Hausa novels

Kanwar Maza Page 69 Complete Novel By Ayshercool

Page 69

 

 

Ruƙayya ta riƙe haɓa ta ce “Kan uban nan, wannan wace irin yarinya ce, mara tarbiyya Binta ta aurawa ɗan ta?”

 

Jin maganar rumaisa ta yi wani iri, yadda ruƙayya ta ambaci sunan Ammi haka kai tsaye kamar sa’arta.

 

Zee ta ce “Ni wallahi da na san irin wannan abun zamu tarar, da ban zo ba, kawai kun zo kuna zubar mana da mutunci a gaban wannan ƴar yarinyar”.

 

Ruma ta ce “Oho dai, in ma ƴar cikinki ce ku ta shafa, aka gaya mini cuta sai na faɗi mutuwa, haka kurum tiƙa-tiƙa da ku, ku zo kuna ci mini mutunci. Wai wani kun zo wurin ɗan uwanku, yo koma menene, duk ƴan uwantakar ta ku, tun da dai ni ta ajiye mussaman yake bani abinci, yake kula da ni, yafi so na”

 

Samha da takaici ya ƙule, ta miƙe a hasale, tana yinƙurin ta ƙarasa ta tsinke rumaisa da mari. Fauziyya ta riƙe ta, ta ce “Ba girmanki ba ne”.

 

“Ki cikani Fauziyya, in zuba mata da haƙora na daki banza, dan ubanta”

 

Rumaisa ta ce “Taɓ ki dakeni ki ga yadda ake ƙaramin yaƙi, wallahi sai yayyena sun yi miki bugun sakwara, bar ganin kin fini girma, ni da maza ma dambe nake ba ruwana da girmanki”.

 

Jin hayaniya ya sanya baba uwani hawowa saman, ta zo ta iskae rumaisa tana ta zazzaga musu rashin mutunci.

 

Baba uwani ta ce “Haba ke kuwa, baƙinki ne fa, ƴan uwan mijinki, ya zaki din ga yi musu wulaƙanci haka, ai ba haka ki ke yi wa ƴan uwanki idan sun zo ba, kuma ba sa’anninki bane ”

 

“Baki san meyafaru ba, dan haka ba ruwanki da ni”.

 

Baba uwani ta dafe ƙirji ta ce “Ni ki ke gaya wa haka?”

 

Rumaisa ta dubi dattijantar baba uwani, ta haɗiye abun da ta yi niyyar faɗa ta ce “Ba ruwanki da abun da na yi, idan ban saka ki a ciki ba, tun da baki san farkon abun ba, kuma kina goyon bayansu”

 

Ta ɗauki kofinta, ta nufi ɗakinta, tare da ce musu “Mahukatan banza kawai”

 

Tun da ta shige ɗakinta, ba ta sake fitowa ba, tayi zamanta tana zane-zane, har aka yi sallar magariba, sannan ta tashi ta yi alwala ta yi salla.

 

Ta idar da salla kenan, ta jiyo takawa yana kwaɗa mata kira, yamutsa fuska ta yi, dan ya tsorata ta.

 

Fita tayi, ta tsaya ta kalli falonta, an ci abinci an ɓata falon gaba ɗaya, har da fasa mata wasu daga cikin farantai.

 

Kasa magana ta yi, a fusace ya kalleta ya ce “Meye wannan?”

 

“Oho” ta bashi amsa.

 

“Which kind of nonsense is this, ina yi miki magana?” Ya yi maganar a zafafe.

 

Nan da nan ita ma ranta ya ɓaci, “Amma dai ka san ni ba ƙazama ba ce, kuma ba ka taɓa ganin nayi irin wannan abun ba, yadda ka gani, nima yanzu nake gani”.

 

“Wai ne ki ɗaukeni ne? Sa’anki or what, kina da hankali kuwa, kalli falon nan fa?”

 

Takaici ne ya ƙule rumaisa ta ce “Ni ba mahaukaciya ce ba, ƙannenka da wannan Samhar su ne mahaukata, dan su suka yi haka da falon ba ni ba, tun da dai baka taɓa gani na yi haka da gidan ba” ta juya ta nufi ɗakinta, ya taka da sauri ya janyota ya mayar da ita falon.

 

“Idan suka yi haka da wurin, ke ba zaki saka a gyara ba, ko ke ki gyara ba? Ba gidanki bane?”

