Hausa novels

Halysaah Page 18 By Khaleesat Haydar

Wajen karfe goma na safe Khaleesat na kwance dakinta idonta rufe duk da ba bacci take ba, ji tayi ana kwankwasa kofa, kamar bazata iya tashi ba daga karshe dai ta mike ta sauka daga kan gadon ta dau hijab dinta ta saka, tana tafiya a hankali ta fito parlor, ta tagar parlon ta duba ta ga Housemate dinta ne, ta karasa ta bude kofar, Yace “Sorry na tashe ki kina bacci, i forgot the key at home” Ita dai bata yarda sun hada ido ba a hankali tace “Ina kwana?” Yace “Lafiya lau, how are you feeling now?” Ta juya going back to the parlor tace “Alhamdulillah” Ya bi ta da kallo sannan ya shiga parlorn, dakinta ya ga zata koma yace “Halysaah” Ta tsaya, after few seconds ta juyo but couldn’t let her eyes contact his, shi dai kallonta kawai yake, ya karasa inda take tsaye yace “What happened?” Girgiza masa kai kawai tayi, lkci daya hawaye ya fara sauka idonta, ya dauke kai na ‘yan dakiku kafin ya sake juyowa ya nuna mata kujera yace “Sit” Komawa tayi ta zauna, ya zauna shima yana kallonta yace “Tell me what’s wrong” Ta sunkuyar da kanta, yace “Are you sick?” Ta girgiza masa kai, yace “Wannan saurayin naki ko?” Ta kasa basa amsa wasu hawayen na sauka idonta, sai kuma ta fashe masa da kuka, mikewa yayi yace “Waye ya hadaki da wannan mutumi ne? Why did u allow him know ur weak point? Why are you always crying because of him? Is he happy making u sad now and then?” Khaleesat dai kuka take a hankali, yayi shiru for almost 2 mins yana jin ransa na baci, can ya kalleta yace “Kee in zaki yi facing study dinki is better you do so, give that ur so called boyfriend space, ur exam is around the corner” Sai a sannan Khaleesat ta daga idanuwanta da suka yi ja ta kallesa, sae kuma ya kwantar da murya yace “Kiyi hakuri Housemate, zan dinga sa ki a addu’ata Allah ya maki mafita, i can’t just intrude cause ban san sanda ku ka san juna da shi ba, ban kuma san me ya hada ku ba, i will only include you to my prayers i promise Halysaah” Khaleesat ta gyada masa kai da kyar, sannan ta mike cikin sanyin murya tace “Nagode” Daga haka ta juya ta nufi dakinta, Jay ya koma ya zauna yana mamakin irin son da take ma gayen da har ta kasa rabuwa da shi duk da musguna mata da yake yi a soyayya, bata da aiki sae yi masa kuka, da kanwarsa ce daga ita har saurayin zai hada ya ci ubansu, kuma ya rabata da shi na har abada, tausayinta yaji har cikin ransa don bai san wani irin so bane wannan take masa da har take iya tolerating abubuwan da yake mata, and ya lura the guy is taking advantage of this to hurt her always, mikewa yayi ya tafi kitchen kamar yanda ya zarga yaga alamar bata yi breakfast ba har sannan don kitchen din ma bata shigo ba, fridge ya bude ganin abincin da Safiyyah ta kawo mata jiya yayi mata microwaving dinsa ya hada mata shayi sannan ya kai mata daki, sai da yayi knocking ta amsa sannan ya shiga dakin, tun da ya shigo Khaleesat ke kallonsa har ya ajiye mata abincin, ta sauke idonta a hankali tace “Nagode” kai kawai ya gyada mata, sai kuma ta bi sa da kallo har ya fita daga dakin, karfe sha biyu saura Khaleesat ta jawo wayarta jin yana vibrate, tana duba screen din taga Abdul ke kiranta, ta sauke idonta kasa tayi picking call din ta kai kunne amma bata ce komai ba, yace “Khaleesah….” ta kasa amsawa hawaye ya fara sauka idonta, yace “Can you hear me?” Da kyar tace “Um” Yace “How was you night” tana share hawayen dake sauka idonta tace “Alhamdulillah” Tun daga wannan rana Khaleesat ta fara avoiding duk wani abu da zai hadasu fada da Abdul, she want just nothing but peace with him for her sanity, bin sa kawai