Mejo Najeeb Page 6 By Autar Alheri
“Atake suka shiga kokawa inda Allah yabawa Isseta sa’arta tadanneta tana Neman bud’e mata fuskarda ke rufe, Hakan yasa Tayi saurin wintsilawa tafice daga d’akin aguje..agigice Isseta tamik’e tsaye tana Neman kunnah fitilar d’akin inda tasamu kunnah mab’illin dakyar sabida kad’uwa, haske namamaye d’akin tabi mutanen dake ciki da kallo musamman anty hawwa da anty bilki suda tagani zaune sunabinta da Ido, hakama juwaira da zubaida domin itadai jidda baccinta takeyi…dafe kanta Tayi kawai tana tinanin cikin yayun nata wacece keneman nakasa mata rayuwa itadai Bata tantance kowacetaba acikinsu Hakan yasa tashiga kogin tinani, Kuma Sam Bata lurada cewar wadda takawo mata hari tafitaba…….suko su anty hawwa tinanin sukeyi wacece keda Irin halinsu agidannan wadda tafarmaki Isseta? Tinda sunsan cewar Basu bane, Amma sunada tabbacin Isseta bazata yadda dacewar Basu bane tinda sune ta tab’a gani. Share zancen kawai sukayi dasukaga Yana Neman damunsu aran anty hawwa tace koma wacece ita tajiyo inaruwanta. Yayinda anty bulki ketinanin kowa Cece ta kyauta mata kuwa domin idan ta koyarda Isseta tahuta zatasamu sauk’i wurin samun Isseta d’in…..to agefen su zubaida ma Hakan abun yake domin duk atinaninsu cikinsune wata tafarmaki Isseta d’in tinda sunada yak’ini akan cewar tafisu komai doline kuwa subukaceta tinda dukkansu kanwar ja ce. Anasu tinanin zubaida ce kawai Bata wani abun se jidda Amma ko zuwaira dake Bata Neman mata Amma tana bibiyar Maza.Isseta kuwa komawa Tayi tazauna tana tinanin wannan abun zuciyarta fall fargaba ga bak’ar yunwarda tadameta ga tsoron abunda kwanciyarya zata Haifar…ahakan takwana zaune har akayi asuba kowana gidan yafito har ita, inda bayan sungama sallah ne kowa Yakoma ya kwanta Amma ita tashiga aikinta kamar yadda tasaba. Tanacikin yin cikon ruwa a panpo abbansu yashigo gidan yadawo daga masallaci akuma wannan lokacinne iyya hassi tafito d’ora sanwar abun Karin kumallo….gaidashi Isseta Tayi cikin son mahaifin nata kamar yadda tasaba, seda ya amsa kana yace “maryama Ina kikaje jiya har dare Baki dawo gidaba? Kuma mikikeyi atsohon gidan biredi keda shamsun mlm lado? Yatambaya Yana kafetada Ido. “Gabaki d’aya jikin Isseta yad’auki rawa cikin muryar rashin sanin abunda zata fad’a “wlh Abba Dama inaso. “Kinsanme? Banace Abar zancenba iyakadai karki koma Allah ya kiyaye gaba. Iyya hassi takatseta Bata bari tagayawa abban nasu abunda takesan fad’aba, kana tad’ora dacewa ai Malam tind’azu data dawo seda nayimata fad’a domin Sam Bata kyautaba annanne take gayamin ai shamsu ne yace tarakashi wurin yaga wasu abokananshi asheto bakowa aciki ita Bata saniba shine fa nayimata tass domin wlh inda zubaida ce senayi mata dukan tsiya to ita ba’abun nahukuntata ba ace nazalunceta shiyasadai na nuna mata illar Hakan Kuma nace Abar zancen anan kar akaishi gaba Kuma wani tsegumin yabiyo baya. Tak’arasa zancen tana wani kif’k’ifta Ido irinna gwaggon munafukan asali…cikin fad’a Abba yace Aida kinsani zaneta kikayi domin hakanne kawai zesa tagane kuskurenta wato sokikeyi kid’auko mana magana ko maryama? Shikenan karma kidena zakiga yadda zanyi dakai yafad’a cikin fishi tareda buka malum malum dinshi yashige k’ofarshi…..seda yad’aga sa’annan iyya hassi ta dallawa Isseta harara tashige warta kicin d’insu. Itakam k’walla ne suka cika idonta tana rasa mizatayi ayanzu k’iri’k’iri tanaji tana gani ansam bad’a mata k’arya Kuma batada halinyin magana yanzu Abba ya lullusata abanza. Ganin zaman baze anfana mata komaiba yasa tamik’e tareda cigabada