Uncategorized

Matar Makaho Hausa Novel Chapter 2

MATAR MAKAHO

Chapter 2

By Rukayya Ibrahim.

 Shanyan kayana da sukaye datti harda zanin gado Ashanye a igiya an wanke  harda kayan yayan Khadija (MAKAHO) 

Khadija na gani cikin kitchen, tana aiki,

* a Hankali na daga kafata na Isa kitchen in,

 “Khadija kece akitchen?” da murmushi a fuskarta ta amsa mini da Aunty, Naga har Rana baki tashiba shine na daura Miki Abinci shinkafa da wake miyane ban Gama ba ya kusa,

“Kayan nan fa waya wanke ?”

Nice Aunty ta bani Amsa, *wallahih in banji Dadi ba nayi karya sosai naji yarinyar ta shiga Raina sosai da fara’a nace Mata” gaskiya Khadija nagode wallahih Amma aikin ya Miki yawa da baki wanke Kaya ba,

La Aunty babu yawa fa kayan, ta bani Amsa 

“Khadija tashi muyi Sallah tukum tunda miyar kin daura a wuta”

..Toh Aunty 

Sallah mukayi, na sauke abinci na raba na zuba Masa na hada Kamar jiya,  na Bata ta Kai Masa  ” in kin Kaifa ki dawo Khadija”  da toh ta amsa mini,

Tana dawowa na iba Mana nida ita a plt daya, Muka zauna a waje munaci muna Hira cikin hiran nema nakejin ainahin sunan sa a bakin Khadija Ashe   *Al’ameen* ne sunan sa saboda larurar da Allah ya daura Masa shine aka batar da sunan zuwa MAKAHO Kai duniya, 

“Tambayar ta nayi a gidan nan take”?

Ah ah Aunty ni agidan Goggon mu nake ,

“Har wani unguwa ne haka”?

Ta bayan layin nan ne tsakanin mu ba nisa sosai Aunty,

Sosai muke Hira Kamar mun Dade da sabawa,

 “Aikin dare na hanatayi nace ta Huta ni nashiga kitchen nakama girki* 

kin zama tayi dutsen guga ta dauka ta fara gogan kayan da ta shanya duk yanda na hanata sai da ta gogi,

4:10  na yamma tace min zata tafi hanata, nayi sai da na Gama girkin abinci na sata tayi wanka Kayana na Bata cikin dogayen rigunana nakanti na Bata daya Dayake tana da tsawo sosai ya zauna Mata na hada Mata da gyele medium size kalar fulawar rigan,

Sosai kayan ya karbe ta na hada Mata da Mai turare harda powder,man baki, da Jan baki biyu, maskaras da sauran kayayakina da basa cikin set na make-up kit Ina na babata daker ta karba sai godiya take min,

KARANTA: “MATAR MAKAHO PART 1 HAUSA NOVEL”


 *nayi nayi taci abinci dare  Amma Taki,zuba Mata nayi a kula Taki karba sai da nace Goggo zata kaiwa kafun ta Amsa ta wace,

Fitar Khadija sai da ta biya wajin yayanta sosai take basa lbrn abin arziki Dana Bata da irin sakar Mata fuska da nayi,

Har cikin ransa yaji dadin  daraja.masa kanwa danayi sosai,

Hatta damuwar da ya fita da ita na safiya ganin yanda yau na tashi da zafi zafina abin ya tsaya Masa a Rai,

Wannan abinda nama Yar uwarsa tilo da yafi so  sai yaji zuciyansa wasai. 

Mangoro ya bata hade da naira dare ta rike a hannunta ya kara Mata nasiya sosai da hakuri A duk inda Allah ya ajita  kafun ta wuce,

*Khadija na fita wanka nayi nasa siket in kanti da t-shirt Mai kyau na daura gyele karami a kaina laptop na…..

Sai kusan shidda ya dawo gida yauma da kwandon sa a hannu, da sallama a bakin sa *amsa Masa nayi, kaina nakan laptop, *

Wanka yayi ya tafi masallaci yauma Bai dawo ba sai Isha waje na fita ganin yau ba NEPA, na fitar Mana da babban darduma na shimfida, 

*abinci na iba masa, nasa nawa na aje  Mana tare da Masa Bismillah zama yayi shima Muka fara ci *

Khadija ta tsanar Dani abin arzikin da kika Bata na gode, naji muryansa cikin sanyi sanyin sanan,

Ba kome wallahih abinda ba yawa,

Jin yanda na Masa magana a mutunce abin sai ya Masa Dadi sosai, mun Gama cin abincin har lokacin NEPA shuru na kasa shiga dakin saboda tsananin zafi da ake yau ga sauro,

Tashi yayi ya fita yaje ya sai Mana maganin sauro, Yana dawowa na karba na kunna,

 kitchen na shiga na yaga caton in indomie, zanyi fifita dashe,

* Wanka na sake shiga tsaban zafin da nake ji Kaya nasa vest sai wando Yale yale dogo har kasa,

Kushin na dauko a daki na zuba akan cafet in na kwanta Ina fifita,Yana zaune a gefe shima ya jingina da jikin gini,

Shuru mukaye dukan mu ba Mai magana,shikam tunani yake azaman da yaye da Sumayya ya fahimci Abubuwa cikin halayan ta,

 in Abu ya Bata Mata Rai, toh kowa ta shafa, in aka faranta Mata kowa zaiga fara’ar ta akwai ta da tsafta akwai iyya girki ga nutsuwa sam.bata da rawan Kai,

*Har Sha biyu bamu shiga ba, ganin dare yayi  ban tashiba ya mike a hankali yaji ya rufe kofar shashen mu, ya dawo ya shiga dakin  ya cire kayan jikinsa yadau wando  iyya gwuiwa sai riga Mara nauye , ya dauko filon kujira ya rufe kofar dakin harda k’wado   key in yasa a cikin filon sa,

Dawowa yayi ya tsaya a gefe cikin sanyin jiki yace “uhmm Daman Naga Kamar baki shiga daki ba kwanan waje zamuyi kenan?

