Uncategorized

Kishi Da Aljan Chapter 7 Complete Hausa Novel

 

Shi kanshi me keken kallon Zainab yake yana dariya ganin irin shaƙiyancin da take zuba ma baiwar Allah

Seda sukai nisa tukun Zainab ta dawo da kanta cikin keken, 

Ɗaure fuska tai mur ganin yarda me keken ke ƙoƙarin fara mata magana,

Haɗe girar sama da ta ƙasa tayi tana ci gaba da shafa bayan ƴar baƙa da ke ta sharar baccin ta.

A daren, Abbah yayi yayi da Abdul ya haye can kan gadon na shi ya kwanta

Ƙememe Abdul ya ƙiya, sedai ya miƙe akan doguwar kujerar dake cikin ɗakin, nan da nan bacci yai awon gaba da shi.

DUNIYAR MAFARKI!!

Daji ne me tsananin duhun tsiya, daji ne dake tsakiyar wani teku da wasu manya-manyan baƙaƙen duwatsu masu irin tsinin nan zagaye da wurin.

 duhu ne ta ko’ina

Shi kaɗai ne halittar shi daban a cikin su.

Wasu halittu ne da baki baze iya misalta su ba, ido baze iya jure ganin su ba

Abdul ne zaune a wata kujera ta alfarma, hannuwan shi a ɗaure haka ma ƙafafun shi, sannan an ɗaure saitin cikin shi da kujerar da yake zaune

Wasu halittu ne tsaitsaye da baya ganin farkon su ballanta na ƙarshen su.

Wurin yayi shiru, baka jin motsin kowa da komi

Hatta da tekun dake zagaye da su baya motsi, a tsaye yake cak kamar yarda wannan halittu ke a tsaye ƙyam

Wata sangamemiyar halittace ce ta fito daga cikin wani kogon dutse

Da wasu kalar kaya da babu irin su a cikin duniyar mu

Tun daga kanta har ƙasan ta gashi ne ya rufe ta, baka ganin komi da zaka iya gane ko tantance kalar ta ko kuma yanayin ta

Irin halittar ta ce sun kai su gome sha tsaye a bayan ta

A firgice Abdul ke kallon ko’ina, 

ƙiri-ƙiri so yake ya kulle idon shi ya dena ganin abinda ƙwaƙwalwar shi take gab da tarwatsewa amma sam kamar an saka hannu an rirriƙe fatar saman idon shi, 

Idon shi ya ƙame, bakin shi ya bushe, miyan bakin shi gaba ɗaya ya ƙame

Tsoro ne ta ko’ina, duk inda ya kalla zega halittar da ta fi wacce ya kauda kan shi akanta

Addu’a yake so yayi, amma kamar ansaka abu an danne meshi harshen shi

Abdul na a wannan yanayi ya fara jin sarewar nan da ke mantar da shi abubuwa da dama

Wannan karon kam, yana fara jin sarewar nan, ya nemi tsananin tsoron nan da yake ji ya rasa

A hankali igiyar da aka ɗaure mishi hannuwa da ita ta kwance,

Na cikin shi ma ta kwance, sannan na ƙafar ma suka kwance

Be ankara ba yaji anyi sama da shi, 

kiftawa da bisimillah aka canja kujerar da yake zaune akai me cin mutum ɗaya, aka maye gurbin ta da wata danƙareriya da zata iya ɗaukan bil’adama talatin, sannan aka maida shi a ka aje shi.

Danƙareriyar halittar nan da ta fito daga wannan kogon ta ƙaraso inda Abdul ɗin ke zaune, itama ta zauna a kusa da shi tana ƙoƙarin janye gashin girar ta da ya zazzago ya rufe fuskar ta gaba ɗaya

Subhanallah! ta na ɗaga gashin girar ta fuskarta ta bayyana ga Abdul

Kallon ta yake sosai duk da ba wannan tsoron a tattare da shi

Ido cikin ido suke kallon juna, 

Can a ƙasan zuciyar shi faɗi yake

“Mummuna ce”

Lafcecen hannun ta taɗauƙa ta ɗora mishi a kafaɗa ta ƙara janyo shi kusa da ita tace

