Hausa novels

Haihuwa Da Hanji Page 29 Hausa Novel

Hasaso Rayyan ɗin ta shiga yi a majigin kwakwalwarta, kallo ɗaya tak za ka yi mishi ka san cewa shi ɗin soja ne a sojojin ma na daban, yana da lafiyayyar jiki murɗaɗɗe kuma a tsaye yake fatarshi babu ɗigon baƙi ko guda ɗaya, Dukda ba zata ce ga yadda yake cikin khaki ba amma ko daga maganar shi zai tabbatar maka jajirtacce ne kuma gwarzon namiji wanda ko daga kallonshi za ka sha jinin jikinka. Zaman shi, tafiyar shi da yanayin dabi’unshi kuwa za ka zaci wani babban sarkin ne na wani yanki na daban, yana da wasu irin idanu kyawawa da ko tuna yanayinsu tayi sai ta ji tsikar jikinta ya zuba kaman ba namiji ba, fasalta kyaun fuskarshi da sauran halittar da Allah yayi mishi ma wani tulin bayani ne na daban, don Allah ina ita ina irin gawurtaccen nan? Ta ina ma Mammi ta fara wannan tunanin? Tazarar da ke tsakaninta da Rayyan kaman tazara ne da ke tsakanin sama da ƙasa ko ta amincewa aurenshi ita ce zata wahala daga karshe saboda ba zai taɓa son irin ta ba, ba zai taɓa kaunar mace kamar ta ba wacce ta fito daga kauye cikin tsantsar jahilai, wacce take da tambarin Maita kuma annoba, wacce ko wucewa ta zo yi gidajen mutane sai an zuba tafarnuwa, Ƙashin kifi da garin kukan miya a wuta don hayaƙin Mayu…. Ai ko da gami wane ita da Rayyan.”Mammi kaman ban ji abin da kika faɗa ba”Ta sake maimaitawa har yanzu a kidime.Miƙewa tsaye Mammi tayi ta riƙo hannunta suka koma zaune.”Ki natsu Afeefah kin ji? Ki ba ni hankalinki kar ki yi wani tunanin fin ƙarfi, namiji bai taɓa fin karfin mace ba in har ta amsa sunanta mace, ke kyakyawace kar kyaun Rayyan ya ruɗe ki, ke yarinya ce mai hankali, ladabi, natsuwa da kuma biyayya kina da zuciya mai kyau, you are the purest soul i’ve ever met… Afeefah ba zan hada ki da Rayyan bane saboda wani ra’ayi nawa ko buri eh ina da buri a kan ku duk biyu, sai dai burin ba na komai bane sai na son ganin rayuwarku duk ya inganta kun tabbata cikin farin ciki””Mammi shi ya ce miki yana so na?”Ta tambaya a sanyaye don ba fahimtar kalaman Mammin take ba don abu ne da take ji ba zai taɓa yiwuwa ba.”Ba shi ya ce ba, ni ce na ga cancantar kasancewarku inuwa ɗaya kar ki damu da halinshi ko yanayinshi na fushi da dacin rai Saraki na da wani tabo ne da ya mayar da shi hakan wanda dole zan faɗa miki Afeefah… Ina so in fada miki ba don tonon asiri ba, sai don ya zama dole ki sani kan ki yanke shawarar za ki aure shi ko ba za ki aure shi ba? Ba zan miki dole ba wlh kuma ba na so ki dube ni a yayin yanke hukunci ki yanke duk abinda ke ranki ni me karɓa ce don sai da na nemi zaɓin Allah kan na tunkareki”Shiru Mammi tayi idanunta sun rine sossai har suka tara hawayen da ya fara bin ƙuncinta, ɗacin maganan da zata faɗa take ji har kan harshen ta maganan da bata taɓa faɗa da Bakinta ba bata taɓa ambata ba sai a yau da ya zame mata dole, idanunta na kallon gefe ta furta”Rayyan ba ɗa na bane!!!”Wani irin bugawa zuciyar Afeefah yayi da har sautin shi na fitowa fili ta zaro idanu gabaɗaya tana kallon Mammi dake ta zubar hawaye “Eh Afeefah ba ni na haife shi ba, hasali ma babu abin da ya haɗa ni da shi na jini ko na kusa ko na nesa… Ni sunana Khadija ni haifafffiyar wannan gari ce ta Kaduna, mahaifina Alhj Isma’il mai rasuwa mutum ne mai tarin dukiya mai