 

“Taɓ, ni zan gyara musu, to wallahi ko kai ne ba zaka yi haka in gyara ba, kai da kake ciyar da ni, balle wasu ƙartin banza”

 

“Shut up! Ƙannen nawa ki ke cewa ƙartin banza? Ki kiyayeni, samo abun gyara ki gyara wurin nan, na baki mintuna biyar kawai. Ki gama ki zo ki gaya mini dalilin da ya sanya ki ke yi wa baba uwani rashin kunya”

 

Wani irin malolon baƙin ciki ya cunkushe mata zuciya, ba ta taɓa tunanin Adam yana da kwarjini, da kima a idanunta ba sai yau, da ta ji tamkar an ɗaure mata harshe, ta kasa bijire masa, wasu hawayen baƙin ciki suka cika mata ido, amma ta danne, ta zo ta fara aikin gyara wurin.

 

Ya nemi wuri ya zauna, ta gyara ta kammala, ba ta ce masa uffan ba, ta tafi ɗakinta.

 

Bayanta ya bi, ya tarar da ita a gaban mudubi, ta cika ta batse, ba wani abu take a gaban mudubin ba, kawai tana tsaye, tana sauke numfashi.

 

Tana ganinsa ya shigo, ta share shi ta cigaba da tsayuwa.

 

“Me baba uwani tayi miki da ki ka yi mata rashin kunya?”

 

Banza ta yi masa taƙi kula shi.

 

“Ina sake gargaɗinki, duk abun da zasu zo su yi, babu ruwanki da su, sannan idan ki ka kuskura ki ka kuma yi wa baba uwani rashin kunya, sai na ɓata miki rai, kawai kin saka tsohuwar mutane kuka, saboda ke baki san abun da ya dace ba?” Yayi maganar yana son ta yi magana, dan ya ji meya haɗa su da su Fauziyya, dan ya san idan ya tambaye ta, yadda ta ƙule ɗin nan, ba zata gaya masa ba.

 

“Wallahi duk wadda ta kuma zuwa ta zageni, sai na rama, kayi zuciya ka mayar da ni gidanmu, sai ka tattaro su su dawo gidan nan su zauna, gida zan tafi dan ni ba banza ba ce, da za su din ga zagina ina jin su ba, me na yi musu? Nima ƙanwar wasu ce, kuma suna sona, dan wallahi ko za su kasheni, suka zageni sai na rama, ita kuma baba uwani ta cigaba da yi mini sharri” ta yi maganar tare da shigewa toilet.

 

Har dare taƙi ko sake fitowa, dan ko abincin dare ba ta nema ba, ta yi kwanciyarta.

 

Sai da takawa ya nemi, Asiya da barira ya tambayesu abun da ya faru, amma suka ce ba su sani ba, baba Uwani ta hana su hawa saman, amma sun jiyo su Fauziyya suna zagin rumaisa tana ramawa.

 

Daga nan gidansu ya wuce, bai ko je sashin Ammi ba, ya nufi sashin Mummy.

 

Ya tarar da su gaba ɗayansu, har da Mahmud da Mummy, da ruƙayya da Fauziyya, sai dai babu Samha.

 

Mummy na ganinsa ta ce “Ahh, takawa barka da wannan lokaci, ƙaraso mana, ya jikin naka, tun da na shiga ban sake zuwa ba, ashe ka samu sauƙi”.

 

Ya ce “Eh”

 

“Sabuwa, ƙaro plates, a zubawa takawa abinci shi ma”.

 

Ya girgiza kai ya ce “Na gode, Fauziyya”

 

Ta kalleshi ta ce “Na’am yaya”

 

“Kun je gidana ɗazu?”.

 

“Eh yaya mun je, zamu sake dubaka ne kuma baka nan, matarka ta yi mana rashin mutunci, har da zagin baba uwani”.

 

Adam ya ce “Daga yanzu, idan har ba alkhairi ne zai kai ku gidana ba, kar ku sake zuwa, ina baku wannan saƙon ne har Samha, idan ma baku gaya mata ba, ni zan gaya mata. Kar ku sake zuwar mini gida ku ci mutuncin mata ta, ni na ajiyeta ba ita ta ajiye kanta ba, kuma ban aurota, dan ku je ku ci zarafinta ba, ita Aisha dama taku ce, kuma mai haƙuri ce. Wannan kuma tawa ce, sannan ba zata iya jure abun da Aisha ta jure ba, yarinya ce ba zan lamunci a saka mata tension depression ya kamata da ƙuruciyarta ba”.

