Hausa novels

Asanadin Makwabtaka Book 2 Page 4 Complete Novel

*ASM Bk2004*

 

_Destiny may be delayed but cannot be changed…._

 

 

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

 

 

 

Koda suka je zama sukayi a parlor suna kallo suna fira sai dae Fatuu bata wani saki jiki sosae ba sama sama take Magana ganin yanayinta yasa Hajiya tace taje d’akinta ta kwanta Fanan ta kama hannunta suka tafi, kwantawa tayi saman gadon Hajiyar Fanan kuma ta wuce Toilet don tayi wanka lokacin data fito har bacci ya kwashe Fatuu itama kayan shan iska tasa ta kwanta gefenta tana son ta kira Haisam don taga missed call d’inshi lokacin data fito daga toilet amman sai kawae ta daure ta kyaleshi wai don yasan tayi fushi, tana ta latsa wayarta har bacci itama ya kwasheta, sai da akayi la’asar Hajiya ta shigo yin salla ta tashesu suma suyi sallar, da daddare bayan isha suna zaune a falo Fatuu duk ta k’agara ta koma gida don bata son Haisam ya dawo tana gidan, har cewa tayi zata tafi Hajiya tace ta bari in Dijen ta dawo ai zata kira ita kuma Fanan cewa tayi ta kwana anan kawae mana ita dae murmushin yak’e kawae tayi, suna zaunen Haisam ya shigo da sallama duk suka d’aga kai suka kalleshi Hajiya ta amsa mashi yayin da k’irjin Fatuu yay mata wani irin bugu tana yin arba da fuskarshi sai dae kuma ta kasa daina kallonshi wani irin fresh taga yayi mata, nufosu yay Fanan ta kauda kanta yana ganin haka yaja ya tsaya Hajiya dake kallonsu na masu Murmushi don tasan yadda sukai da Fanan d’in da safe, juyawa yay zai koma da sauri Hajiya tace “ka rufa man asiri ban shirya yin jinya ba daga kawo man ziyara” ita kuwa Fanan d’in mik’ewa tayi da sauri sauri gudu gudu ta nufeshi tana zuwa ta fad’a bayanshi ta k’ank’ameshi ta yadda bazai iya cigaba da tafiya ba, ruk’e hannuwanta yay ya juyo yana kallonta ta zo6ara baki ya kai hannu ya d’an ja lips d’inta ta saki yar k’ara sai lokacin yay Murmushi ya kama hannunta suka nufo cikin falon, wani irin abu Fatuu taji ya tokare mata k’irji nan da nan zuciyarta ta karye taji kwalla na niyyar zubo mata da sauri ta juyar da kanta ta kalli tv, gefen Fatuu inda ta taso ya kaita ta zauna shi kuma ya zauna saman hannun Sofa har lokacin suna ruk’e da hannun juna kallon Hajiya yay ya gaidata ta amsa tana Murmushi a hankali ya juya ya kalli Fatuu daidai itama ta juyo saida ta had’iye wani abu mai d’aci kafin da k’yar ta iya gaidashi ya amsa yay mata ya jiki tace da sauki, maida kallon yay kan Fanan yace ta gama fushin Hajiya tace “to ai ni bansan wane ma irin fushi ne wannan ba” turo baki Fanan tay ta kwantar da kanta gefen jikinshi tace ita dama ba fushi tayi dashi ba ai, Hajiya tace to kanta dai ta k’aryata ba ita ba duk suka yi dariya, janyeta yay ya mik’e yace zaije yay wanka baiwar Allah Fatuu daurewa kawae take ita kadae tasan abunda take ji yanzu ta tabbatar ma kanta ba k’aramin son juna suke ba, kasa jure zaman tayi ta mik’e tace zata je gida tasan yanzu gwaggo ta dawo Hajiya tace ta lura dae gidan take son tafiya to ta bari taci abinci Fanan ma tace ta bari in sunci dinner sai su rakata ita da Babe Hajiya tace lokacin ma tasan dijen ta dawo, kasa yi ma su musu tay ta koma ta zauna bada jimawa sosae ba Haisam ya shigo ya shirya cikin jallabiya dark ash mai gajeren hannu yana shigowa Fanan ta mik’e ta kama hannun Fatuu tace mashi suje table Zarah nason tafiya gida jinjina kai yay suka nufi dining area da tun bayan gama sallar isha Saude ta shirya komae, kaman yadda suka saba haka suke cin abincin baiwar Allah Fatuu daurewa kawae take idonta akan abincin gabanta da Fanan ta zuba mata ji take kaman ta rushe da kuka, bata wani ci da yawa ba sai faman jujjuya cokali take can ta mik’e tace ta k’oshi fanan tace ta daure ta k’ara bata ci sosae ba tace amai take ji ne hakan yasa Hajiya tace ta k’yaleta fanan d’in tace to ta jirasu a falo su gama ta d’aga mata kai kawae, a tare suka rakota suna ta hirarsu irin ta masoya har wani d’an fad’a mashi a jiki take, lokacin da suka k’araso kopar gidan su biyu suka shiga shi ya tsaya a waje zai jirata, gwaggo bata dad’e da shiga gidan ba suka shigo fanan na dariya tace ta maido yar ajiya tak’i ta kwanan mata itama gwaggon dariya take tay mata godiya sosae ta tafi, kallon Fatuu dake zaune kan kujera tayi tace mata ya jikin ta amsa mata da sauki ta mik’e zata wuce d’akinta gwaggon tace ta tsaya ta zubo mata Abinci sai taje ta kwanta tace taci acan daga haka ta wuce d’akinta tana shiga ta nufi gado ta fada samanshi tayi rubda ciki sai lokacin kukan da take ta rik’ewa ya samu zubowa,wani irin son Ya Handsome take ji acikin ranta bata da buri yanzu sai na auranshi to amman ta yaya shi da baisan ma tana yi ba gashi yanzu tabbas ta gasgata Maganar Haulat na ba k’aramin son juna suke ba shida Fanan, sak’e sak’e taci gaba da yi tana neman mafita har gwaggo ta lek’o ganinta haka yasa tayi tunanin tayi bacci ne shiga tayi cikin d’akin tay mata Addu’oi duk fatun na jinta bayan ta gama ta gyara mata kwanciya lokacin da zata fita daga d’akin ta kashe mata hasken wuta kafin ta fita.

