WACECE ITA⁉️(WHO IS SHE⁉️)
Unique Barakancy🌹
SIXTY-ONE📍
“Eh ina sonsa anna, ina jinsa kamar biological brother na”…..
Cikin rashin fahimta anna tace;
“Bangane ba? Na dauka tuwona mai na za’ayi? Ke yanzu bazaki auri saifu ba?”…..
Zaro ido baby tee tayi tace;
“Aure? God forbid! I only like him as a brother”…
Sai kuma ta mike da sauri tana fadin;
“That reminds me, khaleel yace ze zo, Allah yasa bezo yayita kiran wayata be sameni ba”….
Gyada kai anna tayi tace;
“Au sirikin nawa da akeyi dashi? Maza kirawosa kiji, ya kamata nima yazo na gansa”…
“Yeah zan kawo miki shi ku gaisa anna, let me call yaya saif ya kawomin wayata”…..
Ta fada tana dialing number da yace ta kira in tanasan magana dashi, bugu daya ko ya dau wayar cikin kwantar da murya yace;
“Any problem pretty?, nazo?”…..
“Eh, dan Allah ka kawomin wayata, I need to use it urgently”……
“Me zakiyi? What’s so urgent?”…..
Batareda tinanin komai ba tace;
“Khaleel zan kira, kaga tin dazu ya kirani yace ze zo, probably yazo but he couldn’t reach me”…..
Wani ajiyar zuciya deen ya sauke hade da hamdala na rashin ganin khaleel da batayi ba dazu, it means khaleel yaji haushi ya bar gidan batareda yasa a kirata ba, hakan kuma ya masa dadi and he’ll use this opportunity ya hadasu fada, cikin yanayin daya mata magana da farko yace;
“But no one called you zahrah, kunyi dashi ze zo ne?”…..
Dan jim tayi tana waswasin yanayin daya mata magana, tasan fa yanda baya kaunar khaleel shiyasa ko maganarsa batasan masa, yanzun ma subutar baki tayi amma ga mamakinta taji ya bata amsa a nitse, ganin babu yanda ta iya ya sata cewa;
“Eh, munyi waya dashi tin dazu yace min ze zo”…..
“I have cctv connected to the gate, duk wanda ya shigo ina ganinsa, so gaskiya be zo ba, gashi kuma ko kira daya be miki ba, he definitely discard your invitation and attend to other things”…..
Wani iri taji a ranta har maganganunsa suka nemi suyi tasiri aranta, amma ta daure tace;
“Okay ka kawomin wayata, let me call him inji ko lafiya, I know khaleel will not just disappoint”……
Wani abu ne yaji ya daki zuciyarsa, wai shi take gayawa tasan khaleel will not disappoint sai kace wani kanin ubanta, amma saboda bayasan ta dameshi sai ya bata wayar sai kawai ya biye mata….
“But he should have call you and inform you, wayace miki ana yiwa saurayi haka zahrah? Shi be kira ba sai ke zaki kira bayan you’re the inviter? Gaskiya ki jira ya kira ki kinji yar kanwata?”………
“Okay zan jira, I know he will call”….
Ko gama sauraran abinda ta fada beyi ba ya kashe wayar yana jan wani dogon tsaki……
Komawa tayi ta zauna kusa da anna tana jujjuya wayarsa dake hannunta, tambayarta anna tayi ko takira khaleel din, tace mata eh yana zuwa, sai tace taje tayi sallah toh……
Mikewa tayi sadap sadap tashige bedroom dinta ta kullo kofar a hankali gudun kar mami ko umm su gane tananan…….
Shigewa toilet tayi ta watsa ruwa sannan ta dauro alwala ta fito, tana idar da sallah ta koma kan gado ta kwanta, janyo wayar deen data ajye akan bedside drawer tayi ta kunna wayar dama a haka ya bata wayar babu password, direct photos ta shiga wai ta kalli hotunansa ta rage lokaci……..
Turus umm da mami suka tsaya suna kallon eesha dake kuka harda shidewa sai kace wacce akace uwarta ta mutu…….
Girgiza kai umm tayi tace;
“Hala a gabanki sukayi rungume rungumen ne? Is that why you’re crying this way?”…..
Sai kuma ta juya kawai ta fita…..
Ganin umm ta fita sai hankali eesha ya kara tashi duk a tinaninta umm ta dena yinta, sai ta rushe da kuka tana kallon mami data zauna a gefenta…..
Dafa kafadarta mami tayi tace;
“Ki kwantar da hankalinki Aisha, everything will be alright Insha Allah, kinji ko?”….
Gyada kai tayi ta cigaba da share hawayenta….