take a yanda yake so for peace to keep reigning, in ma bala’i yake mata a waya zata yi shiru ta gama saurarensa sannan daga karshe ta basa hakuri kamar yanda take yi masa da, ranan da bai kirata ba kuwa ita zata kirasa, hakan kuma da tayi ya sa ta samu kwanciyar hankali har take concentrating a karatun ta, amma fa in ta tuna irin kulawar da Housemate dinta ke bata always wanting to make sure she is fine sai taji she isn’t lucky having Abdul, ana haka har exams dinsu ya rage some days, ranan Wednesday tana kitchen da safe taji ana kwankwasa kofa, ta fito daga kitchen din don dama she is expecting Safiyyah, ta bude mata kofa, Safiyyah ta shigo tace “Ai na zata zan zo in tarar baki tashi ba?” Khaleesat tayi kasa da murya tace “Aa i am in the kitchen” Safiyyah tace “Ohk, why are you lowering ur voice?” Still Whispering Khaleesat tace “My Housemate is sleeping” Safiyyah ta sake baki tana kallonta, sai kuma ta rike haɓa tace “Ikon Allah gadinsa kike kenan?” Khaleesat ta hade rai tace “Ban gane gadinsa ba, daxu fa ya zo, and dama bacci yake zuwa yayi da safe don yace min baya bacci da daddare” Safiyyah couldn’t stop smiling tana kallon Khaleesat, Khaleesat ta wani harareta ta juya ta koma kitchen, Safiyyah ta karasa ta zauna kan kujera har sannan bata daina murmushi ba, sai ga Khaleesat ta fito daga kitchen, still tana magana kasa kasa tace “Ko dai kawai mu je waje ki min gyaran gashin, kinga Hand dryer yana ƙara in ana using dinsa, it’s noisy” Safiyyah ta buda baki tace “Ikon Allah, to akwai socket ne a wajen?” Khaleesat tace “Zan sa Extension a kitchen sai mu fito da shi ta window ai zai yi, kuma akwai tap a garden din sai mu wanke gashin ma a nan” Safiyyah dai murmushi kawai take bata ce mata komai ba, yanda Khaleesat tace haka din tayi duk don kar karan Hand dryer ya tada Housemate dinta or any of their noise kamar yanda tace, abinda bata sani ba ashe ba bacci yake ba aiki yake yi a Laptop dinsa a daki, bayan sun isa karamin Garden din dake bayan kitchen Khaleesat ta ajiye duk shampoo da Conditioner din hannunta sannan ta bude gashinta, Safiyyah na kallon gashin tace “Tab, Allah sa Shampoo din da Conditioner su isa dai” Khaleesat ta wani hade rai tace “Ban gane ba, saboda bargo za ki wanke?” Safiyyah tayi dariya tace “To meye banbancin wannan da bargon Khaleesat? Babancinsa kawai wannan akan ki yake, ni naga ma kamar karuwa gashin yake Tabarakallah Maa sha Allah” Khaleesat tace “Ba abinda ya karu yana nan yanda yake” A haka Safiyyah ta fara wanke mata gashin, suka dau time sosai bayan ta gama wankewa ta fara busar mata shi da Dryer, Jay ya shigo kitchen zai yi making Coffee drink ya dinga kallonsu ta window din kitchen, he was confuse seeing her hair, is all that Hair or what? long, full and black, kawai yaji bai yarda gashinta bane, ya juya ya fara yin abinda ya kawo sa kitchen din, Khaleesat ta kasa kunne sosai jin kamar sound a kitchen, ai ko ta jawo mayafinta da sauri ta rufe kanta bayan ta hangosa a kitchen din ya juya masu baya, Safiyyah dai sai kallonta take, Khaleesat ta mike ta isa kusa da window din kitchen din tana kallonsa tace “You woke up early today” Ya juya ya kalleta yace “This is to 12” Khaleesat ta zaro ido don bata san lkci ya wuce haka ba, ashe sun bata lkci sosai wajen wanke gashinta, yace “Me kike yi a nan?” Tace “I am together with my frnd Safiyyah” Ya ci gaba da abinda yake yi yace “Ohk my regards” Juyawa tayi ta koma gun Safiyyah, bayan Drying har Stretching gashin sai da Safiyyah tayi mata, Safiyyah tace “You know what Khaleesat, anjima ki zo can gida sai in maki Kalaba din, i think i can feel