Page 68
Da fari saboda dagewa da neman magani, Adam ya ɗan samu sauƙi, dan ya kammala karatu ma, ya samu aiki a hukumar DSS, kuma ya shiga aiki da ƙafar dama.
Yanayin larurar Adam, da abubuwan da suka faffaru da shi, ya sanya mai martaba yake matuƙar jan sa a jiki, da kwantar masa da hankali, haka zalika turaki da galadima, iyayen nan maza duk suna ƙaunarsa, kusan halinsa ɗaya da mahaifinsa, amma har ya fi babansa taurin kai wasu lokutan, amma akwai ɗa’a da ladabi.
Hakan bai ishi Mummy ba, ta din ga bi wurin matayensu, tana ɓata Ammi da ƴaƴanta, da har sai da wasu suka fara jin haushin Adam a cikinsu.
Bayan auren sa da Aisha, ciwo ya cigaba da tashi lokaci zuwa lokaci, sannan kamar yadda ammi ta din ga yi, haka Aisha ta din ga ɓari, ciki ba ya zama a jikinta, ga ƙannensa suka sakata a gaba, su je har gida su yi mata rashin hankali, su ci zarafinta ga Samha ma a gefe ta sakata a gaba, da makirci da sharri kala. Sannan still daga can gida mahaifiyar su samha ma, ba ta ƙyaleta ba da sharri, da haɗata da Turaki, wai ba ta ɗauke ta uwa ba, komai sai dai ta yi ita da giwar galadima.
Idan Aisha ta samu ciki, da zarar zai zube, sai ta yi magafrki da adam, yazo mata da dogayen haƙora, da kuma farata ya kafa kai a mararta, sai dai da safe ya tashi da zubar da jini.
Adam bayan shigarsa Dss akwai cakwakiya daban-daban, sai dai ya tsaya kai da fata a kan gaskiya, ba ruwansa da cin hanci, da shi da Jamil suka shiga aikin, amma ya fi Jamil karatu, dan haka rank ɗin sa ya fi na Jamil.
Akwai aiki da ƙoƙari, hakan ya sanya shi zama sannane, mussaman da yake kama da mahaifinsa sosai.
Bashi da aiki bankaɗa, da tonawa mugwayen ƙasa asiri. A tone-tonensa, ya tono Usman wakili, da irin yadda yake yi wa ƙasa ɓarna, ya sako shi a gaba, a hukumar wasu suka goya masa baya wasu kuma suka ƙi.
Ba ƙaramin ragewa wakili mutuncin yayi a idon mutane ba, ya cigaba da fafatawa, amma aka ƙi bashi goyon baya, a hukunta wakili. Shi kuma yaƙi sakin aikin, ya cigaba da bin diddigin sa, babu irin jan kunnen da ba a yi wa Adam ya ƙi ji.
Ya koma ya bankaɗo wata tawaga, da suke yi wa kansu laƙabi da SMOKE, sai dai an kasa gano suwaye a ƙungiyar smoke, sai dai ana ganin miyagun ayyukansu, duk wani shige da fice na miyagun kwayoyi, da makamai ta hanyar da ba ta dace ba, suna da hannu a ciki, za kuma kaga tambarinsu na hayaƙi, an rubuta THE SMOKE.
Bincike a kan Smoke, ya sanya ya sararawa wakili, bai kuma waiwayar wakili ba, sai da ya ji ƙishin walili zai tsayar da ɗan sa takarar senator, shi kuma za a ɗauke shi vice president, su yi takara, da ɗan takarar da zai tsaya shugabanci ƙasa.
Wannan dalilin ya sanya, Adam sake saka wakili a gaba a karo na biyu.
Nan da nan sunan Adam ya shahara, shi ma ya haɗa tasa tawagar, da lauyoyi, da ma’aikatan Efcc, da ƴan jarida da suke da burin yi wa ƙasa aiki saboda Allah.
Iman kuwa tun kan ta kai shekaru goma, take samun masu cewa suna riƙo.
Iman tana girma samari kamar me, nan ma Mummy ta ƙwafe a ranta, ya sake mayar da jita-jita a kan Iman sabuwa dal. Na cewa shegiya ce ba wanda ya san iyayenta.
Saurayin babbar ƴar Mummy, Surayya, Wambai ya haɗata da wani babban mutum, amma yana ganin Iman ya ce shi nan duniya wannan jar yarinya yake so.