Nan mami ta cigaba da bata baki da kwantar mata da hankali har tayi shiru……..
“Saif ne da baby tee din umm”….
Cewar sudais yana sunkuyar da kai…….
Kada kai bappa yayi cikin al’ajabi yace;
“Yaushe wannan ya faru?”…….
“Yau ne, dazu”….
“A cikin mutane kuma? In ita yarinta na damunta saifu fah?”……
Shiru sudais yayi kawai ya sunkuyar da kai…..
Nan bappa ya tsare sudais da tambayoyi kala kala kamar shine ya aikata abun…..
Da sauri ta tashi ta zauna ganin tarin hotunanta a gallery dinsa, scrolling up tayi taci karo da pictures din da bata taba tinanin ya mata ba, wasu pictures dinma sakin baki tayi kawai tana kallonsu, har pictures din dazu data baza gashinta saida ya dauka, da lokacin dayace mata kamar mahaukaciya yanda tayi da gashinta shima sai da yayi capturing, har pictures din lallenta hannu da kafa saida ya dauka kuma batasan sanda yayi ba, bude ido tayi ganin wani hotonta sanye da wasu matsattsun kayan bacci tana bacci kuma, mamaki ne ya kamata dan takasa gane yanda akayi ya samu hotunan ko yamata hotunan zatace ne, harda hotonta na lokacin da take yayin saka niqab da hijabi, da hotonta tana cin abinci da sauransu, mamaki ne ya cika ta sosai dan babu wanda ze dauki wayar yace ba tata bace, kuma ko hotonsa guda daya bataci karo dashi ba sai nata, tabe baki tayi ta cigaba da scrolling…..
Zaro ido tayi sai kuma ta saki baki tana bin hoton da kallo trying to recall how and when, hotone yana rungume da ita , ita kuma ta kwantar da kanta sosai a jikinsa idonta a rufe kamar me bacci, tagumi tayi tana forcing kanta ta gano ranar da akayi hoton, kasa ganewa tayi kawai ta hakura ta cigaba da scrolling mamaki fal ranta, sai tambayar kanta take dalilin dayasa yake mata hotuna unaware, it seems he capture every slight moment, but why? Shine tambayan dauketa ringing a brain dinta and he’s not there to give her an answer…..
Saida ta kusa kaiwa karshen hotunan sannan Allah yasa taci karo da pictures dinsa guda uku masu shegen kyau, zooming fuskarsa tayi tana kallon captivating beards dinsa that she’ll not get tired of touching, babu inda batayi zooming a hoton ba a haka har tayi coming into the conclusion that they kinda have same trait, swiping tayi ta koma daya hoton, shima ta kafeshi da ido kamar shi din take gani dagaske, tasha ji yan mata na kodasa amma bata taba tsayawa ta kare masa kallo ba bare taga abinda ake fada, sai a ranar, har subutar baki tayi tace ‘he’s so handsome’ bata sani ba, sai kuma taja karamin tsaki tace ‘khaleel is better’…….
Saida ta gama kallon hotunan tass sannan ta fita daga gallery, curiously ta fada instagram, tana shiga kuma bata duba ko ina ba sai dm dinsa, karo taci da messages din yan mata kala kala, wani irin bacin rai ne yazo bata ba shiri na ganin yanda yan mata ke kaskantar da kansu a dm dinsa, kowa I want to be your girlfriend kamar shi kadai ne namiji a duniya, ita kuma inda abunda ta tsana shine taga mace tana stooping low akan namiji, ita ta fiso mace taja ajinta bawai kiyita bin mutum kamar bakisan mutuncin kanki ba, she so much believe with danne feelings dinka har sai mutum yace yana son ka shima…..
Komawa kan main profile dinshi tayi dan taga yawan followers dinsa dayasa yake da dm rutututu haka, 10k followers ne kawai amma kai kace dm din wani social person, amma ta fahimci abunda duk ya janyo hakan, abun shine picture dinsa guda daya dake kan page dinsa, sai picture dinsa na dp, sosai yayi bala’in kyan da babu macen da zata gani ta dauke ido, amma to her hakan is not enough reason ga macen da tasan abinda takeyi ta bata time dinta a dm dinsa……
Samun kanta tayi da deleting picture din dayasha uban comments da babu wanda ya tanka a ciki, sannan ta chanza masa dp zuwa wani hoton flower data samo a Instagram din, hakan be isheta ba saida ta koma tayi blocking duka wanda suka masa messages sannan tayi deleting chats din duka, still hankalinta be kwanta ba saida ta maida masa account din private…….
