Uncategorized

Abban Sojoji Chapter 41 Book 2 Complete Novel

“`The father Of Soldiers“`

 

Story &  Written 

       By 

      Hafsat Bature

          (Boss Lady)

Sai faman kiciniya fawan yake yi saboda ya kwaci kansa daga hannun haroon wanda ya taushe masa fuska da pillow da mugunta ma yake kara danna masa shi, tun fawan yana wutsil wutsil da ƙafafunsa numfashinsa na kokarin daukewa gaba daya har jikinsa ya fara saki, suna cikin wannan halin aka kwankwaso kopar da karfin gaske,a wani irin tsorace haroon yayi wurgi da filon dake hannun shi, yayi wuff tamkar giftawar walkiya ya afka bayan labule ya boye yana faman zazzare idanun shi kamar na mujiya tsoran shi kar ace wani ne ya taso cikin daren nan,

Hannu yasa a hankali yaɗan buɗe labulen don yaga kowanene, gabansa ne yayi bugun bugu ganin Abbansu ya shigo ciki jikinsa sanye da jallabiya fara, cikin sauri haroon ya mayar da labulen ya rufe ruff tuni zufa ta soma tsattsafo masa a jikinsa tamkar wanda aka tsamo daga kogin maliya,

   ganin yarda fawan ya tashi zaune saman gadon yana faman hargowa yana fadin “zasu kashe ni ! bansan me nayi masu ba! Sun biyo ni don su kashe ni, ku ce musu su daina azabtar dani !!!! Gaba ɗaya ya zauce sai zuba sambatu yake yi yana zazzare ido,

   A hanzarce Abban nasu ya ƙarasa tare da haye wa saman gadon dab dashi yana cewa”fawan sannu ya jikin? ka dawo cikin hayyacin ka ko? ka kwantar da hankalin ka, kana a gida yanzu babu wanda zai iya cutar da kai,’. 

   girgiza kai fawan yashiga yi yana sake maimaita cewa “Har yanzu suna nan, bibiyata suke yi so suke su kashe ni, ni bansan me nayi masu ba,” yana magana daker daker yake sakin numfashi, hancinsa har ya fara bleeding kaɗan jinin ke ɗigowa,

   tallabo fuskarsa Abban nasu yayi tare da ɗago da ita don ya kalle shi sosai yace “fawan Ni ne fa,Abban ku ina tare dakai, babu wani anan da zai cutar da kai,”

  A hankali fawan ke kallon Abban nasu yayin da idon shi ke rurrufe wa yace “Abba ruwa zan sha,” ya faɗi agalabaice,

   Cikin sauri Abban nasu ya matsa tare da kai hannun shi saman bedside drawer ganin dakwai bottle water mai sanyi ajiye asama, ɗauko wa yayi tare da buɗe murfin ya kwafa masa abaki yana sha, jikin shi har wani kerma yake yi tamkar zai kwace roban ruwan daga hannun Abban nasu daya kwafa mashi, ganin yarda yake shan ruwan throat ɗinsa har wani sauti yake fitarwa kwattt!kwattt!! Saboda yarda yake kurbarsa a zafafe,

ba ƙaramin tausayi yaba Abban nasu ba, tamkar ya zubar mashi da kwalla haka yake ji, daurewa kawai yake yi

  Sai da ya shanye kusan rabin ruwan sannan ya janye mouth ɗinsa alamar ya ƙoshi, sannan Abban nasu ya rufe robar ruwan ya mayar da ita saman side drawer din ya ajiyeta,

  Sannan ya mayar da idon shi kan fawan dake ta faman sauke ajiyar zuciya yana fidda sound na radaɗin ciwo abakinsa,

  Haroon daka la6e acikin labule yace “shegen yaji dannar manya,an gaya ma jin ƙamshin mutuwa wasa ne,dole ka nemi ruwa yaro, ba don jatuminka ya faɗo cikin ɗakin nan ba, da yau saina aika ka barzahu wurinsu munkar, gskiya Abba ya kawo mun cikasss amma ba komai mu haɗe gaba,’ ya faɗi yana cizon la66ansa,

  Haroon kenan duk da yana cikin tashin hankali amma hakan bai hana shi sambatun nan nashi ba, mutuwa ce kawai zata iya zuge zeep ɗin bakinsa, 

muryar shi na rawa yace “Abba ashe zan ƙara rayuwa? abba nasha wahala sosai tamkar bazan rayu ba,ashe da rabon na sake ganinku a idona”? Ya faɗi yayin da idonshi ke zubar da kwalla,

   shima Abban nasu jiki asanyaye yace”Fawan nasani wlh,nashiga damuwa sosai game da halin da kake ciki har nagaza runtsawa saboda son nazo naga wani hali kake ciki,kayi haƙuri fawan iya cuta dae sun cuce ka sosai sun raunata dukkan ga66an jikinka, amma nayi maka alƙawarin cewa ɗaya daga cikinsu bazai sha ba, wlh muddin ina da raina da kuma lafiyata saina ƙuntata duk wani jin daɗinsu na duniyar nan,”

  Lumshe ido fawan yayi tare da kwantar da kanshi a kafaɗar Abban nasu yana sauke ajiyar zuciya sannan yace “Abban sunce fansa suke ɗauka akan family ɗin mu,wannan harin da suka kai mana, ba don kowa su kayi shi ba face saboda mu kawai,” 

Jin wannan maganar ta fawan tasa zuciyar Abban nasu yin wani irin bugu duk da yasan maganar revenge ɗin amma baisan cewa akan ƴa’ƴansa bane abun zai afka,

  “Insha Allah, Allah bazai ta6a Basu nasara ba fawan,zamu tashi tsaye wurin ganin mun kawar da koma su wanene su,Kuma zamu dage da addu’a akan Allah ya tonu asirinsu ya Kuma Kare Mana zuri’ar mu da dukkan al’umar musulmi,”

  “Ameen Abbana,” ya amsa mashi daker,

  Haroon dake a la6e bayan curtains duk yana sauraronsu gaba daya ya ƙagu abban nasu ya fuce daga dakin shima ko ya samu ya gudu,tuni kafafunsa suka soma daskare wa suna mashi raɗaɗi saboda tsayuwar da yayi, ga wani irin fitsari daya matse shi, sai uwar zufa ke wanko masa daga fuskarshi, runtse idanun shi yayi yana cewa “wayyyo Allah na, ko yaushe wannan tsohon zai ware nima in samu in gudu,lallaima mutumin nan wato saboda wannan ɗan shilan shine harya gaza yin bacci, ya wani kwaso kafafunshi yazo don ya gan shi,ina sane da komai wato ya daura son duniya ya aza masu,duk ranar dana hallaka ɗaya daga cikinsu zanga in haukacewa zaiyi ko kuma zaiyi suicide ne,’ 

