Hausa novels

Wace ce ita (Who is she) Chapter 62 Complete Novel

WACECE ITA⁉️(WHO IS SHE⁉️)

Unique Barakancy🌹

SIXTY-TWO

“Shikenan, congratulations in advance bro”…..
Sudais ya fada yana dariya….
Kin kulashi deen yayi har suka karasa guest parlor din…..
Suna zuwa suka tarar da parlourn a cike da mutane, babu wani babba dayake gidan da be halarci gurin ba, mami da umm na zaune kusa da juna sunata magana kasa kasa babu wanda yakejin abinda suke cewa, baby tee kuma na daga chan gefe a zaune tayi tagumi kana ganinta kasan duk a tsure take, haka take indai taga taron mutane sai hankalinta ya tashi ta rasa meyasa, ko dan ta taso tana isolating kanta ne?… Abinda yafi bawa deen mamaki shine ganin eesha zaune dan nesa dasu umm kasancewar parlourn me girma sosai ne so akwai distance tsakanin kowa, kome ya kawota cikin family meeting dinsu oho?…..
Kallo daya deen yayiwa baby tee ya gane she’s so nervous, so yayi ya zauna at the extreme end sai yaji baze iya shareta a yanda ya ganta ba kawai ya nufi inda take……
Da mamaki sudais yabi deen da kallo ganin yayi switching ya nufi inda baby tee take, murmushi yayi ya samu guri ya zauna aransa yace ‘soyayya tayi maka mugun kamu kana denying kanka’…….
Jin mutum a kusa da ita kawai baby tee tayi, dagowa tayi da sauri suka hada ido da deen dake binta da wani irin kallo kamar ze hadiyeta, sunkuyar dakai tayi ta mika masa wayarsa dake hannunta….
Karba yayi yace;
“Kingama min binciken kenan?”…..
Turo baki tayi bata dago ba tace;
“Ni babu binciken dana maka”…..
“In kika kara turomin bakinnan saina cinyeshi a gurinnan”…..
Dauke kai tayi tana kallon gefe……
Mintsininta yayi ta juyo da sauri tana bata fuska, murmushi yayi murya chan kasa yace;
“Why did you send my pictures to your phone? Ko kina ciki ne pretty?”……
Da sauri ta juyo tace;
“Ina cikin me?”…….
“Kin fini sani ai, gwara ki fadamin tin yanzu in san me zan gayamusu a meeting dinnan”…..
Tabe baki tayi tace;
“Ni babu abinda na sani”……
“Toh me zakayi da pictures dina da kika tura a WhatsApp dinki?”……
Zaro ido tayi tace;
“Bincike kamin kenan? And besides me kakeyi da pictures din da kake min kaima?”……
Shafa lallausan gemunsa yayi yace;
“Because I enjoy taking pictures of you, what’s your own reason?”…..
“So nake in gane in muna kama dagaske that’s why I sent it”……
“Na karshen kuma fa? You find it romantic?”…..
Shiru tayi bata kara cewa komai ba ganin inta biyemasa sai ya fadi abinda yafi wannan dan ta kula kwata kwata besan kunya ba…..
A hankali kamar me tsoron magana yace;
“Zahrah will you marry me?”…..

Download>>> Yar Harka Romantic Hausa Novel

“Ba magana nake muku ba? Wannan wani kalan sakarci ne? Kunga dunbin mutane a zaune ai kunsan magana me mahimmaci za’ayi, sai ku dasa taku hirar ana magana kuyiwa mutane banza”…..
Bappa ya fada rai a bace dan alamu sun nuna duk fadan daya gamayi basusan yanayi ba sai hirarsu suke kamar su biyu ne a parlour, har anna ta bada labarin da suka bata basu sani ba, ita kanta anna saida taji bakinta ya mutu saboda yanda suke abu hankali kwance…..
“Afuwan bappa, ayi hakuri”…..
Deen ya fada yana sunkuyar da kai…..
Itama sunkuyar da kai tayi kamar yanda yayi tace;
“Ayi hakuri bappa”…..
Girgiza kai umm kawai tayi tana sake sake aranta, sun riga sunyi making decision tin dazu da mami akan al’amarin, jira kawai suke suji ta bakin bappa shima…….

“Naji bayanin da kukayiwa anna amma dukda haka ban gamsu ba saboda wasu dalilai sannan wannan video yanata a gari dan mutanen da suka turomin videon nan sun kai mutum biyar bayan wa’yenda suka zo suka nunamin har inda nake, kuma duk wanda yaga wannan video dole ya fassarashi komin bayanin da za’a masa kuwa, saboda haka na taraku anan domin muyi shawara akan yanda zamu shawo kan al’amarin, kafinnan kai saifu naji alakar dake tsakaninka da wannan yarinya (ya nuna eesha) a bakin mahaifiyarka na kuma ce a dan dakatar da wannan mu fara kashe wannan, inaso yanzu inji gaskiyar abinda yake tsakaninka da fadima”……
Eesha na jin haka wani hawaye ya silalo mata a fuska tayi saurin sukunyar da kai tana sharewa boye, a lokacin ji take da zata iya barin parlourn data bari akan wannan maganganu da akeyi, ta fahimci komai basai an gayamata ba ta fahimci so suke su kulla alaka tsakanin cousins din guda biyu koda basasan junansu, dama batayi niyar zuwa ba tinda ba family bace ita, mami ce tace bappa yace tazo itama….