 

Tun daga wannan ranar Fatuu bata k’ara yadda wani abu ya kaita gidan Hajiya ba don ta fahimci in taga Haisam k’ara shiga mawuyacin hali take, k’iri k’iri ta hakura da ganinshin abunda bata ta6a tunani ba a rayuwarta wato guje ma ganin Ya Handsome d’inta mutumin da ko tafiya yay a k’agare take daya dawo don duk sai tajita ba daidai ba in bai nan, duk abunnan ba wanda ya fahimci halin da take ciki su a tunaninsu lalurar da suke zato ke damunta ita gwaggo bata ma san cewa Fatun bata san da Maganar baikon dake tsakaninsu ba sanin irin shak’uwar dake tsakaninta dasu duka bama kamar Haisam, itama kuma Fanan bata san Fatun bata sani ba, Ranar Asabar ya kama kwanan Fanan shidda da zuwa Fatuu na cikin d’akinta don yanzu ta d’aura aure da zaman d’aki ba kaman in gwaggo bata nan in tana nan ne wani lokacin inta matsa mata take zuwa Parlor ta kunna tv saidae sunan tana yin kallonne amman hankalinta na wani wuri tunane tunane sun zamar mata jiki duk tazama wata so silent Magana saita kama take yi, shigowa gwaggo tayi da sallama ta d’aga kai ta kalleta kafin a hankali ta amsa mata ta nufi gefen gadon ta zauna fatun ta yunk’ura ta mik’e zaune,

“Sannu ya karfin jikin?” amsa mata tayi da sauki, tace “Yanzu ya kike jin jikinne ina yafi damunki?” shiru ta d’anyi idonta akanta kafin a hankali tace “ba ko ina” itama gwaggon shiru tay kaman mai nazarinta hakan yasa Fatun duk’ar da kanta tana wasa da yatsunta,

