Hausa novels

Kurkukun Kaddara Takun Farko Chapter 53 By Hafsat Bature

💋KURKUKUN ƘADDARA💋

E53

Wuff suka mimmiƙe kusan atare suka Juya suna kallonta, Daga ita sai jar vest da short, Ƙirjin nan gasu nan tulu tulu, kana ganin fatarsu daga sama ga zanan tatoo ɗinta na bindin ɗawisu,
Da yake basu iya gulmar ba, da wasu ne cewa za su yi a’a amma sai suka haɗa baki wurin cewa”Eh, muna faɗin ra’ayin mu ne akan ki, An kawo mana masifa ke da Majnun,” ruƙe ha6a tayi can kuma saita saki dariya tana nuna su da zira ziran yatsun hannunta, cike da shaƙiyanci cikin harshen turanci tace”Idan na fahimce ku, kamar kuna kishi ne akaina, saboda kunga abu tubarkalla ba kamar naku ba, ashafe kamar allon bango, Ni fa kokwanto nake yi akan ku anya mata ne kamar ni? Cos ba ku da banbanci da ƙattan dake acikin ku, Komai naku irin na maza ne babu ƙirar mace a jikin ku”

tsabar mamaki yasa suka saki baki kamar wawaye suna kallonta, Hibbe ce tai ƙoƙarin mayar mata da martani wurin cewa”To angaya miki muna son nonon ne, ƴar rainin wayau, sai kace ba ɗazu kika gama yunƙurin kashe kanki ba, ae da mun san haka ki ke wlh da mun ƙyale ki…..” hibba bata ƙarasa maganar ba, sakamakon tsawar da ƴar gidan daddy ta kwatsa mata, har saida suka ɗan girgiza saboda sautin ta da tsiwa yake fita.

“Da alama ku ɗin dabbobi ne, Nasan ba ku san me ake nufi da dabba ba, saboda na lura Jahilai ne ku baku san komai ba, shiyasa aka killace ku kamar yadda ake yi ma dabbobin, A katafaren gidan daddyna akwai irin ku da ake killace wa, muna da zoo don dai banzo da wayata ba dana nuna maku yadda nake watsawa ƴan uwanku dabbobi hatsi Suna Ci” Duk da basu fahimci me take nufi ba, amma sun yi matuƙar har zuƙa, Sai tsuma suke yi.

ita ko sai tiƙar dariya take yi fararen haƙoranta kamar bata ta6a cin abinci ya gifta ta cikinsu ba, hannu takai tana shafa boobs dinta hada matsasu Yayin da take kallon su tace”Gaskiya najiye maku baƙin ciki, Waɗannan da kuke gani, majiyar daɗi ne su, sai da su ake ado, dasu ake jan hankalin Namiji, ae duk macen da bata da wannan to bata da banbanci da dutse a idon namiji, babu wani wuri da za’a ata6a ajikin ku aji shauƙi, A bushe ku ke.

A matuƙar ruɗe suka kallonta, sun gaza gane inda zancen ta ya dosa, da ya ke ta mai da su shashashu hada cewa idan suna son ganin nata zata nuna musu, don su tabbatar cewa ita ɗin macace ba kamar su ba da suke abushe,” shiru su ka yi babu wanda ya tanka mata.

Dariyar shaƙiyanci ta kuma saki tana wasa da harshe tace dasu”wai sun ma san yadda ake yin mu’amala da mace da Namiji? Ko mace da mace? Idan suna so zata koya musu har ma da yadda ake samun baby” Kallon kallo su ka shiga yi atsakaninsu, kamar suce mata eh saboda suna san sanin me take nufi amma sun kasa.

“Alamu sun nuna cewa kuna so, to zan fara koya maku yadda ake yi, ni kawai i naso in wayar maku da kan ku ne, ta yadda zamu dinga jiyar da junanmu daɗi,” babu wanda ya lura cewa azeeza ta gudu zuwa cikin ɗakin su, tana shiga taje gaban gadon angel ta fashe da kuka tana kiran sunanta, a lokacin angel har ta fara bacci can cikin kunnanta ta dinga jin shessheƙar kuka Azeeza, a firgice tafarka tana faman yamutsa fuska, azeeza bata jira ta gama buɗe idonta nata ba, taci gaba da magana tana fadin

“Angel kizo ki gani, ƴar gidan daddy zata 6ata mana tarbiya, wai zata koya mana yadda ake samun baby,” tashin hankalin da ba’a sama shi date, saboda tsabar ruɗu, A fujajen angel ta ƙarasa waro manyan idanuwanta akan fuskar azeexa hannunta dafe da ƙirjinta take kallon azeeza sai ku ke ta ke yi baiwar Allah.

