DA BAN SAN SHI BA
DAGA FAUZIYYA D. SULAIMAN
(KAUYEN SANBAUNA)
Sararin samaniya yayi baƙinƙirin sai tsawa da ci da ake yi, garin ya murtike alamar daga lokacin zuwa ko yaushe za a iya tsinkewa da ruwa, kasancewar lokacin damina ne.
Sumaye tana tsugunne gaban murhun duwatsu guda uku tana hura wutar da bakin ta, kasancewar karan da take amfani da shi gurin girkin ya jike sharkaf da ruwa shi ya sanya yake bata wahala gurin hurar, idanuwan ta sun kada sunyi jajir ga yamma tayi rana na shirin faɗuwa, ga kuma hadari dake shirin zubar da ruwa bugu da ƙari kuma tsohon ciki da take ɗauke da shi duk ta jigata tayi wuki-wuki da ita.
Lanto abokiyar zamanta da ɗiyar ta mari da salame suna zaune a gefe suna ɓarar tumun dawa suna watsawa abakunan su da suka gasa, cikin hira da kallonta suna murmushi daga nesa inda suke zaune. Lanto tayi kwafa “A dai yi mu gani idan tusa zata hura wuta.” Sumaye ta ɗago ta kalleta kamar zatayi magana sai kuma ta fasa ta ci gaba da abin da take yi, amman har lokacin idan karan ya huru sai kuma ya mutu.
Alu ya shugo gidan cikin gaggawa yana dauke da ɗaurin kara timili guda akan sa, yaro ɗan kimanin shekaru takwas, mai kuzari da kazar-kazar, sallamar shi ce ta sanya lanto da ‘ya’yanta waigawa da sauri suka kalle shi, mamaki da takaici ya bayyana akan fuskarsu domin basu yi tsammanin dawowar sa gidan ba yanzu, burin su bai wuce a tsuge da ruwa, Sumaye ta kasa yin tuwon dare maigidan yayi faɗa kamar zai rufeta da duka ba.
Sumaye ta waiga ta kalli Alu farin ciki ya bayyana akan fuskarta, Alu ya isa gabanta ya ajiye damin karan yana murmushi.
“Sannu da aiki Inna?” Sumaye tayi murmushi.
“Sannunka mai Sango, amman kayi sauri, banyi zaton zaka dawo haka da gaggawa ba.” Tana ƙoƙarin zarar karan.
Yayi murmushi ya ƙarasa kusa da murhun ganin hadarin ya gangamo ya sanya nace bari na yi gaggawa, ga shi sai dana kutsa can cikin jeji na samo busasashe, bari na hura miki koma zauna ki huta inna.”
Sumaye ta yi baya cikin farin ciki, Alu ya ɗurkusa gaban murhun duwatsun ya fara zare jikakkun itatuwan yana sanya bisashen, Lanto da yaranta suka zuba masu idanu cikin takaici.
Cikin kankanin lokaci sai ga wuta ta ruru ta fara ci balbal, Alu ya juya ya kalli mahaifiyar sa da ke maida numfashi dai-dai saboda wahalar hura wutar da ta yi yana fadin.
“Inna na gaya miki na fi kowa iya hura wuta a garin nan.” Sumaye ta yi murmushi tana kada kai. “ka dai iya iyacin abin da ka iya Mai Sango. Ta ba shi amsa.
Takaici da bakin ciki ya kara cika Lanto da yaranta da ke zaune suna kallon dukkan abin da ke faruwa, wani irin hali garesu na bakin ciki da nassada ba su kaunar ko wuta ace ta kama ranar girkin Sumaye, matar da bata taba kulawa da halin da suke ciki ba, al’amuran gabanta sune kawai a gabanta.
Salame ta kalli Lanto cikin tsokana da isgili ta na Magana tana kallon Sumaye. “Inna kin taba fada mana kamanni da yanayin yaron da zai iya zamtowa dan Daudu a ravuwar sa ta gaba, amman na manta ko zaki tina mini?
Sumaye ta waiga ta kallesu da sauri, domin ta san da Alu suke, abin da Alu yafi tsana cikin rayuwarshi shine a danganta shi da wannan suna Dandaudu domin irin fashin baƙin da aka yiwa sunan bai kaunarsa, amman yayyan sa suna son gaya masa wannan sunan badon komai ba sai don su bakanta ran Mahaifiyarsa da na shi.
Lanto ta gyara zama tana murmushin jindadi gami da fadin “Tsiya ta dake Salame baki da mantuwa, ai na sha gaya miki, dukkan namijin da ya tashi yana aiki irin na mata kama daga debo ruwa, dauko ice, hura wuta, tankaden garin tuwo da dukkan abubunwan da suka kasance dabi’ar mata, to akwai tabbacin a rayuwar sa ta gaba zai kasance Dan-daudu.
