Hausa novels

Zakuna Biyar Page 47 By Princess Teema

A harabar benen nasu suka tsaya, key ɗin wata dalleliyar mota Lion ya fitar daga aljihun coat ɗinsa. Miƙawa guru key ɗin ya yi, dikkansu da kallo suka bisa suna mamakin ganin yau da motarsa na ainahi zasu fita.Wannan mota dad da kansa ya saya masu su huɗun iri ɗaya, to tin bayan rasuwar dad ɗin suka rufe motocin, dik wani abin da zai sanya a gane suna da alaƙa da Haiza’an sai da uncle yasa suka ajiyesa, dalilin kenan da yasa basa fitowa da Hero, domin kowa ya ga wannan zaki sai ya gane zakin Haiza’an ne, dan wannan zaki ya shiga tarin dad dama duniya bakiɗaya, kuma a jikin Zakin a gaban goshinsa akwai rubutun sunan dad da aka yi mashi da wuta, shiyasa kowa ya gansa zai gane na dad ɗin ne, shiyasa ko waje basa leƙowa da shi, yana gida.Sun yi mamakin ganin zasu fita da wannan mota, motocin nasu dik plate numbersu sunan Haiza’ans family ne a jikinsa, shiyasa suka jinginesu. Tin da suka ga Lion zai fita da wannan mota suka fahimci ya shirya fito na fito da duniya bakiɗaya kenan, lallai kuwa akwai kura, uncle da duniya ta ɗauke ya mutu yana ƙoƙarin tada tarzoma kenan, zai sanya IRON FIST su bayyana a duniya, zasu jingine aikin SSO kenan ko yaya? Ya Aryan zai yi da Seraphina da ta tsani IRON FIST? Me Khaiza’ans family zasu ce? Abba zai yarda da cewa Aryan shi ne Champion na IRON FIST?.Fito da motar guru ya yi, Lion ya shiga gidan gaba, Aryan da Vir suka shiga gidan baya. Kai tsaye HEART OF CRYSTAL PALACE suka nufa. Tin daga kan securitys dake tsaron CRYSTAL PALACE har izuwa kan jama’ar dake ciki sai da suka zubawa motar nan ido, musamman suna Haiza’an dake gaban motar. Mota na farko kenan da dad ya fara sayawa ƴan matasansa a lokacin.Da yake gate ɗin gidan dad automatic ce, suna isa gate ɗin ta yi scanning motar, ganin babu abin haɗari a ciki yasa gate ɗin ta wangale masu kanta. Ciki suka kutsa, kai tsaye suka nufi marking lot, bayan sun paka motar kusan a yare suka fito. Cikin main parlo suka nufa, a jere suke sanya kafafunsu a ƙasa suna ɗaukewa. Suna shiga main parlo suka rabu, kowannensu ya yi nasa hanyar. Kai tsaye cikin ɗakin dad ɗinsu Lion ya nufa, tin da dad ya rasu Lion bai taɓa shiga wani ɗaki a gidan ba face na daddyn nasu, ɗakin mom ɗinsu yana nan yadda ta barshi, bai taɓa shiga ba, baya sha’awar ganin ko kofar ɗakin bare ya shiga.A saman bed ɗin daddy ya jefa wayansa game da cire tail coat ɗin jikinsa ya jefa kan gadon, ya bar iya long sleeve shirt na ciki, toilet ya shiga, jim kaɗan ya fito fuskanta da ɗan danshin ruwa, balconyn daddy ya nufa, tsayawa ya yi yana kallon cikin CRYSTAL PALACE ɗin, a hankali ya ɗan lumshe idanu yana tina da idan ya shigo gidan da fuskan daddynsa yake fara cin karo yana tsaye a balcony, ko yana zaune a kan sofar dake wajen.A hankali iska ta fara kaɗa shi tana kaɗa kitson dake kansa, sai ya ji wani irin daɗi na ratsa shi. Ya ɗan jima a tsaye a wajen kafin ya juyo ya dawo cikin ɗakin. Haka kawai yau ya ji yana sha’awar yi wa daddyn nasa bincike a ɗaki, abin da bai taɓa yi ba, dan kullum ya zo daga toilet sai gado kawai yake amfani da su. Drawers na wajen mirror ya buɗe, babu komai a ciki, rufesu ya yi ya nufi wajen closet na daddy, kusa da wani tangamemen wardrobe ya tsaya, komai yana nan yadda yake, kayan daddy dik baa taɓa komai ba tamkar yana raye. Nisawa Lion ya ɗan yi, hannu ya kai zai buɗe wannan wardrobe ɗin, sai taki buɗewa, zuba mata idanu kaɗan ya yi, nan ya fahimci haɗe take da na’urori, sai da password zata buɗe. Ɗan ɗage kafaɗunsa ya yi alamar anyway, sai ya wuce drawer ta gaba. Hannu ya kai jikinta take ta buɗe kanta. Wasu tsala-tsalan tail coat masu masifa tsada ne a shirye a ciki, a jikin hanger aka shiryasu tamkar mai shi yana raye.Kallo ɗaya ya yi masu ya ɗan ɗauke kai, har zai wuce kuma sai ya lura ai ba iya faɗin wardrobe ɗin ba kenan, tana da zurfi amma a wajen da su coat ɗin nan suke ya yi kaɗan ace iya zurfinta kenan, what’s behind?. Bai yi wani dogon tinani a kai ba ya matsa gaba, dan bai son ciwon kai, saboda yana tinanin dik kaya ne a cike a cikin ko’ina, dan yasan halin daddyn nasa ɗan kwalisa ne, gadon ɗaukar wanka suka yi.Wucewa gaba ya yi, ya dinga yawo a wajen, ko wucewa ya zo yi kusa da wardrobe in dai ta ɗan yi scanning ɗinsa sai kofar ta buɗe, bai damu ya dudduba me a ciki ba, wasu drawers ɗin ma takardu ne a cike a ciki ba kaya ba, amma bai mai da hankalinsa ba, wucewa kawai yake yi.A cikin ransa ya ce. “Ina computer dad? Da wannan computer yake controlling HAIZA’ANS AIRLINE da sauran abubunsa”……. Kada ku manta na ce maku computer hannun Dr James ita ce computer dad. Fitowa daga wajen ya yi, ya dawo tsakiyar ɗakin. Yana tsayawa sai ga Vir ya shigo yana faɗin. “Nan ka yo?”