Labarai

Matar Damisa Book 1 Chapter 13 Complete Novel

🐅MATAR DAMISA🐅
(The Wife Of Tiger)

*MALLAKIN*
*ASMEETAH* ✍️✍️

*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________

https://www.facebook.com/103637491942644/

💫💫 *{{N W A}}* 💫💫

بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم

*BOOK* *ONE*
*PAGE*➡️ 31 & 32

___________________________

Mom ganin Junaid yasa ta ware fararen idanuwanta baki ya gagara rufuwa tace “Junaid my son, taho mana ya ka tsaya daga nesa, am really miss you my son” jiki a mace yake takowa gurin Mom, idonsa kuwa a kan Ayush wacce tin shugowar Junaid jikinta ke 6ari ko ido ta gagara had’awa da shi saboda gudun ganin rikitattun idanuwansa nan, ga wani irin mungun tsoronsa da take ji!

Junaid ne ya zauna kusa da Mommy gwiwowinsa suna gogan na Ayush da sauri ta mi’ke tsaye ta koma kan kujeran dake nesa dasu, shi kuwa ko kallonta baiyi ba sai cewa yayi “Mom what happened to you?”
Mommy kuwa kallon ‘kurilla take yiwa Junaid tana tariyo abunda ta gani game dashi aranta take fad’in “Anya ba mafarki nayi ba, ga fa Junaid lafiya klau yake, toh meya faru da ni?” Idon ta nakan Junaid wanda ya katseta da cewa “am asking you Mom meya faru dake??”
Mom tayi mamakin tambayar da Junaid yake mata sai cewa tayi “what happen to me or what happened to you?”
Junaid kansa ne ya d’aure shifa bai fahimci maganar Mom d’insa ba,
Mommy ce take ‘ko’karin yaye rigar Junaid tana fad’in “jikinka duk ya faffashe, har naman jikinka ake gani, kana saman jikin bango ga kuma jini duk ya wanke maka jiki, Junaid yanzu banga ciwon komai a jikinka ba, wai meyake faruwa ne” idonta duk ya cicciko da kwalla tana abu kamar wata zararriya.
Shifa Junaid abun tsoro ya bashi “karfa ace Mom ta samu ta6in hankali, innalillahi” yana maganar ne a zuciyarsa, ri’ke hannun Mom yayi yana fad’in “nifa lafiya ta klau ba abunda ya sameni, ki kwantar da hankalinki”
Cikin kuka Mom tace “toh meya kawoni hospital”
Kallon yanda Ayush take zaune yayi wani irin harara ya wurga mata sannan yace “Mom ki tambayi wancan yarinyar ita ta Sani” ya ‘kare maganar idonsa akanta.

Ita kuwa Ayush duk abunda suke tattaunawa akai tana jinsu “duk abunda mom ke fad’a gaskiya ne, nasan dalilin daya kawota asibiti sai dai ba nice silar hakan ba, amma yazo yana d’ora mun laifin da banida masaniya akanta” ta ‘kare maganar tana zubda kwalla amma sai dai duk maganganun da tayi acikin ranta tayisu.

Mom ce ta kalli yanda Ayush take tace “Allah sarki yarinyar kirki itace ta taimaka mun a lokacin da na ganka cikin wani hali, tabbas abunda na gani ba mafarki bane amma kuma al’amarin babbane sai dai Kai bazaka fahimci hakan ba”
Ta kalli yanda Ayush take ta kuma cewa “ke alkhairi ce a garemu Ina kuma alfahari dake, nasan ke kika ceto Junaid daga halin da ya shiga, nayi mamakin ganin faruwar hakan, ciwonsa sai gaba yake ba bayaba…..” Adai den lokacin ta face da matsanancin kuka mai ratsa zuciya….

Shi kuwa Junaid kamar ya shige ‘kasi haka yake ji tsabar takaici da ba’kin ciki rufe ido yayi sosai yace “please Mom enough, ya za’ayi kina fad’an sirrina a wannan ‘karamar yarinyar wacce bata mallaki hankalin kanta ba” ya ‘karisa maganar yana watsa mata wani irin kallo na ‘kas’kanci.
A rayuwar shi ya tsani raini especially idan akace macece, ya gama rainawa mata wayo Gashi yana kallon kansa jarumi gashi kuma sojaa…..