“In ba abunda ke damunki yanzu miyasa kika k’i sakin jikin ki kaman da?” da yar damuwa tay Maganar, damm gabanta ya d’an fad’i ta d’ago idanunta har sun canja kala a sanyaye tace “kawae banjin dad’in jikinne kaman ba nawa ba” jinjina kai gwaggon tayi tace “a hankali zaki warware amman wannan k’umshewar da kike cikin d’aki hada shi ke k’ara maki rashin dad’in jikin, ki daure ki rink’a sakin jikin kina fitowa” kai ta d’aga mata tace Allah ya bata Lafiya daga haka ta mik’e zata fita sai kuma ta tsaya ta juyo tace “ko gidan Hajiya ki daure ki rink’a zuwa kinga yarinyar nan Fanan kullum sai tazo dubaki duk ta damu da halin da kike ciki in taga kinje zata ji dad’i, da zaki iya ma kiyi d’an wani abu ki kai mata nasan zata ji dad’i sosae taga kema kin damu da ita kaman yadda ta damu dake” wani irin fad’uwa gabanta yay hakanan ita bata tsani Fanan ba amman data ji muryarta ko anyi Maganarta sai gabanta ya fad’i ganin gwaggon ta kafeta da ido ne yasa tace to mi zata yi mata, tace “yauwa to ko wainar fulawa ce akwae komae na yi kije waje wurin Amadu sai ki amso kwai nasan ba k’aramin dad’inta zata ji ba tunda ita ba ruwanta komae ci take” ta k’arasa Maganar tana nufar kopa, zaune tayi tay shiru bayan gwaggon ta fita, ba wai wainar ke bata son yi mata ba kawae ita gidan Hajiyar ne bata son zuwa don karshenta zata tado ma kanta wata matsalar ne can dai ta saukko daga kan gadon ta fita, ba tare da 6ata lokaci ba gwaggo ta taimaka mata wurin had’a k’ullun wainar ta yi shi mai d’an yawa yadda suma zasu ci, suya Fatuu ta fara cikin Kitchen gwaggo kuma ta yanka mata cabbage da sauran kayan ci, bayan ta soya mai d’an yawa gwaggo tace tay sauri ta shirya ta kaimata ita bari taci gaba da yin suyar, wanka taje tayo har ta wuce kitchen gwaggo ta kirata tazo bakin kitchen d’in ta tsaya tace “nace ko ki saka kayan data kawo maki dinnan suna nan na saka maki acikin kayanki” kai kawae ta d’aga mata ta wuce, kayan na nan yadda suke cikin leda tunda ta kawo su Fatun bata ta6a su ba, d’aukar ledar tayi ta koma bakin gado ta zazzagesu ta fara d’agasu tana dubawa, sari kala ukku ne riga da wando da mayafinsu rigar iya gwuiwa ce sai kuma doguwar riga har k’asa itama kuma tana da wando da mayafi kayan sun matukar had’uwa daka kallesu zaka gane ainihin na india ne sun mata kyau saidae yanayin da take ciki yasa ta kasa yin murnar kayan dama kwanaki can baya Haisam ya ta6a kawo mata irinsu kala biyu da yaje Lagos yace Fanan tace a bata sai yanzu ta fahimci dalilin dayasa yake yawan zuwa Lagos wani lokacin harda wurin Fanan yake zuwa in tazo,wasu sky blue ta d’auka zata sa ta mayar da sauran cikin ledar,bayan ta gama shiryawa tsaye tay gaban mirror tana kallon kanta kayan sunyi mata kyau sosae sai salki stones din jiki ke saki ba don yanayin da kayan suka risketa aciki ba da ba abunda zai hana har rawar india tayi,jiki a sanyaye ta yafa mayafin kayan ta nufi kicin bayan ta sanya takalma masu d’an tudu don bata saka flat shoes shiyasa ma bata dasu sai yan na sawa a tsakar gida, lokacin data je kicin d’in gwaggo har ta had’a wadda zata kaimata tana ganinta ta washe bakin jin dad’in ganin yan matanta yau ta fito tsaf da ita duk da ba wata kwalliya tayi ba iya mai kawai ta shafa sai kayan data sa sosae ta shiga yabon kayan tana sunyi mata kyau sosae ita dae shiru tay tana bin ta da ido, d’aukko mata kwanon dinner set mai d’an girma dake a rufe gefe tay tace gashi nan ta kaimata.