yawa a gaske kuma su biyu Allah ya ba wa iyayensu ɗan uwanshi ma na da nashi arzikin don gada suka yi, mahaifina mutum ne da dukiyar shi bai taɓa rufe mai ido ba, yana da kyauta tsantsa haka yana da taimako don haka ko da na zama ni kaɗai ‘yar shi yana da ƴaƴa dayawa da suke karkashin shi don lakabinshi ma shine Uban marayu da masu uba… Yaran da ya biyawa suka karatu basu kirguwa sai dai in baki zo wurinshi da kuka ba sai ya share miki hawaye, wannan dalili ya sa nima na taso da irin zuciyarshi Dukda rashin lafiyarmu don shi ma ciwon sugar ne ya kashe shi kaman yadda ya kashe baban shi, ƙannunshi ma Uncle Musa haka yake don suna da nasaba mai kyau suna da ilimi boko da arabi. Akan irin rayuwar da na tashi kenan har na kamallah jami’a ta ina da shekaru ashirin da ɗaya a duniya, wata rana ina driving na zo daidai wurin ba da hannu sai na hangi wani kyakyawan yaro da ba zai wuci shekaru shida ba yana da irin kyaun da in ka kalleshi sai ka sake da sauri ya zo ya shiga gaban motana ya fara wanke mini glass don kaman sana’ar da yake yi kenan a wurin ake bashi goma biyar na cin abinci, Dukda fuskarshi a matuƙar haɗe ko alamun dariya babu kayan jikinshi kuma basu ji jiki chan chan ba amma sun dan yi duhu kaman ana yawan tsoma su ruwa, bayan ya gama ya dawo gefena ya tsaya tsantsar tausayinshi ne ya rufar mini, wannan yaro ƙarami da ke bukatar ingantacciyar rayuwa yaron da bai wuce a ce yana gaban mamanshi a kwance ba shine ke wannan walagigi yana neman abin da zai sanyawa cikinshi, sauƙe glass din nayi muka haɗa ido na sakar mishi murmushi “Yaya sunanka?”Na jefa mishi tambayar ga mamaki na ko ci kanki bai ce ba banda idanu da ya tsura min yana kallo, ganin an ba da hannu sai na zari dubu biyu na miƙa mishi kaman ba zai karɓa ba sai ya karɓa ya juya ya bar wurin bai ce min komai ba.Har na dawo gida tunanin wannan yaro ne a raina bayan kwana biyu na kasa mantawa da shi haka na ɗauki mota na koma inda na fara haɗuwa da shi na ajiye mota na shiga yawon neman shi da ƙafa, na yi nema sossai kan na same shi zaune gefen wani juji ya haɗa kai da gwiwa Dukda uban ranar da ke dukanshi ko motsi bai yi ba, daga farin Fatan shi da yanayin sumanshi na gane shi don ya fi yanayi da Fulanin usuli, gangar shi na je na duƙa na taɓa shi ya ɗago ya kalleni da idanunshi da suke a matuƙar rine fuskarshi yayi jazir, dabiun yaron sai bai min yanayi da na sauran yara ba don idanunshi na nuna wasu al’amari da na kasa fahimta, maganan duniya na mishi bai ba ni amsa ba sai ido na miƙe na je wurin wani mai wankin mota a kusa da wurin na nuna mishi yaron “Malam Don Allah wanchan yaron baya magana ne?””Hajiya yadda kika ganshin nan haka mu ma muka ganshi kuma in za ka mishi maganar duniya ba zai amsa ba amma kin ganshin nan idan ya kwana da kayan jikinshin nan da safe zai zo ya ba ni goma in bashi ruwa da bokiti ya kwaba omo ya wanke zai zauna daga shi sai karamin wando idan ya bushe zai saka ya cire wandon ma ya wanke ya mayar da kayan, kin ga inda yake zaunen nan idan ba zai fita neman kudin abinda zai ci bane bai taɓa barin wurin ba sai wanka ko wanki da ya kan zo nan”Wani iri na ji har cikin raina, na mishi godiya na bar wurin na koma wurin mota na tafi na je na sayo duk wani abin makulashe da na san yaro zai buƙata na dawo na