Asanadin Makwabtaka Book 2 Page 56 Complete Novel

*ASM Bk2056*
_Destiny may be delayed but cannot be changed…._
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
……..Washe gari lahadi tun wurin karfe 8:30 Tk ya kawo masu Breakfast daga gidan Hajiya haka wurin 9 ma sai ga Fauzy itama ta kawo masu tace ma Fatun zata je ta dawo Aunty ta aiketa Kasuwa, da har gwaggo ta kira Amadu kan ya had’o masu abun karin kumallo ganin sun kakkawo yasa ta kira shi tace ya barshi, wurin karfe 12 na rana saiga Haulat harda innar su sunzo gaida Fatun take ce mata ita bata san tana Asibiti ba sai da k’anwar ta taje siyayya shagon Kawu Amadu yake fad’a mata, cike da nuna damuwa ta tambayi Fatun wai miyake damunta da har ya kaita ga kwanciya Asibiti tana rungume da Babyn Haulat d’in da ta k’ara girma Tubarkallah ta bata labarin sanadin ciwon, sosae ita ma Haulat ta girgiza da jin zancen Aurenta da Ya Haisam tace Allah kenan mai yin yadda yaso a kuma lokacin da ya so cike da farinciki duk da bata ji dad’in rasa cikin ba tace “K’awata kinga abun Allah ko gashi har kin ci ribar hakurin da ki kai, muna ta ganin kaman shi ba rabon ki bane ashe da rabon a kusa ma” ta k’arasa tana murmushi shiru Fatuu tay da damuwa akan face d’in ta Haulat da ta lura da hakan tace “ko baki farinciki ne Allah ya cika maki burin ki, ko kuwa Saboda rasa cikin ne, kiyi hak’uri duk rashin sani ne ya jawo haka Allah ya k’addara hakan sai ya faru” yar ajiyar zuciya Fatun tay a sanyaye tace “haka ne Haulat na sani kawae dae ina ganin auren ba zai d’ore ba tunda ga dalilin yin shi” da sauri tace “in sha Allahu zai d’ore mutu ka raba keda ya Haisam bi’iznillahi ki kwantar da hankalin ki ni ina ganin hakan hikima ce ta Ubangiji dama ya kaddaro shine mijin ki shiyasa komae ya faru, baki ga da akai auran ba duk da ga yadda aka tsara amman kuma sai bai sake ki d’in ba k’arshe ma ga abu har ya shiga tsakanin ku harda rabo ni na tabbatar auran nan zai d’ore ke yama d’ore kawae” ta k’arasa tana yar dariyar farinciki still da yanayin damuwa Fatuu tace “amman fa Haulat Ya Haisam d’in Fushi yake dani kan wannan abun daya faru yana ganin nayi mashi taurin kai Saboda nak’i in saurare shi naje na zubar da cikin” itama yanayin fuskar ta ne ya sauya ta kai hannu ta kamo hannun Fatun guda tace “kinga wannan ma kadae ya isa yasa ki gane ya Haisam ba don ya sake ki ba ya aure ki in ma farko da wannan niyyar ne to daga baya ya canza ra’ayi tunda gashi har bai ji dad’in zubewar cikin ba wanda da yana da niyyar rabuwa dake ai shi dad’i zai ji koma da kan shi yasa a zubar Saboda kar abun da ya shiga tsakanin ku ya bayyana, nasan shi mutum ne mai fahimta sosae zai fahimci dalilin ki yay maki uzuri tunda ai sun san ke baki san da auren ba kuma Saboda ku duka kika aikata hakan, don haka ki kwantar da hankalin ki ba abunda zai faru kawae yana fushin ne don ya nuna maki kin mashi laifi kuma ki gane bai ji dad’i ba ko don Saboda gaba, keda ma kike yar gidan shi dama ko kin 6ata mashi rai da kin bashi hakuri yake hak’ura ki tuna fa tun farkon sanin shi kafin ku saba ma babbar asara kikae mashi harta kud’in shanu goma kuma kina sane kika aikata mashi amman kina zuwa kika bashi hakuri ya hak’ura balle kuma yanzu da kuka zama abu d’aya ya kuma san abunda kika yi kuskure ne sakamakon rashin sani da Kin san komae baza ki aikata hakan ba kuma yanzu