 

Kasancewar Weekend ne gaba d’ayansu suna zaune a falo duk kaya ba masu nauyi bane a jikinsu Haisam da Fanan na kan 3 seater ya jingina a k’arshen kujerar Fanan kuma na kwance ta d’aura kanta kan kafafunshi Hajiya na akan 2 seater gaba d’aya idanunsu na akan tv suna kallon wani Indian film a Bollywood Fanan d’ince ke fassara masu abunda ake cewa don ta iya indiyanci sosae Musamman akwae lokacin da suka ware suna koyonshi acan, da yar sallama ta shigo Falon saidai ba wanda ya jita hakan yasa ta tsaya idonta akan Haisam wani abu take ji na bin jikinta ga zuciyarta dake bugawa da sauri da sauri ta kasa d’aga kafarta ta idasa shiga ciki kaman ji yay idanu na yawo a kansa hakan yasa ya d’an juyo suka had’a ido da ita shima kallon ya bita dashi from head to toe kafin ya tsaida idon cikin nata suna kallon juna can taji cikin cool voice dinshi yace “Zaraah ki shigo mana” Maganar da yay ce tasa duk suka juya suka kalli entrance d’in koda Fanan tayi arba da Fatuu tsaye da sauri ta yunk’ura ta mik’e ta nufeta ganin haka yasa Fatun nufo cikin falon suka had’e gaba d’aya ita da kwanon da take ruk’e dashi ta had’asu ta rungume tana Fad’in “am so so Happy Sis Zarah kin samu Lafiya sosae” d’agowa tay ta amshi abunda ke hannunta ta rungume a hannunta guda d’ayan kuma ta kama hannunta suka nufi ciki, a Sofa d’in da suke zaune ta zaunar da ita can d’ayan gefen ita kuma ta zauna tsakiya ta aje kwanon k’asa gabanta,

“Hajiya Ina kwana” ta fad’a a sanyaye hajiya dake kallonsu tana Murmushi tace “Lafiya lou Fateema kin yi kyau sosae, ya k’arfin jikin?” da sauki ta amsa mata kafin ta juya ta gaida Haisam da shima kallonsu yake ya amsa fuska a sake yay mata ya jiki shima tace mashi da sauk’i,maido idon tay kan Fanan da ta d’aura hannunta guda kan k’afafunta tana ta sakar mata Murmushi, itama gaidata tayi ta amsa tace mata tayi kyau sosae godiya Fatun tayi mata ta kayan tace basai tayi wannan ba takai hannu ta zame gyalen kanta ganin yadda gashin yake ba gyara tace mata tasan saboda bata lafiya ne bata gyara ba yanzu tunda ta samu sauk’i yakamata a gyara zatafi jin dad’inshi ita dai jinjina mata kai kawae take,

“To ke an kawo man abu kin tasa a gaba ki mik’o man in ga mi na samu haka” Hajiya dake kallon fanan ta fad’a aikuwa a hak’ik’ance tace “ba naki ne ba nawa ne” yar dariya hajiya tayi tace “hak’ilo, yanzu yaushe kika ji ance naki ne” kallon Fatuu tayi tace ita ta kawo mawa ko kallon hajiya Fatuu tay data kafeta da ido kaman zatayi murmushi ta sunkuyar da kanta ta d’aga ma Fanan d’in, yar k’ara tasa tace to gashi nan Sis Zarah tace nata ne, ruk’e ha6a Hajiya tayi tace “Wato dae Fateema an rabamu ko, ada Ya Handsome ya shiga tsakaninmu yanzu kuma ga wannan acicin ai shikenan zasu barni dake ne” yammm taji jikinta yayi jin Maganar Hajiya ta zasu barta da ita dama k’arfin hali kawae take zama a gurin, d’aukar kwanon Fanan tayi ta bud’e kamshin wainar ya daki hancinta har saida ta d’an lumshe ido sai dai bata gane minene ba hakan yasa ta juya ta tambayi Fatuu sunanta tace mata wainar fulawa,