“Wai hada cewa mu ba mata bane, ƙattai ne, saboda bamu da irin ƙirjinta, kuma ma wai jahilai ne mu ana kullemu kamar dabbobin gidansu….’ daƙyar angel ta samu tatattaro maganganun azeeza da suka tarwatsa kwakwalwarta, ta haɗesu wuri ɗaya ta karance su tsaf, tunaninta ya dawo kan saiti lokaci ɗaya ta fahimce su sosai, Muryarta afusace tace”yaushe akai hakan? Ki faɗa min tana ina”

Ta yi maganar tare da wurga eye balls ɗinta kan gadon unaiza bata ga kowa ba, Ruƙo hannunta azeeza tayi ta sauko daga saman gadon taja ta har zuwa sashen toilet ɗin su, tun kafin su shiga ta soma jiyo sautin muryar Ƴar gidan daddy tana koya musu yadda zasu Kusanci junansu, Wata irin kururuwa angel tasaki Yadda kasan Badakare ya durfafi filin yaƙi haka ta faɗa Cikin toilet ɗn, Hankalinsu gaba ɗaya ya dawo kanta, Sai huci take yi idanuwan nan sun kaɗa sunyi jawur, Unaiza kuwa koda angel ta faɗo toilet din bata daina magana ba, saboda tsabar futsara hada cewa”halan itama tazo ɗaukar lecture ne” Wani irin kukan kura angel tayi bata dira akan kowa ba sai asaman jikinta, gaba ɗaya suka kife ƙasa, wani irin jahilin bugu tadinga kai mata kamar xata kashe ta, tana kuka tana fadin”wlh baki isa ba, ashe baki da hankali wawayi kawai Jakkar banza, Ae babu babban jahili sai ke daƙiƙiya, Kuma ke ce dabbar badai su ba, Dama ni nasan zuwanki Cikin rayuwarmu ba alkhairi bane, saboda babu kunya atattare dake ƴar iska kawai…..” kuka sosai Angel da unaiza suke yi, Duk ta gurjar mata baki hada jini, Su hannah sai kuka suke yi suma suna roƙon Angel akan ta ƙyaleta kada ta kashe ta,

tace musu ae ƙwara ta mutu saboda shaiɗaniyace ba mutun ba, Sautin Kukan Unaiza ne Ya isar ma kunnuwan masu bacci na cikin ɗakin, ba arziƙi suka farka danish da Gabriel hada Sarah da jamima, hatta majnun sai da ya farka, Bomb ya tashi sauƙi sai wurin Allah,

Da gudun gaske Su Gabriel suka nufo Ciki toilet ɗin, a lokacin har Unaizah ta sume, Amma ita angel bata sani na, bugunta kawai take yi ta haukace bata ji bata gani, Da ƙarfi Danish ya sanya hannu ya damƙi damtsen hannun angel ya janyeta daga saman Unaiza ya jefar da ita gefe ɗaya, Sai faman haki take yi hawaye ta ko’ina kan fuskarta, Sai kace ita aka buga bayan itace tayi mata jahilin bugu, abunda bata ta6a tsammani ba, Danish Ya rufe ta da faɗa ta inda yake shiga bata nan yake fita ba, Kowa laifin Angel yake gani saboda basu ga hujjar da zaisa ta tayi mata irin wannan mugun mutuwarba, hatta haris sai da yayi mata faɗa, Deeja dai bata ce komai ba, saboda ita ta yarda da angel sosai tasan cewa tabbas wani mummunan abunne Ƴar gidan daddy ke ƙoƙarin bijiro musu dashi shiyasa tayi mata wannan kafurin bugun, Su hanna ma suna abayan angel, gaba da baya, kawai basu ji daɗin bugun da ta yi mata ba ne, Javed ma yana goyan bayanta, shi ko gabriel babu wanda ya ke supporting acikin su, shi da sarah, Waɗanda ke goyan bayan Unaiza danish da haris, ba yadda ba su yi da ita ba akan ta faɗa musu me unaiza tayi mata da har ta sumar da ita amma taƙi gaya musu, gudun kada ta rudar da tunaninsu, abune da basusan da shi ba, yanzu idan suka ji tofa za’a samu matsala wani daga Cikinsu zai ƙwallafa rai akan son sanin ya akeyin abun, daga nan kuma za’a iya samun matsala, su kuma da suka ga taƙi faɗa musu sai suka yi tsammanin ta tsani Unaiza ne shiyasa ta bugeta ba gaira babu dalili.