Ƙarshe dai aka yi biyu babu, Surayyan ta yi aure, amma Mummy ta kai sunan Iman wurin bokansu.
Manyan mutane duk wanda ya ce ya na so, sai ace masa shegiya ce, sai zance ya lalace, a ƴaƴan mai martaba, ɗaya shi ma ya liƙe Iman yake so, Mummy sai da ta yi dalilin da ya sanya, babar yaron ta hana zuwa da iman gidan. Yawan gorin da ake yi mata, ta daina shiga cikin mutane.
Ammi tana tausayin Iman, ga larura ga tsangwama.
Iman ba ta da wata ƙawa, kullum tana manne da Ammi, ko Nusaiba, sai kuma uwar ɗakinta Aisha matar takawa.
Duk wannan abubuwan, Ammi ba ta taɓa nunawa Mummy wani abu ba, kuma ba ta saka wa zuciyarta wai wani ne yake yi mata wani abu, kawai ta saka wa ranta jarabta ce daga Allah.
Sai dai har a lokacin Ammi ba ta daina son ɗan ta ya dawo gareta ba, ta kasa jurewa ta je ta sanar da wambai, dan Allah ya shiga lamarin gidansu, ya sasanta mata yaranta, ko Mahmud ba zai dawo hannunta ba, ya din ga zuwa in da take.
Wambai ya yi ta faɗa ya ce laifin Mummy ne, da ta raine shi a haka, amma ta nuna ita ba laifinta bane, yayi musu sulhu, amma suna zuwa gida, ta sake hure masa kunne.
Cikin ikon Allah, Iman kan ta yi candy, wani ƙanin abokin Adam ya fito zai auri iman, ɗan babban gida ne sosai da sosai, aka saka rana tana kammala sakandare ayi biki, ta cigaba da karatu a gidansa, dan Ammi ta fara tsorata da mazan da suke bin Iman.
Adam kuma shekara huɗu da aure, ciki ya gagara zama a jikin Aisha, ciki na ƙarshe da ta samu, Ammi suka yi shawara a kan Aisha ya je ta yi rainon cikin a saudiyya, wurin wani wan Ammi da yaki zaune a can shi da matarsa.
Ya ce karatu za ta tafi ƙarowa ƙasar waje, aka din ga surutu a kai, ya ce babu mai tsara masa rayuwarsa, tun da matarsa ce.
Iman kuma watan da za a yi biki, wanda zai aureta ya aiko a karɓar masa kayan aurensa wai ya fasa.
Hankalin ammi ya tashi, ta aika a tambaye shi dalili, iyayensa suka ce su manyan mutane ne a ƙasa, ba za su karɓi sirika da ba ta da asali ba.
Ammi ta sha kuka, laila da ba ta ƙasar ma, abun ya baƙanta mata rai, ta cewa Ammi visa za ta yi wa Iman, a tura mata ita can, Ammi ta ce ba mai rabata da ƴar ta sai mutuwa ko aure.
Ammi ta yi shawara da baba uwani, a kan ta bata shawara ko ta roƙi Mahmoud ya auri Iman, dan ta lura wannan mugun tabon da Mummy ya yi mata, ba zai bari ta auru ba, baba Uwani ta ce ai ita babarsa ce, dan haka bakomai.
Daga nan ta kwashe ta je ta gaya wa Mummy.
Ammi ta keta billenta, ta je ta samu Mummy, ta ce mata dan Allah ta na son yin magana da Mahmoud, ta ce mata za ta turo shi.
Sai dai kan ya je, Mummy ta zauna ta kitsa masa, tare da sauya masa tunani.
Ammi ba zata iya tuna rabonsa da sashinta ba.
Ta roƙe shi Allah ma’aiki, ya auri Iman, ko ita kaɗai ce alfarmar da zai iya yi mata a rayuwa a matsayin ta na mahaifiyarsa.
A take ya ƙeƙashe ƙasa, ya cewa Ammi shi ma ba zai auri ƴar da ba ta da asali ba. Baƙin cikin abun da Mahmud ya yi mata, ya sanya ta kamu da hawan jini, saboda ta yi kuka ba kaɗan ba, ta shiga damuwa.
A lokacin Adam ya je umara, ya ga Aisha, cikinta ya girma sosai, ana ta addu’ar Allah ya sa ta haife shi lafiya, bayan ya dawo ya samu labarin, abun da ya faru tsakanin Mahmud da Ammi, ya din ga yi wa ammi mitar meyasa za ta roƙi Mahmoud ya auri Iman, ita kuma gani take ba ta da wata mafita sai wannan.
