Uncategorized

Wace Ce Ita Chapter 11 Complete Novel

     WACECE ITA⁉️ (WHO IS SHE⁉️

       Unique Barakancy

                ELEVEN📍

      Sameer yafi 30mins yana dialing number Deen amma no answer yake ta cewa,daga bisani aka kashe wayar gabadaya… Sosai yaji hankalinsa ya kasa kwanciya da rashin daga wayarsa da Deen yakeyi,a take ya yanke shawarar dole ya tafi Nigeria a yau dinnan,tuno da yawan ayyukan dayake dashi a office kuma yasa yajisa in dilemma,toh wanne zeyi wanne ze bari?…. Bin shawarar zuciyarsa kawai yayi ya yanke barin komai ya tafi Nigeria,abu daya ne ze hanashi tafiya a yau that’s if there’s no available flight.. Luckily yana duba online yasamu flight din 2pm,ba tareda bata lokaci ba ya siya ticket.. Tada motar yayi ya nufi gidansa domin ya shirya…….. 

       

       Tinda sameer ya fita khaleel yaji komai na duniyar nan ya tsaya masa chak,idan wani zai fadamasa sameer can do this for him cewa zeyi karyane amma a gaban idonsa sameer ya kallesa yake fadamasa shima yanason mahadin rayuwarsa?,oh no! This is something he can’t take! Kuma ko shakka bayayi in game zasuyi shi zaici barema bazai bari abun ya zama game ba dan yafi karfin yayi game da sameer…. Sam bayajin fatima zainab dan yasan bazata kula sameer ba,audacity din sameer ne ya bata masa rai…. Girgiza kai yayi yana fadin “Kafi kowa sanin yanda nake sonta amma ka zabi kamin haka,I’ll make sure the game gets over even before it’s started,dani kake zancen!”……..

          

      8:30pm ya sauka a Nnamdi Azikiwe Airport ,Abuja… Number Deen ya sake trying ko Allah zaisa ya shiga but still switched off…. Bolt yayi ordering ya shiga suka nufi Transcorp Hilton kasancewar few days back  da sukayi magana da Deen ya fadamasa yana chan, har room number dinsa ya sanarmasa,sannan ya fadamasa he’s not going back to kano anytime soon….. Shiga cikin hotel din yayi ya nufi room numbern Deen ya shiga knocking,yafi 20mins a tsaye kafin ya koma reception to make enquiry….. Sundai tabbatar masa da Deen bayanan tin safe,daganan kuma basu karaba dan basa bada information akan mutum….. 

Sameer ji yayi gabadaya abin duniya ya ishesa na rashin samun deen,ya tawo nanma still be gansa ba?,he has high hope akan Deen kasancewarsa very smart person so yana ganin Deen yasan everything is solved,toh shi yanzu ta ina ze fara neman Deen?…. 

Lodging yayi shima a hotel din saboda yanda yakejin gajiya sosai….. Wanka da sallah yayi sannan yayi ordering abinci daga hotel restaurant… Koda aka kawo abincin sai yaji duk baya shiga,turewa yayi ya sake dialing number Deen,yanzu kam not available ma yake cewa…. “Shit!” Ya fada indai Deen baya abuja he can be in Kano,bama can be bane indai Deen baya Transcorp to lallai yana kano,wai ya akayi ya mantane? Shida yakamata ya tafi gidansu Deen na kano sai ya tsaya tinanin ze gansa a abuja?…. Mikewa da sauri yayi yana hada kayansa daya dan bude… Airport ya nufa straightly,ko tinanin zai samu flight ko bazai samu beyi ba?…. 

Kamar yayi kuka haka yaji da yaje gaban canter akace there’s no available flight for abuja to kano,hakanan ya hakura ya siya ticket na gobe sannan ya koma Transcorp……….