“NA SO MUYI KOMI TA LALAMA AZIZ, AMMA IN NAYI WASA TABBAS LOKACIN DA ZAMU RABU YAYI, SHIYASA NA ƊAUKO KA NAN A ƊAURA MANA AURE”

Abdul be ce komi ba, kuma beji wani aibun maganar ta ba, hasalima ya fara ɗan jin wani abu kaɗan a ƙasan zuciyar shi game da ita

A can tsakiyar tekun inda wasu gungun jemagu suka zagaye, Abdul ya hango wata me irin tashi halitta tsaye tana kalle-kalle

Da sauri Abdul ya kauda idon shi daga na aziza inda wani abu baƙi-baƙi ya fara fitowa daga idanun ta, ya maida kallon shi can tsakiyar tekun 

A bazata yaga Ammhan shi da tunda Allah yai mata rasuwa be taɓa ganin ta a mafarki ba

Ammah na tsaye tana kuka sosai tana karkaɗa ma Abdul kai, amma kwatakwata ta kasa magana

Waigawa bayan ta tayi, ta jawo hannun Zainab dake laɓe a bayan ta hannun ta ɗauke da ƴar baƙa

Zumbur Abdul yaja baya daga jikin sarauniya Aziza ya maida hankalin shi gaba ɗaya kan Ammah da Zainab

Da sauri sarauniya Aziza ta waiga tana kallon inda Abdul ɗin ke kallo

Ba musu ta miƙe, sannan ta kama hannun shi suka fara tafia zuwa wajen kogon nan da ta fito daga cikin shi ɗazu

Suna tafe waɗan nan halittu na take musu baya

Kuka sosai Ammah keyi tana nuna Abdul, Zainab kuma na gefe tana kalle-kalle

Can daga baya idanun Zainab suka kai kan Abdul da saura ƙiri su ƙarasa cikin kogon nan

Da ƙarfin gaske tace

“Ka nemi ɗaukin Allah, in ka shiga wajen nan ba zaka ƙara fitowa ba!!!!!”

Cak Abdul ya tsaya daga tafiyar da yake

Cogewa yayi ya tsaya, sarauniya Aziza na jan shi, shi kuma yana cogewa

Da ƙarfi Zainab ta fara faɗin

“A’UZUBILLAHI MINASHSHAIƊANIRRAJIM!!!!”

Da ƙarfin gaske Abdul ya maimaita abinda yaji Zainab ɗin na faɗa

Dai-dai nan Abdul ya buɗe idon shi a firgice kuma a bayyane yake furta auziyar da ya fara ta a cikin mafarki.

Yana buɗe idon shi yaga Abbah tsaye a kanshi, yana ta mishi tofi

Tunda Abdul ya fara mafarkin nan jikin shi ke jijjiga yana karkarwa.

Abbah idon shi biyu lokacin, hankalin shi ya tashi jin irin gunjin da yake yi, ga kuma zufa data jiƙe shi sharkaf

Dafa shi Abbah yayi, murya cikin taushi yace

“Ka dage da addu’a Abdul, dukkan tsanani  sauƙi yana tafe, kayi haƙuri Abdul, bazan taɓa dena baka haƙuri ba har ƙarshen rayuwa ta”

Sosai muryar Abbah ta fara rawa, tuna abubuwa da dama da yayi, 

Abdul da jikin shi yayi sanyi ganin yarda muryar Abbahn nashi ke rawa yace

“Ka dena ɗora ma kan ka abunda dama Allah ya ƙadarta ze faru Abbah, kuma ka dena bani haƙuri, inshaAllah inaji a jiki na zan samu kaina nan kusa ba da jimawa ba”

Rungume shi sosai Abbah yayi a jikin shi, yana jin a can ƙasan ranshi yayi wasa ƙwarai da gaske da amanar da masoyiyar shi murjanatu ta bar mishi.

Wajen huɗu da rabi na yamma Muslim ya iso ƙofar gidan su Abdul

Sunyi waya tun ɗazu dashi dama

sanye yake cikin manya kaya da suka karɓi jikin shi sosai ya fito

Be tsaya ba ya zagaya ya shiga motar ya rufe

Kallon Muslim Abdul yayi yace

“Ka gama guje-gujen ka dawo kenan?”

