kasa bud’e baki tace wani abu,

 

“Nayi tunanin koda ace hakan ya faru ne kuma ba aure tsakanin mu zaki man uzuri, for how long muna tare dake na ta6a maki wani abu makamancin wannan? duk wani dama da zan iya aikata maki hakan na samu amman ban ta6a jin ina sha’awan hakan ba kaman yadda kika fad’a man wai ina son jikin ki God forbid! ban ta6a jin hakan ga wata wadda ba halal d’ina ba, kallon da nike ma siblings d’ina shi nike maki before aure ya shiga tsakaninmu amman kin yanke man mummunan hukunci har kin nuna guy d’in da aka so aura maki yafi ni duk da halin shi da aka fad’a man Saboda shi bai cutar dake ba sai ni right?” rai 6ace yake Maganar yana jinjina kai da alama maganganun nata sun tsaya mashi a rai, a rud’e Fatuu ta taso tazo daga d’an gaban shi ta duk’a tana girgiza mashi kai ya bita da ido cikin kuka tace “Don girman Allah ya Haisam kai hak’uri nasan nayi maka ba daidai ba sharrin zuciya ne, wllh ita tasa na kasa maka uzuri duk da nasan halin ka ta raya abubuwa ba daidai ba akan ka, kuma wllh ni ban daina ganin girman ka ba kawae dai nak’i d’aga wayan ka ne Saboda ina tunanin zaka hana ni aiwatar da abunda nai niyya ni kuma ina tsoron matsalolin da zasu biyo baya don bansan da aure a tsakanin mu ba shiyasa naga yin hakan yafi kuma wllh harda k’arin don kada k’imar ka da Mutuncin ka su zube kaji na rantse maka, amman don Allah kayi hak’uri na gane kuskurena ba zan k’ara ba” ta k’arasa fuskarta jage jage da hawaye tana yi tana gogewa wasu na sake zubowa, shiru yay ya jingina da kujerar yana ta kallon ta ita kuma sai motsa baki take ta marairaice fuska can yay sigh yace “is Ok,ai ke zan ba hak’uri na aure ki bada sanin ki ba daga baya kuma na cutar dake am really for dat” da sauri tace “a’a ai ni taimako na kayi kuma ba cutar dani kayi ba don ban sani bane nace haka kuma da na saurare ka da na san komai kayi Hakuri da abunda nayi” ta k’arasa tana ta6e baki yadda ta saba kuka tun yarinta still idon shi na akan ta sai yan kame kame take taji ya sake cewa “I know kinsan girman zunubin laifin da kika aikata amman kika za6i ki aikata and kinsan had’arin da ke tattare dashi but still kika aikata kawae don gudun matsaloli, baki ji tsoron sa6a ma Ubangiji ba?” hannu ta kai tana d’an sosa gefen wuyanta tana kikkafta ido ganin ya kafe ta da nashi idon yasa tace “Sharrin zuciya ne, kuma har yanzu banda cikakken hankali tunda ban girma ba sosae amman na rok’i Allah ya yafe man” bin ta kawae yay da ido ita kuma tsakani da Allah tay Maganar ta, nannauyar ajiyar zuciya ya sauke yace “shikenan kawae you can go back to School nayi hak’urin” kallo ta bi shi dashi har saida yace bata ji bane sannan ta fara k’ok’arin mik’ewa tace mashi ta gode ta juya, har ta fita daga wurin idon shi na akan ta sannan ya maido su yana kallon gaban shi kaman mai tunanin wani abu lokacin yaji k’arar rufe kopar ya mik’e ya nufi hanyar corridor, bada jimawa ba ya fito sanye da jallabiya ya nufi gaban mirror ya d’auki Car key ya fice, lokacin daya fito a harabar gidan ya hangota ta tunkari gate tana tafiya tana goge fuskarta da hannu, parking space ya nufa sai lokacin ta lura da shi ya d’aga hannu yay mata alamar ta tsaya, bayan ya fiddo Motar ya nufo gate d’in a saitin inda take ya tsaya ta zagaya d’ayan side d’in ta bud’e kopar gaba ta shiga, sai da suka fito sannan ta tuna da mai Keke Napep dake ta faman jiranta sam bai ji ya gaji da jira ba don yana sa ran zai samu biya mai kyau ba kamar da ya ga gidan da ta shiga, Haisam na ganin Napep d’in tun kafin ma tayi magana ya tambaye ta tare suke tace mashi eh ya tsaya gefen shi ya kai hannu ya bud’e glove box ya k’irgo 5k ya bata yace ta kai mashi tace to ta amsa ta bud’e kopar, lokacin data ba mai Keke Napep d’in washe baki yay ya shiga yin godiya harda biyo ta bayan ta bud’e kopar ya duk’o da kai yana mashi godiya ya d’aga mashi kai kawae bayan ta shiga yaja suka tafi,

