Uncategorized

Wace Ce Ita Chapter 27-28 Complete Novel

WACE CE ITA⁉️ (WHO IS SHE⁉️)

Unique Barakancy

       TWENTY SEVEN – TWENTY EIGHT📍

       “I know you’re fooling me dan Allah ki tashi!”…

Deen ya sake fada a rude yana kara tarota jin yanda ta sake masa jiki gabadaya…..

Ganin bata motsa ba sai abun ya kara rudardashi ya rasa taimakon daya kamata ya bata gashi ya kasa yarda ba wani makircin takeson shirya masa ba…..

   Kallon gurin yayi yaga babu wanda yake ganinsu sai kuma ya dawo da kallonsa kan fuskarta, murmushi ne ya subucema beneath his breath yace;

    “There’s more to this beauty, it’s still dangerous!”..

      

      “Ke wa zaki maida wawa? Allah idan baki tashi ba zan sakeki ki fadi a gurinnan, I’m serious!”….

Ya fada trying to distract his heart from abinda yake raya masa, shiyasa bayason kallon fuskarta cuz she’s so tempting yanzu saika kauce baka sani ba, since she came into his life komai ya chanja masa, sam baya gane kansa when it comes to her, yasan baya sonta but it seems what he’s feeling over her is just ‘lust’(sha’awa) which is haram in islam and he can’t help it, ya kuma gane hakan ne tun ranar dayayi kissing dinta dan be kara bacci me dadi ba, he just want more and more and more, even beyond kiss, he just want to explore her inner self and see her in her full glory, har ciwon mara ya fara a yan kwanakinnan abinda be tabayi ba…..

       Yafi 10mins yana mata kashedi da warning akan in bata tashi ba ze saketa a kasa, as a Doctor he should have known idan suman gsky tayi amma baya fahimtar karatun likitancinsa when it comes to her, saida yaga kamar dagaske bata numfashi sannan ya dauketa ya sata a motar da tazo….  

Kwantar da kujerar dake kusa da driver seat yayi sannan ya kwantar da ita yanda zeke ganinta sosai sannan ya shiga yaja motar with the thought of ina ya kamata ya kaita, gashi yanzu bayason kaita gidansa cuz he don’t trust himself anymore, a yanda zuciyarsa ke ayyana masa abubuwa dayawa dinnan sam bayasan kebewarsu a inda yasan ba wanda ze iya kawo mata dauki inma wani abun ze mata……

  Tada motar yayi yayi reverse ya fita daga harabar hotel din gabadaya….. 

   Tunda ya hau titi yake tinanin inda ya kamata ya kaita da baze samu problem ba, bama wannan ba a wani yanayi zata farka yanzu? Ze kaita gidan mutane ne ta musu fashe fashen data saba? Ko ze kaita gidan mutane aljanunta su tashi arasa yanda zaayi da ita?… Sai kuma ya kalli zoben daya cire daga hannunta yaga kamar yayi baki ba yanda ya cireshi ba, sai a lokacin kansa ya kawo huta, could it be cire zobennan ne ya sumar da ita? Dan if he can recall yana cirewa ta sume masa, toh meye a tare da zoben? Gashi tabbas ya taba ganin zoben a hannun wani, wanda yaga zoben a hannunshi be kuma yarda dashi ba, sannan according to the tracker taje gidansu alhaji ibrahim mahaifin saurayinta khaleel, toh meya kaita gidan saurayi bayan ancemasa khaleel din baya kasar, toh ko yana kasar ai be kamata taje ba, ko duk rashin kamun kanta ne dan yasan babu abinda bazata aikata ba… 

Dan dakatar da tinaninsa yayi ya juyo ya kalleta, yanda ya kwantar da ita haka take saidai kanta yayi gefe wanda hakan yasa hular datasa zamewa daga kanta dayake tanada tsantsin gashi sosai, mayafinta ko dama tinda ya tareta ya zame, da kyar ya daure yaki bawa kansa damar kallon fiye da fuskarta…..

 Tsaki yaja kamar tana jinsa yace;

      “Wato har attachment kike sawa ko? Tayaya aljanu bazasu dinga bin mutum ba?”…..