Zuciyarta ta ƙuntata sosai Musamman lokacin da Danish ya nuna ta da indext finger ɗinshi ya gargaɗe ta akan karta kuskura ta ƙara ta6a lafiyar jikin ƴar gidan daddy,” Ta zazzaro idanuwanta waje tana kallonshi, muryarta cikin kuka tace”Bazan daina ba, bugunta yanzu na fara wlh, kai ɗin banza har ni zaka nuna da yatsa akan na bugu wannan jakar yarinyar” Sosai angel ta zazzaga musu masifa, daga cikin sashen toilet ɗinsu har zuwa cikin ɗakinsu kana Iya jiyo muryarta, saboda tsiwarta, bayan ta gama masifar, ta kalli su hanna tace su biyo bayanta, su koma ɗaki, Su kuma su haris ga ƙanwar babarsu nan suyi jinyarta, kuma idan ta farka su gargaɗe ta akan karta kuskura koda gigin wasa tace zata ƙara shiga gonarta, babu ruwanta da ƴan uwanta, ” Bayan fitarsu angel daga Cikin toilet ɗin, suna shiga Cikin ɗakin su suka samu Majnun, Ya hargitsa duk wata shimfiɗa, Ya watso da bargunansu da fululluka, wannan karan hada akwatin kayansu ya zazzage komai na Ciki Ya watso su waje, Ya kinkimo madubin nan nasu Yana ƙoƙarin kwaɗa shi da ƙasa, Suka haɗa baki suna faɗin Karya kuskura Ya fasa musu madubi,” Dariya ya kama yi yana yi musu gwalo, hada ɗaga musu gira yana murmura musu idanuwanshi Sai ma ya maida abun wasa idan ya ɗaga sama sai yace musu”In fasa? Zan fasa” Daga ya yi yunƙurin ƙunduma shi da ƙasa da gudu suke tunkarar shi, Ya dinga yi mu su yawo da hankali, har suna tuntu6e wurin binshi, Saboda bargunansu dake yashe ƙasa, duk in suka ɗaura ƙafarsu, laushin jikinsu ke fusgarsu kamar zasu kife ƙasa, Sun ci baƙar wahala gashi suna matuƙar son madubin, Sun rasa ya zasuyi da majnoon akan Ya ƙyale musu madubinsu.

Angel tuni ta nufi gadonta ta kwanta tana ci gaba da yin shessheƙar kuka, zuciyarta duk ba daɗi, zuwan unaiza ya tarwatsa farin cikinsu, Ta zamar musu tamkar annoba, bakomai yafi tsaya mata arai ba face yadda Danish Ya nuna ta da yatsa, duk don saboda ta bugi ƴar gidan daddy, dama ta lura ba ƙaramin jan hankali shi take yi ba da ƙirjinta, nan take zuciyarta ta dinga raya mata cewa sonta yake yi, shiyasa yake goyan bayanta, kamar jinjira haka tadinga kuka bame lallashinta,.

Acan Cikin toilet kuwa, Bayan fitarsu angel, Ya rage saura Danish da Haris sai Sarah da Deeja, don tuni gabriel Ya koma cikin ɗakin su, Da taimakon shi su parveen suka kar6e madubin nan daga hannun Majnun, shi ya damƙe musu shi da dabara, ya cafko shi ta baya, aiko yasha bugu a wurin parveen har zaune shi tai, yai ta ihu yana faɗin zata kashe shi, daƙyar su Hibba suka raba ta dashi, tana huci tana jifar shi da harara, tafi kowa tsanar yaron kamar ta kashe shi.