       Tin bayan sun fesa masa wannan abun be kara sanin inda kansa yakeba… Bude ido yayi kawai yagansa a wani makeken daki na alfarma,da salati a bakinsa ya tashi ya zauna,kalle kalle ya shigayi yana bin dakin da kallo,wani dariya ya saki yace “Wai ni zaayi kidnapping,lallai mutuminnan!”…. Murmushi ya sakeyi sanin wanda ze iya masa haka,dole kuma ya dau mataki saboda an fara wuce gona da iri,but before then he has to leave this house dan haduwarsu da wanda yasa akayi kidnapping dinsa a yanzu kam hadari ne,sannan zaa lalata masa budget,be manta da itaba,be kuma manta da san sanin WACECE ITA ba,saboda hakan nema yasa bayasan haduwa da kidnapper dinsa a yanzu,yafiso ya gama da ita sannan yayi facing koma wani consequences ne ze biyo baya tsakanin shi da wanda yayi kidnapping dinshi……

Mikewa yayi yashiga toilet ya fito daure da towel bayan yayi wanka,nufar wardrobe dake dakin yayi ya dauko jallabiya yana murmushi ganin kaya makil a ciki,yasan kuma saboda shi akasa,rama sallolinsa yayi sannan ya dan kwanta,be dade da kwanciya ba aka turo kofar,wani ne dauke da bindiga da nose mask kamar dai wa’yenda suka sacesa…. Shigowa yayi ya miko masa wani paper… Karba Deen yayi ya duba,wani gajeran murmushi ne ya subuce masa ganin menu ne na varieties of food,sakewa yayi ya zabi abubuwa san ransa ya kuma gayawa guy din ya kawo masa charger…..Guy din bece komai ba ya karba ya fita….. 

After like 30mins sai gashi ya dawo da duk abinda Deen yace,shi kansa mamakin wani kalan kidnapping sukayi haka yake,he was shocked da aka yarda ya kawo masa charger,yaga shi kansa wanda akayi kidnapping dinma be damuba gashi har maganar kisa yaji anayi a kansa…… 

Karban sakon Deen yayi ya rufe kofa,plugging wayarsa a chargi yayi ya shiga cin abincin,yasani barinsa da wayarsa da akayi da kuma bashi chargernan means duk wani calls and communication nasa is recorded,wai shi zaayi playing smart?… Ya fada a ransa yana dan dariya…

        9am dot a filin saukar jirgi dake Mallam Aminu Kano International Airport yamasa….. Yana fitowa ya tarar da Drivern gidansu na jiransa… Gaisawa sukayi yace “Mallam bala da fatan ba wanda yasan ni zaka dauko ko?”……

“Eh yallabai ba wanda yasani kamar yanda ka umarta,cewa nayi zanje nasha mai ne”…..

“Good,idan naji labarin ansan nazo kano to tabbas baza kaji da dadi ba!”….. Sameer ya fada yana danne danne a waya….

“Insha Allahu ba abinda zakaji yallabai,babu wanda na sanarwa”…..

Bece komai ba yayi directing dinshi zuwa gidansu Deen dake GRA….. 

Mansion ne iya mansion wanda aka mishi tsari me kyau,ya kumaji kayan alatu da tsare tsare irin ginin zamani da sai wane da wane…… Bodyguards ne a zagaye tindaga wajan gidan har cikin gidan,sanin sameer a matsayin childhood friend din Deen yasa ko neman izini beyiba suka bude mishi yashiga……. Ashe wajan gidanma wasa ne,wani irin tsari aka yiwa gidan kamar baa Nigeria ba,fadan irin kyawun gidanma bata baki ne ,dan haka nabar muku kawai ku kiyasta……

Har ze nufi part din Deen ya fasa,ya nufi na mahaifiyar Deen,ze iya cewa ya dade bege mutum me kirki kamarta ba shiyasa in dai yazo gidan saiya fara zuwa ya gaisheta….. 

Knocking yayi bakinsa dauke da sallama sannan ya shiga dan shiga yake kai tsaye tsabar yanda ya zama kamar dan gida saboda abokantakar su da Deen….

Zaune take ana mata yankan farce,jin anshigo yasata dagowa…. Murmushi tayi sosai tace “Lah ya sameer yaushe a gari”…. Karasowa yayi yana mayar mata da murmushin yace “Yau dinnan,ina mom?”… Tana ciki asabe tashi ki kirata ta landline.. Mikewa asabe tayi da sauri domin aiwatar da abinda aka sata…..