Sai kuma ya samu kansa da tura hannunsa cikin gashin nata, sosai tsantsi da kamshin gashin ya tafi da imaninsa har besan sanda yace;

     “Dama haka attachment din yake so soft? I love the texture!”…… 

Haka ya cigaba da tura hannunsa a gashin nata at the same time yana driving da dayan hannun………

Horn yaji anayi masa da karfi ashe yabi one way be sani ba, da sauri yayi gefe da motar inda Allah ya taimakesa space ne da Allah kadai yasan me zasu daka daba karamin accident zasuyi ba, yana cemata bata iya driving ba sai gashi shima ze tapka shirme…

Parking yayi ya daki steering din motar yana fadin;

       “Damn it! Kedai komai naki masifa ne, gashi kinsa garin taba artificial gashinki zan kashemu a banza!”……

Sai kuma ya kwantar da kansa ya shiga tinaninta duk da tana kusa dashi…..

Yana cikin wannan hali wayarsa ta fara ringing, dagowa  yayi da sauri yana duban me kiran, sosai hankalinsa ya tashi ganin Mami ke kira, yanzu haka an kirasu ko sunje basu gansaba shine take kiransa a waya, wai ya akayi ya manta da consequences din gudunwan dayayi ne, this girl has been putting him in more and more trouble tinda tashigo rayuwarsa…

Yanke shawarar yayi ignoring call din kawai yayi idan yaso in yagama da issue dinta sai yaje yayi facing dinsu…..

Saida ta masa five missed calls sannan ta hakura, ya sauke wani gauron ajiyar zuciya yana addu’ar Allah yasa karta kara kira…. Saidai kash addu’arsa bata karbu ba dan baifi minti uku ta bayar a tsakani ba ta cigaba da kira, duk yanda yaso ya share kasawa yayi saboda kiran is getting out of hand, saida ta mishi 10 missed calls sannan ya daure ya daga wayar…..

      “Hello son, kana ina? Can you hear me? Is this you?”…..

Shiru yayi yana kokarin tantance yanayin datayi maganar, indai ba kunnensa bane ya jiyomasa ba daidai ba kamar mami kuka take, toh what could have happened?…..

     “Dan Allah Saifuddeen kamin magana, tell me you’re not dead kar zuciyata ta buga, you won’t understand how much I love you”….

Ya sake tsinto muryarta tana fadin haka cikin shasshekar kuka….. 

      “Relax Mami! It’s me meyafaru? Pls stop crying you’re breaking my heart”…..

Ya fada yanajin zuciyarsa kamar zatayi tsalle ta fado, this is unbelievable! Ace Mami na kuka? No!”…..

       “Yimin magana sosai inji muryarka, ka tabbata kaine kuwa?”…..

      “Yes mom, meyafaru dan Allah kidena kuka, tell me what happened?”……

 Katseshi tayi da fadin;

       “Kana ina yanzu?”…..

    “Ina prison”….

Ya fada kasa kasa….

    “It can’t be! yanzu haka muna prison, and I’m glad bakanan, tell me where are you now?”…..

     “Ina wani guri trying to sort some things out, I’ll see you later”…..

     “Start coming home now please”….

   “I can’t come home, I have a very big issue”….

   “Koma menene just come, I promise to help you out, dan Allah ka taho gida”……

    “Bani kadai bane Mami kuma bazan iya barin meshi in tawo ba”….

   “Naji koma waye ku taho tare”…..

Ajiyar zuciya ya sauke dan har lokacin beji ze iya zuwa da ita gidan ba….

Daurewa yayi yace;

     “Promise me you won’t judge me ko dawa nazo?”..

       “I promise you”

Ta fada without hesitation….

     “Kinyi alkawari bazaki min fada ba koda wa nazo?”….

   “Nayi”….

Mami da take cikin tashin hankali ta sake fada batasanma ta fada ba……

       “I’ll be there in 15mins”

Yana fadin haka ya kashe wayar yana tada motar…..

    “I hope he’s fine? Meyace miki?”…..

Umm da idonta itama yayi ja alamun tayi kuka ta tambaye mami a rikice…..

     “Yace nan da 15mins ze karaso, muyi sauri mu karasa gidan”…..

   “Alhamdulillah Alhamdulillah, Allah mun gode maka daka kare saif, rabbil izzati ka cigaba da karesa, Fisabilillahi meya tsare musu ne?”……

    “Ameen ya Allah, hmmm shiko ya tsare musu abubuwa dayawa mana amma ta Allah ba tasu ba”…..

Umm batace komai ba taja motar suka tafi tana dan wani lissafi a ranta game da abinda mami tace…….