  Ya faɗi yana cizon lips dinsa yana wani irin huci, bude idonshi yayi tare da sa hannu ya sake bude labulen a hankali ya leƙa su, har time din abban nasu na zaune dirshan saman bedmattress din, fawan kuma ya kwantar da kanshi a kafaɗar shi,da alama ma bacci yayi awon gaba dashi gaba ɗaya ya lafe masa kwance luffff abunsa, 

  Tuni ran haroon ya ƙara 6aci saboda takaici da baƙin cikin dayake ji aduk lokacin daya ga Abbansu na nuna ma ƴa’ƴan alexandra soyayya,zuciyar shi tafarfasa take yi saboda jin haushi, mayar da idon shi yayi kan pillow dinshi da yayi wurgi dashi kasa, nan gabansa ya faɗi tsoranshi kada abban nasu yaga fillon don za’a iya samun matsala,

  Bari dae in taƙaice maku zance,Abban su bai bar ɗakin ba anan bacci ya ɗaukesu su duka biyun azaune fawan kwance a shoulder ɗinshi,

  Kamar yarda suka kwana a zaune suna bacci haka Sir Commender Haroon ya kwana a tsaye ba bacci duk yarda yayi motsi zai fito sai Abban nasu ya buɗe ido, hakan ne ya hana shi fitowa daga bayan labule, 

  ya kuke tunanin wanda  ya kwana atsaye idonshi buɗe fuskarshi zata kasance, koda yake fa soja ne 😂

   (Wata dae tace commendern ƴan Iska dae, Bana sojoji ba)😹😹😹

****************************Morning

tun da sassafe sehrish tafarka daga guntun baccin daya ɗauketa bayan Sallar asuba anan saman sallayar ta kwashe da bacci, duk jikinta amace tafarka sai faman hamma takeyi saboda yunwar da take ji, gashi yesterday night bata samu enough sleep ba saboda tayi nafilfilin dare,

   tunawa da school yasa ta yin hanzarin tashi tashiga toilet shaf shaf tayi wankan ta,

fitowa tayi jikinta ɗaure da towel fari, a bakin ƙopar toilet ɗin ta tsaya tana kallon uniform ɗinta da sukayi uban squeezing tun jiya da tadawo school ta cicciresu ta jefar saman gadonta bata ninke su ba kuma anan tabarsu,girgiza kai tayi sannan ta ƙarasa agaban mirrow ta tsaya tana shafa body oil ɗinta,bayan ta kammala ta feshe jikinta da turare sannan ta koma ta buɗe wardrobe ɗinta, hannu tasa ta ɗauko ɗayan uniform ɗinta mai pencil skirt ɗin nan sannan ta dawo ta ajiyesu gefen gadon tashiga zura su ajikinta, tana cikin sa kayan maganar haroon ta faɗo mata aranta nace wa ta fara sallar dare domin neman tsari daga sharrin shi, tabbas maganarsa ta girgiza ta saboda tun daga lokacin da ta dawo daki at midnight tafarka tayi nafilfili saboda neman tsari daga sharrin shaiɗanin mutun irin haroon, ta jima tana jin cewa wasu abubuwa zasu faru tabbas acikin gidan!!!!! duba da irin mafarkin da tayi a baccinta na jiya, kuma taci Alwashin cewa ashirye take data fuskanci duk wani abu da zai taso ta ɗaura ɗamarar yin yaƙi da duk wani da zaizo don tarwatsa rayuwarta ko kuma family ɗin SALAHUDDEEN HUSSEIN,

Hakan na nufin SEHRISH ta shirya zama AYYANA wato mai bama family ɗinsu kariyyya daga miyagu irinsu Haroon da kuma ire-irensa masu irin wannan mummunan kuɗirin,nace ba Allah ya ba mai rabo sa’a, 

   Tana cikin wannan tunanin azmee ta kwankwaso ƙopar ɗakin tana cewa “Allah sa dai kin tashi,”

Murmushi sehrish tayi a lokacin ta kammala sanya uniform ɗin, ba ƙaramin kyau sukayi mata ba tafito ɗass especially skirt ɗin da ya bi shape ɗin jikinta sosai, 

  ƙarasawa tayi ta buɗe mata ƙopar ɗakin tana cewa “ae tun ɗazu na tashi nama kammala shirya wa,”

  Bin ta da kallo azmee tayi tana jinjina kai kafin tace “To fa yau wankan skirt aka ɗauka? masha Allah kinyi kyau ƙanwata, ya maganar breakfast fa? ta tambaya tana kallon ta,

  Sehrish dake ta faman murmushi tace “aunty azmee yau a school zanci abinci na gaskiya,amma zansha koda tea ne,”

  Azmee tace “okey, shikenan bari na kawo maki tea ɗin,’

gefen gado ta Zauna tana jiran dawowarta,

A 6angaren haroon kuwa bashi ya samu damar barin ɗakin da fawan ya ke ba har sai wuraren sallar asuba bayan abbansu ya kwantar da fawan dake ta faman sharar bacci a kafaɗarsa, sannan ya samu yabar ɗakin don zuwa yin sallah, sir commender haroon na ganin haka ya lalalla6a ya fito ya sungumi pillow ɗinsa daya shigo dashi, sai da ya jinkirta abakin ƙopar ɗakin ya tabbatar da cewa sun harhaɗu sun tafi gabatar da sallar asuba sannan ya koma ɗakin shi, agalabaice ya hankaɗa kopar bedroom ɗin nasa yayi wurgi da filon hannun shi,sannan ya afka toilet don tuni mararsa ta ɗaure saboda fitsarin dayayi ta ruƙo har na tsawon awannni, fitowa yayi daga toilet ɗin har wani biji biji yake gani saboda yarda idanun shi suka galabaita sun kumbura sunyi jawur saboda rashin baccin da baiyi ba, saman gadon shi ya afka batare da tunanin yin sallar asuba ba, sai ma addu’a daya shiga yi yana cewa “ya Allah ka yafe mun,zan ɗan rama baccin da banyi ba da safe in na tashi zanyi sallar anjima,’yana faɗin hakan ya shiga sharar baccin shi,