Murmushi muslim yayi yace

“Hummm, tunda na samu aka taro ni da ƙyar ai shikenan, kai dai muje”

Murmushi Abdul yayi shima, yace

“Wallahi kunyar haɗuwa da Abie nake guy, 

Ya kirani yafi a ƙirga amma naƙi zuwa, da kan shi ya ƙira Abbah fa yace ya tura ni ko ya kawo ni”

“hummm” kawai muslim ya iya cewa, seda sukai nisa sannan yace

“Yana da fahimta ai, nasan kuma ze fahimce ka”.

Suna ɗan taɓa firar su sama-sama har suka isa ƙofar gidan Abie.

Kallon juna sukai Abdul yace

“nasha yau ba ranar karatu bace guy, kalli yarda wajen ya cika fa”

Muslim yace “kai dai muje”

Shiru Abdul yayi yabi muslim a baya har suka dangane da babban soron gidan Abie 

Mamaki be gama kama Abdul ba seda ya ga Abbah n shi da ƙanin Ammah, da wasu daga cikin uncles ɗin shi

Cikin ranshi yace

“me ke shirin faruwa ne?”

Abie na daga gefe shima zaune da nashi ƴan’uwa

Yafito Abdul da hannu Abie yayi

Kamar soko haka ya tsallake mutane ya ƙure can inda iyayen nashi suke

Gyaran murya Abie yayi yace

“Yaro na ze ƙarɓi auren sa da kansa yanzu inshaAllah”.

Sororo Abdul yayi yana kallon Abbah da ya kafe shi da idanun shi da sukai kaɗa sukai ja, ga dukkan alamu kuka yayi

Maida kallon shi yayi ga Abie dake magana ƙasa-ƙasa da Babban ɗan shi muhammad, 

a hankali ya kalli uncles ɗin shi da suma duk suna zaune a wajen, kuma ga dukkan alamu akwai sanayya a tsakanin su.

Gyaran murya Abie yayi yace 

“Bisimillah, muyi abinda ya tara mu”

Abie be gama rufe bakin shi ba, yaga tawowar inuwa baƙa daga waje

Ita ba a sama ba, ba kuma a ƙasa ba, 

Ratsawa take dai-dai kan mutane har ta dangane da inda Abie yake

A tsakanin  Abie da Abdul inuwar ta tsaya, daga Abdul se Abie suke ganin wannan inuwa

Tunda inuwar nan ta tsaya Abdul ya fara rasa hankalin shi a hankali

Abie na lura da shi, lura da halin da ya fara shiga ne yasa yace

“Alhaji sani matso ka wakilci ɗanka”

Abie ya sake waigawa inda ƙanin shi ke zaune yace

“kaima zo kai ma ƴarka walicci”

Matsowa sukai dukan su kusa

Yarda addini ya shar’anta komi suka fara gabatar wa

Murya da ƙarfin gaske Abdul yaji muryar ta tana cewa

“Kar ka bari su ɗaura maka aure da ita Aziz, wallahi ba zan haƙura ba, zan illatata, zan nakastata, zan cire tausayin ka da na kafu da shi a kai, zan addabi ahalin ku,”

Dai-dai sanda aka shafa fatiha, a dai-dai lokacin Abdul ya dafe kanshi haɗe da toshe kunnuwan shi, saboda tsananin ƙunji da gurnanin muryar sarauniya Aziza da ya cika mishi kunne.

“WALLAHI BAZAN HAƘURA BA! SE NA ƊAU FANSA”!

Ɗif, yaji muryar ta ɗauke, kuma ba inuwar ta

Ana shafa fatiha, Abbah ya sauke wata ajiyar zuciya me sanyi tare da share ƙwallar da ta cika mishi idanu tun sanda aka fara gabatar da ɗaurin auren.

******

Ta inda IYA ke  shiga bata nan take fita ba, faɗa take kamar zata ari baki ta ƙara a nata

Mama da ƙannin ta, se kuma sirikan ta dake zaune, duk sunyi jigum-jigum

Kowa mamakin wannan ɗaurin aure yake na gaggawa da aka sanar musu

 banda mama da Zainab da gaba ɗaya yinin ranar taƙi tankama kowa,

Tana zaune a cikin su, amma ba zaka taɓa gane me ke a cikin ranta ba

Fuskar ta ba yabo ba fallasa, tana ta buga game ɗin candy crush dake a wayar ta.