“Eh wallahih Amma tunda akwai maganin sauro”?

Sake tambaya yaye in akwai wani abin kwanciyan a bani,Gefen dardumar na nuna Masa ya kwanta hade da furta” ita dayace” kwanciya yayi tare da Addu’an bacci, a hankali bacci ya dauke sa

*Sai kusan karfe daya kafun bacci ya dauke ni da ker’

Saboda rashin samun bacci da wure da bayi ba shiyasa yau Bai tashi yin sallar dare ba 

*Nikam ban sake sanin kaina ba sai asuba……..

*A hankali nakejin sanyin asuba na  ratsani har cikin kashi kowa yasan yanda sanyin asuba yake alokacin zafi,

*Juyi nayi a hankali Amma sai me jina nayi Kamar Abu ya tukare ni, bude ido nayi sosai, me Zan gani ni Sumayya  a kwance rabe-rabe a jikin MAKAHO, ai bansan sa’ilinda da na wantsala gefe ba, kwalbar maganin sauro na buge harya fadi a simintin dakali, ya fashe

KARANTA: “MATAN ASOKORO HAUSA NOVEL”


Jin Karan fashewan Abu shiya farkar dashi cikin sauri ya mike Yana tambaya ta lfy?

**Nikam na kasa basa amsa toh me zance? cewa zanyi ka tabani Koh Kuna nace ajikinka na farka na ganni *

Cikin Dan daburcewa nake magana” am am Babu fa Daman na tashine ban sani ba na buge kwalba ya fashe”

Bai dai ji Miki ciwo ba ya fada cikin hanzarin karasuwa wajen da yake jiyo muryata,

“Ah ah  banji ciwo ba”

Ok Allah ya kiyaye gaba, 

*Da Amin na amsa *

Daga ni harshi Alwala muka  hanzarta farawa Jin har anyi raka’a daya a masallaci,

Muna kammala Alwala daki ya bude ya cire kayan jikinsa yadau jallabiya ya saka ya,

 

*Nikam hijab kawai na dauka har kasa, sai sallaya biyu nazo na shinfida Mana Jin an sallame sallah a masallaci, 

*Na hau Kan sallaya Daya nayi gyran  murya *

Jin hakan yasa a hankali ya Suma takawa Yana nufo inda yaji nake tsaye ganin ni yake nufuwa yasa” nace ga sallah na shimfida maka tunda Naga baka samu jam’i ba”

Ba musu ya ringa lalube harya Ji kafarsa ya taka wani abu Mai laushi sosai Wanda laushin ya banbanta da cafet in dakin,hakan yasa she gane sallaya ne ” Hawa yayi ya saita gabar ya Tada sallah Ina binsa,

Muna idarwa Naga ya Kama karatun Alkur’ani cikin suratul Qafe cikin zazzakar muryarsa Mai dauke da nutsuwa irin na mamilallun maza,da Kai (hadda) 

Nima.mikewa nayi na dauko Qur’an na bude Ina duba ayoyin da yake karantawa,harya Kai karshe ba gargada Koh wani harafi an basa hakkinsa, 

sosai nayi mamaki Amma Dana tuna ido kawai Allah ya jarabcisa  ba zuciya Koh k’wakwalwa bane, ba abin mamaki bane, sai da yakai karshen surah.

*Mukaye azkar sai kusan bakwai na tashi nade sallaya nayi nayi waje,

Duk da akwai NEPA hakan Bai saka na kwanta ba fita waje nayi na tattara Mana shimfidar na mayar daki,

Tsintsiya na dauka na share baranda na fara sharan qasa,

Jin Bata dawo ta kwanta ba Kuma yaji tana shara yasa ya mike yayi waje shima,

Gaidani yaye na amsa ba yabo ba fallasa, takalmin sa ya saka cikin lalube yayi kitchen wajen da yasan Ina Tara kwanuka da bojuwaye yafara tattarawa Yana kawowa mawanki harya Gama kwashewa,

Boket ya dauka. Randa ya wuce a hankali ya dau Moda dake Kan randan da hannu daya ya bude randan da daya hannun sa,  moda ya zura a randa zai ibi ruwa yaji wayam,sai da ya rank’wafa kafun yaji  ruwa,

 hakan ya nuna masa  ruwan Randa saura kadan fasa iban yaye ya dauki boket in ya Kama hanyan fita”

Ganin ya Kama hanyan fitane,yasani tambayr sa” Ina zaka da boket kuma”?