 

A daidai inda ya aje ta da safe ya parker tuni an koma break ba kowa a wajen ta juya ta kalle shi idon shi na kallon gaban shi a sanyaye ta furta ta gode ya d’aga mata kai ta juya zata bud’e kopar lokacin taji muryar shi yace in an tashi ta jira zai zo ya d’auketa, d’an juyawa tay suka had’a ido a hankali tace mashi to kafin ta sake juyawa ta bud’e kopar, bayan ta fita ya juya Motar ya tafi tabi bayan Motar da kallo har ta daina ganinta sannan ta juya jiki ba kwari ta nufi class, tana zuwa bakin barandar benen da ajin su yake kawae sai ta zauna a wurin ta jingina da pillar ta d’an d’age kanta sama kwalla suka fara gangaro mata wani irin dana sani take yi ta rasa ya akai ta kasa yi ma Ya Haisam uzuri kaman yadda ya fad’a yakamata ace tunda tasan halin shi bata yi mashi yadda tay mashi ba, amman tasan harda bak’in abubuwan da taga ya fara yi mata ne yasa tay tunani na daban akan shi, tuno yadda ya rink’a yi mata Magana da tsantsar 6acin rai ta shiga yi dama Fauzy tace k’ilan abun yay mashi ciwo sosae ashe hakane ta fahimci bai so ta zubar da cikin ba, girgiza kai ta fara yi a fili ta shiga fad’in “am sorry my husband nasan na aikata kuskure amman cikin rashin sani ne bazan k’ara ba…” haka tay ta sambatu k’walla na zuba, Sa’adatu ce ta fito daga cikin class d’in su zata je toilet ta hango ta saida taje ta dawo sannan ta nufi Fatun ta tsaya gefen ta ta kira sunanta har sau biyu sannan tay d’an firgigit ta sauke kai ta kalleta, ganin hawaye a fuskar ta yasa tay saurin zama a gefen ta kai hannu ta dafa Shoulder d’inta tana tambayar ta lafiya Fatun tay shiru, ta k’ara tambayar ta ko jikin nata ne sai lokacin ta d’aga mata kai alamar eh cike da tausayawa ta hau yi mata sannu ta tambayi to ta sha magani ne ko suje ta rakata Asibiti tace mata daga can take tace to ta taso su tafi aji amman sai tace taje kawae tafi jin dad’in zama anan ta ce to, ta k’ara yi mata sannu tare da mik’ewa ta nufi komawa aji, da yake akwae malami cikin class d’in hakan yasa bata fad’i ma Fauzy game da Fatun ba har saida ya fita sannan ta tashi da sauri taje seat d’in su ta fad’i ma Fauzy aikuwa tun kafin ta gama fad’i matan ta mik’e zumbur tay hanyar fita, tana hangota ta nufe ta da sauri, tana zuwa ta zauna gefenta hankali tashe ta kai hannu ta dafa Shoulder d’in ta ta hau tambayar ta miya faru, tace ta iske Ya Haisam d’in kai Fatuu ta d’aga mata alamar eh, tace to ya sukai dashi, cikin muryar kuka ta shiga fad’i mata Fauzyn nata girgiza kai itama har idanunta sun kawo kwalla bayan ta gama fad’i mata yadda sukai dashi tace “ashe abun ya mashi ciwo ne sosae kaman yadda kika ce Fauzy, ban ji dad’i ba da na kasa yi mashi uzuri har komai ya faru if I had known I would have listened to him da komai bai faru ba nayi dana sani sosae” janyo ta Fauzy tay ta rungume ta ita kanta bata ji dad’in abubuwa data fad’i ma Ya Haisam din ba wanda ta 6oye mata hak’ik’anin yadda sukai dashi lokacin data dawo, jin tana ta kuka yasa tace “shikenan kukan nan ya isa hakanan kinga ba ki idasa warwarewa sosae ba kada kuma wani ciwon ya kama ki, tunda yace ya hak’ura ai shikenan sai a kiyaye gaba” d’ago kai tay ta kalleta tace “ni gani nike kaman bai hakuran ba ya dae fad’a ne kawae tunda har yanzu yanayin da nike gani bai canza ba” Fauzyn tace “kar ki damu tunda yace ya hak’ura to ya hak’uran kin dae san ai ba zai magana biyu ba daga baya yace bai hak’ura ba wannan ai k’aranta ne, dama burin mu ya hak’uran naji dad’i sosae abunda kuma ya rasa in sha Allahu bada jimawa ba za’a biya shi wani” wani kallo Fatun ta d’aga kai tay mata Fauzy tasa dariya,