Matsowa IYA tayi inda Zainab ke zaune ta kai mata ranƙwashi a kai tace

“Wani lokacin bana gane munafuncin ki Zainabu, a kanki nake ta kumfar baki amma na lura ke kam ko a jikin ki, ja’irar yarinya”

Dariya Zainab ta kwashe da ita, sannan  kalli IYA data riƙe haɓa tace

“Ki jimin IYA, so kike in bijire na saɓa dokar Allah kenan? ba ruwa na wallahi, in har ina son in gama da duniyar nan lafia, to se na bi umarnin iyaye na”

Gaba ɗaya palon tsit yayi, kowa yana mamakin dauriya da kuma biyayya irin ta Zainab

Sarai mama ta gani a idon zainab ɗin akwai damuwa, banda ita ta haife ta ba lale ne ta iya ganewa ba

IYA kam daskarewa tai a tsaye tana kallon Zainab ɗin, can ta nisa ta waiga saitin inda mama ke zaune tace

“Binta, Halan ita ta kawo shi tana so?”

Murmushi mama tayi tace

“Ko ɗaya, bata taɓa ganin shi ba ma IYA”

Shiru IYA tayi ta samu waje ta zauna bayan ta zabga uban tagumi.

Kiran sallar magariba ya tashi kusan dukan su daga palon, banda IYA dake zaune tana saƙe-saƙe a cikin ranta,

Ita gani take kamar ba’ai ma zainabun ta adalci ba ace da rana tsaka ba shiri ba komai a ɗaura ma mutum aure ba tare da amincewar shi ba, se kace a zamanin su.

Shigowar Zainab kenan palon taga IYA zaune a inda ta barta, har yanzu bata cire tagumin data rafka ba

A hankali ta saɗaɗa ta tsaya a bayan ta, hannu ta saka ta fisge tagumin da IYA tayi, sannan ta ja baya da sauri kafin taji ranƙwashi a kanta

IYA tace

“Ni ina nan ina tausayin ki, amma ke kina nan kina abunda kika saba”

Dariya Zainab tayi tace

“Bafa mutuwa nayi ba da kika zauna kika rafka tagumi Iya”

Taɓe baki IYA tayi tace

“ni matsa ki ban waje, gara ma da akai sadakar dake ja’ira”

Saitin kunnen ta Zainab ta raɗa mata 

“Kika sani ko ina son wanda aka ɗaura da shin?”

Salati IYA ta buga tai kan Zainab data kwasa da gudu ta fice a palon.

******

Kaɗan daga cikin su ne suka tsaya aka gabatar da sallar magrib tare da su

Ana idarwa yawancin su suka tafi, aka bar daga Abie se ƴaƴan shi su shida, da ƙanin shi Ibrahim.

Se kuma Abbah da Abdul, se muslim shima da be kai ga tafiya ba

A daddafe Abdul ya gabatar da sallar, gaba ɗaya baya cikin nutsuwar shi, ciwon kai yake ji kamar idanun shi zasu zubo saboda azaba

Jijiyoyin kan shi gaba ɗaya sun fito sunyi ruɗu-ruɗu

Kowa na azkar amma banda Abdul da ya ja gefe ya ɗora kanshi a kan gwiwowin shi,

Dukkan motsin shi akan idon Abie, 

Abbah kuma na daga can gefe yana ta zuba nafilolin miƙa godiyar shi ga ubangiji

Fasalta muku irin farin cikin da Abbah ke a ciki ɓata lokaci ne.

Seda Abbah ya idar tukun Abie yace 

“Ku mu ƙarasa cikin gidan, se ku gaisa da IYA”

Ba musu suka tashi gaba ɗayan su, ban da Abdul da be ma san me ake cewa ba

Seda muslim da yayan Zainab, suka kama shi tukun ya iya miƙewa

Dukan su suka ɗunguma zuwa cikin gidan

already babban palon Abie a buɗe yake, kuma a gyara fes

Tunda suka fito daga masallacin Abdul yace su sake shi ze iya tafia

Sakin shi sukai, duka aka shiga

Wasu sun kai ga shiga palon, wasu kuma basu kai ga shiga ba, 

Dai-dai Abdul ya ɗaga ƙafar shi ze shiga palon ya yanke jiki ya faɗi a wajen.