Babu wanda ya tayar da junaid daga bacci saboda basu son kwata-kwata yaga fawan ko kafin su tafi yin sallar asuba sai da Abbansu ya buɗe door ɗin ɗakinsa ya same shi baje magashiyyan yana sharar bacci rungume da pillow, murmushi kawai yayi tare da rufa masa door ɗin suka wuce mosque,

turo ƙopar azmee ta ƙara yi hannunta ɗauke da tea set ta miƙa ma sehrish cikin sauri sehrish tasa hannu ta kar6a tana cewa “Nagode aunty azmee,”

Azmee tace “ki hanzarta fa kada kiyi late dayawa,”

  “Toh,” ta amsa mata sannan ta shiga shan tea ɗin,

. har azmee zata fita sehrish tayi saurin cewa “Aunty azmee dama inaso nakaiwa babban yaya nashi kafin natafi school,”

   tsayawa azmee tayi hannunta ruƙe da door handle ta juyo ta kalle ta tana ɗan murmushi tace “i knew, raina sai da ya bani cewa sai kinyi magana akan RAFAYET,

,ɗan sunnar dakai sehrish tayi tana kallon tea ɗin dake hanunta yana faman tiririn zafi

   “Ni nake maki magana ba tea ɗin dake hannunki ba, naga kin zuba mashi ido,’ guntun murmushi sehrish ta saki kafin ta ɗago tana kallonta daƙer ta iya cewa “aunty azmee baya jin daɗi jiyan nan that’s why nake so nakai masa breakfast ɗinsa,nasan zai buƙace shi,”

  Sakin baki azmee tayi irin mamakin nan tace “to ko dai kece ALEXANDRA ban sani ba,’

  shiru sehrish tayi tana sakin murmushi saboda tagane cewa wannan sunan mommynshi ne,shiyasa azmee ta kirata da sunanta,

   fuce wa azmee tayi tana cewa “shikenan kiyi sauri kizo ki kai masa breakfast ɗin,” tana jin haka tayi saurin ajiye tea ɗin hannunta asaman bedside drawer inda kayan tea ɗin suke,

   hijab ɗinta ta ɗauko ta zura ajikinta yar dai² shoulders ɗonta, sannan ta wuce kitchen ɗin tayi mamakin ganin yarda azmee tayi uban aiki duk ita kaɗai, da alama ma tun bayan sallar asuba bata koma bacci ba,saboda tasan cewa dole manyan baƙi su hallara saboda zuwa duba fawan,

..shirya ma sehrish tayi breakfast ɗin SGR acikin ƙayataccen tray sannan ta miƙa mata, ruƙo wa tayi a hannunta sannan ta miƙi hanyar zuwa part dinsa, tana cikin tafiya taji anyi gyaran murya juyowa tayi da sauri don taga wanene junaid ne tsaye jikinsa sanye da shirt pulover tare jeans,

……har ya kammala shiryawar shi cike da ɗaukin kaita makaranta ya fito, sai faman zabga murmushi yake yi sam baida wata damuwa, ɗan dawowa baya tayi dai² saitinsa sannan tace “junaid ! Ya akai naga kana ta faman zabga murmushi, kai bakasan meke faruwa ba acikin gidan nan”? tayi maganar tana kallon shi,

..cikin mamaki junaid yace “kamarya kenan? meya faru ne ni bansan komai ba,”

  Jinjina kai sehrish tayi tare da cewa”jiya wani abu ya faru mai matuƙar raxanar wa, zan faɗi maka amma bari nadawo,” ta faɗi tare da saurin haye wa upstairs tana murmushi, taso ta faɗama junaid abunda ya faru amma azmee dake tsaye daga kitchen tayi mata alamar karta kuskura ta faɗa masa, shine dalilin dayasa tace mashi ya bari tadawo,

. tuni jikinsa yayi sanyi a ƙagare yake daya ji mai reesh zata sanar dashi,

  Kitchen ya wuce wurin azmee da sallama ya shiga sannan ya gaishe ta yana cewa “Aunty azmee a shirya mun breakfast a yunwace nake, gashi inaso nayi sauri nakai sehrish school,

  Sakin baki azmee tayi tana kallon shi kanta ya gama ɗaure game da lamarinsu su duka biyun, ita tagaza samun natsuwa saboda son takaima babban yaya breakfast ɗinshi, shi kuma junaid damuwarsa yakaita school,kowa da wanda ya damu dashi kenan,

  Zama yayi saman dining chairs yana jiran azmee dake shirya mashi bf ɗinsa ta kawo mashi yaci,

Acan ciki kuwa bayan sehrish ta isa part ɗinsa da sallama ta shiga baya cikin falonsa don haka ta wuce bedroom ɗinsa tsayawa tayi daga bakin door ɗin sannan tayi masa sallama, da wannan sexy voice ɗin nashi ya amsa mata, tare da bata permission din shiga daga ciki,

.a hankali tasa ƙafarta ta shiga ciki tsayawa tayi zuciyarta na faman bugawa ba ƙaramin kyau yayi mata ba,

ya juya bayansa yana tsaye a agaban mirrow jikinsa na sanye da bathrobe white colour wadda ta tsaya mashi dai² guiwarsa,a buɗe rigar take bai ɗaure igiyarta ba, amma akwai shorts ajikinsa,sumar kan nan tashi ta zubo mashi tayi irin Curly ɗin nan dark brown very smooth ta rufar masa abayansa, da alama bai jima da fitowa daga wanka ba,

…gaba ɗaya jikin sehrish ya gama mutuwa murus cos aduk time ɗin da tayi arba da wannan kyakkyawar surar jikin tashi rasa hankalinta take yi gaba ɗaya duk ta bi ta susuce,tana hangen shi ta cikin mirror saboda madubin yana facing dinta,

  tabbas yaji alamar shigowar mutun tun da harya bada iznin shigowa daga ciki amma har yanzu baiji an motsa ba, a hankali ya ɗago da blue eyes ɗinsa ta cikin mirror ɗin karaf suka sauka akan na rishi dake tsaye jikinta na rawa ɗan zaro idanun nata tayi tana kallon nashi dake kallon cikin nata ta cikin mirror, hankali atashe cikin tsananin tsoro tayi saurin sunnar da nata ƙasa gabanta na faɗuwa,

  gyaran murya ya ɗanyi kafin yace”a ajiye mun shi a palor, sannan agyara mun bedroom dina,’ amsa mashi tayi da “toh” sannan ta juya ta fuce tana faman sauke ajiyar zuciya, a saman table ta ajiye masa sannan ta ɗan tsaya tana jiran ya kammala kimtsawa,after some minutes ya fito jikin shi sanye da tunic shirt milk colour tare da trouser, sai ƙamshi yake fitarwa, shiga cikin falon yayi ya samu wuri ya zauna saman royal sofa ɗin sannan ya shiga yin breakfast ɗinsa anatse,