 

Baki a sake Mummy ta ce “Yanzu matarka ka fifita a kan ƙannenka, duk da sun gaya maka ta wulaƙanta su? Bayan kai suka je dubawa?”.

 

“Mummy ko dabba na ajiye na ce nawa ne, bai kamata a je ci mutuncinsa ba, idan har ina da kima a idon su ba, balle ɗan adam na ajiye, idan banda rashin girma, me zai saka su biye mata, tun da ba sa’arsu ba ce ba, na san rigimammiya ce, amma ba ta yi haka kurum, ku kiyaye, aje a ci mata mutunci ace mata ƙwaila, ko ba mace ba ce, ni a idona mace ce kamar kowa.  Dan haka Please allow her to enjoy her marital home. Ko ba ku yi zumunci da ita ba, ni na isheta, na san yadda nake bi da ita mu zauna lafiya”

 

Mummy ta yi murmushi ta ce “Hmm, wannan dai kashedin na samha ne, zuwa aka yi a gaya mana ana son ta kenan”.

 

Ya tashi yayi murmushi  ya ce “Ta cancanci hakan Mummy, a rashin Aisha ita ce uwar ɗana, idan na bari aka wulaƙanta ta, ni aka yi wa, dan haka a kiyaye”

 

Mummy ta yi shiru, tana saƙa wani abu a ranta, lallai akwai ƙura ba ƴar kaɗan ba, Samha tana ruwa, dan ba ta tunanin baba uwani na abun aka sakata yadda yakamata.

 

Mummy ta ce “Gaskiya ne, tayi rawar gani kam, ta cancanci a kula da ita. Duk da ka ɓoyewa duniya ita, da muhimmancin abun da tayi maka”

 

“Ni ta yi wa, ba duniya ba, dan haka ni yakamata na girmama abun da tayi mini”.

 

Mahmud kuwa, ya kammala cin abincinsa, danna wayarsa kawai yake yi.

Har Adam ya wuce shi, ya dawo ya zauna a kusa da shi, yayi ƙasa da muryarsa yadda shikaɗai zai ji me yake cewa ya ce “Am warning you, stay away from my family, da ɗana, da kuma matata”

 

Mahmud ya ɗan kalli Adam ya ce “Ban ji zan iya ko ɗaya ba, ina son ɗanka, ina girmama matarka, kasancewar tana girmamani, we are having a deal together, dan haka you should stay away from us”

 

Wani irin zafi maganganun sa, suka yi wa adam, amma ya shanye ya ce “Shikenan, idan ka ƙi ji, ba ka ƙi gani ba” ya tashi ya fice.

Kanwar Maza Complete Novel Document Txt

Mummy kasa zama tayi, ta tashi ta bar falon, Fauziyya kuma suka cigaba da caccakar rumaisa, suna bawa Mahmud labari.

 

Bayan ya bar sashin Mummy, ya je ya ga Sabir, Ammi ta yi masa ya jiki, tayi masa addu’a kamar yadda ta saba, sannan ya tashi ya tafi.

 

Kasancewar a cikin garin, gidan Jamil yake, ya sanya ya biya gidan Jamil, sai dai ya tarar baya nan.

 

Yau ya ji ƙwarin jikinsa sosai, dan haka ya shirya dan tafiya aiki, ya saba idan da makaranta, shida da rabi, rumaisa za ta zo gyara masa ɗaki, idak bai tashi ba ma, ta din ga ƙwale-ƙwale kenan sai ya tashi ko baya so.

Amma har ya fito breakfast, ko alamunta bai gani ba.

 

Kai tsaye ya tafi ɗakinta, tana zaune dirshen da kayan bacci, ta cika akwatu da kayanta, tana zugewa.

 

“Ba zaki shirya tafiya makaranta ba ne?”

 

“Eh na daina zuwa, gidan matsiyatan iyayena zan koma, in cigaba da zuwa wadda na saba zuwa, sannan in cigaba da cin irin abincin da na saba ci, ba irin wanda nake ci a nan ba ake yi mini gori”

 

“Dalla tashi ki shirya zan makara”

 

“Sai kuma ka yi, ni za a din ga yi wa gori, saboda rashin adalci irin naka, da son kai, ka ɗora mini laifi, kai ƙannenka ba sa laifi, wallahi ko ta katanga sai na haura na koma gida” tayi maganar cikin tsan-tsar takaici.