Ammi sai da suka kwanta da Iman a asibiti, dan ta so Al’amin saurayin da ya fasa aurenta, haka zalika ta so ta samu Mahmoud, duk da yana cikin waɗanda take bala’in jin tsoro, saboda dukan da yake yi mata da hantara idan sun haɗu.
Kuma zance ya fita a dangi, Giwa ta na neman kai da shegiyar ƴar ta, taƙi auruwa, kuma ta karya billenta ta nemi alfarmar ɗan ta, yaƙi yi mata.
A zahiri za ka ga ammi kullum cikin fara’a take, amma ƙasan zuciyarta, tana cikin damuwa da tashin hankali a kan iyalanta.
***
Gaba ɗaya jikin rumaisa ya yi sanyi, ta rungume Iman da take ta sharɓar hawaye, ta rungumeta ita ma ta fara kukan, ta kasa rarrashinta.
Sai da suka yi mai isarsu, danna rumaisa ta din ga share mata hawaye ta ce “Ki yi haƙuri Anty iman, tun da dai ammi ta san iyayenki, meyasa za ki damu dan an ce miki baki da iyaye? Ki fuskanci rayuwarki kawai, kuma in Allah ya yarda zaki auri miji na gari, wanda zai kula da ke, ki daina kuka”
Ta yi maganar tana sharewa iman hawaye, Nusaiba ta yi sallama a ɗakin, suka amsa, ta ɗan yi turus tana kallonsu, yanayinsu ya nuna mata akwai wani abu, amma ta share, ta ƙarasa ta ɗau Sabir da ya yi barci, ta fice daga ɗakin”.
Jabir kuwa rai a ɓace ya koma ɗakin Ammi, ya dubi ammi ya ce “Ammi, dan Allah idan ban takura miki ba, ina son mu yi magana ne”.
Ammi ta ce “To” ta tashi ta bar ɗakin, Adam ya bi su da kallo.
Falonta suka koma, Ammi ta ce “Ya aka yi ne?”
Ya ɗan sunkuyar da kansa ƙasa, sannan ya numfasa ya ce “Ammi wani abu ne ma daɗe ina son in gaya miki, amma na kasa ban sani ba ko zaki bani dama”.
“To ni ɗin baƙuwar ka ce? Faɗi ina jin ka”.
“Dama..dama game da Iman ne Ammi, dan Allah idan babu wani a ƙasa yanzu, ni a bani mana, ina son ta”.
Ammi ta ce “To fa! Babbar magana, ya aka yi ba ka gaya mini tun da wuri ba?”.
“Ina jin nauyi ne Ammi”.
“To meye na jin nauyin ban da abunka, ka san yanayin da take ciki, ta daina saurarar kowa ta daina bawa kowa dama tunda abubuwan nan suka faru, amma na yi mamakin da baka taɓa faɗa ba”.
“Ammi Iman ai ƙanwata ce, na daɗe ina ɓoyewa ne, yanzu kuma na ga yakamata na faɗa, wataƙila dama rabona ce”.
“Haka ne, amma ka san dai case ɗin da yake kanta, kuma babu lallai hajiyarka ta yarda, na san ba za ta amince ba”.
Jabir ya ce “Ammi zan shawo kan ta, in dai kin amince shikenan, idan har ba a cikinmu ba, haka zamu zauna mu cigaba da zuba ido, kowa ya zo ya fasa, Saboda wani dalili mara tushe, ina ga ni ɗin na fi dacewa, na san abun da yake faruwa da ita”.
Ammi ta ce “Na yi farin ciki sosai Jabir, Allah ya tabattar mana da alkhairi, ai kai ɗana ne, na gode da ƙoƙarin share mini hawaye ni da marainiyar Allah, Allah ya biya ka”.
“Amin Ammi, na gode sosai, ina ga zan yi wa mai girma wambai Magana, a nema mini aurenta, zan yi ƙoƙari ya shawo kan Hajiyata ma”.
“To, Allah ya ji she mu alkhairi, ya sanya albarka na gode sosai” Ammi ta ji tamkar ya yaye mata kaso mafi rinjaye na damuwarta.
Da ta koma wurin takawa, ya kalleta ya ce “Ya dai na ga kina fara’a?”