Wuce wa sehrish tayi cikin bedroom ɗinsa ta shiga gyara masa shi komai agyare yake,bedsheet ɗinne kawai da yayi squeezing ya tattare inda ya kwanta, cire shi tayi sannan ta musanya masa wani sabo mai kyan gaske ta shimfiɗa masa, bayan ta kammala gyara ko’ina cikin sauri tafito saboda tunawa da school karta yi late, a lokacin da ta fito samun shi tayi yana yin waya da alama kan fawan suke magana da mutumin daya kira shi awaya, 

      Kama hanyar fita tayi har takai baƙin ƙopa ta ɗan juyo tana kallon shi gudun kar ace yana buƙatar wani abu gashi zata tafi batare daya bata izni ba, ganin alamar mutun ta wutsiyar idonshi yasa shi ɗan juyawa karaf suka haɗa ido da sehrish dake tsaye tana kallon shi cikin sauri tace “Can i go”? tayi maganar aɗan tsorace,

  Lumshe idonshi yayi tare da ɗan jinjina kai alamar eh,

  Murmushi sehrish ta saki sannan ta fuce cikin sauri aranta tana cewa “Sannu bata hana zuwa,”😇

  Saukowa down tayi cikin sauri adai dai lokacin ta ji saukar motoci cikin gidan alamar sunyi baƙi, kitchen ta wuce anan tasamu junaid zaune saman dinner table harya kammala cin breakfast ɗin shi, yana ganinta yace “dama yanzu nake shirin biyo ki, bansan meya tsayar dake ba gashi har time ya ƙure ma,da ace ana bugu a school ɗin wlh da kinsha bulala yau,” dariya sehrish tayi jin abunda yace

  “Bari na ɗauko school bag dita,” ta faɗi tare da juyawa cikin sauri ta koma bedroom ɗinta,

  Sallama junaid yayi wa aunty azmee sannan yabaro kitchen din, jin sallamar Cg Abbas yasa shi ɗagowa cikin tsananin farin ciki yace “Yaya Abbas kaine tare da Aunty Amani !!!” 

murmushi suka saki gaba ɗayansu da yake tare suka zo shi da AMANI yana sanye cikin shigar shadda maroon color ita kuma tana sanye da Arab gown white colour mai kwalliya ajikinta na duwatsu tayi rolling veil a kanta, ba ƙaramin kyau tayi ba,

  sam junaid ya gaza rufe bakinsa don murna, buɗe mashi hannu abbas yayi cikin sauri junaid ya ƙarasa tare da faɗawa ya rungume shi sosai ajikinsa yana cewa “i really missed u our last born, duk da ina fushi dakai saboda baka son zuwa kawo min ziyara,’ yayi maganar a lokacin da ya raba jikin shi dana junaid,

  ɗan turo mouth dinsa yayi cikin shagawa6a yace “Yaya Abbas saboda me zaka ce kana fushi dani dan Allah, bakasan yarda na damu dakai ba koda yaushe inason zuwa amma shaiɗan ya hanani zuwa,’ dariya sukayi gaba ɗayansu jin abunda junaid yace,

  ɗan gyaran murya amani tayi masa tare da cewa”Junaid ni baka ganni bane”?

  matsawa yayi tare da kai hannu zai rungumeta ajikin shi, ae kuwa a razane Abbas ya finciko rigarshi tare da janyo shi baya baya yana cewa “Sannu mati na mata,!matar tawa zaka rungume agabana? salon mu koma gida ta juya mun baya ko?”

  Fashewa da dariya Amani tayi shima junaid ɗin dariyar yake yi cikin jin kunya ya sunnar dakai, shi aganin shi ba wani abu bane don ya rungume matar yayan shi, duk cikin waye wa ne,

  Abbas ya kuma cewa “Oh ni junaid? Yanzu fa in na ƙyale ka sai ka rungume ta ko”? 

  ɗaga mashi kai yayi alamar Eh, hannu abbas yasa tare da ɗan jan kunnan shi har yayi ƴar ƙara yana faɗin “wayyo yaya Abbas karka cire mun kunne na in rasa na jin magana,” 

  “Hanzarta ka cire masa kunnan, hukuma ce zata raba ni dakai,” acewar Abbansu wanda bai jima da fitowa ba ganin su yasa shi tunkaro su,

   Murmushi suka saki gaba ɗayansu, adai dai lokacin Sehrish tafito daga ɗakinta, harta sanya Sandals ɗinta taruƙo school bag ɗinta, ƙarasawa tayi inda suke,

  tunkan taƙaraso Amani ke kallonta cikin jin bugun zuciya, shi kanshi Abbas kallon matashiyar yarinyar yake yi cike da mamakin ina aka samu yarinya mace acikin gidan,

Ganin duk hankalinsu yadawo kanta yasa jikinta ya soma yin kerma, dakatawa tayi da tafiya sannan cikin en ina tace “umm….ina kwananan ku,”

  atare abbas da abbansu suka amsa mata banda Amani dake tsaye ƙiƙam tana kallonta cikin tashin hankali, ita kanta sehrish atsorace take da kallon da Amani ke yi mata, 

  “Zonan My daughter nayi missing ɗin ganinki, gashi bakya zuwa kina gaishe da Abbanki ko”? Yayi maganar yana kallonta,

  Ƙarasawa sehrish tayi gab da Abban nasu ta tsaya tana faman ƙaƙume hannun jakarta da ta sargafo a kafaɗarta,

Hannu yasa tare da shafa gefen fuskarta yace”yaushe kika fara zuwa school ne ba’a sanar mun ba”?

….daker sehrish ta iya cewa “jiya ne nafara zuwa,”

Jinjina kansa yayi tare da cewa “okey,ki maida hankali sosai akaratun ki kinji ko? Banda biye ma ƙawaye 

  “Insha Allah Abba,” ta amsa mashi,

Baki asake Abbas yace “yakamata a wayar mun dakaina mana, ina aka samu yarinya kyakkyawa kodai daga cikin danginmu ne na damaturu ko zariyya”?