 

“Na baki mintuna goma, ki yanke shawara, idan kin zaɓi mu rabu, abu ne mai sauƙi, amma ki sawa ranki, ba zaki sake ganin Sabir ba, har abada mintuna goma kawai gareki” saroro ta yi, ta bishi da kallo har ya fice.

 

Ko mintuna bakwai yi ba, sai gata cikin uniform, kamar zata fashe.

 

A ransa ya ce “Ni zaki yi wa zuciya, bayan na san lagonki?”.

 

Suna tafe a hanya ya saya mata alawar madara, dan ya san tana son harkar madara.

 

Ta ce bata so, bai kulata ba ya ajiye a kusa da ita, suna zuwa ƙofar makaranta, ta buɗe ƙofar motar ta ɗau alawarta ta fice.

 

Yayi murmushi ya ce “Su mimi ba zuciya in dai a kan kwaɗayi ne” tana jin sa a ranta ta ce “So ka ke in kulaka, kuma ba zan kula ka ba”.

 

Ana tashinsu ya je ya ɗaukkota, ya wuce da ita gidan Ammi, ya ajiyeta ya koma wurin aiki, tana jin daɗin hakan nan, saboda yana ɗebe mata kewa sosai, duk da su Iman na makaranta, ta yi ta hira da Ammi, tana wasa da Sabir.

 

Ammi ta ce “Rumaisa, ashe su Fauziyya ne suka je gidanki jiya?”

 

Rumaisa ta ce “Eh Ammi, sun je jiya da yamma”

 

“Ina fatan dai ba wata matsala”

 

Rumaisa ta ce “Eh Ammi babu komai, sun je duba shi baya nan”

 

Ammi ta yi murmushi tana dafa kafaɗar ruma ta ce “Ashe mutuniyar tawa tana girma, da har take iya ɓoye abu. Ban san dai meyafaru ba, amma na san ba zasu je su dawo haka ba, sai sun yi miki wani rashin albarkar. Babarsu ta zo ɗazu tana ta masifa, wai takawa ya je ya ci musu mutunci a kanki, kamar ba ƴan uwansa ba”.

 

Rumaisa ta waro ido ta ce “Papan? Amma ni kuma jiya yayi mini wulaƙanci, suka ɓata ɗaki wai ni zan gyara”.

 

Ammi ta ce “Ki yi haƙuri, ki cigaba da kula da kanki, ban da surutu a gaban wani”

 

“To Ammi in sha Allah”

 

Ammi kuwa daɗi ne ya kamata, ganin alamun soyayya a tsakanin rumaisa da takawa, yadda suka din ga turjiya kan ayi auren, ba ta tsammaci haka ba bayan auren.

 

“Yauwwa, Ammi dan Allah kira mini mama mu gaisa, ke da ita duk kun ƙi zuwa gidanmu”.

 

Ammi ta ce “Bari na kirata, to me zamu zo mu yi muku, ku ba gashi kuna zuwar mana ba”.

 

Ammi ta kira mata mama, ta bata wayar sannan ta tashi ta fita.

 

Mama na yin sallama ta ji muryar ruma, mama ta ce “Ahh babar sabir, ƴar gidan amminta”

 

Ruma ta ce “Mama na tabattar kin daina so na gaba ɗaya, baki taɓa zuwa gidana ba”.

 

“Ai na san kina lafiya ne, ya ɗan naki ya maigidan?”

 

“Ɗana lafiya ƙalau, maigidan kuma mun yi faɗa bama magana”

 

Mama ta ce “Kun yi faɗa ba kwa magana saboda baki da hankali?”

 

Cikin sangarta ta ce “Mama faɗa yake yi mini a kan abun da ba laifina ba”

 

“Yi mini shiru, dan me ba zai yi miki faɗa ba, ya fita ya nemo ya kawo ki ci, ƴan uwanki sun ce mini baki nemi komai kin rasa ba, kuma dan yayi miki faɗa sai ki daina yi masa magana? Idan ma daina yi miki maganar yayi, ke ba zaki yi masa ba? Kin ga ki kiyayeni”.

 

“To mama kawai sai na bashi haƙuri”

 

“Kar ki bashi, zan nemo masa wata matar mai ɗa’a, tun da ke ba kya ji”

 

Rumaisa ta ce “Mama ban gane ba, to wallahi ammi ta ce ba zai ƙara aure ba, daga ni shikenan”.