Download>>> Boddiya Complete Hausa Novel Document

“Pick your call mana umm”…
Cewar mami tana kallon wayar umm dake ta ringing tin dazu…..
“Muhammad ke kira, I’ll call him back after the meeting”……
“Naga call din is getting abnormal, ki dauka kiji menene”……
“Okay”…
Umm ta fada tana picking call din Abby daya sake shigowa…..

Zubawa deen ido kowa yayi ana sauraron abinda zece, ajiyar zuciya ya sauke saboda yasan abinda ze fada will be a shock to most of them especially umm da mami, amma haka kawai yake san baby tee ta bashi hadin kai yanda komai zezo masa da sauki, kasa yayi da murya yanda babu wanda zeji yace;
“Zahrah”….
“Na’am”…..
Ta amsa masa kasa kasa itama….
“You haven’t answered my question?”……
“Ta ina ake aure babu soyayya?”…..
“A fara a kanmu baby girl, maybe we’ll get to love each other later”……

“Kai fa muke sauraro saifu”…..
Cewar bappa dayaga shirun yayi yawa…..

Numfasawa deen yayi kai tsaye yace;
“Eh dama inaso in fadamuku ina….”…..

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!”…….
Umm ta fada da karfi tana mikewa tsaye wayarta makale a kunnenta……
Nan da nan hankali kowa ya dawo kanta harda deen dayaji sauran maganarsa ta makale……
Shiru ta danyi sai kuma chan tace;
“Meya samesa?”….
Basu ji me akace daga daya bangaren ba ta sake cewa;
“Dagaske? Subhanallahi! Yanzu ya za’ayi?”……..
“Toh shikenan gamu nan tawowa da baby tee din”……..

“Lafiya? Meyake faruwa ne sis?”…..
Cewar mami da taga umm tagama wayar…….
Bata iya bata kwakkwarar amsa ba tace;
“Shirya muje, baby tee taso muje, saif daukomin mukullin mota”……
“Ki mana bayani mana Jamila, wai meyake faruwa ne haka?”…..
Cewar anna da hankalinta duk ya gama tashi…
“Abby ne ya kirani likitoci na kan khalee rai a hannun Allah sai kiran sunan baby tee yake”..
Salati kawai mutanen parlourn suka hau yi banda innalillahi ba abinda yake tashi, kowa sai cewa yake aje dashi dan Allah……
Zumbur baby tee ta mike hankali a tashe ta fashe da kuka tace;
“Dan Allah kuzo mu tafi karya mutu ya barni”……..
Deen ji yayi kamar an chaka mishi mashi a zuciya, yaji kamar ya yiwa duka yan parlourn duka, a fusace ya fice daga parlourn batareda kowa ya sani ba……
Kallonsu daya bayan daya bappa yayi yace;
“Ku kwantar da hankalinku, in Allah ya yarda ba abinda ze samesa sannan iya mu hudu kawai zamuje, dani da jamila da fatima sai fatima karama, anna kema ki zauna(saboda ya santa da gigicewa)……
Burum anna tace;
“Wallahi bazan zauna ba sai anje dani”…..
Ba yanda suka iya dole haka suka fito su biyar, ko bi takan saif da akace ya kawo muqullin mota basuyi ba mami ta shiga ta kwaso keys ta mikawa driver daya ya tuka Anna da bappa, su kuma suka shiga daya ita da umm da baby tee..
Umm naso ta tambayi baby tee abinda ya hadata da khaleel amma ta kasa saboda abubuwan duk sun chakudu sun dagula mata lissafi, abinda yafi bata mamaki kuma shine yanda baby tee take biyewa deen kwanannan bayan tasan da maganar khaleel akanta sannan kullum claiming take ita khaleel takeso, but recently ko makaho ne ya shafa yaji yasan da wata a kasa, haka dai ta danne zuciyarta har suka karasa asibitin da khaleel yake……