Itama Mommy ta fahimci Junaid bayason ta yawaita fad’an matsalolin da suke tattare da shi….

‘Ko’karin sau’ka daga gadon Mom take
Junaid yace “Ina zakije kuma?”
“My son am really tired, I want to go home”…
“Please Mom stay here to tomorrow, kinga jikinki da saura, ga can chicken na taho miki da shi”
Ya mi’ke da saurin sa zai d’auko ledar da ya jefar a bakin door,
Kansa ne yayi wani irin sarawa kamar wanda aka buga masa ‘karfe a ka! Wani irin ‘kara yasau ya dafe kansa, still saitin zuciyarsa kamar wanda aka caka masa mashi haka yakai d’ayan hannunsa kan saitin zuciyarsa yana wani irin kuka mai had’e da ‘Kara….
Mom kamar kamar zata had’iyi ranta ta ce “Junaid my son meya faru kardai ciwonka ne nashiga ukuu…….” Kuka ne yaci ranta ta kasa motsawa.

Itama Ayush tinin ta tsorota da ganin halin da Junaid ya shiga lokaci guda, da sauri ta mi’ke tsaye tana kallon ikon Allah.

Shi kuwa ya dafe kansa da saitin zuciyarsa yana tangal tangal kamar zai fad’i wani irin hajijiya ne mai karfin gaske ya tafi dashi zuuuuu zai fad’i
Da gudun gaske Ayush tayo kansa ta rungume shi yayo kanta sukaje ‘kasi a tare kwantar da kansa yayi saman kirjinta yana fad’in ” Ku taimake ni ku kyaleni haka, bansan laifin mai nayi muku ba kuke azabtar dani, ni to Ku d’auki raina mana na huta, wayyo kirjina wuta yake ci kaina guduma ake kwad’a mun……”

Ayush dake zaune tana rungume dashi duk tana jin abunda yake fad’a amma ta kasa ganewa “shin dasuwa yake maganar?…” Tana maganar zuci!

Hannunta takai ta d’ora saitin zuciyarsa ta zagayo da hannun hagunta ta baya ta dafe goshinsa jikinsa duk ya d’au zafi ga kakkarwar da yakeyi kamar mai jin sanyi, addu’o’i ta fara karanta masa tana tottofe shi,
Lokaci guda kuwa yaji wani irin sanyi acikin zuciyar shi, dafe zuciyarsa da tayi sai yaji kamar ruwan ‘kankara aka d’ora masa,
Ajiyar zuciya yake jaa kad’an kad’an gumi ne ya fara keto masa akan goshinsa..

Ganin haka yasa ta fara hura masa iskar bakinta duk sanyin A.C dake cikin room d’in,
Idonsa a rufe jin iskar da ake huro masa yasa shi yin murmushin da baisan yana yinsa ba ga wani irin yanayi da ta sashi, hakan yasa shi fad’awa cikin mafarkin wannan yarinyar data ceceshi a cikin ruwa
“Junaidddd taho gareni zaka samu waraka…”, tana gudu acikin filawowi na alhurma masu launin jaa gata sanye da doguwar riga fara soll irin wedding gown mai dogon hannu suman gashinta ba’ki ‘kirin kwance a gadon bayanta, yarinyar tayi kalar larabawa! Gudu take kafarta ba takalmi tana kuma sanye da sarkar ‘kafa,

Shima binta yake yana so ya isota amma ya kasa domin har ta 6ace masa baya iya hangota
Tsayawa yayi yana kallace kallace a cikin lambun flowers ko zai hangota, sai ji yayi an watsa masa flowers daga saman kansa juyawar da zaiyi ya ganta a bayansa tana sau masa murmushi ga dimple d’inta sun zauna, (haba kyau haka)

Shima murmushi yake mayar mata
Yace “wacece ke?…..”