“Ina ruwanka?”
Yayi murmushi ya ce “Tuba nake”.
Ta zauna ta ce “Kai ban gaya maka ba”
Ya tattara mata hankalinsa.
“Laila za ta shigo cikin sati Mai zuwa”
Ya waro ido ya ce “Yanzu muka gama magana a waya, amma ba ta gaya mini ba”.
“Oho muku dai”.
“To ta koma ba ma so, ba ta zo lokacin rasuwar aisha ba, ba ta zo ta ga ɗan ta ba, na yi aure ba ta zo ba sai yanzu?”
Ammi ta ce “Ai ka san yanayin aikinta a can, amma ta ce za ta daɗe sosai idan ta zo, yaran ne za su koma da wuri, tare da babansu idan ya zo, shi sai next month in Allah ya kaimu zai zo”.
“To Allah ya kawota lafiya, gashi ni zan yi tafiya. yauwwa Ammi, mai girma turaki ya kirani, ya ce mini mai martaba ya tura mu wakilcin taro, kuma da na dawo zan je course ɗin nan ta watanni shida, kin ga ba zan wani daɗe tare da ita ba”.
“To sai ta zo ɗin dai tukuna”.
“Ammi, ina Jamil ne? Ban ƙara ganinsa ba fa, tun da ya tafi ɗaukko Rumaisa”.
Ammi ta ce “Ni ma dai na yi mamaki, ka san da ta zo ta ce wai ƙin hawa motar ta yi, saboda ta san yana jin haushinta, ina ga saɓani suka samu, ya ji haushi, mukullin motar ma, Sidi ya bawa ya kawo”.
Yayi ajiyar zuciya ya ce “To ai ba da ni suka yi ba, ni kaina ba na son surutun nan na ta, ita ba ta iya kara ba ko kaɗan”.
“Ai ƙuruciyar kenan, sai dai ayi ta sakata a hanya, ni maganar da ta faɗa ne a kan Jamila, nake jin tsoron kar ta koma kunnenta, bana son tashin hankali da masifarta, in da na gode wa Allah ma, ba a gaban wani ta faɗa ba”
Takawa ya ce “Ina tsoron wannan bakin na ta a cikin masarautar nan, sai dai Allah ya shirya”.
Can ɗaki kuwa, suka gama koke-koken su, ita da Iman, kamar wata babba haka ta yi ta rarrashin iman.
Can Iman ta ce “Anty rumaisa ba zaki kira mai sunan baba ki yi masa godiya da ya ya je gida ba?”.
Ta yamutsa fuska ta ce “Godiyar me kuma?”
“Dubiya da ya zo mana”.
“Ba ki san halin gayen nan ba, ba lallai ya gode, kina ganin yarfani ya yi dan na ce zan raka shi, wai na je na kula da mijina, yanzun ma zai iya yarfa ni”.
Iman ta ce “Ba haka bane, yakamata ki yi masa godiya, idan yana gida ma sai ki gaisa da su mama, ko yana zama yayi dare a waje?”.
Rumaisa ta kalleta ta ce “To mai sunan baba da mace ne, da an shigesu, ba shi da wasu abokai fa, daga makaranta sai kasuwa, sai gida, su wani ball su wani abubuwan abokai, ko yawo duk ba ya yi, da dai yaya usy ne ko gadanga na mama yaya Aliyu, mama da kanta take fita yawon nemansu wataran”
Iman ta yi murmushi ta ce “Kowa da halinsa kenan, ga wayar ki kira shi”
“Sai dai ke kira shi”
“In kira shi in ce masa me, na gaya miki ya ce na daina kiransa”.
Rumaisa ta ce “Gaskiya idan na kira shi, ya yi mini wulaƙanci sai na rama a kan ki”.
Iman ta bata wayar ta ce “na yarda”.
Sai da wayar ta kusa katsewa sannan ya ɗaga, alhalin wayar na hannunsa, yana kallonta, ya din ga fatan Allah ya sa muryar iman zai ji, ba ruma ce ta kira ta dame shi ba.
“Hello mai sunan baba”
Sak yayi da ba Muryar iman ya ji ba.
“Ya aka yi?”
“Amm dama, kiranka na yi na ji ya ka je gida, na gode sosai”
“Yayi” ya faɗa a taƙaice yana ƙoƙarin kashe wayar.
Ruma ta ce “Dama Iman ce ta ce, na kira ka na tambayi ya ka je gida?”