  Ya tambaya aɗan ruɗe yana kallon Abban nasu, tunkafin Abban nasu yace wani abu junaid yayi saurin cewa “ƙanwata ce yaya Abbas, sunanta Sehrish kuma abbane yayi mun ƙanwa da ita, itama ƴar Abban mu ce, ba’a jima da haihuwarta ba, nasan zakayi mamakin yarda tayi saurin girma har haka, ka tambayi Abba zaiyi maka bayanin komai,’ 

  yana faɗin haka yaja hannun sehrish suka bi ta gefensu suka fuce,

  Dariya kawai Abbansu ke saki hada shi Abbas ɗin,

  “Ji wata shiririta irinta junaid,hakanan kawai ya zabga mun ƙarya, ina na ajiye matar bare harna haifi ƴa kamar wannan,’ 

Ya fadi tare da yi masu alamar su shiga daga ciki, bin shi su kayi tare da samun wurin saman royal sofa mai mazaunin mutun uku suka zauna, Amani na kusa da Abbas yayin da Abban ke fuskantar su yace “sannun ku da zuwa,nayi mamakin ganinku da wuri haka,”

Abbas yace “tun jiya muka so muzo,amma dare yayi sosai lokacin, wlh sam nagaza samun natsuwa ne game da halin da naga fawan a asibiti, shine nace mata tashirya muzo har gida mu duba shi,” 

  yayi maganar fuskarshi dauke da damuwa, Amani ma tace “Abba ya mai jiki? sai jiya da daddare yake faɗamun abunda ya faru dasu fawan hankali na ya tashi sosai, tun jiya nima naso ko wayane nakira na tambayi jikin shi amma duk layin dana kira ba’a ɗagawa,”

Abba yace “ae ba zaki same su ba, saboda duk muna cikin damuwa ne,bakowa ma yasan inda ya jefa wayarshi ba,abun ne ya tayar mana da hankali sosai,

Cikin sanyin murya tace “Allah sarki Allah ya bashi lafiya,ya tashi kafaɗun shi, su kuma waɗanda sukayi mashi wannan aika aikan Allah ya toni asirin su,”

  “Ameen Ameen,” suka amsa mata 

Daga bisani Abbas yace “bari mu shiga ciki mu dubo shi,”

  Miƙewa su kayi hada Abban yayi masu jagowa izuwa ɗakin da aka kwantar da fawan,

  Da sallama suka shiga ciki, har lokacin fawan na kwance sai faman sharar bacci yake yi, Abbas yace “masha Allah jikin nasa yafara sauƙi, tun da harya samu bacci,”

  “Ae tunjiya dana shigo ɗakin na same shi yana ta faman fisge-fisge yana cewa sun biyo shi zasu kashe shi,saina zauna wurin shi anan zaune muka kwana ni dashi da asuba ne nabar ɗakin,” Abban nasu ne yayi maganar ayayin da yake samun wuri gefen gadon tare da zama yana kallon fawan ɗin dake kwance magashiyyan yana kwasar bacci,

  matsawa Abbas yayi shima tare da samun wurin kusa da Abban nasu ya zauna sannan yakai hannun shi ya dafa forehead din fawan yana cewa “Baƙaramin jiki yaji ba gaskiya,sun azabtar dashi sosai bawan Allah, amma asannu zai warware insha Allah,

  Kafin Abban nasu ya kuma cewa wani abu wayar Amani dake acikin handbag ɗinta tashiga yin ringing da ƙarfin gaske,

  Kallonta Abbas yayi tare da cewa “ki fita waje ki amsa wayar,” cikin sauri ta amsa mashi da toh sannan ta fuce,

 dama so take ta fita daga ɗakin saboda gulmar data ciyota kunsan mu mata abun ajinin mu yake,da zarar abun gulma ya samu nan take zaka ga jikin mutun har rawa yake yi don ya faɗama ɗan uwansa, (Amma fa ni bana gulma) 😒

Cikin sauri Amani ta sauko down stairs jikinta har rawa yake yi ganin Azmee na jera masu breakfast a dining table, yasa cikin sauri ta wuce wurinta 

  Azmee naganin ta ta soma sakin fara’a tana cewa “aaa yau kune agidan namu? saukar yaushe,”

Batare da Amani ta amsa mata ba tace “Yawwa Aunty azmee dama akwai abunda nakeso na tambaye ki,”!

  Cikin mamaki azmee tace “meke nan”?

  “Ga me da Yarinyar dana gani acikin gidan nan, wata ƴar matashiyya shin ita ɗin jinin su Abba ce?

  murmushi azmee ta saki aranta tace “Gulma ajali, in ba’ayi ba a mutu,” a fili kuma tace “abokiyar aikina ce a aka kawo don ta runƙa tayani aiki,”

  yamutsa fuska amani tayi kan ta yagama ɗaurewa ta kuma cewa “ƴar aiki fa kika ce? But i was confused ya akai naganta cikin uniform kuma har junaid na kiranta da ƙanwarshi? Kuma naji Abba ma ya kirata da My daughter,duk kuma a matsayin mai aikin?

  dariya azmee tayi ganin yarda amani ta ɗaga hankalinta akan sehrish

  “tabbas mai aiki ce itama, amma abba ya mayar da ita tamkar ɗiyarsa,bata da banbanci da sauran ƴa’ƴanshi a yanzu, saboda yana son Yarinyar sosai,”

  Jin haka yasa Amani ɗan zaro ido waje bata ƙara cewa komai ba saboda wayarta da ta ƙara yin ringing, cikin sauri ta zura hannu tare da buɗe handbag din ta zaro wayarta, tare da duba screen din wayar don taga mai kiranta, sunan Aunty laila ne ya bayyana asama, kallon Azmee tayi tare da cewa “ina zuwa,” tayi maganar tare da kama hanya ta danyi nesa da azmee sannan ta ɗaga kiran tare da kara wayar a kunnanta tana cewa “barka da safiyya Auntyna fatan kin tashi lafiya,”

Murmushi Aunty babba tasa ki daga can 6angaren tace “Lapiya lou Alhmdllh my sister, nazo maki da labari mai daɗi ina fata kina da kunnan saurara,”

  Amani tace “nima ae ina tafe da labari zazzafan gaske, amma bansan wa zai fara bada labarin shi ba acikin mu,” 

  Saurarawa tayi tana jiyo dariyar aunty babba ta cikin wayar sai da ta tsagaita da dariyar sannan tace “ina tunanin labarina yafi naki daɗi kuma zaifi ƙayatarwa, bari dae ni nafara baki,”

  murmushi Amani tayi tamkar tana agabanta tace ina sauraronki auntyna,

  gyaran murya Aunty babba tayi sannan tace “ina yaran nan da nake baki labari Omar ya kawo mun gidana?