da ya baki dama zaki gyara laifin ta hanyar biyan shi abunda ya rasa ba kamar na shanu ba” ta k’arasa tana dariya itama Fatun yar dariyar tayi ba kamar da ta tuno mata da can baya, kwantar mata da hankali taci gaba da yi har saida taga ta washe bayan sallar Azahar suka tafi, wurin k’arfe ukku Fauzy ta dawo harda Abincin rana ta kawo masu Gwaggo tay ta godiya tana fad’in ba’a gajiya da d’awainiya Fauzy na murmushi tace ai an zama d’aya gwaggon tace hakane tay Addu’ar Allah ya bar zumunci, Fauzy da kanta ta zuba ma Fatun ta kai mata saman gado tana ci suna yar fira nan take fad’i mata zancen zuwan Haulat ta nuna bata ji dad’i ba da basu had’u ba amman in suka koma gida zata je ta k’ara ganin Baby d’in su, bayan ta gama cin Abincin Fauzy ta d’aukko mata drugs d’in ta tare da bottle water ta sha, gab da la’asar sai ga su Feenah sun k’ara zuwa yau ma harda Abinci, da Abbas ne zai kawo amman Abdul ya sa rigimar sai anzo aikuwa tunda suka zo ya haye gadon suka kankame juna shida Fatun daga baya Abbas ya shigo ya gaishe da ita tana ta murmushi ta amsa har yana fad’in “Alhamdulillah da alamu Amaryar mu da wuri zata warware ta biya mu abunda muka rasa” murmushi Fauzy da Feenah sukai ita dai d’an sadda kai kawai tay tana d’an murmushi ya tambayi ta ci Abinci tasha magungunan ta Fauzy tace eh, sai bayan la’asar suka tafi da daddare bayan isha Haisam yazo yau ma kaman jiya da manyan ledoji yana sanye da k’ananun kaya yana shigowa Fauzy da har lokacin tana nan don tace yau a nan zata kwana ta mik’e daga kan kujera da suke zaune tare da gwaggo taje ta amshi ledojin tana mashi sannu da Zuwa ya d’aga mata kai ya juya suka gaisa da gwaggo ganin tana niyyar mik’ewa don ta bashi wuri yasa shi ce mata ta zauna zai wuce ne tace to ta koma Fauzy ma bayan ta aje ta dawo kusa da gwaggon ta zauna, slowly ya nufi gadon Fatuu na zaune jikinta sanye da doguwar rigar Atamfa ta jingina da bango kanta sanye da hula ta kallabin rigar tayi wani fayau da ita ta k’ara haske sosae saidae ta rame ba kamar Fuskarta har idanunta sun fad’a, a gefen gadon ya tsaya tunda ya shigo ta sadda kai k’asa saida taji tsayawar shi a wurin ta d’an d’ago suka had’a ido ta gaishe da shi jinjina mata kai yay slowly ya tambayi jikinta ta bashi amsa da Sauk’i, shiru yay idon shi akanta itama shi take kallo tana yi tana d’an maida idon k’asa tana sake d’agowa da su duk ta kame kan ta can ya d’an ta6e baki ya juya ya nufi hanyar fita su gwaggo su kai mashi saida safe ya amsa, tunda ya tafi tay zugudum Fauzy ta taso ta zo gefen gadon ta zauna ganin yanayin Fatun ta tambaye ta har yanzu fushin yake cikin raunanniyar murya tace mata eh Fauzyn tace “ki daina damuwa k’ilan ma fa ba wani fushin da yake tunda irin su dama gane masu yana da wuya kawai k’ila yana canza maki fuska ne don ki gane kin mashi laifi” shiru kawai tay amma ita ai ta karance shi sosae tana gane yanayin shi, yau ma dai kaman jiya suka sha shagalin su da abubuwan da ya kawo gwaggo ta zubo masu itama ta zuba ta koma kan kujera da Fatuu tak’i ta ci Fauzy ta tursasa mata harda yin k’asa k’asa da murya tace “ki saki jiki ki ci ki k’oshi ta hakane zaki samu sauk’i sosae cikin d’an lokaci ko Kya yi sauri ki biya shi abunda kika sa ya rasa ya daina fushin in ma shi yake yi” wani kallo mai kaman harara tay mata Fauzyn ta sa dariya tana d’an gumtse baki daga baya