my period, i need to go home” Khaleesat ta juya ta kalleta tace “Da gaske?” Safiyyah tace “Wallahi, gwara in tafi gida kar ya zo” Khaleesat tace “Ohk, amma ki bari in dafa mana indomie ki ci tukun ki tafi” Safiyyah tace “Ke bazan ci ba, bari in tafi kawai i am uncomfortable” A hankali Khaleesat tace “To shikenan” Safiyyah tace “Sannan pls Khaleesat nace ma Ya Musty ran sunday zaki zo gidan tunda kinga Monday za mu fara exams, ko 2 days ne sai kiyi kafin matarsa ta fito da baƙin halinta gaba daya, kin dai ga bazai ce bamu ji maganarsa ba yace ki dawo gidansa baki dawo ba, even if it’s just 2 days come and spend in his house pls” Khaleesat tace “Wallahi ba wai bana son zuwa bane ko kuma ban ji maganarsa ba Safiyyah, bana son issue ne da matarsa, i don’t want any problem” Safiyyah tace “I know, shi yasa nace ko kwana biyu ne kawai ki zo kiyi ai bazai ce baki zo ba, ranan Sunday sai ki debi kayanki kala uku ki taho kawai, probably ma daga karshe nima nan gidan zan dawo mu yi karatu tare, ni nasan ba lallai ma kiyi kwana biyun ba matarsa bata kirkiro wata matsala ba, so just chill ba zama zaki yi a gidan ba Likewise myself” Khaleesat tayi shiru kamar me nazari, sau biyu Mustaphan ke mata magana da kansa ta WhatsApp akan dawowar da yace tayi gidansa, iyaka sai tace masa in sha Allah tana nan zuwa before exam, Safiyyah ma tayi mata magana yafi a kirga, ko don Safiyyah zata daure kawai taje tayi kwana biyun a gidan, let it not be as if bata jin magana, a haka ta raka Safiyyah bayan tayi order din Uber da zai maida ta gida, Khaleesat na dawowa parlor taga Housemate dinta ya shirya zai fita, yana kallonta yace “Wai duk gashinki ne wannan ko dai ƙarin gashi kike yi Halysaah?” Ta daga idanuwanta ta kallesa bayan tayi realizing ashe ya ganta kenan daxu, sauke idonta tayi tace “Ƙarin gashi kuma?” Yace “Naki ne? Ai na gansa kamar ba naki bane, sorry” Ɗan murmushi kawai tayi without giving him an answer, can yace “Wait, amma ba ki jin zafi na damun ki? I mean baya takura ki gashin? isn’t it too much?” Tace “How?” Sounding so serious yace “Ki rage mana, just cut half of it off kema ki huta, sai kiyi azumi uku, wannan ai burden ne Halysaah, it’s too much, ji fa sai da kawarki ta zo taya ki wankewa don kema baza ki iya wankesa da kanki ba, all this while ni na zata irin wannan acuci mazan da ku ke yi ne kike daurawa a kanki, i never knew gashin ki ne” Khaleesat tayi murmushi ba tare da tasan tayi hakan ba, can ta kallesa calmly tace “But i am not complaining, kuma ai ba nauyi gashin yake min a kai ba” Ya wara ido yace “Ohh! my bad, haka ne kuma fa, hope you are reading so well for ur exam, kinga in few days time zaku fara, i think monday ko?” Ta gyada masa kai, yace “Wishing you the very best of luck Halysaah” a hankali tace “Thank you” Yace “See ya later” Ta gyada masa kai, daga haka ya juya ya nufi kofa ya fita daga parlon…. Da yamma Khaleesat ta gama shiryawa bayan Safiyyah ta isheta da kira wai taje ta mata kitson, Khaleesat ta dau handbag dinta da mukullin gida bayan Uber din da tayi order ya iso sannan ta fita daga gidan ta kulle, tana hanya kiran Safiyyah ya shigo wayarta, ta daga tace “Ina hanya fa” Safiyyah tace “Allah in baki zo ba sai dai gashinki yayi ta zama haka bani da lokacin maki wani kalaba kuma idan aka fara jarabawa” Khaleesat dai tayi murmushi, tasan kawai Safiyyah so take ta je gidan, karfe hudu da yan mintuna ta isa gidan ta sauka Uber sannan tana tafiya a hankali ta nufi apartment din, tsayawa tayi bakin kofa ta danna bell, lkci daya aka bude kofar, sai da gaban Khaleesat ya fadi ganin Surayya ce ta bude mata kofa, ta