….. Bai yi magana ba, ya dai bi Vir da ido. Saman gadon dad Vir ya zauna yana cigaba da kallon Lion ɗin.Aryan kuwa kai tsaye room na mom ya nufa, domin kuwa ya jima yana son zuwa room ɗinta ya yi bincike, amma bai samu dama ba, abubuwa sun masu yawa, kafin su kammala wannan wannan zai sako kai, ko lokacin kansu basu da shi…….. Yana tura kofar yana da kura ta buɗesa, dan kuwa ana gyara ko’ina a gidan banda ɗakin nan, Lion ya hana a taɓa ko kofar ne, shiyasa uban yana da kura ya buɗe koina.Kamar Aryan zai juya sai kuma ya daure ya fara tattare yanar yana shiga ciki, dik in da ya taka sai shaidar kafansa ya bayyana saboda kura da ta yi yawa. Gadonta, drawers komai yana nan yadda ta fita ta bari, har bedsheet baa taɓa ba. Ɗan girgiza kai Aryan ya yi game da cewa. “Sai an share room ɗin nan an gyara zan dawo, dattin ya yi yawa”. Ya faɗa game da ƙoƙarin juyawa zai fita. Idanunsa ne suka sauƙa a kan gadonta, ya ga alamar tudu a bakin gadon, alamar wani abin ne da kura ta rufe sosai, kamar ba zai je wajen ba, sai kuma ya daure ya karisa. Hannunsa yasa ya zaƙulo abin dake wajen, kura ya zama tamkar ƙasa mai laushi aka zuba a wajen.Ya yi mamakin ganin wayarta ce, kenan tashin hankali yasa a lokacin da ta shigo ɗakin ta manta waya? Karkaɗe wayar ya yi game da ɗauka ya fita, rufo kofar ya yi ya nufi room ɗinsu na gidan, a nan ya ɗauki towel ya goge wayar, sai ya yi ƙoƙarin sakata a caji, amma babu caza, addu’a yake ALLAH yasa wayar bata mutu ta daina aiki gabaɗaya ba, ALLAH yasa ta tashi. A aljihunsa ya sanya wayar kafin ya fita ya nufi ɗakin dad. Ko da ya je bai sanar da Lion ya ga wayan mom ba, yana son ya fara binciken komai da kansa kafin ya sanar da Lion…….. In short sun yi kewaye sosai a gidan, amma basu bi diddigi ko bincike-binciken abubuwan ba, sun dai duba komai yana nan, babu abin da zasu buƙata ko da zasu dawo gidan. Sun ɗauki a kallah 3 hours a gidan kafin su nufi gida, suna komawa kuma ɗakin aikinsu suka shiga, aikin awa ɗaya suka yi, a nan Lion ya ce akwai wasu containers da ake shirin shigo dasu cikin ƙasar daren yau, ya yi bincike ya gano ta ɓarauniyar hanya za’a shigo da su, dan haka Vir and guru su dakatar dasu, su kwace containers ɗin dan su san me aka ɗauko a ciki, sannan su kashe dikka direbonin containers ɗin, mutum ɗaya kawai zasu barshi da ransa, su mashi ɗaurin goro su dawo da shi zuwa ɗakin azabtar da mutanensu. A kan haka suka tsai da matsaya yau, daga nan Aryan ya gudu wajen Seraphina. To mu koma kan labarin.Wanka Seraphina ta yi, ta shirya cikin crazy jeans baki, da polo t-shirt fari tas, ta je Madam ta gyara mata gashi tana tambayarta a daren nan kwalliyar me haka?. Cike da soyayya ta ce. “Daddy ne zai zo, shi ya ce in shirya”. Madam ta ce. “To ki zo ki ci abinci kafin ya zo ɗin”……… Ta maƙe kafaɗa tare da cewa. “Kai mom daddy ya ce kada in ci komai sai ya zo”……. Madam tana murmushi ta ce. “To daddy’s girl, ajira ya zo ya baki a baki ko?”. Ta faɗa a lokacin da take kammala gyara mata gashin ta ɗaure suka koma kan gado. Juyowa ta yi ta rungumi Madam tana murmushi.Daidai lokacin Suhana ta shigo cikin ɗakin, wani irin kallon rainin wayau ta yi wa Seraphina, haushin Seraph take ji dan ta fita kyau da komai. A walaƙance ta ce. “Ke tashi ki fita daga ɗakin nan zamu yi magana ya dangi”. Seraphina da bata barin ko ta kwana ta amsa da. “Ɗakinki na shiga ne?”. Ta faɗa tana tamke fuska tamau, irin ba wasan nan……. “Rashin kunya zaki mun ne? Am i your mate?”…….. Taɓe baki Seraphina ta yi, ta mata kallon uku goma kafin ta amsa da. “To sannu dabino sarkin shekaru”. A fusace Suhana ta ɗaga hannu zata mareta Madam ta yi gaggawar rike hannun nata, babu wasa a kan fuskanta ta ce. “Kada ki kuskura Suhana, kada ki yarda ki yi gigin ɗaura hannunki a jikinta”………. Cike da takaici Suhana ta ce. “To kenan Aunty sai in tsaya wannan ƴar kucakar yarinyar tana faɗa mun magana?”