  Amani tace “eh nagane su,”

Aunty babba taci gaba da cewa “ae tuni nasa an kwashe su, an jefar mun dasu bayan gari,yanzu haka hankalina kwance na rabu da alaƙaƙai, yanzu banda wata sauran damuwa saura target ɗina nagaba nake jira….” tunkan taƙarasa maganar Amani ta kwashe da wata irin mahaukaciyar dariya,

Jin dariyar da amani keyi ne yasa aunty babba dakatawa da maganarta tana sauraronta ta cikin wayar, ganin cewa amani bata da alamar jinkirtawa da yin dariyar da takeyi ne yasata cewa “ke bana son iya shege, na ji kina mun dariya kodai daɗin labarina ne yasa ki jin daɗi har haka,” ta tambaya tana jiran jin mai amani zata ce,

  daƙyar Amani ta tsagaita da yin dariyar sannan tace “Aunty laila an fa yanka ta tashi,labari da ɗumi ɗuminsa idan ma kina atsaye to wlh ki zauna don kar in sanar dake ki yanke jiki ki faɗi,”

  Jin maganar Amani yasa hankalin aunty babba ɗugunzuma,murya na rawa tace “ba atsaye nake ba,ina zaune saman 2 seater ne ina shan tea,dan Allah ki sanar mun wane irin labari ne wannan,” 

  wani irin shu’umin murmushi amani tayi kafin ta soma cewa”Yanzun nan muka zo gidansu Abbas saboda mu duba jikin fawan da miyagu suka kai masu hari, ina fata kinsan wannan labarin”? Ta tambaya tamkar tana agabanta,

Aunty babba tace “eh nasani,ae muna nan muma zamu zo tare da ishaq don mu duba jikin shi,”

  Jinjina kai Amani tayi sannan taci gaba da cewa “Shin ko kinsan cewa akwai wata matashiyyar yarinya kyakkyawar gaske da muka tarar acikin gidan !!!’

  darammm !!!gaban aunty babba ya faɗi rasss a firgice ta saki cup ɗin dake hannunta ya tarwatse ƙasa, zumbur ta miƙe tsaye tana cewa “kamarya Amani ! Bangane abunda kike cewa ba anya ba kunne na bane suka jiyo mun hakan”?

  dariya amani tayi kafin tace “ba kunnanki bane Aunty laila,zahiran ne wannan nake faɗa maki, wlh da ido na naga yarinyar,kyakkyawar gaske har na tambayi azmee nake cewa wacece ita yarinyar kodai cikin danginsu Abba take, sai azmee ke sanar dani cewa house maid ce itama amma Abba ya mayar da ita tamkar ƴarsa, har fa school sun sanya yarinyar babban abunda zai tayar maki da hankali sai kin ga yarda Abba ke kiranta da ɗiyarshi, yarinyar ba ƙaramin wuri ta samu ba…….

Fuska a damuje aunty babba tace “nifa hanyanzu ban fahimta ba, shin yarinyar ƙarama ce sosai ko babba”?

  Amani tace “ina fa, wlh balagagga ce nace maki fa matashiyar budurwa kyakkyawar gaske mai cikar sura,ni kaina dana kalle ta sai da gabana ya faɗi to ina ga matasan gidan da suka kasance maza ne dukansu,

  Jin wannan maganar yasa aunty babba dake atsaye tana zarya a falon nata, aza hannunta na dama akanta, ɗayan kuma na ruƙe da wayar tashiga cewa “Ae shikenan wlh an yanka ta tashi, ni ina nan sake da baki ina murnar rabuwa da waɗancan tagwayen da Omar ya kawo min ashe abanza ga wata can ta riga ƙetare iyakar da bana so aje,amma an gama dani wlh ya akai har takai wannan lokacin gidan baki sanar dani ba,”? ta tambaya a kiɗime,

  Amani tace “nafa ce maki ni kaina bansan da zamanta ba, yau ɗin nan muka ganta kwatsam tafito ɗas da ita cikin school uniform wlh abun ba’a magana yarinya haɗaɗɗiyar gaske,tasamu wuri fa sosai agidan, kuma yarda naga Abbansu na kiran sunanta da daughter dinshi kinga kuwa hakan na nufin nan gaba ma da sunan Surikata zai kirata,” 

  ƙasa ƙasa amani ke sakin dariya tana sauraron aunty babba dake faman Zabga salati, dama dagangan take tunzurata don ta rikitar da ita, 

“Nashiga ukuna,wannan masifar har ina matashiyar budurwa kuma agidan surikina, wlh hakan bazai ta6ayiyu ba, wlh saina son yarda zanyi na rabata da gidan, badai zamu zo da ishaq ba hmmmm zanganta ne !! zanga KOWACECE ITA 😳😳😳

  Sun jima suna waya da aunty laila kafin daga bisa ni sukayi sallama da juna amani ta koma daga ciki, ranta fess don tasan yau ko bacci aunty babba bazata iya yi ba har sai taganta a Abuja, gata ga yarinyar data bata labarinta,

Fitowa hafsat tayi daga bedroom ɗinta jikinta sanye da sleeping dress ganin mommyn nata tsaye tana ta faman zarya a falon tana zazzaga bala’e ita kaɗai kamar zararriya, hakan yasa hafsat ƙarasawa kusa da ita tana cewa “wai mommy lafiya kuwa kike ta faman tada jijiyoyin wuya duk akan wanene?