Fatun ta fara ci suna cikin ci cikin rad’a Fauzy tace “akwae wata mai magunguna da Aunty ke siye jiya dana koma muke Maganar da ita tace yakamata a amsar maki su don suna da mugun kyau wllh tunda ita tana amfani dasu ta shaida ingancin su, haka tace su maza ta haka ake kama su Aunty harda cewa wai ba kamar irin wad’annan miskilan mazan an fi kama su ta nan wai har zaucewa suke kaita mamaki kaman basu ba kinsan mijinta shima miskili ne duk da bai kai Ya Haisam ba” cikin rashin fahimta Fatuu da tayi sototo tace mata wai wane irin magunguna ne Fauzy tay mata wani kallo tasa hannu ta ruk’e ha6a tace “yanzu nan wai ke baki gane inda aka dosa ba sai kace wata yar primary magungunan mata fa ake nufi wanda mata ke sha don gyara jikin su Saboda su kama mazajen su badai wai baki san su ba?” Shiru Fatuu tay kaman mai tunani can tace mata ta san su taga ana tallan su a Tv kuma da suna secondary school lokacin da suka kusa gamawa wad’anda zasuyi aure da sun gama suna zuwa da su suyi ta sha harma su samma su har da wani mai kaman chocolate da kwakwa a ciki tana son shi yana da dad’i don Haulat har badawa tay aka siyo mata da yawa suna sha, da sauri Fauzy tace “Chocolate gumba kenan akwae ma ta kwakwa da dabino d’an banzan dad’i ne da ita wllh duk ni ke sace ta Aunty Mareeya tay ta fad’a harma ta gaji yanzu in aka kawo mata sai ta d’ibar man a yar roba ta bani tace in na satar mata nata wuta bal bal” gaba d’aya suka sa dariya Fauzy ta k’ara cewa “kinsan akwae su fa da yawa wasu gari ne da Madara ake sha wasu da Zuma wasu na ruwa ne ke harda itatuwan tsarki tarkace ne sosae ake had’o ma mutum, kuma fa wai kinsan kaman gumbar nan da kika ce kina son ta tana da dad’i wai fa haka suke ji mazan in ku kai Meeting” waro ido Fatuu tay don ta gane meeting d’in da take nufi Fauzy tasa hannu ta gumtse dariya Fatun ta girgiza kai a hankali tace “Allah ya shirye ki Fauzy nidai ba ruwana” da sauri tace “ke kau keda ruwa wllh don ba k’aramin gyara zaki sha ba Aunty tace duk sai an sauke mashi miskilancin da Matarshi ta kasa sauke mashi wai sai an sa duk inda ya zauna sai ya ambaci sunan ki nace mata Aunty kaman wani zautacce tace ai haka zai koma a kan ki” gaba d’aya suka saka dariya har saida suka ja hankalin gwaggo dake cin abu tana saurarar radio ta juyo ta kalle su Fauzy data lura ta wutsiyar ido ta zaro ido had’i da rufe baki da ido tay ma Fatuu nuni da gwaggo itama ta gumtse dariyar, suna haka Amadu ya shigo dama gwaggo ta kira shi don ya kawo mata abun shimfid’a ta kwanta k’asa ita kuma Fauzy sai ta kwanta kan kujerar da fara’a ya shigo ya nufi gwaggo ya kai mata kayan suka gaisa ya juya ya nufi gadon ya tsaya a bakin gadon yana fad’in “kuce kuna nan kuna shagalin ku wannan to jinya kuke ko party” duk dariya su kai Fauzy ta gaishe dashi ya amsa Fatuu ma haka ya tambayi jikinta tace mashi ta samu sauki yace ai gashi nan kam ya gani suka k’ara sa dariya Fauzy tay mashi bismilla yace suci gaba da shagalin su ya juya ya koma wurin gwaggo ya tambaye ta yaushe za’a sallame su ne yaga ai ta samu sauk’i sosae tace to suna dae jiran Dr har yanzu bai ce komae game da sallamar, da zai tafi ta k’ulle mashi sauran abubuwan da suka rage tace in yaje sai yaci ya amsa yay godiya sukai sallama ya tafi, Washe gari wurin k’arfe tara da yan mintuna Dr ya shigo lokacin Fauzy ta tafi tuni Saboda zata