. Kallon uku saura kwata Seraphina ta yi mata, bata sake tanka mata ba, dan kuwa tasan in dai batun duka ne to mutum ɗaya ne kawai zai daketa ta haɗiye ta yi shiru, shi ne kuma daddy Champion, bayan shi wlh ko Madam ta daketa ba tare da kwakkwarar dalili ba sai ta rama, dan ba’a haifota dan wani ya taɓa lafiyarta ba! Tana ji da kanta da kuma jikinta, she respected herself! So dariya ma Suhana ta bata wai zata dage.Miƙewa ta yi ta sauƙo ƙasan gadon Madam, sumbata ta mannawa Madam a cheek game da cewa. “Than you mom, ina ga daddy ya dawo bari in je”. Ta faɗa game da baiwa banza ajiyar Suhana. Madam ta saki hannun Suhana tana ta faman murmushi suka yi sallama.Seraphina na fita Madam ta ce. “Baki da hankali ne zaki ce zaki ɗaura hannunki a jikinta? Me ta yi maki? Baki duba yanayin jikinta bane? Kina ɗaura hannunki a jikinta wlh sai kin yi nadama, dan kuwa ko taɓata kika yi jikinta na nuna alamar hakan, bare mari, tsab yatsunki zasu bayyana a kan fuskanta, kin san waye daddyn da take kiran nan kuwa? Kin san a kanta zai iya komai ko baki sani ba? Zai iya ɗaure dikka zuri’armu, dan haka ki bi a hankali, na kawo ku gidan nan ne dan cikar burinmu ba dan faɗa da su ba, in kin san ba zaki iya jura ba gara ki koma”. Babu wasa a tattare da ita ta faɗa. Zama gefen gadon Suhana ta yi, tana turo baki na rashin kunya ta ce. “Sorry Aunty, it can’t happen again”…… “Ya dai fi maki”. Madam ta faɗa tana miƙewa.Ita kuwa Seraphina ɗakinta ta koma, ta hau feshe jikinta da perfumes da ya saya mata masu daɗin kamshi, ta haɗu matuƙa sosai. Zama ta yi a gefen bed tana laluɓo wayarta zata kirasa, sai kuma ta fasa, ajiye wayar ta yi a gefen gadon ta miƙe da sauri ta nufi wajen curtains dake wajen door, a bayan labulayen ta ɓuya tana ɗan leƙowa.After like 5mins da tsayuwarta a wajen ya shigo bakinsa a ɗauke da sallama. Tsayawa ya ɗan yi a tsakiyar ɗakin yana kalle-kalle game da shaƙar kamshinta da ta fesa yanzu, a cikin ransa ya ce. “Awwa yau ɓuyan mun aka yi kenan”. Ya faɗa game da sake saurarawa, abinku da jami’an kwarai, tuni ya gano tana ɗakin ta hanya biyu, na farko sautin nunfashi wanda shi ko me yaya baya ɓuya a waje, muddin ka saurara sai ka jisa, na biyu kamshin perfume da ta fesa yanzu, ya nuna alamar yanzu-yanzun nan mutum yana cikin wannan ɗakin, dan kamshin bai ko gauraye da airfreshner dake ɗakin bama. Juyo da kallonsa a kan curtains na wajen door ya yi, a nan ya ji karfin fitar numfashinta ya fi yawaita, kun san su a horon da ake basu ana mugun koya masu amfani da nunfashin mutum, ta haka ne suke iya zaƙulo abubuwa dayawa.Ya gane nufinta yanzu, wai tsoratar dashi take son yi, juyawa ya yi kamar bai ganta ba, sai ta buɗe labulen ta leƙo, ganin yana ƙoƙarin wucewa zuwa bakin gado ne yasa ta yi murna bai gane tana wajen ba, a hankali ta fito, ta ɗan yi taku step uku kafin ta daka tsalle ta mashi kukan kare a kunne……… Da gangan ya nuna alamar ya razana, har da faɗawa saman gadonta.Dariya ta fara yi tana karawa, zuba mata idanun ya yi yana ganin tsantsar kyan da ta ƙara. Sai da ta yi mai isarta sannan ta ce. “Daddy kai ba jarumi bane, ka cika tsoro, na fika jarumta, da nice ba zan tsorata ba, ka zo in koya maka jarumtata!”. Tana murmushi ta faɗa. Shi kam kallonta kawai yake yi, yana jin tamkar ya jawota ya rungume, ta yi wani irin musulmin kyau tamkar amarya. Ganin sai kallonta yake yi ne yasa ta natsu tare da komawa kusa da shi, cike da kisisina yarinyar nan har da tsugunnawa a gabansa, sai ka rasa daga ina take koyo kisisina da kirsa yarinyar nan. “Sannu da dawowa daddy, am…… In….. Ka yi hakuri tsorataka da na yi, dik saboda soyayyarka ce”. Tana turo baki ta faɗa. Shi kam izuwa yanzu dik wasu kalaman da zasu fito daga bakinta ya daina mamaki, yarinya kamar wata uwar mata, sai kirsa da kisisina. Uhm rasa abin faɗe ya yi, sai kawai ya bita da ido. Kwanto da kanta a saman laps ɗinsa ta yi, ta riko hannunsa cikin nata, tana turo baki, a shagwaɓe sosai ta ce. “My gentle chaos talk to me mana”. Uhm miƙewa ya yi game da kama hannunta, ya miƙar da ita, ya jata suka nufi waje ba tare da ya yi magana ba. Shopping na sama suka nufa, sai faman kallonsa take yi, taga ya yi tsantsar kyau yau, wannan suit ɗin ta kara fito da kyansa. Kai tsaye wajen abayas ya wuce da ita, da kansa ya zaɓo mata wani haɗaɗɗen after dress mai balain kyau fari tas da veil ɗinsa. Dress room na shopping ɗin suka shiga, da kansa ya ware rigar ya sanya mata a jiki, ya ce. “Haɗe maɓallan mu gani”. Ya faɗa yana mata kallon ƙasa-ƙasan ido. Turo baki ta yi. “Ni daddy ban iya sakawa ba, yadda ka fara haka zaka kammala”…… Ɗago eyes ɗinsa a kan face ɗinta ya yi, da sauri ta ce. “Da gaske ban iya ba, ai kaga ban taɓa sanya irin wannan kaya ba”……. Wani irin musulmin hararar kauna ya dallah mata kafin ya kai hannu saitin kirjinta ya kama maɓallan. Zubawa hannunsa ido ta yi, sai taga yatsunsa suna ɗan rawa, baya son taɓa jikinta. Da sauri ya haɗe mata maɓallai ukun, zuwa flat tummy ɗinta maɓallan suke, sauran gaban rigar a buɗe, rigar ta haɗu sosai. Hannu yasa ya ware