Uban tsoki Aunty babba ta saki sannan tace “wani mummunan labari amani ta sanar dani yanzun nan, wlh nagaza samun natsuwa, so nake kawai naganni a abuja wlh,”

  Wuri hafsat ta samu tare da zama saman 2 seater sannan tace “mommy wannan wane irin labari ne haka daya tayar maki da hankali haryasa kika fasa cup ɗin da kike shan tea dashi,” tayi maganar ayayin da take kallon kofin da aunty babba ta saki ƙasa ya fashe,

  juyo tayi ta kalle ta rai a6ace tace “ba dole hankali na ya tashi ba, ina murnar rabuwa dasu hossana da jahad sai gashi yanzu Amani ta kirani awaya tana sanar dani cewa sunje gidan su Abba, sun tarar da wata matashiyar budurwa wai mai aikice fa, amma abba ya mayar da ita tamkar ɗiyar cikinsa,” tayi maganar tana huci,

  Shiru hafsat ta ɗanyi na wani lokaci kafin daga bisa ni ta saki ƙayataccen murmushi tace “Mommy kenan, dama kina tunanin haƙƙinsu hossana da jahad zai barki ne? to inaso ki sani haƙƙinsu ne yafara bibiyarki, kuma ba zaki ta6a cin nasara ba akan wannan yarinyar da aka baki labarinta yanzu, saboda mommy sam baki kyauta ma rayuwar yaran nan ba, basu miki laifin komai ba kinsa an kwashe su,ki kayi mun ƙaryar cewa gidan marayu za’a kaisu ashe zubar dasu kikasa ayi,yanzu wayasan wani hali suke ciki………’ hawaye ne suka soma zarya a fuskarta saboda raɗaɗin da take ji aduk lokacin da ta tuna dasu hossana da jahad,tun jiya da aunty babba ta sanar da ita cewa ba gidan marayu tasa akaisu ba, zubar dasu tasa ayi bata ƙara samun kwanciyar hankali ba, abun namata ciwo azuciyarta

. kallonta kawai aunty babba keyi ganin yarda take zubar da tears ɗinta akan tsintattun yaran da bata haɗa alaƙar komai dasu ba,

  tsoki ta sake ja tare da cewa “kin dai ji haushin rayuwarki wlh, saboda waɗancan marasa galihun kike ta faman sharara kuka,har kina ikirarin haƙƙinsu ne ke bi na,to ki zuba ido ki gani saina sa anyi waje da waccen yarinyar da amani taban labarinta,” 

  afusace hafsat ta miƙe tana kallonta tace “mommy! Ina miki fatan nasara,” tana fadin hakan ta juya tare da komawa bedroom ɗinta,

  Jinjina kai aunty babba ta shiga yi tana faman sakin huci kamar zakayan, afili tace “Tabbas dole nasan kowacece wannan yarinyar dake ƙoƙarin tarwatsa mun plan ɗina, yakamata nasan abunyi dole na kira HAYAAM awaya in sanar da ita cewa ta tattaro kayanta itama ta koma gidan da zama, tunda har ƴar aiki ta samu irin wannan gatancin ina ga ita da take ƙanwata !!!!!!🤭

  Sai faman balbali bala’e take yi ita kaɗae tana ci gaba da zarya a falon,

*******************************

tun bayan da junaid ya sauke sehrish a school su kayi sallama ta shige ciki shi kuma yakama hanyar komawa gida yana driving yana tunanin fuskar rishi ɗinsa tsantsar sonta ne ke sanya shi jin wata irin kasala a jikinsa, lokacin da ya ƙaraso gida sai da gabanshi ya faɗi rass ganin dandazon motoci suna ta shiga gidan nasu,manya manyan mutane ne aminnan abbansu suke ta zuwa dubiyar fawan, wasu daga cikinsu manyan shuwagabannin sojoji ne da kuma mr president da kanshi ya tako yazo don duba jikin ɗan aminin nasa atare dashi hada mataimakinsa da kuma babban ɗansa Captain Shattima wanda ya kasance aboki ne ga Marshal Omar da SGR tun a U.s don acan shima yayi karatunsa na Airforce, halayyarsa da ɗabi’unsa sak irin nasu ne shiyasa tafiyar tasu tazo ɗaya, ƙwararre ne a6angaren aikin shi, sannan kuma shima mace sam bata gaban shi,tamkar dae su ɗin dae,

  Gida fa ya ɗinke ɗuff da mutane tamkar rasuwa akayi, ta ko’ina jinsin bil’adama ne ke ta shigowa,

  Hankalin junaid ba ƙaramin tashi yayi ba tunkan yayi parking ɗin motarsa yake ta faman sharar hawaye tsoran shi kar ace wani abune ya faru dasu fawan saboda yasan sune basa a gida anturasu aiki,a hankali ya tsayar da motar sannan ya buɗe murfin motar ya fito yana kallon mutanen dake shigowa,

…jingina bayansa yayi ajikin motar tashi sannan ya zura hannun shi cikin trouser pocket ɗinsa, wayar shi ya zaro tare da shiga contact ɗin wayarsa, lambar abbansu ya gano sannan ya buga masa waya,

  ta jima tana ringing kusan sau uku kafin Abban nasu ya ɗaga kiran,

  Kara wayar yayi a kunnansa tare da fashe mashi da kuka,

  Shiru Abbansu yayi yana sauraran kukan da junaid ke yi masa acikin wayar,

  Cikin shesshekar kuka yace “Abba……wanene ya mutu, naga dandazon mutane acikin gidan…’daker ya iya yin maganar zuciyar shi na faman bugawa,

   “Kana ina ne”? abban nasu ya tambaya

..”gani awaje abba, nakasa shigowa,ina jikin motata yanzu haka ban jima da shigowa gidan ba, saboda nakai sehrish school ne,”

  Ajiyar zuciya abbansu ya saki kafin yace “sauraran ni kaji da kyau, babu wanda ya mutu, nasan halinka ne shiyasa tun jiya ban sanar maka ba, amma yanzu zan faɗa maka, but promise me first cewa zaka daina kuka,” 

  Ajiyar zuciya junaid ya shiga saukewa yana cewa “Okey, abba nadaina tell me pls,” 

  gyaran murya abban nasu yayi tamkar yana agaban shi sannan yace “abunda ya faru shine, su irfan da aka tura aiki,miyagu suka farmake su amma alhmdllh duk suna cikin ƙoshin lafiya, fawan ne kawai suka samu nasarar cutar dashi harya zauce ssae tun shekaran jiya suna asibiti ana duba su sai jiya ne muka dawo gida tare da su…………’

  tunkan abban nasu ya ƙarasa maganar tashi tuni Junaid ya saki wayar dake hannun shi sakamakon faduwar da yayi nan take ya sume……………….dama abunda abbansu ke gudu kenan

 hankali atashe yake cewa “junaid!junaid !!! Kana jina kuwa !! Meya faru ne,

  yarda yake fidda sautin maganar yasa kowa dake a falon kallon shi, dama duk suna a falon sun hallara saboda sun fiddo da fawan yana kwance asaman 3 seater yana amsa ya jikin da mutane keyi masa,

gaba ɗaya hankalin kowa ya tashi,suka shiga tambayar shi meke faruwa ne,

zumbur ya miƙe yana cewa “wlh junaid ne daga faɗi mashi halin da fawan ke ciki shikenan ya yanke jiki ya fadi ina tunanin ya suma ne awaje,’