Da sallama ta shigo parlourn fuskarta cike da fara’a na ganinsa…. “Lale marhaban,son yaushe a gari haka ba labari?”……

“Wlh yau nazo kano,jiya dai na iso”…..

“Ah masha Allah,munyi kewarka wlh,sai katafi kayi zamanka a UK?”

“Yanayin aiki ne wlh mom”…

“Gaskiya ne kuma,amma dai ya kamata ana lekomu,Khadija kuje da asabe a shiryama son abinci”…..

“Okay” Khadija ta fada tana mikewa da sauri….. 

Juyowa mom tayi ta fuskanci sameer tace “Kuna waya da Deen kuwa?”….

“Wallahi bamuyi waya ba for the past one week,idan na kira baya picking,yanzu gabadaya wayarma bata shiga,abinda ya kawoni kenan inji ko lafiya”….

Fashewa da kuka mom tayi tace “Sameer na rasa yanda zanyi da Deen,nema yake kawai ya lalata rayuwarsa da gatansa da komai nasa”…..

“Mom pls stop crying dan Allah kimin bayanin abinda ya faru”… Ya fada cike da tausayinta,abun da ciwo ace ka haifi yaro baka haifi halinsa ba,bawai Deen yanayin wani abun banza bane saidai sam Deen bayajin magana,in dai yasoyin abu to fah ba wanda ya isa ya hanasa,kamar wanda ake zugawa sai yayi abinda yayi niya,sam bayajin maganar Dad sai yaga dama,har gwara ma mom yana dan shakkarta,shiyasa kullum basa shiri da Dad……

“Saida mahaifinsa ya basa warning akan zuwa abujan nan ya kiji,infact a ranar daya dawo ma ya koma,sai kawai mukaji kira wai Deen yayi accident,Haka na lallaba alhaji na nuna masa hannunka baya rubewa ka dauka kayar dan da alhaji cewa yayi yaje ya karata tinda bayajin maganarsa,niko bazan iya jurewa ba a matsayina na mahaifiyarsa…..Da kyar na samu ya yadda muka tafi abujan,in kaga halin da muka samu Deen wlh saika tausaya masa saboda sam baya cikin hayyacinasa,haka likitocinnan suka taru a kansa,a washegari kuma aka nemesa aka rasa can you imagine?” Mom ta fada still tana kuka….

Girgiza kai kawai Sameer yayi dan shi ya rasa ma me zece,hango khadija da maids biya da ita dauke da trays ne yasa mom tashi tacewa sameer bari na baka guri kaci abinci…. Binta da kallon tausayi yayi sanin kuka zataje ta cigaba dayi……

Saida suka shirya dining din tsap sannan maids din suka fita,khadija ce tace “bari nima na baka guri kaci abinci,inka gama mayi hira”….. Daga mata kai kawai yayi yana tinanin to ina Deen ya shiga…….. 

Zaro wayarsa yayi ya sake gwada number Deen,cikin ikon Allah ko sai gata tana ringing amma harta katse baa dauka ba,sake gwadawa yayi ko Allah zesa a dace,kamar a mafarki ko yaga andaga wayar……

“Who is disturbing my sleep” Deen ya fada daga daya bangaran dan daga wayar kawai yayi batareda ya duba suna ba…. 

“ Amma dai wallahi kaji tsoron Allah Deen,muna nan a cikin tashin hankali muna nemanka,kai ashe kanachan hankali kwance har complain kake an dame ka”…. Sameer ya fada rai a bace ganin ashe Deen dinma yana lafiya

Jin muryar sameer yasashi cewa “Bangane kuna cikin tashin hankali ba, kai ba mun aikaka UK ba,toh meye hadinka da abinda ke faruwa a naija?”……

“Dude nashigo fa,tin jiya nashigo nake ta nemanka harji nayi kamar kafi komai wuyar gani a duniyar nan,dan iska ayita kiran wayarka kuma baka dagawa,nafi one week ina kiranka fah”……

Dariya Deen yayi yace “Ta ina zan iya daga waya,ina wata farauta,gashi nima an farautoni ansamin takunkumi,amma a sannu zan nuna musu ni din”?