veil ɗin rigar, ya yafa mata a kai, sai ya ce. “Ki yi rolling ɗinsa mu je”. Ɗan turo baki ta yi. “Ni daddy ban iya rolling ba”……. “Wannan kam nima ban iya ba, amma bari in kira ma’aikaciyar wajen ta zo ta maki”. Ya faɗa game da juyawa da nufin ya fita……. Da sauri ta riko hannunsa. “Ni daddy ba sai ka kira wata ba, kada ma ta ji muryanka”. “To ba na sanya nose mask ba sarkin kishi? Ai ba wanda zai ga fuskata”……. Make kafaɗa ta yi. “Ni dai dik da haka daddy ban yarda ba”. Ta kai karshe game da kama veil ɗin, ta fara rolling tana cewa. “Na iya fa”…….Zuba mata idanu kawai ya yi, awww ashe ta iya tsiyace dama. Rolling ta yi mai kyau kamar yadda Rimsha take yi, ta ce. “Daddy na yi kyau?”……. Kawai tsintar kansa ya yi d kashe mata ido ɗaya yana sauke ajiyar zuciya. Waro idanunta ta yi. “Daddy, dama ka iya kashe ido ɗaya?”…… Siririn harara ya dallah mata, bai yi magana ba ya riko hannunta suka fito. Kuɗin rigar ya je ya biya suka nufi waje, suna fita ya rungumo shoulder ɗinta tare da rage tsawonsa, a dan kunnenta ya ce. “Yau fa kin yi kyau over, anya ba zan aureki kawai ba? Na fara jin gajiya a kan wannan shamakin dake tsakaninmu, gara in cire hijabin ta hanyar halatta abin”…….. Da sauri ta ɗago kai, cike da farinciki ta ce. “Daddy ka aure ɗin kawai, kada ka jira komai”. Dogon hancinta ya ja. “Kafin na yi aure dole akwai tsari, sai na bi wasu hanyoyi shiyasa, but lokaci kaɗan ne ya rage, and yanzu akwai very important abubuwa sosai dake taso mana”…… Yana tina tarzomar da zata tashi ne bayan bayyanar IRON FIST a cikin CRYSTAL PALACE, yasan duniya dik sai ta tsaya cak, akwai kura, wannan dalilin yasa ma bai fara batun auren ba, ga shi yana da tafiya a gabansa mai muhimmanci.Turo baki ta ɗan yi ta zura hannunta ta baya ta zagayo da shi har ta wajen flat tummy ɗinsa. A haka suka sauƙo ƙasa. Shopping na ƙasa ya shiga da ita. Kaya sosai ya fara loda mata, bathrobe da sukai mata gajarta na gidan nan dik ya ɗauka mata masu tsawo, ya sai mata abayas sosai, dan yana son ta dinga rufe jikinta.Ita ma zagewa ta yi sai shopping take yi, har da ɗaukar breziya dozen biyu, gani take ta zama ƴan’mata yanzu, musamman da ake ce mata in an ganta kamar mai 16 years, shikenan tana jin kanta ta kai can. Suna tsaka da shopping suna hiran soyayyarsu ne wata mace siririya mai zubin taliyar bua tai masu hello. Kallo ɗaya Aryan yai mata ya ɗauke kai, ita kuwa Seraphina ta fara kallonta daga sama har ƙasa, gara ƴar siririya sai kuma ta ɗauko wasu karuwan kaya, jeans and top ta labka a jiki, ta tara gashin kai a tsakiya ta ɗaure, ta sako jekar gaba, idanunta dara-dara, to a ajiye maganar adawa a gefe kyakkyawar gaske ce sosai, fara tas da ita, sai dai bata da welcome bare kuma goodbye, a shafe take kamar namiji da zani, amma kyan fuska kam akwai shi sosai.Ta kwamo wani uban high heel tamkar wacce ke shirin zuwa taɓa duniyar wata. Yarinyar irin classic lady ɗin nan da boko ya bugasu, wayayyu fiye da misalin nan, a shekaru zata iya kai 25 haka, a nan CRYSTAL PALACE ɗin take, ƴar wani tsohon ƙusa ne na siyasa a ƙasar, dukiya ta yi mubaya’a, suna haya a CP. Seraphina baku abin magana, da ta kare mata kallo sai ta ce. “Wannan fa? Ke babu mirror a gidanku ne?”……. A tinanin yarinyar Seraphina sister ɗin Aryan ce ganinta ƴar karama, sai bata amsa mata ba, ta ɗan matsa dab da Aryan, cikin wani karuwan murya dake maƙale ta ce. “Hii handsome, wajenka na zo, one minute please”. Aikuwa nan Seraphina ta ce ba’a haifi mutum ba, da sauri ta matsa kusa angonta, ta tamke fuska kafin ta bi yarinyar da wani matsiyacin kallo. Aryan dai tamkar ba da shi aka yi magana ba, ya yi banza da yarinyar.Seraphina dan ta gwadawa yarinyar ita ma A ce sai ta ce. “My gentle chaos mu tafi wajen lotion in zaɓa, daga nan ya isa mu wuce”. A shagwaɓe ta faɗa tana riko hannunsa. Tsayar da kallonsa a kanta ya yi, ta marairace fuska tana turo baki. “Kin fasa sayen vest ɗin ne?”