Gabadaya yaran suka fashe da dariya, Sumaye da Alu suka tsaya suna kallon su cike da tsananin bacin rai, Sumaye ta mike da sauri ta nufi Alu da ke tsaye yana huci kamar zai fashe kuka, ta kama hannunsa tana fadin “Mai Sango maza ka wuce gidan Inna wuro ka amso mini sassaken nan, ka ji ko?”
Alu ya kalli yayyan na sa yana kwafa ya fara Magana “Inna ki bar na hura miki wutar ki har ki kammala girkin ki, bana damuwa da dukkan abin da suke fada, kin sha gaya mini dukkan abin da yaro yayi wa mahaifiyar sa cikin lada yake yi, ku ma shi zai kai shi aljanna, ki bari na karasa miki kawai.
Sumaye ta kurawa Alu ido tana kallonsa, karamin yaro ne amman Ubangiji ya hore masa baiwa da fasahar sarrafa zance da kuma wayo.
Ihun dariyar Lanto da yaranya ya kara dauke mata hankali ta waiga ta kallesu da mamaki, bata san me ta tsarewa mutanan nan ba, tun yaran Suna kanana ta iso gidan a mazaunin amaryar mahaifin su, amman har zuwa girman su ba su taba bata mutunci ko girma na sakan guda ba, hakan yana kona mata rai, tsahon zaman ta a gidan nan shekaru kusan goma sha shida ya kamata ace ta sami wannan darajar, riko hannunta da aka yi ya sanya ta waiga da sauri.
Alu ne yana nurmushi ya nuna mata
tukunyar da ke kan wuta “Inna kalli ta tafasa tukunyar, na miki talgen?
Lanto da yaranta suka kuma kwashewa da dariya, Amman Sumaye bata kula su ba ta kalli Alu tana kokarin nanata masa abin da ta gaya masa tun da fari. “Ina bukatar saiwar nan Mai sango maza je ka amso mini.”
Alu ya ɗaga idon sa ya kalli sararin samaniya inda hadari ke kara haɗowa, sannan ya kalli murhun mahaifiyarsa, ya maida dubansa kanta, ta fahimci abinda yake kissimawa a zuciyarsa amman bata bari yayi ƙoƙarin furtawa ba ta katseshi ta hanyar ƙara jajjada abin da ta faɗa tun farko.
Alu ya ɗaga kan shi alamar to, sannan yayi hanyar fita da gudu, Lanto ta bishi da kallo gami da rike haba tana kada kai.
“Tabbas idan kana wannan duniya zaka ga abubuwan mamaki da zaka gaza cewa komai, ban ta6a ganin irin wannan rayuwar ba bayan a gidan danke ciki ba, ɗa namiji daya kasance haramun ayi mu’amala da shi shine abin ja a jiki tamkar ɗiya mace? Tayi kwafa tana hararar sashin da Sumaye take.
Sumaye bata kula ta ba ta nufi gurin da garin tuwon ta ke ajiye ta dauko ta fara zubawa cikin k’warya, daman tana da ruwanta cikin kwatanniya don haka ta isa gurinta ta d’iba ta fara k’ok’arin talga tuwon, dukkan abin da lanto ke fad’i na habaici da k’azafi akan kunnenta har dariyar da yaranta keyi, can kasan zuciyar ta tana tausayin lanto domin tana ganin aibun koyawa yara musamman mata irin wad’an nan halaye da su daza su kasance gidan wasu, amman tasan rashin sauraran rediyo ke sanya Lanto yin komai.
Sumaye bata kasance mai ilimi ba, domin garin su babu wasu makaramtu na islamiyya dana addinin idan ka d’auke wata makaramta allo dake ba hayin garin su wacce sai an tsallaka ruwa ake zuwa, kasancewar su mata subasa zuwa wannan makaranta sai dai tsoffi masu karantun tsakar d’aki kan shiga gida-gida suna koyar dasu, da zarar an yiwa yarinya aure kuma shi kenan sai dai ta mai da hankalin ta ga bautar gidam ijin ta maganar karatu kau ta kare, sai ta fara girma ayyukan gida sun ragu, amman ita sumaye tana da kwakwar jin rediyo wacce ta tara kud’i da kyar ta siya, kusan itace mace ta biyu dake da rediyo a garin, sau da dama zakaga mata sun zagayeta suna jin rediyo, amman bata fiye samun damar kunnawa kasancewar babu hanyar siyan batiri sai an shiga babban gari ko binni wanda tsananin su da babban kauyen da suke hauwa motar daza ta sada su da binni kusan tafiyar kilomita uku ce, don haka sai ranar kasuwa ake samun siyo mata batirin idan tana da kud’in a hannunta.