Cikin sanyin sa na halitta yace, ruwan Randa saura kadan Inna iba bazaki samu na aiki ba shiyasa Zan Iba a rijiya”

“Rijiya”? Na sake tambayar sa,

Eh yaban amsa, Kamar Zan hanasa,sai kuma nayi shuru na Kama kwashe shara,

Jin bance kome ba yasa shi cigaba da tsayuwa,

*Ganin yaki tafiya yasani cewa “yakuma ka saya”

Fita yayi, ni Kuma na shiga kitchen na Kama hada breakfast,

Yana fita rijiya ya nufa da lalube harya Isa Dayake rijiyar ba bakwansa bane Yana gane hanya,  ya lalube guga a gyfen rijiya, ya zura hade da Bismillah,

sai da ya Bari na Yan second kad’an kafun ya sake dagawa Jin ta cika yasa yaja, sai da ya cika boket dam kafun ya sunkuce boket da hannu d’aya d’ayar hannun yana lalubar hanya har ya samu ya shigo kofar ya zuba a Randa, 

Ganin wahalan da yasha kafa d’aya ma kafun ya kawo duk rabi ya zube Masa a jiki gashe yafi minti 10 daga rijiya zuwa kofar mu Yana lalube kafun ya gane,

Haka kawai na tsinci kaina da” dakatar dashi ganin Yana kokarin juyawa ya karo

Ka bar iban ruwan nan an…. Ban karasa ba saboda ganin  d’aya Daga cikin yaran gidan budurwa ta shigo ba Koh sallama, tana cewa

Wai inji inno ka Bata d’ari biyu zata sai goro, 

Cikin sanyi yace  yau ban kwana da kudi ba sai naira d’ari d’aya kacal Kuma ita nake son saya Mana kayan miya zamu karya, tayi hakuri zuwa anjima inna fita na samu ciniki Zan bada a kawo mata,

Cikin bala’i take cewa eh lallai watoh matar ka tafi inno kenan, dadin abin munsan auren liki aka maka ba Wai don ka Kai abaka ba, shidai kala baice Mata ba.

Ke Kuma  duk kudin da kike dashi Koh nace gidanku suke dashi sai kin jira D’arin karyawa  mtwss,tana fada tana nunani,

*Ai bansan lokacin da nayi  super ba na saya a gaban ta ” keee karki kuskura ki sake sakani a cikin haukarki na jahilci karki yarda  in karta Miki layin rashin mutunci a gidan nan iskancin ku ya tsaya ku wak’u karku kuskura ku sani,

idan takamarku bariki da rashin kunya wallahih ni Zan gyara Miki zama,”

“bace min daga gani” cikin tsawa na karasa maganar,Ina nuna Mata kofa,

Tabbas ta tsorata Dani sosai don Bata dauka Ina da baki haka ba,da saurinta harda tuntube ta fita,

Juyawa nayi na kalle sa Yana tsaye Kamar ruwa yacisa,

KARANTA: “MAKAUNIYAR KADDARA COMPLETE DOCUMENT”


Wani abu Mai kamada tausayi-tausayi takaici-takaici ya kamani, ganin kwata kwata na rasa me yasa Yan gidan nan suka Raina Masa wayone oho,

*Daki na shiga na d’au jakana gudan dubu na dauko * fitowa ta yayi daidai da shigowar wata dattijuwar Mata cikin bala’i ta,toh Ina kike karamar Mara kunya, harkin Isa ki shigo gida jiya jiya ki nuna Mana iskanci, Daman tunda Naga yau kwananki uku a gidan nan Koh gaishemu baki zo kinye ba nasan ba banza Kika rasa miji ba Rana tsaka aka lika Masa ke,

* ba tare da na kalle taba nace, 

“Yayan khadija pls ka Bata kudin da ya kwana a aljuhunkan, ba musu ya lalube jallabiyarsa ya d’auka ya Mika mata, fizga tayi tana ta tsababi zadai kaji da munafurcinka, 

*daga ni harshe bamu tanka mataba harta fita,

*Albarkacin girmanta yasa naja bakina bance kome ba,

Jin ta fita yasa na Mika Masa dubu d’ayar “gashi ka sai kayan Miya Mai D’an yawa  Dana shaye ka hada da Kiran Mai ruwa”

cikin sanyi yake cewa, kiye hakuri Sumayya Nike da alhakin daukar nauyinki akaina bazan iyya karban kudin kiba, sannan Ina Mai baki hakuri da abinda Yan gidan mu sukayi Miki,

Bari naje  na karbo kayan miyan da na shaye,

“Da wani kudi Koh ba yanzun naji kace D’arin ne da Kai ba”? 

Eh hakane Amma Zan karbi kayan a shago Inna fita sana’a Allah ya bada kasuwa tunda mak’wancina ne saina Mika Masa Amma ni bazan iyya karban kudinki ba.

“Au ni in cema akaye kyauta na baka ai bashine Inka tashi ka biyani” nace Masa ganin da gaske bashin xai fita ya karba,

D’an Jim yayi sai Kuma ya karba ya fita, kitchen na koma na sauke macaroni ganin ya nuna na juye a kwando,

Wanke wanken da ya Tara na Kama wanke wa da yake babu yawa plt ne biyu sai cup biyu shukali sai bojuwa biyu, kafun ya dawo harna kammala

 Yana dawowa nayi miyan stew da kefe busheshe manya-manya, guda biyu Wanda aka mini caton guda na gara

Wanka yayi ya chanja kaya  ya kwanta a kujiran daki,

Ina Gama girkin na zuba Masa na Kai Masa daki hade da gyran murya na fita 

Wanka nayi  na shiga daki da towel Mai Dan girma na daura yaukam zama nayi na shafa Mai da powder NASA kwalli sai man baki, 

Yana Gama ci ya ibi Kwanukan yakai waje, *Yana fita na ibi Kayana na saka rigane Abaya Mai kyau sosai ya karbi jikina gyelen na  daura a kaina,

Na kurawa kaina ido a madubi bansan lokacin da hawaye ya taru a idanuna ba,

 *Sun Rabani da aikina sun saka mahaifina ya datse mini Account Wanda da gumina na Tara Rabin kudin da ke ciki,sanan

Kaf jalingo su rasa mijin da zasu aura min sai MAKAHON miji Wanda Koh kwalliya nayi baisan nayi ba,  ni Karan kaina ma, sunar Ina matar sa Bai San ya nake ba, in badai muryata yaji ba bazaisan Ina wajen  ba, me nai musu a rayuwa mina tsare musu basa kaunan cigaba na komin kankantarsa, a matsayin su na Yan uwa ga mahaifina. Duk a Raina nake zancen nan hawaye nabin kumatuna,

Kinyi kyau,

*abazata na juya cikin mamaki jin muryansa a dakin wanda bansan yaushe ya shigo ba Yana tsaye idonsa a…….