“Ban gane kana farauta ba?Kodai ka fara biye biyen mata ne bamu sani ba?”…. 

“A’a ya’yan shegu nafara tarawa,idan na gama zan tattarosu in kawo muku”….

“Kai mutumina meyayi zafi haka,ya kamata dai ka chanja hali dan kanasa mom da dad a cikin damuwa”… Sameer ya fada yana dariya,samun Deen dayayi a waya yasasa jin kamar bashi da wata damuwa…….

“Kai bar mom da dad su suke damun kansu,I’m not a kid for God’s sake!”…..

“Toh munji,yanzu kana ina?,there’s something I really want to discuss with you?”…..Sameer ya fada on a serious note

“Kai sanin inda nake yanzu hadari ne a gareka,let’s discuss through phone okay?”….

Numfasawa sameer yayi da yakejin soyayyar fatima zainab ta dirar masa lokaci daya yace”I’m in love”…

Fashewa da dariya Deen yayi yace “sai kamin bayanin kaine ka fara biye biyen matan shine kake going through corners”….. 

“I’m so damn serious bro”…..

“Toh inform her mana,ya kana abu haka kamar wani coward”…… 

“Ba haka bane,the problem is bansan ‘WACECE ITA’ ba….. 

Saida gaban Deen yafadi jin hakan,ya dai daure yace “How can you fall in love with someone you don’t know?”….

“I’ve seen her before,but the issue is khaleel ma yana santa”….

A take ran Deen ya baci jin yarinyar ma wai su biyu suke so,tsaki yaja yace “Kaji wani shirme,ya zaayi ace kana takara da wanchan gayen akan mace,gsky ba girmanka bane,wai ba kacemin yanada budurwa bama,toh wani nonsense ne yasashi son abinda kakeso”…..

“Sunyi breakup da waccan yarinyar ne,shine dan yaga inason wannan yace shima yana so”…..

Tsaki Deen ya karaja yana fadin”Ni wlh takaici kuke bani daga kai harshi,who is she da zakuna irin haka akanta,kilama ba wata abar azo a gani bace,ga mata nan birjik sai wacce ka zaba,kabar masa kawai dan ba girmanka bane takara dashi”…..

“Naso inyi hakan but I love her so much,har wani cika baki yake wai it’s a game muga wanda zeyi winning,kaga idan na hakura sai ya dauka yayi defeating dina ya renani”…..

“Oh haka ma yace?,shidin banza,barshi ze san bashi da wayo,na kuma maka alkawarin saikayi winning game din,dole ya hakura ya bar maka,mark my words!”………

Wani mashahurin farin ciki ne ya lullube sameer,dama abinda yake jira kenan yaji,yasan kuma tinda Deen ya masa alkawari to tabbas ze cikamasa dan shi baya saba alkawari!!……

         Parking motar yayi a parking space din gidan ya fito da sauri ya budemata kamar yadda ya saba,fitowa tayi a hankali ta nufi ciki,karo sukayi da mama da fitowarta kenan daga sashen alhaji….. Fatima zainab bata wani yi mamakin ganinta ba dan tasan dama bazata hakura da alhaji ba….. 

Wani taku mama tayi ta karaso inda take tace “Yan mata yasan ranki?,kinganni nan,nida alhaji mutu ka raba wlh,ina miki albishir da cewa Alhaji ya mayar dani dakina”… Ta fada tana shekewa da dariya…

Bata kulata ba dan bata ita takeba yanzu,abunda yake damunta yafi karfin ta biyewa shashancin mama,part dinta ta nufa mama ta bita da kallo tana jin takaicin kin kulata da fatima zainab batayiba …….

Itako fatima zainab tana shiga ta rufe kofarta ta cigaba da harkar gabanta…….