makaranta Fatuu tayi wanka tana zaune gefen gado tana yin Breakfast da Tk ya kawo masu bayan sun gaisa da gwaggo dake zaune kan kujera tana shan tea yay mata ya mai jiki ta amsa ya nufi Fatuu ya tsaya bakin gadon itama ta gaishe shi da murmushi ya amsa yay mata ya jiki tace ta samu sauk’i yace Alhamdulillah haka ake so ya tambayi tana cin Abinci sosae ko tace mashi eh, jinjina kai yay daga nan ya shiga yi mata wasu tambayoyin tana bashi amsa daga baya yace bari ya duba bp d’inta ta maida kayan breakfast d’in kan drawer ya fara gwada ta harda idon ta ya bud’e ya duba bayan ya gama yace zata iya cigaba da yin Breakfast d’inta tace to, juyowa yay ya dawo wurin gwaggo yace mata yana ganin tunda komae lpy lou za’a sallame su yanzu sai taci gaba da shan magungunan ta a gida tana murmushi ta amsa da to had’i da yin godiya ya juya ya tafi, bayan ya koma Office ya kira Haisam ya fad’i mashi za’ai discharge d’in su yace mashi gashi nan zuwa yana kan hanya, bayan ya iso Office d’in Dr ya nufa yana sanye da jallabiya bayan sun gama tattaunawa ya fito ya nufi Amenity, kwankwasa kopar yay aka bashi izinin shiga sannan ya tura da yar sallama gwaggo da har ta fara packing kayan su ta juyo tana kallon shi da murmushi ta amsa sallamar tay mashi sannu da zuwa bayan ya gaishe da ita ya fad’i mata Dr ya sallame su tace to Alhamdulillah Allah ya k’ara mata lafiya ya kyauta gaba a hankali ya amsa da Amin kafin ya tambayi ko akwae kayan da za’a fitar tace eh ga wasu nan ta juya ta d’aukko mashi jakar kayan Fatuu da Basket ya amsa yana shirin juyawa Fatuu tace mashi ina kwana ya dakata ya kai idon shi kan ta bai amsa ba slowly yace mata ya jiki ta amsa sannan ya juya tabi bayan shi da kallo, bayan ya fita gwaggo ma ta d’auki su bargo da wani basket d’in tabi bayan shi, bayan an kai komae Mota Fatuu ta saukko daga saman gadon ta yafa gyalenta suka tafi bayan sun fito saida gwaggo ta lek’a d’akunan dake kusa da nasu tay masu sallama da Addu’ar samun lafiya sannan suka wuce, lokacin da suka isa Motar Haisam d’in bai ciki gwaggo ta bud’e mata gaba ta shiga itama ta bud’e kopar baya ta shige basu dad’e da shiga ba sai gashi ya fito hannun shi ruk’e da ledar magunguna da Dr ya sake rubutawa bayan ya iso ya bud’e driver seat ya zauna ya rufe kopar a gefen shi ya aje ledar ya tashi Motar suka tafi, tunda suka taho idon Fatuu na gefe tana kallon hanya har suka iso Amadu dake cikin shago yana ganin Motar ta parker da sauri ya bud’e ya fito ya nufo Motar yana washe baki shi ya bud’e ma Fatuu kopar ta fito lokacin itama gwaggo ta fito yana ta washe baki alamar yaji dad’i yace ma gwaggo ashe yau za’a sallame su tace eh suma basu sani ba saida safen nan da likita yazo, kallon Fatuu dake tsaye yay yayi mata sannu ta d’aga kai ya juya ya nufi Haisam da ya fito yana kokarin bud’e boot ya gaishe dashi, tare suka fiddo kayan ciki Amadu ya d’auki wasu ya nufi gida Haisam d’in na niyyar d’auka gwaggo tace mashi don Allah ya barshi za’a kwashe hakan yasa ya dakata, godiya ta shiga yi mashi had’i da Addu’oi a hankali yake amsawa ta d’auki wasu kayan ta juya Fatuu dake tsaye ta bita suka nufi gidan tana tafiya a hankali har ta kusa shiga ta juyo ta kalle shi suka had’a ido har lokacin yana tsaye a bakin boot d’in jiki a sanyaye ta juya ta shige, suna shiga gidan tsaf da gani ma da safen nan an share shi anyi Mopping