. Ya faɗa can ƙasa. Kai ya jinjina mashi. “Yanzu na fasa, sai wani lokaci, kawai ka zo mu tafi”. Ta ƙara kankame hannunsa. Ɗan rungumo shoulder ɗinta ya yi game da cewa mu je. Zame jikinta ta yi daga nasa ta tsugunna a ƙasa, tamkar zata yi kuka ta ce. “Ni ka ɗaukeni”. Waist ɗinsa ya riko da hannayensa dikka biyu, ya sauke ajiyar zuciya kafin ya rage tsawonsa, ya ɗauketa cak tamkar ƴar baby, hannayenta tasa ta saƙalo wuyansa kafin ta kwantar da kanta a gefen lion chest ɗinsa. Wucewa da ita ya yi, sun zo dab zasu wuce yarinyar Seraphina ta fidda tongue ɗinta tai mata gwalo, Seraph ta ji haushin yadda yarinyar ta yi banza da ita ta nufi Aryan ne, ta zage sai ta mashi magana, shi ne ta gwada mata capacity ɗinta.Ai tsaye yarinyar ta yi tana ganin ikon god, babyn daddy ta goge mata hadda gabaɗaya. Da suka je wajen lotion zai sauƙeta ƙasa ta ce ina bata san wannan ba, wai sai dai ya riketa ta zaɓi abin da take so, ta ƙara ƙanƙame shi game da kwantar da kanta luff sosai. Uhm soyayya ai dole ya yi abin da take dan kada ranta ya ɓaci.Ya kuwa biya mata, a haka ta karisa sauran shopping ɗin, wai dan fa yarinyar ta ji haushi ne yasa ta ce kada ya sauketa, a haka zasu yi shopping, dik ib da suka gifta yarinyar ta ganta kwance a kirjinsa. Kai Seraphina duniya, kishi da wanga ɗiya ai balai ne, iya kirsa da kisisina.Har da shafa arab hair ɗin Aryan ta bayan wuyansa tana ɗan turo baki. Shi kam bai kawo komai a ransa ba, kawai dan ya faranta mata yake yi. Bayan sun kammala shopping sai ya ɗauketa suka bakin beach dake cikin CRYSTAL PALACE ɗin, a lokacin dare ya fara yi, karfe 11 ta yi. Suna parking a wajen sai ga kiran Lion. Picking ya yi game da karawa a kunne, shiru ya ɗan yi yana sauraron Lion ɗin, after like 20 second sai ya ce. “Kawai ku yi dinner ɗin, sai can dare zan shigo”. Buɗe baki Seraphina ta yi zata yi magana ya yi gaggawar rufe mata da hannunsa yana ɗan zare mata idanu. Kai ya jinjina kafin ya ce. “Zan kula”. Daga haka ya ciro wayar ya katse. Zai ɗauke hannunsa daga kan ɗan bakin nata ta yi saurin kamawa ta sumbacesa kafin ta ce. “Daddy da waye kake waya?”.Buɗe kofar moyar ya yi, ya fito ba tare da ya amsa mata ba, sai kuma ya ce. “Wait for me bari in maki oder abincin dare a wancan CRYSTAL RESTAURANT ɗin”. Bai jira amsarta ba ya wuce ya nufi wani haɗaɗɗen ɗan karamin restaurant dake wajen.Fitowa ita ma ta yi, ta tsaya a jikin motar game da takure jikinta waje guda, wani irin sanyi na bugata, akwai sanyi sosai.Jikinta na rawa, ta so komawa cikin motar amma babu dama, dan tana fita motar ta rufe kanta, bata san yadda ake buɗeta ba. Unexpected idanunta suka sauƙa a kan beach na wajen, ya ALLAH, zazzare idanunta a kan ruwan ta yi, bata san lokacin da ta raba jikinta da jikin motar ba, da gudu ta karisa wajen tekun tana kallon fitilun dake wajen, ga hasken wata na haska ruwan. Rufe idanu ta yi ta sake buɗewa, a fili ta ce. “Wajen ya haɗu, yaushe zan samu cikar burina na keta cikin teku a jirgin ruwa in je kasar da rana take fara fitowa? Wayyo sea”. Lokaci guda wani iska mai sanyi ya busata, hakan yasa ta yi gaggawar takure jikinta waje guda, hannunta suka fara rawa, tana son kallon ruwan kuma tana son komawa wajen motar ta laɓe kada sanyi yai mata illah. Shiru ta takure a wajen tana ganin haɗuwar ruwan. Unexpected daga bayanta ta ji an ɗaura mata abu a saman shoulder, kamshin perfume ɗinsa yasa ta gane shi ne. Da sauri ta juyo ta faɗa jikinsa, ya rufeta da suit ɗinsa da ya cire, ya gyara mata da kyau, dama suit ɗin ya ɗaura mata a shoulder ɗinta. Zuro hannayenta ta bayansa ta yi, ta yi tighting ɗinsa sosai tana faɗin. “Daddy yaushe zaka ɗaukeni mu ratsa teku mu je kasar da rana yake fitowa ta cikin jirgin ruwa?”…… Can ƙasa ya ce. “Very soon, after our marriage”. Ɗago kanta ta yi, suka ɗan zubawa juna ido, sai kuma ya rabata da jikinsa game da sanya mata suit ɗin nasa. Ya kama hannayenta suka nufi wajen haɗaɗɗun kujerun da aka tanada kusa da beach ɗin dan cin abinci.A nan suka zauna saman kujerun dake kallon juna, ya zuba mata ido yana jin tamkar ya mallaketa ya gama, a daidai lokacin kuwa Abba na can suna plan da Ammie kan a cikin satin nan zai kawo ziyara gidansu Seraphina, Ammie ta bada goyon baya ɗari bisa ɗari saboda dama Seraphina ta shiga ranta.Sai shagwaɓa take zuba mashi tana ƙarawa, shi kuwa yana ta biya mata, a wannan dare ya shirya masu abubuwa dayawa, dan har wajen CP zasu fita. Ƙayattatun abinci aka kawo masu waje, da kansa ya dinga ciyar da ita, sai santi take yi tana karawa, sai da ya cika mata ciki tab, sannan ya ci ɗan kaɗan, ya tashi ya kama hannunta suka nufi cikin mota, daga nan suka nufi ainahin main gate na CP ɗin, sai murna take yi yau zata fita waje, shi kuwa sai farinciki yake yi na ganin tana murna. ——————————🔥D——-O——–L🔥Around 1 na rana, bayan sun yi sallar azahar sun yi lunch, suka zauna Noor yana ɗaukar karatu wajen Leo, while Zaynish ya haɗa kayansa ya nufi bakin ruwa dan yin wankin kakinsa, ya ce ba zai iya baiwa ƙananan sojoji su yi mashi ba, saboda shi in mutum ne yai mashi wanki yana ganin baya fita, ya fi so ya yi da kansa. Vash yana zaune a kan wani dutse yana shan mangoron da sojojinsu suka ciro a wata bishiya da