Download>>> Boddiya Complete Hausa Novel Document
Ajiyar zuciya ta sauke ta fita daga instagram, sai kuma wata zuciyar tace mata ‘toh in kin gama da instagram other social media platforms din fa?’, ai da sauri ta fada facebook zuciyarta na bugawa, wani mugun tsaki taja cin karo da one thousand plus messages, ko tsayawa bata lokaci ta duba batayi ba kawai tayi closing account din gabadaya aranta tace ‘in yaga dama ya kasheni’, sannan ta koma kan WhatsApp, nan ma goge goge ta masa bana wasa ba harda deleting saved contacts, akwai wani chat data shiga taga an mishi dogon wooing message ya karanta yace ok, sai taji ok dinnan ya tsaya mata kamar yace eh ya amince ne, murguda baki tayi kamar tana magana da wani tace ‘wallahi sai yazo ya gayamin meyasa yace ok’, saida ta masa blocking kusa 200+ contacts sannan ta dan ji dama a ranta, bata saduda ba saida ta saka masa timer na disappearing message yanda chats baza suna zama ba sannan taji hankalinta ya kwanta, sai da ta gama masa operation a WhatsApp son ranta sannan ta samu kanta da tura pictures dinsa guda uku data gani a gallery dinsa a WhatsApp dinta yanda inta karbi wayarta ta bude data sai tagani, da kyar ta gano numberta saboda yanda ya mata saving da ‘pretty tee’ sai kuma taji haushin yanda besa mata ko emoji guda daya ba, editing tayi tasawa kanta love emojis guda goma tayi saving sannan ba tinanin komai ta tura pictures din harda hoton daya musu su biyu, sannan ta sauka daga WhatsApp taje tayi downloading games………
Deen na zaune yayi tagumi yana tinanin yanda ze bawa umm hakuri ta dena masa mummunar fahimta, dama tuni yayi blocking number khaleel daga wayarta saboda bayasan karin ciwon kai bayan wanda yake ciki, tabbas beji dadi ba da umm tayi fushi haka but he’s not regretting anything that happen, ko rungumar da sukayi a gabansu umm be dameshi ba so far as baby tee is safe babu abinda ya sameta, he just can’t believe umm tayi laying hands dinta a kansa, baya tinanin tinda yazo duniya an taba dukansa sai ranar, da girmansa da komai umm ta dau charger waya tana dukansa dashi, abun is kinda funny in the other way round especially da tace wayasani ma ko suna zina, shi in zina zeyi ai bazeyi a gida ba, gidanma of all people wai baby tee din umm? Ai zuwa zeyi yayi a inda babu wanda ze ganosa……
Yana cikin wannan tinanin yaji karar shigowar messages a jejjere kamar dai yanda notification keyi idan ba abu daya bane, daukan wayar yayi yaga datan a kunne a kuma daidai nan wani message din ya kara shigowa da numbersa, ko saving numbers batayi ba amma ai shi yasan numbersa, mamaki ne ya kamasa dan gabadaya ya manta wayarsa na hannunta, da sauri ya shiga message din yaci karo da pictures dinsa har guda uku, sai a lokacin ya tina wayarsa na hannunta, wani murmushi ne ya kwace masa yana tinanin meyasa ta turo hotunan, hoton karshe daya gani ya tabbatar masa ta masa bincike a waya, wani murmushin ne ya sake kwace masa aransa yace ‘zakiyi bayani baby girl!’, yana shirin mata reply yaji sallamar sudais, yi yayi kamar beji ba meanwhile ya amsa a zuciyarsa…..
Guri sudais ya samu ya zauna yana facing dinsa murya a sanyaye yace;
“Saif dan Allah ka saurareni I have something very important to discuss with you”.
Banza dashi yayi kamar beji ba, inda badan sudais din bane bama babu wanda ya isa ya barshi ya zauna anan, sai dan akwai wani bond me karfi tsakaninsu da sudais shiyasa kawai…..
“Bro I know what I said is very wrong and I’ve learnt my lesson koda iya shariyar dakamin and yanzu nasan baby tee tafi karfina kuma tamin nisa but please listen to what I’ve got to say”…..
Cikin shan kamshi deen yace;
“Ina jinka”…..
Download>>> Yar Harka Romantic Hausa Novel
Murmushi sudais yayi sannan a nitse yace;
“Allah yasa zaka kwantar da hankalinka ka fahimci abinda nayi ta fuska mai kyau, ina tsoron fushinka saif”…..
“Just go straight to the point and stop beating around the bush sudais!”….
“Na nunawa bappa video of the incidence that happened dazu”….
“Which incidence?”…..