Idon sa a saitin gado, Yana kyetkyet tasu, Anasa tunanin ta saitin inda nake kenan,

**Bansan lokacin da dariya ya kamanii ba hawaye nabin fuska ta duk a tare nace”da wani idon kaga nayi kyau wama yace maka kwalliya nayi nii Koh Kaya bansa ba” na fada ina dubansa, har lokacin bakina d’auke da murmushi Wanda har hakora na masu haske, d’auke da hakoran Gwal na makka har guda biyu a gyfe da gyfe na hakoran gaba,

suka bayana,  na  kasa  rike murmushin abin ya, bani dariya especially lokacin da ya furta Kuma idonsa na kallon wani wajen.

Sam ransa Bai baci ba da abinda nace asalima wani sanyi yaji a ransa Jin sautin dariyar ta na farko a Kan kunnensa,

Zuciya tane ya sanar dani kinye kyau 

“Aiku zuciyar taka Bata fada maka daidai ba, don ni banyi kwalliya ba atoh”

Zaki iyya rantsewa?

“na rantse nayi kwalliya Amma tsakaninka da Allah ya akayi ka gane”?

Uhmm bayan kin shiga dakin nan kin zauna akan dressed mirror Ina ji ki aje Abu kamar gwangwanin Mai kinfi minutes 17 kina ajewa da dauka,hakan ya tabbatar min kwalliya kike,

in Khadija tana kwalliya haka nakejin buruntun irin yanda naji d’azun,danake cin abincin

“Lallai fa,”kawai nace nayi shuru 

Zan fita me da me za’a bukata, yace mini

“No ba kome tunda kayan miyar safiya zai Mana kwana biyar Koh hudu” kaga daidai ya kare ka biyani kudina,

Ok sai na dawo”toh” nace Masa yasa kafa ya fita 

*Komawa nayi na zauna Ina maijin haushin kaina Dana sake baki Ina tanka masa, 

kunna TV nayi ga fanka na kadawa k’wanciya nayi Ina kallo,Tashar zee cinema ana kallon wani film Mai suna bang bang sosai film in yamin dadi,

10:00pm naji sallaman Khadija mikewa nayi Ina amsawa na fito waje itace tsaye hannunta d’auke da kulan jiya,

Ina kwana Aunty,

“Lafiya Alhamdulillah ya Goggo”?

Lafiya tace a gaidaki,

“Aiko Ina amsawa”

“Ki shigo mana” 

ah ah Aunty tafiya zanyi yanzun

” Aiko baki isaba shige muje ciki yau ini zamuyi”

Ba musu ta shigo dakin Muka zauna muna kallo sai 11:00 na mike na shiga kitchen Zan fara aiki, sai ganin Khadija nayi itama ta shigo,

“Ah ah fa Khadija yau Kam zama zakiyi ki huta” 

Yanzun Zan kammala “

Ah ah Aunty wallahih bazan iyya zama kina aiki ba Zan dai tayaki,

Ba yanda na iyya  haka Muka Kama aiki sai 1:30 Muka kammala tuwo da miyar kuka, nayi Tuwon da yawa harda na dare kawai, na huta d’aura sabo, zubawa yayan khadija,akula na zuba na dare a wani kulan  na rufe, mukayi sallah ta Kai masa nasa, 

tana  dawowa na zuba Mana  munaci muna Hira,

“Nikam Khadija wani school kike zuwane”?

Aunty bana zuwa makaranta ai

“Ban gane ba Khadija”

Eh na kammala junior set. 

“Shine zakice kin Gama karatu”?

Eh Aunty na Gama jss 3 Amma ban daura  senior set ba

“Me yasa”?

Shuru tamin Naga alama batason bani Amsa 

,Nima ban takurata ba,

Na chanja zancen da, wani,

“Khadija nikam akwai Wanda kika sani ne? ta iyya kitso, budurwa haka tazo tamin a gida Koh guda shida so nake na wanke kaina”  

Aunty Baga kanki a tsefe ba bazaki wanke ba sai an kitsa?

“Aii Khadija bana iyya wanke Kai a tsefe sani ciwon Kai yake” 

Lallai Kam aunty bara mu kammala ci na kama Maki  Kan in mun gama,

“Au kin iyya kitson kenan”?

Zandai Kama Miki, “Koh Zaki chanchara mini ba”

Hh toh na yarda.