sauke idonta tace “Ina yini?” A takaice Surayya tace “Wa kike nema?” Khaleesat ta daga kai ta kalleta tace “Wajen Safiyyah na zo” Bluntly Surayya tace “To bata nan, sai ki juya ki koma inda kika fito” Khaleesat was just looking at her babu ko kiftawa, sai ga Safiyyah ta fito daga daki fuuu, tana huci tace “Wajenta kika zo da zaki tsaya sauraronta baki bangajeta ba kinyi shigowarki?” Khaleesat ta bude baki tana kallon Safiyyah, wato ta bangaje matar gida ta shigo tsabar neman jifa’i, Surayya ta juya a fusace tana kallon Safiyyah tace “Tunda gidan na ubanta ne ko naki uban sai ta shigo mu ga” Safiyyah tayi cilli da wayar hannunta ta fige dankwalin kanta tace “Wallahi kar ki ga na raga maki daxu saboda yaya, to yanzu baya nan cin kaza kazanki zanyi la’ada waje” Khaleesat was shock, ta kasa rufe baki tana kallonsu, Surayya ta nufi Safiyyah tana kunduma mata zagi kamar dai yanda tayi mata few hours ago a gaban cousin brother dinta, instead sai cousin din ya dinga ba Safiyyah hakuri without taking any action, dama Safiyyah a wuya take, sbda bakin ciki ne ma yasa ta dinga kiran Khaleesat ta zo gidan, Khaleesat ta zaro ido ganin yanda Safiyyah ta finciko Surayya cikin zafin nama, ba ayi wata wata ba suka fara tikar dambe a wajen, Khaleesat ta karasa ciki da sauri tace “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, meye haka kuke yi Safiyyah? Don Allah ku bari” Yaron Surayya dake kan kujera sai tsala ihu yake, Khaleesat tayi kokarin rabasu taga an cillar da ita gefe har sai da ta kusa faduwa, bata sake gigin zuwa kusa da su ba, ta bude wayarta da sauri ta fara neman number Mustapha, tana kokarin kiransa taga Surayya na harin fixgo wani flower vase zata buga ma Safiyyah a kai, hakan yasa Khaleesat ta tafi da sauri ta dauke Vase din daga inda yake, Safiyyah tayi using opportunity din ta fixge vase din a hannun Khaleesat ta maka ma Surayya a goshi, sai ga jini kuma hakan bai sa sun fasa damben da suke ba, ko da Khaleesat ta kira Mustapha ashe yana hanyar dawowa, cikin few minutes sai gashi ya shigo gidan, sai shi ne ya rabasu bayan sun yi ma juna laga laga, Surayya bata daddara ba tayi kukan kura tayo kan Khaleesat zata cafkota tana cewa “Kika bata Vase ta buga min, wallahi kema sai na ci kaza kazan ki” A nan ne Mustapha ya sauke mata mari ya fincikota yace “Ko kin fara hauka ne Surayya? Me kike son mayar da ni a kasar nan ne?” Ita dai Khaleesat ta tsorata sosai, Safiyyah na huci tace “Shegiya bayerabiyar banza kawai jaka jahila…” Bata rufe baki ba ita ma Mustapha ya kai hannu zai gaura mata mari ta kauce da sauri tana harare harare tana huci, Surayya dake kuka wiwi ta figi ɗan ta zuwa sama tana cewa “Wallahi sai dai ka zaba ko ni ko Safiyyah a gidan nan yau, in ko ba haka ba ni zan bar maku gidan kayi zaman auren da ita” Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya ko ba komai dai ta fasa mata kai hankalinta ya kwanta ta kuma ji dadi, Mustapha ya zauna saman kujera ya dafe kai, juyawa Khaleesat tayi sum sum ta fita daga parlon wishing dama bata zo gidan ba kilan da haka bai faru ba, da tasan bala’in da za ayi kenan babu abinda zai fara fitowa da ita daga gida, Safiyyah ta figi dankwalinta zata bi ta, Mustapha ya mata tsawa yace “Kar ki kuskura ki fita daga gidan nan” Safiyyah ta fashe da kuka tana bubbuga kafa tace “Ni wallahi yaya na gaji, na gaji kuma haka, na gajiiii, dubi cin mutuncin da matarka ta min daxu kace in kyaleta, yanzu kuma daga kawata ta zo wajena in mata kitso shikenan sai ta fara kunduma mana zagi ta kamani da dambe??” Yace “Wuce dakin ki nace” Ita dai Khaleesat tuni ta kara gaba ta bar gidan. That