aikinta seda tagama duka kana taje tayi wanka kana tafito atare nufar d’akin nasu.Yauma kamar kullun seda tashirya warta tsabb kana tanufi gidansu halima.Abakin k’ofar didan suka had’u halima zata fito itakuwa zata shiga murmushi suka sakarwa juna tareda tab’awa da hannayensu irinna aminan juna kana Isseta tace “k’awar se Ina Hakan? “Hum kedai bari wlh innah ce ta aikeni gun baba lado tonaje bayanan shine tace nakaiwa yah shamsu.. “to muje mudubashi daganan semuwuce Gurin maah kinsan yau zamu koma asibiti ko? “Eh hakane kuwa to Amma mufara zuwa gun maah Kinga daga mundawo semunemi yah shamsu gaba d’aya semuwuce asibitin tinda Kinga yanzu bawani abun zanyiwa innah ba. Cewar halima tana rik’o hannun k’awar tata domin sutafi. “To shikenan badamuwa muje. Daga Hakan suka kama hanyar Rafi.LegosDa sallama abakinshi yashigo general parlor gidan captain Jameel nabayanshi yayinda general aliyu ketake musu baya, ganin kowa na gidan zaune a perlor ne yasakashi k’arasawa wurinsu hadda dady. Cikin girmamawa ga mahaifin nashi yace “good evening Dad how was you day? “Evening Dad yafad’a atakyaice. General aliyu ne yagaidashi tareda captain Jameel Aiko ya amsa cikin sakin fuska Yana tambayar aliyu mahaifinshi kasan cewar abokinshine. Shima aliyu cikin girmamawa yake bashi amsa daga Hakan suka gaisarda Hajiya Umma da mama. Yauma kamar kullun yadda tasaba Hakan ta amsa mishi adak’ile bayabo bafallasa, mama kenan. Hajiya Umma kuwa cikin farin cikin ganin yaron nata take amsa musu dukkansu tareda tambayar lpyr mejo d’in. Bayan sun Bata amsane suka mik’e dukkansu domin haurawa Saman benen part d’in mejo dominshi tuni yayi gaba bayan ya amsa gaisuwar k’annen nashi. Cikin sauri kuwa siyana tabi bayansu tana fad’ar yah aliyu katsayani bazan iya cinma yah najeeb, tak’arasa zancen tana shek’owa aguje. “Murmushi general aliyu yayi tareda d’aukar ta lokacinda tak’araso yace “to rigimammiyar Umma gani ai Kuma Allah karki karyani domin yanu kinyi nauyi. Dariya kawai siyana keyi abunta bayanta mak’alk’ale general aliyu. Da kallonso da k’auna wa yaron nata tabisu kana tasauke ajiyar zuciya cikin farin cikin ganin yadawo lpy tacewa mansura maza takai musu kayan fruit da abunci.Hajiya Umma kenan uwa maba d’a mamah💃💃 “okay kawai mansura tace kana tamik’e cikin farin ciki tanufi kitchen domin aiwatarda umurnin mahaifiyarta.Suko suna shiga dukkansu a perlor shi sukazube suna tattauna yadda zasu fuskanci abunda ke gabansu gameda wannan tafiyar dazasuyi sabida a kwanakinnan gabaki d’aya sunkoma busy siyana nazaune akan cinyar mejo najeeb tana zuba mishi surutu…da sallama tashigo parlor d’aukeda D’an tire ahannunta tad’ora kayanda tayanka musu na Fruit Akai sewani kwarkwasa takeyi da iyayi kamar wata karuwa😏 captain Jameel ne kawai ya amsa mata sallamar tata Amma general aliyu ko kallanta beyiba domin shi kanshi ba’abaya yakeba wurin jidakai da miskilanci…ganin Hakan yasa ta’ajiye tiren agabansu tana fad’ar gashi yah najeeb Umma tace nakawo muku. “Okay mungode cewar captain Jameel domin haryanzu ba wanda yayi magana acikin basawan…Hakan kuwa bak’aramin konaran mansura yayiba shiyasa tafita afusace tana k’uk’anai kaitsaye bedroom d’inta Takoma inda tasawo wasu arnayen kaya masu bala’in fitarda halittar mace kana tabazawa jikinta mayun turaruka masu Dad’i sosai dashiga Rai wanda doline idan kaji k’amshin zakaso ganin mamallakinshi, Hakan tafito tareda nufar kitchen dukkansu wanda ke parlor da kallo suka bita Amma ba wanda yace mata komai hadda dady kuwa balle Hajiya Umma data d’auke kanta kamar Bata gantaba.