Salatin da suka saka ne ya jawo hankalin su Abie da suka fara shiga palon

Suma da hanzari suka fito, suna tambayar lafia?

Ba wanda yace komi se ƙoƙarin ɗaga shi da suke yi

Kama-kama, sukai aka ƙarasa shigewa da shi palon Abie aka shimfiɗe shi daga gefe.

Abie ya kalli Abubakar yace

“shiga ka samo min ruwa a kofi”

Da sauri ya miƙe ya shiga cikin gidan

Yana shiga da IYA ya fara cin karo, 

Riƙo shi tayi tace

“Basu kammala ɗaurin auren bane har yanzu?”

Tafiya yayi, ya barta nan tsaye, seda ya ɗibo ruwan tukun yace

“an gama mana, angon ma na can baje a sume fa”

Ƙwalalo idanu IYA tayi tace

“Halan shima dolen akai mishi?”

Be ma ji me take cewa ba yayi gaba abinshi da sauri

Kasa haƙuri IYA tayi, ta janyo hijabin ta dake saƙale ta saka, sannan tai hanyar palon Abie.

Baba Ibrahim ne ya fara ganin IYA, 

Da sauri ya miƙe ya tare ta, murya ƙasa-ƙasa yace

“ki koma ciki IYA, in an kammala za’a kira ki”

Ture shi IYA tayi tace

“ai na san an gama ɗaurin auren, kawai dai akwai abunda kuke ɓoye ma mutane ne”

Kallon Baba Ibrahim Abie yayi yace

“ka barta ta shigo mana”

wuri ta samu ta zauna, kamar yarda taga kowa ya zauna, 

Tagumi ta zabga ta kafe Abdul dake miƙe a ƙasa da ido

Shi kuma Abie na daga gefe, hannun shi riƙe da kofin ruwan da aka kawo mishi

murya ƙasa-ƙasa yake tofa ayoyin tsari a cikin ruwan nan

Ya ɗau kusan minti talatin yana tofin shi tukun ya tsaya.

Ajiye ruwan yayi a gefen shi tukun yace

“ku miƙar da shi zaune, mu gani”

IYA na a zaune tana kallon ikon Allah.

Su uku ne suka ɗaga shi zaune, sannan suka daddafe shi dan kar ya faɗi

Ɗakko wannan ruwan da yai ma tofi yayi, yai bisimillah sannan ya guntsa a bakin shi,

Seda ta daidaici fuskar Abdul ɗin sannan ya fesa mishi ruwan dake bakin shin

Sedai yai haka kusan sau bakwai tukun Abdul ya dawo hayyacin shi.

Hannun shi dafe da kanshi yake kallon kowa dake cikin palon, a ranshi yake cewa

“Allah na roƙeka kasa da gaske mafarkin nake yi, bana fatan ƴar kowa ta shiga matsala ta a dalilina”

Be kai da gama maganar zucin da ya fara ba yaji muryar IYA na tambayar “waye angon?”

Murya ƙasa-ƙasa yace  “innalillahi, da gaske ne”

Muslim dake gefen shi yaji shi sarai, shi dai bece komi ba, se ma ƙara haɗiye miyan bakin shi dake neman ƙafewa yake, 

Dan tun sanda Abdul ya faɗi suke jin kukan jemagu daga can waje.

Da hannu Abie ya nuna mata Abdul da yai tsumu-tsumu a gefe

Baki IYA ta riƙe tace “Daɗi ne ya bugar da shi, ko kuwa shima jin auren yayi katsam kamar yarda zainabu na taji?”