dama Amadu baida ganda ya iya komai na cikin gida, d’aki Fatuu ta nufa gwaggo tace ta shiga parlor bari ta canza mata zanin gado tace to, bayan ta d’aukko wankakke a d’akinta ta shiga ta canza mata sannan Fatun ta koma d’akin tana shiga ta nufi gado ta hau ta kwanta, bayan gwaggo ta koma d’akinta ta kira Hajiya a waya ta sanar mata an sallamo su tay mata barka tace sai ta shigo tare da tambayar jikin Fatun suna gama wayar gwaggo ta cire kayan jikinta ta fito don yin wanka dama ita bata yi ba a Asibitin sosae taji dad’in sallamo sun da akai don komi dad’in wuri naka yafi ba kamar kuma wuri irin Asibiti da sam baida dad’in zama sai dole, tana kwance lamo can ta tuna da bata fad’i ma Fauzy an sallamo su ba kuma tasan yanzu an isa yin break hakan yasa ta kai hannu ta d’aukko wayarta dake a gabanta ta kira ta, sosae taji dad’in jin an sallame su tace in aka tashi tana nan zuwa sukai sallama, bayan ta gama wayar ta aje shiru tay tana tunanin Mijinta ta rasa gane mashi yanzu ada in tayi mashi abu ba daidai ba da ta bashi hak’uri yake hak’ura amman yanzu ta lura kaman bai hak’ura ba koda ta bashi hakurin gashi kuma ita a ganinta in ma tana da laifi ai shima yana da shi miyasa tun da abun ya faru bai sanar mata shi mijinta bane koda lokacin da suka je Asibiti ne bayan an gama dubata da suka dawo Mota ya shigo baya yana bata hak’uri har yana fadin zai gyara laifin shi ai tun lokacin ya kamata ya sanar mata, sannan ko da bai K’asar da ya turo mata kud’i har ya kirata daga baya da bata d’auka ba ai ko message ba sai ya turo mata ba yayi mata bayani haka tay ta raya abubuwa a ranta har bacci ya kwasheta, gwaggo na fitowa daga wankan ta sa yar doguwar rigar shan iska ta haye gado don tana da bashin bacci aikuwa nan da nan ya kwasheta, ba ita ta farka ba sai wurin sha biyu ta fito don d’aura girki ta lek’a d’akin Fatuu da har lokacin bacci take sakin labulan tay tana niyyar shiga kitchen ta jiyo wayarta na ringing ta koma d’aki ganin Hajiya ce yasa ta d’aga da sauri bayan ta gaishe da ita tace mata ba sai sun yi Abinci ba gashi nan Saude nayi ta kira d’azun ba’a d’aga ba tasan bai wuce bacci suke gwaggon tace eh wllh tay mata godiya bayan sun gama wayar sosae ta ji dad’in hakan a ranta dama baccin bai ishe ta ba ta koma ta kwanta cikin ranta tana jinjina kirki irin nasu shiyasa sam bata ji dad’in Al’amarin nan da ya faru ba don gaba d’ayan su sun shiga tashin hankali ba kamar Hajiya data sha kuka,
Bayan sallar Azahar Saude ta kawo Abincin lokacin Fatuu ta farka saida ta shiga d’akin tay mata ya jiki sannan ta tafi gwaggo ta zubo ma Fatuu Abincin da aka kawo wanda lafiyayyar sakwara ce miyar egusi da tasha ganyen ugu ga ganda da kuma nama sai farfesun yan ciki wanda hanta tafi yawa a ciki sai uban k’amshi ke tashi ta kai mata d’aki itama Abincin ya burgeta tun bata ci ba, saida ta wanko bakin ta sannan ta fara ci, bayan gwaggo ta zuba ma Amadu ta mik’a mashi itama ta zuba ta koma d’akin Fatun ta zauna kan Carpet tana ci suna d’an yin fira da Fatun dake zaune a bakin gado tana cin Abincin, wurin la’asar Fauzy tazo harda Abinci ta kawo masu bayan ta shiga sun gaisa da gwaggo ta aje mata basket d’in tana ta mata godiya ita kuma tana murmushi tana cewa ba komai ta fito ta nufi d’akin Fatuu lokacin tana kwance tayi wanka ta canza kaya zuwa doguwar rigar material itama Fauzy ita