Da sauri Iman ta ce “Kai Anty rumaisa” ta yi maganar tana karɓe wayar ta kashe.
“To me na yi kuma?”.
Cikin shagwaɓa iman ta ce “Meyasa zaki gaya masa haka, kar ya zaci wani abun fa”.
“Wani abu kamar me?”
Iman ta ce “Bakomai” ta tashi tsaye ta ce “Ki kwana a kan gadon, ni sai na kwana a kan katifa a ƙasa”.
Rumaisa ta kwanta ta ce “Ai ba kara zan yi miki in ce a’a zan kwana a ƙasa ba” Iman ta yi dariya, ba ta sake cewa komai ba, ta yi shirin baccinta ta kwanta.
Har kusan ƙarfe biyun dare, rumaisa idonta biyu, rabon da ta ci karo da abun da zai hanata bacci, tun farkon shigarta hannun kidnappers, daga baya kuwa baccinta take yi, sai lokacin da ta kuɓuta da Sabir.
A hankali ta tashi zaune, ta na jin kanta duk ya yi mata nauyi, tausayin wa ma yakamata ta ji ne?.
Ta kalli in da iman take barci, ta girgiza kai ‘Allah sarki Iman, a yadda ki ka bani labari ke yanzu gaba ɗaya ba ki da uwa ba ki da uba, sun rasu ba zaki taɓa ganinsu ba har abada, ba a san in da za a ga dangin su ba, ba ki da wa ba kuma ki da ƙani ga larura. Ashe ni kukan daɗi nake, na ban san babana sai a hoto, wannan ke ce marainiya.
Allah sarki ammi, ashe da gaske mama take da take cewa aure ɗan haƙuri ne, ni na zata kawai abinci ake ci ayi bacci, amma a ƙwace mini ɗa a bawa kishiyata, wallahi sai dai ayi masifar da za ayi kowa ya huta.
Ga ɗan ta ba shi da lafiya, ɗayan kuma an raba shi da ita, kamar yadda dai mama take sonmu a ƙwace mata ɗaya daga cikinmu, ko kuma kamar ni a ƙwace Sabir ya auri ƙanwar anty aisha ya bata. Kam bala’i wallahi da sai dai kowa ya rasa’.
Ta dafe kanta, abubuwan ba da ita suka faru ba, amma ta ji sun dameta, ammi tana da kirki fiye da tunani, amma meyasa aka tsaneta?.
Ta tashi ta sauka daga kan gadon, ta zauna a ƙasa ta yi shiru, abun duniya duk ya dameta, ƙarshe a nan ƙasa ta yi bacci.
Mai sunan ba tun da ruma ta ce masa Iman ce ta ce, a kira shi, yake jin wani irin nishaɗi a ƙasan zuciyarsa, dan ƙoƙari yake ya hana hakan tasiri a zuciyarsa, dan yaƙi yadda ya sallama cewar ya faɗa soyayya, haryanzu tantama yake yi.
Da asuba bayan sun yi sallar asuba, rumaisa ta je ta gaida ammi, ta tarar da ammi na salla, ga sabir ya farka, yana kuka. Ta hau kan gadon, ta ɗauke shi, ta bashi ruwa ta kwantar da shi ta hau yi masa wasa, daga haka kuma suka yi bacci gaba ɗaya.
Wajen ƙarfe bakwa, ammi ta tashi rumaisa, ta ce ta je ta yi wanka, ta shirya ta je ta duba takawa da ya kwana a ɗakinsa, ta zo a kaita makaranta.
Gaba daya ba ta sanya ran zuwa makaranta ba, a zaton ta tun da bashi da lafiya, ba bu zuwa makaranta.
Ta je ta yi wanka, ta karya, sannan ta tafi ɗakin nasa.
Ciwon kwana ɗaya, amma idanunsa sun yi zuru-zuru.
Ta ƙarasa kujerar da yake zaune, sanye da ashe ɗin jallabiya ta ce “Sannu ka warke?”.
Ya kalleta ya ce “Ina kwana?” Gatse yayi mata, amma cikin ko in kula ta ce “Lafiya ƙalau, ya jiki?”
Jawota ya yi ya zaunar da ita, ya tsura mata ido sannan ya ce “Baki san gatse ba ko? Ban isa ki gaisheni ba?”
Ta ce “Auu, wai dan ban gaishe ka ba, na ɗauka kawai gaisheni ka yi, to ina kwana?”