 

“Kar ki canza hali, na fasa zuwa gidan naki ma, sai kin yi hankali”

 

Kan ta yi magana, mama ta katse wayarta, ruma ta ajiye wayar tana tura baki.

Tayi shiru tana nazarin maganar mama, ba ƙarya duk abun da take so yana bata, ko bai amsa mata ba, za taga abun ya bata.

 

Kuma ga ammi ta ce ya je ya yi wa ƙannensa faɗa.

 

“Ai shikenan, zan daina fushin, amma ba zan bashi haƙuri ba”

 

Har yamma tana gidan Ammi, sai magariba, sannan takawa yayi waya, ya ce Sidi ya mayar da ita gida.

 

Yawan zuwan nan da take yi, ya sanya ba ta damu lallai, sai an bata sabir ba, saboda tana samun shaƙuwa sosai da sosai tsakaninta da Sabir ɗin, da kuma Ammi, gashi akwai fahimta sosai tsakaninta da iman, sannan a hankali take ƙara sanin kan masarautar, dan wataran idan ammi za ta fita, binta take yi.

 

Tana tsaye tana ƙoƙarin shiga motar sidi, sai ga mahmud.

 

“Daughter, ina ta so mu haɗu da ke”

 

“Ai ban san kana nan ba, da sai na nemeka”.

 

“Kin san bana zuwa ko ina. Jiya mijinki ya zo sashinmu, yayi wa Mamana rashin kunya, saboda su Fauziyya sun je muku gida”

 

Rumaisa ta ce “Ai gara shi, kishiyar mamansa ya yi wa, wanda yayi wa maman sa fa”

 

“Ba wannan maganar muke yi ba, idan muna irin wannan maganar, raina zai iya ɓaci. Yanzu dai ina zaki?”.

 

“Sidi ne zai kai ni gida”.

 

“Duk an yi mini kashedin na fita harkarku, amma ba zan iya ba, ɗaukko mini Sabir sai na kai ki gidan, na dawo ni da shi”

 

Rumaisa ta ce “Babu lallai ammi ta bani shi, sai da ka zo mu je tare”

 

“Ina son yaron nan sosai daughter, mu je”

 

Tare suka koma Ammi ta din ga kallon Mahmud, Ruma ta gaya mata abun da ya ce, ammi ta ce “Banda abun sa ai shi ma ɗan sa ne, Allah ya tsare”

 

Ruma ta yi ta murna, ta ɗauke shi suka fita, Mahmud ya karɓe shi, suka shiga motarsa suka tafi.

 

Nusaiba ta ce “Ammi, kina ganin babu wata, ko takawa ya zo yayi faɗa?”.

 

Ammi ta ɗan yi shiru sannan ta ce “Yarinyar nan ta zarce duk yadda nake zato, ko da ba ta gaya mini ba, na san ƙoƙari take ta sasanta tsakanin Adam da Mahmud, tun da ni na gagara yi, ban sani ba ko ita Allah ya sa ta iya, dan haka ba abun da zan iya, yi mata Addu’a, tare da goyon baya ɗari bisa ɗari”

 

Nusaiba ta ce “Ikon Allah, ammi kuma fa haka ne”

 

“Ku tayani addu’a, a dalilinta sau biyu Mahmud yana zuwa in da nake, in sha Allah ko bai dawo wurina gaba ɗaya ba, sai an samu daidaito tsakanin iyalina”.

 

Nusaiba ta ce “Allah ya sa”.

 

Har ƙofar gida ya kai rumaisa, suna tafe suna tattaunawa a hanya, yadda za su fallasa baba uwani, domin sai an katse hanyar kaiwa Mummy saƙo, da samu hanyar dakatar da wasu ayyukan na Mummy.

Rumaisa ta sauka, shikuma ya tafi da shi da Sabir.

 

Sai wajen goma na dare, sannan takawa ya isa gida.

 

Rumaisa tana fallo tana kallon cartoon, kamar yadda ta saba.

 

Sallama yayi da kaya a hannunsa, ta tuna mama ta taɓa cewa, a zamaninsu idan miji ya dawo gida da kaya a hannunsa, jiki na rawa suke tashi su karɓa.

 

Cikin basarwa, ta tashi ta miƙa hannu za ta karɓa, ya kalleta ya ce “Kin ci abinci ne?”