ta nuna gwanin ban sha’awa.A can kuwa, Arya da su Angelina suna ɗaki, Manassa na zaune gefen mattress rike da drink a cup a hannunta tana sha, while Angelina na rike da laptop, yanzu ta mayar da hankali kan aiki sosai, saboda Zaysh baya ɗaukar wasa. Shigowa cikin room ɗin V ta yi, tana ɗan ɗingisa kafa, ba jimawa ta farka daga barci ta yi wanka, tana sanye da kaya marasa nauyi. Kallo suka bita da shi, suna shirin yin magana sai gani suka yi ta ɗauki wayanta ta nufi waje, bayanta suka bi da kallo. Kusan a tare suka miƙe Manassa rike da cup na drink ɗin suka biyo bayan V dan su ji meyasameta, sun ga idanunta sun yi jajir sun kumbura tamkar ta sha kuka, ga shi tana ɗingisa kafa, abinku da shagwaɓɓaɓiya sai shagwaɓe fuska take yi.A bakin tantinsu suka isko V tsaye tana ƙoƙarin kara waya a kunne, Arya rike da hannun Jehan, Manassa ta zauna a wannan dutse dake bakin tantin nasu tana kora drink ɗinta, Angelina ta tsaya gefen Manassa ɗin, suka tsaya jiran ta kammala waya.A natse murya can ƙasa ta ce. “Hello friend”. Ta faɗa tana ɗan matsawa daga kusa da su Angelina, taga miss call ɗinsa sama da 20 ne daga daren jiya zuwa yau, shi ne ta ce bari ta kira ta ji menene, wannan causin ɗin nata ne. Daga can ɓangaren ya ce. “Ina kika shiga ne beb, tin jiya ban jiki ba, dik na damu, na yi kawarki sosai, naki kewar daddaɗar muryar nan taki”…….. “Sorry friend, nima ai na yi kewarka kuma na yi kewar daddaɗar muryanka ɗin, aiki ne ya sha kaina, yasu Aunty Bee?”. “Suna lafiya to ya aiki?”……. Ɗan juyawa ta yi zata amsa da lafiya idanunta suka sauƙa a kan Noor dake tsaye ta bayan tantinsu, ya yi folding hands ɗinsa a kirji, kallonta kawai yake yi, fuskanta a tamke tamau, dik ya canza. Ya shiga cikin tantinsa ne yaga bata ciki, to sanin bata jin daɗi yasa ya ce bari ya dubota, sai ya bi ta bayan tantin nasa zai shigo nasu kenan ya ji tana cewa ta ki kewar daddaɗae muryan friend, shi ne ya tsaya a wajen.Ai jikinta take ya hau rawa, ta wani irin mugun shan jinin jikinta, da sauri ta zare wayar daga kunnenta, tana ƙoƙarin yi mashi magana ya matso cikin zafa ya kwace wayar, wancan karon ma da ya raga mata dan bai san me mata yake nufi gabaɗaya ba, aikuwa yanzu ya sani, dan haka bai ga dalilin da zai sa wani ya nemi shiga harkarsa ba, yanzu auren sunnah ma suka yi bana zobe ba, kuma ya je duniyar sama jiya ai sai shiru.Jikinta na rawa ta sake mashi wayar tana kallonsa. Bin kan screen ɗinta da kallo ya yi, sai ya kara wayan a kunnensa, a daidai lokacin Friend yake ce mata. “Da gaske voice ɗina na maki daɗi beb?”…….. Wani irin tsananin takaici ne ya turnuƙe zuciyansa, a fusace ya ce. “Who the hell are you?!”.Zuba mashi idanu su Manassa suka yi, zallar kishi ne malam a kan fuskansa, har idanunsa sun ƙaɗa sun yi jajir. Kit Friend ya katse kiran, dan a tinaninsa oganta ne a wajen aiki. Bin kiran Noor ya yi, amma ba’a ɗauka ba, cikin zafa ya ɗago da kallonsa a kanta.Hannu ɗaya ya zura cikin aljihun combat trouser dake jikinsa, ji ya yi tactical tshirts dake jikinsa ma zafi take haɗa mashi tsabar ya fusata, abin takaicin yai mata warning a farko ranar, amma yau ta sake yi.Cike da zafin kishi ya ce. “His voice is so sweet, and you missed him so much, who’s he?!”. In a harsh way ya faɗa, hakan ya ja hankalin sauran sojojinsu dake sansanin, amma dik sai suka yi ƙasa da kai tin da ogansu ne a wajen.Gagara bashi amsa V ta yi, idanunta suka ciko da kwallah, hannunta sai kerma suke yi…….. “Okey you love his voice, you missed him? You love him right? You want to marry him?”. Cikin zafin kishi ya faɗi maganar, bai ma san me yake faɗe sosai ba.”Please stop it, stop saying that, It’s not what you’re thing……”. Tamkar zata sanya kuka ta yi maganar….. Wani irin mugun kallon da ya dallah mata ne yasa ta haɗiye sauran maganar. Cikin fushi yana wani irin huci tamkar zai kama da wuta ya maka wayar tata da ƙasa, take ta tarwatse raga-raga. Hannu bibbiyu ta sanya ta toshe bakinta jikinta na tsananta kerma, hawayen da take ƙoƙarin rikewa ne ya fara zuba tamkar an buɗe tap, da kyar ta iya ɗagowa ta kalli rikitatcen face ɗinsa da gabaɗaya ya canza, har ja fuskar tasa ta yi tsabar fushi. Sai ma in ya tina ta ce i missed you and i missed your sweet voice, ya rabb, sai ya ji tamkar zai haɗiye zuciya. Muryarta na rawa ta fara ƙoƙarin sake yi mashi magana ko zata dace. Cikin zafa ya ɗaga mata hannu game da cewa. “Don’t say anything here!!”