Da murmushi akan face d’inta lips d’inta ne kawai suke motsi wanda ba jin abunda take fad’a yake ba
(Toh nidai kamar naji tana cewa)

“Ayyyshh! 👄 Ayyssh!! 👄 Aysssssh!!! 👄….”
Kallon lips d’inta yake yana so ya saurara yaji amma ya kasa,
Hannu ta ware mishi alamar yazo ya rungumeta
Da sauri ya nufeta ya zaro hannayensa biyu ya Kai mata runguma adai dai lokacin ya dawo daga mafarkin a hankali yake bud’e idonsa a cikin yana ganin dishi dishi har idon ya washe
Gani yayi ya rungumi Ayush sosai har numfashinsu yana gaurayuwa
Shi a tunaninsa yarinyar ya runguma ta cikin mafarkin sa,

Mommy hankalinta ne ya kwanta ganin Junaid manne a jikin Ayush yayi Luum yanata sau murmushi ido a rufe…

Ita kuma Ayush ta kasa sakewa ganin yanda Junaid ya ‘kan’kameta a gaban Mommy duk da ba’a cikin hayyacinsa yake ba
Amma tasan yanzu hankalinsa a kwance yake…..

Doctor Hasheem ne ya shugo duba Mommy shi da nurses en mata su biyu, ganin Junaid rungume da Ayush suna zaune abun ya basu mamaki suka tsaya suna kallon ikon Allah.

Ita kuwa Ayush kunya duk yabi ya isheta ji take kamar ta nitse ‘kasa….

Junaid yana farkawa yaga a halinda suke a razane ya mi’ke tsaye yana maida numfashi, itama Ayush tashi tayi ta tsaya a gabansa,

Wani irin hankad’a yayi mata ya tureta baya sauran kad’an ta fad’i ‘kasi amma ta bugu da jikin gini
Yana fad’in “whattt! Are you crazy, ni zaki runguma? Ni zaki bawa kunya a cikin mutane? Banza ‘kazama fool like you…”
Yana magana yana nuna jikinta da hannunsa, sannan ya kuma cewa
“As from today kika ‘kara gwada mun wannan iskanci saina murd’e miki wuya,
Are you going to rap me? Eh answer me nace kinaso kiyi mun fyade ne? Karo na biyu kenam Ina samunki a jikina because you are a useless, mtsswws shameful girl….”

Yana gamawa sai fuuu yayi hanyar fita daga cikin room d’in da sauri nurses dake wajen suka bashi guri ya fice..

Yana fita kuwa nurses suka kwashe da dariya
Suna fad’in “woo gaskiya kinji kunya har ki kawowa namiji hari kin ganshi gantsalelen saurayi…..” Basu ‘karisa ba Dr. Hasheem ya daka musu tsawa sukayi waje suna gutsiri tsome
Inajin d’aya daga ciki tana cewa “muma munyi kwad’ayinsa mun bari, ina ma ace nice na rungume shi haka wayyo dad’i amma sai dai Ina gudun naushi…….” Suka ‘kara tintsirewa da dariya…….!

Bayan fitar su kuwa
Ayush fashewa tayi da matsanancin kuka ta dur’kusa gwiwowinta a ‘kasi ta kifa kanta ‘kasan tiles tana sheshshe’ka kukanta mai cin rai……

Girgiza Kai Dr. Hasheem yayi Sam baiji dad’in abunda Junaid yayiwa yarinyar nan ba
Shi kansa Dr. Yasan lalurace tasa kuma banda iskanci irinta Junaid shine fa yake rungume da ita..

Mommy itama ‘kololuwar ba’kin cikine yasa ta kasa yin magana
Kamar zata fashe da kuka itama.رَّ

A ranar a asibiti suka kwana mommy da Ayush,
Dakyer Mommy ta iya rarrashin Ayush akan wulakancin da Junaid yayi mata, zuciyarta ya sosu sosai sai dai duk fad’an dayafi karfinka saika mayar shi wasa!!
Inda sabo ai an saba indai akan halin Junaid ne.

Zuwa washe gari da safe Ayush ta mance da Abunda Junaid yayi mata, zuciyarta wasar yake, Ayush bata saka abu aranta sannan da wuya tayi fushi akan abu, duk abunda Junaid ke mata ko sau d’aya bata ta6a tsanarsa ba saima ‘Kara sonshi da take yi!
Tin ranar da Baba tsoho ya sanar mata shine Junaid d’in da Umanta take magana akai
Saita fara jin tausayinsa da kuma sonsa domin tabbas an cutar da rayuwarsa …

Shirye-shiryen komawa gida suke, sun kuma shirya tsaff, Junaid ne ya shugo hannunsa ri’ke da key d’in motor
Fuskar kuwa a murtu’ke ba alamar annuri ga idon yayi wani irin jaa, hatta fuskarsa sai data canza yayi kamar wanda aka watsa masa ruwan zafi duk ya yi wani iri kamar kamar dai gashi nan dai an canza masa kamanni, ga wani birtsi-birtsi akan fuskar kamar tabon duka, gaskiya yadaiyi muni a wannan karan..