“Wasu kuma suna ce mata kalalla6a wasu suce waina gira ko alallagira wasu ma yar cana suke cewa” suka ji Hajiya ta fad’a, bud’a ido Fanan tayi jin wasu sunaye ta fara k’okarin maimaitawa tace “K…kal…kallalla6iya…” tunkan ta rufe baki suka sa dariya gaba d’ayansu ita dae Fatuu d’an Murmushi kawai tay Hajiya tace “Da alama dai za’a maimaita na taliyan hausa” da sauri Fatuu ta juya ta kalli Haisam suka had’a ido ya saki Murmushin gefe tunowa da ranar data kawo mashi taliyan hausa mai daddawa sanin Murmushin kona miye yasa itama tayi kafin ta juyar da kan,

“Idan baki ci ki mik’o man nan k’amshinta duk ya cika man hanci” hajiya ta Fad’a idonta kan Fanan, da sauri ta girgiza kai tace ai ko bata ci sai taci abunda Sis Zarah ta kawo mata, d’aukar kwanon tay ta nufi dining Hajiya tace bata ci anan tace zata d’aukko fork ne,

 

“Shine sai kin tafi da ita wato kar ki barma kura ko” d’an d’aga murya tay tace eh cinye mata abunta zatayi, ta sake cewa to wayace mata da fork ake ci hannu ake sawa bazata ji dad’in cinta da fork ba jin hakan yasa ta wuce dining area ta wanko hannunta ta dawo, daga inda Hajiya take ta fara nuna mata yadda zata ci ta nade d’aya da kayan cin acikinta ta dangwala yajin kamar yadda hajiya tace ta tura baki ta fara taunawa, d’an bud’e ido tay lokacin da ta cinye ta yarfa yatsa tace “it’s so yummy” dariya hajiya tayi ta juya ta kai sauran ta hannunta bakin Haisam ya kalli abunda take bashin kaman bazai bud’e bakin ba sai kuma ya bud’e ta saka mashi ya gatsa ta janye sauran ta tura baki hajiya dake kallonsu tace “Fateema dai duk ta koya maku kwad’ayi, shima kwanaki a waya naga wainar fulawar ta burgeni nasa Saude tayi mana ita da rana ina tunanin shi ayi mashi wani abun yaci sai ce man yayi wai zai cita nayi mamaki don nasan ba lalle in ya ta6a ganinta ba balle ma ya iya cin dana tambayeshi dama yasanta ne yake ce man ai da Salla da ban dawo bane ta kawo mashi ita nan ya fara cinta” dariya Fanan keyi tana taunar wainar ita kuwa fatuu a hankali ta d’ago ta kalli Haisam da d’an Murmushi suka sake had’a idon gaba d’ayansu Maganar Hajiya ta tuno masu da can baya sallar farko data fara yi dashi lokacin daya dawo ta rink’a kawo mashi abinci har ya rink’a yi mata lesson lokacin ya koyi cin wainar don farko data kawo mashi cewa yay bai iya cinshi ba saida yaga kaman bata ji dadi ba har zata tafi yace ta kawo yaci tace mashi ita ba fushi tayi ba tunda bai iya ci ba bari taje zata kawo mashi wani Abincin amman yace karta damu zai ci don ta gaya mashi musamman don shi ta soya dama kuma saida gwaggo tace mata ba lalle fa in ya iya cin ta ba wannan dalilin ne yasa ya daure yaci amman kuma sai yaji dadinta musamman data kasance ba abinci ce mai nauyi ba tun daga nan duk in ta kawo mashi yana ci, janye idonta tayi ta maida kan tv kaman tana kallo saidae a can k’asan zuciyarta wani iri take ji tunawa da rayuwarsu ta baya rayuwa mai cike da nishad’i daidai da rana d’aya bata ta6a tunanin komae zai sauya haka ba tsakaninta dashi,

 