Muna Gama cin abinci Khadija ta Kama mini kaina guda shida, na tashi naje nayi wanka na hada da Kai,

*Sai dana rike Khadija har yamma kafun na barta,ta tafi,

Sai yamma ya dawo  Kamar yanda ya Saba haka yauma yayi wanka da sallah sai Isha mukaci abinci yau akwai NEPA tun na safe har yanzun Basu dauke ba dukan mu muna zaune a daki Ina kallo shima dai idonsa biyu, sai 10:25 na sa kayan bacci  muka kwanta, 

Misalin karfe daya na dare na farka da wani irin azababben ciwon ciki Wanda tunda nake da wayo bantaba yin irinsa ba,

 Mai tsanani gaskiya tun Ina daurewa har dai na fara kuka Ina nishi duk iskan fankar da yake kadawa a dakin gumi nake,

Cikin bacci yakejin kuka-kuka, Nishi daga ji na azaba ne, cikin D’an hanzari ya mike ya sauka a kujiran cikin azama yake magana muryarsa na rawa,Jin da gaske Sumayya ce Mai kuka da Nishi 

Sumayya!! Sumayya!! Lafiya kuwa ya fada Yana laluben inda nake, 

nikam saban azaba nama tsullubo kasan cafet daga Kan gado Ina durkushe reke da ciki,Koh amsa na kasa basa,

Da lalube ya lalubo ni kafada ta ya dafa yana cewa, muryar sa na rawa,Sumayya lfy meke faruwa ne kimin magana mana,

“cikina ” nace Ina Kara fashewa da kuka,

Hankalin sa in yayi dubu ya tashi, hannu yasa ya dauke ni cak kamar ya dauki Yar baby da lalube ya daurani akan gado.

Nikam tashin hankali Bai barni nama San ya dauke ni ba, tsaban azaba, jikina har bari yake ,, sosai hankalinsa ya Tashi ,mikewa yayi zai fita cikin rawan jiki na kama Masa hannu na damke cikin nawa dake rawa sosai, ciki muryan ciwo yaci karfina nake cemai”D’an Allah karka tafi ka barni Zan mutu ka mikamin waya ta na Kira babana karna mutu”

Sosai zuciyarsa ta tsinke Jin tana am batar mutuwa,Amma ya daure cikin sanyi murya yake cemin Kinga yanzun dare ne Bai kamata ki kirasa a daga Masa hankali ba,

 bara naje Koh Allah zaisa na samu iro ya kaimu asibiti da keke napep NASA kinji, sannu,

**Gaskiya ya fada hakan yasa na sakar Masa hannu ya fita,

Waje ya fita Yana lalube ya dauki sandar sa a dakali da lalube ya fita a kofar shashen Yana lalube harya Isa hanyan kofar gida wanda ke dauke da d’akunan samarin  kusan bakwai,

 a kofar dakin iro ya tsaya ya fara buga Masa kofa Yana Kiran sunan sa,

Cikin bala’i ya bude kofar ya fitoh kai don Allah lafiya Ina cikin bacci karfe daya zakazo ka bugamin  kofa Dan wulakanci kome,?

Don Allah iro ka taimake matatace ba lfy sosai shine nace Koh zaka taimaka mini ka kaimu asibiti,

Buran uba a Daren nan ba shegen da ya isa yasani in fitoh wallahih Koh inno ne ba lfy ba inda zani bare wata banxa Wai matarka don Allah ware ka ban waje nikam, Yana Gama masifar ya koma daki ya banko kofar,

Haka ya juya don yasan tunda har iro yace bazai taimake Saba ba Wanda ya Isa yasa sa daukan su , waje ya fita Amma titi shuru. Ba motsin kome,yakai minutes 30 baiji motsi ba dole ya hakura haka ya juya da sanyin jiki ya koma cikin gidan,kofar ya shigo cikin hanzari ya Isa dakin har yanzun dai kukan take,gadon ya hau a hankali ya Isa gareta cikin sanyi yake ce mata, don Allah Sumayya kiye hakuri wallahih ban samu abin hawa ba,

cikin muryar kuka nace “ka dubamin wayata tana Kan dressed mirror,ka bani na Kira Abie”

Ba yanda ya iyya  dole ya Bata wayar  ganin irin azabar da take Sha gashi ya kasa Nemo Mata mafita ga ciwo na cinta,

Sauka yayi a gadon Yana lulube harya gane dressed mirror in, har Allah yasa ya samu wayar mikamata yayi,

Karba nayi cikin Nishi nake lalubo number Abie na na Kira yakai sau biyar baya dagawa Daman tun Randa aka kawoni gidan nan Koh na Kira sa baya dagawa sai ana biyar in nayi sa’a ya daga cikin muryar kuka nake cewa abie Zan mutu cikina ciwo kazo ka kaini asibiti,, 

abinda naji abina ya fada shiya Kara hargitsamin k’wak’walwa, yau nice yau abie ke cewa  Inna mutu baida asara Kuma karna sake kiransa tsakiyar dare Yana bacci,

**Anya abie nane kuwa? Mai Sona da tausayina Mai son ganin farin ciki na yake furta wannan magana gareni,shikinan shima abie yanzun baya Sona 😭 wayar na sake daurawa a kunne na Amma abie ya kashe call in ban daddara ba na sake kiransa wannan Karo Kam line busy ya Danna mini.

**Me nai Masa lfy lfy Muka rabu cikin kewan juna da Addu’a tare da fatan alkhari hade da nasiha,

bansan lokacin da wani sabon kukan ya barke,min ba

Sosai hankalin Al’ameen ya Tashi baisan lokacin da ya iso garita ba ya Kamata ya runguma cikin wani irin yanayi na tashin hankali yake lallashin ta,

**Kara rungumar  sa nayi na yenyene Masa  ajikinsa Ina kuka maitaba zuciya wannan kukan bana ciwo bane kadai  harda na bakin ciki Abiena shima ya juyamin baya adaidai lokacin da nafi bukatar sa,

Haka nayi ta fama da ciwo daga ni harshe bamu rintsa ba sai addu’i yake tufa mini har hudu na asuba,

Yaji taja numfashi da karfe sai Kuma yaji kome nata ya sake Daman har lokacin tana jikinsa,

 cikin wani irin rikice wa jinta ta Bata motse yasashi mikewa ya sabeta cak  a kafada Yana lalube ya fita a dakin Koh kofar Bai rufe ba tsabar tashin hankali,fita yayi a shashen  yayi hanyar kofar gida…………..