Sai huci yake shi kad’ai
Mommy na ganinsa a haka tayo kansa tana fad’in “My son lafiya kuwa? Meya faru da Kai? Dambe kukayi ne?…….” Bata ‘karisa maganar ba ya katseta da cewa “please mom nazo d’aukanki ne bawai sauraron Questions d’inki ba” yana kaiwa haka ya kawar da kansa gefe fuska a cur6une.

“Innalillahi Junaid meya sameka akan wuyan ka? Kamar yagunin kare, wallahi faratun kare nee… Tana shirin kuka tana fad’in “dan Allah my son talk to me meya faru dakaii???”

Juyowa yayi yana kallon Mom kamar zaiyi kuka yace “ba kare bane, Damusa ne!”

Cikin firgici Mom tace “Damusa kuma aina? Aina kaga Damusar? Jiyan ka sake mafarkin Damusan ne?” Ta karisa maganar tana kallon fuskar sa wanda hawaye ke tsiyaya daga cikin idon jarumin sojaa!

“Mom! Ba mafarki nayi ba, a zahiri yazo mun, ya kawo mun hari, amma na samu na ku6uce masa karki damu..”

Fashewa Mom tayi da kuka ta kifar da kanta akan kirjin Junaid tana fad’in “Allah ka kawo mana d’auki a cikin al’amuran mu, ka dubi yarona ka kawo masa agaji ya Allah ka warkar dashi daga wannan cutar, ka kawo karshen azzaluman da suke azabtar mun da shi!..” Kuka ne yaci ranta sosai har ta gagara maganar.
Shi kuwa bubbugan bayanta yake a hankali yana rarrashin ta cikin kulawa….

Duk halin da suke ciki kuwa Ayush na tsaye ta gefe guda tana sauraronsu, ta fahimci suna cikin tashin hankali itama sai data zubda hawaye ganin halin da Mommy take ciki da kuma Junaid..
A ranta take fad’in “kuyi hakuri nasan duk wannan halin da kuke ciki iyayena ne suka jefaku ciki, Damusar daya fitowa Junaid kuma tayi tunanin shine ya fitowa mahaifiyarta tana gudu tana ambaton Damusa! Damusa!! Har Junaid ya bugeta da mota ta rasa rayuwarta..

A hankali abubuwa suna dawo mata kwakwkwalwa,

“Tabbass wannan Damusar da ya sha jinin Junaid dashi mahaifina yake amfani waran cutar da Junaid, shine yake zuwa wa Junaid a mafarki har kuma ya fara fito masa a zahiri..”

Fashewa Ayush tayi da matsanancin kuka, ita kad’ai tasan rad’ad’in da takeji a zuciyarta
Bataso ace mahaifita ya zamto a haka ba, tayi tirr da halin mahaifinta!!

Hannu ta d’ora a kaa tayi wani irin ihu na gaske
Tana fad’in “wayyoo Allah na, na mutu na lalace,
Innalillahi wa inna’ilaihi raju’un,” kuka take sosai
Wai abun ba’kin ciki ta hanyar fasi’kanci aka sameta
Abun yanayi mata ciwo a rai…

Mommy ce ta nufo waranta tana fad’in “lafiya kuwa Ayush meya sameki”

Ita kuwa cewa take “mutuwa zanyi na huta, rayuwata batada wani amfani,
Um Um Um Umaaaa naah wayyo nagaji da ganin takaicin nan, bazan iya cika miki alkawarinki ba, I can’t, I can’t wallahi…..

Umanta ne ta fara yimata gizo a cikin fararen kaya da hawaye kwance saman fuskarta,

Hannu Ayush take mi’ka mata alamar tazo ta tafi da ita…….
Muryarta ne ya dishe ta gagara yin kukan ma!
Sai idonta daya fara kakkafewa, yawu ne yake gangarowa ta gefen bakinta
Daga nan aka nemi hankalin Ayush aka rasa ta sumaa!!

Shima Junaid ne yayo kanta yana bubbugan gefen fuskarta amma ba numfashi ya tsaya cakk sai ido a bud’e ya ‘kafe….