“To sarakan son kai sai ci kuke kun barni da shak’ar kamshi da alama cinyewa zakuyi ma ba tare da kun bani ba ko” Hajiya tayi Maganar idonta akan su Fanan dake dariyar Maganar Hajiyar tana niyyar ba Haisam wadda ta gutsira ya girgiza mata kai yace ta kai mata cike da tsokana ta mak’e kafad’a alamar bazata bata ba Fatuu data juyo ta kalleta tunda hajiya tayi masu magana ganin abunda tayi yasa ta mik’e idonta akan Hajiyar tace bari taje tayo mata wata, da sauri Fanan ta kamo hannunta tace wasa take zata bata ba sai ta k’ara wahalar da kanta ba ta mik’e ta tunkari Hajiyar ta aje kwanon gefenta itama ta zauna tace to gashi nan su ci yar harararta tayi tace ita da bata da masoyi ko to itama a bakin zata bata tasa dariya tace wannan ai ba matsala bane ta d’aukko ta fara bata itama tana cigaba da ci, daga inda take bayan ta cinye wainar bakinta tace ma Haisam “Babe we need to go 4 an outing sis Zarah zata k’ara jin dad’in jikinta” tana rufe baki Hajiya tace “ba dai Ajiwa Dam d’in zaku je ba?” yadda tayi Maganar har saida taba Fanan dariya ta girgiza mata kai alamar a’a, tace “ato ai naji kina ce mashi ne kina son zuwa wurin da kika ga hotunansu nayi zaton can kike nufin kuje ince to kuje ku kad’ai banda ita a samu ma ta idasa dawowa daidai” sunkuyar da kai Fatuu tayi cikin ranta ta ayyana koda ma ance za’a can d’in ba zuwa zatay ba don yanzu Ajiwa Dam na d’aya daga cikin Wuraren da bata fatan k’ara zuwa fit ya fice mata arai ya kuma shiga cikin tarihin rayuwarta ko hotunan datayi a wurin bata son gani, tana son ta tafi gida amman tasan sai gwaggo tayi Maganar dawowarta da wuri gashi bata son taga tana sa gwaggon damuwa, kiran sallar Azahar ta tadasu gaba d’aya suka tafi yin salla bayan sun gama ne kuma Saude ta sanar ta shirya Table lokacin da Haisam ya dawo gaba d’aya suka nufi Dining din harda Fatuu da suka matsa mawa duk da tace masu ta koshi taci waina amman Fanan tace taci ko kadanne ai suma sunci wainar ba yadda ta iya, ita ta fara tashi tace ta koshi don ba k’aramin karfin halin zama take tana kallon yadda suke ciyar da junansu ba Fanan tace ta jirata a parlor inta gama zata gyara mata gashinta ta amsa mata da to kawae, bayan sun gaman visitor room ta kai Fatun taje dakin Hajiya ta daukko wani dan babban kit ta dawo lokacin data bud’e ba komai ne aciki ba sai uban kayan gyaran gashi da mayuka, nuna ma Fatuu dake zaune gefen gado stool din gaban mirror tayi tace tazo ta zauna, bayan ta zauna ta fiddo stretcher ta fara mata stretching sosae take yaba kyaun gashin Fatuu da yake cike gashi baki wuluk duk da na Fanan d’in yafi shi tsawo saidae baida cika, sosae ta gyara mata shi sai shek’i yake ta d’aukko wayarta ta fara masu hotuna ta rink’a masu styles da gashin kansu iri iri, dole Fatuu ta saki ta rink’a yin yadda duk tace mata tayi sosae hotunan su kai kyau ba kamar daya kasance ita gashinta brown na Fatuu bak’i bayan sun gama yin hotunan ta maida komae cikin kit ta maidashi Bedroom din Hajiya ta iske hajiyar kwance tana bacci hakan yasa data dawo tace ma Fatuu su kwanta suma su huta ba kowa a Parlor tace mata to kawae, zuciya nason mai kyautata mata duk da halin da Fatuu take ciki sam ta kasa jin tsanar Fanan din hakanne ma yasa wani lokacin bata iya yi mata gardama, har aka kira la’asar suna bacci ringing d’in wayar Fanan ne ya tasheta ta duba screen din taga Haisam ne ke kira bayan ta dauka ya tambayeta