“The video you hugged and picked baby tee”…….
Sudais ya fada a hankali yana addu’ar Allah yasa kar deen ya fusata….
Ga mamakin sudais sai yaji a nitse deen yace;
“Why?”…..
“Saboda nasan idan bappa ya gani the matter can’t just go scout free, dole ya dauki mataki a kai har sai kowa ya gamsu da dalilin faruwar al’amarin”….
“And why did you want that?”….
Deen ya sake tambayarsa a nitse, sudais sai mamaki yake……
Dauke kai yayi yayi gathering courage yace;
“Because I know you’re in love with her!”…..
Wata muguwar dariya deen ya fashe da ita harda dukan tebirin dake gabansu kamar wani zararre, sai kuma ya saita kansa kamar bashi ya gama dariya ba yace;
“Ni in ina sonta bansani ba sai kaine zaka sani? Kawai saboda I hugged her, pick her up or whatsoever shikenan ina sonta? If that’s what you call love then you’re kidding and I don’t like this child play sudais!”…..
Zagewa sudais yayi ganin in aka cigaba da tafiya a haka deen will keep fooling himself yace;
“Believe it or not kana son baby tee because babu wani sign na sonta da baka nuna ba, ni dama shawara nazo baka akan kar kayi wasa da damarka because it might be your last chance!”……
Harararsa deen yayi a yatsine yace;
“To hell with the believe! And bangane kar nayi wasa da damata ba?”……
“Yes saboda bappa zeyi calling meeting, za’a taru kowa da kowa and I’m very sure ze tambayeka in kana son yarinyar nan, please saif I’m begging you don’t say no, wallahi karka cuci kanka”…….
Duka ya kaiwa sudais a kafada yace;
“You’re mad dude!!”…..
“Wallahi it’s the fact, let me tell you something, kasan meyasa na hakura da yarinyar nan naji tafi karfina all of a sudden? That’s because I know you love her, duk wani abu da kakeso da sunan soyayya kuma ya haramta a gurina bruh, apart from me kasan mutane nawane suka ajye makaman yakin neman soyayyar yarinyar nan just because of the incidence saboda kowa yayi tinanin soyayya kuke, infact har abbas saida ya sameni wai ya gani yanaso, ina nuna masa videon nan yace wallahi ya hakura, so it’s left to you now ka taimaki kanka kayi accepting kana sonta a gaban kowa, kai inma baka sonta kace kanaso trust me you’ll get to love her later kuma itama zata so ka dan babu macen da zata ki ka, in koh kace bakaso toh wallahi wallahi kaji na rantse bude baki zanyi ince ni inaso saidai duk abinda ze faru ya faru, just watch and see”….
Lakwas hakan jikin deen yayi sanyi kamar ba shi ba, be taba tinanin akwai maganar da zata bashi tsoro ba irin last sentence din sudais, a sanyaye yace;
“She’s in love with someone else sudais and her father wants him”…..
Cikin tausayawa sudais ya kalleshi ganin yanda jikinsa yayi sanyi kamar ba rough saif din daya sani ba, dafa kafadarshi yayi yace;
“It doesn’t matter! Gida be koshi ba za’a dauka a bawa waje? Kai fa na hannun daman umm ne, ita kadai is enough for you to win this game”…..
Numfasawa deen yayi yace;
“Sudais umm fushi take dani, you know how I use to lose control sometimes especially now abun yafi damuna, she caught me injecting myself, secondly she saw this particular video and she was so pissed off, can you believe har zargin zina ta mana nida yar’ta? So do you think she can fight for me?”…
Zaro ido sudais yayi yace;
“Innalillahi for real? Zina fa kace?”…..
“Eh wallahi sudais”…..
“Well I believe she can still fight for you regardless, inma zinar kuke ai gwara ta aura maka ku karasa abinda kuka fara than ta bawa wani, bare tasan ba haka bane, I know she’s just pissed off just like you said shiyasa ta fadi haka but deep down she doesn’t mean it, saif din umm ne fa? Wallahi just a word with her everything is alright, try it nasan zata tsaya maka wallahi”…
“Okay sudais”……
“Kayi alkawarin zakace kana sonta a gaban kowa?”……
“Nayi!”…..
“That’s my dude, let’s await the call for the meeting”…….
Da gudu hussy ta shigo ta rungume baby tee bayan ta bude musu kofar, sai ga sauran duka suma sun yo kanta, da sauri ta mike tana fadin;
“Meye haka zaku danneni, meya faru?”….
