Uncategorized

Gidan Aro Complete Hausa Novel

 

Abuja, Nigeria

National Police Headquarters.

_Criminal Investigation Department (CID)_

Cikin k’warewa da sanin makamar aikinta budurwar mai kimanin shekaru 29 taci gaba da kwararo bayanai tana mai nuni da Farin allo wanda hasken k’wan wutan projector ya haskesa, Ko ba’a fad’a maka ba zaka fahimci cewa cikin d’akin gudanar da binciken manya manyan laifuka suke musamman irin laifin da ya shafi kisan kai, fyad’e, Garkuwa da mutane da sauransu..

Hoton wani matashi ne na’urar Ta hasko, kwance yake a k’asa tamkar bai numfashi, ga dukkan alamu babu rai tattareda shi.. Ko ina na wajen a kewaye ne da Doguwar igiya mai launin ruwan d’orawa, jikin igiyan an rubuta _Restricted Area_ da manyan bak’ak’e…

Budurwar ta k’urama hoton idanu Wanda ya bayyana Babba gabansu kasancewar da na’uarar projector ake hasko hoton.. Ta matso sosai tana mai rage girman idanunta tana kallon hoton, a hankali take furta “Da hannun hagu ya rik’e bindigar, direction d’in da bindigar Ta kalla bai kamata harsashi ya samu k’irjinsa direct ba, ya kamata harsashin ya huda ribs d’insa kafin ya ratsa cikin k’irjinsa indai har da hannun da aka sami bindigar a ciki yayi harbin..”

Wani matashi mai kimanin shekaru 32 ya taso yana k’arasowa kusanta wanda shima d’aya ne daga cikin ‘yansanda masu gudanar da bincike da suke zaune a madaidaicin Zauren gudanar da binciken.. Hannayensa sakale cikin aljihun wandonsa, idanunsa naga hoton yake furta “Well done Agent Maleeka.. But wani hanzari ba gudu ba.. Baki tunanin idan mutumin nan ya kasance bahago zai iya karkata hannunsa har harsashin ta iso daidai tsakiyar k’irjinsa ta hudasa..?”

Karkatowa Maleeka tai tana duban wanda Yai maganar kafin ta d’an tab’e baki tace “Bani da tabbaci Inspector Assad.. Amma hakan nake tunani..”

KARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA2022


Gurbin Ido… Na Huguma (Zafafa2022)

Inaya By Mamuhgee (Zafafa2022)

Sanadin Labarina By Hafsat Rano (Zafafa2022)

Babu So… By Billyn Abdul (Zafafa2022)

Farhatal Qalb By Mss Xoxo (Zafafa 2022)


Bata Kai aya ba wata murya ta katsesu da fad’in “Oh shut up.!”

Gaba d’aya suka juyo suna dubansa, kusan tun shigowarsu d’akin kansa a k’asa yana aikin murza zoben dake mak’ale yatsarsa guda wanda yin hakan kusan d’abi’arsa ce musamman idan yana nazarin bincike..

Ya d’ago kai yana dubansu, kallon da yake sanyata daburcewa ta rasa mai take ciki, tunaninta duk su sakwarkwace shi ya jefata dashi kafin yace “Tunani kikeyi.? Ko kuwa kin tabbatar..?”

Kasa furta komai tai sai yin k’asa da idanunta da tai 

Hannayensa biyu sakale cikin aljihun wandon jeans d’insa, yana tsaye gabanta yana iya hango tsakiyan kanta sabida ratan tsawo dake tsakaninsu.. Cikin muryarsa da yake tsakanin kashe mata jiki lak’was wanda yake sanyata losing kanta gaba d’aya ya soma furta “We are investigating a murder  here, in case you forgot.. There’s nothing like you thought, everything here must be known.. You must Know.. I want results and  not assumptions.. Kin fahimta..” Ya k’arashe yana kwanto da fuskarsa kusan nata, idanunsa da suke matuk’ar furgitata dab kusan nata…

A hankali take jinjina kai cikin yanayi na d’an daburcewa “I..I’m sorry Inspector, Sir..”

“I don’t need your apology.. Just do your work correctly.. Or else, you’ll be kicked out of this team..!”

Yanda yake maganar cikin tsananin zafin rai zaka fahimci ransa a matuk’ar b’ace yake..

Mutumin dake tsaye gefen Maleeka ya d’an girgiza kai kad’an kafin yace “But..”

Katsesa yai da fad’in “What do you mean but.?.. You know me quite well Assad, you know I hate incompetence.. And I easily get irritated by people like her around.”

Assad ya d’an shafi kansa dan yasan Wanene abokin nasa da kuma yanayin da yake ciki “MU’AZZAM.. will you please calm down.. I was only asking you to go easy on her..”

“Oh really..! Da gaske Assad..  Am I really being too strict?.. Let me remind you idan ka mance.. Mutuwar k’anwata muke bincike a nan Assad.. K’anwata was found dead tareda wannan d’an ta’addan.. And you’re asking me to go easy on her… My sister Assad.. My only Sister.. An kasheta in a cold blooded murder.. Someone murdered her Assad.. Sannan na kasa aiwatar da komai domin wad’anda suka kasheta su biya abinda suka aikata.. Tell me, a haka ne kake ce min na natsu.. A haka ne kake ce min I should calm down and go easy on her Assad.!” Ya k’arashe cikin tsananin d’aga murya gashin jikinsa na kuma mimmik’ewa…

WRITTEN BY:   SAMEENA ALEEYU

NOVEL NAME:   GIDAN ARO COMPLETE

UPLOADER:     AIHAUSANOVELS 

  DOCUMENT SIZE:         1.5MB

DOCUMENT TYPE:              TXT

MODIFIED DATE:    1- OCTOBER -2022

CATEGORY:               LOVE   STORY

PRICE:                            FREE

Proceed To Download Gidan Aro Hausa Novel Document.

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Domin Karanta Littafin Sai ku Danna Inda Aka Saka Read More

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels

Copyright 

If you are the right owner of this novel and you want us to remove it from our site please mail Us at aihausanovels@gmail.com

Back to top button