ce a jikinta tayi rolling veil tana rataye da side bag suna had’a ido suka sakar ma juna murmushi ta nufi gadon Fatuu ma ta tashi zaune, hayewa gadon Fauzy tay ta yadda suke facing juna tace “sannu Amaryar mu ya k’arfin jiki?” Yar harararta Fatuu tay Fauzyn tana dariya tace “ai dai ba k’arya nayi ba ko kuma wasa da gaske amaryar ce ke, kinsan kuwa a Makaranta dana fad’a cewa ke matar aure ce akaita mamaki” Fatun tace miyasa ta fad’a tace “to ai kinga dama anata gulma gashi yau baki je ba sai tambayata ake wai badai jikin naki bane yay tsanani shine nace masu miscarriage ki kai dama ke matar aure ce mijin naki ne ba zaune yake a K’asar ba yana dai zuwa, aikuwa kinga yadda akaita mamaki kuma wllh nan da nan suka yarda har wasu na cewa wai shiyasa wani lokacin kike zama hostel wani lokacin kuma kiyi day nace masu eh har na bud’e pictute d’in ki wanda kikae tare dashi na nuna masu wasu suka ce sun ta6a gani ya kawo ki wasu kuma ya zo d’aukar ki Zainab Muhammadu ma cewa tay tabbas ta ta6a ganin shi har sukai ta yaba kyawun shi ita da su Sa’adatu nan fa ta hau shela harda hawa saman Desk tana fad’in to masu gulmar Fatima Ard’o na da ciki tabbas tana da shi kuma na halal ne don da auren ta kuma gashi nan sun ja sakamakon gulmar da suke cikin ya zube sai Allah ya saka mata bak’in k’azafin da akai tay mata, sosae ta bani dariya wllh” d’an murmushi Fatuu tay ta d’an ta6e baki tace “Auran dake lilo” da sauri Fauzy tace “in sha Allahu ba wani lilon da yake komai zai daidaita mu sha biki….” Katseta Fatuu tay “har yanzu fa Fauzy fushi yake” Fauzy tace “zai yi ya gama ne amman ni na tabbatar ya riga ya gama shigowa hannu tunda abunnan ya faru kin ma tuna man ga sak’o Aunty Mareeya ta bani in kawo maki” tana kai Maganar tasa hannu ta ciro side bag d’inta ta bud’e wata kullin bak’ar leda ta fiddo bayan ta bud’e ta ciro wata yar kwalba madaidaiciya ta mik’a ma Fatun ta amsa ta fara karanta sunan maganin da bayanin yadda ake amfani dashi ba Arzik’i tasa hannu ta rufe baki Fauzy ta kyalkyace da dariya tace “Wllh nima sunan maganin ya ban dariya lokacin da zata bani sak’on fa hana ni tay in duba aikuwa ina hawa Napep na bud’e nima saida na rufe baki nace Ya Haisam ya bani ana shirya mashi makaman da zasu tarwatsa miskilancin shi” yar dariya Fatuu tay tare da d’an girgiza kai Fauzy ta shiga fiddo sauran tana mata bayani wani da Madara zata sha wani da nama haka tay ta mata bayani ita dae tayi zuru saida ta gama sannan tace “Dama sana’ar kika fara yi kinga yadda kike bayani sai kace kece mai maganin” Fauzy ta kyalkyace da dariya Fatun ta k’ara cewa “kema yakamata Fauzy ki manta da abunda ya faru ki fara saurarar samari ko Kya samu miji kema kiyi auranki, lokaci tafiya yake muna k’ara shekaru gashi mutuwa ake yakamata muyi auren ko don mu samu masu yi mana Addu’a” idanun Fauzy ne suka ciko da k’walla cikin raunanniyar murya tace “Wllh Zarah na kasa mantawa da Mujaheed duk da irin abunda yay man ba kuma wai ace in ya dawo gare ni zan iya auran shi ba wllh tllh ko da ace misali dole sai shi zan aura to saidai in mutu ban auren ba, kawae zuciyata ce sam bata man Adalci data kasa cire man shi a rai”,