bashi ya ƙi karɓa a ƙarshe ajiye mishi nayi na tafi, Washegari na sake komawa don tausayi da kaunar shi ya riga ya samu gurbi a zuciyata, a ranar takalmina na cire na yi irin zaman da yayi nima Dukda ina jin zafin ranar minti minti sai ya ɗan waigo ya kalleni ban ce komai ba shima kuma bai ce komai ba, har dare ina tare dashi sallah kawai nake zuwa wani masallaci a wurin dake da ɓangaren mata abin da ya bani mamaki kuma shima haka zai je Sallar ya dawo ban tafi ba ranar ma sai da na sake cika mishi gaba da abubuwan cima kala kala, a takaice na jera kwana uku ina zuwa wurinshi a na huɗu ne ina zaune kawai sai na kama kuka, yayi shiru sai ya juyo ya kalleni kaman zai share chan dai na tsinci muryarshi kaman daga sama yana cewa “Me ya same ki?”Numfashi mai nauyi na sauƙe ashe ba kurma bane “Ba ni da lafiya ne kuma bana son zaman rana”Ga mamakina sai ya miƙe ya kama hannuna muka koma inuwa duk muka zauna bayan nan duk yadda zan yi yayi magana ya ƙi na sake yin kwana biyu muna zama a inuwa kan ranar kawai ya kalleni ya ce “Me kike so?”Ina mamakin yadda yake magana wane babba “Kai nake so in taimaka kai nake so in ɗauke daga wannan jujin in kaika gidan mu kayi rayuwa mai kyau, za ka bi ni?”Kallona kawai yake, ni kuwa ina hakan ne da zuciya ɗaya ba zan so rayuwar shi ya ƙare a kan titi ba ba zan so ya tashi a haka ba zai iya shiga ko wani hali.Kai ya gyaɗa min na yi farin ciki kwarai na kira babana ina mishi albishir don ya san labarin yaron har ya yarda duk ranar da yaron ya tanka ni kuma ya amince ya biyo ni ina da kyautar kujerar umura na yi farin ciki sossai da amincewarshi Dukda ba don kujerar ba saboda ko a lokacin na je Makka so ba adadi, na dauke shi daga nan muka dawo gidan mu.Ban barshi cikin ma’aikata ba na kaishi ɗaki na musamman na fita na yi mishi sayayya kan na dawo yayi wanka ya ci abinci na bashi kayan a hankali ya ce min “Na gode”Murmushi nayi a raina ina raya wannan yaro idan ya girma ba karamin mutum za’a yi ba don bashi da rawar kai irin na yara masu shekarun shi.”Ya sunanka?””Ban sani ba”Abin da yace kenan na yi mamaki ƙwarai kuma kaman akwai abinda ya ɓoye min amma ban bincika ba nace “Zan saka maka suna amma sai na yi tunani sunana Khadija, mahaifiyata ta rasu ni kaɗai ce sai babana a gidan nan ka ɗaukeni tamkar mahaifiyar ka duk wani abin da kake so ni kuma zan cika maka shi ka ji?”Ya kalleni nayi murmushi “ban kai in haifeka bane? Shekarunka nawa?”Ya ɗaga min yatsu shida nace”To ka ga, da na yi aure ina 15 da na haifeka irin auren kauyen nan da ma ba’a kai hakan”Ya ɗan yi murmushi daga nan na fahimci shi mai ɗabi’ar miskilanci ne tsantsa babana na samu da shawara shi ya ba da sunan Rayyan in saka mishi ni kuma nake ce mai Saraki don ko sarki bana tunanin ya kai shi sarauta..A lokacin gab aurena da baban su Jannah ne ko da ya zo shima farar daya son yaron ya shiga ranshi yayi alkawari zamu rike shi kaman mu muka haife shi ko da zan kaishi makaranta tare muka tafi da Mahaifin su Jannah shi yayi mishi komai aka ba da sunanshi Rayyan Mohd Khamis, bayan aurena da baban su Jannah bai fi da shekara ba Allah yayiwa mahaifina rasuwa ta hanyar ciwon sugar da ya sha fama da shi, na shiga tashin hankalin da Saraki ne kawai ke iya saka ni cin abinci kan daga baya na zo na watsakke don