Yayi shiru bai amsa ba yana bin ta da kallo.
“Ai ka ga matsalar, mutum ya gaisheka, ka ƙi amsawa wai sai an yi maka irin taka”. Bai ce mata komai ba ya cigaba da kallonta.
“Barka da wannan lokaci ranka ya daɗe, na sameka lafiya?” Ta yi maganar tana risunar da kai, kamar yadda ake yi masa.
“Ki tashi ki je, sidi zai kai ki makaranta”.
Ta tashi ta amsa masa da to, tayi waje.
Sai dai a harabar gidan, ta haɗu da Mahmud, yana shirin fita.
Gaisawa suka yi, ya ce “Ya mai jiki?”.
“Ai ba zan amsa ba, sai ka je ka duba shi”
“Anya zuwa dubiyar nan kuwa? Taho mu je in kai ki makarantar, ya sunan makaranta”..
Sunan kawai ta gaya masa ya gane, ta buɗe motar ta shige.
Sidi ya taho da sauri, ya ce “Ranka ya daɗe, jiranta nake giwa ta ce zan kaita makaranta ne”.
Mahmud ya ce “Mayar musu da mukullin, zamu tafi tare” ya ja motar suka tafi.
Suna tafe a hanya, tana zuba masa shirme, yana biye mata.
Can ta ce “Kai ina son mama a rayuwata daddy, a duniya bayan Allah da Manzonsa, ba abun da nake so kamarta, dama ban san babana ba, amma mama dai kam, Allah ya tsundumata a aljanna. Allah ya bani abun da zan shagwaɓa ta, in ta sai mata abubuwa”.
Ya ce “Amin, sai ki yi ta mata biyayya da addu’a”.
“Ai ina yi mata, har da ammi ma dukkansu yi musu nake yi, mutane su yi ta hantarata wai ba na ji, har da yayanka ma hantarata yake yi wataran amma dai ya na da kirki wasu lokutan, idan na yi masa laifi sai ya yi mini banza. Ammi ka ga da mama da Ammi, da yayyena, da Anty Aisha da Sabir, da mai girma turaki, da gwaggo, da iya, da malam habibu na islamiyyarmu, da barde ɗan bindigar da yake bani abinci, da Bashir abokin takawa da ya tsinceni, da Iman kai duk wanda suke yi mini mutunci a rayuwa, kullum sai na yi musu addu’a da fatan alkhairi”
Ya ce “wonderful, gaskiya nima a taimaka a sakani a ciki”.
“Eh zan saka ka, amma kai wa ka ke yi wa addu’a, tsakanin Ammi da wannan matar?” Shiru ya yi jikinsa ya yi sanyi ya kalli rumaisa.
“Daddy, duk yadda nake son Sabir, da anty aisha na raye, duk wahalar nan da na sha, ba shi da kamarta, kuma dole ne ya bita, to kamar haka ne fa, kai da wannan matar, duk rashin ji na, Mama sai dai ta yi ta cewa Allah ya shiryeni, amma kai har ka saka Ammi ta yi maka kuka, kana da kirki amma ita ba ka yi mata meyasa?”
A dai-dai nan, ya iso ƙofar makarantar su, bai amsa mata ba, yayi shiru.
Ta ce “Yauwwa, ya batun baba uwani, ta je kuwa?”
Ya girgiza mata kai ya ce “A’a, kuma ban ji mummy ta yi maganar ba, ina ga ba ta kai ga faɗa mata ba”
Ta buɗe motar ta ce “Shikenan sai an jima, na gode sosai Daddy” ta nufi cikin makaranta.
Sosai maganganun rumaisa suka ratsa shi, baya samun wanda zai din ga tattauna maganar nan da shi, yana ji a jikinsa abubuwan nan da suke faruwa, tamkar juya sama ne a ƙasa, gaba ɗaya abubuwa basa tafiya daidai, amma jin sa yake, tamkar an ɗora masa dutse, kuma kamar a cikin wata kurku yake da ruhinsa ya kasa samun salama.
Ranar da ammi ta zubar da hawaye, saboda ya ƙi auren iman, ji yayi kamar zuciyarsa tana ci da wuta, ya daɗe yana ganin abun a idonsa, amma ya ji farincikin mummy shi ne a gaba, dan haka wannan bakomai bane ba.