 

“Yanzu kinga sai muji dad’in fara shirye shiryen duk da banji dad’i ba da ba wani shagali da za’ai amman mun biyo bashi koda in kika haihu ne sai mun yi shagali sosae, yanzu yaushe kike ganin zamu je ai maki k’unshi da gyaran kan?” d’agowa tay daga jikinta ta zauna sosae tace mata itama bata sani ba Fauzy tace “tun yau yakamata a fara maki gyaran jiki gobe ma a k’ara sai a gyara maki gashi jibi in Allah ya kaimu sai ayi maki k’unshi bari in aka tashi zan je gida sai in sanar ma Aunty Mareeya zuwa da la’asar sai muje wurin gyaran jikin” kai Fatun ta d’aga mata alamar to Fauzy ta kai hannu taja kumatun ta tana fad’in ta saki ranta Amarya da farinciki aka santa ta d’anyi murmushi kawai ta kama hannunta tace ta tashi su koma aji suka mik’e, Bayan an tashi Hostel suka wuce ta tattara kayan ta da suke a nan kaman yadda gwaggo ta bata umarni Fauzy nata fad’in zatai missing d’inta kad’aici zai dameta amman tana farinciki da abun Alheri ne yasa zata bar zama hostel d’in, Fatun nata murmushi itama duk wani iri take ji tasan dole ta damu da tafiyar ta, indomie Fauzy ta dafa masu harda kifi sardine suna cikin ci Haisam ya kirata yace yazo ta fad’i mashi suna cin Abinci ne amman sun kusa gamawa yace ba wani abu ta gama, bayan sun gama Fatuu tace mata to tazo ba sai a ajeta a gidan ba kawae, cike da tsokana Fauzy tace a’a wai kada ta shiga tsakanin Masoya ta hana su sakewa inta gama kimtsawa zata tafi Fatun ta harareta ta saka dariya, tare suka fito Fauzy ta kamo mata trolley d’inta dama iya shi kadae ne sauran abubuwa kaman provisions wannan ta bar ma Fauzy, lokacin da suka iso inda ya parker Motar back door ta bud’e ta saka akwatin bayan ta rufe ta bud’e kopar gaba ta shiga yana sanye da k’ananun kaya Fauzy ta lek’o ta gaishe da shi fuska a sake ya amsa yay mata ya karatu daga baya ta k’ara yi ma Fatuu sallama tace sai ta zo anjima ta rufo mata k’opar, saida ya ja Motar ta gaishe dashi ya amsa idon shi a kan hanya ta juyar da kai tana kallon gefen hanya har suka iso kopar gidan su ya parker, d’an kallon shi tay tace ta gode ya jinjina mata kai still bai kalleta ba ta juya ta bud’e kopar bayan ta fita har zata rufe sai kuma ta tuna da fitar da zasu yi anjima da Fauzy tasan in ta fad’i ma gwaggo sai tace ta tambaye shi hakan yasa ta duk’ar da kan ta ciki a sanyaye ta fad’i mashi sai lokacin ya juyo suka had’a ido, jinjina mata kai yay tay mashi godiya bayan ta janye kan ta rufo mashi kopar ta bud’e back door ta fiddo trolley din, har saida ta shige gida sannan yaja Motar, tana shiga d’akin gwaggo ta nufa ta d’aga labulan taga bata ciki ta saki ta nufi d’akinta, tana shiga ta aje trolley d’in a bakin gado ta aje jakarta saman gadon ta cire Hijab d’in itama ta d’aura ta saman gadon, tana juyawa zata nufi hanyar fita taji wayar ta tayi k’ara alamar shigowar message ta koma bakin gadon bayan ta bud’e jakar ta ta fiddo wayar ta fara dubawa, alert ne na 500k daga Haisam har saida ta d’an zaro ido dama wanccan da ya turo mata suna nan bata ta6a ko sisi ba yanzu ga wasu sun kama 1 million kenan d’an jinjina kai tay ta ayyana in gwaggo ta dawo sai ta nuna mata, har zata aje wayar wata zuciya ta raya mata yakamata tay mashi godiya d’an jimm tay tana yin wasi wasi na ta kira ko kar ta kiran, can dae ta kira saidae har ta yanke bai d’aga ba jikinta ne yay sanyi lakwas ta ji dama bata kira ba don a tunanin ta yana tare da wayar tunda yanzu ya turo mata sak’o, har zata ajeta kan gado sai gashi ya kira tabi kiran da kallo kaman bazata d’aga ba can dae tay picking ta kara a kunne bai tanka ba cikin yar inda inda tace taga sak’o ta gode sai lokacin ya furta Ok tay shiru can taji ya furta “da wani matsala ne?” da sauri tace a’a ta katse kiran, bin wayar tay da kallo a ranta ta ayyana halin Ya Haisam sai shi ta d’an ta6e baki sai kuma tay d’an murmushi ta aje wayar ta juya, d’akin Kawu Amadu ta nufa ta iske shi yana ta bacci hakan yasa ta juyo ta koma d’akin ta, a bakin gado ta zauna ta d’auki wayar tana kokarin kiran gwaggo, tana fara ringing ta d’aga bayan ta gaishe da ita ta tambayeta ta dawo ne tace mata eh ta iske bata nan ko ta tafi aiki ne tace a’a taje inda zata kai aikin su dublan ne, ta tambayi taci Abinci ko tace mata taci a Makaranta bata jin yunwa amman duk da haka saida tace mata ta k’ara taci ta k’oshi tace to, daga baya ta sanar da ita zancen zuwa gyaran jikin da zasu yi da Fauzy a kunyace gwaggon tace mata to amman ta kira shi ta sanar da shi har saida ta d’an yi murmushi dama saida ranta ya bata ta fad’i mata ta tambaye shi daya kawo ta harma da kud’in daya turo da wanccan daya fara turowa itama gwaggo saida ta jinjina yawan kud’in tace saidae ta dawo tay amfani dasu suyi duk abunda zasu yi tace to, bayan sun gama wayar ta mik’e ta nufi kitchen ba laifi taji damuwar da take game da yanayin Ya Haisam ta ragu,

