Hausa novels

Halysaah Page 83 By Khaleesat Haydar

HALYSAAH PAGE 83…Sun sauka garin Kano karfe takwas bai karasa ba na safiyar, motar da zai dauke su har ya iso airport din yana jira, bayan drivern ya saka luggages din a booth Jay ya bude ma Khaleesat back seat ta shiga tana dan murmushi cikin sanyin murya tace “Thank you” murmushin yayi mata shi ma ya bude front seat ya shiga, Khaleesat tried her best to stay positive kamar yanda Jay yace mata all through the ride home, but she is excited and still tensed at the same time, suna isa layinsu driver yayi parking dai dai inda Jay yayi instructing dinsa, Khaleesat ta sauke boyayyen ajiyar zuciya, Jay ya juya ya kalleta tayi murmushi a hankali tace “Thank you soo much Housemate” Har ta mance rabon ta kirasa da hakan a gabansa, shi dai kallonta kawai yake can yace “I don’t understand why you are thanking me for” Langwabe kai tayi tana murmushi tana kallonsa yace “Za ki sani” Tuni Drivern ya sauka daga motar ya zaga zuwa booth, Jay ya sauka shi ma ya nuna masa luggages din ta, Khaleesat na sauka daga motar yaran makotansu na kyallara ido suka ga ita ce suka taho da gudu suka baibaiyeta suna Oyoyo, Jay dai ya juya yana kallon ikon Allah, yaran ta hada da boxes dinta su shiga mata da shi gida, duk suka fara rige rigen dauka, ta juya ta kalli Jay tana murmushi tace “Zaka shiga ciki ne?” Ya rungume hannunsa yace “A’a, amma da yamma zan zo in sha Allah” A hankali tace “Allah ya kai mu” Yana murmushi yace “Ameen Halysaah” Ita ma murmushin tayi tace “Amma zaka dan kwana biyu a Kano before going to Bauchi?” Yace “A’a, gobe zan tafi in sha Allah, Mai martaba is worried about how of recent we are traveling separately with Ajay which is unlike us, kinsan for many month now bama tafiya tare kuma ba haka muka saba ba, duk tafiya tare muke yi da shi, so his highness is worried may be we had issues that we are hiding away from him, muna Turkey ya kirani nace masa gobe zan shiga Bauchin in sha Allah….” Khaleesat dai tayi shiru tana kallonsa, can ta sauke idonta tace “Toh Allah ya kai mu goben” Yace “Ameen” Dubu hamsin rudin Nigeria ya dauko a gaban motar da alama Drivern ya sa ya taho masa da shi, ya mika mata yace “In case you will need anything Halysaah” Khaleesat ta zaro ido tace “A’a ni babu abinda zan bukata wallahi” Juyawa tayi zata bar wajen yace “Halysaah” Ta juyo amma bata ce komai ba, yace “Bana son kina min haka, ba ni na baki ba?” Ta marairaice tace “Wallahi ni babu abinda zan yi da kudi, beside i have money in my account, don Allah kayi hakuri ka bar shi Nagode” Ya hade rai yace “I didn’t ask weda you have money or not, ni na baki ki amsa bana son musu” Khaleesat tayi shiru tana kallonsa, lokaci daya jikinta yayi sanyi sosai, ganin kallon da yake mata ta dan risina ta amshi kudin a sanyaye tace “To Nagode, thank you soo much, Allah ya saka da alkhani… Bai jira ya gama sauraronta ba yace “Ki gaida rain su Umma, sai na shigo anjima in sha Allah” Ta gyada masa kai tana kallonsa, ya zaga ya bude front seat ya shiga, Jiki a sanyaye ta juya zata shiga gida taga Mama Shatu da Mama Zubaida suna lekosu ta bakin kofa da ‘ya yansu kariana gaba daya, sai a sannan ta lura da sabon kofar da aka saka a entrance