Sosai Adam yake masifa, jin wai mahamud ya ɗauki rumaisa zai kaita makaranta.
“Takawa, ka sakawa zuciyarka salama, dan Allah ka yi haƙuri mana”.
“Ammi kin san ba shiri muke ba, idan ya kitsa mata wani abun fa? Ko ya bugi cikinta ta saki baki tana zuba, meye haɗinsa da matata? Yarinyar nan ba cikakken saiti ne da ita ba, kar a cutar da ita*.
Ammi ta ce “Kana da gaskiya, amma na ga ta su ta zo ɗaya, in sha Allah babu wani abu da zai faru, tun da ka ji sauƙi ma, sai ku tafi amma dan Allah kar ka ce zaka yi faɗa, kaga ba ka da cikakkiyar lafiya. Kuma ka sani ko a dalilinta komai ya dai-dai ta tsakaninka da ɗan uwanaka?”
Kallon idon ammi yake, tuni har hawaye sun cika mata ido.
“Shikenan ammi, ba zan yi magana ba, ki yi haƙuri, amma dole in raba shi da iyalina”.
***
Da aka tashi daga makaranta, Adam ne ya zo ɗaukar ta, saboda ya ji sauƙi sosai, ciwon bai kuma tashi ba.
Tana ganinsa ta hau dariya “Ka warke ne ka zo da kanka, da adaidaita sahu zan hau na tafi ai”.
Fuskar sa babu walwala, yayi mata banza, ya ja motar suka tafi, sai dai ta ga ya nufi gidansu, maimakon na Ammi, ganin ya na ta cika yana batsewa, ya sanya ba ta kula shi ba, ta cigaba da harkokinta.
Ko da suka je gida, su Asiya suka din ga yi musu sannu da zuwa, suna yi wa Adam sannu, dan baba uwani ta gaya musu, maigidan ne babu lafiya.
Ya wuce ɗakinsa ta wuce nata, ta yi wanka, ta kwanta baccin da ba ta samu yi jiya ba.
Sai da aka yi la’asar, sannan ta tashi, taje kitchen ta haɗa shayi, ta zuba madara fal da milo, ta dafa ƙwai ta ci abunta, sannan ta ɗau littafinta, ta tafi ɗakin Adam.
Yana zaune a kan kujerar ɗakin sa, yana dudduba wasu takardu, ta yi sallama ya amsa mata a ciki, ba ta damu ta je gabansa ta tsaya, ta ce “Albishirinka?”
Ya kalleta ya ce “Ya aka yi?”.
Ta nuna masa littafinta, na assignment ɗin da ta yi, ta zana malaminsu, ta ci 10/10.
Ya ɗan kalli littafin da mamaki, sannan ya kalleta, alamar yana jiran bayani.
“In gaya maka har malamin ya kirani gaban allo, zai yi disgracing ɗina, ya ɗaga littafin ƴan ajin suna dariya, ya tambayeni da turanci wai meye wannan? Ni kuwa na ce ni ban iya ƙirƙirar komai ba, amma idan malamai suka yi kyau kamar zanen nan nawa, to za a samu ɗalibai masu ƙoƙari da tsara zane kamar nawa, koma fiye da nawa, Aikuwa aka dinga tafa mini,ya ka ji azancin nawa”
Ɗan murmushi gefen baki ya yi, dan ya fuskanci ita fa dan kana fushi da ita, kai ta shafa.
Ya ce “You try”.
“Yauwwa, sai ka saya mini kyauta, teddy bear nake so, da kuma ƴar tsana babba, sai lunch box ɗina”
Yayi mata kallon ba zaki girma ba.
“Ya naga kana kallona?”
“Mahmud, Alaƙarki da shi bana so, kar ki kai ni bango a kan haka”.
“Wai meyasa zaka saka ni a cikin faɗa ku? Ni meye nawa yana yi mini kirki, shikenan dan kuna faɗa nima sai na din ga jin haushin sa. Jamil, Jabir, Samha alaƙar ka da su bana so, Jamil da Samha, sun wahalarsa da matarka, su meyasa ba ka gaba da su?” Ta yi maganar tana tsare shi da ido.
Rasa bakin magana yayi, duk yadda kake tunanin rumaisa ta wuce nan, a zahiri tana da ƙuruciya da wauta, but she have a very sharp brain, ba shi da amsar bata a yanzu dan ta ƙure shi.