Fatuu tace “matsalar daga wurin ki ne Fauzy kin k’i ba wani namiji dama da zaki daure ki ba wani da yake son ki dama a hankali zaki ga kin fara cire shi a ran ki, ki daure Pls” ta kai hannu ta kama hannunta guda, d’an murmushin yak’e Fauzy tay tace “zan jaraba in sha Allahu duk da a yanzu ba wani da zan ba damar amman k’ilan ko da bikin ki kinsan ance a bikin wata wata ke samun miji” ta k’arasa tana d’an murmushi haka Fatun ma tace “wai wane biki abunda an riga da an d’aura tuni” da sauri tace “aikuwa dole in komae ya daidaita mu sha shagali sai kace wani auren mak’iya za’a yi shi lami dole musha anko mu cashe bikin d’an Senator guda” dan ta6e baki Fatun tay can tace “Don Kawu Amadu bai had’u ba dana had’a ku” yar harara Fauzy ta wurga mata “Kawu Amadun ne zaki ce bai had’u ba santalelen saurayi dashi ga tsawo gashi fari ga kyau daidai gwargwado” dariya Fatuu tay tace “ai ba wannan had’uwar nike nufi ba ta kud’i nike nufi shi baida kud’i ke kuma na fi son ki auri wanda Mujaheed zai girgiza in yaji” d’an murmushi Fauzyn tay “Allah ya za6a mana abunda yafi zama Alkhairi a gare mu” Fatuu ta amsa da Amin suka cigaba da hira har Fauzy na ce mata ta tashi ta 6oye magungunan kada gwaggo ta shigo ta gani tace to tana k’ok’arin sauka daga gadon.
Tun bayan da Haisam ya maido su G.r.a ya wuce don yin wani aiki a computer sai da akai Azahar sannan ya dawo gidan Hajiya ya kwanta bacci, saida aka fara kiran sallar la’asar sannan ya tashi yay wanka ya shirya ya wuce Masallaci, bayan ya fito daga Masallacin parlon Hajiya ya wuce lokacin da ya shiga ba kowa ya nufi ciki ya zauna kan 2 seater ya d’auki remote yana canza channel, bai dad’e da zama ba Hajiya ta fito jikinta sanye da doguwar riga da mayafinta hannunta ruke da sandar ta haka idanunta na saye cikin medical glasses d’inta hango shi da tay yasa ta nufi cikin parlon don da gidan su Fatuu ta fito zata, tana zuwa cikin parlon ya d’aga ido yana bin ta da kallo har ta zauna a kan one seater d’in dake gefen shi itama kallon shi take bayan ta zauna tace “ashe ka tashi” kai ya d’aga mata,
“ai tun d’azu nike dakon ka bansan ma ka dawo gidan ba saida Saude ta dawo daga gidan su Fateema
nike tambayarta ko taga Motar ka a parking space tace man eh” shiru kaman bazai ce komae ba sai kuma yace “ba sai ki kira ba” d’an ta6e baki tay tace ai na kira ka sau biyu ko, farko landline na kira ba’a d’aga ba na kira wayar ka itama baka d’aga ba nan nagane bacci kake” yana ta kallonta har ta gama sannan ya d’an d’age gira yace “Wani abu?” tace “kaci Abinci ne?” Kai ya girgiza mata alamar a’a, “to sai kai zaune da yunwa baka iya shiga kaman magana” tay Maganar tana d’an hararar shi d’an guntun murmushi yay “ban jin shi sosae ne” tace “uhmm kai dai ka sani wa zai zauna yay ta fama da kai kan abunda amfanin kan ka ne alhali kai ba damuwa kai da halin da mutum zai shiga ba ya mutu ko yay rai ba abunda ya dame ka” d’an murmushi yay kawae ya fahimci kan zancen ciki daya zo yay mata take Magana da alama dae abun yay mata zafi,
“Am all ears da wani abu ne?” Fuska a kwa6e tace ya ci Abinci tukun ta juya tana k’wala ma Saude kira bayan ta fito ta bata umarnin kawo mashi Abincin, akan c-table ta d’aura tray d’in kayan Abincin tana kokarin yin serving nashi ya d’aga mata hannu alamar ta bashshi ta mik’e tace aci lafiya ya jinjina mata kai, a nutse ya fara cin Abincin yana yi yana kallon channel d’in daya kamo Hajiya ma idonta na akan Tv d’in tana kallon American film d’in da ake yi tana yi tana d’age kai had’i da yamutsa fuska wani lokacin