Shiru ba wanda ya bata amsa, se Abbah ne ma ya maye amsar da rissinawa yana gaishe ta

Baki sake ta amsa ma Abbah gaisuwar shi, ta shaida shi, duk da dai ba wani farin sani tai mishi ba

Kiran Mama Abie yayi a waya itama ta zo, duk da ita tasan da maganar da Abien zeyi

Yace “ku tawo da Zainab”

Zainab na ɗaki kwance, ta duƙunƙune a kan gado

Ta rasa gane me take ji a cikin zuciyar ta, ita dai bata wani farin ciki da wannan auren, kuma bata ji ƙin shi ba, 

amma dai tana jin kanta wani iri ne

Duk da Abie yay mata bayanin dalilin auren, kuma ya kwaɗaitar da ita da irin ɗimbin ladar da zata samu in tai wannan jihadin, 

Amma har yanzu zuciyar ta rawa take

Tana a kwancen nan har mama ta shigo ɗakin bata sani ba, har seda ta dafa ta

Tausayin ƴar tata fal ranta tace

“Taso muje Abie na neman ki”

Ras, haka Zainab taji gaban ta ya faɗi, murya na rawa tace

“Mama badai tafia zasuyi da ni ba a yau ko?”

Shiru mama tayi tana kallon ta,

Can cikin sanyi murya tace

“Ban san auta ta da wannan tsoron da nake gani a fuskar ta ba ni kam, ki nutsu, ki kuma sani, duk da dai nasan kin sani ɗin, ubangiji baya taɓa ɗora ma bawan sa abinda yasan baze iya ba,

Kuma kin san Abie n ki baze taɓa cutar da ke ba”

Kamata tayi ta miƙar da ita tace

“saka hijabin ki muje, suna jiran mu”

Jiki a mace zainab ta ɗauki zumbulelen hijabi ta saka, 

Har sun fita, ƴar ɓaƙa ta sakko itama ta biyo su da gudu

Mama na gaba Zainab na biye da ita a baya, haka sukai sallama suka shiga palon da kusan a cike ya ke.

kan Zainab a ƙasa ta shigo, bata yarda ta kalli kowa ba, 

inda IYA ke zaune kawai ta nufa, gaf da Zainab zata zauna suka ji ance

“MUNAFUKA, KAR KI ZAUNA A KAI NA”!

Da sauri Zainab ta ja baya, murguɗa baki tayi tace

“Kece dai munafuka bani ba wallahi”

IYA kam a guje ta miƙe daga inda take zaune ta zagaye tai can gefe

Muslim dake can ƙarshe, shima ya ƙara shigewa yana baza idanu

Abbah kam, ido ya firfito waje yana ƙara mamakin naci da ƙunatar aljanar nan

Sauran ƴaƴan Abie, kam sun ɗan saba da irin abubuwan nan, duk da dai jin muryar ta akwai babban ruɗani a ciki.

Can ƙasan ranshi Abbah yace

“Allah kaine abin godiya, juma’ar da zatai kyau tun daga laraba ake gane ta”

Duk da yarda kan shi ke sara mishi, be hana shi shaida muryar ta ba,

Ƙiri-ƙiri so yake ya ɗaga kan shi, amma sam ya ƙasa ɗagawa, Tun yana yunƙuri har takai ga ya haƙura da ɗaga kan na shi.

Can ƙarshen bango IYA ta manne, baka ganin fuskar ta sam, tsabar yarda ta nane ma bango.

Ƴaƴan Abie su shidan nan kaf ba wanda ya motsa daga inda yake, dama Abie yayi musu bayanin komi

Baba Ibrahim yaso ya ɗan tsorata duk da shima yasan komi, haka nan dai ya dake kamar yarda yaga sauran sun dake suma.

Zainab na daga tsaye, tana ƙara kallon inda taji maganar, abun na ƙara bata mamaki a cikin ranta

Can cikin ranta tace

“wai dama abinda Abie yace min ɗazu da gasken gaske ne ashe?”

Muslim kuwa tunda yaji muryar mutuniyar sa ya tashi daga kusa da Abdul ya dawo tsakiyar inda yayun zainab ke zaune, yana ta raba idanu.

Gyaran murya Abie yayi ya kalli zainab da mama da suke a tsaye, yace

“ku zauna mana”

Guri kowa ya samu ya zauna, banda IYA da tai zurfi a can duniyar tsoro

Seda kowa ya nutsu, tukun Abie ya farga da IYA dake can ta manna fuskar ta jikin bango

Murmushi yayi yace

“Zainab, je ki tawo da mutuniyar ki mana” ya ƙarashe maganar yana nuna mata Iya dake can manne.