 

 

Saida Fauzy tay wanka ta shirya sannan ta fito don tafiya gida, bayan ta isa bata iske kowa a parlor ba yaran Aunty Mareeyar basu kaiga dawowa daga School ba don suna tsayawa extra lesson, Bedroom d’in ta ta nufa tay knocking ta jiyo Muryar ta tana a shigo sannan ta tura kopar da sallama ta shiga, tana kwance saman gado tayi wanka jikinta sanye da doguwar rigar Atamfa kallabin ta aje a gefe kanta yasha kitso yar yar Tubarkallah dama akwae gashin kitson ya zubo gefe da gefen wuyanta tana ruk’e da wayar ta, tana ganin Fauzy tace lafiya dai ko ta dawo don jiya ta tafi, a bakin gadon Fauzy ta zauna tana kallon ta da murmushi tace mata lafiya lau, Aunty Mareeyar tace “kenan hakanan kika dawo, ko missing d’ina kike shine kika zo ki gan ni?” Yar dariya tay tace mata eh amman harda Albishir tazo yi mata, tana jin hakan ta aje wayar ta maido hankalin ta gaba d’aya kan Fauzy tana fad’in ta bata ta sha, cike da tsokana Fauzy tace “Dama Daddyn su Hanif ne na gani ya kai wata Makarantar mu amman shi bai ganni ba saida ya sauketa ya tafi naje muka gaisa nike tambayarta inda ta san shi take ce man wanda zata Aura ne har an sa masu rana shine nace bari in zo in fad’i maki kin kusa yin k’anwa mu kuma zamu yi sabuwar Aunt……” bata k’arasa ba Aunty Mareeya ta kai hannu ta janyo ta ta daddage ta d’uma mata dundu tana fad’in bari ta fara ta kanta ita yar zuwa ta fad’i, wata irin gantsarewa Fauzy tay sosae taji zafin dundun har saida ta saki k’ara tana fad’in “Aunty Mareeya so kike ki kashe ni kika buga man wannan k’aton hannun naki tubarkallah” sakin ta tay tana dariya tace gobe ma ta k’ara fad’i mata irin wannan mummunan labarin Fauzyn ta tashi zaune tana yamutsa fuska kaman zatai kuka har kallabinta ya cire Aunty Mareeya dake ta dariya tace mata tana jin ta wane Albishir ne zata mata, tana tura baki tace ta fasa fad’i mata ta fara k’ok’arin mik’ewa da sauri ta janyo ta ta fad’a saman gadon ta rungume ta tana bata hak’uri sannan ta shiga fad’i mata zancen tarewar Fatuu, har saida Aunty Mareeya ta rangad’a gud’a ta shiga washe baki tana fad’in Alhamdulillah an zo daidai inda take so, ta bata labarin zuwa da tayi d’azun bashi hak’uri da yadda sukai dashi, yamutsa baki Auntyn tay tace “in ma bai hak’uran ba ta lalama zai hak’ura ne don dole, wllh ni dama fatana auren dai ya d’ore duk wannan miskilancin sai an sauke mashi shi sai ya rasa sukuni duk in bai ji Zarah a gefen shi ba, shiri za’ai mata na musamman ba boka ba Malam amman fa sai ya susuce a kanta mu da muke da AUNTY BEE KAYAN MATA AND SUPPLEMENTS ai zance kuma ya k’are, mu mata da Allah yay mu masu daraja ai duk kika ga mace bata da k’ima da daraja a wurin mijinta wllh ita taso, macen data san kanta wllh bata zama ba tare da gyara kan ta ba musamman da kaya masu tsananin inganci na Aunty Bee, ai ance ko kana da kyau to ka k’ara da wanka” Fauzy da tay sototo tana sauraren ta tace “Aunty su kayan Aunty Bee d’in nada kyau sosae kenan” hannu Aunty Mareeya tasa ta ruk’e ha6a tace “Uhmm bazaki gane ba yarinya tunda baki san yadda karatun yake ba, amman wllh kin