 

“Na ci a gida”.

 

Ya ce “Dafo shayi cup biyu, ki sameni a ɗaki”

 

Ta jinjina masa kai, ta tafi kitchen.

 

Kan ta dafa ta dawo, har yayi shirin kwanciya, sai dai yana gefen gado, yana danna waya.

 

Ta ajiye cup da flaks ɗin, za ta fita ya ce “Zauna ki haɗa mana”

 

Su ruma da yake ba kowacce bisimillah take wucewa ba, ta zauna ta haɗa tea cup biyu.

Gasashshen nama ne, da ƙaton bredi, ba kunya ta saka hannu tana ci, tana basar da shi, ita dole ba ta daina fushi ba.

 

Hannu ya sa, ya matse kumatunta ya ce “Can’t you smile, or say thank you? Kin shanye mini alawar madara, kuma kina wani kumbura baki”

 

Tura baki tayi, ta cigaba da kora shayi, suka gama ciye-ciye, ta tashi zata kwashe kwanuka ta fita.

 

“Zauna zamu yi magana”.

 

Ta zauna tana lashe hannu. Ya ɗaukko tissue, ya goge mata hannun.

 

Sannan ya dubeta ya ce “Cikin satin nan zan yi tafiya in sha Allah, zan yi sati biyu, idan na dawo kuma, zan je ƙaro karatu, na tsawon watanni shida. Wannan asabar ɗin in sha Allah, za a saka ki a Makarantar islamiyya ta matan aure”.

 

“Islamiyyar matan aure, salon su rainani, ba manya ne matan auren ba? Kuma wai ka tafi ka barni nikaɗai?”

 

Takawa ya ce “Eh, sidi zai din ga kai ki yana dawo da ke makaranta”

 

“To sai in daina ganinka?”.

 

“Kina son ki dinga gani na ne?”

 

Ta ce “Eh mana, nafi son ka dinga kaini makaranta da kanka”

 

Yayi murmushi ya ce “Abokin gabar naki? Da ki ke yi wa rashin kunya?”

 

Tayi dariya ta ce “Ai amanarka aka bani, sai na gama sauke amanar, sannan zan rama abun da ka yi mini, dan ban manta ba, kuma kai ne ka ke sawa na yi maka rashin kunya ai wataran, amma dai ka yi haƙuri.

 

Wani irin murmushi yayi, yana jin daɗin jirar ta su.

 

Ya ɗora hannunsa a kafaɗarta, kamar ƙawarsa ya ce “Ban haƙura ba, fitsararki ta yi yawa, haƙurina ya kusa ƙarewa”

 

Ita ma ta ɗora hannu a kafaɗarsa ta ce “Allah ya sa kar haƙurinka ya ƙare, ai da ban taɓa sanin kana da haƙuri ba ma sai yau. Allah ya sa in yi tsawo in kamo ka a tsayi”

 

“Ba wannan nake so ba, ki yi girma ki biyani bashina nake so”

 

Ba tare da ta gane me yake nufi ba ta ce “Ai da na gama makaranta, na fara aiki, dubu goma ma zan baka”.

 

“Zaki ga idan kin gama makaranta, na gaji, baby nake so, ayi wa sabir ƙani ko ƙanwa”

 

Ta ce “Eh wallahi, nima ina so”

 

Yayi dariya ya ce “Are you sure?”

 

Ta ce “Yes” cikin murna.

 

Yayi dariya ya ce “zamu gani ai”.

 

Ya ɗan yi shiru sannan ya ce “Duk da na yi maganar a baya, amma yanzu zan sake jaddadawa, ki din ga iya bakinki, a al’amuran da suka shafi masarautar nan. Abu na gaba a duk lokacin da abu ya faru, idan nayi magana ko kina da laifi ko baki da laifi, bana son musu, idan baki da laifi, da kaina zan yi bincike in gane”

 

“Idan bani da laifin sai ka bani haƙuri?”

 

Ya ce “Ya danganta, ba sai lallai na fito kai tsaye na ce kiyi haƙuri ba, sannan a duk lokacin da wani daga familynmu, ya sake zuwa, idan har suka yi miki magana ta rashin kyautawa, kar ki kula su, idan na zo ni ki gaya mini. Sai kuma alaƙarki da wancan yaron Mahmud, ina sake maimaita miki bana so, ki kiyaye abun da ba na so mu zauna lafiya”.

