Labarai

Bakon Munafiki Complete Document

Description/Story:

Bakon Munafiki! Complete Hausa Novel Document Written By Miss Xoxo 

 

Description

BAKON MUNAFIKI!!!*_

_(BA NA MUTUM DAYA BANE)_

_👺🏡👩‍👩‍👦‍👦_

 

 

 

 

_FREE PAGE: 001_

 

 

 

_MADINATUL_MUNAWWARA_

_(ABA’ AD’ DUD)_

 

 

*AMB. JUNAID MUHAMMAD MAHMUD منزل القصر*

 

×××××

 

*AMB. JUNAID MUHAMMAD MAHMUD RES.*

 

shine sunayen da ke rubuce a jikin wani signboard dake nunawa da kyalkyalin rubutu masu ba da wasu kyawawan kaloli….

 

Bishiyu ne ke ta kadawa da ke gewaye da dogayen tsaunukan gidajen dake da matukar tsayi. Gefe daya kuma wata iska ce ke busawa tamkar anyi ruwa. Karatun Qurani mai girma ne ke tashi daga wani masallaci dake gefen kasaitacciyar unguwar da ke mamaye da gidaje da kayayyakin more rayuwa na yau da kullum…

 

Dogan gini ne a tsaye wanda sai kai ya daga sannan zai hangi karshen tsayin sa. Shafe yake da fenti mai matukar kyalkyali da daukar idanu.

 

Waata kasaitacciyar kofa ce da zata sadaaka da cikin gidan. Wadda kofar itake budewa ta rufe idan za’ai shige da fuce na gidan.

 

Kana shiga cikin gidan kayayyaki ciki masu kawaata idanu da daukar hankali ne zasu fara maka maraba. Baya ga haka wami tafkeken allo/frame ne mai dauke da manyan rubutu na sunan Allah mai girma ‘Yaa Hayyu Yaa Qayyum..’

 

Bene ne hagu da dama daka shiga gidan yayin da lifter ke kallon gabas. Iya tsaruwa da kawaatuwa gidan nan yayi. Domin alkalami yayi kadan wajen bayyana adadin kyawun gidan da ma mutanen daya kunsa…

 

×××Sake gyara zaman sa yayi akan kujerar da yake zaune. Hadi da saka hannu ya dedeta zaman gilashin da ke kara gani a idanun sa.

 

WhatsApp din ya sake shiga a karo na ba adadi. Ya dubi sunan group din da ke rubuce da manyan baki na ‘Zuri’ar Ardo Kandemi’

 

Dukkanin yan uwan nasa sun yi ma sa da iyalin sa adduar Allah ya dawo da su lafiya ya kuma sanya alkhairi. Idan ka tsame biyu daga cikin sauran yan uwan na sa ka ajiye a gefe.

 

Sam basu tofa komai ba game da dukkanin abubuwan da ya fada. Ya sake chika da mamaki kwarai matuka dayaga sun sake tsallake maganar da yayi mu su bayan ya kira sunayen su daya bayan daya.

 

Basu amsa shi ba. Sai suka cigaba da wata maganar ta daban. Ransa ya sosu kwarai matuka. Amman ya danne kawai.

 

Ya sake musu magana hadi da sallamar cewa: Nan da yan awanni zasu tafi airport su kamo hanyar kasar su ta Nigeria.

 

Kashe wifi din yayi gaba daya ya zura wayar a aljihun gaban rigar sa ta jallabiya doguwa shudiya.

 

Yana zaune ya hade hannuwa ya lula duniyar tunani yar sa ta shiga cikin parlorn nasa bakin ta dauke da sallama. Ya amsa yana mayar mata da murmushin da takeyi wanda kumatunta suka lotsa.

 

Sanye take cikin doguwar riga kalar sararin samaniya dake sheki da kyalyalin kalar hoda. Ta yane kanta da mayafin rigar. Gefen kafadar ta daya jaka ce ta ratayawa sai yar wayar da ke hannun ta.

 

“Abbiey barka da safiya…”

 

“Barkan mu dai mama na.”

 

Ta sake sakin wani tattausan murmushi tana mai hade yatsunta waje daya bakin ta yana mai kokarin motsawa.

 

Ya nazarceta don haka shima ya mike tsaye yana mai kallon agogon hannun sa

 

“Ina jin ki…”

 

“Abbiey dama zan je shagon da na gaya maka ne jiya.”

 

“Mun kusa tafiya airport fa. Ko kin manta tafiya zamuyi?”

 

“Ban manta ba abbiey.. naga ne kamar da sauran lokaci.”

 

“Wai dole sai wannan mall din dai?”

 

“Abbiey suka dai ne suke sales yau…..”

 

Ya bude baki zeyi magana ta riga shi sanin yanzu zai hanata zuwa ko ya saka dakarai su rakata abunda kuma bataso kenan. Don haka tayi saurin sake cewa,

 

“Abbiey dan Allah ka barni naje ni kadai ba tare da masu fararan kaya ba, babu abinda zasu tsare min wanda Allah bai tsara ba, please Abbiey dan Allah.”