Murmushi itama zainab ɗin tayi, sannan ta yunƙura ta tashi,

Ta saitin Abdul dake zaune kai a ɗuƙe tabi, 

Kwata-kwata bata gane shi ba, bama taga fuskar shi ba ballanta na ta sheda shin

Wuce shin da tai, ya shaƙi iskar sansanyan ƙamshin dake fita daga jikin ta

A hankali ya lumshe ido yana ƙara buɗe ƙofofin hancin shi dan ya shaƙa da kyau

A saitin kunnen shi Aziza tace

“KAFIN DAI KA SHAƘA DA GA WAJEN TA A WAJE NA KA FARA SHAƘA”

Bece komi ba, be kuma nuna yajin ba.

Zainab na zuwa bayan IYA bata ce komi ba, hannun ta saka ta kamo hannun IYA da ta dafa bango ta rike shi ƙam 

Dama wanda ze dafa mata take nema, idon ta a rufe ta rinƙa bin zainab,

Har seda Zainab ɗin ta zaunar da ita akan kujerar dake kusa da mama, sannan ita  ta zauna a kasa kusa da ƙafar IYA.

Shiru palon ya ɗauka, ko da abinda yake saƙawa a cikin ranshi

Shirun da IYA taji yayi yawa ne yasa ta buɗe idon ta a hankali

lungu da saƙo na palon tai ta raba idanu, kaf seda ta kewaye idanun ta tako’ina tukun ta dawo da kallon ta gefen da mama ke zaune

Murya can ƙasa IYA tace

“Binta, kunji abinda naji kuwa? kodai ruɗin tsufa ne ya fara kamani?”

Yarda IYA ke magana abun se ya baka daria,  dauriya sosai mama ta yafa ma kanta sannan tace

“Kowa da ke cikin palon nan yaji IYA”

Ajiyar zuciya me nauyi IYA ta sauke, tasa hannu ta share zufar data tsatstsafo daga goshin ta, sannan tace

“TIRƘASHI!”

Tirƙashin da ta faɗi yasa gaba ɗaya palon suka dago kai suka kalle ta, harda Abdul da a ɗazu ya kasa ɗaga kan shi

A dai-dai nan kuma Zainab sukai ido huɗu da Abdul

Ido cikin ido suke kallon juna,

Ita dai zainab a sace take kallon shi, shi kuma kai tsaye ya zuba mata idanun shi bako kyaftawa

Gira ɗaya Zainab ta ɗaga mishi,

Tai mishi alama da hannu, irin me yakawo shi gidan su

Kamar yasan me tace, murmushi yayi ya ɗan langaɓar da kan shi gefe guda

Langaɓar da kanshin da yayi ne yasa ta tuna cewa fa kurma ne

Tun sanda suka haɗu da shi take ce mishi kurma, anata tunanin kurma ne.

Bayan dogon shirun da palon ya ɗauka na ɗan lokaci, Abie yayi bisimillah, tukun ya fara da

“Alhamdulillah, ina godiya ga ubangiji da ya bani ikon cika wannan alƙawari da nayi tun ranar da Aljahi Hamza ya ziyarce ni sannan kuma yazo min da matsalar ɗan shi.

Duk da dai shi kan shi Alhaji Hamza be san da wannan alƙawarin da nayi ba, 

A lokacin na bashi shawarar da yayi ma ɗan shi aure, saboda magance problem ɗin nashi

A yarda muslim ya same ni ya faɗa min cewa, bafa yarinyar da shi Abdul ya taɓa zuwa wajen ta da sunan neman aure yasa na ƙara samun ƙwarin gwiwar abin alkairin da nake ƙoƙarin yi

Kuma mun kai kusan sati da mukai magana da shi Alhaji Hamza, amma naji shiru ba wani ƙarin bayani daga wajen shi ba

Da na kira shi da kaina a ɗazu da safe, se yake gaya min duk inda ya buga ba sa’a

Ƙwarai abun be min daɗi ba, amma da yake na yi niyar temakon shi Abdul ɗin, tunda yaron kirki ne, yasa naje na shawarci IYA da maganar”

Da sauri IYA ta ɗaga hannu ta dakatar da Abie tace

“Rufe min baki a nan, kar ka ambaci suna nan ka saka ni cikin lukutar masifar da ba lale ka iya fitar da ni ba, 

Ni dai baka ce min Zainabu na zuwa zatai ta yi KISHI DA ALJANA ba,

Ce min kai wani jihadi zatayi, da yake ka san ta kan ɗaɗin baki, har ka sa na yarda, amma se da nazo na tarar da wata danƙareriyar lukutar masifa zaka wani ce ka shawarce ni?