dama wannan dole ne, ranar da na haifi Jannah a ranar Saraki ya fara kirana da Mammi don tunda muke bai taɓa kirana ba ko zai yi magana sai dai kawai yayi na ce ko Aunty ya ce min ya ƙi, Rayyan bashi da lafiya don yadda yake ganin rana haka yake ganin dare idan yayi bacci kuwa haka zai yi ta wani irin juye juye yana haɗa gumi daga karshe cikin wani mummunan yanayi zai farka tun yana ƙarami muka fara ganin likitocin psychiatric su ma da kyar da pills ake samu yake dawowa daidai idan abin ya zo mishi especially lokacin zafi kasancewar a tsakankanin ne muka hadu.Baya so a mishi magana akan abin da ya kawo shi wurin ko iyayenshi tunda na fahimta ban sake yi mishi ba ko da wasa, irin kiyayewa da kular da muke bashi shine sanadin da ya sa ya samu ingantacciyar rayuwa yayi karatu mai zurfi har ya zama soja, bayan nan ne aka gano ina da Ciwon ƙoda Rayyan yayi fadi tashi kwarai har ƙodar shi yayi offering mini Mahaifinsu Jannah ya hana aka biya makudan kudi aka yi min dashe amma ba’a dace ba, a lokacin da nake jinyar Baban su Jannah ma ya rasu ga rashin lafiya ga rashin miji na yi ciwo sossai duk Rayyan ne yake tsaye tsayin daka a kaina ga ƙannenshi Jannah da Abeeha bai bari na tagayyara ba, yana mini son da iyakaci kenan ko da ni ce na haife shi.Saraki ya taso mai tsananin jarumta gashi dama magana ma bata dame shi ba don ko abokai bashi da su, sannan yaro ne da idan yana abu dole ka kalleshi yana da jin ƙai ko magana yake dole ka kalleshi, dalili na ya tafi short service a harkar lafiya don dama science ya karanta a secondary school, ba’a fi shekara biyu ba na matsa mishi da zancen aure ya nuna akwai wacce yake gani zai iya aure, magana ta fara nisa ranar ya je wurinta babanta ya zo ya same shi ya ce mishi “Ina so in ka koma ka tambayi asalinka sai a fara batun neman aure amma ba zan ba da auren ɗiyata wa marar cikakken asali ba”Wannan magana ya dake shi sossai, wanda ni na ɗan lallaɓa shi na tura uncle Musa sai ce mishi suka yi ba za su bada auren ba basu sani ba ko ba ɗan sunna bane ko an same shi ta gurbattacciyar hanya, magana ce mai girma a gareshi wanda ya tado ciwon baya da kyar muka samu ya dawo daidai bayan tsawon wata shidda baya bacci kuma ya ki faɗa mini wani irin mafarki yake ko wa Dr ɗinshi, gashi Rayyan baya taɓa zubar da hawaye, tunda ya girma rabon da in ga hawayenshi kila da wani abu zai ragu a zuciyarshi, daga nan yayi alkawarin ba zai sake neman aure ba don duk wanda ya sake kallonshi ya mishi gorin asali sai ya kashe mutum har lahira.Afeefah kin ji waye Rayyan, kin ji cewa bashi da cikakkiyar asali sai dai yana da tarin nagarta, ilimi, natsuwa da sanin ya kamata ga ibada tsantsa, yana da ni matsayin uwa da na bashi duk tarbiyar da uwa za ta iya ba yaro daga yarantarshi har girmanshi, ya samu gatan iyaye both uwa da uba don baban su Jannah har ya rasu bai taɓa nuna ko da da second daya cewa ba shine Uban Rayyan ba, kin ji cewa bashi da cikakkiyar lafiyar kwakwalwa ba na hauka ba sai na tsantsar damuwa akan abinda ya shafi rayuwarshi da ciwo a zuciyarshi wanda ya mayar dashi mai irin zafi da faɗan nan, tun yana yaro ba za ki taɓa ganin dariyar shi ba sai murmushi shima sai ya kama, shin za ki iya auren Rayyan a haka? Afeefah za ki iya yi min wannan alfarmar??

Back to top button