Ko breakfast basu iya sunyi ba suka tafi prison dan su samu information a gurin Deen kan yanda zasu fara neman yarinyar mutane, only for them to get to to a burnt building, prison din ya kone kurmus kamar baa taba gini a gurin ba, a rikice suka shiga tambayar yan kallo abinda ya faru dan sun kasa fahimtar komai, kadama Umm taji labari dan har tayi breaking down tun kafin taji abinda ya faru as the emotional person as she is, bayani aka fara musu akan wurin aka kaiwa hari cikin dare aka kona komai naciki da mutanen dake ciki………

Tsabar rikicewa Mami batasan sanda ta fara dialing number Deen ba kamar basu suka dawo dashi gurin jiya ba…. Miraculously sai wayar tashiga har tana ringing, hakan yayi diverting attention dinsu suka kasa jin karshen labarin, saidai Deen sam yaki dauka ita kuma taki hakura har Allah yasa a kiran data masa na goma ya dau wayar…. 

Bayan ya daga wayar ta dauka hallucinating takeyi har saida taji maganarsa radau harda kokarin mata karyan yana prison besan barinsa prison din shine alheri agaresa ba, for the first time taji taurin kan Deen ya birgeta dukda batasan meyasa ya gudu ba amma alamu sun nuna besan aika aikan da aka yiwa gurin ba, koma meyasa ya bar gurin taji dadi sosai….. 

Within 10mins suka karasa gida dake basu da wani nisa da prison din,zama sukayi jigum bayan sun karasa parlour suna jiran zuwan Deen…..

 

         Jingine yake jikin mota bayan yayi parking, ko ciki be shigaba yasa aka tara masa securities din gidan gabadaya da zasu kai hamsin, ya musu warning me kyau akan barinta ta kara fita daga gidan bayan ya tabbatar sun gane wa yake nufi, hakuri suka shiga basa da nunamasa cewa baa basu order din hanata fita ba da baza su barta ta fita, be damu ba ya kara musu kashedi me kyau akan barinta ta fita kome zatace musu su hanata, cikeda ladabi suka amsa masa da tabbatar masa zasuyi yanda yace, be kara ce musu komai ba ya bude mota ya dauketa kamar yanda ake daukan jarirai ya shige ciki ya barsu a gurin……

       “Baba anya ba matarsa bace kuwa?”…..

Cewar daya daga cikin securities din yana dariya….

     “Gaskiya daga gani ma, amma sun dace sosai”….

   “Kaidai bari ya’yansu ba karamin kyau zasuyi ba, gaskiya oga ya more ko a ina ya samota?”…

    “Toh ya isa kowa ya koma aikinsa, Idan ya jiku zakuyi bayani”…..

Chief security na fadin haka suka watse kowa ya koma bakin aikinsa…….

       Suna zaune tagumi dauke akan fuskokinsu sun zubawa sarautar Allah ido suga dawowar Deen sukaji sallamarsa …. Dagowa sukayi da sauri sukaci karo dashi yana shigowa kamar yanda sukayi tsammani saidai kafadarsa dauke da wata da basusan wacece ba kuma, haka suka daure sukayi gum da bakinsu musamman mami da tayi alkawari bazata ce komai ba……

Yana jin idanunsu akansa dukda basuce komai ba hakan ba karamin kashe masa jiki yayi ba, for more than three times kenan yana daukanta a gabansu bayan Mami har warning ta bashi akan hakan saidai ba lefinsa bane yarinyar ce abu kadan saita suma inbe dauketa ba bari zeyi wani katon ya tabata?, Sai kuma ya diririce ya rasa ina ze ajyeta irin guilty conscience dinnan kawai ya direta a three sitter dake facing dinsu…..

    “Erm I’m sorry kince karna kara daukanta.

, she’s unconscious that’s why”…

Tasowa sukayi da sauri jin abinda yace, ko be musu bayani ba sungane wa yake nufi, suda suketa nemanta hankali tashe, itace ma silar zuwansu prison gurinsa dan su tambayesa information akanta indirectly yanda zasuje su nemota basai yasan ta bata ba, sai sukaji mummunan labari kuma, cikin ikon Allah kuma sai komai yazo musu da sauki…….

      “A ina ka ganta saif? Tun safe muke nemanta”..

Umm data kasa hakuri tayi magana ……

      “It was a coincidence! Kawai haduwa mukayi a hanya, nima nayi mamaki dana ganta, all my thought is that tana nan, how comes ta fita baku sani ba?”……

     “We never thought zata fita saif damunsa an hanata fita, bakaga yanda hankalinmu ya tashi ba”…

     “I understand, na fadamusu karsu kara bari ta fita”…….

      “How did you manage to escape”……

Sai a lokacin mami tayi magana……

Dan jim yayi yana tinanin abinda ya kamata ya gayamusu gashi bayaso yayi karya dan yaga a kwana kinnan yana neman farawa abinda ba halinsa bane;

      “I left because of her, I had a very bad dream about her that she isn’t safe shiyasa kawai nayi sneaking out, ina fitowa kuma naganta”….