Download>>> Dr Bobby Hausa Novel Document – 

Tinda momma ta kawosa duniya be taba riskar tashin hankali irin wannan ba, yayi facing abubuwa kala kala akan baby tee amma babu makamancin wannan shiyasa ko sau daya be taba giving up akanta ba har Allah ya taimakesa ya samu soyayyarta ta bude baki da kanta tace tana sonsa, amma yau yaga abinda ko a mafarki be taba tinanin gani ba, baby ce tazo cikin dubban mutane sannan a gaban idonsa dan ze iya rantsewa ta gansa ta rungume deen, suka kuma yi ido hudu da deen ya rungumeta shima akan idonsa sannan ya kashe masa ido daya yayi sama da ita suka wuce mutane sai ihu suke suna musu video, a lokacin ji yayi inama Allah ya dau ransa da wannan mugun gamo da yayi, abinda yafi bakanta mishi kuma shine yanda baby tee ta dinga jaddada masa yazo wai zatayi introducing dinsa to her family members, ashe irin wannan introduction din take nufi, wato yazo yaga yanda zatayi displaying love dinta to her new lover kowa yagani ya shaida, zubewa yayi a kasa be sani ba feeling so betrayed, wallahi da yasan irin abinda ze tarar kenan da be zoba sannan da tasan abinda takesan nuna masa kenan data taimaki zuciyarsa tayi abunta without inviting him atleast kazantar da baka gani ba tsafta ce, amma harda kiranshi dazu wai yazo fa tana jiransa ashe she’s on a mission, shi dama yasan haka kawai bazata dameshi yazo ba, a lokacin ji yayi rayuwarsa is completely miserable, he felt so shattered and hurt kamar ya hadiyi zuciya ya mutu…..
Babu wanda ya kula da halin da yake ciki saboda hankalin kowa na kansu deen da aketa cewa sun dace, be taba sanin yanada tsananin kishi ba sai ranar, lallabawa yayi ya mike ya nufi inda yayi parking motarsa, a daddafe ya bude motar ya shiga ya tadata ya bar gidan…
Driving kawai yake besan ina kansa yake ba, ga wani zafi da zuciyarsa ta fara masa, hakan kuma alamu ne na ze iya collapsing any moment….. Kiranta ya farayi ba kakkautawa ko zata gayamasa abinda zesa zuciyarsa tayi sanyi amma ina sai rejecting take, karshe ma sai aka sasa a line busy, hakan kuma ya sake tabbatar masa da abinda yake zargi, toh in banda abunsa dama wannan bibiya da deen ya musu a banza zeyi? Dukan daya masa kawai saboda sun gudu ai abun dubawa ne, sannan wa zega mace kamar baby tee ya kyale? kawai yana overlooking ne saboda baby tee bata kula deen tana kuma nunawa ta tsanesa amma yau ya tabbatar da maganarnan ta hausawa da suke cewa wata kusar tafi wata kusar, tabbas yaci ace ya gane deen ya fishi kusanci da power da ita a matsayinsa na dan uwanta koda ta tsaneshin kuwa, be hakura ba ya cigaba da kira har wayar ta fara cemasa switch off which means an kashe wayar gabadaya….
Besan ya akayi ba kawai ganinsa yayi a parking space din Abby cikin ikon Allah, fita yayi daga motar hannunsa dafe da zuciyarsa har ya karasa parlourn abby, luckily for him Abby na shirin fita sukaci karo Allah yasa be fitan ba….
Sosai hankalin Abby ya tashi ganin yanda ya shigo kamar an jehosa, a kidime yace;
“Subhanallahi! Lafiya khaleel?”…
Ai kawai gani yayi khaleel ya zube kasa a sume hannunsa dafe da kirjinsa……..
Salati Abby ya hauyi ya kira securities dinsa da sauri sukazo suka saka khaleel a mota suka nufi nearest good hospital……
Suna zuwa akayi diagnosing khaleel, Abby yayi tagumi yana jiran yaji daga garesu, gaba ki daya sai tinanin abinda ya samu khaleel yake….
Da kyar suka samu suka shawo kan khaleel sannan suka masa allurar bacci, beyi baccin daya kamata ace yayi ba ya farka yana ihun ‘wifey’ ‘wifey’, ba shiri likitoci suka kira Abby yazo khaleel nasan ganin matarsa saboda wifey din da sukaji yana kira sun dauka matarsa ce, Abby na jin sunan da yake ambata yasan baby tee yake nufi, shine ya dauki waya ya kirawo umm, ba karamin tashin hankali ya kara shiga ba da umm bata daukan waya sai yayi switching call din to number baby tee, ita wannan ma gabadaya a kashe yake cewa, daya wayar kuma yana shiga ba’a dauka itama, dole haka ya cigaba da kiran na umm gashi bashi da number mami bare ya kirata har Allah ya taimakesa umm ta dau wayar….

Kiran Abby a waya umm tayi ta fadamasa sun karaso asibitin, da kanshi ya fito ya samesu, gaishe da anna da bappa yayi cikin girmamawa yana kasa hada ido dasu, amsa masa sukayi cikin mutunci sannan ya musu jagora zuwa ciki………
Suna shiga deen daya kasa hakuri ya biyosu ya karaso gurin shima, bin bayansu yayi batareda kowa ya lura dashi ba…..
Ba karamin tashin hankali suka shiga ba ganin halin da khaleel yake ciki dan babu wanda ya kawo abun ya kai haka gashi har lokacin be dena kiran wifey ba, da sauri baby tee ta karasa gabon gadon da yake ta fashe da wani kuka me ban tausayi……
“Zahrah!”…..
Da mamaki gabadayansu suka juyo jin muryar deen…..

Download>>>

Back to top button