din shiga cikin gidan nasu, lokaci daya su Mama Zubaida duk suka bar bakin kofar, ta kalli yaran da suka shigar mata da akwatunanta don auk suna tsattsaye a kofar gidan suna kallonta tace “Nan da minti talatin duk ku shigo ku amshi tsaraban ku kun ji” Murna suka fara yi gaba daya suna tsalle, ita dai tayi murmushi ta karasa ta shiga cikin gidan, step Siblings dinta duk suka yo kanta suka rungumeta suka dinga mata Oyoyo cike da farin ciki dama iyayen ne suka hana su fita kofar gida su je wajenta, Khaleesat tace “Ba ku je islamiyya bane?” Dan Mama Shatu me suna Sulaiman yace “Ba a biya mana kudin wata ba Aunty” Khaleesat tace “Nawa ne kudin watan?” Yace “Dubu uku ne” Khaleesat ta kalli Aunty Farida da ta fito daya cikin dakin Umma ta tafi cike da farin ciki ta rungumeta, Aunty Farida dai sai murmushi take ta dago kanta tana kallonta ganin yanda ta yi kumari sai wani glowing skin dinta yake, Aunty Farida tace “Sannu, ya hanya Khaleesah, Junaid din na kofar gida ne?” Khaleesat ta bude ido tace “Ya Jawwad fa nace maki ba ya Junaid ba, ai ya ma tafi yace sai da yamma zai dawo, Aunty su Islam sun tafi islamiyya ne? Ummata fa?” Aunty Farida tace “Su Islam na islamiyya, Umma tana daki” Khaleesat na murmushi tace “Toh ina zuwa in ba su Sulaiman kudin wata” Daga haka la koma gun Step Siblings dinta dake tsaye sun yi cirko cirko a tsakar gidan suna kallonta, Dubu hamsin din hainunta ta cire dubu uku ta mika ma Sulaiman don shi ne babba cikinsu, sauran kananun yaran maza da mata ma haka ta dinga bin su tana kirga dubu uku uku tana mika masu, nan take sai da ta rabar masu da dubu talatin da shidda, suka diriga cewa saura Munzali, Khaleesat tace “in ya dawo ya sameni sai in basa” Murna yaran suka dinga yi a tsakar gidan, ta juya ta kalli inda kishiyoyin Ummanta ke zaune daga bakin kofar su ko wacce ta tabe baki gashi sai naso suke, ga wani uban tagumi da Mama Zubaida ta zabga, karasawa tayi har inda suke ta gaida su with respect, a dakile duk suka amsa mata kamar dole, babu ya hanya babu komai sai ido da suke bin ta da shi, Khaleesat ta juya ťa tafi dakin Ummanta don Allah Allah take ta ganta, tana shiga cikin dakin ta rungume Umma cike da farin ciki tace “Ummana na dawo” Umma na murmushi tace “To sannu da zuwa Khaleesah, ya hanya?” Khaleesat tace “Alhamdlih, Babana fa?” Umma tace “Ya fita kasuwa, Ahmad din ya tafi ne?” Khaleesat na murmusii tace “Eh ya tafi, yace sai da yamma zai zo” Umma tace “To Allah ya kai mu” Umma dai kalionta kawai take ganin yanda tayi kyau sosai, Khaleesat ta mike ta jawo akwatin ta zata bude wanda tulin Chocolates din da Jay ya siya mata suke ciki, ta ciro daddaya zata ba yaran makotan da suka shigo mata da kayan daki, ta hada ma ko wani yaro da dubu daya, don duk baza su wuce su goma ba, Aunty Farida ta kasa daina kallon Khaleesat don taji dadin yanda ta ganta sosai ba kadan ba, Aunty Farida tace “Ki garra rabe raben tsaraban ki je ga ruwa can zan juye maki kiyi wanka sai ki karya” Khaleesat dai sai kirga Chocolates din take don har da na Step Siblings dinta take son ta cire. Karfe sha biyu da yan mintuna Nenne ta shigo gidan fuskarta babu yabo babu fallasa, har ta cire gyalenta zata rataye saman igiya ganin tsakar gidan cike