Ya fada yana nuna fatima zainab da har lokacin take a sume…….

Ajiyar zuciya Mami ta sauke itama tana kallon fatima zainab tace;

    “Ke alheri ce!!!”……

   “Indeed! Badan ya fita nemanta ba da yanzu wani labarin akeyi, Allah mungode maka”….

Umm ta kara da fadin haka….

     “Meya sumar da ita?”..,,

  “Wallahi Mami bansani ba, nadai cire wani zobe daga hannunta shikenan ta suma”…..

   “Ikon Allah, toh yanzu meye abin yi? Ka zuba mata ruwane bata farfado ba?”…..

Shiru yayi yana ayyana haukar daya tafka, mutum ya suma amma ace ya kasa basa taimako as a Doctor? Shidai wannan yarinya na barar masa da karatunsa…. Kada kai kawai yayi alamun be zuba mata ruwa ba…..

     “Allah dai ya shiryeka, you’re a disgrace to the Doctors”….

Umm ta fada tana tashi ta dauko ruwa…… 

Dan diban ruwan tayi tashiga shafa mata a fuska kamar dai tana wanke mata fuska, saida ta mata sau biyar sannan ta fara tari alamun ruwan ya shigar mata hanci…..

Dagota tayi ta kwantar da ita a jikinta tana bubbuga bayanta tana mata sannu….. 

Sunfi minti uku a haka kafin a hankali taji ta dena tari, dagota tayi tana kokarin tattare mata gashinta daya wargaje aranta tana fadin ‘masha Allah’……

Yana tsaye akansu har aka gama tattare kan sai tsaki yake wai an bawa gashin doki mahimmanci haka, babu wanda ya kulasa dan batashi suke a lokacin ba..

Ruko hannunta Umm tayi tana fadin;

       “Meyasa kika tafi ba sallama?”….

   “Ba tafiya nayi ba I went to get something”….

   “Basai ki fada ba a siyomiki ba, sannan you went to get something amma kika ki dawowa saida Saif ya sake gano ki”…….

Shiru tayi kamar bazatace wani abuba sai chan kuma ta dago ta kalli Deen tana shirin yin magana ya katseta da fadin

     “Kya kalleni mana tinda kinsan bakida gaskiya da idonki irin na yan shaye shaye ni dena kallona ma”…

Batarai tayi sosai tace;

     “Toh ba school naje ba, Mami ki fada mishi karya kara zagarmin ido”……

     “Barshi he’s just jealous dan yaga idonshi beda kyan naki”……

Mami ta fada tana murmushi……

     “Tabb koda kudi me yawa akace na karbi idonta akai kasuwa wallahi, kuma ba school kika jeba gidan saurayinki kikaje, ko kin dauka bansani bane?”….

So take ta bashi amsa daidai dashi amma bataso tayi magana a gabansu cuz she’s good at playing her games yanda idan yace ta mishi wani abun bazasu yarda ba shiyasa takeso ta musu two face……

Cikin muryar shagwapa ta kalli Umm tace;

      “Dan kaga mamanka anan shine kakemin sharri”…

Dan duk a tinaninta Umm ce mamanshi kamar yanda ta fadamata….

      “Rabu dashi aikema ya’ta ce kinji ko?”…..

Sai kuma ta harari Deen tace;

     “Dan kaga bata da baki kake mata sharri ko?”….

Dariyar rainin hankali Deen yayi irin Umm bakisan halinta dinnan ba yana shirin magana kenan sukaga ta rike kai sai juyawa take kamar kadangare…….

        “Kehhhhh!!”….

Deen ya fada a tsawace….

A rikice ta dago still hannunta dafe da kanta, sai kuma ta kwalla wani kara tana kurawa kofar parlourn ido……

Sosai su Mami da Umm suka tsorota da wannan kara data saki, daurewa kawai sukayi sukaci gaba da zaman a gurin suna tambayarta meya faru……

Bata kulasu ba ta sake kwalla wata karar datafi ta farko sai kuma ta fashe da wani matsanancin kuka me hade da shassheka……

       “Kehhhhh shut up!”…. 

Ya kuma daka mata tsawar dataji kamar hanjin cikinta zasu fado tsabar yanda ta firgita dama a firgice take……

      “Ki nutsu nace!!”…..

Tsit tayi sai dan shasshekan kukanta dayake tashi….

     “Dago ki kalleni!”….

Da sauri ta dago ta kallesa dan ba karamin shiga taitahinta muryarsa yasa tayi ba…..