 

Rumaisa ta ce “Gaskiya papa, ni ba kullum nake ƙarya ba, maganar gaskiya ba za aci mini mutunci nayi haƙuri ba, tun da dama can Allah bai yi ni a cikin masu haƙuri ba. Sai kuma maganar daddyna, dan Allah meyasa ba ka son alaƙarmu?” .

 

“Ban ji na yadda da alaƙar bane, zai iya yin komai dan ya cutar da ni, dan haka ba zan so yayi involving ɗinki da Sabir ba. Mussaman da ki ka kasance abokiyar gabata”

 

Ruma ta yi murmushi ta ce “Amma ka yadda ka yi mu’amala da su Jamil ko? Kai baka san farincikin ammi ne papa? Ba zai cutar da kai ba, idan kuma kana son mu rabu, to ka rabu da su Jamil kai ma”.

 

“Alaƙata da su daban….”

 

“Amma duk wata alaƙa barin jini ce da ciki ɗaya, wai ba Jamil ɗin ba ne yake yekuwar sai ya bincike ka ba a kan Anty Aisha, haka son da yake makan yake? Maiyasa da tana raye basu damu da ita ba, sai bayan ranta har da barazanar zai yi bincike a kanka, wataƙila ma da saka hannunsa, shiyasa yake son ya ji ta ina kake binciken naka, ya ji ko asirinsa zai tonu, ka din ga wayo kamar ni mana”

 

Gaban Adam ya yanke ya faɗi, kar maganar rumaisa ta zama gaske fa, gaba ɗaya jikinsa yayi sanyi, take ya ƙaryata maganar rumaisa a zuciyarsa, ya san abun da ba zai taɓa faruwa ba kenan. Ruma ta tashi ta ce “Papa sai da safe” ta kwashi kwanukanta, ta bar shi da tunani.

 

Haka ya kwana wa wayi gari, maganganun rumaisa na kai komo a kansa, idan ya ƙaryata sai yaji abun bai kama zuciyarsa ba, kamar da wayo clue ta bashi, a kan binciken, idan ba rami meya kawo rami?

 

Washegari a wurin aiki, takawa da kansa ya je office ɗin Jamil, Jamil ya wani tsuke fuska.

 

Adam ya ce “Jamil lafiya kuwa? Tun da ka kaini gida, na ce ka ɗaukko rumaisa, ban sake ganinka ba”

 

“Me zan zo na yi maka? Dama kana sane ka tura ni ɗaukko fitsararriyar matarka, ta yi mini rashin kunya, tun da ka gama zubar mana da mutunci a idonta, ni zata kalla ta ce wai ba ƙaunar aisha muke ba, ka je ka gama zazzage mata sirrinmu, meye amfanin dawo da abun da ya wuce? Adam turaki yaƙi gaya mini komai a kan abun da ta gaya masa, dole na cigaba da bibiyarka da tuhumar ka akan dalilin ɓatan aisha bamu sani ba”.

 

“Kuma ni ta ce maka na gaya mata?”

 

“Idan ba kai ba waye ya gaya mata? A ina zata sani ko ta ji? Kuma dole ka gaya mini abun da kake ɓoyewa, dan na fika kusanci da Aisha, ai jini ya fi ruwa kauri. Kuma zan cigaba da bibiyar yarinyar nan, sai na san gaskiyar abun da yake faruwa.

 

Adam ya haɗiyi yawu ya ce “To shikenan, ai matata ce, na gaya mata ɗin, kuma Jamil kar ka fasa tuhumata da bibiyata, ka yi duk abun da zaka yi”

 

Ya daki tebur da ƙarfin gaske ya ce “Kuma ina yi maka rantsuwa da Allah, idan wani abu ya samu matata, sai dai ayi mutuwar kasko da ni da kai, ka je ka cigaba da bincike a kaina, amma idan har zaka bibiyi matata ita za ta gaya maka abun da ya faru, ka shirya cewa watan faɗuwarka ya tsaya, dan tana da ƙwaƙwalwa fiye da lissafinka, kuma gaskiya ta faɗa, a da baku damu da ita ba, kun cutar da ita meye na tayar da jijiyoyin wuya a yanzu? Idan ka matsa za ta saka ka a sarƙa, kuma muddin ka faɗo cikin suspect ɗina, aikina zai bi ta kan ka”

 

READ ƘANWAR MAZA PAGE 70 HERE


Proceed with your download by clicking the below button

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button