Lokaci guda Junaid ya rikice yana fad’in “mo mo momm moomm Doctor zata mutu fah,” ya nufi waje da gudu yana kiran ” Doc Doctor! Doctor!! Doctor!!! Gaba daya ya fita hayyacinsa…..

*****

Abunda ya faru da Junaid kuwa a daren jiya
Shi kad’ai ya kwana a gida sai kuma mai gadi dake d’akinsa wanda yake bakin gate…

1:00am yana cikin baccinsa yaji wani irin gurnani a cikin baccin a hankali yake bud’e idon a tunaninsa mafarki yake kamar Wanda ya Saba, ashe abun ba haka yake ba a zahiri aka fito masa wannan karan!
Idonsa ya bud’e sosai still bai daina jin gurnanin ba
Yakai hannu ya kunna ligh d’in d’akin
Haske ne ya bayyana idonsa ne ya sau’ka akan wani ba’kin Damusa ‘katoto dashi ga idonsa jawurrr daga gani kasan na tsafine,
Junaid ja da baya yayi ya manne a jikin karfen gadon,
Tsorone ya bayyana akan fuskarsa gaba daya ya mance da Addu’o’in da akace yanayi, jikinsa 6ari ya soma yi!
Shi kuwa Damusan kansa yake yowa da wasu fikokinsa a waje
Wani irin sufa yakai wa Junaid
Shima Junaid yun’kurawa yayi da ‘karfin gaske ya cafki wuyan Damusa…..
Ido cikin ido suke kallon juna idon Junaid ne ya Fara komawa na Damusa sai dai shi nashi Blue eyes ne,
Wani irin yakushi Damusan nan yakaiwa Junaid a wuya, jin zafin yakushin ne yasa Junaid yayi wulli da Damusar jikin mirrow saida madubin ya dagargaje,
Cikin karfin hali Junaid yayo kan Damusan zai kai masa naushi rashin sa’a yasa Damusar zamewa Junaid kuwa ya doku a ‘kasi, hakan ya bawa Damusar daman hawowa kan Junaid ta baya yakai bakinsa saitin wuyansa zai cije shi,,,
Wani irin juyi Junaid yayi ya cakawa Damusan glass d’in jikin mirror a wuya….
Wani irin Ihu Damusar yayi ya 6ace 6aatt!
Jinin Damusan daya zube a tiles shima kamar Wanda aka goge waran ba alamun jini…
Damusar ya tsani ganin jini a jikinsa domin yana had’e da jinin Junaid ne hakan zai bada matsala sosai daga 6angaren su,
Hakan yasa Damusar yayi saurin 6acewa….

Junaid kuwa kansa ne daya bugu a ‘kasi ne ya fara ciwo sosai ga jinin da Damusar ya yakushe shi a wuya sai zuba yake ga rad’ad’i ga ciwon jiki, gaba d’aya jikinsa ne yahau yin ciwo
Abu kamar a mafarki!!

Sai a yanzu Junaid yake furta
“Innalillahi wa inna’ilahi raju’un, wannan wani irin masifa ce..”

Dakyar ya tashi ya shige toilet yayi wanka ya fito ya shirya ya nufi falo d’akin medicine ya nufa yaje yayi treat d’in ciwon dayaji a wuya,,,
Daga lokacin bai samu yin bacci ba har asuba
Yayi sallah…..

Ya wayi gari da mungun 6acin rai, bayason kula kowa, da haka har yaje hospital d’in, yana tsananin mamakin kansa “how comes Zan iya ya’kar Tiger?” Abunda yake yawo masa a rai kenam………

Domin Sauke Cikakken Littafin Sai Ku Danna bulun Rubutun dake kasa 👇👇

Matar Damisa Book 1 Complete Novel Document 

Sorry my fans kuyi manage da wannan banida time ne 🙏🙏🙏🙏

Some of related Hausa Novels

*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝*
*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦350
2GB = ₦600. 2GB = ₦700
3GB = ₦900. 3GB = ₦1000
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1300
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1600

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦250
2GB = ₦700. 1GB ₦500
3GB = ₦1050. 2GB ₦1000
4GB = ₦1400. 3GB ₦1500
5GB = ₦1750. 4GB ₦2000

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
*🪀08066268951*

 

*ASMEETAH* *CE* ✍️✍️✍️

Back to top button