“Subhanallahi,” mutanen wurin suka haɗa baki wurin cewa haka, fawan dake kwance kuwa tuni ya shiga kiran sunan junaid yana fadin “Abba akawo mun junaid inason ganin shi,” ya faɗi akasalance,tun jiya dama yake so yasa shi a idonshi amma bai samu dama ba,

  atare abbansu da cg abbas suka fito domin ɗauko shi, tun kan su isa sai gashi ɗaya daga cikin soldiers din dake cikin gidan ya ɗauko shi sa6e a kafadarshi, cikin sauri Abbas ya kar6e shi tare da yima sojan godaiya, sannan su ka koma ciki dashi,

********************SGR hospital

tun safe su hossana da jahad suke ta faman jiran yaya Omar ɗinsu saboda yazo ya ɗauke su amma shiru babu alamarshi, suna kwance a gado ɗaya saboda since yesterday night hossana ta maƙale ma jahad aɗaki ɗaya suka kwana tana agefenta,hankalinsu kwance saboda kyakkyawar kulawar da suka samu a wurin nurse Camila,tun da sukayi breakfast wanda anan asibitin suke rabawa marasa lafiya abinci kyauta kuma lafiyayyen gaske,sunci sunyi hani’an suna jiran omar yazo, duk in Camila tashigo duba su sai sun tambayeta yaya Omar dinsu yazo? Sai tace musu a’a su ƙara jira kaɗan tun suna tambayarta har suka gaji suka daina,

Around 12 na rana, Motar Omar ta shigo cikin asibitin, bai samu damar zuwa ba saboda busy ɗin daya shiga hakanne yasa shi aiko major domin ya ɗauko su kamar yarda yayi musu alƙawarin cewa da safe zai sa asallame su, dalilin dayasa ya turo masu da major kenan amaimakon shi,

  Bayan major yayi parking ɗin motar sannan ya fito ya shiga ciki, kai tsaye ɗakin dasu su hossana ke ciki ya nufa,

  suna ganin shi suka fara murna don sunsan cewa yana tare da Ya omar, 

    “Ya jikin naku”?

Cikin sauri suka amsa mashi da cewa “Alhmdllh jiki da sauƙi,”

Yace “masha Allah,kun ganni ni kaɗai ko?

Hossana tace “eh, ina ya omar din, shi bai zo ba tun ɗazu muke jiran shi,”

  Murmushi major yayi kafin yace “kuyi mashi Uziri yana busy sosai, amma ya aiko ne nazo don na duba ku,sannan nasa a sallame ku mu tafi gida,”

  ba ƙaramin daɗi suka ji ba, don aƙagare suke da su ga inda zasu zauna wurin da zasu fara sabuwar rayuwa,

  “bari naje naga dr, yanzu nan zan dawo,” yayi maganar tare da fuce wa daga ɗakin,

  Cike da murna hossana tace “Shikenan mun rabu da wahala, yanzu zamu fara kyakkyawar rayuwa, saboda nasan yaya omar har makaranta zai samu,har na hango ni yarda zan koma nan da 1 month,” 

Kallonta jahad tayi da yake sun tashi daga zaune tace “jibgegiya zaki koma kamar buhun fulawa,nikaina naƙosa naga yarda rayuwarmu zata canza,abu biyu nake tunawa da suke sani kwanciyar hankali na farko shine bani da wata sauran damuwa dama hossana ke nafi ji, damuwata aduk lokacin da muka shiga hadari kece ina tsoran kar na rasaki,abu na biyu kuma shine ƴar Uwarmu SEHRISH,duk da bansan a ina take ba amma inaji araina cewa TANA TARE DAMU, INA NUFIN TANA A KUSA DAMU SABODA INAJI A ZUCIYATA!! With confidence tayi maganar in serious matter,

  jinjina kai hossana tayi kafin tace “Jahad nima inaji araina cewa REESHI TANA A KUSA DAMU,komai ma zaizo mana cikin sauƙi yanzu tunda zamu samu kwanciyar hankalin nemanta,ga kuma YA OMAR,NASAN DAGA MUN FAƊA MASA CEWA ƳAR UWARMU TA 6ATA MUNA NEMANTA KUMA KAMANNIN MU ƊAYA SAK MU TRIPLET NE,SAI MU FAƊA MASHI SUNANTA NASAN ZAI TAIMAKA MANA WURIN GANO TA……………..✍️💋

Shin mai zai faru idan Aunty babba tayi arba da fuskar Sehrish😳 yaya zata kasance tsakanin Haroon da twins? Baku tunanin cewa dole ALEXANDRA tazo nigeria domin duba jikin fawan😲? haka zalika AMMI ma muna hasashen zuwanta domin ganin fawan😲, ga kuma goggon katsina karfa ace itama zata zo domin ganin fawan shin ya zatayi a lokacin da tayi arba da fuskar sehrish wadda takasance kamanninta ɗaya da ƴa’ƴan abusufyan ɗinta?🤣, to kodai shima abusufyan dake zaune ƙasar turkey zaizo nigeria ne?😯, ni duk bama wannan ba🤨 abunda yafi damuna shine HAYAAM ƙanwar aunty babba wadda ke shirin dawowa gidan da zama 🥱 in har dagaske ne kenan sehrish itace a tsaka mai wuya tabɗijan can, ga haroon ga aunty babba ga wata wai hayaam🥴 wayyo har kaina yafara ciwo don tunanin yadda zatakasance, yakamata naje na kwanta fa, amma kafin nan akwai hasashe ɗaya daya rage mun shin ya zata kasance idan Hossana da jahad suka sanar da Omar game da ƴar uwarsu wadda takasance ita ɗin ƴar ukunsu ce kuma sunanta SEHRISH 🥺🥺🥺

  

  

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Alhmdllh last page da nayi alƙawarin zan saki kafin na tafi hutu till 10 oct zamu cigaba insha Allah, nagode ssae da fahimtata da kukayi kuma insha Allah nima bazan baku kunya ba da zarar lokaci yayi zamu ɗaura daga inda muka tsaya in darai da lafiya,🥳

…Much Love to my novel readers am really proud of u guys😍😘🥰 Anatare insha Allah kuma Allah yabar zumunci atsakanin mu daga nan har gidan aljanna😍💃

  Ya Allah kasa mu cika da kyau da Imani🙏

Back to top button