da hayaki don su Mama Shatu na ta girkin siyarwan su ta fasa ta nufi dakin Umma da gyalen a hannu, ko amsa gaisuwan su Mama Shatu bata yi, tun da Umma taji muryar Nenne ta fara ma Khaleesat mita tace “Sai da nace ki je ki gaisheta kafin ta samu labari kin dawo, yanxu sai abinda ta manta ne bazata fada mana ba” Khaleesat dai na kwance saman gadon Umma tana danna wayarta, tun da tayi breakfast take son tayi bacci amma yan unguwan sai shigowa dakin Umma suke wai yi mata sannu da zuwa, alhalin da yawansu gulma ce ke shigo da su ba komai ba, ga Sha’awa da taki tafiya tun da ta shigo dakin kusan awa daya da rabi kenan, har da wasu makotansu biyu duk sun zauna sun ki tafiya ko me suke jira oho, Nenne na tsaye daga bakin kofa don labulen dakin a dage yake tace “To Zahra’u sai me don Khaleesah ta dawo anki zuwa a gaya min ko kuma a turata ta gaisheni har sai da almajirina ya shigo ya gaya min, naga dai ba don ni ba ai ko iyapot bazata sake zuwa ba balle har ta koma wata Amurka, kuma ba wani ya haifar min uban nata ba dai da za a dinga nuna min an fi ni iko da ita” Khaleesat dai tayi murmushi ta sauko daga kan gadon ta zauna kasa tace “Sannu da zuwa Nenne” Nenne ta kauda kai ta tsirtar da yawu ta kalli su sha’awa tace “Su kuma wa ennan fa? Baku ganin dakin babu sareri gashi duk ya dume bayin Allah sai shakan raumfashin juna ake, ke sha’awa zanin daddawan naki kika shigo dakin mutane da shi kika zauna? Haba ki dinga ji tsoron Allah mana sha’awa” Mikewa sauran makotan biyu suka yi suna kallon Khaleesat suka ce “Allah ya huce gajiya Khaleesah” Daga haka suka nufi kofa suna gaida Nenne suka fita, Nenne ta tsirtar da wani yawun tace “Tabdijam….” Sha’awa ta mike tace “Nenne shigowa ta kenan babu dadewa na zo yi ma khaleesah sannu da zuwa, ashe ma tun da safe ta iso, ina can na gama curin daddawa ban san ta dawo ba” Nenne ta bata hanya da sauri don kar ta goga mata jikinta, a haka Sha’awa ta fita daga dakin, Nenne ta kalli Umma tace “LallaiZahra’u kina da aiki, ke ba kazama ba ki bar mata kazamai su shigo maki daki su cıka da warin jiki har da me daddawa? duk dakin ki ya dume ba dadin shaka? yanxu da kin yi bakon kunya ina zaki ajiyesa, ga daki ba daki ba kamar zuciyar talaka, halan ina parida ta tafi don dai nasan da tana nan da tuni ta fatattake yan iska ta koresu, to dai duk komai ya zo karshe, Alhamdulillahi tun da Khaleesalı ta dawo lafiya zuwa nan da yan kwanaki kadan sai mu tattara mu bar tsinannen unguwan nan mu koma inda bawon Ailahn can dan albarka Ahmad ya siya mana, dama dai ni ce nace lallai sai an jira ta dawo tunda ta dalilinta aka yi mana wannan abun arziki baza mu yi mata butulci mu tare a gida babu ita ba, shi ne nace lallai ita zata jagorance mu zuwa sabon gidan a bude mu shiga cikin farin ciki, saukan al-qurani dama na saka anyi yafi a kirga a gidan, shikenan Allah ya rabamu da masu warin unguwan nan kuma haka” haka Nenne ta ajiye kwanon hannunta tace “Ga shi nan kwadon zogala na maki da naji ance kin dawo, to Ahmad din fa?” Khaleesat tace “Sal anjima zai shigo” Nenne tace “Ai ko bari in maza in tafi in dora masa tuwon shinkate da miyar agushi, in bada dubu biyu a siyo min nama me kyau in zuba a miyar” Daga haka ta juya da sauri tana yafa