Wani irin ihu siyama tayi tana kamo hannun baby tee tace;
“Babe what did you add to your stew? Ya akayi kika sace zuciyar yaya saif? Oh my God you will make a very beautiful couple, ke kyau yaya saif kyau, wayyo Allah can’t wait”…….
Fizge hannunta tayi tace;
“Bakida hankali, waya gayamiki soyayya muke?”…..
Hussy ce ta karba da fadin;
“Guys ku kalli hannunta wayarshi ce, God when?, dan Allah baby tee ki mana story time on how it’s started”…….
Download>>> Dr Bobby Hausa Novel Document
“Kinga banasan irin wannan wasan fa, kunsan eesha? Toh wallahi itace budurwarsa ba ruwana in taji”……
Tsaki raihan tayi tace;
“Wace kuma wata eesha? Gaskiya bama san kalan dangi, babe wallahi kun dace, karki wani yarda ya kula wata eesha, kinsan kuwa bamu taba ganin yaya saif so gentle with someone ba kamar yau? Like he picked you up fa a cikin dubban mutane, can’t you feel that, oh my God ina ilham take mu bata shawara ta fita sabgar yaya saif dan wallahi she can’t compete”……
Dauke kai baby tee tayi ta koma ta zauna tana fadin;
“Ai sai kuyi kuma, ni bakusan inada darling khal dina ba? He’s so gentle ba irin wannan matsifaffen yaya saif din naku ba”….
“Munji shi masifaffe ne amma karya kike kice yana miki masifa, harfa hajajju ya dinga ce miki? If I’m not mistaken kamar naji yace baby girl ma, baby tee who are you fooling? Wa ze samu kamar yaya ya tsaya iyayi?”…..
Hassy da tin dazu batasa musu baki ba ta fada sitting close to baby tee….
Juyowa baby tee tayi ta kallesu daya bayan daya sannan tace;
“So kuke inyi accepting dinshi by fire by force kenan? Toh wallahi baku isa ba dan inada wanda ya fishi, someone I can control ba kazamin yaya saif dinku ba me lashewa mutum jiki”…..
Tana fadin haka ta tashi ta fice ko a jikinta……
Dora hannun aka safiya tayi tabi bayanta da kallo tace;
“Did I just hear her said me lashewa mutum jiki? Is she even serious? Yaya saif fa?”……
Dariya fahima tayi tace;
“Zata mishi karya ne? Wayasani ko ya lashe mata jikin dagaske? Ah Ke ko yaga shape ba dole ya zauce ba? Kina ganin yanda ya wani rungumota kamar dama chan yana hannu, ya dauketa kuma yayi ciki da ita, saida suka dade kafin su dawo fa, toh kika sani ko lashetan yayi da suka shiga?”…….
Ihu siyama tayi tace;
“Wayyo Allahna it will feel so good wallahi, he’s so romantic from all indications”…..
“So good ko? Sai kicewa saurayinki ya lashe ki kema ai”
Cewar fahima tana dariya….
“Dan Annabi kiyi shiru fahima kar wani yazo wucewa yaji maganarnan”…..
Cewar hassy tana rufe mata baki……
Zare hannunta daga bakinta tayi tace;
“Kefa hassy shegen tsoro ne dake, dallah barmu muyi gulmarmu, ko chanza suna ne ba sai muyi yanda baza’a gane ba”……
“Rabu da ita kedai, wannan hot zancen takeso mu share, mutum sai tsoro kamar farar kura”……
Cewar khairat tana shekewa da dariya itama…….
Nan suka cigaba da shakiyancinsu har da planning ankon da zasuyi a bikin…….
Hira suka cigaba dayi da sudais, sudais nata bashi tactics din yanda ze shawo kan baby tee karta bashi wahala as per shida yasan takan mata, shi kuwa yayi shiru yana sauraronshi deep down ko dariya yake wai sudais ne ze koya masa yanda ze tsara mace, macen ma kuma baby tee? In yayi using tactics din sudais ai ta rainashi ta gama………
Suna cikin wannan hali kiran bappa ya shigo dayan wayan deen as expected, dauka Deen yayi da sauri ya saka a handsfree, ce mishi kawai yayi yazo ya sameshi a guest parlour sannan ya kashe wayar, abunda deen be sani ba kuma shine bappa hotline dinsa yayita kira daga karshe baby tee ta dauka tace wayan yana gurinta, sai kawai yace tazo ta sameshi a guest parlour dama ita yake nema sannan haka ya kara tabbatar masa akwai wani abu a tsakaninsu….……
Dafashi sudais yayi yace;
“Bro karka manta da alkawarinmu fa”….
Gyada kai deen yayi yace;
“Yeah zan fadamusu su bani aurenta! Shikenan?!”…..