To wallahi ban yarda da auren nan ba, haka nan zaka haɗa min jika zama da wanda ba jinsin mu ba? 

Tun wuri a sauya magana, kafin gaba ɗaya tai mana wankin babban bargo.

Tsit palon yayi, 

Ƙasa Abbah yayi da kan shi yana satar kallon Abdul da shima tunda IYA ta fara magana ya sadda kanshi ƙasa.

Kafin Abie ya ƙara cewa komi, Baba ibrahim yace

“To ai wannan ne babban jihadin da ake nufi IYA”

Taɓe baki IYA tayi tana ɗan matsawa daga jikin Zainab dake ƙara shige mata

A kaikaice IYA ke satar kallon Abdul da kan shi ke a ƙasa, in yayi kamar ze ɗago kan shin se tai maza ta ɗauke idon ta

Gyaran murya Abie ya sake yi, sannan yace

“Ki gafarce ni IYA, banyi tunanin baki fahimce ni ba, 

yanzu dai tun da har an ɗaura kuma nayi gaban kaina, zainab ta riga da ta fita a hannu na, 

yanzu dai ga ki ga Abdul’aziz ki nemi sakin ta a hannun shi”

Abie na sane da abinda yace, yasan wacece iya, yasan ta ciki da bai.

Mama da  yaran ta ma ƙunshe dariya suka fara yi ƙasa-ƙasa, sarai sun san suma me Abie ke nufi

Abbah da ya fahimci wasan da za’a buga shima dai ya gyara zama, 

Ba’a maganar muslim da ke gefe yana ta zuba addu’oin da yanzu kam sun zame mishi jiki

Abdul da se a yanzu ya gane me madara itace dai matar da Allah yaci da shi

Shiyasa da yaji maganar da Abie yayi na a nemi saki a wajen shi, yasa ya zuba ma iya manyan idanun shi yana kallon ta ko ƙyaftawa babu

Ido rufe iya ta waiga inda Abdul ke zaune da niyar magana

Kallon shi kawai tayi ta haɗiye maganar ta ƙutt, ta kasa cewa komi

Ta fara zare idanu

Murya can ƙasa Zainab tace ma iya

“kiyi magana mana, ya akai kikai shiru?”

Da ƙarfi Iya ta ture Zainab daga jikin ta tace

“Naga alama kin fara rikiɗewa kema, tunda ubanki ya janyo mana lukutar masifa har gida, ai bani data cewa

Kuje can kuyi ta gasar dafa tatsotse(jellop), dake da abokiyar zaman naki”

Bata jira cewar kowa ba, ta miƙe tai hanyar fita daga palon,

A dai-dai nan ƴar baƙa  ta danno da gudu, tai cikin zanin Iya da ya kwance tana ƙoƙarin gyara shi

Iya ce kawai taga tawowar ta,

Su dai daga sama suka jiyo salatin IYA da iyakacin ƙarfin ta, faɗi take

“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un,

Zainab tuna mun addu’ar da kika koya min ɗazu, wayyo nayi mummunan gamo

Dukan su suka rufan mata, duk a tunanin kowa da gaske gamon tayi

Riƙe ta Abie yayi yana cewa

“Ki nutsu Iya, bafa komi, kawai kin tsorata ne”

Ruɗewa sosai Iya tayi tana zuba surutai

Tunda Iya ta kurma ihun nan, muslim ya ƙara mannewa a jikin kujera yana ci gaba da  addu’o’in shi

Murya ƙasa-ƙasa kamar wanda baya so a ji yace

“aifa, na kawo kaina da kaina ni muslim”.

ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU.

Back to top button