Haka ya ringa lalube don Koh sanda Bai rike ba ya fita waje, da ita,yaje

 titin shuru haka ya ringa takawa a Gefen titi ba tare da yasan inda zai nufa ba,

cikin ikon Allah sai ga wani Mai mota yazo wucewa ganinsu cikin wani Hali yasa shi tsayawa a saitin, Al’ameen Yana tambayar sa lfy kuwa ya gansa da mace a bakke a kafada Bata motse gashi Koh takalmi babu a kafarsa da asuban nan?

Da sauri ya juyo wajen da yakejin muryar Mai motan don Allah ranka shi Dade ka taimaka mini matatace ba lfy wallahih tun jiya yanzun haka Suma tayi Ina son kaita asibiti Amma ban samu abin hawa ba,

Allah sarki shiga muje Nima kwanace ta kamani a hanya sai yanzun na shigo gari,

Allah ya saka nagode,ya fada Yana laluben murfin mota tsabar tashin hankali Yama  kasa budewa ,abin ya bawa Mai mota mamaki, yadai malam lafiya Naga kana lalube baka shiga ba,?

Bana ganine,ka taimaka ka bude mini,

Ba karamin mamakine ya Kama Mai mota ba ace mutun Kamar Wannan baya gani lallai Koh wani bawa da kaddaransa,

Fita yayi yazo ya bude Masa 

A hankali ya shimfida Sumayya asset in baya shima ya shiga Mai mota ya rufe ya zagaya shima ya shiga mazauninsa yaja motar ,

Wani asibiti Zan kaiku?

Duk asibitin da yafi kusa damu ka kaimu 

Ok ya kara gudun motar lokaci kankani  suka iso FMC don yafi kusa da SINTALI ( sunan unguwansu Al’ameen)

KARANTA: “TUBALI BOOK 1 COMPLETE DOCUMENT”


Suna Isa emergency Mai motar ya kaisu fita yayi ya shiga Hall in ya Kira nurses za’a d’auki Mara lafiya suka fitoh da sauri aka aza Sumayya bisa keken marasa lfy aka wuce da ita dakin taimakon gaggawa,

Likituti suka,rufu a kanta don Bata taimakon. Gaggawa 

shi kuma nurse tace Masa yaje ya sai Mata card a bude mata file,

Wajen sai da card in ma da taimakon Mai motar ya gane, 

kudin card naira 300 matar da ke windown tace,

 ba karamin tsinkewa yayi ba sai yanzun tunaninsa ya dawo jikinsa, don Koh sisi baida shi sai naira dari da hamsin na cinikin jiya, ya Allah ka taimake ni abinda ya ke fada kenan a ransa,

Malam.koh bakaji bane nace 300 ne kudinka  shuru yayi Yama ya kasa magana,

Mai motar ne ya fahimci Koh sisi baida shi kenan

 fitar da dari uku ya Biya kudin card 

Menene sunan majinyacin?

 tambayar sa akaye me sunan Mara lafiya, Sumayya

,sunan surname?? Shuru yayi yana tunani a hankali yace Abdulsalam shugaba,ya fada Dan in Bai manta ba haka yaji agun daurin aure aka fada,sai da ta daga kai ta sake kallonsa Jin sunan da ya fada amasayin sunan mahaifin maralafiyar da suka kawo,

lokaci kankani aka bude Mata file in ,

Yama rasa bakin godiya sai gode ma mai motar yake, nagode nagode bawan Allah ba abinda zance maka sai Allah ya saka maka,

Ba kome ai ka gode Allah,

sunana Ammar Ina zaune da iyayena a unguwan millionaire’s sweet,ya fada Yana Kama hannun Al’ameen Yana Masa jahora zuwa masallacin asibitin sukayi sallah suka dawa Kan kujirun da ka jera a Hall in,suka zauna,

Nurse ce ta fitoh tana tambayar suwaye suka kawo Sumayya Abdulsalam shugaba?

Mekewa sukayi Ammar na rike da hannun Al’ameen suka Isa wajen da take 

Gamu nan 

Mika musu takardan magani,doctor yace ku saya  maza-maza don ana bukatar sa emergency,

Hannun Al’ameen na rawa ya amshi takardan hade da tambayar ta don Allah ta farfado ne ya jikin nata,??

Eh ta farfado Amma ana bukatan kuje ku sai Abubuwan da aka rubuta muku,..

Kama Masa hannu Ammar yayi suka wuce pharmacy suka je 

Mika takardan maganin sukayi

 karba sukayi suka duduba ruwane da allurai sai maganguna,

Kudin ku naira dubu bakwai da dari biyar,

Shikam Abu ya hade Masa goma da ishirin Ina zai samu kudi Mai dunbin yawa har dubu bakwai da dari biyar,

 Koh Kama sayar baidashi bare ya Kama ya sayar ya Saya mata magani Innalilahih wainnailaihir rajuun yake furtawa hade da karban takardan balance ya fita tsabar rudewa shikamma ya manta da wani Ammar suke tare,

Ammar ne ya biyosa ganin yana faman lalube zai fita a pharmacy in da sauri ya rike Masa hannu,

Habba Dan uwa karka dagawa kanka hankali Mana Yana fada  ya karbi takardar ya rike hannun Al’ameen suka shiga waje biyan kudi

Ammar ya biya kudin suka karbi magangunan da su ruwa da allurai suka Kai emergency, suka mikawa nurse in ta shiga dakin,

 sai a lokacin hankalin Al’ameen ya kwanta sosai yayita ma Ammar godiya shikam ma har kunya ya kamasa Kamar  Wanda ya bawa million biyar,. 