gyalenta ta rufi kofar fita daga gidan, Umma dai murmushi kawai tayi, Khaleesat ta kalleta tace “Dama Nenne ce tace baza a koma gidan ba Umma?” Umma tace “Gashi nan ta gaya maki kuwa, babanki ma bai yi na’am da gidan ba har yanxu” Mikewa Khaleesat tayi bata ce komai ba, ta dauko kwanon da Nenne ta ajiye mata ta bude, ai ko taji dadin ganin zogalen don hadadden hadi Nenne tayi masa. Wajen karfe hudu da rabi Jay ya zo gidansu Khaleesat, bayan sun gaisa da Umma da Aunty Farida Khaleesat ta dauko masa bottle water din da ta siyo masa ta ajiye masa, Aunty Farida dai sai godiya take masa ya ma kasa kallonta yana dan murmushi kawai, Khaleesat ta zauna gefen Uinmanta tana kallonsa babu ko kiftawa, tsadadden Gezna ne fari jikinsa, kayan sun masa kyau ba kadar: ba, anya ta taba ganinsa da manyan kaya kuwa, ya fito sak Hausa Fulani yau, Aunty Farida tace “Za ku karasa canı gidan Nenne da shi ai ko?” Khaleesat ta gyada mata kai sannan ta mike, Hijab dinta ne har kasa jikinta dama, ta dau nikab ta dora, ta fita tsakar gida tana jiransa, after almost 5 minutes ya fito daga dakin, step mothers dinta dake tsakar gida duk suka kafesa da ido kamar yanda suka yi san da ya shigo, Khaleesat dai ko kallonsu bata yi ba ta nufi kofar fita gidan ya bi bayanta, sai da suka fita kofar gida ya kalleta yace “What is this u are covering ur face with Halysaah?” Dariya tayi tace “Nikab ne baka sani ba?” Kallonta kawal yake suna tafiya, can yace “Tell me why you are covering ur face?” Tana murmushi tace “Saboga kallona za ayi ta yi a unguwan, kuma na saba sakawa in zan fita dama” Murmushi kawai yayi bai ce komai ba, a hankali tace “Ko in cire?” Ya kalleta yace “A’a, gwara haka, kinga za a rage kallon ki” A haka suka isa gidan Nenne. Nenne ta rasa inda zata sa Jay tsabar tarba, ta kinkimo masa gaba daya coolern tuwon da tukunyar miyan ta dire a gabansa, lemon kwalba kuwa dama guda biyar ta sa aka siyo masa da ruwan gora biyu, shi dai sai murmushi yake gashi ba yunwa yake ji ba, Khaleesat ma sai murmushi take, can ta cire nikab dinta ta ajiye, Nenne tace “In ma kunyata kake ji bari in shiga makota ka ci tuwonka ka koshi, don kai kadai nayi tuwon nan wallahi in ma baka ci da yawa ba wallahi bazan ji dadi ba, wanda ka rage ma a leda zan juye maka ka tafi da shi, ni ko gurin Zahra’u sai in je anjima ta tsam min tuwon daren ta…” Daga haka Nenne ta yafa gyalenta ta fita daga gidan, Khaleesat sai kallonsa take tana murmushi, ya cire hulan kansa ya ajiye gefe don har ya fara zufa ganin abincin da aka dire masa, yana kallon tuwon yace “Ya za ayi da tuwon nan Housemate, Ni fa na ci abinci kafin in fito wallahi” Khaleesat tayi dariya tace “Haka nan zaka tuttura ka ci, kasan tun yaushe take maka girkin nan kuwa?” Plate ta jawo ta saka tuwo daya, ya zaro ido yace “I can’t finish even quarter of this Halysaah, a koshe fa nake” Dariya kawai take bata tankasa ba ta bude tukunyar miyan dake ta kamshi ta zuba miyar a wani bowl daban, ta saka nama yanka hudu, ta maida tukunyar miyar gefe tace “Oya gashi” Ya kalleta yace “Where am I going to start from? Billah i am full, ki ci don Allah…” Khaleesat ta wanke haniunta ta dau cokali ta dibi tuwon da miya tana kallonsa tana….

Back to top button