. Ya faɗa yana pointining ɗinta da hannunsa. Ba shiri ta haɗiye abin da take son faɗe, jikinta ya tsananta kerma sosai wanda yasa ta gagara iya rike kanta dama ba lafiya ba, sai kawai ta durkushe ƙasa a wajen, wani irin kuka mai tsuma zuciya ta fashe da shi. Da gudu Angelina ta kariso in da take, durkushewa ta yi ta rungumi V a jikinta tana satar kallon Noor dake ta uban huci tamkar zai kama da wuta. Gabaɗaya takaicinsu ya gama cika Arya, ji take tamkar ta shake V da ta zubar masu da mutunci take baiwa namiji hakuri a kan laifin da bata aikata ba, yaushe ta ce tana son friend?. Ita dai Manassa abin da kowa ya sani ne, watau komai normal, bata wani damu ba, dan faɗa tsakanin V da Noor ai ba sabon abu bane, zama su shirya ne babu wanda ya sani, ranar da suka yi wancan uban faɗa waye ya taɓa zatan zasu shirya? Ba sai ga shi ko kwana ɗaya ba’ayi ba har sun shirya! Dan haka su rataye kansu idan sun ga dama ita babu ruwanta. Noor ne ya cika baƙin kishi, ga ɗan banzan saurin fushi, ya koyi saurin fusatar Leo, in ban da haka yanzu me abin fasa mata waya daga jin tana magana da wani? Ko damar yin magana yaki bata, shi sarkin zuciya.Siririn tsaki Arya ta ja tare da juyawa da sauri ta bar wajen, dan zata iya kai duka idan ta cigaba da tsayawa. Manassa dai hannu ta miƙa ta ɗauko drink ɗinta dake ƙasa ta cigaba da sipping, dan ita faɗar ma sugar yake mata, ai in basa faɗar basu cika masoya ba. Juyawa Noor ya yi cikin fushi zai bar wajen. Da sauri muryarta na rawa ta ce. “Please, my heartbeat, just listen to me, give me one chance to tell you who I truly am, don’t be upset with me for a mistake I never made, let me hold your trust close to my heart”.Ai ko kallon in da take bai sake yi ba, da sauri ya wuce gudun kada ya kai mata duka, dan wlh ya rike kansa ne, ba dan haka ba time ɗin da take cewa friend voice ɗinka da daɗi da sai dai ta ji hakwaranta a ƙasa ya zubar mata saboda balain kishi. Ita ma bata ji, gata mai aboki, ai taga aboki yau kam.Wucewa ya yi ya barta a wajen, ta rungume Angelina tana wani irin kuka mai ban tausayi, dama ga ciwon da ya ji mata. Shi kuwa cikin tantinsa ya koma, ya zauna a gefen mattress yana huci. After like 5 mins ya miƙe cikin zafa ya fito. Suna nan in da ya barsu, Arya da Jehan ne kawai suka koma ciki. Su ya nufo gadan-gadan, yana zuwa ya ɗauki V cak sai saman buɗaɗɗiyar kirjinsa, cikin zafin jini ya wuce cikin tantinsa da ita, ba zai iya barinta tana kukan nan ba dan yasan bata da lafiya, kada wani ciwon kuma ya kamata. A saman mattress ya kwantar da ita, a tsawace ya ce. “Ki mun shiru, idan na sake jin koda tarinki ne sai kin gane kuranki”. Babu wasa a tattare da shi ya faɗa. Hannu tasa ta toshe bakinta game da haɗiye kukan nata, tana kallonsa cikin ido, ya dallar mata harara kafin ya miƙe ya fice ya barta kwance, sai shessheƙar kuka take yi.Lamarin Noor da V sai su wlh, ga balain kaunar juna ga zafin kishi, ga kuma faɗa, kai suna bani ciwon kai.After some hours.Bayan sun yi sallar mangrib da ishai, sojojin dake sansanin suna hakin wuta, har team one suna tare a bakin wuta except Leo dake cikin ɗakinsa, V tana ɗakin Noor kwance zazzaɓi ya rufeta saboda kukan da ta sha ga ciwon da angon nata ya bata jiya, sai zazzaɓi ya rufeta, har yanzu kuma Noor yana kan dokin zuciya, yaki sauraranta, da ya kawo mata abincin dare ma tana son yi mashi magana ta faɗa mashi tana jin zazzaɓi sai ya dakatar da ita, ya wuce ya fita ba tare da ya ji me take son ce mashi ba. Su Angelina suna tare da Arya a cikin ɗaki suna hira, shiryawa Arya ta yi cikin normal kayan gida kamar yadda Leo yai mata message, wandon jeans baki da top ash, ta ɗauki karamin pistol da ake basu dan kare kai, sannan ta ɗauki laptop ɗinta cikin rucksack ɗinta, bata yi wa su Angelina magana ba ta wuce ta fita.Da sauri Jehan ta taso tana nuna mata alamar zata bita. Riko hannunta ta yi, ta miƙawa Angelina ita tare da cewa. “Zan je wajen sir Nirash ne, akwai aikin da zamu yi, ki kula da ita”. Ta kai karshe game da rage tsawonta ta sumbaci goshin Jehan, sannan ta saketa ta juya.Da sauri ta nufi tantin Leo, tsaye ta iskosa ya kammala shirinsa cikin combat trouser ɗinsa da normal tshirt, yana kokarin sanya wuƙaƙensu na sojoji a mazaunansu a jiƙinsa. Kamewa ta yi game da sara mashi kafin ta ce gata nan. Bai yi magana ba ya wuce gaba, bayansa ta bi, suka fita ta baya babu wanda ya sani, ko su Noor basu sani ba.Tafiya mai mugun nisa suka yi har zuwa in da gwamnati ta gina ginin office ɗin sojojin ruwa dake ɗan nesa da bakin ruwan. Dik juriya irin ta Arya sai da ta gaji a wannan tafiya, shi dai ya wuce gaba, ko sau ɗaya bai waigota ba, ga rucksack na laptop ɗinta da ta goyo a baya ko shi bai karɓa mata ba.Haka ta jure wahalar har suka isa, dik jikinta ya yi tsami. Tsarin ginin offine ɗin nan ya tsaru kam, ga tsawo sosai. A jikin katangar ta baya suka tsaya, Leo ya juyo da kallonsa a kanta, tana tsaye tana ɗan haki. Can ƙasan maƙoshi ya ce. “Zaki iya haurawa?”