Sai 8:30 aka barsu suka shiga suka ganta  ta farfado Ansa Mata ruwa da alluran bacci don ta samu hutu sosai  ciwon ya lafa

Toh abokina Zan wuce Naga gari ya fara wayewa gashi sai kirana ake daga gida kasan Dana shigo *Jala* na Kira gida nace musu na shigo,

Ba kome wallahih nagode sosai Ammar Allah ya saka da alkhari 

Habba wanna godiya ya Isa haka,baka fadamin sunan kaba fa har yanzun?

Suna na Al’ameen,ya basa amsa

A unguwan da na dauke ku kake ? 

……Eh 

Ok toh insha Allah  Zan dawo na duba Mai jiki 

Nagode nagode Ammar

Sai anje ma, ya fada Yana kokarin fita a Hall in sai Kuma ya dawo,

  Koh xan kaika gida ka dauko Mata Kaya da Abubuwan bukata Kamar Kayan da zata chanja su maclen da brush da abubuwan bukata kaima ka samu ka kimtsa jikinka Naga Kamar a birkice ka fitoh Koh takalmi babu nasan har yanzun baka San kafarka ba takalmi ba hh ya fada cikin wasa Yana dariya,??

Shima Al’ameen in dariya yayi kawai, Yana cewa toh muje don wallahih rudewa Kam na rude,

Hannunsa Ammar ya rike masa suka fitoh ya bude Masa mota ya shiga ya ja suka wuce, suna tafiya suna Hira 

Amma dai ku sabbin aure ne Koh?

Eh yau kwanan mu hudu,

Kai kace ango ne da kansa Koh dai Mai kashane, amarya har asibiti

Dariya kawai Al’ameen yayi baice kome ba don bazai iyya fadawa Al’ameen sirrin Saba duk da yaji bawan Allah ya kwanta Masa arai Yana da kirki sosai koma zasuyi sa’o’in juna Amma hakan bazaisa ya tsake jiki dashi ba don mutumin duniya ba abin yarda bane lokaci guda,

Sun Isa har inda ya dauki Al’ameen tukunna ya tambaye sa sun iso wajen da ya dauke sa da asuba ata Ina gidan naku yake?

Ah ah Ammar sauke ni ma anan na gode 

ah  ah kaidai kamin kwatance 

Ah ah wallahih hakan ma nagode,ganin ya nace yasa Ammar sauke sa

Sukaye sallama

A hankali Al’ameen ke tafiya Yana Dan yaryarfa hannunsa don Ya tabbatar  inda yake sa kafarsa ba mutum Koh wani abu inda Allah ya Sosa ma tsallaken titine aka sauke sa ta barin gidansu a hankali yake tafiya Bai Ankara ba yaji an bangajesa haryaso faduwa saura kadan da yakai kasa, wani zafi yaji a yasansa don ya buge dutse sosai yatsan ke Masa zafi a hankali ya mike, Jin Wanda ya turesan Yana bala’i, ku wasu irin mutane ne in ka San baka gani wani rawan Kaine zaisa ka fitoh babu D’an jagora babu sanda, irin hakane ai sai ku hau titi mota yabi ta kanku kujawa mutum jaraban jinya inkun mutu Kuma kusa mutun azumin kaffara mtwss,,

Ya fada Yana tafiya 

A hankali Al’ameen ya d’uka ya taba yatsar Jin damshi yasashi gane jini ke zuba,

Bai damu ba ya cikaba da tafiya har Allah yasa ya iso kofar gidansu ya shiga,

Yana shiga cikin gidan ya samu Yan gidan a filin tsakar gida kowa na sha’aninsa daga masu wanke wanke sai masu wanki sai masu kitso masu Jan ruwa  wasu Kuma group aka hada ana ta gulma ana xagin juna,,,

Ganinsa ba takalmi sanan ga jini a kafa Yana zuba, yasa Rabi’u  fara magana Kai MAKAHO daga Ina haka a bujaje yau tun safe ma bamuga fitarka ba?

, kafun ma yayi magana iro dake goge takalminsa zai fita yace Wai fa D’an rainin wayon nan jiya Ina bacci yazo karfe kusan daya Wai nakai matar sa asibiti Bata da lfy kaji Dan rainin wayyo wama ya sani Koh turmushe Yar mutane yayi xaizo tsakan dare yana tashina,,gabaki dayan su suka saka dariya,

Shidai kala baice musu ba hanyan shashen su yayi da lalube harya shiga sai a lokacin ya tuna Ashe fa kofa a. Bude ya barta cikin D’an fargaba ya shiga dakin don shi tsoronsa ma kar Yan gidan su shigo su Ma Sumayya sata don shikam baida abinda za’a sata, wayarta daya Mika Mata jiya da dare shiya fara lalubawa akan kadon aiku yajisa, 