     “Menene?”….

     “Wanchan”…

Ta fada tana nuna jikin kofa hawaye na zuba a idonta…..

Sosai ta basa tausayi amma ya dake dan yanaso ya gano inda matsalar take ganin kamar a tsorace take sosai, dan dai yasan haka kawai bazata masa biyayya ba…..

      “A ina yake?”….

    “Jikin kofa”…..

Kallon kofar su dukansu sukayi sukaga ba kowa alamun ita kadai ke ganin abunta, kasa motsi Umm da mami sukayi dan ba karamin daga musu hankali abun yayi ba…. 

Gyara tsayuwarsa Deen yayi yace;

   “Meyace miki?”…..

  “Yace in taso mu tafi”….

Kwafa yayi yace;

    “Taso muje ki nunamin inda yake”…

Ya fada yana mika mata hannunsa alamun ta miko hannunta ya taimaka mata, ba musu ko ta mika hannun, taimaka mata yayi ta tashi har lokacin be dena mamakin yanda bata masa musu ba…..

Hannunta ya rike gam a cikin nasa sannan ya nufi kofar da ita a ranshi yana ayyana yanda zeci uban koma waye dan yasan baze wuce mahaukatan aljanunta ba……

Suna zuwa bakin kofar abu kamar almara ta nemi wanda take gani ta rasa…..

Hannunta ya kara damkewa a cikin nata sannan yace;

      “Maza nunamin shi inci ubansa!”…..

    “Ya gudu, bana ganinsa, yace meyasa nazo dakai amma ze dawo”…..

     “Ina nan ina jiran dawowarsa koma wani dan iska ne, aida ya tsaya danayi maganinsa!”….

Deen ya fada ransa na sosuwa da guduwar da meshi yayi, saidai ya shiga kokwanto sosai akan anya aljanunta ne wannan kuwa? Saboda bega alamun aljanu ba a abinda yaga tanayi saidai babu abinda is not possible a game da aljanu…… 

Dawo da ita tsakiyar su mami yayi sannan ya kunna karatun qur’ani a home theater ya kure volume din, nan da nan gidan ya dauka bakajin komai sai sautin daddadan kira’ar sheikh sudais……

A hankali fatima zainab taji tana samun nitsuwa sosai har wani daddadan bacci ya dauketa a kafadar Umm, gyara mata kwanciya sukayi Mami ta dawo da kanta kan cinyarta, Umm kuma ta daura kafafunta kan cinyarta tana mata tausa kadan kadan…….

Suna zaune a haka har aka kira sallar azahar Deen ya mike yace bari yaje yayi sallah ya dawo sai suma suje suyi dan bayaso a barta ita kadai.. Haka kuwa akayi har sallar la’asar shiya farayi kafin…..

Ganin karfe biyar tayine yasasu tashinta dan ba kyau baccin yamma, Mami da kanta ta kaita dakinta ta sata tayi wanka tayi alwala sannan ta bata kaya ta chanja ta tada sallah, ko nan da chan bata motsa ba harsaida taga ta idar da sallah sannan suka fito tare, sai a lokacin suka tuna ko abincin safe basuci ba ranar, wato cin abinci ma guri ya samu, wani tashin hankalin idan kashiga saika manta da wani abu wai shi abinci….

Dining ta nufa da ita suka tarar da Umm da Deen suna dan hirarsu ga abinci nan a jere kala kala sai kamshi ke tashi, ga tray din kayan fruits kala daban daban an ajye incase in yauma bazata iya cin abincin ba……

Da kanta ta zauna a gaban kayan fruit dan tasan bazata iya cin abinci ba, dan kallonta Deen yayi ganin ta zauna a chan gefe inda aka ajye fruit means bazata abinci ba kenan?…..

     “Taso ki dawo nan”

Ya fada yana nuna mata kusa da Mami….

   “Abincin ne fa batasan ci, last time ma bataci ba, ta cemana bata cin abinci”……

    “And who does that? Mami saiku zuba mata ido tace batacin abinci?”…

   “Toh ya kakesu muyi? Fruit dinma kinsha tayi saida na bata a baki”….

Bece komai ba ya mike yana diban varieties na abincin dake gurin a cikin plate sannan ya nufi inda take…. Jan kujera yayi ya zauna a gefenta yana kallonta jajayen lebenta daketa sheki ya dibo abinci ya kai bakinta yana fadin;

     “Open your mouth”…..

Dan karyar da wuyarta tayi alamun baza taci ba…..

    “Kinsan abinda ake cewa dure? Like forcing someone to eat irin yanda akeyiwa babies a toshe musu hanci toh haka zan miki idan bakiyi wasa ba”..