. Kallon tsawon katangar ta yi, ya yi tsayi sosai, amma da yake basu san kalmar no ba sai ta ce. “Yeah sir”. Hannu ya miƙa kan ta bashi rucksack ɗinta. Ba musu ta cire ta miƙa mashi, karɓa ya yi ya goya a bayansa game da tura wayansa cikin anjihunsa, ya haɗe hannayensa dikka biyu ya ware mata tafukansa.Baya-baya ta koma, sai ta zo da gudun gaske ta taka kan hannun nasa da ya haɗa mata, ta daka tsalle shi kuma ya ƙara ɗagata da hannun nasa, ta kama saman katangar ta haura, a hankali ta fara nishin gajiya. Sauke rucksack ɗinta dake bayan ya yi, ya jefa mata sama ta capke. Gefe ya ɗan koma, ya yi baya da gudu ya zo ya taka jikin katangar ya yi tsalle ya capki saman. Ya haura ya sameta. A tare suka dira cikin wajen. Tamkar ɓarayi haka suka fara lallaɓawa a wajen har suka samu wani ɗan lungun da kafa basa iya bi. A nan suka tsaya, ya juyo da kallonsa a kanta, a dake ya ce. “Kunna laptop ɗinki, dik wani na’urar dake amfani da network a nan nike son ki datsan mun, da son samu ne ku datsan mun babban na’urar da suke amfani da ita dan aiki, dik wani bayanansu ki sauke shi a laptop ɗinki”. Kai ta jinjina mashi game da taugunnawa a wajen, ta fito da laptop ɗinta ta ɗaura a saman laps ɗinta. A gaggauce ta kunna, kai tsaye ta nemi yin connecting na network ɗinta da nasu. Ta kuwa yi sa’a da yake tana kusa da su sosai, a take ta haɗe nata da nasun. A gaggauce ta fara ƙoƙarin yi masu kutse, a yadda take pressing laptop ɗin sai kun sara mata, cikin kwarewa da zafin nama. Kewaye Leo ya ɗan fara yi a wajen, ya je ya dawo, ya je ya dawo, yana duba masu babu mai zuwa ne. Tin around 12 suka isa wajen tana wannan aiki har 2:30, ta yi mugun gajiya, bayanansu na da mugun yawa, da kyar ta iya haɗosu ta fara ƙoƙarin saukewa a kan nata na’urar, kafafunta da take taugunne sun gaji sosai, hannayenta dik sun gaji, yadda ta sunkuyar da wuya yasa wuyanta ya rike kam yana mata zafi. Dawowa kusa da ita Leo ya yi, can ƙasa ya ce. “Mintuna nawa ya rage komai ya sauƙa?”……. Tamkar zata yi kuka, da kyar ta ce. “A ƙallah 40 mins”. Yadda ta yi magana da kyar yasa ya sauke kallonsa a kanta sosai, sai yaga tana ta ɗan jujjuya wuyanta alamar gajiya, wuyar ta rike mata sosai tana son ta ɗan sake, ga shi wajen da suke ɗin akwai ciyayi ne sosai ba hakin zama, ta gaji matuƙa. Ganin hakan yasa ya dawo dan ita, durkutsawa ya yi ta bayanta, ya gyara hands glove ɗin hannunsa game da riko shoulder ɗinta dikka biyu. Take ta ji komai ya tsaya mata cak, slowly ta ɗan juyo ta kalli hannunsa dake kafaɗar tata.Nisawa ya yu tare da fara mammatsa mata wuyanta a hankali-hankali, daga kafaɗarta zuwa bayan wuya, ya sake komawa wajen damtsen hannunta, so yake yi ta yi sauri su bar wajen, dan sun shiga hurumin da ha nasu ba, binciken bayan fage yake yi a sirrance, idan aka kama shi ya shiga wannan hurumi ba karamin balai zai shiga ba, dan ya keta in da ha nasa ba, shiyasa yake son ta yi sauri su bar wajen, ga shi ta gaji aikin ya daina gudu, bata iya pressing laptop ɗin sosai bare ta iya kwasan bayanai dayawa a lokacin guda, kaɗan kaɗan take copy ta yi paste, shiyasa ta fara mata tausa dan ta samu kwarin jikinta.Aikuwa tamkar ya sanya mata battery ne, yana fara yi mata tausan ta fara jin gaɓoɓin wajen wuyanta sun fara sake mata, take ta fara pressing laptop ɗin da sauro, ganin haka yasa shi ma ya kara yi mata tausan da kyau, musamman wajen bayan wuyanta, da ya zo wajen ya sanya hannayensa dikka biyu ya kama wajen, ya sanya ɗayan hannu ya riko wuyanta ta gaba, ɗayan kuma ya fara………*Jama’ar kirki littafin ZAKUNA BIYAR STEP 1 ya zo gangara, zamu shiga STEP 2 wanda shi ne ainahin labarin yake cikinsa, ZAKUNA BIYAR iya STEP 1 ne kawai free, daga STEP 2 zuwa karshe paid ne, 1k kacal yake, ki hanzarta making payment kada mu tafi mu barki, dan labarin bai ma fara ba, tarin ilmin, faɗakarwa, waazantarwa, wayar da kai, nishaɗantarwa dik yana cikin STEP 2, yanzu dik ba’ayi komai ba, STEP 1 dik sharar fagece, ainahin labarin yana gaba, in kin shirya makin payment ga account ɗina, 2308489938, Musa Fatima Zahra UBA bank. Sai ki turo mun evidence ta wannan number 08161390581. Mutanen Niger ku mun magana ta numberta sai in baku Nita ɗin da zaku yi payment ɗinku a ciki, idan kuma kati ce ku mun magana dai zan faɗa maku komai.*

Back to top button