ji na rantse kayan ta Kat ne ingancin su ba’a magana sai mutum yayi amfani dasu zai shaida don sha yanzu ne magani yanzu, gashi abun burgewa abubuwan mune na gargajiya ake sarrafawa ayi magungunan sam basu da wata illa sa6anin wasu magungunan ke da kinji kin san harda surkulle” Fauzy ta tambayeta a ina Aunty Bee d’in take tace “a Kano take nima yadda akai na santa nan Neighbor d’ina Maman taufiq taji ina complain kan sai aita zuzuta magani amman in na siya sai inji ba haka ba k’arshe ma na daina siya nace gwara in cigaba da shan su Fruit dasu Fresh milk shine fa tace ai in jaraba kayan Aunty Bee d’in, farko k’iyawa nay nace kowane Magani haka ake cewa amman ta matsa man ta bani wasu in gwada…..”

 

Hannu tasa ta ruk’e ha6a tace “Fauziyya….” Itama Fauzyn ruk’e ha6ar tay tana gumtse dariya tace “Aunty…” ajiyar zuciya Aunty Mareeya ta sauke tace “naga abun Al’ajabi wllh, amman mu bar Maganar daga nan bari in kira ta in mata zancen Zarah” tana rufe baki Fauzy ta kyalkyace da dariya itama Aunty Mareeyar dariyar take ta fara k’ok’arin kiran layin Aunty Bee kamar haka, 08144224934 wayar na fara yin ringing Aunty Mareeya ta d’aga ma Fauzy gira tace “yanzu zata d’auka ta bala’in iya haba haba da customer da kin kirata ko kika tura mata sak’o ta WhatsApp ba 6ata lokaci zaki ji ta d’auka saidae in wani babban uzurin ya hanata d’agawa da wuri amman data gani ko daga baya ne zatay ma mutum magana…” Jin Aunty Bee d’in ta d’aga kiran yasa tay shiru suka shiga gaisawa cike da mutunta juna daga baya ta shiga yi mata bayanin K’anwarta take so a gyare mata sosae kaman yadda aka saba harda cewa mijin miskili ne na gaske so take asa ya magantu ba tare daya shirya ba Aunty Bee d’in tay dariya irin ta mata da suka amsa sunan su tace mata karta damu wannan ba matsala bane saidae in bata yi amfani da magungunan ba amman tabbas zai magantu, gaba d’aya suka saka dariya Aunty Mareeya tace tana son ta turo mata hotunan packages na magungunan zata tura ma Mamar Amaryar tace ba matsala ta duba WhatsApp yanzu zata turo mata in sha Allahu sukai sallama, suna gama wayar ta shiga WhatsApp d’in dama anan take Fauzy ta shigo, ba 6ata lokaci sai ga hotunan ta turo Aunty Mareeya tay ma Fauzy alamar ta matso ta gani ta k’arasa hayewa kan gadon, baki bud’e take ganin hotunan magunguna ba kamar package na Amaren ya burge Fauzy sosae tun ma a ido, magunguna ne sosae Aunty ta shiga fad’i mata sunayen su, su Zakaran mak’alemata, kazar gadali, zabuwa, cicci6i, tsumi kala kala masu wanke mara suyi maganin sanyi, gumba ma kala kala ga garirrrika wato daka akwae d’akan yar gata, k’orama, green emergency, bata gaban kishiya , a ciji kunne…..” Aunty bata k’arasa fad’in sauran ba Fauzy ta kwashe da dariya harda tuntsirawa ta d’ago tana fad’in Aunty badai kunnan Zarah za’a cije ba da sauri Aunty Mareeya ta kai mata bugu tana fad’in mara kunya kawae ita tana nuna mata ne don in za’a ma k’awayen ta aure ta taimake su ta tallata masu don su gyara kansu, k’arshe sai ta fita daga cikin hotunan Fauzy nata rok’on ta taci gaba da mata bayani tace bata yi,