Wani dariya mama ta saki tuno da sai yanda tayi da alhaji yanzu,abu kamar wasa mallamin chan yace ta kawo dubu dari biyar kan aikin da ze mata akan alhaji,hankalinta ne ya tashi ganin batada wani isassun kudi tinda tabar gidan alhaji,gashi ta tatike kanta tasiya wani dan karamin gida dan bazata iya komawa garinsu ba,hakuri ta dinga bawa mallamin akan dan Allah ya mata ragi,shiko ya rufe ido yace aikinsa kamar yankan wuka yake dan haka shi baya ragi….. Buga buga tashiga yi amma shiru ta kasa hada kudinnan,haka tayi shahada ta karbi loan a bank akan in an mata aikin ta koma tasan dubu dari biyar chicken change ne in tana gidan alhaji…… Haka kuwa akayi takai masa kudin,a take akayi aikin ya bata wani kwalli yace tasa ta kuma tabbatar ta hadu da alhaji dan baa so abun ya kwana gudun kada aikin ya lalace,daga gurin mallamin office din alhaji ta nufa straight da yake da rana ne bayan tasa kwallin,batareda neman izini daga gurin alhaji ba suka barta tashiga dan su sun dauka har a lokacin matar alhaji ce ita…. Tana shiga sukayi ido hudu da alhaji,atake alhaji yaji wata zazzafar soyyayar mama ta saukarsa,yaji duk duniya ba macen daya keso ya kalla yaji dadi kamar mama,wani mahaukacin soyayyar mama ce ta lullubesa har yakejin ba abinda baze iya sadaukarwa a kanta ba,yaji duniyar tadawo masa sabuwa gabadaya…… Daga nan komai ya chanjawa mama,take jin kamar duniyarma a tafin hannunta take tsabar yanda alhaji ya sakar mata komai take jansa kamar rakumi da akala…..

Karasawa parking space tayi tashiga motar data zabi fita da ita a ranar…..

 Driving take  amma ko in kular da fatima zainab tamata ya tsaya mata a rai,bata tabajin ta tsani mutum kamar yanda takejin tsanarta ba,ita bataki  ta taka fatima zainab da mota ta mutu kota ji sanyi a ranta,wata zuciya ce tashiga zugata akan tayi wani abu yau,yanda ganin fatima zainab ya zama kamar ruwan dare gwara tayi using wannan opportunity din,gashi kuma sai yanda tayi da gidan a yanzu so ko tayi wani abu tasan babu wanda ze daga ido ya kalleta,petrol station din dake kusa dasu tanufa,shiga tayi ta siya petrol 25ltr,sukasa mata a boot ta nufi gida….. Me gadi na bude mata gate tace yazo inya rufe… Sashi tayi ya daukar mata petrol din ta nufi sashen fatima zainab yana biye da ita….. Sashi tayi ya ajye ya dauko mata ashana,dauko ashanar yayi yana mamakin mezatayi dashi….. 

“”Dauki petrol dinnan ka watsa minshi a ko ina na building dinnan”…. 

“Ban fahimceki ba hajiya” Ya fada a diririce ganin fatima zainab na ciki dan yaga shigarta,yana zaune kuma bega ta fito ba

Wankeshi da mari mama tayi tace “Dauki ka zuba nace,ko a bakin aikinka wlh”…..

Dafe inda ta maresa yayi ya shiga bata hakuri yana fadin “Da mutum fa a ciki hajiya”….

“Eh ai nasan da mutum din,konata zanyi”…

“Dan Allah dan annabi hajiya kiyi hakuri karkiyi kisa”…

“Ina ruwanka dan ubanka,zaka zuba ko kuwa?”….

A guje ya fita daga gidan ganin kiri kiri zaa sashi yayi kisa,shiko da yayi wannan danyen aikin gwara ya rasa aikin kawai….. 

Kundume kumdume mama ta hau yi ganin ya fita a guje,nan ta dau petrol din ta hau watsawa a ko ina na building din,da yake kamar isolated site haka yake a gidan,shine gini na karshe kuma da tazara da sauran……

Saida ta tabbatar ko ina ya juku da petir sannan ta kyatta ashana,take ko ginin ya kama da wuta,budar bakin mama ta furta “Alhamdulillah” tanajin wani sanyi a ranta,sun rabu da alakakai!!!!

I guess this will be the longest page ever😪

~Unique Barakancy~

Back to top button