tana ina ne ya shigo har Bedroom bai ganta ba ta fadi mashi suna bacci ne a visitor room yace su tashi suyi salla ta shirya tace to don ta gane shirin zuwa gym yake nufi, tashi tay ta koma Bedroom d’in Hajiya within few minutes tayo wanka ta fito,shiryawa tayi cikin workout outfit riga da wandonta Ash colour rigar tight long sleeve ce irin mai dogon hannu ta kamata sannan iyakarta tsakiyar cikinta sai wandon shima skin tight ne dogone ya kai har kasan rigar sun matukar fiddo mata da dirinta kuma tayi kyau sosae hijjabai guda biyu ta d’auka ta koma d’akin da Fatuu take har lokacin bacci take dama tana fama da karancin baccin yan kwanakin nan, tashinta tay ta bud’e ido tana kallonta da Murmushi tace mata ta tashi lokacin salla yayi ta d’aga mata kai kawae ta saukko, lokacin data fito Fanan din ta kabbara salla don tayi Alwala a toilet hijab din data gani ajiye ta d’auka tasa itama ta kabbara sallar, bayan ta gama saida ta jira Fatuu ta gama sannan ta sanar da ita zasu tafi Gym ne ko zata k’ara kwanciya tace mata a’a gida zata tafi hakan yasa suka fito tare Fanan ta shiga d’akin Hajiya ta maida hijjaban tasa takalma sneakers farare ta d’aura farar jacket kanta kuma ta rufe shi da veil Ash kalan kayan tayi kyau har ta gaji, sallama tayi ma Hajiya tace adawo lafiya ta fito lokacin Fatuu na zaune kan kujera a Parlor tana ganin ta fito ta mik’e ta nufeta suka fita tare suna fitowa cikin harabar gidan Haisam ma ya fito cikin shirin gym hannunshi guda rataye da katuwar jakarshi abunda Fatuu ke ji duk ta ganshi shi taji gashi ta kasa barin kallonshi har ya k’araso inda suke Fuskarshi a sake yana kallonta Fanan ta kai hannu ta curo jakar ta rataya shi kuma ya nufi Parking Space don ya fiddo bike din lokacin Fatuu tace ma Fanan ta tafi gida ta dafa Shoulder d’inta tace in ta dawo zata zo kai kawae ta d’aga mata ta nufi hanyar gate, tana karya kwana bayan ta fito gate d’in gidan bike d’insu ya taho taja gefe don su wuce, dukkansu sun sa helmet a kawunansu Fanan na goye da katuwar jakar suna zuwa inda take Fanan ta d’ago mata hannu suka wuce fuuu,tsaye tayi a wurin tana bin su da kallo har suka yi nisa kafin suka 6ace ma ganinta, kasa d’aga kafafunta tay taci gaba da tafiya, da k’yar ta matsa ta jingina da fence a cikin zuciyarta ta ke ayyana Ya Handsome baisonta bai ta6a sonta ba yanzu ne ta k’ara gaskata hakan don ta gano dalilin dayasa bai ta6a goyata a bike d’inshi ba tunda suke, duk in ta nuna tana son su hau shi in zasu fita sai yace Mota zasu hau ko kuma in yaga kaman bata ji dad’i ba yace ba yanzu ba ashe duk don kar jikinsu ya had’u ne sai yanzu ta fahimci hakan ganin da suka wuce gaba d’aya Fanan na kwance a bayanshi ta sakala hannuwanta a cikinshi, wani 6angare ne na zuciyarta yace kawae ki cireshi a ranki tunda baison ki yayin da wata zuciyar kuma tace yanzu shikenan sai ki hakura dashi duk irin son da kike mashi ina kike tunanin zaki samu wani kamarshi, wasu kwalla ne masu zafi suka fara gangaro mata ta shiga yin kuka ba tare da sauti ba don ta rufe bakinta da tafin hannunta guda,can bayan wani lokaci tasa hannu ta fara gogewa kafin da k’yar ta d’aga k’afafunta da suka yi mata wani irin nauyi ta fara tafiya, tana karasowa kopar gidansu har zatai kwana sai kuma ta tsaya kaman mai yin tunani can ta mik’i hanya taci gaba da tafiya…………..

.

Asanadin Makwabtaka Book 2 Complete Novel Txt

Back to top button