     “I’ll take the fruit”…..

Ta fada kamar zatayi kuka….

Dan jim yayi yana tinanin har lokacin she’s not ok…..

     “Fruit aiba abinci bane, kici abincin sai ki kara da fruit din”…..

     “Ni banaci….

   “Open your mouth my friend!”…..

Ya daka mata tsawa….

A take ta bude bakin jikinta na dan rawa alamun har lokacin tanajin tsoro……

Haka yayita bata abincin a baki, data ki karba saiya zare mata ido, saida taci rabi taga bazata iya karaci ba kawai tasa masa kuka”……

 Dariya yayi sosai yana tashi daga gurin, cikin rarrashi yace;

     “Sorry karkiyi kuka, ko kefah dan Allah?”……

Ajiyar zuciya tashiga saukewa a jejjere,daga bisani kuma ta mike tabar parlourn, ganin bedroom din Mami tayi ya sashi dawowa inda su mami suke yana dariya……..

     “Allah ya shiryeka Saif, kawai kasa yar mutane kuka, irin wa’yennan da lallashi ake binsu ba masifa ba”…..

Cewar Umm tana harararshi…..

     “Itafa wannan zumace saida wuta, na bita a hankali ma rashin kunya zatamin”….

    “Toh sannu gyambo sarkin san girma, yanzu kasata tayi tafiyarta”…..

  “Fushi fa tayi, yar yarinya da ita sai zuciyar tsiya”..

  “Kadai chanja hali na fadamaka, inba hakaba matarka nada aiki wallahi”……

Bata rai yayi sosai irin anmishi maganar da bayaso maganar aure…..

      “Ai kuma kin tabo abinda baya son ji”….

Cewar Mami tana dariya….

    “Aure ko dole mutum sai yayi ba! So kake mu zuba maka ido kenan”…..

    “Mami dan Allah ya sunan yarinyar nan naji kamar rannan kuna tambayarta?”….,

Ya fada yana kokarin kauda wanchan maganar….

   “Ikon Allah ba tare muka ganku ba? Kai bakasan sunanta ba?”….

     “Bansani ba wallahi, tell me pls”….

  “Okay, sunanta fatima zainab”…..

Zama yayi a kujerar dake facing mami yace;

    “Bangane fatima zainab ba? Fatima ko zainab? Which one is her name”…..

     “Both haka ta fada mana ko Umm?”….

Gyada kai Umm tayi alamar tabbatarwa….

     “Gaskiya it can’t be, karya takeyi saidai in sunanta zainab dan banaso ta zama namesake dinki mami, she doesn’t deserve the name”…..

     “Ikon Allah sai kallo niko inaso ta zama namesake dina, na rasa ganemaka akan lamarin yarinyarnan Saifuddeen, kace kana taimakonta amma sai kaita mata wulakanci da masifa?”……

Sosa keyarsa yayi yana mikewa yayi hanyar dakin Mami, dawo dashi tayi da fadin;

     “Where to?”

   “Zanje in kirata ne karta zauna ita kadai”….

 “Barta yanzu zamu tafi dakin ai salon kaje ka kara takura mata”……

  “Toh mami ku kwana ku dukanku a dakin sai kusata a tsakiya ni kuma a parlour zan kwana inga ta inda zatabi ta sake fita yau”……

      “Angama bappa”……

Ta kirashi da sunan mahaifinta ganin yanda yake basu instruction kamar wani ubansu, sudai sun rasa ina Saif ya dauko wannan authoritative halin nasa, tsabar san girma wani zubin idan ze musu magana kamar da ya’yansa yakeyi, insu ya musu haka toh inaga matarsa? Haka kawai yar mutane taje tana shan wahala dashi……..

      “Allah ya shiryeka, ya maka albarka”….

Mami ta fada ganin ko ajikinsa yayi wucewarsa ya barsu a gurin…….

    Kamar yanda ya fada ko haka akayi, suka sata a tsakiya shikuma yasa pillow a kasa ya kwanta a parlourn dan yasan in yace ze hau kujera babu wacce zata daukeshi kasancewarsa giant mutum…….

Su Mami da Umm na bacci sukaji shesshekan mutum, Mami ce ta fara farkawa taganta tana sallah tana kuka sannan Umm itama ta farka, sosai ta basu tausayi sunata tinanin abinda yake damunta haka, dan daga jin irin kukan da take kasan wani abu damunta sosai amma ba karamin burgesu tayi ba da take kaiwa Allah kukanta, so suke su tashi suma suyi sallar amma basa so su katseta, haka suka kasa bacci suna mata addu’a daga kwancen har akayi sallar asuba sallar asuba…..