Hakan ya tabbatar Masa ba Wanda ya shigo tunda ga waya a fili Amma da an shigo wayar nan dake zaune a fili haka da an sabe sa hamdala yayi ya gode Allah Basu San ya fita ba,

 iban ruwa yayi yashiga bandaki yayi wanka yasa wasu Kayan  ya rufe kofar ya fita don bazai iyya gane inda kayanta suke ba,

Sandar sa ya dauka ya fita a gidan hanyar gidan Goggo Amina ya nufa,

Yana Isa kofar gidan ya tsaya a waje yayi sallama,

Shan cikin gidan kuwa Khadija nawa Goggo Amina kitso taji sallama Kamar ta yayanta Aiko ita ince amsawa tayi tare da daukan hijab inta ta fitoh waje 

Yana tsaya yaji isowar Khadija  bakin ta na amsa sallaman sa 

Ina kwana Yaya ya aunty?

 lafiya Alhamdulillah Khadija

Ka shigo mana Yaya Goggo ne kawai a gidan yau ?

Toh ya amsa Mata 

Ta Kama hannunsa suka shiga cikin gidan kujira ta aje Masa ya zauna Yana gaida Goggon tasu, Ina kwana Goggo?

 Ta amsa da kulawa 

Lafiya Alhamdulillah Muhammad y’ay’a  iyalin taka?

Lafiya Alhamdulillah sai dai bataji Dadi ba jiya da ciwon ciki ta kwana yanzun ma daga asibitin nake nazo na dauki Khadija tazo muje zata dauka Mata kayayyakinta Koh kadanne Zan Kai Mata asibitin,

Subhanallah Allah ya Bata lfy wani asibiti ne?

Ameen a FMC ne ya amsa Mata

Khadija tashi maza kuje, toh Goggo ta amsa Mata tana mikewa 

Shima Al’ameen mikewa yayi,hannunsa Khadija ta Kama suna tafiya a haka,

Yaya jikin nata da sauki Koh?

Da sauki Khadija Yaya zan bika muje asibitin?

Ah ah Khadija ki tsaya a gidan namu ke dafa mana abinci tunda Kinga asibitin FMC ne babu nisa saiki Kai Mana can,

A wani block ne yaya?

emergency ne

 har suka Isa gidan nasu suna Hira dakin ta shiga ta dau jakan Sumayya  mabi da ket ta Ajjye tana iban Kaya a whtdrp tana zubawa hijab D’aya, sai dogayan rikuna biyu, zani fille fille guda biyu,sabbine kal ta hada da t-shirt biyu, da hula biyu, sai maclen da brush ta hada Mata da kananan Kaya su pants brz da vest  ta rufe akwaitin,

Yaya na Gama Amma dai tunda kace tun asuba kuke asibiti baka samu kaci karyawa ba koh?

Kai Khadija kin cika surutu wallahih inkin gama kika kawo Mana ai zanci,

Amma yaya yanzun fa ana neman 09:30 na safe baka karya ba in kaje asibitin Yaya ka samu abinda zaka saya muku kuci Kaida Aunty kafun na Gama, 

Toh Addata Khadija

Hhh ye Hakuri yayana ..

Baice Mata kome ba illah daukar jakar da yayi Yana lalube zai fita a dakin idon Khadija ya sauka a Kan kafarsa a matsanancin damuwa ganin yatsan sa a kumbure gashi ya karce sosai,

Yaya meya same ka a kafa haka,?

Tuntube nayi kawai yace Mata Yana fita,,

 fita yayi bakin titi Yana tare keke da hannunsa har Allah yasa wani ya tsaya,

Malam Ina zuwa?

…FMC yace Masa 

Shiga muje, da lalube ya shiga keken suka wuce cikin kankanin lokaci suka Isa hospital ya sauke sa abakin get don in ba majinyaci bane a Keke ba’a Bari ta shiga asibitin, ya bawa Mai keken kudin sa naira 50,

Ya Kama hanya da lalube ya Isa cikin asibitin security n get yake tambaya don Allah wani shashine zaibi zuwa emergency don lokacin da suka zo da Ammar a motane bazai gane hanya ba gashi asibitin fadine dashi ga shashe daban daban,

Kabi nan ka Mike  har emergency zai kaika

  haka kuwa yayi har ya Isa emergency Yana shiga ya gane dakinda aka kwantar da ita

 yazo shigane ya hadu da nurse in d’azon tana ganinsa ta rufe sa da masifa

Kai wani irin mutum ne zaka kawo Mara lfy kasa kafa ka fice ka barmu da ita, tun dazun nemanka ake likita nason ganinka,

Kiye hakuri gida naje na dauko Mata kayane

Me yasa she dayan bazai je ya dauka mata ba Kai ka zauna?,

Taimakona yayi Kuma ya tafi,

Jeka aje kayan kazo   likita nason ganinka

Da toh ya amsa Mata da lalube ya Isa inda gadon ta yake har lokacin Bata farka ba,

Juyawa yayi ya fita a dakin sai da ya fita kafun, ya tuna baisan office in likitan bama tambayar wata nurse yayi da taimakon nurse innan ya gane office in doctor shiga yayi da sallama doctor ya amsa masa matashine kamarasa,

Kaine ka kawo Sumayya Abdulsalam shugaba?

Eh nine doctor ya basa amsa

..ok Sumayya na fama da apendes ya kunbura sosai don haka dole za’a Mata tiyata ga wannan sai kaje ka biya kudin,

Atake zufa ta fara karyo Masa Innalilahih wainnailaihir rajuun,likita kudin zai Kai nawa,yafada Yana tambayan sa?,

Bani bane Mai karban kudi  in kaje wajen biya za’a fada maka……………..

Back to top button