*Toilet*

Sarah ce ta ɗebo musu ruwa a tafin hannunta suka watsa saman fuskar Unaizah nan take tafarka tana kuka tana ambaton Sunan mommy da daddy tana faɗin where are they? Suna gani mahaukaciya zata kashe ta, zata rabata da rayuwanta amma basu iya zuwa sun cece ta ba, ita ba za ta Iya zama School ɗin nan ba, ko dai su cire ta ko kuma ta kashe kanta, ta gaji da rayuwa cikin dabbobi, ” duk wannan Sambatun da ta ke yi akan kunnan su haris, kuma ko kaɗan basu ji haushin kalamanta ba, saboda kallon yarinya suke yi mata,

“Jikinta zafi, ba ƙoshin lafiyane da ita ba, amma taƙi natsuwa ta kwantar da hankalin ta,” sarah ce tai maganar, Haris yace”Batasan ciwon kanta bane shiyasa, Ni zan koma ɗaki, Danish gata nan kusan yarda zaku yi da ita, lamarinta ya fara gundurata,” da biyu yae maganar ganin irin kallon tsanar da Unaiza ta ke jefa mashi, jini duk a hancinta amma masifa ta hana ta shiga taitayin ta.

Fuce wa yae daga cikin toilet ɗin, kamar jira ta ke haris ya fita, ta ɗaura idonta akan Danish dake zuƙunne gabanta, duk da tana acikin mawuyacin hali, hakan bai hana ta nuna halin nata ba, hannayenta ta ɗaura saman shoulders ɗinshi, ta rurruƙeshi tana zuba mashi ruwan shagwa6e, A ƙarshe ma sai ta kalli sarah da ta rage acikin toilet ɗin tace da ita”Ki tafi kawai, nagode da taimako, Danish zai ɗauke ni mu dawo ciki,”

Sarah na fita daga cikin toilet ɗin Ya rage saura su biyu, Cikon na ukun su shaiɗan sai kuma ni da nake rubuta littafin.

janyen hands ɗinta tai daga saman kafaɗunsa ta tallabo fuskarshi da su, ta marairaice mashi fuska tana faɗin”Kana ganin irin bugun da ƴar uwarka tayi mini duk ta fasa mini jiki, ni bansan me na mata ba, she hates me for no reason, i don’t know why bata son gani na”

magana take yi amma hankalin shi gaba ɗaya yana kan ƙirjinta da take ta turo mishi su, sun cika mishi idanuwan shi, ta ko’ina ya rasa sukuni ya rasa madafarshi, linzamin shi na niyar kubce mishi, Shu’umin murmushi ta saki ganin yadda maƙogaran shi ke ta yin sama da ƙasa kamar yana haɗiyar yawu, Ƙara kashe mishi mirya tayi tana fadin”kalli fa gani duk ta raunata min jikina” tae maganar tare da sakin face ɗin nashi da ta tallabe da hannunta biyu, ta zaune dirshan tana ƙoƙarin zame ziririn hannun vest dinta, Gabanshi yae mugun faɗuwa, da sauri ya damƙi hannunta yana girgixa mata kai, muryar shi ƙasa ƙasa ya furta”Ba sai na gani ba its ok, ki yi haƙuri bata kyauta miki ba, amma kema ki daina yin abunda zai 6ata mata rai, angel tana da mutunci bata tsani kowa ba, sai dai rashin fahimta ne dake atsakaninku,” Yatsina fuska tayi, tana faman cizon le6enta, ta kuma cakumo gaban rigarshi tana yamutsa tace”ni ba wannan bane damuwana ba, ka tuna alƙawarin da ka yi mini na cewa komai nake so zaka yi min” lumshe mata ido yae alamar ya tuna, hakan ba ƙaramin daɗi yae mata ba, ɗaga mashi gira tai tare da cewa zan fada maka, amma a kunnanka, bana son wani yaji,” kafin yace wani abu ta rungumo shi jikinta, tare da kai bakinta saitin kunnan shi tayi mishi raɗa, Ni kaina bansan me ta faɗa mishi ba, raba jikinta ta yi daga nashi, yayin da idanuwansu ke kallon Cikin na juna, batare da ƙyaftawa ba, Allah kaɗai yasan me ta faɗawa babyn angel,

(Yanzu zan saka maku page 54, Idan kun gama da wannan ku duba zaku ganshi, Masu son karanta middle Step book 2 whatsapp suyi min magana 08103884440 masu son facebook paid group Ga link ku danna shi za kaiku ga wadda zaku yi ma msgana👇)

 

Click Here To Download Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete

 

 

( mu hadu next page In Allah yakaimu da rai da lafiya, masu yi mun ya jiki ina godiya)

Back to top button