 Mikewa sukayi kowa da abinda yake rayawa a ransa akan abinda suka gani, a gaban idonsu tafi hour biyu tana sallah tana kuka a hakanma basusan tashinta ba……

Alwala suka dauro sukayi sallah suma sannan suka shiga lazimi har lokacin itama bata tashi daga kan sallaya ba….

 Murmushi Umm tayi ta kalleta tace;

      “Daughter ba gaisuwa?”…..

    “Ina kwananku”…..

    “Lafiya lau, kin tashi lafiya?”….

    “Alhamdulillah”…..

Sai kuma ta tashi ta ninke  abun sallar sannan ta koma ta kwanta……..

     Kasa bacci yayi kamar jiya dan ji yake kamar zata iya fitowa ta gudu be sani ba, alwala ya dauro ya shiga sallah yana mata addu’a kamar jiya har aka kira sallahr asuba……

      Karfe takwas ta fito parlour a shirye cikin peach abaya cikin kayan da Mami ta kawo mata jiya, sosai kayan suka mata kyau kamar ba ita ba, itada kanta wani iri takejinta idan tasa mayafi amma tarasa meyasa bata shaawar sa hijabi yanzu…..

Dagowar da zatayi sukayi ido hudu da Deen dake zaune akan three sitter yana danna waya……

    “Kehhhh?”…..

Dauke kai tayi kamar bada ita yake magana ba…

     “Baki iya gaisuwa ba?”….

Sai a lokacin ta juyo ta kalleshi ido cikin ido tace;

     “Gaisuwa my foot! Kai a suwa da zan gaishe ka?”…

Dauke idonsa yayi daga kanta yace;

     “Oh harsun sake ki kenan shine zaki zo ki faramin rashin kunya ko?”…..

    “Kai kasan wannan kuma!”….

   “Ina zaki da sassafennan, wato kin lalace dasa karamin mayafi yanzu ko?”…..

    “Inda ka aikeni zani sannan ko yawo babu kaya zanyi be shafeka ba tinda ba ajyeni kayiba!”…..

Badan ba kyau mugun fata ba da yace ya fisan suyita riketa sunasa mata tsoro ko banza ta masa biyyaya, wani smirking yayi yace;

   “It’s alright zoki wuce toh”…….

Hankali kwance ta tawo zatabi ta gabanshi ta wuce..

Tazo daidai inda yake yasamata kafa tayi taga taga zata fadi sannan ya tarota ta fado jikinsa…..

     “Ouchhh zata karyamin hannu”…..

Ya fada kamar bashi yasa mata kafa ba….

     “Ke wallahi saina rama”….

Yana fadin haka ya gyaramata zamanta a jikinsa sannan ya murde mata hannu daya….

Wani ihu ta saki tana fadin;

     “Ka sakemin hannu mugu kawai”…

Sake murde hannun yayi yace;

     “Nine mugu ko?”…..

Zafin dataji ya rasata yasata fadin “A’a ba kai bane” da sauri….

Sake murde dayan hannun yayi yace;

    “Ni sa’anki ne?”….. 

        “A’a wallahi”…

Ta sake fada tana kokarin janye hannunta…..

       “Kice min yaya saif toh”….

      “Wallahi bazan ce ba”….

Hannayen duka biyu ya kara lankwasawa yanda yasan zataji zafi yana shirin magana ya jita cikin ihu tace;

       “Yaya saifffffff”……..

Wani murmushi me kyau yayi yana shirin magana kenan yaji takun mutum, da sauri ya sauketa daga kan cinyarsa yana turata gefe…..

     “Wani mugunta kake mata hakane? Meyasa bakada kirki ne wai?”…..

       “Bafa abinda na mata Umm, aljanunta ne suka tashi fah”…..

     “Kaine aljanin ashe?, ba sunanka naji ta kira ba?…

     “Shine fah ya murde min hannu kuma ban masa komai ba”…….  

    “Taso rabu dashi, zan rama miki kinji koh?”…

Mami ta fada tana yafito ta…..

 Tashi tayi ta koma kusa da Mami tana harararsa ta kudirta a ranta saita rama kota wace hanya ce dan baa tabata ta kyale, shine mutum na farko daya taba mata mugunta ya kwana lafiya….. Tana zama idonta ya sauka akan wani hoton mami dake manne a jikin bangon parlourn an rubuta Justice Fatima a kasan hoton da manyan rubutu, zaro ido tayi ta dago da sauri tana kallon mami tace;

      “Kece Justice Fatima?”…

      “Yes dear, meya faru”….