 

Yarinyar yar shekaru goma sha shida ta fada cikin muryar ban hakuri hadi da roko mai tattare da shagwabe fuska sosai… Tare da sake langabar da kai ..

 

Sosai Amb. Junaid yake kallan yar tasa yana kuma karantar yanayinta, yasan abinda ta fada gaskiya ne komai sai Allah yayi shike tsara kowa da komai , amma Allah yace tashi in taimake ka.

 

Don haka ya furzar da iskar bakin sa kawai.. Bayasan ya sake shiga tashin hankalin da ya shiga a baya na tarin shekaru masu dimbin yawa.

 

“Abbiey….”

 

“Uhm…” Ya amsa ta kansa a kasa.

 

“Na je?”

 

“Ki je Allah ya kiyaye hanya… Allah ya tsare…. K”

 

“Ki tsare mutuncin ki…” Ta karasa fada tana dariya.

 

Shima dariyar yayi. A tare suka futa daga cikin parlorn bayan ya dakko kudi ya mika mata. Dakyar ta karba saboda ko jiya ya babbasu kudin kan tsaraba da sauran su.

 

Ta balcony ya hango ta futa. Ya sake sauke wata nannauyar ajiyar zuciyar kawai ya cigaba da salati.

 

Tana fita ta tare mota ta shiga ta zauna. Direba ya tanbayeta adireshin inda zai kaita ta amsa shi tana kallon agogon da ke daure a wutsiyar hannun ta.

 

Har kofar shirgegen shagon ya kai ta ta mika masa kudin motar ta shiga ciki…

 

Kai tsaye ta shiga cikin katafaran shagon siyayyar. Ta wuche wajen dogayen riguna. Hamdala ta sauke a lokacin data hango rigar data dorata a burnin ranta saboda tsabar kauna. Har da ita acikin sale din.

 

Don haka, Nan da nan ta dauka ta duba size dinta. Komai da komai yayi dai dai. Don haka ta karasa wajen biyan kudi ta biya kudin rigar tare da matsawa wajen talkalma ta dauki wasu flat guda biyu.

 

Ta dauka shima ta biya. Ranta fes tayi hanyar fita kenan ta na kallon hannun ta na hagu ta hango masu milkshake suna ta hadawa kala kala.

 

Da sauri ta karasa wajen ta sa akai mata hadin chocolate chunks. Tana tafe da shi a hanyar fita.

 

Rike yake a hannun ta na hagu. Yayinda Jakarta da suaran kayan ta na hannun dama a kafada.

 

Mayafin ta ne ya shiga yayewa a lokacin da wata niimatacciyar iska take turara wajen. Mayafin ya yaye gefe sosai. Ta soma jansa da gefen habarta wajen kasar habar sosai.

 

Batai aune ba jikake shaaaa . Kofin ya kanchale ya haure ya tangade a kyakkywar t-shirt din bakin balataben dake tsaye a gabanta milkshake har kan fatar idanun sa da kan tsinin hancin sa. Harda leben sa duk koina ya samu rabon sa.

 

Jikin ta ya fara kyarma. Nan da nan ta tuno magnar abbiey. Da ta amince ya hadota da dakarai da kilan hakan bata faru ba.

 

Ta ja baya da sauri ta ajiye kayan hannun ta. Jikin ta ya fara kyarma sosai. Yayin da shi kuma ya runtse idanun sa.

 

Cike da takaicin abunda ta aikata masa. Badan mace bace da tuni ya dade da wanketa da mari don haka ya bude idanun sa ahankaki ya sauke su a kanta. Alokacin ta curo tissue paper da yawa tana kokarin tunkarar sa ya shiga ja baya.

 

“أرجو أن تتقبلوا أعمق اعتذاري”

 

Bata karasa ba ya kwace tissue din hannun ta ya chusa a bakin ta.

 

Bai jira sake cewar ta ba yayi gaba yana gurnanin numfashi tamkar matashin zaki.

 

Bayan sa tabi da kallo ‘Hisham 07’ aka rubuta a bayan rigar. Ta mike dakyar tana yatsuna fuska. Jakarta ta dauka ta kayan ta tayi gaba tana jera kananun tsaki.

 

Bandakin shagon ta shiga. Ta wanko bakin ta da fuskar ta. Hannun ta kalla lokacink agogo. Da sauri ta fice daga ciki ta tare mota ta shiga.

 

Gabanta na dukan tara tara. Sanin lokacin tafiyar su airport yayi….

 

 

 

 

File Name   Bakon Munafiki… Hausa Novel Doc.
Title   Bakon Munafiki Complete
Author    Miss Xoxo 
Group    Ai  Hausa Novels
Genre    Fiction Story
Published Date    17/07/2024
File Size    200KB
Format Size    TXT
Book Price    Paid
Phone No
Download Bakon Munafiki Complete Novel Document By Miss Xoxo

Click the below green button to read the novel online

 READ THE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

 

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button