 

“To amman Aunty kince a Kano take yanzu yaushe har aka kawo su Zarah tai amfani dasu saura fa kwana ukku ta taren” murmushi Aunty Mareeya tay tace “ai wannan ba matsala bane Aunty Bee bata da wasa a kasuwarta in yanzu nace duk ana son wannan kayan a gobe insha Allahu zaki ga ta turo su ke ko Lagos kike kika ce kina son kayanta cikin kwana biyu zasu iso maki kuma abun mamakin kayanta basu lalacewa yadda ta turo su haka zaki amshe su ba cuta ba cutarwa, kuma koda yan kud’i k’alilan zaki samu kayanta, kai ai Allah yaba Aunty Bee gaskiya ba k’aramin taimakon mata take ba shiyasa a koda yaushe Allah ke k’ara ma kasuwarta Albarka wllh” Fauzy tace “to yanzu tura ma Zarah za’ai ta gani in mata bayani?” Yar harara Aunty ta wurga mata “wata Zarah can, kenan ita zata gyara kanta sai kace mara gata gwaggon zaki kira man in mata bayani kina da no d’inta?” tace mata ba’a rasawa ta ciro wayarta a cikin jaka ta fara dubawa cikin sa’a akwae lambar tace ta kirata, tana fara ringing ta d’auka Aunty ta amsa cikin girmamawa ta gaishe da ita tay mata Allah yasa alheri Fauzy ta fad’i mata zancen tarewar Zarah, daga baya ta shiga yi mata bayanin magungunan sosae gwaggo taji dad’i tay ta godiya tana shi Albarka tace duk kud’in da ake buk’ata tay ma Fatun Magana zata turo sai a kawo tace to, daga baya sukai sallama suna gama wayar gwaggo ta kira Fatuu tace mata Auntyn Fauziyya zata kira inta fad’i mata kud’i ta tura mata tace to, ba tare da 6ata lokaci ba bayan ta kira Fatuu ta tura mata kud’in ita kuma nan take ta tura account d’in Aunty Bee daga baya ta kirata tace ta tura mata receipt ta duba, bayan ta gani ta tabbatar mata gobe in Allah ya kaimu wurin k’arfe 10 na safe magungunan zasu iso tace harda gudummawarta ta k’ara aba Amarya, dama haka take da wuya kai siyayya bata k’ara maka ba Aunty tay mata godiya sosae sukai sallama har Fauzy na yamutsa fuska tana ita baza’a siyar mata koda kazar bace Aunty tace asarar kud’i kenan, ana yin sallar la’asar Fauzy tay ma Aunty Mareeya sallama ta tafi gidan su Fatuu don zuwa gyaran jikin………..

 

(Aunty Bee Kayan Mata And Supplements TESTED AND TRUSTED duk abunda Aunty Mareeya ta fad’a game da kayanta gaskiya ne ni shaida ce don haka kar ki bari a barki a baya wllh ki zama tauraruwa a idon oga ta hanyar amfani da kayan Aunty Bee, Mace mai gyara bata boranci).

Asanadin Makwabtaka Book 2 Complete Novel Txt

Back to top button