Zatayi magana kenan sukaji karar landline….

Deen ne ya dauka dayake yafi kusa da nan….

     “Your guest is here mami”

Ya fada yana sauke wayar…..

      “Ok”….

Mami tace sannan ta tashi ta fita…..

      

Tin kafin ta karasa ciki ta jiyo kamshin turarensa da ko shekaru nawa zaayi bazata kasa ganewa inba chanjawa yayi ba…. Toh amma bashi take expecting ba, wato wayo yayi ya biyo ta hannu deputy governor  kenan?……….

     “I know you were expecting the deputy governor, I don’t have choice shiyasa nabiyo ta haka dan nasan stubborn self dinki bazesa ki yarda nazo ba!”….

    “Enough of all the surutu! Meya kawoka gidana?!”.

    “Su gida manya! well nazo tafiya da da’ na ne”…..

    “Dan daya kone? Ka taba zuwa ko sau daya ka dubashi a lokacin da yake prison dinne, sai yanzu zaka zo min da wani nonsense after an kona gurin!”…

     “Watch your words! Da kika hana kowa ganinsa ta ina zan gansa? Sannan na baki dama inga irin abinda zakiyi but you failed har saida aka kusa kashesa, now I need my son back I want to protect him with all my life”…..

    “Your son indeed! Niko nayi protecting dinsa , daba danni ba da mutanenka tuni sun kashesa ai!”….

   “For the second time watch your tongue Justice fatima! Ni kike cewa mutanena zasu kashe dan ciki na?”……

     “Anki ayi watching tongue din!! In ba mutanenku na banzar siyasan da kuka daurawa kanku ba suwaye suke neman ganin bayansa?!!”……

     “It’s alright, I won’t talk much anymore dan banida lokacin shirmen da kike fada, ki bani dana kawai na tafi dashi in masa aure ya zauna guri daya”…..

     “In aure ne nima zan iya masa, he has been with you all his life now it’s my time! And I already have someone for him!”…..

    “Baki isaba dan na riga na masa mata!”…

    “Nima na masa mata, saidai ka hakura ya auri zabi na!”….

    “Wallahi bazai yiwu ba dan bazan zama karamin mutum ba, kuma ki tambayesa dan yasan da maganar”…..

     “Wannan ba matsalata bace! All I know is that zabina ze aura”….

    “Look Fatima niba da wani hayaniya nazo ba so don’t provoke me, na amince ya auri duka zabinki da nawa”…….

     “Wallahi baze yiwu ba, yanda ban zauna da kishiya ba shima baze auri yar mutane ya mata kishiya ba!!”…..

     “Toh sai ki haramta abinda Allah ya halasta, inko haka kika zaba saidai ya dau zabina ya bar naki!”…

     “In your dreams! Mu zuba mugani”….

Tana fadin haka ta fita ta barshi a gurin………

Ko kulasu Umm dake zaune a parlourn batayi ba ta wuce bedroom rai a bace…..

     “Wai waye yazo ne take fushi haka?”….

Umm ta fada tana kallon Deen kamar shida mamin suka fita tare..…..

Deen zeyi magana kenan yaga dad na kiransa a waya, be daga ba yayi dariya yace;

     “Ashe tsohon mijinta ne yazo, shi yake kirana yanzu”….

Dakuwa Umm ta masa tace;

     “Kaniyarka, nace kaniyarka Saif!”…..

Dariya yayi ya tashi ya fita daga parlourn ya tafi gurin dad…….

Mami na shiga ta dauki wayarta ta shiga dialing number eesha, bugu biyu eesha ta dauka….

     “Hello daughter”….

  “Yes mom, ina kwana”…

   “Lafiya lau, ya school?”….

   “Alhamdulillah, nayi missing dinki sosai, jiya nake maganarki ina cewa zan zo na gaisheki”…

  “Allah sarki dear, dama zan fada miki yayanki Saifuddeen ya dawo ne”….

Wani tsalle eesha ta daka jin ance crush dinta ya dawo, mutumin da taki kula kowa saboda son da take masa, cikin farin ciki tace;

     “Wayyo Allah, yaushe ya dawo mami? Inzo yanzu dan Allah?”……

     “Aa ki bari anjima da rana sai kizo, akwai maganar da zamuyi in kinzo”…..

Domin Karanta littafin daga farko sai ku danna bulun Rubutun dake kasa 👇👇👇

https://www.aihausanovels.com.ng/2023/01/wace-ce-ita-chapter-21-complete-novel.html

Share and comment🌹

Back to top button