same day wajen karfe biyar da rabi sai ga Safiyyah ta zo gidan Khaleesat, Khaleesat ta zauna gefenta bayan sun shigo parlor tana kallonta tace “Ban ji dadin abinda ya faru ba yau Sophie, da na sani da ban je gidan ba ma wallahi” Safiyyah tace “Ai abun duniya ne ya dameni kamar in hadiye zuciya shi sa nayi ta kiranki ki zo daxu, wai fa bayan na gama yi maki gyaran gashi na koma gida matar nan kamar jirana take ta kama zagina ta uwa ta uba a gaban mijinta wai don me zan zubar mata da sauran miyarta dake kitchen, kuma fa kar kice da miya a tukunyar Khaleesat, wallahi ba komai ciki sai wani guntun miya da yayi tsami sai bugawa yake, ni kuma na wanke na dafa indomie na ci kafin in taho nan daxu in maki gyaran gashi, Ya Mustapha ya hanani cewa komai ya bani hakuri na wuce daki, a banza tunda dai shi ma har uwayensa ta zaga, shine bata daddara ba da kika zo zata sake hadamu ta zage ga yan iska sai muyi shiru muna kallonta, ni wallahi so nayi ace ma na cire mata hakora biyu ta dawo wawulo, amma dai a juri zuwa rafi wallahi sai na mata illar gaske kafin in gama karatu a kasar nan, dama tun 3 weeks ago da muka zo muka kawo maki abinci da ni da Y Mustapha ta kara kullatata ta kara tsanata tunda har yau tayi tunanin da akwai wani abu tsakaninki da Mustapha, ko ga maciji fa bama yi da ita a gidan” Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya ta kamo hannunta tace “Ki dai dinga hakuri plss Sophie wataran sai labari, da ni ce ke ma wallahi bazan dinga biyeta ba a gidan nan” Safiyyah tace “To ai ba kowa ke da matattciyar zuciyar da kare ya lashe irin taki ba, amma wallahi tayi kadan in ki biye mata, tana ce min kule zan ce mata casss don ubanta, an gaya mata ita ta isa ta shiga tsakanina da Mustapha? Cousin dina ne fa, Uwarsa ce ta sha nono ta bar ma uwata, Babansa kuwa Cousin din babana ne halaq malaq, ina ga bai taɓa zaunar da ita ya mata bayanin nan dalla dalla bane, kuma ya ci sa’ar bana kai karar abinda matsiyaciyar matarsa ke yi min gida, don wallahi da tuni an dau mataki, amma dai bari mu yi hutu in koma Nigeria” Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya tace “Zancen gaskiya ke ma fa kina da naki Safiyyah, babu ta yanda za ayi kina zaune da mata ko ɗan wanke wanken nan da shara baza ki ke taya ta ba a gidan, Abinda fa idan an mana mun san baza mu ji dadi ba to kar mu yi ma wani, she is also human, kuma at times bacin rai ne ke triggering wani mugun halin mutum, kece kika yi triggering din halinta a gidan, babu ta yanda zaki ji dadi wataran kanwar mijinki ta zo gidanki ta zauna bata taya ki aikin komai sai dai in kinyi girki ta deba ta ci ta ajiye maki plate, ki duba wannan lamarin fa, mu mata muna da son kanmu wani lkcn…” Safiyyah ta dakatar da ita tace “Ohh wato goyon bayanta ma kike kenan Khaleesah? you are trying to say duk abinda take min yayi dai dai ko?? To nagode, dama ke baki taɓa goyon bayan mutum a duk halin da yake ciki, in dai mutum zai kawo maki damuwarsa to ya kara dulmiya kansa cikin damuwa ne, ni kuma ban taɓa kin supporting dinki ba no matter the situation, ko Abdul da nake zagi kullum kamar ɗa na nake goyon bayanki an gaya maki kema baki da naki baƙin halin ne wani lkci? Dama mistake nayi ma na zo gidan nan asirina a rufe da gidan Sandra na wuce da ba a kara bata min rai ba” Tana fadin haka ta mike ta figi jakarta ta nufi kofa kamar zata tashi sama, Khaleesat ta mike tace “Safiyyah” Banza da ita Safiyyah tayi har ta fice daga parlon ta kullo mata kofa, Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya ta koma ta zauna, a hankali tace “Ae shikenan”07087865788✍🏻

Back to top button