Amma saboda kar ta ga ta yi nasara ya ce “Ni ne shugaba, a gaba nake da ke, dan haka duk hukuncin da na yanke dole ki bi”.
Ta ɗau littafinta ta ce “Babu biyayya ga abokin halitta wurin saɓawa mahalicci, duk daƙiƙancina a makaranta, na san wannan, kuma Allah ya yanke rahamarsa ga mai yanke zumunta, Annabi ma ba ya tare da mai yanke zumunci, sai ka din ga jin tsoron Allah wurin yanke jiki kai ma” ta fice ta koma falo ta bar masa ɗakin.
Mintuna kaɗan ya fito ya fice daga gidan gaba ɗaya, ya dafe kanta ta ce “Na shiga uku wannan wane irin abu ne, anya kuwa zan iya, ni duk na gaji” tayi tsaki, ta tashi ta je ta ciko roba da gugguru, ta ɗaukko lemo, ta zo ta saka a gaba tana ci, tana kallon cartoon.
Hayaniya ta ji ana hawowa sama, ta tsaya tana jiran taga waye zai shigo?
Samha ce da Fauziyya, da kuma ruƙayya sai zee ƙanwar Samha, baba uwani biye da su, hannunta riƙe da foodflask.
Babu ko sallama suka zo suka zazzauna, baba uwani ta ajiye kwanukan, ta ja gefe.
Samha ta kalli rumaisa ta ce “An samu duniyar da babu a gidan tsoho, an yi ɗai-ɗai a katafaren gida, da duk dangi babu irinsa” rumaisa ta yi mata banza, ya cigaba da kora lemonta.
Ruƙayya ta ce “Allah wadaran naka ya lalace haryanzu ban ga technology a auren wannan busashiyar yarinyar ba, da ko rantsuwa na yi babu kaffara, ragowar masu garkuwa da mutane ce, sun gama lalata ta” ɗan shiru ruma ta yi tana tunanin, me take nufi.
Fauziyya ta ce “Ba wani technology, wulaƙanci ne kawai, dan Allah dubi Samha ki dubeta, ita ta isa ta kira kanta mace ma wallahi wannan ko a mai aikin samha ba ta isa ta zo ba, kalli bakin shegiya yadda take auna madara, saboda samun wuri, ga ƙirjinta fayau kamar faifai ba wata mamora, amma wai ita ya aura”.
Rumaisa ta yi gyatsa ta ce “Gidan miji daɗi, mussman irin gidan papa, auren mai kuɗi daɗi ba, na samu promotion, gida babu, na samu a gidan miji” tayi maganar tana lashe madarar hannunta.
Fauziyya ta ce “Ke dalla rufewa mutane baki, tashi ki kira mana ɗan uwanmu, mun zo duba shi”
Cikin tsawa rumaisa ta ce”Ba zan kirawo shi ɗin ba tun da ke ba uwata ba ce”
Samha ta ce “Ke, uban wa ki ke yi wa tsawa”.
“Uban duk wanda ya tsargu, ba sunana Aisha ba, sunana rumaisa Mahmud, ƙanwar maza, ku tambayi yayan naku wace ni, kawai ku zo ku cika mini kunne, wai ko a ƴar aiki ba zan zo ba, ai Allhan ba naku ne ku kaɗai ba, da ban zo a ƴar aikin ba, sai na zo a matar gida, antynku ce ni, tun da matar yayanku ce ni, ke kuma da ki ke cewa ke ce mace, na ji ni namiji ce, ni duk wadda ta yi mini, wallahi sai ta ci ubanta, babu wata barazana da tashin hankali da ban gani ba, dan haka ba zaku ɗaga mini hankali ba, ke kuma da ki ke cikakkiyar macen, kin san idan ki ka gama cikar, zubewa zaki yi ki fara tsufa, kin ga ni kuma a lokacin da ki ka fara tsufa na cika ko? Banza kawai”
“Ke! Kina ƴar matsiyata ni ki ke gayawa haka? Kina da hankali kuwa, waye ubanki a ƙasar nan, har ni ki ke cewa ubana zaki ci?”
“Eh na faɗa, sai na ci ubanki, da ke da duk wanda ya ce zai zageni, ƴan fashin daji ma, ba su razana ni ba, balle ku shashashai, gwalagwaje, marasa mutunci, idan tunaninku gayya, ku taron mata ne, ni kaɗai dai-dai nake da tunanin maza bakwai”.
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page : Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page : @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel: Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.