Sumaye ta kammala talgen ta fara zubawa cikin ruwan da ke tafasa tana juyawa da muciya aka fara yayyafi, Lanto da yaranta suka tashi da gudu suka shige cikin dakin su wanda ya kasance na kasa suna dariya.
Sumaye tayi tsaye cikin damuwa, ta daga kai tana kallon ruwan, wanda ya fara saukar mata akan fuskarta, ta maida dubanta ga karan data sanya cikin wuta, ruwa ya fara sauka akansa kad’an-kad’an, duk ida ruwa ya ta6a wutar gurin ta mutu, idamuwan ta suka kawo kwallo tausayin kanta da irin faɗan da malam Belɗo zai yi idan ya dawo bata kammala tuwon dare ba ya bijiro mata, ta durkusa ta fara kokarin maida kararan tana hurawa, yayyafin bai karu ba bai kuma ragu ba, amman wutar bata mutu gabad’aya ba, hakan ya bata kwarin gwiwar cigaba da yin abin da take yi.
Kamar an wurgo shi sai ga Alu ya dawo da gudu cikin gaggawa, rigar dake jikinsa ‘yar shara ta yadin dan madima ta jike da ruwa sharkaf, ta kalleshi da mamaki bakinta a bud’e.
“Maisango har ka dawo? Ya daga kai yana haki “na dawo inna, acan baki ga ruwan da akeyi ba, amman nan ba’ayi da yawa. Ya mika mata sassaken dake hannunsa wanda babu ko leda a jikin sa. “Gashi tace tana gaisheki.”
Sumaye ta amsa tana murmushim jin daɗin” allah yayi maka albarka, maza wuce d’aki kada ruwan ya kara jika ka. Alu ya kad’a kai “Inna kije d’aki kizauna ki huta tuda bakya jin dad’i, bari na kular miki da wutar kada ruwa ya jika ki ciwon ki ya tashi. Sumaye ta yi murmushi ta nufi hanyar d’akin ta, domin bata son hana shi aikin ladan da yayi niyya, a cikin ranta tana godiya ga ubangiji daya bata Alu.
Har zuwa sanda ta kammala tuwan daran ruwan nan bai tsuge ba, sai dai kamar jira ake ta kwashe cikin kwanika ta mik’awa kowa nashi ruwa ya kece, lokacin tana kwance akan gadon ta na karfe, tayi murmushi da godiya ga allah ya sanya sai yanzu ruwan ya kece.
Ta kai dubanta ga Alu wanda ya fara bacci yaci tuwansa ya ƙoshi ta yi murmushi, haihuwar ta takwas amman dukkamsu basu zama, wani wata uku yake ya mutu wani shekara, waini wata biyar, Alu kaɗai Allah ya bata wanda shine ɗana biyar cikin yaran data haifa, sai kuma kanne guda uku da suma suka rasu, shi kansa Alu bata ta6a sanya rai zai kai wannan lokacin ba, amman sai allah ya raya mata shi, domin an sha gaya mata tunda wabi takeyi baza ta samu d’an da zai rayu ba sai tayi haihuwa goma, amma ciki ikon Allah Alu ya rayu har tsohun shekaru takwas, hakan ya sanya suka shak’u, bata da abokin hira sai shi, kasancewar basu zaman jituwa tsakanin ta da kishiyarta.
Lanto tana daga cikin matan da ake labarin kishin su ciki garin san6auna, sannan shi kansa maigidan nata ya kasance mutum ma’abocin fad’a da saurin fashi ya sanya ta kasance cikin damuwa, domin babu wanda zata gayawa abin da yake damunta, Alu shine wanda take zama dashi tayi hira taji dad’i, wanda hakan ya sanya kishiyar ta da yaranta tsangwamarta.
Yayan Lanto bakwai, maza uku mata hudu, mazan sune manya, don haka basu gidan an kaisu almajiranci, domin kusan d’abi’ar garin ce dukkan yaran su akan fita dasu binni yin karatu wanda aka fisani da almajiranci, sai matan suka rage a gabanta, babar cikin matan salame, itace mai shekaru goma sha hud’u, sai mai bi mata da take shekaru shabiyu sai ta ukun mai shekara biyar karamar shekarar ta uku, daga kanta bata kara haihuwa ba, hakan kuma bakaramin k’onatamata rai yake yi ba, don haka kullum cikin hanyar da zata samu ciki take, bayyanar wannan cikin na jikin sumaye ya tsaya aranta kwarai da gaske, har ya zamo bai barin ta bacci, ita da take burin ace yau Alu ya fad’i ya mutu kamar yanda sauran ‘yan’uwansa keyi amman sai hakan ya kauce sa6anin zaton ta kullum kara girma yake yi da kua k’aunar taimakawa mahaifiyar sa, wannan shine abin da keci mata tuwo a k’warya, sai kuma wannan cikin na jikin sumaye, wanda bata san me za’a haifa ba.