har hannu take d’an d’agawa in anyi abun tashin hankali, bai d’auki lokaci mai tsawo ba ya gama ya yago tissue yana goge baki, kallon Hajiya yay bayan ya gama yace mata “am done” ta maido idonta kan shi saida ta gyara zama ta fara magana “dama game da Fateema ne tunda an sallamo ta ina son in ji miye matsayin ta tunda bai yuwuwa a barta tay ta zama da aure a kanta ba kamar yanzu da tasan da shi” shiru yay yana kallon gaban shi har saida tace mashi kar ya 6ata mata lokaci ya bud’e baki yay mata magana don fita take son yi, sigh yay ba tare da ya kalleta ba yace “I will divorce her” wani kallo Hajiya ta bishi da shi jin bata ce komae ba yasa ya juya ya kalleta ganin kallon da take mashi yace “dama haka aka tsara ai ba Abbas ya fad’a maki ba?” a k’ufule tace “eh ya fad’a man hakan aka tsara amman bai ce acikin tsarin anyi da kai zaka rabata da budurcin ta ba” yana jin haka ya juyar da fuskar shi daga barin kallon ta taci gaba “Yanzu kai irin Adalcin ka kenan? Sai da ka raba yarinya da pride d’inta sannan zaka ce ka saketa wato k’aramar bazawara kake son mayar da ita kenan, idan k’anwar ka ce zaka so ai mata haka?” Shiru bai ce komai ba bai kuma kalleta ba a fad’ace tace “ba tambayar ka nike ba Haisam! idan Jidderh ce Fateema zaka so ai mata haka?” Sai lokacin ya d’an juyo slowly ya furta “am sorry for dat” daga haka yay shiru itama bata k’ara cewa komae ba sai da aka d’an d’auki lokaci sannan ta dasa fad’in “ko kusa ban amince wai kace zaka saketa ba yanzu ta riga ta zama Matar ka dole kaci gaba da zama da ita don haka yanzu dole ta baro gidan su akawo ta part d’in ka nan zata cigaba da zama kafin muga abunda Allah zai yi sai kasan yadda in ka koma zaka sanar ma Matar ka ni kuma daga baya zan kira iyayenka su zo harda ita ta Lagos din sai in sanar masu su kuma ganta ko don Saboda halin rayuwa bai kamata ace duk basu san da Maganar ba auren ba” shiru yay can ya kalleta yace “is dat all?” Kai ta d’aga mashi ganin yana K’ok’arin mik’ewa yasa da alamun mamaki tace “au tashi za kai bazaka ce komae ba?” Dakatawa yay yace “So What do you want me to say ba kin tsara komae ba kiyi yadda yay maki” wannan karon bud’e baki tay galala tana kallon shi ganin hakan yasa shi d’an d’age gira “ba haka ya yi maki ba so just go ahead do as u wish” ta6e baki tay tana mashi wani kallo tace “to yalla6ai shikenan” mik’ewa yay ya nufi hanyar barin parlon walking majestically Hajiya ta saki baki tana bin bayan shi da kallo har ya fuce, hannu ta kai ta ruk’e ha6a a fili tace “tabbas Yau na shaida Miskili yafi mahaukaci ban haushi kaji fa yaron nan don Allah wai ni zai ma duniyanci, in da farko ya aure ta don ya taimaketa wannan na yarda don zai iya yin hakan amman na tabbatar yana son zama da Fateema shiyasa bai saketa ba kamar yadda suka tsara” ta kai Maganar tana ta6e baki had’i da yin k’wafa tana niyyar mik’ewa Saude ta kawo mata wayarta data baro d’aki tace anata kira ta amsa ta duba mai kiran kafin ta d’aga suka hau yin wayar, sun d’auki lokaci suna wayar kafin sukai sallama ganin yamma tayi sosae yasa ta yanke barin zuwa gidan su Fatun sai da daddare………….
….
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page :Â Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page :Â @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel:Â Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.