Rayuwar gidan mai mutuƙar wahalar ce, domin mai girki ita zata yi surfe ta daka garin tuwan ta d’ebo ruwa a rafi sannan tayi girkin, don ma girkin sau d’aya ake yi tak, shine tuwan dare, shi za’a ci da daddare sannan a dumamashi da safe, sai kuma aci da rana idan yayi saura, idan kuma bai yi saura ba sai mutum ya nemarwa kansa abin da zaici da yaransa, kamar tafasa ko sauran kayan anfanin gona idan lokacin sune, idan kuma ba lokacin su bane ba, sai mace ta daka fura kamar ta sati guda suna damawa da ruwa suna sha, kusan wannan itace al’adar dukkan mutanan garin, domin babu wadatar arzik’i a garin bayan noma da kiwo.
Rayuwar dukkan matan garin tana cikin wahala, domin tsakanin mace da miji shine yayi noma ya kawo mata danyan abinci, ita zata sissika abin da za’a dafa sannan ta daka kuka ko kubewar miya, ita zata samarwa kanta daddawa da gishiri da manja da barkono wanda sune kayan hadin miyar kawai, lanto bata da matsalar samun duka wad’an nan abubuwan kasancewar tana da ‘ya’ya mata da takan dora musu talla musamman a bangaren sumaye abin ya kan zamo mata mai wuya, hakan ya sanya take amsar surfe ko wani abin da ta san za ta samu kudin da zata sai waɗan nan kayan, maganar sutara ma ba su santa ba, daga kayan lefe sai kuma idan mace ta haihu mijin yayi mata zanin goyo.
Kamar kullum yau ma haka sumaye ta kwana juyi bata iya bacci domin nauyin cikin dake jikinta, tana kai kallonta ga Malam Belɗo dake baccin shi a baban gadon ƙarfe wanda ya zamto na shi shi ɗaya, shi kuma Alu yana kwance akan ƙaramin gadon, ita kuwa tana zaune bisa tabarmar karauni ta jingina jikinta da garun ɗakin, haka nan rayuwar ke zuwar mata ko da yaushe musamman idan tana da ciki.
Amman akwai wani abu dake damun ta cikin ranta, hakan ya sanya duk lokacin data kalli Alu sai idon ta ya cika da kwalla, kullum tayi sall tana addu’a akan wannan abin dake yawo cikin ranta game da ɗanta, ta mike tsam daga inda take ta taka da kyar kasance kafarta akwai kumburi, takai dubanta ga maigidanta Malam Belɗo, sai ta ƙara kai kallon ta ga Alu ta isa kusa da shi ta zauna ta kura masa ido, sai ta sanya hannunta bisa goshin sa ta fara addu’a tana tofawa a hannunta tana shafa masa, duk da bawani ilimin kirki gare ta ba, amman ta ji a rediyo ana cewa ka yi addu’a da abin da ka iya, don haka fatiha da kulhuwallahu sune abin da tayi, sutake yiwa yaronta addu’a dasu kullum.
Ta jima tana yi masa addu’a, amman bata san mai ya sanya yau zuciyar ta ke rawa gabanta ke fad’uwa akan yaron ba, tana jin kamar zata iya mutuwa ta barshi, tana jin kamar yaune dare na karshe da zasu kara rayuwa tare, tabbas wannan cikin dake jikin ta yana daga cikin dake bata wahala kwarai da gaske a rayuwarta, sannan shine cikin da ya daɗe a jikin ta har ya wuce ƙa’idar sa, idan ba taba bata lissfi ba kusan watanshi goma shadaya kenan yana jikin ta, haka ke sanya hankalin ta tashi a duk sanda ta tina halin da Alu zai iya shiga bayan bata duniyar ko kuma d’aya tinanin da yafi damunta cikin ranta, sai wajan gefen sallar asuba ta sami bacci ya ɗauke ta, shima ba mai daɗi ba, domin tanayi tana farkawa.
SABO TIRKEN WAWA
Tun da gari ya waye Sumaye batajin dad’in jikin ta, dukkan abin da ta ke yi rfin hali takeyi amman bata jin dadin…